Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan karon tana ɗan jin tausayin Nafin. Ta ajiye kofin ta fara magana, “Kin san me ne a ciki?” Nafi ta girgiza kai da sauri, “Ƙwaya ce me ruɗarwa da saka barci ake ba ki don a ji daɗin amfani da ke cikin sauƙi” Ta tsaya tana kallon ta cikin rashin fahimta ba ta ce komai ba. “Hmm!. gaskiya da alama har yanzu ƙuruciya na ɗawainiya da ke sosai ɗin nan! kin ba ni tausayi gaskiya ba zan so Rayuwarki da ke kanki ki lalace ba, Ki ji ni da kyau; idan har Hajiya ta sake ba ki wani abinci kar ki ci, ki yi yanda kika yi kika san ba ki ci ba, ba tare da ta gano nufinki na ƙin cin abinda ta bakin ba.” Cikin sauri Nafi ta jinjina kanta, sannan Tala ta ci gaba da magana ta ce, “Ki yi ƙoƙari ki jure idan har na bar ɗakin nan ki kwanta ki yi kamar kina barci ko ni da Hajiya mu ka dawo kar ki kuskura ki nuna idonki biyu, duk wani abu da za ki ji ta miki ki daure idan ba haka hmm... Ki bari sai ta fara fita hayyacinta ki fara wani abu me kama da ba kya cikin hayyacinki kina abubuwa kamar kina cikin mawuyacin hali kin ji ko idan kika yi haka za ki kuɓuta daga sharrinta.” Ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Umh na ji” Tana gani Tala ta zubdo Zoɓon da ta shigo da shi a kewaye ta dawo, kusan mintuna biyar ta ce ma Nafi ta yi yanda ta sanya ta. Ta gyara kwanciyarta ta rufe idanuwa ta yi kamar tana barci. Tala ta fita ta bar ta ta koma Parlourn. Inda Hajiya Safee take ta je ta ce “Hajiya ta gama sha za ki yi iya shiga inda take”. Ta saki murmushi tana mata godiya ta sallame ta, Ta koma ɗakinta da ke kusa da na Nafin wanda Ɗaki ɗaya ya raba su, ta shige bedroom ɗinta ta kwanta, tana wasu Saƙe-saƙe cikin ranta game da Nafin. Cikin jin daɗi Hajiya Safee ta shiga ɗakin da Nafin take ta kulle ƙofa ta kashe fitila, duk Nafi na jin ta tayi lamo, Ta tuɓe ta nufo gadon inda Nafi take, Ta fara mata wasu abubuwa da suke barazanar tarwatsa mata kwanya tun tana jurewa har ta fara ɗan motsi sosai, Tun da ta riƙe hannun Hajiya Safee jikinta na kyarma Ba ta sake sanin a wace duniyar take ba....Bubbuga filon da take kwance Tala ke yi a hankali tana kiran sunanta a hankali, da ƙyar ta fara buɗe idanuwanta da suka yi nauyi, Tala ta jijjiga ta, Ta ɗan waro idanuwa a kasalance, tana kallon ta idanuwanta na ƙoƙarin lumshewa, Tala ta watsa mata ruwa masu sanyi, Kawai ta fara numfarfashi tana sakin ajiyar zuciya. “Ke! ki tashi mana” Sai Time ɗin ta ɗan wartsake kaɗan, ta dube ta har lokacin dai mugun barci da kasalar da ke jikinta ba su bar ta ba, Ta sake faɗin “Ai kun ɓata komai kin ji daɗi, kin kuma janyo ma kanki matsala tun da har ta fahimci Kin san da abin da take aikata miki”. Zumbur ta yi ta zauna tana zare idanuwanta a tsorace. “Sai dai wani lokacin ko kina samun damar kuɓuta amma ba yanzu ba, maza ki tashi ki kimtsa safiya ta yi ki ci Abinci”. Ta yi fiƙi-fiƙi da idanuwa tana kallon ta, ta kasa ko motsawa dan kasala take ji sosai. Hakan ya sa Talar Kamo ta ta miƙe, Ganin babu kaya a jikinta ne ya sanya ta Ɗauko mata tawul ta ɗaura, suka Shiga Banɗakin ta nuna mata komai sannan ta ce ta yi Brush ta ajiye mata tooth paste ta fita. Ba ta wani jima ba sosai ba ta fito saboda jiƙa-jiƙa s yi gabaɗaya hankalinta ba ya tare da ita yana chan wani wajen daban ta ma rasa me ke mata daɗi. Haka ta shirya suka Nufi Dinning ɗin. Tun kafin ta ƙaraso Hajiya Safee ke feshe ta da wani Makirin murmushi me tsoratarwa har suka Zauna Tala ta zuba mata abinci, amma sam ta gaza sakewa ta ci sai motsa abincin take yi, komai ma tsoro yake ba ta....
Tukwici me faranta rai Galadima ya bawa Baiwar da ta sanar da shi Zancen su Abdul da Ahmaad. Tana fita ta miƙe cikin jin daɗi ya nufi Turakar Ummi, yana shigowa ta sallami bayinta su duka da waɗanda ke hidima ɓangarenta. Yanda ta ga yana fara'a ta san ba banza ba, Ya fara mata magana ya ce, “Albishir me daɗi...Aikinki ya yi ɗari bisa ɗari ko ma na ce fiye da haka! don Wannan abin wasan ya suɓuce musu” Cikin farin ciki ta miƙe zaune tana murmushi dan ta gama fahimtar inda ya dosa. Sai da ta juya idanuwanta sannan ta ce “Hmm..Kana wasa da Malika ke nan”. Ya zaro idanuwansa ya ce ‘‘Kai! wane ni ai na karaya da al’amarinki ke ɗin gaskiya kin fita zakka fa tabbas!’’ Sun daɗe suna Ƙulle-ƙullen abubuwa tsakaninsu suna murna. Daga ƙarshe ya miƙe ya fita dan yana son samun bayani daga wajen Akarsh likitan Dr. Tana ganin ya fita ta ja tsoki tana hararar ƙofa ta kuma tuntsure da dariya a fili ta ce “Soko kawai”...
Waziri Mahaifin Abdul ya sake tsattsare sa da idanuwa ya fesar da numfashi ya ce, “Ka tabbata babu wata matsala tsakaninka da Ahmaad??” ya jinjina kai ya ce “Eh Abba na tabbata.” Ya sauke ajiyar zuciya ya sake faɗin, “Dan Allah Abdul'aziz kar ka bari wasu su shiga tsakaninku cikin ƙanƙanin lokaci don naga abinda ake son aikatawa ke nan. Tashi ka tafi Allah ya tsare ku.” Da 'Amin' ya amsa ya fice daga Sashen. Haka nan yanzu yake jin ɓacin rai ko sunan Ahmaad aka kira, Shi kanshi bai san dalilin da ya sa yake jin haushinshi ba sosai....
_*#K_shitu🦋.*_
_*Z U C I Y A*_
Paid book two hundred naira 200.
*9201739091*
*Stanbic IBTC Bank.*
*Mohd K*
*Evidence of Payment Via* *09117440993*



_Wattpad@Kshitu_
_BakandamiyaHikaya@Kshitu._

*ZUCIYA...!!*

*(20).*
Shiru-shiru Ammi ta ji Ahmaad har safiya ta yi, wajen Ƙarfe tara, ta yi niyyar share sa amma ta kasa ta aika Imaan ta dubo shi ko yana lafiya. Tana shiga Parlourn Ta gan shi kan kunjera kwance, ta ƙarasa da sauri tana kiran sunansa “Yaya Kana lafiya?” Yana jin ta amma ba zai iya komai ba kansa ya masa nauyi sosai ko magana ba zai iya yi ba. Ta ƙarasa kusa da shi ta ɗan taɓa shi, ta ji jikinsa ya yi mugun zafi sosai, Ta fice da sauri ta koma ta faɗa ma Ammi. Sosai Hankalinta ya tashi, ta kira Abdul ta faɗa masa ya ce yana nan tafe. Duk yana jin su amma ya yi shiru . Shi ma Abdul ya shigo Parlourn yana sallama, haka nan yana ganin Dr. ya ji wani mugun ɓacin rai Ya ƙaraso ya gaishe da Ammi ta amsa cikin damuwa ya tambayi Ammi me ke damun sa ta ce ba ta sani ba, ya matsa kaɗan ya ɗan taɓa jikinsa ya ji zafi sosai rau. Ya koma cikin mota ya ɗauko wata jaka ya dawo, Ya ce “Ammi ina tunanin zazzaɓi ne bari na sa masa ruwa ban zo da kayan awo ba da na auna shi”. Ta jinjina masu kai Abdul ya riƙe hannunsa har ya saka Cannula ko bai yi wani ƙwaƙƙwaran motsi ba. Sai da ruwan ya ƙare ya ɗan ji ƙwarin jiki kaɗan da zufa, Cikin dauriya ya miƙe zaune fuskarsa a haɗe ya cire Cannular ba tare da ya tanka ma kowa ba har Ammin ya shige bedroom ɗinsa ya rufo ƙofa. Cikin ɓacin rai Ammi ta sallame su, suka bar sashen nasa shi ma Abdul ya bar gidan ya koma office ɗinsa. Cikin gaggawa ya shiga ya yi wanka ya sanya Manyan kaya shadda light brawn sai wula kalar aikin shaddar Coffee, ya yi kyau sosai ya ɗauko makullin wata motarsa da waya ya zo Dinnig ya zauna. Kukunsa ya fito yana gaida shi ya amsa fuska a sake Ya zuba masa abinci ya ci sosai, Sai kallonsa Kukun ke yi dan ya yi wata irin muguwar rama ga kuma hasken da ya ƙara sosai, Ya ɗan harare sa, Shi kuma ya sunkuyar da kansa, Ya jawo wayarsa ya ɗan latsa ya dube sa ya ce “Ba ni account numbernka” ya karanto masa ya rubuta daga nan ya lallatsa, Ya ce a taƙaice “Na tura maka kuɗi, Ka amso mini Account Numbers ɗin masu aikin gidan nan duka” Cikin murna ya shiga yi masa godiya da addu'a ya ɗan sunkuyar da kai ya ce “To Yallaɓai na gode albashina ne ko hasahin da aka saba mini??” Ya mike yana 'koƙarin fita ya ce “Idan ka duba za ka gani”. Yana gama faɗin haka ya fice daga Parlourn Kai-tsaye ko Part ɗin Ammi bai kalla ba ya nufi Parking Lot ɗin gidan ya buɗe Wata farar mota ya shiga, ya tada ya ba ta wuta sosai. Gabaɗaya yanzu abin da yake son aikatawa kawai yana so ya gana da Nafeesa kwata-kwata hankalinsa ya gaza kwanciya. Ya ɗauki hanyar rugarsu....
Ammi zaune a Parlournta hannunta riƙe da Ipad da alama video call suke yi irin yanda ta maida hankali a nutse tana Magana cikin girmamawa kaɗai ya isa ya nuna ta ba wa Wayar muhimmanci sosai. Abdurrahim wanda take roƙo ya dan fesar da nufashi daga bisa kujerar da yake ya jujjuya kafin ya ce, “Shi ke nan Amm! Amma fa saboda ke zan yi wannan alfarmar da kuma dear Imaan Anyway ni ma zan shigo Nija nan kusa, zuwa dare zan saka agent ɗinmu na nan Cikin Nigeria ya kawo muku, dama muna ajiye maganin incase of unexpected things. Zan turo miki Account Numbern.” Ta amsa tana ta godiya cikin girmama Lafuzanshi sannan suka katse kiran, Ya turo mata account numbern na Nigeria Access Bank. Take ba ta wani tsaitsaya ba ta tura masa zunzurutun kuɗaɗe Naira Miliyan Biyu da dubu ɗari Takwas da saba'in 27070 sai kuma Cash waɗanda ya turo mata text zata ba wa wanda ya kawo maganin Dubu ɗari Shida da hamsin. Imaan da ke zaune ɗan nesa da ita kaɗan Ta turɓune fuska ta ce “Ammi wai nawa kika tura masa? kuma a haka kike cewa ni in aure shi kam”. “Bai shafe ki ba” ta ba ta amsa tana miƙewa tsaye ta bar parlourn. Ita dai Ammi yanzu ba ta da burin da ya wuce Rayuwr Dr. Ta gyaru komai ya zo ƙarshe ba wata damuwa ai ita a ganin ta Abdurrahim ba shi da wata matsala ko da ace ya so Imaan....
“Nafeeesa!!” Hajiya Safee ta kira sunan Nafi cikin wani salo tana jan sunan tare da Kashe mata ido. Ba ƙaramar razana Nafi ta yi ba, har wani fitsari ta ji tana ji, Cike da fargaba muryarta har tana rawa ta amsa “Na...nnnNaam” Jin yanda muryar Nafin ke rawa ya sa Hajiya Safee sakin wata dariya irin ta Shahararrun 'yan duniya gogaggu. Ita kana Tala sai da ta ɗan dara, Hajiya ta sake faɗin, “Wai me ke damunki ne haka ki saki jikinki mana”. Ta girgiza kai alamun babu komai, Hajiyar ta sake cewa “Okay ci Abincinki”. Ta ɗaga kanta, da dole ta fara tura abincin bakinta. Da gani cin na dole ne take yi, ga Idanuwa da Hajiya Safee ta tsare ta da su, ta turo mata kofin ruwa gabanta, ta ɗauka ta fara sha har tana ƙwarewa. Hajiya ta ce, “Idan kin koshi za ki iya zuwa daki, Tala za ta buyo ki daga baya”. Kamar jira Nafi ke yi jikinta na ɓari ta miƙe ta bar Parlourn ta shige Ɗakin da aka kaita, Ta wuce bedroom ɗin ta kwanta kan gado ta ja Bargo ta rufe har kanta. Ta jima na kwance shiru sai hawaye kawai take yi, Jikinta duk ya yi sanyi gabaɗaya Kewar Baffanta ta ishe ta Tana ta nadamar yarda da Hinde da ta yi, ga shi ta kawo ta inda za a kashe ta, Sam hankalinta ba a kwance yake ba, komai ya fice a ranta. A haka Tala ta shigo ɗakin ta kunna fitila da Ac ta ce “Nafi ki tashi! wai ke ko zafi ba ki ji.” Ta yaye bargon ta zauna tana bin ta da idanuwa, Tala ta sake faɗin, “Taso mu je Yau zan zagaya da ke cikin gidan nan ne” ta fito suka Fice daga Parlourn Hajiya, Tala na gaba Suka fito Harabar Katafaren gidan danƙarere Me tsananin kyau da girma, Nafi ta baza idanuwa tana kallon tsarin gidan kamar ba a duniya ba, Hankalinta ya sake tashi sosai kanta sai juya mata yake gidan ya yi biyun na Hajjaju wajen kyau da Girma Parking Space ɗin gidan kanshi abin kallo ne, Tsarin gidan ya yi sosai, Idan ka ga Ɗakin me gadi kaɗai da masu aiki daga wajen sai ka ce Tabarakallahu saboda haɗuwa, Idan ka kalli Zubin ginin yake ma haka sai ya burge ka sosai saboda haɗuwarsa. Ɓangarori uku ne na ɗaya na biyu sai na ƙarshen da ya ke ɗan ƙaramin wanda Su Nafi suka fito daga cikinsa. Securities sai kai-kawo suke yi riƙe har da bindigu ga me gadi da wasu samari zaune kan benci. A zubure ta kalli Hannunta da Tala ta riƙe sai kuma ta saki ajiyar zuciya Ita ma tala ta ga wani zanen star me kyau a hannun Nafi ta yi shiru ta ƙura wa Zanen ido tana raya abubuwa da dama cikin ranta sai kuma ta basar ta ja ta tana magana “In kin gama kalle-kallen mu je ko”. Ta ja ta suka fara shiga Ɓangaren da ke kusa da nasu, Nafi ta ga Ikon Allah dan babu kowa A ciki tsit amma ya fi na su haɗuwa da tsaruwa sosai dan ba a haɗa su ma. Daga ƙarshe suka nufi bayan Ɓangare na ƙarshe wanda ba su shiga ba inda Wajen shaƙatawa yake, suka nemi waje suka zauna kusa da Sweeming Pool, Nai sai zare ido take tana ji bayanin Talar, amma ko maganar sashen da ba su shiga ba bata yi mata ba. Ta dubi Nafi a tsanake ta ce “Humm! wallahi Nafi baki da wayau sam...Yanzu in ban da abinki ke haka ake rayuwa kin kama kin fara wasu abubuwa ke da kanki za ki ja ma kanki matsala, wa ya ce miki ana ma Hajiya haka, to yanzu ki tabbata duk abin da za ki yi akwai Na'urar da ke naɗa komai da kika yi sai ta gani, dan haka ba za mu dinga magana a chan ba sai dai mu zo nan . Sannan kuma waɗannan 'yan abubuwan da kike yi ban jin daɗinsu, ki saki jiki idan ba haka ba za ki sha wahala sosai gaskiya.” Ba ta iya cewa komai sai gyaɗa kai kawai da take yi dan bakinta ya mutu. Daga nan ita ma Tala ba ta sake cewa komai ba. Suka miƙe suka koma Ainahin inda suka fito, Suka shiga Kitchen tare, ta nuna ma Nafi kujera ta zauna ita kuma ta ci gaba da aikace-aikace Nafin na bin ta da idanuwa..
Ƙarfe Tara na dare Akarsh Likitan Dr A. ya iso Nigeria ya sauka a gidansa shi da wani ƙwararren likita wanda ake ji da shi sosai da sosai a America Doctor Danial suka yi waya da Abdul akan yanda Aikin da za a yi ma Ahmaad zai kasance.....
*_#K_shitu._*







Paid book 200 Vip 500
*9201739091*
Stanbic Ibtc Bank
Shaidar biya 09117440993



*ArewaBooks:Kshitu*
*Wattpad:Kshitu*
*BakandamiyaH:Kshitu*
*OkadaBooks:Kshitu*

*ZUCIYA...!!*

*(21).*
Ya yi yawo sosai cikin rugarsu Nafi amma bai ga bafullatanin da suka yi magana da shi ba. Sai wajen ƙarfe tara da wani abu ya dawo gidan. Ammi na ganin shigowar motarsa ta tashi Imaan dan har ta fara barci Ta ba ta Coffee ta ce ta je ta kai masa, amma kar ta nuna wani ya ba ta ta kawo ta nuna masa ita ce ta haɗa, kuma ta tabbatar ya sha. Ta karɓa jiki a sanyaye haka nan take jin zuciyarta babu daɗi, Ta nufi Parlournsa ta yi sallama har sau Biyu amma shiru bai amsa ba, ta nufi bedroom ɗinsa tana sallama ta shiga ciki. Zaune ta same sa Kan Gado ya dafe kansa da hannayensa duka biyun ya yi shiru. Gabanta na faɗuwa ta ƙarasa gabanshi a ce “Yaya ina wuni” Ya ɗaga mata hannu yana murmushi. Ta miƙa mishi Kofin hannunta na kyarma. Ya ɗan tsare ta da idanuwa ta rikice kamar marar gaskiya sam hankalinta bai kwanta da Coffee ɗin da ta kawo masa ba. Su ka yi shiru su duka tsoro ya hana ta magana jira take yi kawai Ta ji ya tuhume ta amma ta ji shiru da ƙyar ta yi ƙarfin halin faɗin “Yaya ga Coffee nan na haɗa maka ni zan je na kwanta Dan ALLAH ka sha”. Ya miƙa hannu ta ba shi ya karɓa ya ce “Thank you Dear”. Ta yi murmushi ita ma ta ce “Good night” tana ficewa daga ɗakin. Tun da ta fito daga ɗakin take jin babu daɗi a ranta miye dalilin da ya sa Ammi take ta fushi da shi kwana biyu. Kuma ta ce kar ta nuna ba ita ce ta haɗa ba. Tana waɗannan tunane-tunanen ta shiga Parlourn. Gani ta yi Ammi na ta kai-kawo ta yi saurin tamabayarta “Ya karɓa ya sha??” Ɗaga kai ta yi tana faɗin “Umh Ammi do you know something?” Ta girgiza kai Imaan na hawaye ta ce “Wallahi Ammi I really dont know why i'm feeling somehow, like i've done something wrong or...” Katse ta Ammi ta yi da sauri gabanta na faɗuwa ita ma hankakinta ya kasa kwanciya ta ce “Imaan what do you mean i can't understand what you saying go straight to the point” Ta goge hawaye ta ce “Ina gani kamar na aikata wani abu marar kyau wa Yaya, Kawai ina jin faɗuwar gaba hankalina ba a kwance yake ba. Ammi kin ga idanuwan Yaya wallahi na ji tsoro da na gan shi I dont think he's okay i believe that i love him i love him he's my Happiness!!” Ta fashe da kuka jikinta na wata irin rawa zuciyarta na bugawa. Duk yanda Ammi ta so daurewa sai da hawaye suka zubo mata. Ta share su tana ɗan murmushin ƙarfafa kanta, Gefe ɗaya kuma ta fara nadamar abubuwan da ta yi masa kwana biyu da kuma fushin da take yi da shi. Ta ce “Ban san yaushe kika zama raguwa irin haka ba, Yayanki yana lafiya babu abin da zai same shi, in sha Allah. don't think about bad things, oya go and sleep don't forget to pray nd Off the light”. Ammi na gama faɗar haka ta yi saurin Nufar bedroom ɗinta ta bar Imaan ɗin nan. Ji take yi kamar ta koma ta dubo sa amma ta daure ta koma ɗakinta ta kwanta tana ta kukan da ba ta san dalilinsa ba...Imaan na fita ya ajiye Cup ɗin ya ɗauko DIARY ɗinsa ya daɗe yana rubutu sosai kafin ya rufe ya ajiye. Ya shiga duba saƙonnin da aka turo Ya tura wa duk ma'aikatan Companies ɗinshi salary da ƙarin kuɗaɗe masu tsoka, sannan ya suba Account details ɗin da Kuku ya turo masa suma duk ya tura musu nasu. Sai wajen sha biyun dare Ya kwanta, har barci ya fara ƙoƙarin ɗaukar sa ya tuna da Coffee ɗin da ta kawo masa ya tashi duk da ba zafi ya ɗaga kofin ya shanye. A matsayinsa na likita ɗanɗanon Coffee ɗin da ya ji, ya san an sarrafa da wani abu na daban ba mai kyau ba, Ya ajiye Cup ɗin, ya gyara kwanciya. Cikin dare ya dinga jin raɗaɗi da Wani irin dunƙulallen abu, a zuciyarsa ga kuma zafin da jikinsa ya ɗauka Zuciyarsa ta shiga wani irin bugu, Ya rasa wata irin azaba yake ji Har wani huci me mugun zafi yake saki Zuciyarsa kamar ta tsage tsabar irin Tururin azabar da yake ji gabaɗaya jikinsa ya ɗau wata irin rawa. Tun yana iya tuna wasu abubuwa ya lumshe idanuwa har ya kasa jin sa da ganinsa suka ɗauke..
_Daren wannan Ranar mutane da yawa masu alaƙa da Doctor Ahmaad Abubakar Yusuf Lamiɗo ba su rintsa ba..._
Cikin wannan daren Galadima ya ɗauki waya ya kira Doctor Akarsh. Sai dai a mamakinsa Bugu biyu ya ɗaga da alamu ma ba barci yake ba, Sun jima sosai suna tattaunawa Kafin daga Ƙarshe suka yi sallama.
Sam Ammi ta kasa rintsawa Barci ya ƙauracewa idanuwanta. sai kai-kawo take a ɗakinta daga Ƙarshe ta shige Toilet ta yi Alwalla ta fito ta fara jera salloli tana ta addu'o'i.
Abdul ma sam ya kasa rintsawa da ya rufe ido sai ya ga Fuskar Ahmaad yana masa murmushi lokacin da ya yi masa wani hoto.
Tun da Nafi ta ji Hajiya ta ce mata ta kwan ɗakin Tala hankalinta bai kwanta ba har are ya raba barci bai ɗauke ta ba. Jin ta take cikin wani irin da ba za ta iya fasalta shi ba, Zuciyarta ba daɗi......
_*©️ K _ S H I T U . 🦋*_

*LITTAFIN KUƊI NE..*
Ga wanda ya shirya biyan na kuɗin littafin Z U C I Y A Naira ɗari biyu 200 VIP 500.

*9201739091 STANBIC BANK, Shedar biya 09117440993.*















*KS..*
*•HOME OF NATURAL HERBS🔥🌸✨*
_Ina kuke 'Yan'uwa mata da maza manya da ƙanana, matan aure Zawarawa 'Yan'mata! ku matso kusa Na ce Sanyi fa ya zo😫 Akwai ingantaccen Maganin Sanyi/Infection sahihi me aiki da izinin Ubangiji duk wanda ya yi amfani da maganinmu ya sani Ana samun waraka da yardar ubangiji ga arha ba mu tsawwala ba kowa zai iya amfani da shi. Akwai na Ɗari *800,* sai kuma na *1500* da na *3000* In sha Allahu ba za ku yi nadamar Amfani da Maganinmu ba, muna bada sari da siyan ɗai-ɗaya. Muna aikawa ko ina da izinin Allah_ _*DA NAGARTA MUKE ADO!🤗💯*_
*9201739091*
*STANBIC IBTC BANK*

_Domin neman ƙarin bayani,_
*09117440993 WhatsApp*
*09060584800 Call.*



https://wa.me/p/6447799395325349/2349117440993
*ArewaBooks@Kshitu.*
https://www.arewabooks.com/u/kshitu


*ZUCIYA...!!*

•💔
*(22).*
Tun da safe wajen ƙarfe Takwas Abdul da doctor Irfaan suka zo gidan, Parlourn Ammi suka karya, sannan Abdul ɗin ya miƙe jiki ba ƙwari ya ce bari ya je Ɓangaren Ahmaad ɗin ya gano shi, dan Ammi ta ce ko sallar asuba ba ta ga fitarshi ya je ba. Ya yi sallama a Parlourn ya ji shiru, hakan ya sa ya kusa kai cikin bedroom ɗin na shi. Kwance ya hango shi kan gado, ya kunna fitila haske ya gwauraye ɗakin. Yanda ya gan shi kwance kan gadon kamar gawa ba ƙaramin bugu zuciyarsa ta yi ba, lokaci ɗaya kuma ya ji ƙafafuwansa na gagarar ɗaukarsa. ya ƙarasa gaban gadon da sauri yana kallon sa. Ba shi da maraba da gawa, idanuwansa ne kawai a buɗe yana kalle-kalle amma ko motsa kansa ba ya iya yi. Abdul ya kira sunansa A hankali “Ahmaad!” Bai amsa ba sai lumshe idanuwansa ya yi waɗanda suka rine suka yi wani irin ja sosai. Hankalin Abdul ya kai ƙololuwar tashi zuciyarsa na wani irin bugu ya miƙe jikinsa ba ƙwari yana jin fargaba da wane ido zai dubi Ammi. Ya durƙushe nan ya kasa tafiya gabaɗaya jikinsa ya gama yin sanyi. Jin da Ammi ta yi shirun ya yi yawa bai dawo ba ya ƙara sanyaya jikinta, suka nufi Ɓangarenshi ita da imaan da Dr. Irfaan, Tun kafin su ƙarasa take jin faɗuwar gaba sosai da wani irin yanayi me wuyar fasaltuwa. Ammi ta yi sallama a Parlournsa, jin shiru ya sa ta tura ƙofar bedroom ɗin sa a hankali. Abin da idanuwanta suka gano mata ne ya haifar mata da wata irin bugawar zuciya lokaci ɗaya kuma kanta ya sara, ta lumshe idanuwanta ta sake buɗewa. Shesshekar Abdul kawai ke ta shi cikin ɗakin. Ammi ta zube nan ƙasa tana fitar da numfashi da ƙyar, tuni hawaye suka fara zubowa daga idanuwanta, ta fara raira kuka tana karanto addu'o'i gabaɗaya ranta a dagule yake ba ma za ta iya misalta irin mummunan yanayin da take ciki ba. Ta ja jiki cikin sarewa da Al'amarin Ahmaad ɗin ta isa bakin gadon da yake. Jikinta na wata irin rawa ta kamo hannayenshi ta riƙe, tana son karanto addu'o'i amma zuciyarta

Please Login or Register in order to submit comment