Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*


*Boss Bature ✍️*



_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.✍️_


Gargarɗi

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_


*E1*


Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe ɗaya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer ƙirar Samsung Galaxy ta soma ruri da ƙarfin gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na huɗu ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah, jikinsa na sanye da singlet da gajeran wando fari, aƙalla ya kai shekaru 40 a duniya. A launin fata kuwa wankan tarwaɗa ne, da ƙyar yake iya ware manyan idanuwansa a kan katafaren gadonsa kafin a hankali ya mayar da ƙwayar idonsa kan agogon bangon, tafin hannunsa ya kai tare da shafa fuskarsa cikin sanyin murya ya ambaci sunanta, "Angel!"

Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer ɗin ya ɗauki wayar, cike da mamakin wane ne yake kiran shi a irin wannan lokaci? Anya kuwa Lafiya?

Lokacin da ya kalli screen ɗin wayar sunan Aminina ne ya bayyana, ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da ɗaga kiran ya manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, "Aminina!" Kafin Ya ƙarasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ruɗe yake faɗin,"Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta ƙare."

A firgice ya dakatar da shi, "Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?"

"Sun kama ni ina yi musu leƙen asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su ƙyale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu, yana a cikin memory ɗina, ita kaɗai ce hujjar da asirinsu zai tonu..." Bai kai ƙarshen maganar ba, ɗif ya ji kiran ya katse.

A gigice yake kwaɗa masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa'a aka ɗaga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matuƙar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, "Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka." Jiki na rawa ya ɗago da wayar yana kallon screen ɗin yayin da suka canza kiran zuwa Video Call.

Saboda tsabar firgita, a ruɗe ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar ƙwayar idon za ta faɗo kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a kiɗime ya shiga furta, "No, no!" Duk ya firgice, rejecting call din suka yi.

Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arziƙi ya zube gefen gadon ya zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake yi masa daɗi duniyar nan.

Yana cikin wannan halin ha'ula'in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, "Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku." Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face ƴarsa ɗaya tilo da ya mallaka wato Angel.

A matuƙar ruɗe ya miƙe, ko jallabiya bai zura a jikinsa ba, iya key ɗin motarsa ya ɗauko saboda tsabar ruɗu wardrobe ya dosa zai buɗe a matsayin kofar dakin, har sai da kansa ya bugu tukunna ya ankare, ya nufi ainihin ƙofar, da sauri-sauri ya fito daga bedroom ɗinsa da ke a downstairs ya nufi cikin babban falon, kai tsaye Upstairs Ya haye. A kiɗime yake tattaka staircases din benen, bai nufi ko'ina ba sai ɗakin Angel, bugu ɗaya ya yi ma ƙofar ta buɗe, ko'ina duhu, kunna hasken ɗakin ya yi, nan take haske ya gauraye ko'ina, wurga kwayar idonsa ya yi kan Angel da ke ƙunshe cikin lallausan bargo, a hanzarce ya ƙarasa shiga ɗakin, tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira, "Angel, Angle my daughter!Azeezaty!" Babu alamun za ta farka, a hautsine ya cakume ta ya saba ta saman kafaɗarsa. Da sauri ya fito daga bedroom din nata, ya sauko downstairs, kai tsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke, ɗaya daga cikinsu ya buɗe ƙirar Range Rover, back seat ya buɗe ya kwantar da Angel tukunna ya buɗe driver seat ya shige ciki, a gaggauce ya yi wa motar key, a daidai bakin gate ya tsayar da motar, a hanzarce ya fito ya buɗe gate ɗin, kafin ya koma cikin motar ya fusgeta da gudun gaske. Fitar motarsa ke da wuya, wasu danƙara-danƙaran motoci kusan su shida suka nufo shantalelen titin da zai sada ka da gidansa da alama sun hango motarsa hakan yasa suka bi bayan motar da wani irin matsiyacin gudu. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda ya hangi motocin da ke biye da motarsa ta cikin mirror ɗin motar, hakan yasa shi ƙara gudun motar. La66ansa na kyarma yake ambaton La'ila'ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Shi kansa bai san inda zai dosa ba, driving kawai yake yi a makance, shessheƙar kukan Angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi, da alama ta farka sakamakon gudun ceton ran da yake yi da su, yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar, har hancinta ya fashe jini ya soma zuba.

A ruɗe take furta,"Daddy...What's happening, where are u going in this darkness night?"

Karamar yarinya ce da ba za ta wuce 11 years a duniya ba, maganarta ma daƙyar take fita saboda halin da take ciki, hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana-sanin yin aikin jarida fiye da tunanin mai tunanin, saboda shi ne silar shigar shi cikin wannan tashin hankali.

"Angel am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya ceton ki ba, Angel ba zan jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba." Yana magana cikin kuka, tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding, jini duk ya 6ata fuskarta, cikin shassheƙar kuka ta kuma cewa, "Dad! My nose is bleeding, zan mutu, gabaɗaya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa ya ji daɗi. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya sorry kawai yake iya furta mata.

Har yanzu motocin nan na biye da motarsu, lokacin da ya fara jin saukar alburushin bindiga a bayan motar a gigice ya karya kwana ya faɗa wani kurmin daji, mai duhun gaske, shi kansa bai san ina zai dosa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar, a ruɗe ya yi parking ɗin motar ya fito ya zagaya ta back seat din motar jiki na kyarma ya zura hannu ya ɗauko Angel, daga ita sai rigar barci a jikinta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, da gudun gaske yayi cikin dajin da ita yayin da take sa6e a saman kafaɗarshi. Hasken motarsa ne da ya bari a kunne yake haskaka masa gabansa, yana cikin gudun nan ba tare da ya ankara ba, ya ɗaura kafarsa saman wani ƙarfe mai tsatsa, wanda ke a tsire cikin ƙasa, kaifinsa tamkar na wuƙa, zuruf karfen ya shiga ta cikin tafin ƙafar ya 6ulo ta sama, wani irin raɗaɗin azaba ne ya kai masa ziyara, tsikar jikinsa duk ta tashi, tuni jini ya wanke ƙafarsa, sam ya kasa motsawa daga tsayen da yake a hankali ya shiga furta, "Innalallahi wa'inna ilaihir raji'un." Cikin kyarma yake ambaton hakan, muryar Angel ce ta katse shi, "Dad let's go home, nan fa daji ne, akwai kura da zagi za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?" Ta yi tambayar still tana shassheƙar kuka.

Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, "Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne." Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, "Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji." Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji,

A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin da ya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan da ta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta.

Ba ƙaramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar ɗiyarsa.

Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya faɗi a mace.

A daidai lokacin suka ƙaraso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka buɗe wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito.

Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arziƙi ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi.

Guntun tsaki ɗaya daga cikinsu ya ja, "Mala'ika ya riga mu ɗaukar ransa, ba haka na so ba."

Na gefensa ya ce, "Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir."

Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka ɗaure fuskokinsu. Ɗaya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan ɗaya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, "Miƙo mini galon ɗin fetur tare da lighter." A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu.

"Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abu ne mai sauƙi." Bai kai ƙarshen maganar ba, aka miƙo masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur ɗin a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi.
Dalilin da yasa za mu ƙona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu.

Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus

*Boss Bature ✍️*

dedicated to Aunty kubra😘


*E2*

_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.✍️_


Gargarɗi

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_




The Begining Of The Story,(Farkon Labari)

ƙasa ƙasa Cikin baccinsa ya soma Jin sautin kukan Jariri acikin kunnuwan shi, tun abun bai damun shi har kukan Ya fara addabar shi, ya hana shi sakat wanda Hakan Yayi silar farkawar shi daga bacci, a hankali ya ɗan ware manyan idanuwan shi masu ɗauke da Bacci don da alama bai gaji da baccin ba, Ceilling Ya ƙurawa ido kamar mai karanto wani abu, a ƙoƙarin shi naya tariyo abunda kunnuwanshi ke jiyo mashi wanda Yayi silar farkawar sa daga Bacci,


Yana ƙoƙarin tunanowa Kwatsam Yaji kukan Jaririn Inya inya, mai sautin gaske, Zumbur ya ƙarasa Janye Blacket ɗin daya Lullu6a dashi Yayi wurgi dashi gefe ɗaya, kayan Bacci ne Ajikinshi Brown Colour Riga da wando, yayi mamakin ganin babu ita asaman gadon, ko ina taje ne? sauko da ƙafafun shi ya yi ƙasa ya yi, Cike da fargaba Ya miƙe yana mai tunanin Inda aka samu Kukan Jariri Acikin Gidansa, Shi dai A iya sanin shi Matar shi bata haihu ba,duk da cikinta nata yakai wata tara,


Gaba ɗaya ya ruɗe Yama rasa Ta ina zai ga Jinjirin dake kuka, Domin kuwa sautin ya karaɗe Ɗakin nashi,zukunnawa Ya yi tare da leƙa ƙarƙashin gado, wayam baiga komai ba miƙe wa ya yi da sauri ya nufi wardrobe Ya buɗe ya zazzago da kayan dake acikinta, duk a ƙoƙarin shi naya gano inda aka samu kukan Jariri aɗakinsa, Tuni ya haɗa uban gumi ajikinshi, aran shi harya fara tunanin kodai Aljanune!? abu kamar wasa idan jaririn yayi kuka sai ya lafa ƙasa ƙasa,wannan karan Yanayin kukan tamkar Ana zare Ranshi ne, har wani jan kukan akeyi inyaaaaaaa,

"Ka duba toilet"?zuciyar shi ce tayi mashi tambayar, shiru ya ɗanyi kamar me tunanin wani abu,tun da yake arayuwar shi wani abu bai ta6a tsorata shi ba irin na yau, kukan jaririn duk ya firgitar da shi,har wani gumi ya haɗa,

Ja da baya da baya yayi a hanzar ce Ya juya gaban Faskeken Madubin ɗakin, Wayar shi ya ɗauko yana dannawa Call logs Ya shiga, missed calls Ya tarar Na Uzair, babban amininsa

Calling Layin yayi tana fara ringing, uzair ya ɗaga kiran ko sallama baiyi ba ya soma magana"Uzair Akwai matsala Cikin gidan nan fa!" muryarshi na kerma yayi maganar,

On the other hand Uzair yace"Wata irin matsala kenan?
  "Kukan jariri ne Ya tashe ni daga bacci,Bansan a ina aka samo kukan ba, kuma na tashi banga benazir ba"

"Ka kwantar da hankalin ka, Gani nan zuwa"
  "Yawwa,dan Allah kayi sauri" rejecting call ɗin yayi kafin Ya ajiye wayar saman bedside drawer,


Walking Slowly Ya nufi hanyar toilet ɗin Cike da fargabar abunda zai taras, cikin sanɗa yake yin tafiyar, jikinshi na kerma,a hankali ya ruƙe Handle ɗin ƙopar ya buɗeta

  Haɗadɗen toilet ne Ko'ina Na Cikinshi Fari ƙal atsaftace ba ƙazanta, kamar ance Ya kalli ƙasan tiles,Ba zato ba tsammani Yaga ɗigon jini, Gaban shi ne Yayi wani irin mugun bugu ji kake daram! a firgice Ya ɗago da idanuwan shi yana kallon Cikin toilet ɗin,Wani irin tsoro ne Ya kama shi lokacin daya hango Jikin Bathtub(kwamin wanka) jaga jaga da Jini kamar an yanka ɗan akuya, a ruɗe ya soma ambaton Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un, kamkar a mafarki yake kallon Lamarin, Cike da fargaba ya ƙarasa shiga cikin toilet ɗin don ya gane wa idanuwanshi, a dai dai bakin kwamin wankan Ya tsara turus, Yana Kallon Jinjirin dake Acikinsa kwance,duk jini Ya wanke jikinshi Sai tsanyara kuka Yake yi,
   Lokaci guda gabanshi Ya faɗi rass tunawa da wasu maganganu da suka tsaya mashi aranshi tun shekaran jiya
 
  Tuni ya karaya hakan na nufin a daren Jiya ta haihu acikin toilet, saboda ƙarfin hali irin nata har ta iya haihuwa da kanta ta kuma Gudu duk da irin Jinin da ta Zubar, abun yayi mugun ɗaure mashi kai, ga wani irin ƙunci da yake Ji acan ƙasan Zuciyarshi, Tuni hawaye sun wanke fuskarshi, sam bazai juri ganin jaririn shi a cikin mawuyacin hali ba, sosai ya fashe da kuka tare da kai hannayenshi cikin bathtub ɗin Ya ɗauko Jaririn, bai damu da kayanshi su 6ace ba ahaka ya ƙanƙameshi ajikinshi yana shar6ar hawaye,

"Taj!taj!! muryar amininsa ce da alama sun shigo cikin gidan, Atare suka faɗo Cikin ɗakin nashi a fujajen, Su Biyu ne shida Matarshi wadda ke sanye Cikin Jallabiya baƙa, Ta yafa mayafi akanta, farace tass doguwa,Shi kuma Uxair din, Jallabiyace ajikinshi brown color

Shigarsu keda Wuya Sai gashi Ya fito rungume da jaririn a ƙirjinshi,

Aruɗe suke kallonshi, murya na kerma Aneelarh tace"Ta haihu ne"?
Tunkafin ta rufe baki Uzair ya kar6e da cewa"Meya ke faruwane taj?wannan Jaririn fa?Kodai ta sauka ne"?
  Daƙyar ya iya daidaita natsuwarshi ya soma magana"Ita ce tabar mun shi, nima bansan meya faru ba, kawai naji kukan jariri, shine ma Ya tashe ni daga bacci,a toilet na sameshi cikin bathtub"
  Atare suka haɗa baki suna salati, Kafin Aneelarh ta kar6i Jinjirin Tabi ta gefenshi ta nufi toilet don ta gyara mashi jikinshi,

Uzair kuma Yaja Hannun Taj suka fito falo, tsayawa Sukayi suna fuskantar Juna, ran kowannan su a6ace,
  "Amma dai matar nan anyi ƴar akuya, dama can Ni bata kwantamun araina ba, In banda daƙiƙanci taya laifin ka zai shafi abunda ke cikinta"?

tun kafin yakai ƙarshen maganar taj ya katseshi da cewa"Laifin me nayi mata Uzair!? meyasa wasu mutanan basu da tunani ne?sun ɗauki duniya wurin zama,Suna manta cewa wata rana dole su koma Ga Allah, kuma zasu yi bayanin duk wani abu da suka aikata mai kyau ko mara kyau," dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yaja numfashi kafin yaci gaba da magana,. 
   "Benazir Ta ƙona mun rai, bazan ta6a yafe mata ba, Allah ya isa tsakanina da ita,Ta nuna mun rashin imaninta ƙarara akan Jariri na, In sha Allah Zata ga Sakayyar hakan......"kafin Uzair Ya kuma Furta wani abu, Sae ga Aneelarh Ta fito hannunta ɗauke da jaririn cikin lallausan towel fari, wani irin farin Cikine akan fuskarta,tunkafin ta ƙaraso wurinsu ta soma ambaton"Tabarakallahu Ahsanul kaliqin, Tunda nake amsar haihuwa a asibitin mu ban ta6a Cin karo da kyakkyawar Jinjira ba, Irin wannan Hurul ainin dake a hannuna ba....

A sukwane Uzair da Taj suka kalli juna kafin suka mayar da idanuwansu kanta,
  "Am just Speechless wlh, Ka gode ma Allah, Da Benazir bata yi tunanin kashe maka itaba, da kuwa munyi Babbar asara,"takai ƙarshen maganar adai dai lokacin ta ƙaraso gabansu,.

  Slowly Taj da Uzair suka ɗaura Idanuwan su kan Jaririyar, Saboda tsabar Kyanta har Razana saida Suka ɗanyi, Babu wanda yayi tsammanin ganin jaririyar haka, farko ma sun yi tunanin Namiji ne saboda hankalinsu ba'a kwance yake ba, ashe ta maca ce,

Fara ce Sol har wani shining skin ɗinta take yi saboda tsabar haske, Natural Beauty ce, Bakomai yafi jan hankalin su ba, face Ƙwayar idonta (vivi gray) mai launin ruwan Toka ash Colour, ta ciza har ƙyalli take Yi, Sumar kanta Brown Colour ce Curly mai nannaɗa, har saman goshinta wani kwantaccen gashi ne, kuma kan nata acike yake da yalwataccen gashi, ga dogon hanci Allah ya bata, ga kuma Ƙaramin baki, mai ɗauke da siraran la66a Pink colour kamar an shafa mata jan baki,

Saboda tsabar farin Ciki,taj Ya kalli gabas Yay sujjada Yana kuka Yana Gode ma Allah.

"Ka fara tsarka ke jikinka mana,"Uzair ne yayi mgnr.

Murmushi suka saki gaba ɗayansu a ya yin da suke Kallon shi,
  "Ina taya mu farin Ciki sosai, Aneelarh Wannan kyautar Allah ce agaremu, Naji dadi da Benazir batayi tunanin kashe jaririyar ba,
  Murmushi aneelerh ta ɗanyi"Ji nake kamar nafi mahaifin Yarinyar Farin Ciki, yau Rana ce me cike da tarihi, Ranar da Taj Ya zama Uba,
  Murmushi suka kuma saki atare,A lokacin Taj ya ɗago daga sujjadar, hawaye sharkaf akan fuskarshi, Bazai iya misalta irin farin cikin da yake Ciki ba,

Miƙewa Yayi tsaye Ya koma gabansu, hannu ya miƙa ma aneelerh ta bashi babyn, maƙe mashi kafaɗa tayi, tare da yi mashi nuni da idanuwanta, sai lokacin ya tuna da yadda jikinshi ya ke, duk ya 6ace da jinin babyn sa daya ɗauke ta ɗa zu, Mirmishi ya sa ki da sauri Ya kama hanya zuwa

Please Login or Register in order to submit comment