Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ke ba ta da shamaki, ko me tuhumarta.” Nafi ta zaro idanuwa a ruɗe bakinta na motsi a hankali ta ce “Dama a binni a saida mutun??” Ta fashe da dariya sosai, Sai da ta yi mai isarta sannan ta ce “Lallai Nafi na sake yarda ke yarinya ce sosai, ai idan kika ji saidawa ɗaya ke nan, ke dai kawai ki kwana cikin shiri gobe, Kuma ki saki jikinki kar ki nuna kin san komai zan taimake ki ki bar Gidan nan duk da Aikata hakan abu ne mai matuƙar wahalar gaske amma zan ƙoƙarta.” Jiki a sanyaye ta kwanta tana jan bargo har kanta..
Ummi ta dubi Bilkisu ta ce ‘Tirr da ke! Gaskiya kin ba ni kunya yanzu kan mutuwar Maƙiyinmu kike damuwa Mts! Ni na rasa ke da Zubaida wa ya fi wani Sakarci da rashin sanin ciwon kai, ku rasa wanda za ku so duniya sai Yarima, ga Hisham nan da Adam masu jiran gado amma duk ba su yi maku ba dan lalaci sai Ahmaad.” “Haba Mammy ya za ki ce haka ni fa ba sakarya ba ce na san me nake yi” Bilkisu ta faɗa cikin ɓacin rai dan su Mammy suke ce ma Ummi. Ta harare ta cike da Rashin mutunci ta ce “Kin yi daidai bari na kira Ubanki sai ki faɗa masa haka, shashashar banza Mts!’ Tana gama faɗar haka ta fice daga ɗakin Hankalinta a tashe. Ta tura ma Galadima saƙo......*Littafin ZUCIYA. . . Na kuɗi ne Naira ɗari biyu 200, Vip kuma ɗari biyar 500, ga wanda ya shirya biyan nasa 1634835509 Access Bank. Sai a turo shaidar biya ta wannan Lambar 09117440993. Waɗanda basa son hayaniyar group da waɗanda ba 'yan Nigeria ba za su iya siya a Arewabooks, ko ku yi Subscribing a BakandamiyaHikaya.*

Wannan Page ɗin daga shi sai Last Free page, Ki yi ƙoƙari 'Yar'uwa ki biya naki Kuɗin, saboda masoyana Na sauƙaƙa ɗari biyu, Ku turo ta wannan Account ɗin 1634835509 Access Bank. Ina ba ku Tabbaci in sha Allahu ba za ku yi nadamar siyan Littafin Zuciya ba.

~*#K N W CHANNEL.*~
_*#Q A L B*_
#09117440993.


https://wa.me/p/6447799395325349/2349117440993
*K_shitu’s Noble World Channel.*
*Khadija Muhammad Shitu*
*ArewaBooks:Kshitu*
*Wattpad:Kshitu*
*Bakandamiya:Kshitu*
*OkadaBooks:Kshitu*
*Paid book 200, Vip 500*
*1634835509 Access Bank.*
*End of free Pages*
*Reposted.*
*09117440993*

*ZUCIYA...!!*
(Qalb).

*(25).*
Tun da Abdul ya shiga motarsa ya fara tafiya kan titi zuwa Asibitin Dr. A yake jin gabaɗaya duniyar ta yi masa zafi, ya kasa ci gaba da tuƙin da yake yi, ya yi Parking ɗin Motar gefen titi ya duƙar da kansa yana jin ɗaci a ransa. Bai taɓa sa ran zai Rasa Ahmaad nan kusa ba, Ashe ba shi da tsawon rai, Kai ya ma kasa gasgatawa har lokacin Ahmaad ya bar duniya. Ya fesar da huci mai zafi wasu hawaye na bin kuncinsa. Lokaci ɗaya kuma Rayuwarsu ta baya da suka yi shi da Ahmaad ɗin ta soma dawo masa tamkar a wasan kwai-kwayo ya lumshe idanuwansa Yana tunane-tunane. Ya ɓata lokacin a nan ba tare da ya taɓuka komai ba, Da ƙyar ya ja motar ya ƙarasa Asibitin. Ya yi Parking ɗin motar ya fito ya shiga ciki ya nufi hanyar Office ɗinsu, Ya wuce Office ɗin Ahmaad ɗin ya tsaya ya Kalla sannan ya wuce tuna fitar da suka yi ta ƙarshe yake yi. Ya kasa shiga nasa Office ɗin ya nufi na Irfaan duk da ya san ba lallai ba ne ya same sa ba. Ya buɗe Ƙofar a hankali cikin Rashin kuzari ya shiga. Ga mamakinsa sai ganin Irfaan ɗin ya yi, yana harhaɗa abubuwansa Cikin wata jaka da Alama fita zai yi, Ya yi sallama a hankali suka gaisa tare da yi ma juna ta'aziya Sannan Abdul ya zauna yana faɗin “Lafiya dai Irfaan Ina za ka je ne?” Ya numfasa cikin nuna damuwarsa ya ce “A gaskiya Abdul ba zan iya zaman Hospital ɗin nan ba, Komai ya fice daga raina ina son komawa gida ne.” Ya dafa kafaɗarsa cikin dakiya ya ce “Ka yi haƙuri ka ji! Komai yai farko yana da ƙarshe in Allah ya yarda ka ƙara haƙuri dan Alkah kar ka ce za ka bar asibitin nan” Ya numfasa ya zauna sannan shi ma ya fara magana a hankali, “Wallahi Abdul gabaɗaya zaman Asibitin ya gundure ni ne”. “Ka yi haƙuri duk da haka Dan Allah”. Ya ce “Shi ke nan ba matsala. Ka zauna mana”. Ya zauna ya fuskace sa sosai Sanna ya fara magana, “Na ce Irfaan wai yaushe Akarsh ya tafi ne da Dr Daniel sun yi maka bankwana ba a sallame su ba fa??” Ya yi masa kallo irin na rashin fahimta sannan ya ce “Kana nufin sun tafi ke nan? To ni gaskiya tun washe garin rasuwar ban sake ganin su ba.” Ya kalle sa cike da tsananin mamaki ya ce “Kana nufin ba ka san sun tafi ba sai yanzu da nake faɗa maka?” Ya jinjina kansa don tabbatarwa ya ce “Gaskiya sai yanzu da ka faɗa na sani, amma akwai wata matsala ne?” Ya ɗan zaro idanu ya ce “Hum! tambaya ma kake yi, Wallahi sam hankali bai kwanta da Daniel ɗin nan ba daga baya haka nan nake jin tsanarsu har Akarsh ɗin, kai ba ka ga alamomin rashin gaskiyar da suka bayyana ba tattare da su lokacin da Ahmaad ya rasu??” Irfaan ya sauke numfashi ya ce “Ni kaina tuntuni na dasa musu alamar tambaya, sai dai tun da na ga har kai ka aminta da su ne ya sa kawai na share. Amma ka tabbatar Sun bar Ƙasar nan kuma ka kira layinsa na India da na Nija??” Ya girgiza kansa a hankali ya ce, “Duk na ruɗe ne, ban yi wannan tunanin ba bari na kira shi. Yai saurin riƙe masa hannu da yake ƙoƙarin kiran Akarsh ɗin ya ce, “Ba buƙatar ka kira sa, ka bari mu je gidan Kawai mu ganewa idanunmu.” Ya miƙe tsaye yana faɗin “To mu je ga mota chan a parking lot.” Suka shiga Motar Abdul ya tuƙa su ya ɗauki hanyar Gidan Akarsh. Suka ƙarasa gidan ya yi Parking daga waje suka Yi Knocking ɗin Main Door ɗin amma ba a buɗe ba, sun fi mintuna goma nan ba su haƙura ba, suka ci gaba da bugawar, suna ta jin hayaniya. Maigadin ya buɗe a fusace dan ganin su waye, Ganin Abdul da ya yi da wani ya sa, ya ɗan sassauta fuskarsa ya ce “Sannu Yallaɓai” Abdul ya amsa yana ƙaƙaro murmushi sannan Ya ce, “Dan Akarsh fa yana nan??’ Sai da ya ɗan yi jim kafin ya ce “To ban dai sani ba gaskiya ku dai shiga ku duba. Yallaɓai Ashe abin da ya faru ke nan da Dakta Ahmaad, Duk waɗanda suke da hannu a kan mutuwarsa Allah ya gaggauta tona musu Asiri, Allah kuma ka rabamu da zaluncin nasara! Duk yanda kake ƙaunar kafuri baƙin kafurci ba zai taɓa bari ya ƙaunace ka ba, kullum cikin yunƙurin ganin bayanka zai kasance, Allah ya kunyata su a mika mini ta'aziya ga ‘yan’uwansa”. Da 'Amin' Abdul ya amsa suna shiga cikin gidan, Ƙwaƙwalwarsa sai juya maganganun Kamal Maigadi take yi, Ya yi shiru har suka ƙarasa cikin gidan sai dai A mamakinsu suka ji tsit saɓanin da, da suke ta jin hayaniya sosai. Lokaci ɗaya gidan ya yi tsit, suka nufi Main parlourn suka yi, Knocking suka ga ƙofar a buɗe take suka shiga ciki. Shiru Parlourn babu kowa sai dai Waren takalmi da suka gani tsakar parlourn, sai kuma abinci da aka zuzzuba a dinning da ƙamshin girkin da ke tashi an fara ci. Ga kuma Tv kunne amma kan kashe ƙara, sun dudduba ko ina sun ƙwala kiransa amma babu Akarsh babu dalilinsa. Cike da ƙuluwa Abdul ya ɗaga waya ya kira sa, Ringining biyu suka fara jin ƙarar waya, sai kuma suka daina ji, Miscalls Bakwai ya yi masa amma bai ɗaga ba, kawai Abdul ya girgiza kai ya kalli Irfaan suka fice. Lokacin da suka fito Maigadin bai nan, suka buɗe gate kawai suka fice. Abdul Yana Driving ya kalli gefen titi kaɗan ya ce “Ka san me Irfaan?” Irfaan ya girgiza kai alamar A'ah. “Me ka fahimta, ka kuma gane da zuwanmu Gidan Akarsh!” Yay jim kaɗan kafin ya ce “Kamar yana cikin gidan bai bar ƙasar ba kuma baya son haɗuwa da mu”. Abdul ya ɗan yi murmushi sannan ya fara magana. “Hum! Irfaan. Kafin mu shigo Cikin Parlourn muna magana da Kamal na ji Hayaniya sosai da sautin kiɗa da ke tashi, sannan A Maganganun Kamal ɗin baka hango abin da yake nufi ba, kuma Yanayin Parlourn da yanda yake ka hararo wani abu??” Ya girgiza kai da sauri ya ce “Ka ɗan ƙara mini haske Please kana nufin Akarsh ba ya son ya haɗu da mu shi da Daniel ne??” ya ce “Good Ka fara ɗaukar hanya, Ina zargin Akarsh akan abubuwa da dama, gobe za mu yi magana bari na yi droping ɗinka nan zan shiga Masarauta.” Ya shiga cikin asibitin ya ajiye sa, sannan ya Juya ya ɗauki hanyar masarauta. Tun da ya shiga yay Parking ya fito, mutane da yawa ake ta gaishe shi da yi masa ta'aziyar mutuwar Abokinsa, yana ta amsawa, Ya ɗauki hanyar ɓangaren Waziri mahaifinsa, Ya shiga Parlourn mahaifiyarsa, ta sallami Hadimanta suka gaisa tana ma Ahmaad addu'a. Ya miƙe ya shiga ɗakinsa da ke cikin Parlourn dan ya yi Wanka. Ko mintuna goma bai yi ba da shiga ba, Bilkisu ta faɗo Parlourn mahaifiyarsa tana wani tattauna cingum cike da tsageranci da rashin Kunya. Ta zo ta tsaya kan Mama ta fara surfa mata tijara da tsantsar rashin mutunci har tana jijjiga jiki. “Wai me ya sa kike wasu abubuwa kamar ma ke ce sarauniya matar Sarki Mts! Wallahi idan ba ki kama kanki ba za ki sha mamakin rashin mutuncin da zan miki, sai kawai ki je ki kai ƙara ta wajen Mammy tsabar wulaƙanci Mts...,”. Ƙarar saukar marin da ta ji da zafinsa ne suka hana ta ƙarasawa, cikin Zafin nama ya ingiza ta ta faɗi. Mama ta yi saurin miƙewa tana faɗin “Hum ai da ka ƙyale ta, ni nan da ta ganni a yanzu daidai nake da kowane shege mai jin kansa na masa tururin tsageranci, Maza ki fice mini dga sashe tun kafin nasa bayi su yi miki korar karya sakaryar banza, shashasha marar Tarbiyya.” Cike da tsananin mamakin da ya kasa barin kan fuskarta ta ce, “Ni kuka maka haka?? Wallahi ku sani sai na tozarta Rayuwarku Ni Bilkisu!!” Ta fice tana sakin wani zazzafan huci da sake jin wata muguwar tsanar Abdul da Mama. Ta nufi Ɓangaren Mammy a fusace. Ko iso ba ta jira an yi mata ba ta faɗa Parlourn tana ƙwala mata kira, “Mammy! Mammy! Kina ina??” Tsabar rufewar da idanuwanta suka yi ba ta ma hango su ita da Galadima ba a Dinning ba. Ta ƙarasa fuu.. Cike da Rashin Tarbiya, “Wai Mammy dama kin san tozarci da za a min ke nan, shi ya sa kika tura ni wajenta?” Galadima ne yay saurin fadin “Calm Down my daughter! I'll explain everything for yuh so that you'll understand what i'm trying to do, Please have a seat” “I Cant! Dad you said I should calm down! Do you know what they have done to me she nd her Son?? i can't even repeat this kind of shameless to anybody, just keep waiting i'll surely suprise them”. Tana gama faɗar haka ta wuce cikin zafin nama ta faɗa ɗakinta. Mammy ta dubi galadima cike da son jin ƙarshen maganar da suka fara. “Kana faɗin min” ta ce tana gyara zama. “Ai ina tabbatar miki da Ahmaad ya daɗe da mutuwa, Dan kuwa..,” Ta yi saurin faɗin 'Shh! Ya ɗan yi 'yar dariya zai yi magana ta yi saurin katse sa. “Wallahi na kasa yarda ya mutu, kullum ina tunanin Asirinmu ne zai tonu, ina jin tsoro sosai fiye da zatonka, na kasa aminta da zance mutuwarsa. Na kasa samun salama kullum cikin fargaba nake da Ruɗani” Ya numfasa ya ce, “Hum! ba ke kaɗai ba Malika Ni kaina haka take ban taɓa tunanin al'amarin zai dame ni ba, Shi ya sa na yanke shawarar bin umurnin ...A... mu kawar da Likitocin nan kafin barinsu ƙasar dan Alamominsu sun nuna akwai wani abu da suke shirin aikatawa tun kafin mu kwashi abin kunya. Kin ga bara na je, da dare ma ƙarasa tattaunawar.” Sai wajen Ƙarfe bakwai na dare sannan Abdul ya ɗauki Hanyar zuwa wajensu Ammi. Ya Parking ɗin motarsa yay Knocking ƙofar bakinsa ɗauke da sallama ya shiga jin door ɗin a buɗe. Zaune ya samu Ammi na karatun Alqur'ani ya ƙarasa yana ɗan murmushi ya zauna. Wayarsa ce ta fara Ringing ya kalli sunan Akarsh yay saurin ɗagawa. “Hello.. Akarsh” Ya fada a hankali. Muryar Wani ya ji ya fara magana. “Ba likita Akarsh ɗin ba ne, Jami'an tsaro ne, Yanzu haka an kashe Ɗayan likita da suke tare, shi kuma yana cikin wani irin yanayi, shi da Maigadin gidansa, Ko za mu iya samun ganinka yanzu.!” Wata irin faɗuwa gabansa ya yi, cikin Rawar murya ya ce “E.” Ya ajiye wayar jikinsa a matuƙar sanyaye. Ammi ce ta dube shi ta ce “Lafiya?” Ya ja numfashi A hankali ya faɗa mata komai. Sosai hankalinta ya tashi ta ce “Innalillahi Wa'inna ilaihi raji'un ka san Nasaran nan ba su da imani azzalumai ne basa ƙaunar musulmi kullum cikin nemanmu da sharri suke yi ba mu yi musu komai ba, ina ga an kashe musu Ɗanƙasarsu Ya ilahi. yanzu tashi ka je da sauri” Ya miƙe cikin kyarmar jiki, sai kuma aka sake kiran wayar, ya ga Private number ya ɗaga ya sa Handsfree dariya aka dinga yi ba ƙaƙautawa sannan aka ce a daƙile. “Ka duba whatsApp ɗinka akwai saƙonmu.’ Yaraf ya faɗa kan kujera yana dafe kai Ammi ta ce ya shiga su gani. Saƙonni na cikin shigowa ya ga wata baƙuwar number an turo masa photo, Yana buɗewa hoton suka ƙura mishi ido. Hoto na farko na Mariganyi Sarki Abubakar Ahmaad Lamiɗo ne, wanda aka yi ticking ɗinsa, sai kuma na Tsohon galadima da ya rasu shi ma aka yi ticking ɗinsa, Na uku kuma Ammi ce ba a yi ticking ba sai kuma Imaan, sannan Ahmaad shi ma an yi ticking, sannan waziri ba a yi ticking ba, sai kuma, Matar sarki ta yanzu Halimatu ba a yi ticking ba, sai kuma na Akarsh da Daniel da aka yi Ticking suma. Hankalinsu ya yi mugun Tashi suka shiga nazarin Hotunan, ba wanda ya iya furta ko da kalma ɗaya ce.....
Washe Gari...Nafi na cikin Barci Hinde ta tashe ta, ta ce ta shiga ta yi wanka, ta yi, ta ba ta wasu kaya masu kyau ta saka suka fito Parlour dan ba Maganar sallah. Hajiya Safeena da baƙinta duk sun hallara a dinning. Ta gaishe da su suka amsa suna sakar mata murmushi tare da tukwicin kallon ƙurilla da ya saɓa ma addinnin musulci mai cike da zallar Sha'awarta da Kwaɗayinta. Suna gama cin Abinci Hajiya Safee ta ce ma Tala ta sake shirya ta da wuri za su fita Shopping yanzu. Suka koma ɗaki ita da , Tala, suka shige Toilet tare ta kamo ta ta ce, “Ki natsu ki saurare ni da kyau, karki aikata abinda zai halaka ki mutu Bakiɗaya dan da Alamu aurenki hajiya za ta yi.” Ta raɗa ma Nafi wasu maganganu, sannan ta fito da waya Ta miƙe mata ta ce “ki ɓoye ta har sai kun je, Akwai Ɗansahun da zai ɗauke ki indan kika fito daga Shopping Mall ɗin wanna shi ne hallacin da zan iya miki a matsayinki na mai ƙananun shekaru,”. Ta sake ɗaukar wanka cikin wata Arniyar Gown mai tsananin kyau Army green da veil Milk color sannan ta ba ta takalma da 'yar purse. Ta fito Parlourn da ita Hajiya Safee har ta shirya. Ta kamo hannunta suka fara takawa har Zuwa Parking Lot ɗin gidan. Ta buɗe wata ƙatuwar mota ƙirar Lexus baƙa siɗik, har glasses ɗin tinted. Ta ja su da mugun gudu Gate man ya buɗe musu ta fara tafiya. Nafi sai kalle-kalle take zuciyarta cike da tsananin tsoro tana ta tunane-tunane har suka iso Bata sani ba, sai da ta ji hannun Hajiyar a jikinta sannan ta yi firgit ta dawo hayyacinta, ta sakar mata wani makirin murmushi ta ce “Nafeesa mun iso fito mu shiga ki zaɓi duk abin da kike so”. Ta ɗaga kai sannan ta buɗe motar suka fito. Haɗaɗɗiyar S Mall mai kyau ta kawo su, Suka shiga Nafi na ta kalle-kalle irin na ƙauyanci, ta bata Basket ta ce ta jidi duk abin da take so, ita dai haka nan take zagayawa tana ɗaukar abubuwa waɗanda ba ta ma san amfaninsu ba kwata-kwata. Ta shiga jerin inda kayan sawa suke ta ɗauki wata riga ta ce ma Hajiya bari ta gwada, daɗi ya kama hajiyar ta ce to ta mata kwatancen inda ake gwadawar, Tana shiga ɗakin ta kashe fitila ta yarda rigar ta fara kallon ɗakin Ƙofar da ta sake gani ce ta sa ta murɗawa, ta ga banɗaki ne, ta shiga ta yi sauri ta kulle, ta fara leƙen tagar banɗakin, Ta ga wani Ɗansahu daga waje ya yi Parking sai dube-dubae yake, ta gyara yanda zata diro duk da kuwa tsananin tsayin ginin. Amma ta rufe idanuwa kawai babu ko ɗar a ranta ta faɗo ƙasa wajen Shoping Mall ɗin daga baya. Sai kuma ta tsaya tana kallon tsananin Tsayin inda ta faɗo kuma ba abin da ya same ta ko ƙwarzane, ta faɗa cikin Napep ya ja ta da gudu, suka fara tafiya, Sai nishi take yi da sauke Ajiyar zuciya.......
*#K_shitu🦋*
*#ZUCIYA. . .*
*#Q a l b*
*#AhNaf💔*
*#End Of Free Pages*
*-2023*

_MA SHA ALLAH..ALHAMDULILLAH A NAN NA KAWO ƘARSHE FREE PAGES ƊIN WANNAN LITTAFIN NA ZUCIYA, MAI SON CI GABAN ZAI BIYA NAIRA ƊARI BIYU KACHAL..,KAR KU MANTA WANNAN LABARIN DA KUKE KARANTAWA K_SHITU CE TA ƊAUKI NAUYIN KAWO MUKU SHI KUMA TA TSARA TA RUBUTO✌🏾🌝📕MUCH LOVE REAL FANS NA GODE, NA GODE DA KARAR DA KUKA NUNA MANI NI DA ZUCIYA. . . INA MUKU FATAN ALKHAIRI.♥️🦋💋_

*Littafin ZUCIYA. . . Na kuɗi ne Naira ɗari biyu 200, Vip kuma ɗari biyar 500, ga wanda ya shirya biyan nasa 1634835509 Access Bank. Sai a turo shaidar biya ta wannan Lambar 09117440993. Waɗanda basa son hayaniyar group da waɗanda ba 'yan Nigeria ba za su iya siya a Arewabooks, ko ku yi Subscribing a BakandamiyaHikaya.*

From The Writer of;
Takobin sirri
Ƙurarren Lokaci
Shekeruna
Sarautar Iko
Baƙin buri
Dafin Namiji
Baƙar Illah
Sihirtaccen iko
Na'aj
Sirrina
Izzar sarauta
Zuciya. . .

Za ku iya Tuntuɓa ta ta wannan Lambar 09117440993.

```Yanzu ne wasan zai fara..```
-🦋✌🏾💋🌝-.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment