Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiyar Zuciya tai ta soma takawa ta kusa isa rumfar ta tsaya sakamakon kallon da Aliyu ke mata taji Sam bazata ita 'kasarawa ba sai kawai ta juya ta nufi gate din gidan.

Mikewa Aliyu yai yana bin bayan ta batare data sani ba ta tsaya amma securities sun hana ta shiga saita cire likaf gurin wa tazo yar waye ita wa take nema.

Tambayoyi masu ban haushi suka rika yi mata wacce bata basu amsar ko daya ba ta juya zata bar gurin kusan karo sukai da Aliyu da sauri a firgice ta ja da baya tana yada littafin.

Rawa sosai jikin ta keyi wanda kana gani kasa ba kamarar tsorata tai ba , ba ganinsa ne ya tsorata ta ba karon da suka kusa yine.

Daukar littafin yai yana kallon ta kafin ya danna wani abu dake ri'ke a hannun shi saiga gate ya bud'e da kansa.

'kamewa masu tsaron kofar sukai tare da bashi girma bata littafin yai dakyar ta karba tana shiga.

Kallon su yai yana cewa "wannan yarinyar 'kanwa tace kada ku sake hana ta shiga daga yau".

Cikin girmamawa suka ce "yes Sir".

Juyawa yai bai shiga gidan ba ya koma gurin Samir wanda yake kallon su yana mamakin wanne kalar so Aliyu yake wa 'yar uwarsa bai ta'ba gani ba Aliyu yayi matukar damuwa da Zainab sonta a jininsa yake yawo.

Da sallama ta shiga katafaren parlon wanda Afifah dama tana jiran tane ta dau ado kamar saurayinta ne zai zo ganinta.

Daidai ta sauko daga stairs hango Zainab yasa da gudu ta sauko tana .

"Oyoyo oyoyo Aunty zee oyoyo gaskiya nayi murna aosai yau kin zo min ziyara sannu mu karasa parlon".

"Amma ina mummyn ku"?.

"Tana part dinta".

"Gaishe da ita nake son yi kafin na tafi".

"Ok muje part din nata sai ki gaida ita".

"Amma da kin kirata".

"Meyasa"?.

"Saboda Kinga baki sani ba ko tana wani uzurin".

"Kai babu abinda nake muje".

Shiga sukai suka sameta a parlor tare da Daddy suna zaune abinsu Husnah na gefe tana rubutu.

Da sauri Zainab zata juya Afifah ta riketa tana cewa.

"Haba dan Allah".

Tsayawa tai tana juyowa tai sallama amma taki fitowa normal tana bayan Afifah kamar wacce tai laifi".

"A'a Zainab kin shigo kenan ai Afifah ta fad'a min zaki zo"?.

Durkusawa Zainab tai tana gaida su mummy tace.

"Ya da ra'bewa ki shigo sosai mana".

Daddy kam cewa yai "nidai bazan karba daga nan ba".

Matsowa tai tana d'an zama a kasan carpet ta gaida su day fara'arsu suka amsa mata lallai yarinyar nan akwai nutsuwa sanadin rabarta da Afifah keyi yasa itama ta kasance mai hankali suna godiya da samunta matsayin 'kawar yarsu.


Bayan sun fita Daddy ya kalli mummy yana cewa "ni dai ina yiwa Aliyu kwad'ayin yarinyar nan saidai kinsan jiki da jini ba lallai tai masa ba".

Numfasawa mummy tai "haka ne amma ai ba shi zamu biya ba mezai hana kawai muyi magana a junan mu damu da iyayen ta".

"Haka ne kema kin kawo magana amma bana son abinda zai zama damuwa a tare dasu damu gara a fara tuntubar sa idan yana ra'ayi shikenan idan yace a'a sai a 'kyale shi".

"Aiko nasan Aliyu da son mace mai tarbiyya bazaice a'a ba domin yasha fad'a min kudi basu bane samun mace ta gari shi yake so kuma ma bayan haka yace min yana da wacce yake so".

"A ina take"?.

"Ni kaina ban sani ba domin bai fad'a min saidai na sake tambayar sa".

"To ki tambaye shi ina fata ta kasance wannan yarinyar ce ina so ta zama daya daga cikin ahli na".

"Amin alhaji Allah ya amshi rokon ka".

Zainab suna fita parlor ta mayar da likaf dinta dariya Afifah tai "kai dan Allah a gida ma ko dama haka kike zama ko a gidan ku"?.

"A'a".

"Oh anan saboda akwai samari a gidan"?.

"Eh".

"To meyasa bakyason a kalli fuskar ki".

"Saboda na tsare kaina daga shiga fitina ina yiwa Wanda zan aure tattalin kaina da taya shi kishi".

Dariya sosai Afifah keyi tana kuma tafa mata tace.

"Gaskiya ne Zainab ni kaina da nake mace kuma kawar ki zan iya kirga sau nawa naga fuskar ki".

"Marshall na tambaye ka"?.

"A'a ni karka tambaye ni๐Ÿคจ".

"To shikenan in fad'a maka wani abu"?.

Ba tare da Aliyu ya d'ago ba yace "bana bukatar ji ka rike kayan ka".

"Aiko wallahi saina fad'a dama akan batun kane da Zainab".

"Meya faru"?.

Hade rai Samir yai yana cewa "bazan fad'a ba yanzu nan ka dizga ni ba baka so kaji ba kace min"?.

"Eh haka nace but na dauko shirme zakai min".

"Eh ai dama shirmen zan fad'a maka gaskiya ka burge sosai".

"Game dame kenan ban fahimce kaba"?.

Gyara zama Samir yai yana cewa "akan mu'amalar ka da Zainab nake nufi banyi tunanin zaka iya fad'awa tarkon sonta har kamar haka ba".

"Oh haka ne"?.

" 'Kwarai gaskiya na gode da nunawa 'yar uwata 'kauna da kake ita ma ina taya ta murna da samun ka matsayin miji da tai".

"To mun gode yayan mu".

"Kai yayan ku"?.

"Eh babban yayan mu".

"Baban yayan ku kuma wa kenan"?.

"Ina wani bayan kai".

Ihu Samir yai yana kallon Aliyu yace.

"Rufa min asiri wanne yaya Marshall ka barni kawai matsayin Samir dina ina ganin hakan zaifi".

"A gurin ba".

"Kaima hakan take a gunka".

"To naji ina son zuwa gurin hajiya".

"Wai rigimammiyar hajiyan mu kake fad'a"?.

"Eh ita".

"So kake yau ka kwana da ciwon kai Kenan"?.

"Eh dasu nake son kwana ka tashi muje idan mutum na neman arziki dole saida kyautatawa balle babban abu mai muhimmanci irin jikar ta lallai ahlin ku yayi dace da samun ta kasancewar ta cikin ku ba 'karamin haske bane shiyasa a duk sanda nai sallah nake ro'kon Allah ya nuna mini ranar da zan mallake ta a rayuwa ta na samu kyakkyawar zuri'a daga gareta bayanba ni da wani buri Samir๐Ÿ˜’".

Kallon sa Samir yai farin ciki fal ransa na jin yabon da yakewa yar uwar sa yace.

"Ayya karka damu Aliyu insha Allahu zai tabbata wata rana zaka bude idanu kaga Zainab a gidan ka matsayin matar auren ka".

"Allah yasa Samir".

"Amin muyi sauri mu isa gurin hajiya kafin wancan yarinyar ta gano mu".

"Wacce yarinyar kake magana akai"?.

Nunata Samir yai da hannu tana tsaye a bakin wani shago tana sayayya".

"To kai meye damuwar ka da ita da har baka so ta ganka".

Sauke numfashi Samir yai yana cewa "wai dan rainin hankali sona take 'kiri 'kiri ta tare ni tana fad'a min".

"Eh kaga laifinta 'yar uwar Amira ce".

"Ni kuma ai batai min saboda kula kulen samarin ta sunyi yawa".

"Saika fito fili ka fad'a mata cewa ba ita kake so ba tai hakuri dan me zaka takura kanka".

"Shikenan shawarar ka zanbi bari mu fito daga gun hajjaju" shiga gidan sukai yara da manya sai kallon Aliyu suke suna nuna bakin ciki da 'kyashi muraram.

Tsaki Mairo tai bayan shigar su kofar hajiya ta kalli Kaltume dake daurin tafarnuwa tana cewa.

"Gaskiya Hauwa anyi muguwar mace wannan ran mutuwar ta za'a kallo"๐Ÿ™Š.

"Da akai mefa" Kaltume tai maganar tana aje daurin cikin son jin 'kwa'kwaf ta sake matsawa kusa da Mairo tana cewa.

"Kawar arziki fad'a min abinda ya faru".

Kasa Mairo tai da muryq tana cewa.

"Baki gani bane magana nake akan yaron nan Aliyu da suka shigo tare da Samir............

Daidai Zainab zata fito jin abinda suke cewa yasa ta tsaya cak jikin ta na 'bari cikin damu da tashin hankalin meyasa Aliyu zai shigo mata rayuwa gabadaya tundaga ranar da yan gidan nan suka fuskanci yana sonta suka kafa mata 'kahon zu'ka daga 'yar matan harda manya iyayenensu.....

Shiru tai tana sauraron su bangare guda hawaye yana zuba tana gogewa.

"Jin sun fashe da dariya yasa ta dawo daga tunanin da take.

Jin mairo na cewa "ke wallahi da gaske nake Hauwa asiri taiwa yaron nan.

Har suka bar gurin Zainab na tsaye ta kasa gaba ta kasa baya goge fuskarta tai tare dasa likaf dinta ta fito daga gidan kai tsaye gidansu Aliyu ta nufa ranta a 'bace da yake securities yanzu sun rika sunsa wace ita da matsayin yasa tun kafin ta karaso suka bud'e mata kofa.

Tana shiga kuwa tai sa'a ya fito daga ciki yayi mamakin ganinta amma saiya share domin yasan ba dan shi tazo ba maybe gurin Afifah ne.

Rumfar motoci ya wuce yana budewa ya shiga dama anguwa zaije da yanzu ya wuce ma Samir ya tsaya jira ya shirya sai kuma yai Kiran yace ya fito yana kofar gida.

Ya tada mota kenan yaga ta nufo inda yake bai tsaya ba saida ya shawo kwana da motar yazo saitin ta sannan ya tsaya tare da sauke glass dama ba komai take gani ba sai hoton ta cikin glass din saifa yanzu daya sauke.

Cikin alamun tambaya yace "yadai ko kema anguwar zaki raka ni"?.

Kaita girgiza hawayen da ke tare a idonta ya fara zuba ba ganin fuskarta yai ba dan haka baisan kuka take ba Saida ta fara magana.

"Aliyu dan Allah meyasa ka shigo cikin rayuwa ta meyasa ka hana naji dadi meyasa ka zaba min na rika kwasar bakaken maganganu wanda Sunfi karfin kaina ya dauka na rokeka ka rabu dashi".

Da bai kashe motar ba saida yaji abinda tace ya fito daga ciki yana kallon ta maimakon ya bata amsa sai tambayar daya jefa mata cewa.

"Kuka kike"?.

Shiru tai ta kasa magana sai kukan nata da yake kokarin fitowa fili amma tana danne shi.

"Ba dake nake ba? Ko ban kai matsayin da zaki fad'a min matsalar kiba"?.

Da sauri ta girgiza kai tana sauke kanta kasa.

"Meye damuwar ki"?.

"Damuwa ta Aliyu ka je kacewa su baba ka fasa aure na".

"Why"?.

"Dan Allah Aliyu ka taimaka"".

"But why"?.

"Aliyu".

"Suna na kenan fad'i abinda kike son fad'a".

Sauke numfashi tai tana cewa "kayi hakuri kaje kacewa su baba ka fasa aure na".

"Shine abinda kike so"?.

"Eh ka taimaka".

"Karki damu zanyi hakan".

"Nagode Aliyu nagode sosai".

"Ba matsala jeki abin ki komai ya wuce".

Kaita jinjina cikin jin dad'i tana juyawa zata fita hango Afifah tai tsaye jikin wata flower๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐ŸŒทtana kallon ta amma fuskarta sam babu fara'a.

Dakatawa tai a saitin ta tana cewa "Afifah lafiya kuwa"?.

'Dan dauke kai Afifah tai kamar bazata bata amsa ba sai kuma tace.

"Lau nake".

Da mamaki Zainab ta sake kallon ta jin amsar data bata yasa dole ta sake matsawa kusa da ita tace.

"Akwai abinda ke damun ki"?.

"Babu kinga wani abu ne"?.

"Afifah nayi miki laifi ne"?.

"A'a nace kin min laifi ne"?.

"Baki fad'a ba amma labarin Zuciya".

"to Zainab me kike so bace bayan aikin gama ya gama kince yaya Aliyu ya yanke alakar auren ku a ganin ki kin kyauta min Zainab shin kinsan irin son da yaya Aliyu yake miki kullum burinsa ya mallake ki shine zaki masa sakayya da haka nagode ba damuwa kiji dadin rayuwar ki yaya Aliyu ya fita a ciki dama shine matsalar ki".


Barin gurin Afifah tai wanda Zainab ke kwalla mata kira Amma ko kadan bata juyo ba tai cikin gidan jikin Zainab a nace ta fita daga gidan da tunani kala kala a Zuciyar ta.

Saida tazo saitin kunnenta ta rafka gud'a kamar zata cire hanci tana cewa.

"Allah yayi amarya zee zee yau ranar kice zaki zamo mata a gidan jarumi Aliyu Marshall na taya ki da murna".

Ganin kanta a sunkuye bata d'ago ba yasa Murja zama kusa da ita tana rike hannunta tace.

"Zainab ya dai? Lafiya naga kamar bakya cikin walwala me ya faru"?.

Hawaye ne ke saukawa Zainab lokacin data d'ago tana kallon Murja cikin kuka tace.

"Aunty Murja mai zance yau ranar tashin hankali ce a gare ni ranar damuwa bansan yadda zan kwatanta miki ba amma zan so ace mafarki nake ko ace ba gaske bane".

"Meyasa Zainab amma Aliyu kin san shi sani na ha'ki'ka da familyn sa ga 'kanwar sa Afifah 'kawar kice to meye abin damuwa"?.

"Aunty Murja nasan da haka saidai ba wannan ne damuwa taba Aliyu yafi karfi na ba sa'an aure na bane bakiji irin zagin da akewa mahaifa na ba wai sun hana ya sayyadi aure na sun bi kud'i da son Zuciya".

"Humm lallai kema Zainab indai zaki biye bakin mutane baza ki ta'ba yin abin arziki ba ki toshe kunnen ki kada ki kula kowa ki rabu dasu 'yan bakin ciki ne da haddasa ko sune suka samu dama irin taki baza suyi wasa ba".

"Amma aunty Aliyu fa shine wanda zan aura".

"Na sani Zainab ba wanda zaki aura ba saidai kice Wanda kika aura domin kin riga kin zama matar sa tun awa biyu daya wuce".

Wasu Sabin hawayen ne masu zafi suka sake zubo mata tana kallon Murja tace.

"Yanzu wai shikenan fa daske na zama matar aure? Kuma a hakan ma wai matar Aliyu"?.

"Ba fa wai bane Zainab kin zama kuma muna fatan gidan Aliyu idan kin shiga keda fitowa sai a makara".

Zumbur Zainab ta mike tana girgiza kai tare da fara tafiya zuwa jikin window tana cewa.

"Dan Allah aunty Murja ki shiru bana fata Aliyu ba mijin aure na bane".

Mikewa Murja tai tana zuwa inda take tace.

"Zainab kada ki sa'bi Allah dan ya baki ni'ima ki butulce masa maimakon godiya kin manta yana daukaka Wanda yaso cikin bayin sa meye yasa bazaki tuna da haka ba kefa malama ce".

"Aunty Murja ki fahimce ni".

"Na fahimce ki Zainab kiyi shiru haka kinji, kuma kinsan wani abu...........

Shiru Murja tai tana kallon Zainab ganin ana Kiran wayar ta amsa ta'ki dagawa.

"Ki dauka mana".

Kai Zainab ta girgiza zata fita a d'akin aunty Murja ta riketa tana dauko wayar ta daga cikin had'e rai ta mi'ka mata.

Karba Zainab tai tana karawa a kunne saidai maimakon taji magana sai 'karar TV kadai take ji sauke wayar tai tana kallon Aunty Murja.

"Meya faru"?.

Girgiza kai Zainab tai "Babu komai".

"Amma ai banji kinyi magana ba".

"Shima ba maganar yai kawai karar TV naji".

"Zainab kina da matsala baki magana ba shine zai miki yanzu kina kasan sa dole ki masa biyayya".

Numfashi mai d'umi Zainab ta sauke tana maida wayar tare da yin sallama muryarta na rawa.

Daga can bangaren Aliyu dake zaune gaban laptop yana kallon ta tun lokacin da aunty Murja ta shigo kuma yana jin duk wata magana da suke yace.

"Kina malama amma sai an tuna miki cewa kina kasan mijin ki a tunani na kece zaki fad'awa wani haka"?.

Shiru Zainab tai tana sauraron sa ta kasa cewa komai.

"Me yasa kikai shiru ki bani amsa? Kinsan abinda yake bani mamaki dake?.

"Kina da cika baki amma wani lokacin kamar mai jinnu haka kike meye matsalar ki?.

"Kodan bana bukatar jin komai zaki bayani idan an jima zanzo ki tanada min wasu amsoshi da zan tambaye ki"?.

"Kina da kyau mai haskakawa ina alfahari da na sameki matsayin mata ta ina sonki ki kula min da kanki".

'Dif ya kashe Kiran Wanda ita kuma Zainab ta sankare a gurin ta kasa daga koda motsi.

Murmushi Murja tai tana rike hannunta tace.

"Zainab ki godewa Allah ya baki miji na gari Aliyu na matukar sonki kiyi tunani kafin yazo".

Tana gama fadin haka ta saki hannunta ta fice shiru Zainab tai kanta na juyawa da tunani kala kala mai zai kawo Aliyu ga mutane da 'baki yau tana cikin matsala komawa bakin gado ta zauna tana kalle kalle take da mamakin ta ina Aliyu yake ganin ta amma bataga wata alama ba.

Bayan sallah isha Aliyu ya fito part dangi na zaune a main parlor ganin yasa suka fara yaryara masa gud'a.

Tayi tunanin idan ta fito a zaton ta zata ganshi sai kuma ta tarar ya fita sauke ajiyar Zuciya tai cikin jin dad'i saidai me zata dau hijab dinta taga baya nan mamaki ne ya kama ta tasan akan gadon ta aje ta shiga toilet.

Kiran daya shigo wayar tane ya dakatar da ita daga duben da take ganin mai Kiran yasa sabon mamaki fil a leda ya sake kamata ta daga Kiran kafin tace wani abu taji yace.

"Sorry nine na taho da hijab dinki je d'aki na ki dauka nina fita".

Yana fadin haka ya kashe d'an bata fuska tai kafin ta fita daga d'akin ta bude kofar bedroom dinsa ta shiga turus tai ta tsaya guri daya tana kallon yadda ya kwanta yabi lafiyar gado idansa a rufe yace.

"Ya kika tsaya gashi nan kizo ki dauka".

'karasa shigowa tai tana zuwa bakin gadon duk tsikar jikin tane taji yana tashi sakamakon sanyi da yaiwa d'akin yawa kamar baza tace komai ba sai kuma tace.

"Amma wannan sanyin yayi yawa baka tsoron yasa ka mura"?.

'Dage gira yai yana kallonta yace "zo ki dau remote din ki rage min amma kafin nan bari na d'an lullu'ba da hijab dinki".

Tana kallo ya ja hijab din ya rufe jikinsa duka yana cewa.

"Nikam na shiga kwana saida safe please ki rufe min kofa sosai idan kin fita domin tsoro nakeji".

Mamaki ya kamata har batasan lokacin da tace.

"Tsoro dai"?.

"Eh tsoro kinga laifi nane"?.

"A'a kamar ba namiji ba"?.

"To da me kika dauke ni mace"?.

"A'a amma kai fa soja ne"?.

"Eh du da hakan".

"Amma..........

"Amma me? Kinga malama sanyi ya fara ratsa ni zoki rage min".

Hannu tasa zata dauka ya riketa tare da yaye hijab din yace.

"Wacce kalar sallah zaki ne"?.

Muryarta na rawa tace.

"Nafila ce".

"Oh na gane to yanzu dai ba wannan ba nima ina so na koya miki wata nafilar mai matukar lada".

"Nafila"? Ta tambaye shi".

"Eh nafila 'karasa hawowa gadon mu fara a aikace".

Jin abinda yace yasa da sauri taso kwace hannunta ta matsa baya amma ta kasa saima ji tai ya jawota ta fad'o gado".

"Ya haka? Please Aliyu ka 'kyale ni".

"Ya haka kamar ya? Dan kawai yau daya zaki taya ni kwanan".

Zaro ido tai tana kallon sa cikin firgici jin abinda yace yasa ta soma girgiza kai tana cewa.

"Na rokeka ka barni na tafi".

"Na barki kije ina"?.

"Na tafi d'aki na".

"Ok da yake nan a jeji kike ba haka ne".

"A'a".

"To indai ba son maimaita magana kike ba zaki iya yin shiru ๐Ÿ˜ฒ.

Rungumo ta yai wanda hawayen ta dazai sauka ya diga akan fuskarsa dage mata gira yai tare da murmusawa wanda tana ganin murmushin ta fassara shi.

"Yadai kina jin dadin ki irin wannan hawaye haka da suke zuba amma da kin baiwa kanki shawara ba yanzu ne lokacin kuka ba sai anjima bari kuma ki gani".

Jin da gaske ba mafarki take ba yaja zip din rigarta yasa da karfi ta runtse ido tana 'kankame jikin ta juyar da itan dayai yasa ta bude ido ta kalleshi shima ita yake kallo kafin ya kalli agogo yana cewa.

"9 o'clock muje zuwa kamar karfe uku na dare muga abinda zan iya yi kin shirya"?.Da sauri ta girgiza kai.

"Nima ban shirya ba amma zan jarraba shikenan".

Ganin zaiyi kissing dinta yasa cikin kuka tace.

"Dan Allah Aliyu ka tsaya".

"Umhum ina jinki na tsaya saidai ki sauri jirki na zai tashi karna makara idan sako zaki bani mi'ko"?.

Ya fad'a yana bud'e mata hannuwan shi tare da sake rungumo ta jikinshi sosai baki ta bud'e zatai magana bai bari ta yiba ya dakatar da ita ta hanyar rufe mata baki da nasa bata da wani za'bi bata da karfin ceton kanta bata da ikon hana sa hakkin sa sai kawai ta rufe idon 'kam ta bashi dukkan wata dama๐ŸŒน๐Ÿ‘๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘.


Da muryarta cikin sanyi tace "Aliyu ina son zamuyi magana".

Bai d'ago fuskar sa daga kallon laptop din dake gaban shiba yace.

"Sai yanzu ne kikai lokaci na"?.

Jitai jikin ta ya saki ta sake kasa da murya tana cewa.

"Kana lafiya kuwa"?.

"Eh fiye da kowanne lokaci".

A yadda yake bata amsa tasan yayi fushi da ita hakan yasa duk ta rasa mai yake mata dad'i.

"Ka bani aron minti talatin muyi magana".

"Ba bukatar yin hakan bazaki samu ba koda rabin minti ba".

"Meyasa baza ka saurare niba"?.

"Saboda baki da wani abu da zaki fad'a min".

"Amma na dauka abinda ya faru jiya ba wani bane".

"Eh a gun ki ba, ba wani abu bane kamar yadda kika ce dole ce tasa kike zaune dani ai ban sani ba da yanzu nadau mataki".

Shiru tai tana kallon sa har lokacin bai ko kalli bangaren da take tsaye ba hawaye ne ya fara yi mata zarya da sauri ta juya zata bar gurin.

Ri'ko hannunta yai yana dawo da ita tare da zaunar ta akan kafafun shi ganin hawaye a fuskarta yasa yai murmushi yana dauke gira.

Dauke fuskarta tai zata mike ya mayar da ita yana rike fuskarta idonta har yayi ja.

Shafar hawayen yai yana jinjina kai yace "meye magana ta dake akan wannan"?.

Da sauri ta soma gogewa tana sake daidaita kanta tace.

"Ka taimaka ka saurare ni".

"Shikenan yi magana ina jinki".

"Aliyu kasan ya nake ji a raina a kanka kuwa amma kake shashshare ni dan Allah kayi hakuri na tuba kana sona fa".

Ba tare da ya kalleta ba ya maida hankalin sa kan aikin sa yana cewa.

"Waye ya fad'a miki"?.

Zaro ido tai tana kallonsa cikin firgici tace.

"Kenan ka daina so na"?.

"Waye ya fad'a miki"? Nan ma har yanzu bai kalleta ya sake bata amsa.

"To meyasa kace haka"?.

"Amsar data dace dake na baki".

Sauke ajiyar Zuciya tai tana kallon sa lallai kam Aliyu kyakkyawa ne na kwatance shiyasa ta kasa sakin jiki dashi tana ganin kamar yafi karfin auren 'yar talaka irinta.

"Ina jin ki".

"Kaii kare ka iya bakin ka"๐Ÿ˜ .

Cikin isa yace "ai Aliyu ba ni kadai bane kare harda kai domin baka kyale niba ka biye ni tare muke hauhin koba haka bane".

Tsananin 'bacin rai ne kadai yake yawo a fuskar Aliyu Wanda mutum bazai so kalla ba yace.

"Na rantse maka da Allah ko waye kai ko dame kake ta'kama duk ranar da muka had'u idona idonka saina kashe ka".

Juyawa mutumin yai yana kallon Zainab wacce ke hawaye sai kawai ya kama dariya zuwa mintu biyu kuma ya tsaya yana cewa.

"Hello Marshall kana jina ko ka fusata ka kashe"?.

Jin anyi banza dashi yasa ya kalli secreen din wayar kiran ba'ai reject ba cigaba yai.

"Aliyu kake jarumi taya kenan zaka kama ni idan ma Zuciyar ka tana fad'a maka haka ta yaudare ka domin na maka nisa baza ka ta'ba kamo ni ba ko ka gane inda nake".

"Bugu da 'kari abar 'kaunar ka na hannu na sai yadda nai da ita idan naga dama na 'kyale ta idan Zuciya ta taraya min nasa bullet na kashe ta kamar haka.................


Ya karasa maganar yana harbin jikin bango da sauri Zainab ta toshe kunne tare da sakin 'kara cikin tsoro tana kuka ta sake kame jikin ta guri daya.

Rufe ido Aliyu yai ji yake inama zaiga mutumin nan face to face da baisan wanne irin kisan zai masa ba dan ya huce..............

"Hello Aliyos to ya kaji kana bukatar na sake harbawa ko itan matar taka kake bukatar jin muryarta? Bari kaji".

Harbin ya sake yi mai karfin gaske wanda dole a gigice Zainab ta kuma fasa wata 'karar.

Dariyar mugunta mutumin yana cewa "kaji ta ko? To na gama lokacin ka nikam ayi bacci lafiya hhhhhhhhh!!!!!.

'Dif Aliyu yaji an kashe waya kallon agogo yai 'karfe uku da rabi na dare d'an shiru yai cikin zurfafa tunani kafin kamar an daga shi ya mike yana daukar bindiga yai waje.

TOFA READER'S INA KUKE TUNANIN ALIYU ZAIJE A WANNAN TSOHON DAREN?.

SHIN ZAI GANO INDA ZAINAB TAKE?.

TO WAI MA WAYE YASA A SACE ZAINAB?.

Ku nemo mana amsa zuwa gobe dan Allah duk wacce ta nemo akwai gagarumar kyauta mai tsokana da zanyi mata.

Ina jira๐Ÿค—.

Ina Hajara ta Aminun ta b/kd maman Aliyu Haidar ki bamu amsa daya nasan ki da kokarin fahimtar abu๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿ™ˆ.

Zarah Musa d'an Adam maman Ruky ki bamu ta biyu kema ba baya ba wajen comment da basira.

Sai ke Naja'at Musa Abubakar )maman Amatul-azeez( na zaba miki tambaya ta uku nida sauran yan uwa marubuta da makaranta muna sauraron amsa๐Ÿ™‰๐Ÿค“๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜›๐Ÿ˜๐Ÿคฃ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜….

Taku har kullum Yusrah 'yar Musa jikar Abubakar Muhammad ina muku fatan alkairi๐Ÿคฒ๐Ÿ‘.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment