Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tuna da ita ba, sai daga baya ne deeja tana kwance saman gadonta, ta yi zurfi acikin tunaninta, kwakwalwata ta soma tariyo mata abunda ya faru kafin atafi da Batool, Nan take ta dafe ƙirji, ta miƙe zaune tana Ambaton sunan azeeza, Koda sauran ƴan uwan nasu suka ji tana kiran sunan azeeza, suma sai suka wartsake kowa Ya sauko daga saman gadon shi, A gaggauce Deeja ta ɗauko dayar fitilar data rage a ɗakin, Ta ajiye ta daga ƙasa gefen gadon Azeeza, Ta zuƙunna tana leƙa kanta ciki, Anan ne taganta xaune Kamar gunki babu abunda ke motsi ajikinta, Ta fashe da kuka Tare da kai hannu ta 6an6arota daga Jikin bangon data jingina, ta janyota wajen gadon, ta kwantar da ita saman jikinta, Su Hanna duk suka kewayesu, kowa ya zuƙunna suna ta kuka suna ambaton Sunan Azeeza, Zuciyoyinsu duk sun karaya, ganin yadda jikinta ya sandare, Cikin shessheƙar kuka hibba tace su jira ta dauko ruwa a yayyafa mata wata'ƙil su samu ta farka, tana karasa yin maganar ta miƙe ta ɗauki fitilar ta nufi gadon batool, tana laluban robobin ruwan da suka ajiye, sai dai bata samu ko ɗaya ba, duk sun ƙare, Jiki amace hibba ta dawo tana haska su da fitilar hannunta tace babu ruwa, bari naje toilet na ɗebo, har ta juya zata nufi toilet ɗin, Muryar deeja ta katse ta da cewa"Ina haris yake? Naji motsin shi ɗazu, Ya sauko daga saman gadon shi, ina tunanin toilet ya shiga, Bari na kwala mishi kira yazo," Batare da6ata lokaci ba, deeja ta shiga kwala mishi kira, Sai gashi ya faɗo Cikin ɗaki,

Haris na ƙarasawa kusa dasu, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunan azeeza tare da cewa Meya faru da ita? Nan suka sanar dashi komai, tun daga zuwan Giant, dafe kanshi yai da hannu ɗaya, idanuwanshi sunyi jajur, zuciyarshi duk ba daɗi, Yau dai gaba ɗaya basu ji daɗin ranar ba, sun yini da baƙin Ciki acikin ransu,

Kallonsu parveen yae ganin yadda suke ta yin kuka babu ƙaƙƙautawa, Cikin sigar lallashi yace"Ku kwantar da hankalin ku, azeeza zata farka suma ne tayi, bari naje na ɗebo ruwa a yayyafa mata" yakai karshen maganar tare da juyawa Ya nufi cikin ɗakin, Yana laluban Inda ya jefar da robar ruwan daya watsa ma danish ɗazu, Cikin sa'a yaci karo da ita can gefen dining carpet ɗinsu, Da azama ya je ya ɗauko bottle water ɗin Ya juya ya nufi sashen toilet ɗin su.

Lokacin daya shiga, baiga danish ba, babu shi babu alamarshi, Sai dai bai kawo komai aranshi ba, ganin ɗaya daga Cikin ƙopar toilets ɗin nasu a garƙame, sai yayi tsammanin ko yana aciki ne, ɗayan toilet ɗin ya shiga ya kunna fanfo ya tarba robar ruwan, sai da ta Cika tab, kafin Ya kashe fanfon Ya fito daga Cikin toilet ɗin Ya koma inda su deeja suke a zazzaune, Zuƙunnawa yai, bayan ya ajiye fitilar hannunshi, Ya tarba ruwan a tafin hannun shi ɗaya, Ya watsa ma azeeza saman fuskarta, Kowa ya baza ido yana jiran ganin ta farka, amma shiru ko motsi bata Yi ba, Nan fa hankulan su suka ƙara tashi matuƙa,

Cikin shessheƙar kuka suka haɗa baki suna roƙon azeeza akan ta taimaka musu ta farka, Haris dasu Javed sai lallashinsu suke Yi, ganin yadda duk suka shiga damuwa, parveen na kuka tace"tun da muke arayuwar mu ba mu ta6a fuskantar tashin hankali, irin na yau ba, An ɗauke mana batool, ga azeeza kuma taƙi farkawa, Ni tsorona ma kada ace ta mutu....." kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan daya ciyota, ta kifa kanta saman gwiwarta, muryar deeja adisashe tace"dan Allah ku daina maganar mutuwa, wlh bana sonji, in sha Allah azeezan mu zata farka, babu abunda zai same ta, addu'a ya kamata muyi mata," Haris yace"wace irin addu'a? Babu abunda zata yi mana, kawai dai mu jira zuwa lokacin da zata farka," idanuwanta cike tab take ƙwalla take kallon shi,

Tsananin tausayinsu ne ya kamata haris, bayin Allah, tun safe hankalin su ba'a kwance yake ba, ga shi har dare ya ratsa basu runtsa ba,

Kusan sau uku haris yana yayyafa ma azeeza ruwa akan fuskarta amma taƙi farkawa, Jikinsu duk yai sanyi, haka suka zauna a kewaye da ita, suna kallonta yayin da hawaye ke cigaba da sauka a kan fuskar kowannan su.

"To ko dai mu yi ma tsohuwa magana tazo ta duba ta kada ta mutu" acewar yasmin, har suna haɗa baki wurin cewa"Taje ta kirawo ta," Da sauri yasmin ta miƙe ta dauki fitila ta wuce ɗakin tsohuwa, lokacin da yasmin ta bubbuga ƙopar ɗakin tsohuwa bata buɗe mata ba, kusan sau takwas tana yin knocking kamar zata 6alle ƙopar har saida haris yace mata ta dawo zai iyayiyuwa bata nan,Tukunna ta ƙyale ƙopar ta dawo wurinsu ta zuƙunna,
Magiya suka soma Yi mata akan tafarka

"Azeezan mu ki tashi dan Allah, Badan halin mu ba, wlh ba mu gaji dake ba Muna matuƙar ƙaunarki ƙaramar mu kuma babbar mu, pls wake up, kome kike so zamuyi maki, bazamu ƙara 6ata maki rai ba, kuma ba zamu bari giants su ɗaukar mana ke ba" kamar wasu sabbin mahaukata haka suka dinga yi mata sambatu akan tafarka, tun sunayin maganar da ƙwarinsu har ta kai ga muryoyinsu sun disashe, kowa yaja gefe suna matsar ƙwalla, idanuwansu duk sun kumbura saboda tsabar kukan da suka sha,

"Wai ina angel take ne!? Nifa banganta acikin mu ba? Yakamata wani yayi mata magana tazo taga halin da azeezan mu take aciki, tayi mata addu'a ko mun samu tafarka" Kallo kallo suka shiga yi a tsakaninsu, Jin abunda deeja tace, gaba ɗaya sun manta da babu angel acikinsu sai da tayi wannan maganar su ka tuna da ita, Hanna tace"ɗazu acan nabarta zaune bakin ƙopar shiga sashen toilets dinmu," tayi maganar tare da juyawa tana nuna musu wurin, Basu ga komai ba, naufal yace"kodai tayi bacci ne"? Haris ya bashi amsa da cewa"ae bata a saman gadonta, ɗazu da zan shiga toilet na duba naga babu ita" a matuƙar ruɗe suke kallon juna, Eve tace"kodai ta shiga toilet ne? Bari inje in dubo ta"

da sauri haris ya dakatar da ita tare da cewa"Ni zan dubo ta" Ya miƙe tare da kai hannu ya ɗauki fitila Ya juya ya nufi sashen toilet ɗinsu, yana gab da zai shiga, ba zato ba tsammani sai ga danish Ya faɗo hannayenshi biyu suna rungume da angel, ya tallabota a jikinshi, babu alamun tana motsi, A wani irin yanayi Su Hanna suka mimmiƙe tsaye suna kallon shi, mamaki ƙarara akan fuskokinsu, Yayin da zuciyoyinsu ke acunkushe da tambayoyi dangane da abunda ya faru da ita da har ta sume bata motsi,


An rasa me buɗe baki yayi mishi magana A cikinsu, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye Ya wuce da ita saman gadonta Ya kwantar da ita, sumar kanta duk ta hargitse, Fuskarta tayi jawur, musamman tsinin hancinta, hada ɗigon Jini, daga gani ba ƙaramar wahala tasha ba, hawayene ta ko'ina akan fuskarta, kayan Jikinta sunyi uban squeezing, Hada wandonta Daya maida mata ajikinta, Da gudu Su Hanna suka Tunkaro gadon suna tambayarshi Meya faru da angel a ina ya ɗaukota? bai tanka musu ba, Domin kuwa A yanzu baya atare dasu, itace A gabanshi, zuciyarshi sai harbawa take yi da sauri sauri, numfashin sa da hucin zafi yake fita, a wani irin yanayi yake bin fuskarta da kallo...................."

"Shin meya faru da angel Bayan ta dura tagar nan"?

Lokacin da Angel ta haura tagar nan, ta faɗo ta baya wani irin duhu ne ya mamaye idanuwanta, kanta ya soma juyawa, Ta sanya hannayenta bibbiyu ta dafe kanta, Jikinta ya soma kerma a hanzarce ta fara ƙoƙarin kamo sunan Allah acikin bakinta, sai dai abun ya faskara, sautin shessheƙar kuka ta dinga Ji acikin kunnuwanta, ranta ya dinga bata cewar batool ce take kuka, Cikin duhunnan, ta miƙi hanya gudu gudu sauri sauri hada tuntu6e, ita kanta batasan ina zata dosa ba, domin kuwa notikan kwanta sun kwance, bata ji bata gani, a makance take tafiya burinta takai ga inda take jiyo sautin shessheƙar kukan nan, Haske ta fara hangowa a ƙarshen hanyar data biyo, da gudu ta nufi inda take hango hasken nan, tana faɗowa cikin wurin, Idanuwanta suka sauka akan katafaren filin dake da manya manyan benaye, a ƙalla sun kai Shida benayen kuma kowane matakalarshi ta haura goma sha, don akwai wanda matattakalarshi takai talatin shine wanda idan ka hau zai kai ka har third floor na ginin, Ginin yana da tsayi da faɗi, Daga sama wasu irin manya manyan fitilune da suke haskaka wurin, idan ka kalli kowani hawa na benan zakaga Wasu Tagogi wadanda glass din Jikinsu launin Ja ne, Masu girma, Babu ƙofofin ɗakuna Sai dai da alama za'a Iya samun ƙofofinsu ta can cikin hanyoyin dake akwai, wani irin kurman Ginine, Mai matuƙar ruɗarwa, wani irin fargaba ne ya ɗarsu acikin zuciyarta lokacin da tafara Jin wani irin gurnani, Ginin Ya dinga juya mata, benayen suka dinga motsi Suna Yin ƙasa da sama, Waro ido waje angel tayi Jikinta na 6ari, Ta zabura zata Juya ta koma Inda ta fito, sai dai ina babu hanya, tama rasa gane ta inda ta faɗo Cikin wurin, Tsabar ruɗi yasa ta baza da gudu ta faɗa tsakiyar wurin, hannayenta dafe da kanta saboda wani irin firgici da take aciki, tuni zufa ta wanke Jikinta sharkaf, Bata gama rikicewa ba, Daga can saman hawa na uku ta soma Jin muryar mahaifinta tajudden Yana kuka yana kwala mata gira, A matuƙar ruɗe ta juya ta baya tare da ɗaga kanta saman benan, A tsaye ta hango shi, tare da Wasu irin haluttu masu gashi gashi ajikinsu, Jibga jigba, Sun kewaye shi, Sai Cuzgar naman Jikin shi suke yi, Wata irin gigitacciyar ƙara angel tasaki, mai kuwar gaske, Ta fashe da matsanancin Kuka tana fadin"Daddy! wayyo Allah na daddyna! Shikenan sun kashe mini daddyna!! nashiga uku, Dan Allah ku ƙyale mini daddyna" Tana kuka ta watsa da gudu ta nufi ɗaya daga Cikin benayen da nufin taje ta taimaki daddynta, tana gudu ana maida ta baya, Da zarar takusa kaiwa saman benan sai taga Sun juya mata, Benan yaja da baya, Ya koma can Ciki, Haka ta dinga bin benayen tana ƙoƙarin hawa samansu, Amma wani abun ruɗarwa benayen tamkar masu Rai, sosai suke motsawa wurin yin ƙasa da sama, Jikinta duk zufa ta galabaita sosai, idanuwanta sunyi jawur, Jijiyoyin wuyanta duk sun fito ruɗu ruɗu Jikin fatarta, Muryarta har ta disashe, Duk da mawuyacin halin da tashiga na tsoro da firgici hakan baisa ta fasa yunƙurin hawa benan ba, Bakomai take ji ba face mahaifinta da take hangowa can saman waɗannan halittun suna Cin naman jikinshi, sai kuka yake Yi yana miƙa mata hannu akan tazo ta taimake shi, Akan idonta halittun suka gutsire ƙafafuwanshi, Jini ya dinga tartsatsi yana gangarowa ta saman benan, Angel tashiga ruɗani, addu'a ta kubce mata, gaba ɗaya tunanin ta ya gushe, Tun tana yin kuka har ta koma tana yin na zuci, Ƙafafuwanta sai zogin azaba suke yi mata, saboda zarya da tadinga Yi, Lokacin da benayen suka gama yi mata wasa da hankali, Suka koma yadda suke, waɗannan halittun suka 6ace ma ganinta, sai dai gangar jikin mahaifin ta dake a yashe saman hawa na uku, Da gudu ta haura saman dogon benan nan wanda ya ke da matattakala Talatin, Tana tafiya tana zamewa, a haka harta samu ta haura saman shi, Tana ƙarasawa inda gangar jikin tajudden take, ta zuƙunna saman gwiwowinta, ta dinga kuka hada majina tana ambaton sunan shi tana faɗin sun kashe mini daddyna, sun rabani da farin Cikina, Wayyo Allah na, Ya Allah ka ɗauki raina nima in huta, yatsun hannunta na kerma ta ɗaga su da nufin ta shafa gangar jikinshi, nan take gangar jikin ta 6ace 6aat, a matuƙar gigice ta zazzare idanuwanta eye lashes ɗinta suka bubbuɗe, tsigar jikinta ta dinga tashi, zufa ta ko'ina, kwakwalwarta ta burkice, kafin ta yi wani yunƙurin motsawa ta soma Jin motsin tafiyar wasu abubuwa ta ko'ina, a firgice ta ɗan juya baya tana kallon Jikin wata taga dake a datse, Ras taji gabanta yai wani irin mugin bugu, Bakomai bane angel ta gani face wasu irin manyan kunamu sun ɗaga ƙarin su, Yayin da suke gangarowa daga Jikin bangon suna tunkaro inda take zuƙunne, wa'iyazubillah, ƙiris ya rage zuciyarta ta buga, saboda tsabar razanar da ta yi, ga shi jikinta babu ƙwarin da zata Iya saukowa daga saman benan, Jikinta na 6ari ta soma rarrafawa tana tunkarar banen dan ta sauko ƙasa, tana kuka tana waiwayon kunamun dake tunkarota, a wannan lokaci ta dinga kwala ma danish kira na fitar hayyaci tana faɗin yazo ya taimake ta, zasu kashe ta, ta mutu ta bani ta lalace ƙarshenta yazo,

Adai dai wannan Lokacin Danish Ya faɗo Cikin wurin, Hannun shi ruƙe da wandonta, sai faman waige waige yake yi, karaf idanuwanshi suka sauko akan angel da ke yin rarrafe tana saukowa daga saman benan, Hankalinshi yai matuƙar tashi, da ƙarfi ya ambaci sunanta yana faɗin ta tsaya kada ta motsa ba abunda zasuyi mata, sai dai kash angel bata Iya fahimtar maganar shi, saboda bata acikin hayyacinta, Da gudu ya nufi benan da niyar yaje ya taimaka mata, kafin ya ƙarasa gwiwowin ƙafarta suka sage, Tun daga kan matattakalan farko Angel ta burki ce ta dinga mirginowa tana gangarowa ƙarshen stair ɗin, kanta da hancinta duk suka fashe suna bleeding, kafin ta faɗo ƙasa, sai da ta fita hayyacinta, Jini ya wanke fuskarta, har saman wuyanta, hatta knuckles ɗinta saida suka gurguje, A ƙarshe ta ƙundumo kan ground floor ɗin, kanta ya dake shi, goshin ya fashe, ƴar rigar uniform ɗin dake ajikinta, tuni ta yaye ta nannaɗe ta dawo saman Cikinta, tsiraicin ya bayyana sosai, gashi ko pant babu ajikinta, Wasu irin zafafan hawaye ne suke wanke fuskar danish time ɗin daya ƙarasa ya zube agabanta saman gwiwowinshi, yayin da numfashin shi ke fita a wahalce, A wani irin yanayi mara misaltuwa yake kallonta, dama abunda yake guje mata kenan, Amma ta ƙi jin maganarshi, hannunshi na kerma ya ruƙo rigarta data nannaɗe, ya janyota ya rufe mazaunanta, a saman laps ɗinshi ya ɗaura wadonta, kafin ya sanya hannayenshi biyu ya ɗago da ita, zuciyarshi ta ƙara karaya ganin irin mummunan raunin da taji akan fuskarta, idanuwanshi ba zasu juri ganin angel cikin mawuyacin hali ba,

da sauri ya kwantar da ita saman ƙirjinshi, ya matseta da hannayenshi biyu, ya kwanto da kanshi saman sumar kanta dake a yamutse, ya ɗan lumshe idanuwanshi, saboda tsabar zafin jikinta har a jikinshi yana ji, cikin wata irin raunatacciyar murya ta wanda ya galabaita ya jigata ya fita hayyacinsa ta dinga kira mishi sunan daddynta, ta zagayo da hannayenta zuwa bayanshi, ta cakumi rigarshi tana yamutsa ta, babu alamun hankali atattare da ita, santala santalan cinyoyinta sun fito farare sol dasu, sai faman motsa su take yi, tana harɗesu jikin juna, ganin rigarta na ƙoƙarin kwarewa ta ƙara nannaɗewa yasa shi yin saurin kai hannu ya damƙi ƙasan rigar ya gyara mata ita,

A hankali Ya sanya hannayenshi biyu ya ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi, Jininta duk ya 6ata mishi gaba rigarshi, ya tallabo fuskarta, Yana ƙare mata kallo, Idanuwanta sun ƙanƙance, tausasan la66anta sun kumbura sun ciza launinsu, tsinin hancinta yai ja sosai, jinin ne ke gangarowa ta cikin ƙofofin hancinta, Cikin karyayyiyar murya ya ambaci sunanta Angel, bata amsa mashi ba, don a halin da take aciki batasan wanene akanta ba, sunan daddynta kawai take iya ambato,

Cikin harshen turanci yaci gaba da cewa "Angel, kinga abunda kika ja ma kanki ko? Yanzu da ace banzo ba ya zaki yi? Kalli yadda kika raunata kanki, ta ko'ina babu lafiya a jikinki, saboda kafiya irin taki na gargaɗe ki amma kika ƙi jin magana ta, saboda baki ɗauke ni abakin komai ba, kin ɗauka cewa shiga cikin prison abune mai sauƙi, yanzu gashi nan kin ja ma kanki yin jinya, nasan ko gobe aka nuna maki hanya fita ba zaki ƙara gigin binta ba" shi kaɗai yake ta sambatun shi, baiwar Allah, sai nishi take yi, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji ajikinta,

Haɗe fuskokinsu yai wuri ɗaya, ya mayar da hands ɗinshi Tsakanin sumar kanta da wuyanta, harshen shi ya ɗaura saman fuskarta, a hankali ya soma lashe jinin dake zuba, har sai da yaga babu sauran jinin dake ɗiga tukunna ya zame tongue ɗinshi, idanuwanta sai rurrufewa suke Yi, biji biji take ganin shi, tun tana yin numfashi daƙyar daƙyar har ta kai ga sumewa saman jikinshi, da dabara ya samu ya zame wandon unform ɗinta daga saman laps ɗin shi, Ya damƙo dogayen ƙafafuwanta, Ya shiga kiciniyar sanya mata shi, daƙyar ya zura mata wandon yaja shi har saman waist ɗinta, bayan ya kammala, Ya ɗaɗɗago da ita, ya yarfata saman kafaɗarshi Ya miƙe Ya juya Ya nufi hanyar komawa ɗakin su, sai dai da alama danish bata taga ya koma Cikin ɗakinsu ba, 6acewa yai ya faɗo Cikin toilet ɗinsu ɗauke da ita a hannunshi, a lokacin Har ya gyara ɗaukar da ya yi mata, ya sauko ta daga saman kafaɗar shi, Ya yi mata irin ɗaukar da ake yi ma jariri, Yana kan hanyar fitowa daga Cikin toilet ɗin, Yaji motsin mutun Yana tunkaro ɗakin Da wani irin sauri Ya faɗo bakin ƙopar sashensu, Kunji yadda akai danish Ya ɗauko angel,

*PRISONERS💔*

hankalinsu yaƙi kwanciya, Ganin irin raunatar da angel tayi, masu karyayyiyar zuciya acikinsu tuni sun fashe da kuka, Hibba tace"wannan wata irin rayuwace, daga wannan sai wannan, yau dai bata yi mana daɗi ba, muna fama da azeeza data sume ga kuma Angel itama asume jikinta duk ciwuka, wai dan Allah meya faru da ita ne? Tana rufe baki hanna tace"pls danish ka faɗa mana a ina kaga angel, can fa nabarta a zaune, Yanzu kuma sai gashi ka shigo da ita daga Cikin toilet, yaushe ta shiga ciki? A matuƙar ruɗe tayi mashi tambayar, haris yace"Allah yasa ba wani mugun abun ka yi mata ba, Wama ya sani ko bugunta ka yi don ka huce haushin abunda muka yi maka," da sauri danish ya ɗago da idanuwanshi ya ɗaurasu kan fuskar haris da ya yi maganar, wani irin raɗaɗi yake ji acikin zuciyar shi, ƴan uwanshi suna yi mishi kallon mugu mara tausayi mara imani, duk sai yaji ya tsani kanshi, sam ya kasa furta komai, duk da ya ɗago ne da niyar ya mayar mishi da martanin maganar shi amma sai ya kasa,

"Yakamata muyi ƙoƙarin wurin ceto rayuwan ƴan uwanmu bawai mu tsaya muna surutu mara amfani ba" Acewar Mubeen,

Cikin fushi haris yace"Ka faɗa mana me ka yi ma angel da har ta suma? Hawaye ne suka cika idanuwanshi, Cikin sanyin murya yace"ka bari tafarka sai ka tambaye ta me nayi mata, idan har ni na zalunce ta, kuna da right da xaku iya rama mata, amma bai kamata ace kuna tuhumata ba"

Naufal yace"zamu zuba ido mu gani har zuwa lokacin da zata farka wlh idan har ta fada mana cewa kaine silar halin da tashi ga, to ka kwana da sanin cewa ba zamu ƙyale ka ba," Yana magana yana galla mishi harara, Girgiza kai danish ya ɗanyi batare daya tanka ma naufal ba, ya lura gaba ɗaya shi suke zargi akan halin da angel ta shiga, basu son cewa itace ta ja ma kanta ba,

"Ina azeeza take"? Yayi tambayar yana bin fuskokinsu da kallo, kusan atare suka haɗa baki wurin cewa"Ina ruwanka da ita? Ka damu dasu ne"? Girgixa kai ya ɗanyi tare da cewa'taya bazan damu dasu ba, ƴan uwanane su, baku isa ku hanani tambayarsu ba"


Javed yace"Har kana da bakin cewa su ɗin ƴan uwanka ne? Mugu dakai saboda rashin imani ka damƙi hannun batool ka miƙa ma wani ƙato ya ɗauke ta don aje acutar da ita, a haka har kake kiransu da ƴan uwan ka"? Tuni idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla, tunawa da rashin imanin da ɗan uwansu danish yayi musu, jikin shi duk yayi sanyi, har lokacin yana zaune gefen gadon angel, daƙyar yake kallonsu saboda nauyin haɗa ido da su ya ke ji.

"Ka faɗa mana wanene kai!" har saida gabanshi ya faɗi jin tambayar da haris ya jefa mishi, muryarshi na kerma yace"wha..what u mean? Haris ni kake tambaya wanene Ni"? jinjina kai haris yai tare da cewa"Eh, so nake insan wanene kai! Danish bani kaɗai ba gaba ɗayan mu nan zargin ka muke Yi, Kawai ka faɗa mana gaskiyar wanene kai, meyasa kake atare damu" a ruɗe danish yake kallonsu,

Naufal yace"bana tunanin danish cikakken mutun ne, Saboda babu zuciya a ƙarjinshi, Haba rashin imanin yayi yawa, ka duba kaga yau tsawon shekara nawa, danish yana atare da batool, tun kafin mu mallaki hankalin mu yake atare da ita, baida wani makusancin daya wuce ita, in ka cire haris, amma yau rana ɗaya ka gaza ceton rayuwarta, sai ma ka taimaka wurin miƙa ta ga azzaluman da zasu azabtar da rayuwarta......" wani irin kukane yazo ma naufal ba arxiƙi ya katse maganar, hawaye suka soma bin fuskarshi,

Haris ya ɗaura da cewa"ba zamu ta6a mantawa da wannan ranar ba, danish ka cika butulu, mara imani da tausayi, Yarinyar nan babu irin ciwon kan da batayi ba akanmu, tana matuƙar son ƴan uwanta, idan wani baya lafiya acikinmu, batool ko bacci bata iya yi har sai yaji sauƙi, ka cuce mu danish, kuma ka karya mata zuciya, nasan batul bazata ƙara yarda dakai ba, saboda kaine silar duk wani hali da zata tsinci kanta,"

Tun da suka soma yi mishi magana, yayi shiru yana binsu da kallo bai ko tanka musu ba, duk yadda zaiyi musu bayani yasan ba lallaine su fahimce shi ba, amma yafi su jin raɗaɗin rabuwa da batool, shi kaɗai yasan irin ƙuncin daya shiga lokacin daya janyota ya miƙa ma giant,

Sun tasa shi gaba suna jiran jin amsar dai basu, bai bi ta kansu na, ya miƙa ya tunkari inda su deeja suke zuƙunne, yana yunƙurin zuƙunnawa don ya duba lafiyar azeeza, naufal ya damƙi hannun shi tare da cewa"kada ka kuskura ka ta6a ta, babu ruwanka da rayuwarmu" murmushin takaici danish ya sakar mashi, batare daya mayar da martanin maganar shi ba, ya fusge hannun shi daga ruƙon da yae mishi, Ya zuƙunna agabansu deeja, wani irin haushin shi take ji kamar ta shaƙe wuyan shi, Tun da ya zuƙunna take ta aika mishi da harara kamar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, wanda ake yin hararar domin shi baima san tana Yi ba, hankalin shi gaba ɗaya yana akan azeeza, dake rungume jikin deeja,

Robar ruwan da haris ya ajiye a ƙasa, Danish Ya miƙa hannu ya ɗauko ta, A baki ya kur6i ruwan, duk suna a tsaye suna kallonshi, A saman fuskar azeeza ya watsa ruwan, Wani iko na Allah nan ta ke azeeza taja dogon numfashi, Jikinta ya soma kakarwa, Cike da mamaki suka dinga kallon danish da kuma azeeza, ganin yadda yai nasarar watsa mata ruwa ta farfaɗo,

Hannayenshi biyu ya sanya ya tallabo fuskar azeeza yana kallonta, muryarta adisashe take faɗin dan Alah kada ku bari su ɗauke ni, wlh mutuwa zanyi, ni bazan bi su ba, "

"Azeeza"! Muryar danish ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, ta ɗan buɗe idanuwanta tana kallon shi biji biji saboda matsalar idanuwanta, da sauri su haris dasu hanna duk suka zuƙunno agabanta, suna ambaton sunanta, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, badan tana gane su ba, yayin da idanuwanta ke lumshewa, muryarta na ɗan rawa tace"Dagaske ba'a tafi dani ba, ina atare da ƴan uwana"? Atare suka haɗa baki wurin bata amsa da cewa"Eh, muna atare dake" har xatayi murmushi sai kuma ta fasa, tunawa da batool, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke. A tsorace tace dasu"Ina Batool take" nan fa kowa yai shiru, hakan yasa ta fahimci cewa An ɗauke batool, shessheƙar kuka ta fara yi musu, Danish yace"its okey azeeza, ba lafiya gare ki ba, kina buƙatar ki huta" girgixa mashi kai tayi hawaye ta ko'ina akan fuskarta tace"Yanzu shikenan

Please Login or Register in order to submit comment