Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga zafi ta ko'ina, numfashin ta kanshi daƙyar take fitar dashi, atakure take jin kanta, tun tana kukan a bayyana har ta koma tanayin na zuci, Cikin disasshiyar muryarta ta soma ambaton duk wata addu'a da tazo bakin ta,
Tsawon mintuna talatin kenan, tana acikin wannan yanayin ta haɗa uban gumi, duk ta cicci je la66an ta sun faffashe, Saboda ƙuncin da take Ciki, takaici ya isheta, ta kuma rushewa da kuka tana faɗin"Wai ba kowa ne a kusa, Ku faɗamun ina ne nan! Wayyo Allah na! Danejo! daddy Can you hear me! its me ur angel, pls if u are hearing my voice, Answer me, Am really scared of being alone in this darkness......" cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar,
Wani irin raɗaɗi maƙoshin keyi mata hada ƙaiƙayi,Tana Cikin buƙatar ruwa, throat ɗinta ya bushe ƙamas,
Ƙoƙin motsa lips ɗinta tayi da niyar ta ƙara magana, Ba zato ba tsammani, haske ya soma bayyana Acikin wurin da take, nan take ta dakata da yin kuka biji biji ta fara gani kafin idanuwan nata su ka washe ta ƙura ido tana Kallon Ceiling ɗin da take fuskanta,
Dogon Ginin dutse ne mai matuƙar Girma da faɗi da tsayi, Ceilling ɗin Yayi uban soro daga inda take daƙyar ta ke iya hango ƙarshen shi, wasu fitilu ne jere can saman ceilling ɗin, hasken su ne ya gauraye Cikin ɗakin da ta ke, sauke idanuwanta tayi tare da yin ƙoƙarin miƙewa zaune, don ta samu damar ƙarewa baƙon wurin kallo,
tamkar hostel na kwanan ɗalibai haka wurin ya ke, daga 6angaren da take kwance 6angaren yamma ne tana fuskantar gabas akwai jerin gada je da a ka yi su da Metal(ƙarfe) A ƙalla sun kai goma sha biyar, single bed ne na mutun ɗaya kowane gado yana da lallausar mattress a saman shi, tare da matashin kai (pillow) da kuma duvet, launin farare, a ɗaya daga Cikin gadajen ANGEL take a zaune, tana bin kowace kusurwa ta ɗakin da kallo, akwai wasu kujeru da a kayi su da Katako zubin armchairs guda biyu dake ajiye, agaban kujerun there's a table an ɗaura wasu fitilun kusan uku a saman shi, daga tsakiyar ɗakin akwai shimfiɗaɗɗen red carpet,
Saukowa Tayi daga saman gadon Cike da fargaba take kallon baƙon wurin da ta tsinci kanta a cikin shi, juyawa tayi tana kallon bayanta bene ne madaidaici, da alama akwai ƙopa a can saman stairs ɗin, Amma daga inda take tsaye bata iya hangen ƙopar ta yi lungu,
Lumshe idanuwanta ta ɗanyi tare da buɗe su akan ƙopar dake a rufe, saman ƙopar taga an rubuta "Toilet" nan take ta gane makewayi ne, ɗakin yana da tagogi both left and right na jikin bango amma an garƙame su, ginin da alama tsohon gini ne aka sabunta shi,
A ruɗe take zazzare gray eyes ɗinta da suka jiƙe sharkaf da ruwan hawaye, long eye lashes ɗinta duk sun cukurkuɗe, dogon hancinta yayi jawur da shi saboda matsar da ya sha lokacin da take ku ka, heart shaped lips ɗinta sunyi light pink sun bushe ƙamas, gaba ɗaya ta rikice musamman da ta shafa jikin ta, a hautsine ta kalli uniform ɗin da aka sanya mata, launin baƙaƙe zaro ido tayi ganin an canza mata kaya ita a iya saninta kayan fulani ne ajikin ta lokacin da ta gudo daga hannun fulanin daji, hatta kanta kitson kalaba ne da danejo ta yi mata amma yanzu an warware mata kitson an sakar mata gashin ga shi nan a haukace har kusan waist ɗinta ya yi mata tamkar hijabi, uniform ɗin jikinta riga ce me dogon hannu takai mata har guiwarta, sai dogon wando har kasa, a bayan rigar an rubuta no 1,
Juyawa ta yi da gudun gaske ta nufi benan nan, a zafafe take tattaka matattakalar har takai bakin ƙopar sai dai a garƙame take an rufe ta,
Hankali a matuƙar tashe ta dunga bubbuga ƙopar tuntana yi a hankali tana tambayar bakowa ne anan har takai ga kai ma ƙopar naushi ta ƙafa ta hannu, tamkar ƴar dambe duk ta raunata jikin ta, Saboda ƙopar ta metal ce,
Jiri ta fara gani acikin idanuwanta ba arziƙi ta dakata tana fama mayar da numfashi, zufa ta ko'ina a kan fuskarta,
Jingina bayanta ta yi a jikin hand rail ɗin benan a galabaice, ga uwar yunwa tana ji kamar tacin ye ƴan hanjin cikinta,
Tana cikin wannan yanayin ta jiyo motsin tafiyar mutane can kuma taji alamun ana buɗe ƙopar ɗakin da take ciki, a hanzarce ta wurga eye balls ɗin ta kan ƙopar tana jira taga wata ja'irar ce ko wani ja'irin ne xai shigo, domin kuwa ta ɗaura ɗamarar yin yaƙi da duk wanda ya yi silar ɗauko ta daga saman titi ya kawota wannan wurin mai kama da prison.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka buɗe ƙopar tare da turo ta, awani slow angel ke kallon ƙafar mutanan da suke ƙoƙarin shigowa ciki, wasu gabza gabza Mutanene masu tsayi da faffaɗan ƙirji, Wata kalar ƙira gare su mai ban tsoro kowannan su na a cikin Shiga ta baƙaƙen kaya long coat har guiwa sai dogon wando, sunyi 6adda kama ta yadda ko akaifar hannunsu baka iya gani, sun sanya mask a fuskokin su, Sun 6oye ainihin halittar su, ƙafafuwansu kuwa Army boots ne suka sanya, kawunansu na sanye da cowboy hat, dai dai da ziririn gashin kansu baka iya gani ko'ina arufe ya ke, motsa lips ɗinta ta soma yi da niyar ta yi magana sai dai kafin ta yi yunƙurin furta wani a bu, idanuwanta suka sauka akan ƙafar matashin saurayin da ke ƙoƙarin shigowa, kalar uniform ɗinta ne ajikinshi baƙaƙe masu ɗauke da No 1 A halitta dogo ne fari sol da shi, kyakkyawan gaske, Droopy eyes ɗin shi farare ƙyal da su, Yana da dogon hanci, full lip ɗinsa red colour ne, yana da dimple ɗaya a gefen fuskar shi wanda ko motsa lips ɗinsa ya yi sai ya lotsa, Yana da yalwatacciyar sumar kai, ta kwanta luf har mid back ɗinsa dark brown saboda tsabar kyanshi sai ka rantse da Allah maca ce ba namiji ba,
ta yi tunanin shi kaɗai ne wuce warshi ke da wuya, sai ga wata matashiyar budurwa me sanye da black uniform no 2, itama fara ce sosai doguwa kamar angel tana da manyan idanuwa ga dogon hanci, soft lips ɗinta brownish colour ne, tana da yawan gashi ya cika kanta kamar an kifa mata kwando, tsayin shi ya haura kafadarta,
Tana ƙarasa saukowa sai ga wasu matasan ƴan mata masu sanye da red uniform kowanne da numbers a bayan rigar shi, gasu nan kala kala wasu baƙake wasu farare wasu wankan tarwaɗa, kamar yadda angel ke kallonsu haka suma suke binta dana mujiya,
A kalla mata sunkai goma acikinsu maxa kuma biyar, sai da suka kammala shigowa tukunna waɗannan GIANTS ɗin su ka fuce daga ɗakin bayan sunyi locking ƙopar,
Cikin tashin hankali angel ke bin kowannan su da kallo, can dai tace"wai uban wanene ya kawo ni wannan wurin! Menene alaƙata da ku!"nuna matasan ƴan matan ta yi da yatsan hannunta "ku faɗamun su wanene ku?kuma ina ne wurin nan? kun wani tsare ni da ido kuna kallo na" a harzuƙe ta yi maganar,
ɗaya daga cikinsu ce wannan me black uniform no 3 ta soma magana cikin harshen turanci"kamar yadda kika tsinci kanki a cikinsa batare da sanin ki ba, mu ma haka muka tsinci kan mu, abu ɗaya na sani shi ne, kurkukun ƙaddara gida ne na marayu wanda basu da gata,'
girgiza kai angel ta yi'ae ni ba marainiya ba ce, iyaye na suna araye wlh bazan zauna acikin kurkukun nan ba, i must find away to leave........" kafin takai ƙarshen xancen nata wata matashiya me ɗauke da uniform jajaye no 4 baƙa siririya tace"ba gidan cutarwa bane, gidan taimakon marayu ne zasu tallafi rayuwarki, dayawa ma anan aka rainesu tunkafin su mallaki hankalinsu, xamu samu kulawa tunda bamu da kowa kurkukun ƙaddara shi ne gidanmu"
Uwar harara angel ta wurga mata"prison will neve be a home for me, ba zan ta6a lamunta ba, taya za'a sato mutun akawo shi wani baƙon wuri sannan ace gidan marayu ne? Ta gidan ubanwa aka gaya masu cewa ni marainiya ce, da uwata da ubana kuma da dangina, ba daga sama na faɗo ba," yadda take magana rai a6ace har wani huci ke fita daga cikin bakinta,
Takun tafiya suka jiyo daga cikin ɗakin muryar wata tsohuwa tukuf suka jiyo tana faɗin"Ina Magana"da hanzari dukansu suka sauka daga saman benan xuwa cikin ɗakin hada angel,
Tsayawa su kayi idanuwansu akan tsohuwar, a tsaye take jikinta na sanye da doguwar riga mai gashi gashi ajikinta, launin ja hannunta na ruƙe da sanda fara ce tass ta tsufa tukuf idanuwanta duk sun zurma, fuskarta ta yi uban tamoji tamoji, kanta babu gashi ko ɗaya da yake baƙi, gaba ɗaya uwar hurhurace hatta jagirarta hurhura duk ta kamata, hada gemu gare ta fari fatt yadda kasan namiji, ga wani katon hanci dake gare ta, uban gi6in dake abakinta yadda kasan ƙogon dutse, haƙora huɗu kaɗai suka rage abakinta na sama dana ƙasa, can cikin kursurwar bakinta, dogayen haƙora ne ko ta rufe baki sai na saman sun leƙo waje, hannayenta kuwa xaƙo zaƙon akaifu ne haka ƙafafuwanta wasu tsoffin takalma ne launi rigarta jajaye, kunnuwanta falo falo an manna masu bari ma,
Mamaki ne ƙarara akan fuskan angel, ta ya akai tsohuwar ta shigo cikin ɗakin batare da ta biyo ta ainihin ƙopar shigowa cikinsa ba? To kodai ta saman rufi ta duro ne ?ko kuwa bango ta tsaga ta shigo?
Kamar daga sama angel ta ji tsohuwar tace"ko ɗaya! ta ƙopa na shigo ciki" ta yi maganar tare da juyawa tana nuna mata wata ƙopa dake a ɗaya daga cikin kusurwowin ɗakin,
"Nan ɗaki na ya ke, Ni tamkar uwa nake awurin ku, dayawa sunsan wacece ni saboda na shayar da wasun ku, wasu kuma na rainesu kamar DANISH da BATOOL!" ta kai ƙarshen maganar tana nuna wannan mai kyakkyawar matashin nan da sandar hannunta tare da wannan matashiyar mai kama da larabawan, sunayen su ne ta faɗi, masu kalar uniform ɗin angel,"
Angel dai wani irin kallo take binta da shi, mamakin ta ke taya akai tsohuwar take karantar abunda mutun ke saƙawa acikin zuciyarshi"?
"Ni duk ba wannan ba! Meyasa aka kawo ni gidan nan? Nifa ba marainiya bace, Ko da ace ni marainiya ce taya za'a sato mutun akawo shi cikin wannan munafukin ginin ace wai gidan marayu ne? Taya akai ku ka san cewa ni marainiya ce? That means ku ne ku ka kashe mun mahaifina kenan? Sannan ku ka raba ni da mahaifiyata itama ku ka kashe ta ko? Dama can kuna bibiyar rayuwata in ba haka ba ta ya akai ku ka san ina a hannun fulanin daji? Har ku ka tura aka ɗauko ni? wai menene manufar ku tayin hakan huh?
"Gidan kurkukun ƙaddara Gidan Marayu ne wanda suka rasa gatansu, duk yaron da ki ka gani acikin prison ɗin nan to ba shi da iyaye! Zai iyayiyuwa iyayenki sun mutu batare da sanin ki ba, sa'annan duk wanda ki ka gani acikin kurkun nan na jininsa ne ya sadaukar dashi zuwa gare mu don mu gatanta shi har zuwa lokacin da zai mallaki hankalin shi" tsohuwa ce ta kora mata wannan jawabin,
Still angel ta gaza fahimtar inda zancen ta ya dosa cikin ɗaga murya tace"If it's an orphanage, then why is it called a prison? You just wanna mislead me with your lies, I won't believe you, idan har kuna son zaman lafiya ku mayar dani inda ku ka ɗauko ni cikin salama in ba haka ba zan addabi rayuwar ku" takai ƙarshen maganar tana haki ta harzuƙa sosai,
Sauran prisoners ɗin duk suna a tsaitsaye cirko cirko suna sauraran tattaunawar baƙuwar yarinyar da su kayi tare da tsohuwa, tun da suke a gidan prison ɗin ba'a ta6a samun yarinyar me taurin kai da kafiya ba irin baƙuwar da suka tsinta yau acikin su,
"Bansan wacece ke ba, amma na lura kamar kina son wuce gona da iri, yakamata ki kiyaye harshen ki, wannan tsohuwar da ki ke gani tamkar uwa take agare mu, tun da mu ke da ita bata ta6a cutar damu ba, muna samun kyakkyawar kulawa daga gare ta, don haka bazamu bari zuwan ki ya zama silar tarwatsewar farin cikin mu ba hope u understand me!"
A wani slow angel ta juya don taga wani isasshe ne ya yi mata magana, sauke idanuwanta ta yi akan kyakkyawar fuskarshi sai ka rantse da Allah bashi bane ya yi maganar, daga ganin shi akwai izza atattare da shi,"
"Sannu isasshen me walkin sa! Kai kuma a suwa ɗan wake a hotel? am talking you are talking? duk wanda ke son zaman lafiya acikin ku, kada ya kuskura ya shiga gona ta, domin ni ba irin ku bace! Wlh uban mutun zanci kuma a zauna lafiya!"
Tana huci takai ƙarshen maganar tare da ɗauke idanuwanta daga kan shi ta mayar dasu kan tsohuwar" ke kuma tsohuwa na dawo gare ki! Ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, Kuma a faɗa mun uban wanene ya sadaukar dani xuwa gidan nan! Saboda idan na samu damar fita daga cikin sa inje in naƙasa rayuwar shi"
Lallai angel ba sauƙi a zafafe take magana tana huci yadda kasan mayunwaciyar zakanya,
Sassauta murya ta yi"idan kun saba rainawa mutane hankali kuna ɗaukosu ku kawo su cikin gidan nan da sunan zaku gatanta su, to ni ba kalar su bace, ni ba marainiya bace kuma ni bana buƙatar gatanci daga wurin ku, Gata na shi ne Allah koda kuwa bani da kowa a duniyar nan ina da Allah,"
Murmushi tsohuwar tasa ki yayin da take kallonta tace"buri ya yi kama da mutun, da ace baki yi wannan haukan ba, da bazan tabbatar da cewa ke ɗiya ce ga Zaheer tajuddeen ba, hatsabibiyar yarinyar da ta addabi mahaifinta ina da labarin ki tunkafin zuwan ki duniya"
Ruƙe qugu angel ta yi yayin da take kallonta, jin wani soki burutsi da tsohuwar ta yi mata,
"Bazan yi jayayya dake ba, saboda nasan wacece ke! abu ɗaya nake so in tunasar maki shi ne, ke marainiya ce mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan mahaifiyar ki ma ta rasu babu ita, danginki kuma su ne suka damƙa mana ke don mu raine ki wannan dalilin ne yasa kika kasance acikin Gidan kurkuku saboda mu ne gatan ki, kuma muke da alhaƙin ɗaukar responsibilities na rayuwarki, kama daga cin ki shan ki da sauransu....idan ki kayi biyayya mu kuma zamu sama maki farin ciki,"
Hawaye ne suka wanke fuskar angel jin cewa mahaifinta ya rasu duk da bata gasgata maganar dattijuwar ba cikin shessheƙar kuka tace"kiji tsoron Allah ki fada mun gaskiya daddy na bai mutu ba! Kuma ƙarya ki ke yi mun na cewa dangina ne suka kawo ni cikin wannan kurkukun,"
Matsawa tsohuwar ta yi zuwa inda angel take atsaye, ta tausasa murya tare da cewa"ƴar nan ki kalle ni tsofe tsofe dani da ace na ta6a aure da yanzu nayi tatta6a kunne dake, amma har kika iya buɗe baki ki kace mun ƙarya nake yi? Lallai babu tarbiya atare dake shiyasa ƴan uwanki suka kawo ki prison don mu koya maku ladubban rayuwa, sa'annan ina mai ƙara tabbatar maki da cewa mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan, nasan ke bakisan da hakan ba saboda ya jefa ki acikin ruwa shiyasa baki ga lokacin da ya rasu ba, idan har kina son sanin komai game da mutuwar mahaifin ki, zan fada maki hatta wanda su kayi silar mutuwar shi, amma fa ba yanzu ba sai naga hankalin ki"
Tana kai ƙarshen maganarta, bata jira angel ta bata amsa ba, ta juya tana dogara sandarta a daddafe ta nufi ƙopar shiga ɗan ɗakinta,
Zubewa angel ta yi saman guiwowinta tare da fashewa da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, gaba ɗaya ta ji ta tsani kanta, komai ya sire mata zuciyarta ta karaya dama saida ranta ya bata cewar kodai daddynta ya mutu ne, dama yasan mutuwa zai yi shiyasa ya jefa ta acikin ruwa shi kuma ya tsaya waɗannan mutanan da suka biyo su da mota suna harbinsu suka kashe mata daddynta,
Ƙara sautin kukan nata ta yi tana ambaton"Innallahi wa'inna ilahirraji'un! Wayyo Allah na daddy na! Sun kashe mun daddyna shikenan sun raba ni da farin ciki na, sun raba ni da Mahaifina sun naqasa mun rayuwata, ya Allah ka ɗauki raina nima in huta........."sosai take kuka fuskarta ta yi jawur jaga jaga da hawaye hada majina,
Duk suna tsaye suna kallonta, an rasa wanda zai lallashe ta, saboda basu saba da ita ba, wasu kuma shakkar ta suke ji yayin da wasu kuma suke jin haushinta saboda ta zagi tsohuwa wadda suka ruƙa amatsayin mahaifiyarsu,
Tuntana yin kukan nata da sauti har takai ga kakarewa muryarta ta dissashe ta, anan ta yanke jiki ta faɗi a sume.
Guntun tsoki matashin saurayin nan yaja, tare da ta6e lips ɗinsa ya yi gaba abun shi ya nufi gadon shi me ɗauke da no 2 haka kowani gado yake da number,
Suma sauran matasan suka wuce zuwa saman gadajen su, mutun ɗaya ce ta kasa tafiya saboda tsananin tausayinta da take ji, kuma ita har ga Allah yarinyar ta kwanta mata aranta,
Hannayenta bibbiyu ta sanya tare da tallabo kan angel dake a ƙasa ta ɗaura shi saman cinyarta, juyawa ta ɗanyi tare da kallon kowannan su dake kishingiɗe saman gadonshi, tsayar da ƙwayar idonta ta yi akan Hannah ta ɗan ɗaga murya tare da cewa"abunda ku kayi ba ku kyauta ba, kuna ganin halin da take aciki na rashin mahaifinta amma kowa ya yi shiru ya wuce ta babu me lallashinta?
Ta6e baki hanna ta yi"rashin mahaifi akanta aka fara rashi? tafi mu gata fa dayawan mu nan tun muna jarirai aka kawo mu kurkukun nan, mun ta shi ba mu san kowa namu ba, bamu da wanda ya damu damu tsohuwace kaɗai gatan mu, kuma agaban mu ta zageta tass ba ta ga girman gemun ta ba, saboda rashin kunya irin ta ta," Hanna na rufe baki, wani saurayi dake a cikinsu tuttu6e6e me suna haris yace"nifa bata kwanta mun araina ba, kyau kamar aljanna, kuma daga gani ma duk mun girme ta, "yana rufe baki mubeen ya kar6e da cewa"bazata wuce shekara takwas ba wannan jibi yadda take raira mana kuka kamar ba'a gama rainon ta ba,"
Gaba ɗaya suka sanya dariya, ran batool ya 6aci,
"Is enough, kunsan bana son hayani ya" wannan kyakkyawar saurayin ne da tsohuwa ta kira da sunan DANISH ya yi maganar tare da lumshe idanuwanshi ya kwantar da kanshi saman pillow,
Jinjina kai batool tayi, jiki asanyaye ta sauke kan angel a ƙasa, ta miƙe da hanzari ta nufi toilet ɗinsu, jim kadan ta fito hannunta ɗauke da ruwa sai sauri take yi saboda zubar da yake yi, adai dai saitin fuskar angel ta yarfar da ruwan, nan take taja dogon numfashi batare da ta buɗe idanuwanta ba, yatsun hannunta ne kaɗai suke kerma, miryarta adisashe take faɗin daddyna bai mutu ba, he is still alive ina ji araina sai sambatu take yi, ga wani irin matsanancin ciwon kai daya far mata ga yunwa da ƙishir ruwa duk ita kaɗai,
Cikin sanyin murya batool ta yi mata magana"SISTER" har cikin kunnanta taji sautin kiran yadda kasan wadda aka tsokano a hargitse ta buɗe idanuwanta da suka kada su kayi jawur da su, yunkurawa ta yi da hanzari ta ɗauke kanta daga kan cinyar batool, ta jefa mata uwar harara tare da cewa"bana son ganin kowa a kusa dani, bana son kowa,"


❤dedicated to Aunty kubra❤


*Daga alƙalamin Boss Bature✍️*

*E11

Tuntsirewa su hanna su kayi da dariya jin yadda ta gwasale Batool,
"Bai kamata ki yi mun haka ba, kowa yaƙi kula ki a lokacin da ki ka suma ni ce kaɗai na damu da ke amma shi ne kika watsa mun ƙasa a ido"?
Cigaba da kuka angel ta yi ba tare da tace mata uffan ba, ita kaɗai tasan raɗaɗin da take ji,
Zuba mata ido Batool ta yi batare da ƙyaftawa ba,
Adai dai wannan lokacin suka soma jiyo motsin buɗe ƙopa, gaba ɗaya suka kai idanuwansu bakin benan
Turo ƙopar a kayi waɗannan Giants ɗin ne su uku masu sanye da baƙaken kaya su ka shigo hannayen su ɗauke da Faffaɗan wooden trays masu ɗauke da kayan abincin su, kowanne na a ruƙe da faranti ɗaya,
Bayan sun ƙarasa sauko wa kai tsaye su ka nufi jan carpet din nan, a saman shi su ka sauke farantan, kafin suka ja gefe ɗaya suka goya hannayen su asaman ƙirjinsu, dama ƙa'idar aikin su ce idan suka kawo masu abinci ba su tafiya tsayawa suke yi har sai sun kammala tukunna su kwashe kayan abincin su tafi, kuma basa magana sai in ta kama dole,
one by one su ka soma saukowa daga saman gadajen su, izuwa gaban kayan abincin kowa ya samu wuri ya zauna, ruƙo hannun angel batool ta yi tare da cewa"ki taso muje mu ci abinci," fusge hannu angel ta yi" bazan ci ba, ni kawai a mayar dani inda aka ɗauko ni,"
"This is the only chance u ave to eat, we get food once a day, if u don't eat it now, u will lose ur food," cikin sigar lallashi batool ke yi mata magana, ita kuwa ta kangare akan baza taje taci abincin ba.
Miƙewa batool ta yi duk bata ji daɗi ba, taso ace yarinyar ta saki jiki da ita amma ta nuna kafiya, wuri ta samu saman carpet ɗin ta zauna,
faranti na farko Grilled Chicken wraps ne guda goma sha biyar a jere, iya adadin su, faranti na biyu kayan marmari ne nunannu an yayyanka su, a faranti na uku wooden cups ne guda goma sha ɗaya, sai jugs guda biyu ɗaya na ruwa me sanye ɗaya kuma na Lemu ne da aka hada da nau'ikan kayan marmari,
A tsanake kowa yakai hannu ya ɗauki chicken wraps ɗinsa, suna Ci suna satar kallon angel, batool dai bata ji daɗi ba, ganin taƙi tasowa taci, ga nata nan ajiye shi kaɗai, idan wani ya cinye tayi asara, in kuma ba'a samu wanda yaci ba, zasu tafi da shi ne.
baiwar Allah ta galabaita sosai, ga jaraba nacin ta ga yunwa ga kuma abinci amma taƙi ta shi taje ta xauna cikin su ta ci, wani irin ƙululun baƙin ciki ne acan ƙasan zuciyarta, eyes ɗinta a rufe hawaye ke gangarowa saman kuncinta,
Ƙasa ƙasa da murya batool ke yi mata magana"ki taso ko ci," maƙe kafaɗa angel ta yi, alamar baza ta zo ba,
A ƙarshe ma sai ta miƙe tana tangal tangal zata faɗi amma ta jure a haka ta taka izuwa gaban waɗannan Giants ɗin ta ci burki ta tsaya,
"Ku maida ni inda

Please Login or Register in order to submit comment