Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

TYPING 📲 {WED 20 DEC 23 8:43AM} YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

WHATSAPP NO: 234 905 527 3614

💞 KOWACCE 'KWARYA💞


DEDICATED TO
MY FATHER MUSA ABUBAKAR MUHAMMAD may Allah help u may Allah bless u may Allah protect u anywhere u are may Allah accept ur du'as amin.

STORY BY
🏵️👌 BATILAH ABDULLAHI)(Batul)(

✍️ WRITTEN AND EDITING
YUSRAH MUSA ABUBAKAR {maman Fatima Elham little Zaran aunty 🌹💕}

I'm here to make u happiness educated hhhhhh!😜 domin nifa I have no girman kai if u're fushi dani😠 to wallhi u're just 'batawa kan k lokaci🙉 ni ta kowa ce.

Godiya sosai sosai godiya masoya babu bakin da zanyi muku albarka dashi bisa kauna da kuke gwada min saidai nace Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa a duk inda kuke amin.
💕 Zarah Musa d'an Adam
💘Naja'at Musa Abubakar
😜Rakiya Abdullahi
🙉Ruwainah Abdullahi.
Ranar kuce masoya maza kada kuyi sanya muyi rausaya 'yan uwa mu taho da baya baya mune muke cashewa💃💃 a group.

In the name of Allah the most benefits and the most merciful we luv our nabi we like him he's the mirror of our life no success with out him he haven't limit peace be upon him amin.

#YUSI CE#
PAGE 0️⃣1️⃣👉0️⃣2️⃣
Parking yai da matukar 'karfi a cikin tabkekiyar babbar rumfar aje motocin dake 'katuwar harabar gidan su wanda da sauri wani mutum dake sanye da uniform yazo ya bude masa.

Yana cewa "u're welcome sir".

Fitowa yai cikin taku mai kyan burge mai kallon sa ya nufi kofar da zata kaishi cikin palor yana rike da rigar suits dinshi.

Yaji mamaki har yana d'an zaro kyawawan idanuwan shi waje ganin babu wanda ya kula da shigowar shi hankalin su naga kallo wasu naga waya.

Gyaran murya yai wanda a tare gabaki dayan su suka juyo suna maida hankalin su kansa.

Duk idanuwa suka zaro kamar zai fito waje dan tsoro da mamki lokaci guda suka rud'e kowa ya gigice.

Murje ido Afifah tai ganin da gaske shine yasa tace.
"Yaya kaine"😭?.

A yadda tai masa maganar yasa ya sake zaro mata idon ta gansu dakyau 'kila ko ta dawo hayyacin ta.

'Dora hannu tai aka da gudu tabar falon tai stairs tana cewa wayyo Allah shikenan discipline ya dawo zaman bedroom ya dawo jama'a ku fito".

"Hummm Afifah is so funny zan kama ki zaki baya ni" yai maganar a ransa ya wucewa.

Da kallo sauran suka bishi suna sauke ajiyar xuciya gashi 'kafafun su sunyi nauyi balle su tashi kafin ya dawo su gudu ita kam mummy lamarin su na bata dariya.

Shigowar Daddy kenan ganin yadda yaran nasa suke yasa shi dakatawa yana karantar yanayin su domin ya sani matukar suna halin lafiya yana dawowa zasu tare shi da farin cikin su sa'banin yau da yaga damuwa a fuskokin su.

Hannun karamar ya riko yana mikar da ita tsaye yace.

"Auta na miye yake faruwa ne"?.

Kafin tai magana Fati dake gefe tai wuf tace "Daddy ka taimake mu wallhi ya dawo".

Cikin rashin fahimta Daddy yace "waye ya dawo kuma"?.

"Yaya boss😂" Elham dake gefe tai maganar kamar zatai kuka.

Kallon ta Daddy yai da d'an mamki a fuskarsa yace "wai Aliyu Haidar d'ina ne ya dawo gida"? 'Dana ya dawo my son💘 is back 🙉".

Duk zaro ido sukai jin abinda daddyn yace ga kuma farin ciki ya bayyana a fuskarsa.

Kallon su yai yana murmushi yace "haba Koda naji shiyasa naga kun nutsu yanzu wace a cikin ku zata je ta kira min shi"?

😲Duk shiru sukai suna sunkuyar da kai aka rasa mai tari yar dariya Daddy yai yana girgiza kai yace.
"Ke Elham je ki Kira min shi".

Kallon Daddy tai hawaye ya kawo a idon ta lokacin data mike da d'an mamki Daddy yace.

"Wai duk maye hakan d'an uwan kune fa".

Goge hawaye Elham tai tana cewa "Daddy ba gudun shi muke ba lamarin yaya Aliyu sai shi".

"To kinga bar kukan je ki Kira min shi".

Wucewa tai yayin da Daddy ya bita da kallo yana murmushi kafin ya kalli sauran yaran nasa.

Tafiya Elham take tana tsara da yadda zata iya shiga dakinsa a hankali ta bud'a kofar falon ganin baya nan yasa ta wuce bedroom d'an kwankwasa kofar tai amma shiru ta sake ba amsa hakan yasa ta bude yana kwance a kan gado ya zubowa kofar ido yaga wanda zai shigo.

Tsayawa tai daga jikin kofa tane cewa "yaya kazo Daddy na neman ka".

Kamar tana tafe yana bin bayanta haka ta ganshi a falon daidai Afifah ta sauko ya jawota yana tuma mata dundu a bayanta 'kara tai da gudu tana yin bayan Daddy.

Elham kam tunda ya fito jikin ta yadau rawa bata farga ba ta ganshi a gabanta ri'ko hannun ta yai cikin fad'a ya soma magana.

"Ke dan uban ki ni sa'an wasan kine da zaki min magana ta kofa"?.

"Yau nake ganin ikon Allah a gurin ka to da ta ina zatai maka magana ta window"? Mummy tai maganar.

"A'a mummy yarinyar nan dan rainin hankali babu sallama taje tana min ihu harda gudu kamar taga mala'ika".

"To da meye kai mala'ikan yara ne mana kaga sakar min hannun yarinya".

Sakin hannunta yai yana bata ran'kwashi mai zafi wanda yasa da sauri ta dafe kanta.

Kallon Afifah yai yana cewa "ke discipline ya dawo Fati matsalar ki ya dawo Elham damuwar ki ya dawo Husnah kukan ki ya dawo mai hana ku shan iska mai dad'i kamar yadda kuka ce to kusa Allah a ranku ban canza ba ina nan yadda nake yadda kuka sani har nafi da kuma na dawo babu wacce zata sake jin dad'i a cikin ku".

"Nikam yau nake ganin wata 'kaddara ayi mutum fad'a kamar kububuwa dan Allah ka rika shan ruwan sanyi".

"Mummy yaran kin nan basa jin magana gabaki dayan su".

"Shikenan to idan ka gama fadan ka zauna mu gaisa daga dawowar ka duk ka hargitsa gida".

Zama yai suna gaisawa suna masa sannu barka da dawowa yana fad'a musu abinda ya cancata ya fad'a.

Daddy ne ya tambaye shi "yaushe zaka koma amma dai bada wuri ba fatan zaka dad'e"?.

"A'a Daddy karamin hutu na kar'ba maybe two weeks ma na koma".

Ya fad'a yana kallon Afifah da Elham lokacin da suka tafa cikin murna murmushi yai yana jinjina kai lallai yaran nan basu da hankali.

Maida hankalin sa kan Daddy yai jin yace "haba dai sati biyu fa Aliyu da wuri haka? Shekarar ka daya da rabi fa baka zo gida ba"?.

"Kuyi hakuri Daddy yanayin aiki ne".

"Babu komai munsan da haka Allah ya taimaka ya kuma albarkaci rayuwar ka da zuriyar ka".

"Amin Daddy na gode".

Kiran sa akai a waya ganin mai Kiran yasa yace.

"Ina son zan fita".

"Ok ba matsala".

Mikewa yai yana fita da sauri Afifah tazo gaban Daddy tana durkusawa tace.

"Dan Allah Daddy kasa shi ya koma yai hutun sa acan".

Kallon ta Daddy yai kamar zaiyi dariya ganin duk tabi ta burkice yace.

"Me kika ce Aliyun nawa zance ya koma d'ana nefa yaushe rabo na dashi"?.

"To amma Daddy kana ganin abinda yake mana daga dawowar sa".

"Eh na gani ai baifi gyara ba".

Tashi Afifah tai tana cewa "to wallahi zaman lafiya na kawai naje na hada kayana gara na tafi gidan su mummy kafin ya hutunsa ya koma dan na tabbata idan na zauna ko burbushi na baza'a samu ba".

"Kada ki soma had'o kayanki babu inda zaki je".

Tuntu'be ta kwasa jin abinda Daddy yace yasa ta tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya.

"Afifah idan baki tsaya kun fahimci juna ba a matsayin ku na yan uwa sai yaushe ko sai bayan mun mutu"?.

"Bana so na sake jin wata magana ki dawo ki zauna cikin yan uwan ki".

Dawowa Afifah tai tana zama batare da tace komai ba yayin da Elham ke mata dariya a boye.

Aliyu na fita yaga Samir yana sake gwada kiransa ganin ya fito yasa yace.

"Haba Aliyu tun dazu inata jiran ka".

"Eh kayi hakuri na tsaya gurin Daddy ne".

"Ok barka da zuwa gida bayan lokaci mai tsawo muje ka bani labarin inda kuke".

Wucewa sukai Aliyu na cewa "Amm Samir yaya ajiya ta take fatan tana lafiya right"?.

Murmushi Samir yai 'ai Marshall albishirin ka ajiyar ka tana lafiya ina kula da ita yadda ya kamata".

"Ka tabbata"?.

"Kwarai aboki na".

"Bana son wasa Samir".

"Ka yarda dani Marshall ba wasa abinda nake fad'a maka tsantsar gaskiya ne".

"Shikenan amma zan iya ganin ta"?.

"Mazai hana muje na nuna maka ita".

Fita suka daga harabar gidan suna tafiya wani gida suka shiga mai gate saidai ya tsufa har tsatsa yake kuma a hakan ta waje yafi ta ciki dama dama domin gidan a ru'be yake.

Magidanta uku ne a gidan kowa da kofar sa da iyalan sa da tsohuwar gidan tana nan a raye ita ta da part dinta.

Ba tsananin talauci ne ke damun gidan ba a'a ido ne yai musu yawa mazan gidan kowa bazai fidda kudi ya gyara shi kadai ba kuma a had'u a gyara rashin hadin kai ya hana.

'Daya headmaster ne na primary daya d'an sanda ne dayan shine baya da aiki saidai yana dan kasuwancin sa ba laifi.

Akwai gwarama a gidan akwai gulma munafinci yida wani hana zaman lafiya da akwai matan aure shida a gidan kowa macen shi biyu da yara.

Kofar tsohuwar gidan suka fara shiga da akwai yara da yawa suna zaune ganin tayi ba'ki yasa suka mike suna fita.

Zama sukai bayan sun gaisa kaka dake cin goro tace "Samar waye ne wannan din na kusa dakai"?.

'Bata rai Samir yai "kai hajiya dan Allah miye wani Samar kuma"?.

Aje goron tai tana masa dakuwa tace "naci gidan ku tun kafin a haifi ubanka nake rayuwa shima nice na raine shi saida ya taso na nuna masa komai zakai min wata magana".

"To hajiya ke dince da kayan haushi shi yasa ban cika shigo miki ba saboda fad'a muke idan ma nazo".

"Karka sake shigowa daga yau ai ba kai kadai bane jika na gasu nan da yawa saina za'ba".

"Basai kin za'ba ba kowa jikan kine".

"Nidai akwai wadanda ba jikanu na ba domin ni jikanu na suna da farin jini".

"To kuma waye mai 'bakin jini a gidan"?.

"Ban sani ba matse ni saina fad'a maka".

Zaro ido Samir yai "wa Nina isa nima da su Abba sun matse ni".

Kinga hajiya duk mubar wannan ga jikan ki yazo gaida ke".

Kallon sa hajiya tai "waye ne ban gane Shiba d'an nan daga ina"?.

Samir ne ya bata amsa "Aliyu ne daga gidan Daddy Ahmed".

"Tofa waye dad'i Ahmad kuma"?.

"Bafa dad'i Ahmad ba Daddy Ahmed nace".

"To ai ban gane ba kamin yadda zan fahimta mana".

"Hajiya nan kusa damu nake nufi gidan alhaji Amadu minister.

'Yar zabura hajiya tai tana zaro ido cike dake da son zuciya tace "ayya yaron daya tafi soja ne kaga marmari daga nesa ku ake wa kirari tuwon 'kaya Allah sarki yaro ashe ka dawo kullum saina yi sallar dare saboda kai da safe na sayo 'kosai nayi sadaka nace kuna can jeji ba gida ba gari fata na ka dawo lafiya sai kaga kwatsam kayya rayuwa" hajiya ta karasa maganar tana kuka.

Shiru Aliyu yai yana kallonta Samir na cewa "ki daina kuka hajiya ai tafiya ba mutuwa ce ba".

"Ka barni nayi Samar ka barni".

"Shikenan to hajiya zamu tafi" .

Mikewa sukai kudi Aliyu ya ciro yana bawa Samir ya Mika mata wanda dama tana goge idanu tana kallon shi ta tsananin yatsun ta da sauri ta karbe tana masa godiya suna fita ta daga fulo ta saka tana cewa.

"Haba malam zamanin nan Saida basaja Saida farauta ba gashi na samu kudin batarwa ba.

Suna fita daidai 'yan mata biyu zasu shigo gidan wacce tafi shishshigin da sauri tace.

"Yaya Samir waye wannan kamar yaya Aliyu na gidan su Afifah"?.

Daidai zasu fita Samir yace "ba kama bace shine".

Zaro ido tai tana dafe kirji tace "wow lokacin wanka yazo lokacin sa kyawawan kaya lalle akai akai zuwa gyaran jiki saloon ba kama hannun yaro zanyi bari naje gurin hajiya".

Daidai sun ci gaba da tafiya dayar da batai magana tace "ai bake kadai ba zaki nima haka mai rabone zai samu kusan mu biyar ne ke sonsa a gidan nan".

"Na sani amma ina ganin duk na fiku son sa".

"A yadda kike ji a ranki ba".

"Zance me kuke kuda kullum kuna tafe kuna magana kamar wasu ta'ba'b'bu"?.

Zama sukai Rasheedat na cewa "akan Aliyu ne dan gidan ministan nan alhaji Ahmed san kowa".

"To me ya faru" hajiya ta tambaya tana sake zaune fulon da tasa kudin.

Bilki tace "babu komai kawai son shi muke".

"Da gaske kuke yaran nan"?.

"Allah hajiya".

'kasa hajiya tai da murya tana cewa "yauwa yan albarka haka nake son ji kwanan nan zan jike da kudi idan dayar ku ta aure shi ku dage yasan daku".

Kudin daya bata ta dauko tana nuna musu tace.

"Kunga yanzu Samar ya kawo min kalli alherin daya min idan kuma akace yayi aure a gidan nan kullum jalaf din taliya🍝 da kifi🐟 ga zobo🍷 mai sanyi nasan shine abinci na dan Allah yaran nan kada kumin bakin ciki".

Kallon juna sukai suna shekewa da dariya suka ce "sai hajiyan mu muna yinki".

Washe baki tai yauwa ko kufa haka nake son ji".

Cikin wayo Bilki tace "amma hajiya kinsan bazai somu a haka ba dole sai muna kyawawan shiga irin ta 'ya'yan masu kudi muna kwalliya kuma bamu da kudi yanzu ni saurayi na yayi tafiya".

Dariya Rasheedat tai "nima nawa garan yayi tafiya shekaran jiya kuma banda ko sisi hajiya a cikin kudin daya baki zaki bamu ko dubu biyar ce".

Zaro ido hajiya tai "caf dubu me lallai yaran nan baku da hankali ko biyar bazan bayar ba balle dubu biyar".

Hada ido sukai suna 'kiftawa Rasheedat tace "shikenan hajiya zamu nema amma ki sani idan yazo yace yana son mu ya aure mu kada muga yar 'kafar ki a gidan idan ma kinje zamu sa securities suyo waje dake mu nuna bamu sanki ba daga mu sai iyayen mu".

Shiru hajiya tai jikin ta yayi sanyi ta dauko kudi tana cewa "saidai na baku Kowaccen ku dubu biyu nima fa dubu goma ne kawai".

"To shikenan munji bamu".

Mika musu tai suka mike suna fita hajiya data bisu da kallo tace " jimin shegun yara da wayon banza kodan idan dadin yazo tare zamu ci🤣.

Fita sukai suna dariya Bilki tace "wallahi dama yau haka na tashi ko sisi banda amma yanzu ga dubu biyu ziyau muje muyi wanka muzo muci uwar dubu hudun nan".

Fita sukai daga bangaren hajiya kowa yana shiga kofar su dan yin abinda suka ce.

Fitowar su waje Aliyu ya kalli Samir yana cewa "Kai Samir wannan wanne irin wulakanci ne ka nuna min"?.

"Eh da nai me "?

"Da kai ban sani ba cewa fa nai muje ka nuna min ajiyar dana baka"?.

"Oh sorry sorry my buddy kayi hakuri zan nuna maka ba yau ba".


"Sai yaushe"?.

Cikin tsokana Samir yace "tommorow morning"?.

Hade rai yai "tommorow morning kuma"?.

Shiru Samir yai kallon sa Aliyu yai ganin dariya yake masa yasa yadan daki kafadar sa yana cewa.

"You're not so kind mutumi na kana bani ciwon kai".

"Yi hakuri Marshall insha Allah gobe da safe zan baka magani zaka warke".

Amira na jin labarin cewa Aliyu ya dawo ta ciko trolley da kaya ta dawo gidan cikin farin ciki da nuna za'kuwa ga soyayyar da take masa 'karara baya boyewa.

Wace Amira 'Yace a gurin professor Bashir da hajiya Laraba ala'kar abota ce tsakanin Daddy da mahaifinta kuma akwai shakuwa mai karfi.

Bugu da 'kari Amira ta taso da ciwon son Aliyu a Zuciyar ta hakan yasa kullum tana zarya a gidan tun tana karama ta shiga makarantar aikin soja saboda Aliyu saidai dole ta hakura da aikin sakamakon cutar asma da take damunta.

Saita sauya karatu zuwa bangare irin na babanta tayi zama da Aliyu a kasashe daban daban shine yake kula da karatun ta saida bayan ta kammala ya dawo da ita gida cikin aminci kamar yadda aka bashi amanar ta..

Tun bayan rabuwar su basu sake haduwa ba shekara uku da rabi sai yanzu 'kawarta khulsum dake aiki a airport tai kiranta a waya ta sanar mata cewa taga Aliyu ya dawo.

Afifah na zaune a d'aki taga an budo kofa sai ganin Amira tai jikin ta har mazari yake ga trolley sha'ke da kaya da mamaki tace.

"Amira yaushe rabon da na ganki kusan shekara uku fa tun lokacin da yaya discipline ya dawo dake".

Murmushin farin ciki Amira keyi tace.

"Yau kuma sai gani bayan wadannan shekarun naji labarin Aliyu ya dawo shiyasa kika gan ni".

"Oh wa ya fad'a miki"?.

Zama Amira tai tana zuge zip din Jakarta ta dauko phone dinta zata kira Aliyu kafin tace.

"Ina da 'kawa a airport Khulsum itace taga saukarsa sannan ta kira ni ta fad'a min".

Murmushi Afifah tai tana cewa "gaskiya yayi fa to sannu da zuwa, Amma Amira yaushe zamu sha biki ne"?.

Batare data d'ago ba tace "taya zaku sha biki bayan baku shirya ba".

"Kamar ya meye namu a ciki bayan anko ko a dangin mu angon yake"?.

Rolling eyeballs dinta Amira tai tana cewa.

"To da fa ina kike kaini".

Da mamaki Afifah tace "wa kenan".

Zaki sani ba yanzu ba sainan gaba fata na zaki taimake ni wajen cika buri na".

Kai Afifah ta jinjina "ba damuwa".

"Am dan Allah Afifah kisa a kawo min abin sha mai sanyi".

Mikewa Afifah tai daidai zata fita tana cewa.

"Ok".

Yayin da Amira ta kwanta tana sake kallon secreen din wayar ganin kiran na shiga amma ba'ai picking ba karshe idan ta tura kira ma sai ai reject.

Aje wayar tai tana jan tsaki wato Aliyu har yanzu yana nan kamar da bai canza ba lallai da 'kura a gabanta zata sha fama.

Washe gari da wuri Amira ta fito ko Allah zaisa ta ga fitowar Aliyu domin duk jiya basu hadu dashi ba.

Tana zaune Afifah ta fito ganinta ita kadai yasa ta karaso tana zama tace.

"Yadai Amira ya haka"?.

Dagowa Amira tai cikin damuwa tace.

"Ya me"?.

Kallon ta sosai Afifah keyi tana nazarin ta tace.

"Naga kinyi tagumi kuma da alama kamar baki breakfast ba"?.

"Eh Afifah ba banyi ba taya zan iya cin abinci ni Aliyu zai wulakanta har kamar ni na masa kira yakai ashirin amma bai picking ko daya ba karshe har rejecting yake lallai kuwa zaisan yayi Dani saina nuna masa Fushi na".

Wani kallo Afifah tai mata tana cewa "caf karki soma shawara ce nake baki ki fita hanyar yaya discipline kafin ki tafi gidan ku da 'kafa ta koma daya da rabi ya Aliyun kike fadawa hak......


Shiru Afifah tai tana rufe baki ganin Aliyu ya sauko kuma ya kalleta yasa tadan kau da kai.

Zama yai a dinning yana daukar karamin kofi zai hada tea Afifah ce ta karasa inda yake batare daya dago ba yace.

Kina neman wani abu ne"?.

Ja da baya Afifah tai tana cewa "a'a yaya dama kai zanyi serving".

"I don't want bar nan kafin ke na 'balla miki 'kafar da kike magana".

Barin gurin Afifah tai tana komawa parlor da sauri d'aram Amira ta mike tana zuwa inda yake cikin shiahshigi tadau plate tana serving dinsa Irish Wanda yaji 'kwai tana direwa a gaban sa ta kama kujera ta zauna itama tana serving kanta.

"Ke meye haka"?.

Daidai Amira takai loma bakinta ta dago tana kallonsa cikin yanga tace.

"Da nai me"?.

"Do you want to know why"? Dan rainin wayo na miki tambaya kema ki min ni sa'anki ne"?.

"A'a ba daya Amma ai masoyi na ne kai ko ba haka ba"?.

"Waye masoyin naki"?.

Fari tai tana murmushi tace "ina wani bayan kai Aliyu kaine".

"Ki daina 'bata lokacin ki a kaina Amira".

"Me yasa"?.

"Bana so kiga kamar na cuce ki a gaba".

"Bazan taba gani ba Aliyu ko maye dan Allah ka aure ni"?.

Hannu ya daga mata "listen up daina ro'ko na Amira ni ina da wacce nake so".

Zaro ido tai firgici dimuwa damuwa tashin hankali razana sune suka sameta lokaci guda tea din data kurba ya kwareta ta soma tari mai karfi.

Yana kallon ta baice 'kala ba har ta gama Afifah da ta taho da gudu tana bude fridge ta dauko mata ruwa tana kawo mata kallon da Aliyu ya mata yasa da sauri tabar gurin tana rike baki cikin mamakin wa Aliyu yake so dama yana soyayya Amma bai ta'ba nunawa ba lallai kwanan nan zasu samu aunty.

Kasa daukar ruwan Amira tai balle ta sha ga zafin da 'kirjin ta ke mata kamar gidan gasa biredi hawaye ya cika mata ido yana gangarowa amma taga Aliyu kawai breakfast dinsa yake.

Kuka ta fashe dashi tana cewa "Aliyu dama kayi haka da niyya ne a Zuciyar ka dama son kashe ni ne 'kudirin ka".

"Ke are you out of your sense 🙄 ni kike fad'awa haka? Kinyi hauka ne"?.

Cikin kuka tace "ba hauka ne ya kama niba Aliyu kaine kake neman haukata ni da maganganun ka".

"Da nace miki me".

Kana da masoyiya".

"Eh zan miki karya ne saboda gudun 'bacin ranki"?.

"Kuma auren ta zakai"

"To da me kika dauka zan yaudare tane?.

"Ka bani amsa aurenta zakai"?.

"Ban sani ba"😠.

"A ina take"?.

"Meye matsalar ki da inda take"?.

"Had'uwa nake so muyi da ita domin naja mata kunne cewa ta fita layin da ba nata ba kafin tai asarar rayuwar ta dan wallahi saina kashe ta".

Mikewa yai cikin halin ko in kula alamun maganganun ta basu sha masa kai ba yace.

"Look it up on Google madam zaki ga komai nata da adireshin ta da mahaifinta da inda suke sai kije ki sameta".

Zai bar gurin a gigice Amira ta mike tana shan gaban sa cikin kuka tace.

"Meye sunan ta da ya zan gane ta"?.

Murmushin ganin haukan ta yai yana d'an girgiza kai yace.

"Never mind 'yan mata karki damu kanki ba sunan ta zaki nema ba ita ya kamata ku had'u".

'Kara ta saki mai karfi tana dukan bango tace.

"Ka fad'a min sunan ta".

Lamarin ta na bashi dariya matuka amma ya dake dan baya son raini yace.

"Sunan ta Mrs. ALIYU MARSHALL anguwar da take gidan Aliyu quarters gidan da take part din Aliyu d'akin da take Zuciyar Aliyu na gama

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment