Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bedroom ɗin sa, within mins sai gashi ya dawo jikinshi sanye da jallabiya, ya gyara jikinshi miƙa mata hannu ya yi batare da musu ba ta miƙa mashi ƴarshi, Yasa hannu biyu ya kar6e abunshi, sosai ya ƙanƙameta, Ya tsare ta da idanuwashi yana kallonta, Sae faman mutsu mutsu take Yi, ta tura yatsanta ɗaya acikin baki sai tsotsa take Yi,

Ba komai ya fi ɗaure ma shi kai ba a game da yarinyar face kwayar idonta, kaf dangin su babu mai irin launin ƙwayar idonta, sai dai ko acikin dangin mahaifiyarta,


Cikin sanyin murya ya soma magana Yana kallonta"ke kyautace agare Ni, Inasonki Sosai, Allah ya raya mun ke bisa tafarkin addinin islama, Allah Ya bani ikon kula dake Alfarmar annabi muhammad (SAW) Allah ya tsare mun ke, Allah kuma yasa ki xama silar farin Cikinmu," haka ya dinga Jero addu'o'i, Suna uxair suna amsa mashi Ameen ameen

*SHIN WANENE ZAHEER TAJUDDEEN?*

Tajuddeen ɗan asalin Wani ƙauye ne da ake kira Buzaye wanda ke a ƙarƙashin ƙaramar hukuman ɗanja dake a jahar katsina, Haifaffen ɗan garin ne, nan ne tushen shi, anan dangin su suke,mahaifin shi da mahaifiyarshi Auran Zumunci ne, Ƴa'ƴan wa da ƙanine, Malam Zahiru shine sunan mahaifinshi, Mahaifiyar shi kuma Yahanasu, tun da su ka yi auren Allah bai ba su haihuwa ba, abun tun bai damun su harya fara damunsu, mutanan garin har sun fara yi masu surutu kan rashin haihuwa, haka dangin su ma, sun fara tanka masu akan Haihuwa, musamman Deeje Mahaifiyar malam zahiru, kullum mitar rashin haihuwar matarshi take yi, Ita dai burin ta a haifa mata Jikoki, sun shiga mawuyacin hali,Har shirin zuwa asibiti su ka yi don a duba lafiyar su a gano inda matsalar take, A wannan Lokacin basu da babban asibiti A yankin sai da su ka yi tafiya zuwa cikin jihar katsina, Suka sauka agidan balaraba ƙanwar Yahanasu da ke aure anan Cikin garin, sun samu kyakkyawar tarba a wurinta,haka mijinta ma, ya yi farin Ciki da zuwansu, domin kuwa malam zahiru Abokin shi ne ta silar shi Ya haɗu da balaraba, Kwanan su ɗaya a gidan ta, a washe garin ranar Suka je asibiti aka duba su, A ƙarshe dai Likita ya tabbatar masu da cewa Lafiyarsu qalou Lokacin haihuwarsu ne baiyi ba, Su Cigaba da addu'a kawai in dai suna da rabon haihuwa aduniya to zasu ga jininsu duk mun daren da ɗewa, kwanansu Uku a katsina suka dawo nan buzaye, Koba komai hankalin su Ya ɗan kwanta,tunda an tabbatar masu da cewa basu da matsalar Haihuwa,

Bayan tsawon Lokaci Da yin aurensu, Kusan shekera ashirin da biyar kenan, A wannan Lokacin Allah Ya kawo ƙarshen koken rashin haihuwarsu, wato Yahanasu ta samu Ciki, saboda tsabar farin Ciki har ƴar ƙwarya ƙwaryar walima suka shirya aka kira masu kiɗan kwarya, Aka ci aka sha,

A kwana a tashi, yahanasu ta haifi kyakkyawan jaririnta wanda yaci sunan shi Tajuddeen sunan Mahaifin Malam Zahiru, Tun yana yaro suka ƙwallafa rai akanshi, Kowa son shi yake yi, kuma tun daga shi Allah bai ƙara basu haihuwa ba har suka tsufa, a lokacin da taj ya fara girma, kawun shi ƙanin mahaifinshi Ya kwallafa rai akan subar mashi Yaron tunda basu da hali, Yanaso ya ɗauki nauyin karatunshi, acan inda yake aiki Jihar Jos, a lokacin ƙin yadda su ka yi saboda shi kaɗai ne ɗansu wanda suke kallo suji daɗi a duniyar nan, sunfi son ko da yaushe Ya kasance atare dasu, Babu yadda Uncle ɗin nashi ya iya dole yabar masu abunsu, Amma duk da haka sai da ya taimaka masu da abunda zasu kula dashi, don kafin tafiyarshi,Sai da ya tabbatar sun sanya shi makarantar Boko da islamiyya, tukunna Ya tafi,


Tajudeen tunda ya taso Yaro ne mai hankali da natsuwa akwai na annabawa wato haƙuri mutun ne maison Jama'a, ga son Ibada,ga tsafta sam baida wata damuwa a rayuwarshi, ga kyautata ma iyayen shi, tun yana ɗan shekara Goma shabiyar aduniya yake ƙoƙarin ɗaukar nauyin iyayen shi,Wasu aiyukan na mata duk ya iya su, Share share wanke wanke,wankin kayan su da guga, Ɗebo ruwa a rijiya,Hatta girki Mafi yawan lokutta indai ba makaranta, shi yake zama ya girka masu abinci, shiyasa a kullum iyayen shi suke ƙara sonshi, kullum Cikin sanya mashi albarka su ke yi.


Bayan Tajudden Ya kammala Secondry school, Wannan uncle ɗin nashi dake a Jos Ya ƙara kawo masu ziyara, Ai tunda Yayi arba da tajuddeen yaga Yadda ya sauya, Ɗan kyakkyawan matashi, nan fa ya ƙara sa naci akan subar mashi yaron Ya tafi dashi Can Ya sanya shi Jami'a dama yana da ɗa ɗaya Tilo mai suna Uzair burin shi ya haɗasu Wuri ɗaya su yi karatu atare, Nan ma suka ƙi amince mashi, haka shima Tahujudeen ya kafe akan baison zuwa yafi son zama da iyayenshi,

Babu yadda Uncle ɗin bai yi dasu ba, Amma suka ƙi yadda,a karshe Ya yanke shawarar zuwa wurin mahaifiyarsu deeje,

Lokacin daya je wurinta, Sosai ya Tunzurata, Ya nuna mata irin Albarkar da zasu samu da yaron idan ya tafi dashi birni,A ƙarshe dai hada Cin hanci Yaba uwar tasu, da yake tsohuwa deeje akwai shegen son kuɗi, Shiyasa Ko tsakaninshi da malam zahiru, tafi ji da shi saboda duk in zaizo Buzaye sai ya haɗo mata sha tara na arziƙi, haka idan zai tafi ma,

Babu Yadda Yahanasu da malam zahiru suka Iya, Ba da son ran su ba, A wannan lokacin suka rabu da tajuddeen, Suna kuka yana kuka, gwanin ban tausayi duk da Uncle ɗin ya yi masu alƙawarin duk In suka samu hutun makaranta zai turo masu shi, hada mai aiki ya ajiye masu agidan wadda za ta ci gaba da kula dasu kamar yadda tajuddeen yake yi masu, hatta Ginin gidansu sai daya sabunta masu shi,

Bayan tafiyarsu Jos, Rayuwar Tajuddeen ta canza sosai, Yana samun kyakkyawar kulawa a wurin Uncle ɗinshi da kuma matarshi Hajiya Adama, ga kuma aboki daya samu ɗan uwan shi Uzair, wata irin shaƙuwace a tsakaninsu, kullum suna atare, dare da rana a tare Uncle abdallah ya sanyasu A university kuma Course ɗaya suke karanta 6angaren jarida, da yake ra'ayinsu yazo ɗaya, duk in lokacin hutu ya yi Sukan shirya shi da Uzair su tafi Buzaye wurin danginsu, Har hutunsu ya ƙare tunkunna suke dawowa gida,

Bayan Wani Lokaci, Tajuddeen da Uzair Su ka kammala degree ɗinsu, dama kuma tunkafin Su yi graduation, kowannan su yana da budurwar shi wadda yake da burin aure, Taj dai Wata ɗiyar hamshaƙin mai kuɗice ɗan siyasa Allah Ya haɗa shi da ita, Kyakkyawar gaske Asalinta ma half cast ce,mahaifiyarta balarabiyar Egyp ce, mahaifinta kuma Bahaushe ne gaba da baya, Sunanta Benazir Sam bata da sauƙin kai, maca ce mai matuƙar Ji da kanta, Sam bata mu'amala Da mutun idan har mahaifin shi ba shahararren mai kuɗi bane kamar mahaifinta, kuma ba'a ta6a ta a zauna Lafiya, shiyasa kowa ke shakkar shiga gonarta, ƙawarta ɗaya kwallin kwal wadda Jinin su ya haɗu da ita, amma kuma halinsu yasha banban, Aneelerh maca ce mai sauƙin kai, ita kanta ƴar masu kuɗi ce amma bata ɗauki duniya da zafi ba, Tana bin komai asannu, Ga tarin ilmin addini da take dashi, Dukkanninsu kowa da Course ɗin da ya karanta,Ita Benazir Business administration ta karanta, Aneerlerh kuwa Medicine ta karanta, tunkafin ma ta kammala karatu mahaifinta Ya gina mata Privet hospital mallakin ta, atare su ka yi karatunsu ƙasar germany ita da aneelerh, farkon haduwar su A cikin jirgi ne suka fara sanin juna, A lokacin zasu tafi Germany ƙaro karatu, sun zauna a seat ɗaya cikin jirgin, kasancewar aneelerh bata cika shariya ba, ko batasan mutun ba, takan gaida shi harma taja shi da fira, ita ta fara yi ma benazir magana suka fara fira sama sama, tana ta shan ƙamshi, sai ga shi daga baya da suka isa ƙasar germany sun kuma haduwa a University ɗaya, Sunyi mamaki daganan kuma suka ƙulla zumunci,

Bayan sunyi degree suka dawo Nigeria, Sati ɗaya da dawowar su suka shirya zuwa Shopping Mall domin yin siyayya, anan Allah ya haɗa su da Su tajuddeen suma ranar sunje yin siyayya, basu sha wahala ba, wurin samun amincewa daga wurinsu, In a short time soyayya mai ƙarfi ta kullu atsakaninsu, har takaisu ga yin aure, Wannan shine farkon haɗuwarsu, Taj bai tashi sanin wacece Benazir ba, Sai bayan da aka shafa fatihar auransu, Aka kaita Gidanshi, ta hana abokan ango shugowa Siyen baki, dama Ko time ɗin da aka kaita gidan, Family ɗinta ne zalla babu ƙawaye don bata Hulɗa da mutane, Aneelerh ce kawai Aminiyarta da akayi masu aure rana ɗaya, Sati ɗaya su ka yi suna shan soyayya, Ta iya tarairayar miji da bashi hakkin shi akan lokaci, sai dai bata Iya girki ba, kuma bata iya Gyaran gida ba, dai dai da gyaran gado wannan batasan Ya zata yi shi ba, saboda tsabar sangartata da akayi, ranar da ya yi mata complain kan cewa Tayi mashi girki sai cewa tayi, ba'a halicci Hannayen ta donsu girka ma ƙato abinci ba, tsabar 6acin rai kamar Ya rufeta da bugu bata iya komai ba, sai danne dannen waya ko salla sai taga dama take yinta don wani lokacin Sai dare take hada sallar Azahar da isha'e da magrib duk tayi su a lokaci ɗaya.Salatul fajr kuwa, Sai ƙarfe goma na safe take Yinta, idan ya yi mata nasiha sai tace "Ae ba a ƙabari ɗaya za'a binne mu ba, mommy ta sanar dani cewa in yi sharholiya ta son raina Aljanna tamai rabo ce,"

Bawan Allah taj, da yake yana sonta, haka yaci gaba da zaman haƙuri da ita, kullum shi ne Zarya zuwa restaurant Cin abin, daga bisani ne da abun ya dameshi, ya samu Uxair Ya kwashe komai game da zamanshi da Benazir Ya sanar mashi, Ba ƙaramin tausayin shi Yaji ba, a ƙarshe Yace mashi Ya daina zuwa restaurant Cin abinci, Ya dinga zuwa gidanshi suna ci, idan ma bai iya zuwa kullum zai dinga kawo mashi,

Tun daga ranar duk in Aneelerh zata Yi girki hada Taj take haɗawa, daga baya kuma Aneelerh ta fara zuwa aiki, hakan yasa suka nemi ƴar aikin da zata dinga yi masu aikin cikin gida kada abun yayi mata yawa, koda uzair ya sanarma Mahaifiyarshi hajiya adama game da neman masu aikin da zasu dinga yi masu aiki a gidanshi dana Tajuddeen, Cikin sa'a Hajiya adama tayi ma mai aikinta Esther magana akan ta nemo masu masu aiki mutun biyu, Batare da 6ata lokaci ba, Esther ta samo masu ƙannanta dake cikin buƙatar aikin yi, dama su ukune Kuma marayu, suna a Cikin buƙatar abunda zasu tallafi rayuwarsu dashi, Sai gashi Allah ya kawo masu aikin yi, Sunan ƙannan nata Ana da Janet Ana itace take aiki agidan Uzair janet kuma agidan tajuddeen,

Rayuwar Janet a gidan Tajuddeen,Ta aikatu kamar jaka a wurin benazir, Gashi abu kaɗan saita rufeta da bugu saboda tsabar Zalunci, haka ta jure zama da ita, kodan saboda albashin da take samu mai tsoka awurin Taj, Yana ji da ita mutunne mai kirkin gaske,

Tun bayan auransu da Sati biyu dai dai da rana ɗaya Taj bai ta6a jin dadin zama da benazir ba saboda baƙin halinta mahaifinta kanshi kuka yake da ita, duk Cikin ya'yanshi babu mai irin halinta, ga shegen yawon tsiya,da auranshi haka take fita Night club kuma ba yadda zaiyi da ita kusan kullum sai sunyi sa'insa da ita, hatta Cikinshi data ɗauka, ba irin maganin da bata shaba don ta zubar dashi amma Abun ya faskara, Allah ya riga daya ƙaddara zuwanshi duniya, ita fa duk duniya ba wanda ya isa yayi mata faɗa taji, wata irin bauɗaɗɗiyar macace, mai wuyar sha'ani hatta Aneelerh ta sha yi mata nasiha akan tagyara rayuwarta a karshe ma saita yaki ce aneelerh daga rayuwarta, ta ɗauki gaba da ita ko magana bata haɗa su, lokacin da Cikinta ya soma Girma kamar tayi hauka saboda ba ta san Ganin shi ajikinta, kamar ta sanya hannu ta danna shi ya baje haka take ji, Taj yasha kamata tana kokarin shan maganin don ta zubar dashi,Wanda hakan yayi silar da har su ka yi faɗa da ita kaca kaca, kuma Tace mashi koda ta haihu kada yayi tunanin zata shayar mashi da abunda ke acikinta, ashe dama jira take ta haihu tabar gidan, Shine ta tafi tabar mashi jaririya cikin kwamin wanka, dama kuma tunkafin tafiyarta, Ta kori mai aikin gidansu Janet, Batare da saninshi ba wannan kenan.........


*Boss Bature*

Cigaban Labari

Bayan sun samu natsuwa, Aneelerh ta basu shawarar su ta fi asibiti don ta duba lafiyar babyn, Ta kuma Yi mata injections ɗin da ake yiwa kowani yaro da zarar an haifeshi, domin bashi kariya

Atare suka tafi asibitin wanda Ya kasance Mallakin Aneelerh ne, Ƙaramin privet hospital acan aka duba Lafiyar babyn, tana da ƙoshin Lafiya bayan dawowarsu gida Aneelarh taso ta shayar da babyn Amma Taj ya hana saboda gudun kada Ya haramtawa ƴarshi auren ɗansu,wanda burinsu ne shi da Uzair, su haɗa Ya'yan su aure, duk da ita aneelerhn har yanzu shiru,


A ƙarshe sai dai ƙanwar maigadin gidansa ce Inna kuluwa Take shayar da ita, dama Tana Cikin shayar da jikanta da mahaifiyarshi ta rasu tabar mata, watan shi shida a duniya shima yabi mahaifiyarshi, baba maigadi ne ya bashi shawarar ya bata Babyn ta shayar da ita, baiyi gaddama ba ya amince, a ranar tazo daga ƙauyen su, Sai da aneelarh taje da ita asibitin su aka duba lafiyar jikinta tukunna aka bata Rainon Babyn, Acikin gidan taj ya ware mata haɗaɗɗen bedroon ɗin da zata zauna,

Ranar suna Yarinya taci sunanta *UNAISAH* shine sunan da mahaifinta ya naɗa mata Amma Yana kiranta da *ANGEL* a matsayin Nickname dinta, Bayan kammala sallar juma'a akayi naɗin sunan,

Tun ana saura kwana Biyu suna, Mutanan Buzaye suka zo, daga Ciki hada Mahaifiyar tajuddeen Yahanasu ta tsufa tukuf tare da mahaifinshi malam zahiru, hada kakarsu deeeje suka zo, tare da wasu daga Cikin danginshi, a daren ranar da suka ƙaraso, kowa Ya soma tunanin ina Uwar yarinyar take ne, sai a lokacin yake sanar dasu game da guduwar benazir da ta tafi tabarshi da yarinyar, Ran danginshi ba ƙaramin 6aci yayi ba, sunji haushin Abunda Matarshi tayi, dama tun fil azal basu so ya auri bare ba, sun so ace cikin dangi ya samu mata ya aura, don ba yadda zasuyi ne ƙaddara ta riga fata,

A 6angaren Taj kuwa yaso ace uncle abdallah ƙanin mahaifinshi, yana nan a ka yi sunan sai dai kash, tunda jimawa sukayi tafiya zuwa South korea, da ya ke acen kasuwancinshi yafi ƙarfi, duk da haka Sunyi waya dashi, Har video call suka kira shi don ya nuna masu babynsu, aikuwa sunsha ruwan mamakin ganin kyakkyawar ɗiyar tajuddeen, Don ita Hajiya Adama matar Uncle din, cewa tayi da zarar sun dawo nigeria zata ɗauke ɗiyarta, saboda ta raineta ko alokacin Taj bai sanar da su game da Abunda ya faru tsakaninshi da benazir ba, don baiso ya tashi hankalinsu ya bari ne sai Sun dawo tukunna Suji komai,


Alhamdulillah An kammala taron suna Lafiya, ƴan uwa da abokanan arziki sunci sun sha sun shaida Zuwan *UNAISA* duniya, aranar Tajuddeen kamar yayi hauka saboda tsabar farin ciki, domin kuwa ya samu alheri sosai awurin abokananshi, da kuma masoyanshi don hada key ɗin mota ya samu, ga kuma kayayyakin da suka dinga haɗawa ƴarsa, manya manyan akwatina na kayan baby, shi kanshi ya samu kyautar shaddoji a daren ranar sunan Tare da Uzair suka shiga ɗakinshi suna ƙirga kyaututtukan daya samu, A kalla ya samu kuɗi Sama da 3m, baya ga kayayyakin da ya samu har hawaye saida taj ya zubar, dama shanun da aka yanka ranar sunan bai ƙarasa biyan kuɗinshi ba, bashinsa yaci har uzair na gargaɗin shi akan karya ɗauki abunda yafi ƙarfinshi Ya siya masu rago kawai ya wadatar, Amma yace ina ƴar shi tafi ƙarfin rago sai dai sa.sai gashi Allah Ya rufa mashi asiri,

Sai da su Deeje sukayi Wata ɗaya Cuf tukunna suka shirya komawa Buzaye, Sunyi tunanin taj zai bar masu yarinyar ne su tafi da ita can ƙauyansu buzaye kafin Ya samu matar aure, Amma ina koda Su ka zo mashi da maganar tafiya da babynshi, Sai ya juya masu ƙeya, alamar bazai bayar ba,don dole suka haƙura, dama deejen ce ta matsa su tafi da ita,amma mahaifiyarshi Yahanasu sam bata ayyana hakan aranta ba, musamman da ta ga yadda Inna kuluwa ƙanwar baba maigadi take kula da ita Sai hankalinta ya kwanta,

Ba ƙaramin alheri taj yayi masu ba lokacin da zasu tafi, kusan abunda ya samu ya kasa uku, ya basu kashi ɗaya,Kashi ɗaya kuma yaba Uzair amininsa, Amma yaƙi kar6a saima ya ƙara mashi sunyi rabuwar arziƙi da iyayenshi Sunata sanya mashi albarka har kwalla saidaya zubar bayan tafiyarsu Allah sarki rayuwa kenan

A 6angaren inna kuluwa kuwa babyn Tana samun kyakkyawan kulawa a wurinta, duk da ba'a tare suke yini ba kuma ba a tare suke kwana ba, saboda taj da kullum yana manne da ita, sai dai fa duk lokacin da tafara tsala kukan yunwa, dakan shi yake daukar ta yakai ma inna kulu aɗakinta, Yaƙi yarda yabar mata Yarinyar Saboda ya mutu akan sonta, kona seconds baisan rabuwa da ita zuwa aikine kawai yayi mashi cikas, ba ƙaramin abu ke rabashi da babynshi ba, ko aiki yaje yana dawowa jiki na rawa ya ke zuwa ɗakin inna kuluwa ya ɗauketa, idan dare yayi kuwa dama atare da ita yake kwana, Saman kirjinshi yake kwantar da ita Su sha baccinsu,

A daren ranar wata Alhamis ne Yana zaune saman Sofa Yana danne danne acikin Laptop ɗinshi, Ya jiyo sautin dirar motoci a lokacin angel tana a hannun inna kulu, bai kaiga zuwa ya ɗaukota ba, Yana jira ya kammala aikinsa ne kafin ya Amsota don su kwanta,

Zugudum yayi yana jiran ganin wanene Ya kawo mashi ziyara a irin wannan Lokacin Kusan ƙarfe 9 na dare,

Daga wajen Falon yaji anyi mashi sallama, muryar babban mutum,

Da sauri ya kalli agogon dake manne a bango, kusan ƙarfe tara na dare, duk a tunaninshi uzairne don bai ɗauki murya ba,


hakan yasa shi ɗan ɗaga murya tare da cewa"Come In"

Turo ƙopar akayi, a hankali Ya shigo bakin shi ɗauke da sallama,

Da mamaki akan fuskar taj yake kallonshi,

Babban mutunne yana sanye Cikin kaya na mutunci na hausawa, Shadda tare da malun malun mutun mai cikar kamala,
fuskarshi ɗauke da murmushi,

Bakowa bane face Alhaji Ubaid Mahaifin Benazir Kaka Ga Angel,

Fuskar taj ɗauke da murmushi ya miƙe tsaye Yana kallonshi, kowannan su da abunda yake saƙawa aranshi,

"Taj nasan ban kyauta ba, wlh naji kunyar haɗa ido dakai," cikin sanyin murya yayi maganar, da sauri uzair ya qarasa inda yake a tsaye, ya miƙa mashi hannnu don su gaisa,girgiza kai yayi tare da cewa,

"Bana jin zan iya haɗa hannu dakai don bancancanta ba"

Tausayinshi ne ya kama Uzair, cikin sanyin murya yace"kada ka sanya damuwa aranka komai ya wuce,"

Damuwace ƙarara akan fuskarshi"ɗane ka haifeshi baka haifi halinshi ba,"

Murmushi taj ya ɗan saki, kafin ya ruƙo hannunshi zuwa cikin Falon, Suka zauna saman Sofa suna fuskantar Juna,

"Baba yaushe kuka dawo ƙasar bansani ba? ya kuma Jikin naku"?


"Jiya muka dawo, Jiki yayi kyau Alhamdulillah,wlh taj naso nazo tun lokacin da ka kirani waya ka sanar dani rashin Hankalin da benazir tayi maka, Naji takaicin abun nan ƙiris Ya rage in kwashe mata albarka" yakai ƙarshen maganar fuskarshi duk a hautsine, bawan Allah da alama Yaji jiki, tun lokacin da Taj ya haɗu da benazir kafin auransu mahaifinta baya qasar saboda lalurar da ya ke fama da ita, Na ciwon ƙafa mai raɗaɗin gaske,

Alhaji ubaid tsohon gomna ne, bai jima da hawa mulkin ba, Shekara ɗaya kacal Lalurar ta sameshi,Ba ƙaramar wahala yaci ba, Don kowa yayi tunanin bazai rayu ba kullum Ciwon nashi ba sauƙi,ƙara gaba yakeyi,Gashi mutane suna matuƙar sonshi,Yana da farin Jini sosai, adalin shugaba ne mutumin kirki Mai son talakawa, Ga kyautata masu dayawa suna tunanin Abokan hamayyarsa ne suka Yi mashi Asiri, wanda hakan yasa shi ajiye shugabancin, kuma tun daga lokacin zama Nigeria ya gagares hi,da zarar yabar ƙasar Sai yaji sauƙi, da zarar ya dawo sai ciwon nashi ya dawo sabo,tun daga nan ne yabar ƙasar gaba ɗaya tare da Iyalinshi ya koma Dubai da zama, benazir kaɗai Ya bari anan saboda auran da tayi,

"Allah ya ƙara Lafiya, Allah kuma ya kare ku daga sharrin makiya da mahassada,"

"Ameen ameen tajo, ae ina ganin saƙon gaisuwarka da kake turamun kullum ta waya, Inajin dadi sosai," shiru suka ɗanyi kafin Alhaji ubaid yaci gaba da magana"Abu biyu ya kawoni wurinka, Na farko ina mai baka hakuri game da abunda Benazir ta aikata mata, yanzu haka maganar da nake yi maka, Na yafeta acikin zuri'ata Saboda bata jin maganata, tafi karfina......"tunkan yakai ƙarshen maganar, taj yayi saurin katse mashi hanzarinshi"kada ayi haka baba, Ayi mata uziri, dukkan mu nan babu wanda yasan dalilin dayasa benazir ta gudu tabar jaririyar ta, Kowa yasan tsakanin Uwa da ɗanta akwai soyayya mai karfi, Ni nasan ba hakanan benazir ta tafi ba, Dole akwai wani abu da yayi silar tafiyarta,

Girgiza kai Alhaji ubaid yayi"bakasan halinta ba ne, ni da na haifeta ni nasan halin kayana, Tagagari kowa, halinta sak dana jatumarta,dama ƙaddara ce tasa na aurota,

Murmushi taj ya ɗan saki"Adaiyi hakuri baba,".
"Bazan bari ayi 6arna ina kallo ba, Benazir so take tajamun zagi a idon jama'a, tana so ta zubarmun da mutuncina da kuma ƙimata,sai kace ita ta haifi kanta? Babban abunda yafi damuna, bansan a ina take rayuwa ba,Gaba ɗaya ta kashe layinkan wayarta, nasa A binciko mun ita amma an nemeta ƙasa ko sama babu, Ita kaɗai tasan uwa duniyar data shiga,"dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana mayar da numfashi,

Mu haɗu a Next Page, yanzu wasan ya fara gaba ɗaya book one Introduction ne wannan story ɗin cakwakiyar dake acikin shi, is hardly to make a prediction about what wll happen next😂 ...................

*Boss Bature ✍️

Taj kuwa tuni jikin shi yayi san yi, duk da ba su yi zaman lafiya da benazir ba, hakan bai sauya komai ba na daga son da yake Yi mata, Yana jinta sosai acikin ranshi, kusan tun ranar da ta gudu, kullum sai ya jaraba kira layin ta da daddare ko Allah zaisa ta buɗe shi, Amma kullum a kashe yake samun shi,

Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mashi tunaninshi"Ka sawwaƙe mata kawai, da ta je tayi ta aikata zunubi da auran ka akanta, don nasan ba dawowa zata yi ba,"

Girgiza kai taj yayi "baba bazan Iya ba, zan jira ta ne har ranar da Allah zai dawo mun da ita nasan zata dawo ne duk mun daran daɗewa"

Gyaɗa kai Alhaji ubaid yayi"Abunda nake fata kenan Yanzu ina jikar tawa take ne? Inaso na ganta,'

"Tana hannun Inna kulu, Ƙanwar matar maigadina ce, itace ke shayar da ita"

"Allah sarki Amma naji daɗi sosai, ka ɗauko mun Jikata na ganta kafin na tafi da yake bani kadai nazo ba akwai escorts dina dake awaje suna jirana"

Amsa ma shi ya yi da toh, kafin ya miƙe da sauri Ya nufi corridor ɗin da zata sada shi da ɗakin inna kuluwa Lokacin daya ƙarasa a kwance ya samu inna kuluwa tana bacci angel kuma na kwance gefen ta an sanya mata kayan sanyi ajikinta, sai faman tsotar yatsanta take yi, Murmu shi ya saki tare da kai hannu ya ɗauketa Ya fito da ita,

Ƙarasa wa yayi tare da miƙa ma alhaji ubaid ita Wani irin farin Ciki ne akan fuskar shi "Tabarakallahu ahsanul khalikin Taj kaga ikon Allah, Yarinya ƴar kyakkyawa sai kace rainon turai wannan idan ta girma ae zata iya ciyo mana gasar miss world,

Murmushi taj ya saki yana kallonshi addu'o'i ya shiga karanto wa yana tofa mata Taj na amsa ma shi da ameen ameen har ya kammala yi mata addu'ar, Fira sosai su ka yi da surukin nashi, har lokacin Angel na a hannunshi Sai da ya ta shi tafiya ne tukunna ya miƙa ma Taj ita

"In sha Allah zan dinga zuwa akai akai ina duba jikata, Yanzu ka tura mun

Please Login or Register in order to submit comment