Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta raunata sosai ta kasa, Ta rushe da wani irin kuka tana jijjiga shi tana ba shi haƙuri, magana take yi ita kanta ba ta san me take furtawa ba. “Ahmaad ka tashi dan Allah ba zan tilasta ka ba, na yafe maka ba zan sake fushi da kai ba..” Kamar daga sama Imaan ta faɗo ɗakin jikinta na rawa tana ganin halin da suke ciki ta fashe da kuka jikinta sai wata irin karkarwa yake ta rugo da gudu ta tsaya gaban Ahmaad wanda har lokacin yana yanda yake ta durƙushe ƙasa tana wani irin kuka mai raunata zuciya ta kamo hannayensa duka tana magana muryarta na shaƙewa, irin yanda hankalinta ya tashi dole mutum ya fahimta ko kallo ɗaya idan aka mata.“Yaya Please wake up! and say something, don't brake our hearts, you're our only hope and everything, i can't even imagine it, Dan Allah Yaya ka tashi, ka ce wani abu Zuciyata za ta fashe, Ba zan iya rayuwa kana cikin wani hali ba a saboda ni! Na sani ni ce silar komai ka tashi ni ce na chancanci mutuwa!!” Imaan ta ci gaba da kuka mai tsayawa a ƙarƙashin zuciya. Duk maganganun da take yi da kukan da suke yi Yana ji, amma ba zai iya aiki da kowane sashe na jikinsa ba, Ya lumshe idanuwansa wasu hawaye masu ɗumin gaske suka zubo daga idanuwansa. Ta miƙe jiri na ɗibar ta Hankalinta a tashe kamar za ta faɗi ta fice tana ƙwala ma Dr Irfaan kira. Shi kanshi da ya shigo ya ga yanayin da suke ciki sai da ya yi hawaye. Cikin gaggawa ya fara kiran Asibiti. Mintuna goma bisani suka ji ƙarar Amblance daga Asibitin, da ƙyar ya samu Abdul ya miƙe suka kama Dr. A suka fito harabar gidan suka saka shi cikin Ambulance, Irfaan ya shiga suka bar gidan, suka nufi Asibiti. Kafin su ankara Ammi ta yanke jiki ta faɗi Tashin hankali da ruɗanin da suka shiga ɓata baki ne tsayawa misalta shi, Abdul ɗin ma ya rasa taƙamai-mai mai zai yi. Kuku da ya shigo tuntuni komai ya faru kan idanunshi shi ma sai hawaye yake, dan dama godiya ya zo ya yi akan maƙudan kuɗaɗen da Dr A ya turo masa Naira dubu ɗari biyar. Sai kuma ya ci karo da wannan tashin hankalin. Driver ne ke tuƙa motar Abdul na gaba Imaan da Ammi sun baya. Suna ƙarasawa Asibitin suka nufi Office ɗin Abdul da Ammi, ya kira wani Likita ya ba ta taimakon da ya dace, dan a irin yanayin da yake ciki ba zai iya taɓuka komai ba. Sai da ya tabbata an yi wa Ammi allurar barci kuma numfashinta ya daidaita sannan ya bar imaan gurin ta. Ya nufi Emergency room ɗinsu. Akarsh da Doctor Danial ma duk sun iso Asibitin suna Emergency room. Abdul ya chanza kaya, ya saka hula da nose-mask ya tura ƙofar gabansa na faɗuwa ya shiga. Jigum-jigum ya gansu tsaitsaye kowanensu na iya bakin ƙoƙarinsa, gabaɗaya sun kasa shawo kan matsalar duk yanda suke tunanin tsauri da tsananin Tasirin maganin da kuma tasirinsa me matuƙar hatsari ya zarce tunaninsu, Tun da suka shigo su ke ɗirka masa allurori daban-daban da yi masa aune-aune kala-kala, ZUCIYArsa ba ta buga ba tana aiki, Tsananin zafin jikinsa da yanda zuciyar ke bugawa ne ya yi bala'in sake rikitar da su. Ba su taɓa tunanin hatsarin abin ya kai haka ba. Abdul ɗin shi ma ya yi iyakar yinsa da ƙoƙarinsa amma al’amarin ya girmi tunaninsu, Duk da Akarsh, Irfaan, Abdul, Uwa uba Doctor Danial ƙwararrun likitoci ne na gaban kwatance amma kaf ɗinsu sun kasa taɓuka komai. Doctor Danial ne ya fito daga Emergency room ɗin yana goge zufa, ya koma Office ɗin Abdul ya buɗe Laptop ɗinsa da take nan Ya shiga searching akan matsalar, Bai jima ba ya koma Emergency Room ɗin. Wata allura Dr Saleem abokinsu ya ɗauko Pharmacy da garin da ake kwaɓa ta, ya shigo Babban Ɗakin da ke cike da Na'urori sai gadajen Marassa lafiya me girma guda biyu, ɗaya Dr. A ɗin na kwance a kai. Ya kawo Allurar, dan da nan suka kwaɓa aka tsira masa ita, suna gani Ya lumshe idanuwansa lokacin da suka zare syringe. Allurar za ta ba shi damar ci gaba da rayuwa idan har Ubangiji ya nufi hakan, kuma yana da rabo, kuma zai samu barci. Daga nan kuma su ci gaba da ƙoƙartawa a kan lamarin. Amma kusan Mintuna Talatin da yi masa ita babu alamun komai, ba wani ci gaba, illa ma wani jini da suka ga ya fara zuba da hancinsa. Ficewa Dr. Saleem ɗin ya yi yana goge Hawaye sai lokacin ne ya fahimci dalilin Kyautar zunzurutun kuɗaɗen da Ya yiwa Ma'aikatan, da shi kanshi da kuma yafe ma duk wani mara lafiya kuɗin magani da komai. Sai lokacin ya sake tuna dalilin da ya sa Shekaranjiya ya ce musu a kai Ziyara asibitoci aka yi hidima sosai an taimaka musu, asibitoci da Na gwamnati da na kuɗi da na ƙauyuka kusan Talatin duk sun je cikin Satin har kuɗaɗe sun raba, Amma da ya faɗa masa Sai kawai ya masa godiya da nuna jin daɗinsa sosai, ya sake tura masa kuɗeɗe. Kafin wani lokaci hatta ƙananan likitocin da ke Aiki a babban asibitin sun san Halin da yake ciki, Asibitin ko ina ka gitta sai addu'a ake masa da kuma fatan samun sauƙi, Wasu har da kuka. Sam Al'amarin ba sauƙi babu wani ci gaba, ga uban jinin da yake ta zubarwa. Abdul ya kira har masarauta ya faɗa wa Iyayensu da kowa. Ana ta addu'o'i. Ammi ta yi suma fiye da Biyar, yanzu haka ma tana Vip Room an yi mata allurar barci. Imaan ma Allurar barci Aka mata dan Abubuwan da take yi tamkar ta zare faɗi take ita ce dalilin ciwon nasa. Abdul na gama waya da mahaifinsa Jiri ya ɗebe shi ya yanke jiki ya faɗi. Duka likitocin sun yi iyakar iyawarsu an kira Manyan likitoci an yi Posting a social media Ƙwararrun likitoci na bada shawarwari, amma Lamarin ya zarce duk yanda suka zata. Hankulansu sun kai fiye da ƙololuwar tashi, Duk sun yi zuru-zuru. Still har lokacin idanununsa biyu yana bin su da kallo, Abun ya tsorata su fiye da tunani ba su taɓa zaton akwai ciwon da ya fi ƙarfin ƙwarewarsu ba sai ranar. Sun ma rasa ta ina za su fara komai. Ba su taɓa cin karo da Rikitaccen al’amarin irin wannan ba, da ace wani ya faɗa musu akwai irin wannan matsalar da hankali kan gaza ɗauka tabbas za su ɗauke shi fiye ma da abin da ya fi gawurtacce kuma shahararren maƙaryaci. Za su iya cewa a lokacin sun gama sarewa dan yana da ransa sun kira sunansa sun yi masa magana Yana ta lumshe ido alamun yana jin su, yana da rai kuma, zuwa lokacin sun saduda lamarin ya fi ƙarfinsu.....
Tala ta gama komai ta jera Abinci a dinning Nafi dai ba ta yi magana ba. Har dare ya yi, ga mamakinta maimakon ta kwana ɗakinta sai ji ta yi Hajiya ta ce Ta je ɗakin Tala su kwana tare za ta ɗan yi tafiya sai jibi za ta dawo ita. Ta amsa suka shiga ɗakin Tare, Nafi ta yi wanka Talar ta ba ta kayan sawa ta sanya. Duk Nafi ta zama wata shiru-shiru lokaci guda. Tun da ta sanya kayan ta ga Talar na ta Kallon bayan hannunta Tafin fari tas da shi, sai fatarta da ke fara ita ma. Kafin wuyan hannun an yi wani zanen TAMBARI mai matsanancin kyau da jan rubutu, Kamar wata Star amma me kyau har sheƙi take yi, Wanda sai ka lura sosai za ka gan ta. Ita dai zazzaɓi-zazzaɓi take ji, ba ta yi wani abu ba ta haye gadon Tala ta rufa mata Blanket ta fice. Wani irin ciwon Kai take ji, ga kuma zuciyarta ba daɗi sam..
Galadima ya sake duban Ummi a karo na biyu yana sheƙewa da dariya. “Hahhhaha!! Kina wasa da Galadima gaskiya, dan duk inda kike tunanin na kai na wuce nan! Dama Hatsabibi ya ce Yau sihirin zai bar jikinsa, zai dawo ya yi nadama marar amfani a banza...” Ya kuma tuntsurewa da dariya ita ma tana taya shi. “To Amma Zubaida fa, yau tun da aka sanar da maganar situation ɗin da yake ciki ta kulle kanta ta ƙi fitowa ko Breakfast ba ta yi ba dan ma na hana ta fita??” Ya murtuƙe fuska yana miƙewa ya ce, “Kar ki damu da ita. Ni zan kula da komai”. Yana gama faɗar haka ya fice.
Hatta masarautar Suna cikin damuwa a kan Halin da Yarima Ahmaad ɗin ke ciki. Duk wani makusancinsa me ƙaunarsa ƙarya yake ya ce ba ya cikin yanayi na ruɗu da karyewar zuciya. Waziri ya fito daga Ɓangaren Hajja, Ya shiga motar tsakiya, Aka shiga fita da motoci daga masarautar, Biyu gaba biyu baya, sai wadda yake ciki a tsakiya. Aka tuƙa shi har zuwa Asibitin da Dr A ɗin yake.....*Littafin ZUCIYA. . . Na kuɗi ne Naira ɗari biyu 200, Vip kuma ɗari biyar 500, ga wanda ya shirya biyan nasa 1634835509 Access Bank. Sai a turo shaidar biya ta wannan Lambar 09117440993. Waɗanda basa son hayaniyar group da waɗanda ba 'yan Nigeria ba za su iya siya a Arewabooks, ko ku yi Subscribing a BakandamiyaHikaya.*

*#K_SHITU🦋*
*#ZUCIYA. . .*
*#Q a l b#*
*AhNaf.*
*#K N W Channel*
*#Paid Book*
*#09117440993*






















Real fans a matso a yi min kara🌝💖🥰🙏
*KS..*
*•HOME OF NATURAL HERBS*
_Ina kuke 'Yan'uwa mata da maza manya da ƙanana, matan aure Zawarawa 'Yan'mata! ku matso kusa Na ce Sanyi fa ya zo😫 Akwai ingantaccen Maganin Sanyi/Infection sahihi me aiki da izinin Ubangiji duk wanda ya yi amfani da maganinmu ya sani Ana samun waraka da yardar ubangiji ga arha ba mu tsawwala ba kowa zai iya amfani da shi. Akwai na Ɗari *800,* sai kuma na *1500* da na *3000* In sha Allahu ba za ku yi nadamar Amfani da Maganinmu ba, muna bada sari da siyan ɗai-ɗaya. Muna aikawa ko ina da izinin Allah_ _*DA NAGARTA MUKE ADO!🤗💯*_
*9201739091*
*STANBIC IBTC BANK*

_Domin neman ƙarin bayani,_
*09117440993 WhatsApp*
*09060584800 Call*


_Khadija Muhammad Shitu_
_Wattpad@Kshitu_
_BHikaya@Kshitu_
_09117440993._

*ZUCIYA...!!*
(Qalb).

*(23).*
Waziri ya isa Asibitin ya shiga Office ɗin Abdul, Dr Irfaan ya yi masa bayanin duk abin da ke faruwa da Ahmaad ɗin. Bai ɓata lokaci ba ya ɗaga waya ya kira Mai martaba ya faɗa masa halin da ake ciki. Sun jima sosai suna waya da shi, Kafin suka yi Sallama ya dubi Irfaan ya ce, “Ina Likitan da ya zo jiya??” Cikin girmamawa ya ce “Bari na kira shi Ranka ya daɗe.” Ya fice da sauri Ya nufi Emergency Room ɗin inda Doctor Danial yake, suka taho tare zuwa Office ɗin Abdul ɗin. Doctor Danial ɗin ya sake yi wa Waziri bayani a kan ciwon Ahmaad ɗin, Daga Ƙarshe suka yanke shawarar fitar da shi Ƙasar Malaysia a ranar suka tattauna da wani babban likita da ke chan wanda ya san Me martaba soaai. Sun cikin Maganar asibitin da za a kai shi a ƙasar malaysia Abdul ya shigo ɗakin. Yanayin yanda ya shigo yana wata tafiya a hankali, ya sa duk suka zuba mishi ido ko wuni ba a yi ba amma har ya ɗan faɗa. Dr Irfaan ya sanar da shi Abin da waziri ya ce, Ya yi Na'am shi ma da batun Mahaifin nasa. Da kanshi ya ɗaga waya ya kira matuƙan Wani Private Jet ɗin Ahmaad ɗin Ya samu duk suna Cikin Garin Kano ɗin, Nan take Abdul ya tura masa kuɗi, ya ce su ɗauko Jirgin Su haɗu a Airport. Ana fitowa daga Sallar Azahar aka shirya Ahmaad ɗin wanda har lokacin yana a yanda yake. Aka saka shi cikin Ambulance Ammi da Imaan sai Abdul Su ma sun shiga wata mota driver ya ja motar Zuwa Airport ɗin. Dukansu sun yi shiru cikin Motar babu mai magana sun yi jugum-jigum, kowa ka kalla fuskarsa cikinsu za ka hango tsananin damuwa tattare da shi. Har suka Iso Airport ɗin Driver ya yi Parking babu wanda yai ko ƙwakƙwaran motsi, Sai da Drivern ya ce ma Abdul da ke gaban motar, “Ranka ya daɗe mun iso.” Bai ce komai ba sai ajiyar zuciya da ya sauke, kusan a tare su Ammi ma suka ankare suka buɗe motar suka fito. Jerowa suka yi suka sa Ammi tsakiya har bakin Inda jirgin ya tsaya za su hau, suna gani Likitoin Asibitin, suka shigar da shi cikin jirgin sannan suka Ammi da Abdul da Imaan kuma suka yi Sallama da 'Yan'uwa da abokan arziƙi, su Akarsh da Dr Danial ma duk sun shiga suka tsaya kan Ahmaad ɗin, Aka rufe ƙofofi da Tagogi, jirgin ya fara ɗagawa A hankali. Suna cikin jirgin har sun fara lulawa ciki Sararin samaniyar, Dr Akarsh da Abdul na ta ƙoƙarin saka masa Oxcygen Suna cikin kiciniyar sanya masa suka ga Murmushi mai kyau kan fuskarsa da kuma zufa sosai a goshinsa, Sai kuma bakinsa da ya ɗan motsa daga nan idanuwansa suka rufe ruf. Cikin murnarsu da tunanin ko ya samu barci ne Suka saki murmushi. Irfaan ne hankalinsa ya gaza kwanciya ya matso sosai Yana kallon Abdul ɗin Kuma ya ga yanda jikinsa ya sake ne Ya ruɗa shi, ya ɗauko Kayan aune-aune ya fara masa, Zuciyarsa ta daina bugawa Ya daina numfashi! Hannuwansa ban da Kyarma babu abin da suke yi, Ya matsa ya yi wa Dr Danial magana ya matso ya dudduba sa. Sai kawai ya girgiza Kansa. Ya ce Musu ya mutu. Ba shi da aka shaƙe ake ma ihu ba har Matuƙan jirgin sai da suka razana da irin ihun da Abdul ɗin ke yi da Ammi suna sanbatu, Irfaan ne ya matsa Idanuwansa na zubar da wasu zafafan hawaye ya ce ma matuƙan idan da hali a koma Kano Allah ya amshi Rayuwar Ahmaad ɗin. Tamkar Abdul ɗin ya zare ya fara dukan Dr. Danial yana kuka yana sambatu, “Who are you?? Ƙarya kake yi ka ce min Ahmaad ya mutu, i can't believe it, you are a mad man, i'll Kill you!!” Imaan ma kukan ta shiga taya su cikin Karayewa da kuma sarewa da al’amarin ta durƙusa gaban Gawar Ahmaad ɗin tana kallonsa hawaye kawai ke zuba daga idanuwanta, Numfashinta na fita da sauri-sauri, ta kasa yarda ma. Audugar da aka sanya aka toshe hancinsa da ke jini da ita ce ta ga ta fara rinewa daga jini zuwa wani baƙin Abu. Cikin su kowa ya ruɗe an kasa samun mai rarrashin Wani Ba wanda ya iya bi ta kan Ammi, Irfaan na kuka idanuwansa sun yi ja fuskarsa ma haka sai jan majina yake, Ya ɗaga waya hannunsa na kyarma ya dannawa waziri kira da Lambar da ya Ba shi bugu biyu ya ɗaga kamar jira yake dama ya ce, *“WE LOST HIM..DR AHMAAD ABUBAKAR LAMIƊO IS DIED!!!”* Daga Chan Waziri ya saki wayarsa ta faɗi ƙasa ya ji jiri na neman ka da shi, ya faɗa kan kujera yana Ambaton sunayen Allah. Lokacin da Jirgin ya sauka Airport Irfaan ne kawai yai Ƙarfin Halin fitowa da Akarsh, suka tari Amblance ɗin Asibitin, aka saka su su duka, suka Nufi Gidan Ammi. Kafin ƙarfe uku duk 'Yan'uwa da abokan arziƙi sun haɗu, a nan gidan ana ta koke-koke har da masu suma, Ammi dai tun da Ta farka take zaune kamar butum-butumi kwata-kwata ta kasa Aikata komai ko motsi ta kasa yi......*Littafin ZUCIYA. . . Na kuɗi ne Naira ɗari biyu 200, Vip kuma ɗari biyar 500, ga wanda ya shirya biyan nasa 1634835509 Access Bank. Sai a turo shaidar biya ta wannan Lambar 09117440993. Waɗanda basa son hayaniyar group da waɗanda ba 'yan Nigeria ba za su iya siya a Arewabooks, ko ku yi Subscribing a BakandamiyaHikaya.*

🥺😭Na kasa yin dogon Typing...
*ZUCIYA. . .*
*_Q A L B_*



https://wa.me/p/6447799395325349/2349117440993

*ArewaBooks:Kshitu*
*BakandamiyaHikaya:Kshitu*


*ZUCIYA...!!*
(Qalb).

*(24).*
Ƙarfe Biyar aka saka za a yi Jana'izar Dr A. Zuwa wannan lokacin Garin Kano ya ɗauka da Mutuwar Dr ɗin, An yi kukan rashinsa sosai. Huɗu da rabi aka gama shirya shi Aka sa shi cikin Mankara daga nan Aka fara kiran Makusantansu su zo su yi masa Addu'a. Hatta Sarkin Kano Sarki Usman Ahmaad Lamiɗo sai da ya zo Gaban gawar Ahmaad ɗin ya yi masa Addu'a sannan 'Yan'uwa suka fara zuwa suna yin tasu. Tun da Ammi ta zo ta yi sujjada tana karanta addu'o'i kusan mintuna Arba'in ba ta ɗago ba, har An fara ba ta haƙuri ɗago tan da za a yi har ta siƙe. Da ƙyar aka mai da ta wani ɗaki da ke kusa da nata. An yi Jana'izar Ahmaad Abubakar Lamiɗon da Kowa ya fi sani da Dr. A An kai shi makwancinsa, wanda ya samu dubban jama'a na ban mamaki, Haƙiƙa idan ka ga irin mutanen da ya yi Tabbas za ka yi tsananin mamaki har aka rufo shi aka dawo gidan Ammi ba ta san inda kanta yake ba. Imaan ce ke Amsa gaisuwar waɗanda suka dawo daga maƙabarta sai kuma Umma Matar Waziri.....Har Aka yi sadakar Uku Ammi ba ta Um ba ta A'a magana ba ta daina yi kwata-kwata kullum cikin Addu'a take da kuka, ita da Imaan sun rame sosai gwanin ban tausayi ga ba wani makusancinsu, dan Duk dangin Ammin babu wanda ya zo Ita dai Imaan dama ba ta san kowa na Ammin ba shi ya sa ba ta damu ba. Abdul ne kawai ke tare da su, sai kuma Bayi uku da Mai martaba ya aiko musu da su, Kullum nan yake wuni. “Shi ke nan Rayuwa ba Tabbas Yanzu Abdul'aziz ɗana Ahmaad ya mutu??” Abin da Ammi ta faɗa ke nan, dan Sam ta daina magana sai dai ta ɗaga kai ta zuba wa mutum idanuwa. Abdul ya share Hawayen fuskarsa Yana ajiye wayar Ahmaad ɗin. “Ammi ki yi haƙuri dan Allah! Addu'a ya kamata a ci gaba da yi masa. Ni kaina na kasa yarda har yanzu, Mun rasa Ahmaad! Ya ilahi.” Imaan da ke shigowa Parlourn ta zauna kusa da Abdul ɗin tana matse ƙwalla, duk ta yi sukuku ita ma. Abdul kanshi ko kallo ɗaya ka yi masa za ka fahimci tsan-tsar ramar da ya yi, da Alamun damuwa Tattare da shi. Ammi ta fashe da kuka mai raunata zuciya. “Abdul'aziz Ashe ya riga ya ji a jikinsa zai bar duniyar nan shi ya sa bai damu da duk abin da muka yi masa ba, Wallahi da ace na san Ɗana ba zai yi tsawon rai ba Ubangiji Zai amshi rayuwarsa da ban ƙuntata masa ba, Allah ya sani ba a son raina nake fushi da shi ba sai don lafiyarsa, Ashe shi ya sa ya sallami ma'aikatan gidan nan da albashi Shekara guda. Tun bayan rasuwar Iyayena da Mijina ban taɓa jin Mutuwar da ta ruɗa ni ta gigita ni ba irin ta Ahmaad, ina ji a jikina ya riga ya san sai wani ikon na ubangiji ko zai rayu, Amma ina sa ran yanda ya ɗauko hanyar ganin bayan waɗanda suke ta kashe-kashen nan da Azzalumai jininsu ba zai ɓata tafiya a banza ba, Na sani ya riga ya yi wannan Alƙawarin da ZUCIYA...” Kuka ne ya ci ƙarfinta sosai ta kasa ƙarasa maganar, shi ma Abdul ɗin kuka yake yi sosai da Imaan an rasa mai Lallashin wani. Sai da ta zuƙe majina sannan ta ci gaba da Faɗin, “A da ban taɓa tunanin Alƙawarin da muka yi na kawo ƙarshen azzulumai zan tafi haka nan ba, Amma yanzu ko da ace ban aikata komai na kuma yi babban rashi ba zan sare ba akwai Ubangiji yana sane da mu, bai manta mu ba! Zuciya! Zuciya!! Kun ce Zuciyarsa ta buga ya mutu Mahaifinsa ma haka, Ya mutu ta dalilin bugawar Zuciya, Shi ke nan duk wani mai kyakkyawar Zuciya ba za a bar shi da ranshi ba?? Amma Abdul'aziz ka faɗa min Ahmaad ɗina ya chan-chanci a wahalar da rayuwarsa kafin a kashe sa Shekaru fiye da Uku yana ƙuntatacciyar Rayuwa daga ƙarshe ya mutu! Ka faɗa min miye laifinsa dan yana da Kyakkyawar Zuciya nagartacciya ya cancanchi a raba shi da wannan duniyar, Shi kaɗai nake da sai Ƙanwarsa haba wane irin rashin Adalci ne, Ni ma ina jin Zuciya..,” Saurin katse ta Abdul ya yi cikin sarƙewar Murya. “Kar ki kice haka Ammi ki yi Addu'a ni kaina na san Ahmaad ya san Abubuwa da dama amma yana riƙe su a Zuciya, Ammi na sani na ɓata masa rai gab da zai rasu a kan rashin sani, tun bayan da ya fita daga ɗakin na ji komai ya chanza mini, ina ta wasu abubuwa tamkar ba ni ne nake sarrafa kaina ba, Ya ubangiji ka sa Mutuwa ta zama hutu a gare sa ya ɗanɗani ƙuncin rayuwa sosai!” Ajiyar zuciyar kukan da ta sha kawai take yi. Wayar Ahmaad da Abdul ya ɗauko ce ta fara Ringing kamar ya share mai kiran dan ya yi tunanin Dubban mutanen da ke kira a kullum suna masa addu'a ne, sai kuma sunan mai kiran ya ja Hankalinsa. Sai kawai ya sa hannu ya ɗaga ya saka wayar Handsfree. Maimakon Sallama ko wani abu sai dariya Da aka fara ba ƙaƙƙautawa marar daɗin ji da murya mai amon sauti sosai. Abdul ya yi shiru bai ce komai sai da mai dariyar ya tsagaita sannan “Abdul ya ce Wa ke magana??” Sai da aka sake darawa kafin cikin Kausasshiyar aka fara magana “Izuwa yanzu na san cewa kun rufe babin Ɗan tsaurin ku ko, Mun gama da shi, SauraKai muna nan juyowa kanka...Hahhhaha!!!” Kafin ya yi yunƙurin ba da Amsa an datse kiran. Ammi da Imaan da suka gama Sauraron komai suka yi zuru.Ammi ta nisa ta haɗe hannayen biyu alamun roƙo ta ce “Abdul'aziz dan Allah ka fita daga harkarmu, A halin yanzu ba na son na sake yin wani Rashin da zai Tarwatsa komaina, Ina jin Ƙaunarka cikin Zuciyata ban san ya zan yi ba idan har Aka ce ka rasa rayuwarka ba!” Abdul ya saki Wani murmushi mai tsananin ciwo ya ce “Ammi ina farinciki ko da a ce na rasa rayuwata ne, In dai ta dalilinku ne, Alhamdulillah Ubangiji na sane da mu, ban zan taɓa barinku ba In sha Allah sai ranar da na bar Numfashi.” Abdul da kanshi ya shiga Kitchen ya yi girki ya ɗauko magungunan Ammi ya tasa su gaba suka ci su duka sannan ya ce zai fita Asibiti ya dawo....
Kwana biyar ɗin da Nafi ta yi Gidan Hajiya Safeena babu abin da ke mata daɗi komai ya fita daga ranta dan ma Allah ya sa Hajiyar ba ta nan. Yau ma kamar kullum suna zaune A Parlourn Tala. Nafi ta lula duniyar Tunanin Baffanta da kuma Hamma ta sauke ajiyar zuciya lokacin da suka haɗa ido da Tala na ma Hannayenta Kallon ƙurilla wanda take yawan yi mata kwanakin nan. Suna Cikin Kallon TV suka fara jin Ƙarar shigowar motoci, Tala ta ja ta cikin Sauri suka fito Parlourn, Hajjaju ta gani ta fara shigowa sai wasu Manyan Hajiyoyi da Hajiya Safee, Suna ganin Nafi duk suka fara tururuwa wajen Rungumar ta. Hajiya Safee duk ta riga su ta Rungume Nafi tsam a jikinta kamar za ta maida ita cikin cikinta. Bayan sun ci abinci Mutanen Hajiya su ka tafi ɗakinta dan Chan za su kwana, Ita kuma suka koma suka yi shiri suka kwanta ita da Tala. Har ta fara barci Tala ta tashe ta suka zauna ta fara magana A hankali cikin raɗa. “Kin san me su Hajjaju suka zo yi gidan nan?’ Nafi ta girgiza kai da sauri. Tala ta ci gaba da Magana “So take ta siye ki! tana so ki zama tata gobe za su yi shagalinsu daga nan kuma kin zama Mallakinta! Za ta yi yanda ta ga dama

Please Login or Register in order to submit comment