Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'a miki komai a kanta idan kika sake tara ta akan wata magana saina 'balla ki".

Yana gana fad'a mata haka ya bi ta gefen ta ya fita a parlon 'kamewa guri daya Amira tai ta daskare ta kasa motsin kirki.

Ganin haka yasa Afifah tasowa zata zo gurin ta kafin ta iso taga Amiran ta yanke jiki ta fad'i 'kasa.

Da gudu Afifah ta karaso tana kiran sunanta daidai Elham da Fati sun sauko da sauri suka zo inda suke.

"Lafiya ita kuma wannan fa meye ya sameta"? Elham tai maganar cikin mamaki.

Afifah batai magana ba ta kallesu tana cewa "ku taya ni mu dauke ta kar mummy ta fito".

Du'kawa sukai suna d'ago ta sukai stairs da ita har bedroom suka ajeta akan gado.

Zama Afifah tai tana cewa "Fati miko min ruwa".

Dauko mata tai da mamaki Fati tace "wai dan Allah meke damunta ne"?.

Sau'ke ajiyar Zuciya Afifah tai kamar mai yin rad'a tace.

"Ita da yaya discipline ne".

Zaro ido sukai a tare suna cewa "yaya boss me ya hada su".

Dariya Afifah tai harda tafi tana kallon fuskar Amira dake ri'ke shakaf da ruwa tace.

"Maybe Amira na son yaya discipline ne shi kuma ya fad'a mata da wacce yake so".

"Wacce yake so!!!😲🙊?. Cewar Elham tana mikewa tsaye.

"Eh wacce yake so akan haka ta fad'i, kunsan ma wani goge hadda irin tasa da tace ina anguwar su take cewa yai tai sacin a Google zata gani ya sunan ta yace Mrs Aliyu Marshall".

Kallon juna sukai basu san lokacin da suka fara dariya ba kai Fati ta girgiza tana cewa.

"Lallai Amira ta sayi damuwa da kudin ta dan yaya boss ko mutuwa zatai ta dawo tunda yace bai yinta fa'kat karshen magana baya 'karya".

"Kenan da gaske ne da yace yana da wacce yake so".

"Kai da gaske ne mana Elham mukam ai biki zamu sha".

Mikewa Fati tai tana cewa "ai ko bari yanzun nan naje na fad'awa mummy Dan a bari ya huce yana kawo rabon wani".

Daidai ta juya zata fita Afifah ta jawota baya tana cewa.

"Da alama ki manta waye ya discipline ko gulmar sa zaki kai tab idan rabon shan na jaki ne yake rud'ar ki ga hanya nan".

Ai da sauri Fati ta zauna kamar an tura ta tana cewa..

"Amma Aunty Afifah na gode wallh kin cece ni da naje ina ga yau yaya farfesu na zaiyi".

"Humm lallai yarinya iya farfesu indai ya tsaya iya haka ya miki da 'kauna idan bai saki a inji ya markad'a 'kasusuwan ki ba🤭".

Dariya suka sa lokaci guda suna tafawa Afifah tace.

"Nikam zaman d'akin nan ya ishe ni bari na koma parlor".

Mikewa Fati tai tana cewa "nima bari na biyo ki".

"Ahh to wa zaku bari gadin mai suma wallahi nima gani nan bisa sawun ku".

Saukowa sukai suk su ukun Afifah tai hanyar library ta dauko littafi ganin mummy zaune a parlon yasa da saurin su cikin zumud'i suka karaso inda take suna zama kusa da ita.

TV suka kunna Afifah data fito tana zama a can gefe jin zasu takura mata yasa tace.

"Malamai zaku iya kashe tv nan ko kuma ku sauya ku tafi wani palon".

Kafin suyi magana suka ji daga bayan su ance.

"This is not place for reading zaki iya komawa inda kika fito".

'Daga ido Afifah tai ta gano Aliyu tsaye saman balcony yana watso mata kallon gargadi".

Bata sake magana ba ta aje book din alamar ta hakura.

"Baza kije ki karatun ba kenan dan nayi magana shine kika aje book din saboda ga sa'an wasan ki"?.

Da sauri Afifah ta mike tana daukar littafin ta tabar gurin.

Dakatar da ita yai "baki iya bada hakuri ba kenan ko wato ke jar wuya"?.

Dafe kai Afifah tai tana juyowa kamar zatai kuka tace.

"Kayi hakuri".

"Repeat".

"Kayi hakuri".

"Again".

"Kayi hakuri dan Allah yaya".

"Yaya wa"?.

"Yaya Aliyu".

"Dama haka kike kira na"?.

"Eh yaya kayi hakuri".

"Ba discipline Daddy da mummy suka rad'a min ba"?.

"Eh yaya kayi hakuri"?.

Kin iya bada hakuri kamar matar aure ta gari bace min da gani zan kama kine".

Wucewa Afifah tai tana d'an yin kasa da murya tace.

"Oh ni naga ta kaina yaya discipline akwai masifa harda ta saidawa a gurin sa so yake ya dora min hawan jini kamar yadda ya dorawa Amira".

Su kam su Elham da suka samu shiga ba'a biyo ta kansu ba yasa suka d'an sake har sun manta da tsayuwar Aliyu zasu fara yiwa mummy shagwa'ba suka ji murya ance.

"Can you be quite? Which rubbish is this zaku sa min uwa gaba kuna mata ihu dama haka kuke mata to kusa Allah a ranku na dawo".

Kallon kofar palor sukai harda mummy cikin mamaki suka zaro ido kamar yadda nasa suke a zare wanda basuyi zaton gani ba suka ganshi tsaye lokaci guda suka 'kankame mummy suna cewa".

"Wata damuwar is back shikenan dayan ma ya dawo yaya Afif🤣🙊".

Da gudu Afifah ta fito yayin da su kuma suka mike da gudu suna yin stairs rikicewa Afifah tai tana kallon sa tace.

"Afif da gaske kaine"?.

Murmushin daya bata amsar tambayar ta yai mata yana kallon mum da itama murmushin farin cikin ganin sane a fuskarta.

Hannu ya bud'e mata wanda da sauri Afifah ta buga tsallen murna tana dariya ta rungume shi sosai.

'Dagowa tai har lokacin tana dariya tace "gaskiya nayi kewar ka bros yanzu lokacin mune nima d'an uwa na ya dawo".

Saukowa Aliyu yai yana riko hannun Afif tare da hararar Afifah yace.

"Muje ka gaida mum ke kuma zan kama ki".

Wucewa sukai Afifah dake tsaye a gefe tana kallon su a ranta tace.

"Perfect much👌 gayun gidan sun gama kammala yanzu zaman d'aki ya fara gara ni zan samu sauki ta bangaren Afif tunda Hassan dina ne saidai naji da takurar yaya discipline".

Wucewa tai tana dariya mugunta a ranta da yadda zata ga su Elham a d'aki tasa suna nan sun zubowa kofa ido kamar zasuyi kuka.


'Dan yana zaune wata 'yar tsohuwa take a 'kar'kashin bishiyar zaitun mai yalwar inuwa a tsakar gida tana gyaran shinkafar tuwo lokaci zuwa lokaci tana d'agowa ta gano ko wutar na ci.

Kasa hakuri tai ta d'an kallo kofar d'akin ta ganin takalmin wacce take tunani yasa tace.

"Zainab kina ina ne"?.

"Gani a d'aki kaka A'i ina zuwa".

Wata sassanyar murya zazza'ka ce ta bata amsa yayin da ta fito sanye da bakar doguwar riga tana murmushi.

Kai masha Allah kyakkyawa ce fara da gani bata da hayaniya zama tai tana dauke tiren shinkafar cikin tsokana tace.

"Lallai kaka A'i akan kimin maganar cewa an kawo na fito shine kika dora da kanki? Kuma da wanne idon kike gyaran shinkafar"?.

Dariya yar tsohuwar tai tana cewa "da idanuwa na mana da naki na ara? Ke daina min kallo mai dindimi ras nake ganin ki".

"Au ni da yaushe nace kina dindimi kaka A'i"?.

"Ba fad'a kikai ba amma niyyar ki kenan? Duba inaga kamar ruwan yayi kadan".

Mikewa Zainab tai tana zuwa inda murhun yake bata buda tukunyar ba ta tsaya tare da juyowa jin A'i na cewa.

"Yaushe zaki tafi Zainab"?.

Kafin ta bata amsa wata budurwa ta shigo da sallama tana cewa "kai kakus miye zaki bata idan ta fad'a miki"?.

"Babu fa kawai dai na tambaye tane".

"To rabin shekara zatai".

"Haka tace miki uwar ma'karyata? Kinga Najat ina raba ki da kiwon aura kina cewa aura ta haihu".

Dariya Najat tai tana cewa "to me za'a fasa mutuwa ko hisabi"?.

"Ba wanda za'a fasa saidai kimin shiru domin ba ke na tambaya ba sai naji daga bakin ta".

Mikewa Najat tai tana shiga d'aki tace "to shikenan bari nai baccin rabin lokaci kafin a gama yi mana tuwon muzo muci dad'i".

"Haka kika iya baki iya aiki ba sai ci kamar gara zan hada ki da Balarabe ne bari yazo gidan gaishe ni".

Fitowa Najat tai tana daukar wu'ka ta soma yanka ganyen da za'ai miyar tace.

"Shikenan kakus na fito sai komai ya wuce basai kin fad'a masa ba".

"Ke kika sani yarnan idan baki tsaya kin koyi girki ba yanzu yaushe zaki koya"?.

"Cab jimin tsohuwa ce miki akai ban iya girkin ba ko me? Bari na baki mamaki Zainab zo ki zauna nayi mata tuwon nan yau dai tasan ni ba kanwar lasa bace".

Daidai Zainab ta zauna tadan girgiza kai tana kallon Najat kafin tace.

"Amm kaka ranar juma'a ta sama zan koma insha Allah".

"To Zainab Allah ya kaimu".

"Amin kaka A'i".

Maida kallon ta tai kan Najat tana cewa "ke kuma gwana bani yankan ki koma can tunda kince kece zaki aikin".

Mi'ka mata tai tana tashi ta koma wajen murhun yayin da suka cigaba da shirar su.

🌹🌹🌷🌷🥀🥀
"Amma dai Aliyu abincin ya maka dadi ko"?.

Bai amsa mata ba Samir da yake lura da yanayin kowanne a cikin su yace.

"Marshall dakai fa take ka amsa mata shin abincin ya yi maka"?.

Ganin har lokacin yayi banza kamar ba dashi ake ba yasa cikin tsokana Samir yace.

"Bai yi magana ba yana zilama😂".

Sai lokacin Aliyu ya d'ago tare da kallon Samir wanda ya kau da kai yana dariya sai kawai ya aje spoon din hannun shi tare da mikewa yabar gurin.

"Aliyu ya haka ka koshi ne"?.

Banza yai mata yana nufar parlor da sauri Amira ta mike tana bin bayansa har harabar gida inda ya aje motar sa.

Da mamaki tace "wai meya faru ne naga ka tashi tafiya zakuyi"?.

"Eh mun gode".

Shine amsar daya bata yana bude murfin motar tare da shiga ya zauna.

Kallon sa tai tana cewa "to amma Aliyu ai baka biya kudin abincin ba".

"Mene dama hotel nazo"?.

"A'a amma Aliyu.............


Katse ta yai "amma Aliyu me? Kinga Amira bana son wasa".

"Ba wasa nake idan saurayi yaje gurin budurwa ta masa liyafa ko yaci ko bai ci biya yake".

"Waye zai biya kin? Dama nace ki dafa min abinci ne bayan ma ko dad'i baiyi ba".

"To nidai ba wannan ba ka biya kawai".

"Na biya me? Kinyi hauka ne"?.

Amira zatai magana Samir ya karaso yana cewa.

"Kaifa malam ba wani hauka da tai haka ake".

"Haka ake me"?.

"Haka ake biyan 'yan mata idan anci abincin su".

"Bazan biya ba saboda ba ni nasa taba ra'ayinta ne zaka iya shigowa mu wuce idan kuma ba bukatar hakan na tafi dan naga dad'in tsayuwa da ita kake ji".

"A haba kaifa Marshall kaima kana ji".

"Kaga ni karka damu dani kaji da kanka idan kuma tayi maka ne na saitawa kaina hanya"?.

Dariya yai "a'a ni bance maka haka ba".

Juyawa gurin Amira yai wacce ta kafe Aliyu da kallo kafin ya d'an girgiza kai yana cewa.

" Kinga Amira kiyi hakuri abincin ki yayi dad'i kuma mun gode nawa ne kud'in"?.

"Kawai kai dai bayar yadda ya kama".

'Dauko kudi Samir yai wanda ya kasance na Aliyu ne canjin da sukayo mata shopping ya bata kirgawa tai ganin dubu goma yasa ta hade rai tana cewa.

"Wannan ai ko kud'in drinks baku biya ba".

Kallon mamaki Samir yai mata yana bude motar ya dauko mata shopping din yana cewa.

"Haka ne kinyi gaskiya Amira saidai ba komai ake nema a samu ba kin gane".

Kunya ce ta kamata sai kawai ta kasa cewa ma ta gode ganin irin kayan kud'in da suka jibgo mata dakyar tace.

"Thanks na gode sosai Aliyu".

"Bani zaki godewa ba wanda ya baki" yana fadin haka ya tada mota yana nufar kofar gate da kallo Amira ta bisu har suka fita sannan ta debe kayan ta cikin murna ta shige gida.

A hanya Samir ke cewa "kai amma fa ka iya kafce Marshall".

Kallon sa Aliyu yai cikin alamun tambaya yace.

"Wanne irin kafce"?.

"Irin wanda kaiwa Amira yanzu".

"Haka ne"?.

"Eh mana da dukkan alamu Amira na sonka fa matuka son da take maka har baya iya boyuwa".

"To Amma kai me ka gani dangane dani"?.

Kallon sa Samir yai cikin tsokana yace.

"Nidai banga wani abu ba tayi maka"?.

Kai tsaye Aliyu yace.

"A'a".

"To kana son ta"?.

Nan amsar daya ce.

"A'a".

Da karfi Samir yace.

"Amma zaka iya auren taaaa😂😂😂"?.

Wanda da sauri Aliyu yai wani irin taka burki saida Samir ya bugi kujera juyowa yai yana kallon sa.

Dariya Samir keyi harda rike ciki ya kasa ma magana ganin yadda Aliyu yai da fuskar sa.

Dafe saitin 'kirjin shi Aliyu yai jin yadda Zuciyar sa take bugawa yasa ya d'ago yana kallon Samir yace.

"Amma wallahi kai dai baka da mutunci wata rana in dai ina yawo dakai sai dai aga gawa ta saboda maganganun ka masu kama da saukar tsawa".

"Sorry Marshall dama na jarraba kane".

"Kuma ka rasa ta yadda zaka jarraba ni saida haka"?.

"To ai naga ba wani abu bane a ciki dan kawai na tambaye ka".

"Eh ba wani abu bane mana tambaya mai muhimmanci ya kamata kaimin".

"Wacce Iri kenan"?.

"Ka fini sani".

"Oho so kake nace maka kana son Zainab? Tayi maka? Zaka aure ta abinda kake son ji kenan ba"?.

"Eh shine nake so naji ba waccen shirmen ba".

"Shikenan to yanzu dai tada mota muyi sauri mu isa gida".

"Kana da uzuri ne"🤔?.

"Ni ko nake da uzuri ka manta kaima zaka ga Zainab".

"Haka".

Tada mota yai suka ci gaba da tafiya suna karya kwanar anguwar su kuwa sai gata ita da Afifah sun fita daga gate din islamiyyar su.

"Assalamu alaikum wai Zainab tana nan"? Wani yaro yai maganar.

Juyawa Zainab dake gurin wanke wanke tai tana cewa.

"Eh ina nan waye ya aiko ka"?.

"Nima ban santa wata ce tana waje".

"To kaje kace mata ta shigo".

Fita yaron yai sai gashi ya dawo da sauri yana cewa.

"Wai tace ki fito".

"Na fito sai kace wata namiji zan fito mata waje idan bazata shigo ba ko ma wace ta koma inda ta fito".

Yaron zai tafi mama ta fito daga d'aki tana dakatar dashi da cewa.

"Kai tsaya kace tana zuwa".

A damuwance Zainab tace "mama".

"A'a Zainab kece ya kamata kice wa wani babu kyau wulakanta d'an adam kije ki gani".

Mikewa tai yayin da mama ta maye kujerar ta dan karasa wanke kwanukan.

Fitowar Zainab da dogon hijab dinta kamar kullum tana Shirin sa likaf mama tace.

"Haba Zainab nan da kofar gidan kuma fa yaron yace mace ce ina shigowa da ita zaki"?.

Sauke ajiyar Zuciya Zainab tai tana aje likaf din akan keken dinkin ta dake kofar daki tare da fita.

Kusan karo sukai da kishiyar mamanta wanda da sauri Zainab ta matsa mata hanya cikin ladabi amma duk da haka Saida ta biyo ta saitin ta ta bangaje tana cewa.

"Ni sa'ar kice zaki tare min hanya ba dake nake kishi da tsohuwar kine dan haka ki fita idona mara kunya kawai".

Kallon mamaki Zainab tai mata batare da tace komai ba tabi ta gefenta ta wuce.

Asabe tai tana cewa "ke sumore ina zakije yau kuma babu dan gadon ko kanki ya gwaro da bango shine zaki koyi fita haka ki nunawa samari fuskar ko Allah zaisa wani ya kwashi tsiya yakai gidansa".

Tari da bai kama Zainab ba batai mata ba tana jinta amma ta share duk da yada girma da asabe take a gurin ta daidai da ranar daya bata ta'ba mata rashin kunya ba tana mata kallon uwa matsayin ta na matar ubanta.


Zainab na fita ta hangota tsaye jikin mota da waya a hannunta alamar magana take.

Karasawa tai zatai magana taga ta daga mata hannu takaici ne ya kama Zainab domin bata ta'ba ganin wannan budurwar ba sai a yau zata juya taji ta kamo hijab dinta kallon ta tai sai kawai taga ta girgiza mata kai tana sauke wayar.

Tare da zare glass din fuskarta tace.

"Barka da safiya malama Zainab nasan baki sanni ba baki ta'ba gani na ba sai yau hakan zai baki mamaki amma wata yar bazata ce Zainab nazo miki da wani d'an karamin abu kalli".

Ta fad'a tana nuna mata photo a wayarta kallon photon Zainab tai idan ba gizo idanuwan ta kemata ba Aliyu ne zaune tare da wannan budurwar a wani kyakkyawan guri da alama ba Nigeria bace wata kasar ce sunyi photo a bakin ruwa.

"Wannan ya baki amsar tambayar dake Zuciyar ki ta koni wace ko kuma daga ina nake right"?.

'Dagowa Zainab tai tana kallon ta tace.

"To maye had'ina da wannan"?.

"Au tambaya kike maye had'in ki dashi? To amma ba kece Zainab ba"?.

"Eh nice".

"Amma zaki bani irin wannan amsar bakiga abinda na nuna miki ba"?.

Ran Zainab ne ya soma baci jin zata mayar da ita shashasha kamar yadda ta mayar da kanta tace.

"Kinga dan Allah zaki iya tafiya bani da lokacin wannan shirmen".

"Shirme? Nice nake miki shirme? Har yanzu baki fahimci maye ma'anar zuwa na nan wajen ba kinsan dai matsayi na da girma na kamar nafi karfin tsayuwa anan amma nazo saboda mu daidai ta dake ki fita rayuwata".

Da mamaki Zainab tace "rayuwar ki"?.

"Eh rayuwata".

Wayar ta kunna tana nuna mata photon Aliyu wanda yake shi kadai da kayan dai da bata son ganinsa dasu wato 3Quarter ba'ki sai fara singilet.

Tsuka taja tana kauda kai tace "wai ke maye haka ne"?.

Sauke waya tai tana kallon ta tace "fatan kin san waye wannan da matsayin sa kinsan yafi karfin diyar talaka Irin ki dan haka nazo na miki gargadi ki fita hanyar sa dan masoyi nane ni kadai zai aura muyi rayuwa bazan ta'ba hada kishi da kowa ba".

Wani razanan nan kallo Zainab tai mata ranta a matukar bace jin zata raina mata hankali a gidan uban wa take son Aliyu waye ya fad'a mata har zata zo tana mata ihu Allah ya sauwake ta auri Aliyu gara ta zauna haka babu aure.

"Tambayar kifa nake kinyi shiru ki bani amsar da nake son ji".

"Bani da lokacin amsa wannan wofantacciyar tambayar taki kin gane ina da abubuwa masu mahimmanci daya fi wannan shirmen".

"Keee ni kike fad'awa haka"?.

"Toke wace ba haihuwan ki akai ba kinga madam nina wuce ki gaida gida".

Barin ta a gurin Zainab tai tana shigewa gida kai ta jinjina lallai tana da aiki a gabanta da Aliyu da Zainab kusan halinsu daya akan iya fadar magana amma tasan yadda zata bi dasu shiga motar tai tabar gurin.


Zainab na komawa ganin mama ta karasa wanke wanken yasa ta cire hijab dinta tana zama a kujera ta fara dinka kayan data yanka jiya.

Kiran wayarta akai ganin 'kawar yasa tana murmushi ta daga tana cewa.

"Hello Afifah ya kike"?.

"Lafiya Zainab kwana biyu shiru idan babu hello ai akwai hay baba 'kira mai zaici gawayi"?.

"Tofa da nai me"?.

"Kai ji dai ina ta kiran wayar ki a rufe kuma kinsan yaya discipline bazai barni na fito ba ahiyasa banzo naga ko kalau kike ba".

"Ayya Afifah yi hakuri lafiya nake wayata ce ta fad'a a ruwa taci secreen shine yaya Samir ya saimun wata jiya".

"Oh nasan dai halin lafiya bazaki bar wayar ki kwana kusan biyar a rufe ba dama na kira kine dan Allah littafi na yana gunki".

"Eh yana nan ai biyu ne ba daya ba".

"Yauwa to dan Allah daya zai same ni yanzu"?.

"Ok bari nasa yara su kawo miki".

"A'a".

"Kamar ya a'a".

"Ke nake so ki kawo min da kanki".

"Amma meyasa saini Afifah dinki nake".

"Dan Allah Zainab kwana biyu bamu hadu ba yau kam kizo ki d'an taya ni hira bansan meyasa ba bakya son shigowa gidan mu".

Shiru Zainab tai cikin rashin jin dad'i zata iya rantsewa bata shiga gidan sau uku ba a rayuwar ta".

"Kinyi shiru Zainab"?.

"Karki damu Afifah gani nan zuwa yanzu".

"Yauwa ko kefa" kashe kiran Afifah tai tana cewa.

"Bari na hada mata liyafa domin a rayuwata yauce rana ta farko da Zainab zata shigo gidan mu".

"Wacce Zainab kenan" Elham tai maganar.

"Zainab fa ta gidan su yaya Samir abokin ya discipline".


"Oh malama zaki ce min sai nafi ganewa ayya ai aunty Afifah kinyi dacen 'kawa bari ma ni na dauko littafi na daga tazo ta dora min".

"To kin gani dai bari ni na sama mata abubuwan tarbar bako domin tunda muka taso ban ta'ba ganin ta a gidan nan yau dinma kamar mafarki nakeji saidai idan naganta tazo da gaske".

Dariya Fati tai "kai wallahi aunty Afifah kema dai".

"Ah to dole nace haka kunga laifi nane"?.

"Ina a'a bari mu ma mu taya ki had'awa Aliyu na kallon su kome suke saidai yaji d'an mamaki da yaji suna cewa wai Zainab zata zo gidan anya ba kunnen sane baiji daidai ba".

Tashi Zainab tai bisa dole dan kada Afifan taji babu dad'i shiyasa zataje saidai bataso tana baya baya da Afifah ne saboda bata son ayi mata kallon mai son Zuciya.

'Dan gyara jikin tai tana shafa hoda da d'an lipstick ta debo litattafan daidai zata fita kofar su ta hadu da mama.

"Mama ina kika je harda hijab"?.

"Mun shiga gurin hajiya ne taron mu tai matan 'ya'yanta wai kwana biyu sun daina bata kud'in kashewa ko mune muka hana su bata".

Murmushi Zainab tai wato hajiya bazata ta'ba daina rigima saima abinda ya 'karu tunda kullum tsofa take".

"Mama haka zakuyi ta hakuri da ita".

"To ya muka iya Zainab hajiya uwa ce".

"Mama zan fita".

Da mamaki mama tace "Zainab ina zakije"?.

"Amm mama dama neman ki zanje na fad'a miki zan d'an shiga gidan su Afifah ne".

"To shikenan sai kin dawo karki dade kinga dinkunan mutane sunyi yawa ga bikin gidan Dattijo ya kusa kuma ko mutum daya baki wa ba".

"Eh mama bazan dade ba".

Daga bayan su suka ji ance "oh kai jama'a gaskiya zilama batai ba wato Zainab gidan alhaji Amadu zaki shiga ko harda fakewa da daukar littafi dan munafinci bayan maula zaki Allah ya sauwake a haka zaki 'kare ba aure sai yawo a gari".

Hade rai mama tai "Asabe ki iya bakin ki akan 'yata domin baki isa ki ramar min ita ba alhamdulillah ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli ya riba mai yawa ma kuwa kuma bari na fad'a miki baza a taba samun 'diya a gidan wacce zata kama 'kafar Zainab ba a komai badan cin fariya ba na fad'a miki gaskiya ne".

Shewa Asabe tai "ahayye nanaye yau nake ganin sabon salo Kiran sallah da usur jimin mace wato kece mai goya mata baya shiyasa taki aure sai cin kudin wannan bawan Allan kuke maye ma sunan sa"?.

Ta fad'a tana kallon Zainab wacce ta sunkuyar da kanta kasa.

"kuka kike ne dan na fad'i gaskiya"?.

D'ago fuska Zainab tai tana kallon ta tare da girgiza kai zatai magana mama ta dakatar da ita.

"Tafiyan ki Zainab ke 'ya ce a gurin ta koda bata son haka nice daidai da ita".

Wucewa Zainab tai cikin damuwa domin batason yiwa maman musu tun daga ciki ta fara jiyo muryar Bilki da Rasheedat suna dariya a waje.

Bilki na cewa "wow! Dan Allah Rasheedat ki kalle shi gwanin burgewa kyakkyawan saurayi d'an gayu ga kud'i gaskiya fa ya had'u saidai bani da kwarin gwiwar zuwa inda yake tunda yana tare da wadancan mukarraban nasa".

Dariya Rasheedat tai "ke Bilki mai zai kai mutum can su karya masa kafa mudai tsaya daga nan muyi ta kallon abun mu".

Bud'e kofa Zainab tai tana fitowa tare da kallon su ganin bama su lura da ita ba yasa tai gyaran murya amma a banza mamaki ne ya kama ta harma ta kalli inda suke kallo da abinda ya dauke musu hankali.

Aliyu ta gano zaune akan kujera cikin katuwar rumfar kofar gidan su yasha ado da kayan gado wato dai shi waccan a haka rayuwar sa zata kare kullum da 3Quater kamar dashi aka haife shi.

'Dan tsaki taja zata wuce Rasheedat tace "a meye abun tsakin dan kawai mun kalli abinda yai mana".

" 'kwarai ko ke nasan kin 'kyasa shi dan kawai ace miki ta Allah wato malama shine kika 'ki nunawa".

Wani kallo Zainab tai musu saidai damuwar dake tare da ita bazata bari ta musu magana ba kawai ta wuce.

"Au ai da kinyi magana muna daidai da Kowacce budurwa a gidan nan".

Tana jinsu ta share domin rashin tarbiyyar ba a su bane a uwayen sune da basu basu ta gari ba.

Tana cikin tafiya taga an Sha gabanta tana dagowa taga Mansur.

Ranta a bace tace "wai maye haka"?.

"Yallabai ne ke son magana dake".

Hade rai ta kuma yi "waye wani yallabai"?.

Nuna mata yai "sir Aliyu".

"Ka bani hanya na wuce".

"Zan barki ki wuce ne kawai idan har kika saurare shi".

"Hakan bazai samu ba bani da lokacin sa".

"Uban gidan nawa"?.

"Koma waye kaga malam ka matsa min na wuce ko nayi maka kama da irin matan dake tsayuwa a layi suna magana ne"?.

"A'a baki min kama dasu ba nafi kowa sanin ki Zainab kuma zan bada sheda a kanki ke kamila ce kuma me saukin kai".

"Naji to ban hanya na wuce".

"Karki sa nai laifi ki taimaka kije".

"A'a ni baza ni gurin sa me zanyi mai"?.

"Dan Allah Zainab ki rufa min asiri bakisan waye sir Aliyu ba rashin zuwan ki zai iya haifar min da hukuncin sati ina wahala".

Dagowq tai ta kallo ina Aliyu ke zaune ta cikin likaf dinta ya dauke kai daga saitin su.

Haushi ne ya 'kara kamata zata wuce da sauri mansur yace.

"Zainab dan Allah".

Tsayawa tai tare da juyowa tace "shikenan karki damu saboda kai yaci albarkacin ka".

Zaro ido mansur yai "ki daina cewa haka idan yaji sai hukunci na yafi na 'kin zuwan ki".

Sauke

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment