Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi. lumshe ido batul ta yi tare da ɗan jinjina mata kai, hawaye ne masu ɗumi suka soma gangarowa ta cikin idanuwan nata, nan take Angel taji gabanta ya faɗi, sai dai bata tambayeta hawayen menene ba, ta bari sai zuwa gobe su yi magana.

kasa tafiya tayi, komawa tayi daga gefen gadon ta ɗan zauna tare da duƙar da kanta saitin fuskar batul, ta manna mata kiss saman forehead ɗinta da cheek nata, a hankali batul ta ɗan ware idanuwanta tana duban Angel wadda tuni ta miƙe daga gefen gadon, sai da ta fara ɗaukar jamimah, kafin ta juya ta kwantar da ita saman gadon Danish itama ta kwanta daga gefenta tare da rungume jamimah a jikinta, sai kallon juna suke yi ita da batul da ke akwance saman gadonta, Da yake suna fuskantar juna.

Tsawon lokaci sunata ta kallon juna, ɗakin yai tsit baka jin sautin komai, sun ƙi bari bacci ya ɗauke su, gani su ke yi kamar in suka runtsa za'a ƙara zuwa a ɗauke masu ita, zuciyoyinsu a cike suke da tambayoyi iri iri da suke son su yi mata, idan gari ya ware, sun kwana da wadataccen farin ciki acikin zukatansu saboda dawowar ƴar uwarsu batul, kaɗan daga cikinsu ne suka samu damar tuntsawa.

❤PRISONERS💖

A washe garin ranar tun da sassafe, ta soma jin hayaniyarsu a cikin kunnanta, muryoyinsu da alamun farin ciki atattare da su, a hankali ta ɗan buɗe idanuwanta, biji biji ta fara ganinsu a kewaye da gadonta, har saida ta ɗan firgita, daga bisani ne idanuwanta suka dawo normal taga fuskokinsu a washe sai murmushi suke sakar mata, azeeza da ke a gefenta kwance, ta ɗan tada kanta saman gwiwar hannunta, ta ƙura mata ido sai kallonta ta ke kamar zata lashe ta.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah! Allah mun gode maka daka dawo mana da ƴar uwar mu batul, Nifa jiya da daddare dana kwanta, gabana ya dinga faɗuwa gani nake kamar in na runtse idanuwana zan farka inga babu batul ɗin mu" Deeja ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki.

Parveen tace"wlh nima haka naji araina, shiyasa yau da safe ina farkawa nai wuff nazo gaban gadonki don in duba in ga ko kina nan" ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskar batul, ta rasa akan wa zata tsayar da idanuwanta, sai faman jujjuya eye balls ɗinta ta ke yi akan faces ɗin su.

"Ni kaina da mafarkin ki na kwana, ƴar uwata rabin raina" da sauri ta wurga eye balls ɗinta kan fuskar Angel wadda zuwanta kenan, Tana agefen Hibba, wani murmushin ne ya ƙara bayyana akan fuskarta, wanda ke nuni da irin farin cikin da take a ciki.

"Fatan ba mu takura maki ba, mun tada ki daga bacci, wlh mun yi kewarki ne kamar mu zauce" acewar hibba, calmy ta soma magana"Nafi so ku takura min hibba, aini abunso ne a wurina, in gan ku atare dani, ko na minti ɗaya bana son wani a cikin ku ya nisanta dani, ba dan ƙaddara ta rabani da ku ba, ku kan ku kun sani, da ƙafafuwana bazan ta6a yin nesa da ku ba" muryarta na ɗan rawa ta ƙarasa maganar, tuni idanuwanta suka cicciko da ƙwalla, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta.

"Batul pls don't cry, idan har ba so kike zuciyoyin mu su raunata ba, mun fi buƙatar farin cikin ki ayanzu, ki daure pls," Deeja ce tai maganar, lumshe idanuwanta ta ɗanyi yayin da take binsu da kallo, su kansu sun fahimci akwai wani abu dake damunta.

"Azeeza irin wannan kallo haka, " daƙyar ta furta maganar, tana kallon azeeza, murmushi ta sakar mata tare da cewa"Ƙaunarki nake yi batul, dole in kalle ki don baki san irin kewarki da nayi ba. Kamar in haɗiye ki" tayi maganar tana wage bakinta, Hakan da ta yi ba ƙaramin dariya ta basu ba.

Ita kanta batul ɗin saida ta ɗan murmusa, a hankali ta yunƙura ta miƙe, itama azeeza ta miƙe zaune saman mattress ɗin, Saukowa ta yi daga saman gadon taci gaba da tafiya tana bin ɗakin nasu da kallo, ganin irin sauye sauyen da a ka yi mashi, gaba ɗaya suka bi bayanta suna tafiya atare da ita, dakatawa tayi da yin tafiyar tare da juyowa ta kallesu tace"Jiya na tambaye ku amma ba ku bani amsa ba, ina Danish dasu haris su ke ne"? Deeja ce tai ƙarfin halin faɗa mata cewa anzo an tafi dasu almost one week, An riga tafiya da Danish," iya abunda ta sanar da ita kenan, bata faɗa mata awani hali aka tafi da shi ba, jinjina kanta ta yi ba tare da tace komai ba, sai dai fuskarta ta nuna alamun damuwa, kuma idanuwanta hawaye ne acike dasu.

"An kawo mana sabbin prisoners ne? Jiya kamar naso inga wata ƙaramar yarinya," tai tambayar tana kallonsu "naga kuma sabbin gadaje, kusan goma sha biyar" yasmin ce ta bata amsa dacewa"Eh, bayan tafiyarki aka kawo su, Amma mutun biyar ne prisoners ɗin, sai dai daga cikinsu Giants sun tafi da mutun uku, yanzu biyune atare damu. jamimah itace ƙaramar sai Sarah," ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa"ku bani labari mana, dame dame ya faru bayan bana nan"? A taƙaice Angel ta sanar da ita duk wani abu da ya faru bayan bata nan sai dai bata faɗa mata wanda zai sanyata damuwa ba.

"Mu koma mu zauna batul," yasmin ce tai mata maganar, ganin sai yawo su ke yi cikin ɗakin, ga shi daga gani jikin nata babu ƙwari, ga ƴar guntuwar rigar dake a jikinta sai ɗagewa ta ke yi.

"Kina jin yunwa" parveen ce tai mata tambayar, ɗaga mata kai ta yi alamar eh, langwa6e kai parveen"wayyo Allah, ga shi babu abinci sai giants sun kawo mana" ƴar dariya Batul ta saki kafin tace"Ki kwantar da hankalin ki, kallon ku da na ke yasa naji na ƙoshi, babu wani yunwa atare dani,"

"Batul baki bamu labarin ina aka kai ki ba tsawon wata uku? Sannan waye ya dawo mana dake ko giant ne, mun ga kin canza mana sosai, kin rame kamar babu ƙoshin lafiya atare da ke" rubina ce tayi maganar,

Shiru ta ɗanyi kamar bazata amsa mata tambayoyin ta ba, duk su ka tsareta da ido suna kallonta, tun kafin ta fara magana Angel ta raya aranta cewa batul baza ta faɗa masu gaskiyar abunda ya faru da ita ba, ko dan kada ta sanya su damuwa.

A tsanake ta soma magana"bakomai ne zan iya tunawa ba, tun time da aka tafi dani, na dai san ba a cutar dani ba, ramar da ku ka gani a jikina bata komai bace face rashin ku atare dani, na tsinci kaina acikin wani ɗaki ina rayuwa ni kaɗai, ban rasa ci da sha ba, ana kawo min lafiyayyen abinci, ina yin wanka har ma in kwanta in yi bacci, mafi yawancin lokutta, ina yawan yin kukan rashin ku, in dinga ihu ina ambaton sunayen ku don kuzo ku ɗauke ni sai dai shiru babu mai jina........." iya abinda ta faɗa masu kenan, kuma sun yarda da maganarta, banda Angel, don koda tana basu labarin idonta akan Angel don tasan bazata yarda da ita ba, abunda yasa su deeja suka yarda da labarin da ta basu, saboda an dawo masu da ita ba kamar yarda aka saba dawowa dasu ba, Cikin mawuyacin hali, wasu ma basa a cikin hayyacin su.

"Batul yakamata kije ki yi wanka, akwai sabbin kaya da muka fada maki tsohuwa tamira ta bamu zamu ɗauko maki naki ki sanya, sannan muna so zamu gyara maki gashin kan ki" fuskarta ɗauke da murmushi tace masu toh, Eve tace"wai ina Uniform ɗin ki su ke ne? Ya akai aka sanya maki wannan guntuwar rigar launin Ja"? Muryarta da en ina tace"am..in..nima bansani ba, bansan waye ya canza min ita ba, kawai rana ɗaya na farka na ganni da ita a jikina" wani irin kallo Angel take binta dashi, kallon ban yarda da maganar ki ba, sai faman wurwurga ƙwayar idanuwanta ta ke yi, da zarar sun haɗa ido da Angel saita kawar da kanta gefe.

Ganin hakan yasa Angel ta ruƙo hannunta a cikin nata sosai ta damƙe shi tare da cewa"Muje na taimaka maki kiyi wankan" da sauri ta girgiza kai tare da cewa"Zan iya Angel, ki bari zanje nayi da kaina" a ruɗe tayi maganar, hakan ya ƙara tabbatar ma Angel abunda ta ke hasashe akanta, ta 6oye masu abunda ya faru da ita.

Gyaɗa kai Angel tayi"Its ok, amma mu fara shiga toilet ɗin, mu wanke maki kanki, In yaso daga bisani saimu fito mu barki ki yi wankan" muryarta adarare ta amsa mata da toh.

Mutun uku ne suka haɗu wurin wanke mata gashin kanta saboda yawanshi, Angel da Hanna sai Seeja, Sosai suka murje gashin kan nata, Bayan sun kammala wanke mata kan, suka barta cikin toilet din don tayi wanka, Angel fa jikinta duk ya yi sanyi, a ƙagare take da su samu damar da zasu ke6e da ita don suyi magana, sai dai ga dukkan alamu ita batul ɗin bata son su yi magana, shiyasa take kakkauce mata, Bayan wasu ƴan mintuna, Batul ta fito daga wakan, dama tun kafin fitowarta Angel ta ɗauko mata sabbin kayanta, ba tare da 6ata lokaci ba, ta zura uniform din a jikinta, Masha Allah, zayyana irin kyan da batul tayi a cikin kayan nata 6ata baki ne, abunka ga fara sol, Sun ƙara fiddo mata da kyanta, don ma ta ɗanyi rama.

daga ciki ta sanya red vest dinta, sama ta ɗaura wrap coat dinta, kafin ta sanya black trouser din, Angel ce ta taimaka mata wurin ɗaure igiyar coat ɗin, ta ɗaura mata Cotton scarves ɗinta saman wuyanta, Bayan ta kammala gyara mata su tsaf a jikinta.

Su Parveen sai santin kyanta su ke yi, Hannu biyu angel ta sanya wurin janyota a jikinta, sosai ta rungumeta, tana ɗan bubbuga bayanta, in a low voice ta furta mata"Ina son magana da ke, amma na lura kamar baki so why"? Muryarta na ɗan rawa tace"Angel, banason tuna abunda ya faru dani, pls kada ki matsa min kada ki tambaye ni komai, na roƙe ki, kuma bana so hakan ya 6ata maki rai" suna yin maganar ne ba tare da sun raba jikinsu daga na juna ba.

"Shikenan batul, bazan tambaye ki ba, ni kaina bana son na takura maki, zan jira ki har zuwa time da kika ji zaki iya sanar dani sai ki faɗa min" ta amsa mata da toh," Deeja dake ta kallonsu manne da juna ta fahimci cewa magana su ke yi, bayan sun raba jikinsu, ta dinga bin su azeeza tana rungume su a jikinta tana faɗa masu irin kewarsu da ta yi, Deeja kuma taja hannun Angel su ka koma gefe ɗaya,

Tambayarta ta yi me suka tattauna da batul, ta sanar da ita cewa ta tambaye ta ne game da abunda ya faru da ita amma bata faɗa mata komai ba, Deeja tace"kada mu takura mata, tunda ta nuna bata son mu sani, mu ƙyale ta kawai, wata kil hakan zaifi mana kwanciyar hankali," Angel ta gamsu da maganar deeja.

Badajimawa ba, Giants suka kawo masu lafiyayyan abinci, Saboda tsabar ƙauna, a baki suka dinga ba batul tana ci, sunƙi bari ta sanya hannunta taci, hakan ba ƙaramin karya mata zuciya yayi ba, tabbas an zalunce ta da aka raba ta da ƴan uwanta, amma yanzu Alhamdulillah tunda gata a cikinsu, da ranta da lafiyarta.

Bayan sun kammala Cin abincin, Giants suka tattara Farantan suka tafi dasu, A saman shimfidar sarah, suka zazzauna suna fira tare da batul, Angel tana zuƙunne gaban akwatinansu, Ta buɗe ta ɗauko Nail cutter da nail filler tare da madubi, ta dawo ta miƙe ma Sarah tace gashi ta gyara ma ƴar uwarsu akaifa, Murmushi sarah tasaki, tare da sanya hannu ta kar6a, Kafin su fara gyaran akaifar, Angel tace ta ɗan dakata, tana so su kalli faces ɗinsu a cikin madubi, ita da ƴar uwarta batul, Gefen batul ta zauna tare da ɗaga madubin, Ta haɗa fuskokinsu wuri ɗaya, Suka natsu suna kallon juna, hakanan Angel ta dinga jin faɗuwar gaba a yayin da take kallon fuskar batul ta cikin mirror, su azeeza sai faman leƙo da fuskokinsu suke yi suna kallon su.

"An ta6a faɗa maku cewa, Kuna bala'en kama da juna" Sarah ce tai maganar, parveen tace"wlh kuwa nima saida ki ka yi maganar nan tukunna na lura da hakan, Angel da batul suna kama sosai, musamman ta wurin shape ɗin bakinsu, duk da ba launi ɗaya bane, da kuma hasken fatarsu, gashin kansu ma Ya yi shige, hatta tsawonsu iri ɗaya,"

Deeja tace"ae hatta Yatsun hannuwansu dana ƙafafuwansu iri ɗaya ne sak babu bambanci, najima da sanin wannan ban ta6a faɗi bane" sarah tace"to kodai ƴan gida ɗaya ne"? Girgiza kai Yasmin tai tare da cewa"A labarin da Angel ta bamu, ita kaɗaice Awurin daddynta, mommynta ma, tun tana yarinya ta gudu tabarta, bata da ƴar uwa mace tun da ta taso a rayuwarta,"

Sarah tace"hmmm adai yi shiru kawai amma fa ni akwai abunda nake zargi, ina da wata baiwa da ku ba ku sani ba, tun kasancewa ta a prison, nake wannan hasashen, nasha ganin masu kama da juna wanda su basu lura da hakan ba, sai dai ina tunanin zaman tare ne yasa muke kamanceceniya da juna, yanzu a cikin ku nan, kaf ɗinku Naga kamanceceniya atsakaninku da junan ku, Hatta wannan yarinyar da aka kawo mu tare da ita, Me take da suna....." Eve ce ta ƙarasa mata maganar da cewa"Kina nufin Ƴar gidan daddy" jinjina kai tayi "eh ita nake nufi, akwai kamanceceniyarta da wani acikin ku, amma bazan faɗi ba" tana ƴar dariya ta yi maganar,

"Ko kina nufin azeeza? Don kinga kalar gashinsu yayi shige da launin fatarsu," girgiza kai tayi"a'a, ba azeeza ba, bana so na faɗi maku ne"

Roƙon ta su ka dinga yi haɗi da yi mata magiya akan ta faɗa masu da wa take kama, da kuma sauran waɗanda ta ke hasashen suna da kamanceceniya a tsakaninsu, tace masu itafa su daina yarda da maganarta, Ƙarya ta ke yi masu"

Haushin da suka ji ne yasa suka dunƙule hannu suna yi mata dundu abayanta, Abun saiya koma wasa, duk wannan abun da suke yi Angel da batul suna sauraronsu, sai dai hankalinsu ba akansu Ya ke ba, Yana akan junansu, Sai kallon fuskokinsu suke yi ta cikin madubi kamar zasu lashe juna, Sai da suka gama ƴar buge bugen da sarah, kafin daga bisani, kowannansu Ya natsu, suna ta nishi kamar waɗanda suka sha gudu.

Bayan sun samu natsuwa, Sarah ta soma gyarama batul akaifarta, Allah yayi mata baiwar Iya gyara akaifa, Batul taji daɗin ganin yadda ta gyara mata akaifarta, ta dinga yi mata godiya, Sarah tace tadaina yi mata godiya, domin kuwa babu godiya a tsakanin prisoners,"

Ataƙaice, Cikin ƴan kwanakin nan da aka dawo masu da batul, Sun samu farin ciki mara misaltuwa, Tamkar an ya ye masu damuwar dake damun so, koda yaushe suna atare da ita, dama batul akwai iya kalami mai ratsa zukata, haka zata zauna tana kwantar masu da hankalinsu, da deeja tare da Angel, waɗannan mutun ukun sun zama tamkar iyaye agare su, yanzu batul ta fara murmurewa, tsawon sati biyu da aka dawo da ita Jikinta yafara dawowa normal, babu ramar nan, hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba, har tambayar Angel tayi bayan bata nan an ƙara ɗaukar wani cikin su Hibba, ta sanar da ita cewa ba a ƙara zuwa ɗaukarsu ba, saboda babu wanda ya ƙara yin jinin a cikinsu, Allah ya yaye masu, sun samu salama, har cikin ranta taji daɗin jin hakan, Angel taso ta tambayi batul game da labarin da Gabriel ya bata na yarinyar daya gani tana gudu saman hawa na uku, saboda a suffar da aka dawo da batul yayi dai dai da yarda ya zayyana mata ita, hada guntuwar rigar daya gani a jikinta, Tabar abun a cikin zuciyarta ne, tun da ta nuna bata son maganar.

Har ila yau shiru ba'a dawo dasu Haris ba, Sun zuba ma sarautar Allah ido, addu'a kawai suke binsu da ita, A 6angaren Angel bata ƙara tada zancen dura tagar nan ba, saboda alƙawarin da Danish yace ta ɗaukar mashi akan bazata haurata ba, duk da a lokacin bata amsa mashi ba, sai dai taji ba za ta iya karya mashi alƙawarin ba..........

💔PRISONERS💔

Kwakkwance suke saman gadajensu, suna ta sharar bacci, har safiya ta yi amma basu farka ba, Jiya sun aikatu sosai, sai da suka wanke uniform ɗinsu duka da tsafaffin da sababbin kamar yarda suke yi in zasu wanke su sai su ɗaura bargunansu a jikin su,

Bayan sun kammala wankin su ka shanyasu zuwa lokacin da suka bushe suka mayar da tsoffin a jikinsu, sababbin suka ninninke su acikin akwatinansu, basu huta ba saida suka wanke bargunansu, suka shanyasu saman igiya, bayan sun kammala suka wanke toilets dinsu duka uku, suka bama furennin nan ruwa, Daga bisani, suka dawo cikin ɗakinsu, shima suka gyara shi tsaf tsaf komai Ya koma normal, a lokacin dare yayi suka kwanta don su huta, in the midnight Angel ta tada kowannansu don su yi addu'a kamar yarda suka saba, ga bacci a idonsu da gajiya amma ahaka suka zaune tare da ɗaga hannayensu sama suna kai kukansu wurin Allah, bayan sun kammala ne wani baccin ya ƙara yin awon gaba dasu, Shiyasa har gari ya waye basu tashi ba, saboda basu samu isasshen bacci ba jiya.

Azeeza da Jamimah suna a kwance saman gaɗo ɗaya, sarah tana a kwance ƙasa saman shimfiɗarta, yayin da batul ta ke a kwance saman gadon Danish ita da Angel, ƙudundune cikin bargo, atakure su ke gadon ya yi masu kaɗan ahaka suka kwana, su parveen duk suna asaman nasu gadajensu.

Wata irin zufa ce ta soma wanke fuskarta, ta dinga tsastsafo mata daga jikinta, Yatsun hannayenta da ƙafafuwanta suka soma kakarwa, Mafi yawancin lokaci idan hakan ya faru to mafarki ne ta ke yi acikin baccin ta,

_Ta tsinci kanta acikin wani gini mai girman gaske, mai ɗauke da tagogi babu ƙopa ko ɗaya a jikin shi, tsananin tsoro da firgici ya kamata, ta dinga kuka tana ambaton sunan Allah akan ya kawo mata ɗauki, wasu halittu ne ke fitowa ta jikin bango ɗauke da suffar namun daji, munanan gaske, gaba ɗaya ita suke tunkarowa, gashi babu hanyar da zata gudu daga cikin ginin, fashewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai tana girgiza kanta tamkar zai 6alle, Halittun na dab da ƙarasowa gabanta, Sai ga wata halitta ta faɗo ta saman ginin ɗauke da manyan fuka fuki sai shawagi take yi tana kewaye tsakiyar Ginin, kafin ta karyo kwana ta sanya hannayenta biyu ta ɗauke Angel tayi sama da ita ta fuce daga Cikin Ginin_

A dai dai nan mafarkin nata ya katse, A firgice ta farka daga baccin tana faman zare idanuwanta, hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta da ke ta harbawa, zufa duk ta wanke fuskarta, muryarta na rawa ta soma ambaton

"A'oothu billaahi minash-Shaytaanir-rajeem" sau uku tana ambatonta.

Bayan ta kammala taji sauki acikin ranta, ta juya ta kalli batul dake ta sharar baccinta, ajiyar zuciya ta sauke tare da zuro ƙafafuwanta ƙasa ta sauko daga saman gadon, zuciyarta acunkushe da tunanin mafarkin da ta yi yau, ta rasa gane me ma'anar mafarkin ke nufi kodai shaidan ne ya haddasa mata yin shi, sai dai tana ji acikin ranta kamar akwai wani abu da ake son nuna mata acikin mafarkin, Taya zata iya fahimtar hakan? Wani ginine ta gani acikin mafarkinta? Babu ƙofa a jikin shi sai dai tagogi, ga wasu halittu na ƙoƙarin kawo mata hari, abun da ya ɗaure mata kai, wannan halittar data 6ullo ta saman ginin dake a datse babu ƙopa, taya akai ta shigo ita? Harta taimake ta kuma ta fitar da ita daga cikin ginin da babu ƙopa a jikin shi?

Ganin tana ƙoƙarin burkita lissafin ƙwaƙwalwarta ne yasa ta dakata da yin tunanin, da sauri ta juya ta nufi toilet don ta yi fitsari, shiga ciki tai tare da jan jam lock ta datse ƙopar, Juyawar da zatayi keda wuya taji gabanta ya faɗi ras! Ba tare da sanin dililin hakan ba, Acikin zuciyarta ta soma ambaton Innalallahi wa'inna ilaihirraji"un"

kusan sau shida har saida taji zuciyarta ta ɗan lafa tukunna ta ƙarasa shiga ciki, Tayi abunda ya kawota, bayan ta kammala kafin ta fita ta ɗan juya ta kalli furennin dake acikin tukunyar, wannan dogon furen daya kere tsayin sauran launin punch pink, ganyayyakin Jikin shi sunyi baƙiƙƙirin dasu, hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, da sauri ta koma ta ɗebo ruwa a bucket takai shi bakin tukunyar ta zuƙunna tana goge bakin jikin shi da hannayenta gani take kamar goga mashi baƙin akayi, sai dai koda ta goge babu abunda ya canza har ruwa ta zuba mashi ta wanke shi yaƙi canza launi, miƙewa tayi taje ta ɗauko detergent tsabar hauka hada Soso ta zuƙunna gaban tukunyar ta dinga goge ganyayyakin jikin furen don su koma launinsu na asali, sai dai kash sunƙi komawa, kamar tana ƙara masu baƙi, a ƙarshe data gaji ta maida soson da omon, ta fito daga Cikin toilet ɗin Jikin ta ba ƙwari, hakanan ta dinga jin kamar faɗuwar gabanta yana da nasaba da canzawar launin ganyan furen nan, duk da batasan ran wanene akan shi ba.

A bakin ƙopar toilet ɗin ta jingina bayanta, Idanuwanta acike tab da ƙwalla, daga Cikin ɗakinsu ta soma jin motsin buɗe ƙopa, da farko ta yi tunanin giants ne masu kawo masu abinci, shiyasa taƙi motsawa

kwatsam! Ta soma jin shessheƙar kukan mutun acan cikin ɗakinsu, Da gudun gaske ta faɗo ɗakin a sukwane ta kai idanuwanta kan benan inda take jiyo sautin, Bakowa idanuwanta ke nuna mata ba face Majnoon fuskarshi ta yi jawur da ita, jan tabo ta ko'ina a jikin shi, jini ya kwanta sosai, daga shi sai jan wandonshi a jikin shi babu riga, ya rame sosai, kamar ba mutun ba, hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, tana ƙoƙarin motsa la66anta donta kira sunanshi karaf idanuwanta suka sauka akan fararen ƙafafuwan mutumin dake a gefen shi, a matuƙar ruɗe Angel ta shiga bin ƙafafuwan da kallo daga gani macace, koma wacece taji jiki na fitar hayyaci ta jigata sosai, duba da irin yarda jikinta keta kerma babu alamun lafiya atattare da ita, Hannunta ɗaya ruƙe da pant na mata launin Pink colour..........."


💋PRISONERS💋




Muryarta a ruɗe ta ambaci sunan ta,

"UNAIZA"! a yayin da ta ke ƙare mata kallo na ban al'ajabi, kamar fatalwa ta rame ta bushe ta ƙanjame, Irin rigar da aka dawo da batool itace a jikinta launin ja guntuwa wadda da kadan ta zarce mazaunanta ta yi wani irin haske, babban abunda ya tayar ma Angel hankali yakushin akaifar da ta gani akan fuskarta, wuyanta da fuskarta duk sun faffashe ta ko'ina red marks ne, hatta la66anta a fashe su ke sun kumbura, idanuwanta sun ƙanƙance daga gani ba ƙaramin kuka tasha ba, kamar ma bata a cikin hayyacinta, tsananin tashin hankali ne akan fuskar Angel, zuciyarta ba ƙaramin tashi tai ba, ta rasa akan wa zata tsayar da idanuwanta, tsakanin majnun da ya ke yin shessheƙar kuka da kuma Unaiza da ke A tsaye jikinta na kerma, gabanta na faɗuwa ta soma tafiya tana tunkarar su, koda majnoon yai arba da fuskar Angel nan ta ke ya kware baki yana kuka yana ambaton sunanta, da gudun gaske Angel ta nufe shi tunkan ta ƙarasa gaban shi a wani slow ta zube saman gwiwowinta dab da shi ta sanya hannayenta biyu da ke yin kerma ta rungumo shi zuwa jikinta, tsabar tausayin shi da ta ji ne yasa ta fashe da matsanancin kuka mai sautin gaske tamkar ranta zai fita, sautin kukanta ne ya karaɗe cikin ɗakin nasu, Wanda silar hakan ya farkar da masu Bacci, A firgice kowan nan su yai wurgi da bargon shi a lokaci ɗaya su ka mimmiƙe zaune saman gadajen su suna faman mutsustsuke idanuwan su da hannayen su, ba zato ba tsammani idanuwan suka sauka akan Angel da ta rungume majnoon a ƙirjin ta, babu wanda Ya lura da Unaizah

Please Login or Register in order to submit comment