Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shafe-shafe kan dress mirror ɗin gwanin ban sha'awa.Ta kalli kanta ta cikin madubin ta yi saurin zaro idanuwa waje ganin wasu Fitsararrun Sleeping dress a jikinta gabaɗaya babu wani abu da ya ɓuya a zubin halittarta, ta kalli ƙafafunta da suke a waje dan ɗan wandon daga gwiwa kawai ya tsaya.Jin motsin da ta yi daga Waje ya sa ta saurin komawa ta kwanta ta lulluɓe da bargo, ta yi lamo kamar tana barci.Hajiya Safeena ta shigo cikin ɗakin ita da Hinde tana mata magana “Gaskiya hinde na ji daɗi sosai daren jiya Maganin nan ya yi aiki sosai, ga ragowar na barcin nan Idan ta tashi zan sake ba ta, Ki riƙe waɗannan kuɗin ita hajjaju zan mata sallamarta, za mu yi waya da ita dan yarinyar nan za ta ɗan yi min ko sati biyu haka zan sake wayar da ita ni so nake ma Hajjaju ta bar mini ita, ai Rukky Kano zan tura ta kar ta ɓata min jindaɗina,Alhaji ma kin ga Saturday ya tafi kuma zai daɗe bai dawo ba..” Nafi na jin su ta yi tsit har suka gama surutansu suka fice. Tana ganin sun fita ta yi zumbur ta miƙe da sauri a ɗan tsorace ta fito. daidai lokacin Hajiya Safeena ta shigo Parlourn da zai sada ta da Bedroom ɗin da Nafin ke ciki, Har karo suka kusa yi Nafi ta ja baya tana Hammar ƙarya Hajiya Safeena ta washe haƙora tana murmushi ta dubi Nafin ta ce “Nafeesa kin tashi ke nan, ki shiga toilet akwai brush da mark-clean ki kimtsa ki fito mu je mu yi breakfast” Ta ɗaga kai kawai ta shige cikin Toilet ɗin, cikin sauri ta yi brush ɗin ta fito saboda yunwar da ke ƙwaƙularta. Hajiya ta miƙe tana gaba Nafi na bin ta a baya har suka fito daga Ɗakin suka Zuwa Haɗaɗɗen Parlour, Nafi ta ruɗe ta sake baki sai kallon Tsarin Parlourn take kwata-kwata ma ba za a haɗa shi da na gidan Hajajju ba, Wannan ya fi kyau nesa ba kusa ba ga wani ni'imtaccen sanyi da ƙamshi ta lumshe ido. Sai kuma ta yi saurin buɗewa saboda tuntuɓen da ta yi da Kujerar da ke dinnig area ɗin, Hajiya Safee ta juyo ta kalle ta, tana ta mata sannu ta ja mata kujerar da ke dab da tata. Suka zauna Tala ta shigo da sauri jin Motsi a dinning ta ƙaraso baki hat kunne tana gaida Hajiya Safee, ta dubi Nafi ta ce “Lale sannu baƙuwa ya aka kwana, bari na zuba muku abinci kar na ishe ku” ɗan murmushi kawai Nafi ta yi ba ta ce komai ba. Tala ta matso ta buɗe Kulolin da ke jere bisa teburin ta fara zuba musu Farfesun Ƙafar sa da Soyayyar doya marar ƙyau, sai ƙamshi ke tashi, Tuni yawun Nafi ya tsinke kamar ta duma hannu ta fara kai ma bakinta ta ke ji. Allah ya yi ta da masifaffen kwaɗayin Abinci. Ta shaƙe mata plate ta turo mata shi gabanta sannan ta zuba mata Kunun gyaɗa, Ita ma Hajiya Safee ta zuba mata sannan ta bar Dinning ɗin bisa Umurnin Hajiyar.Jikin Nafi har kyarma yake yi ta duma hannu duk da tururin da Naman yake yi amma ta saka hannu ko ɗar bata yi ba duk da ta ji zafi burinta kawai ta kai ma cikinta. Ganin yanda ta zage tana cin Abincim ne ya sanya Hajiya Safee yin murmushin mugunta, sai kallon ta take yi, ita kuwa Nafi ta maida hankali duk yawan Abincin ta cinye tas. Sannan Hajiya ta ce ta wuce Ɗakin da ta kwana ga shi chan Tala tana ciki, ta miƙe kamar za ta yi amai saboda cin da ta yi....
Washe gari Dr ya shirya yana tunanin Samun kiran Abdul amma shiru, Ya shirya ya ɗauki wayarsa ya nufi Sashen Ammi. Tun da ya shiga Gabansa ke faɗuwa Saboda Abdul da Irfaan da Abdul da ya gani cikin Parlourn sai Ammi suna tattaunawa. Ya shiga fuskarsa a haɗe Ya gaida Ammi ta amsa ba Yabo ba Fallasa, Yana shirin Yi ma Abdul magana ya ga ya haɗe fuska ya ɗauke kansa. Ammi ta dube sa ta ce “Za ka iya tafiya” Ya miƙe ba tare da ya ce komai ba Ya fice ransa a ɓace, Ya koma ɗakinsa ya duƙufa yana amfani da system ɗinsa ko breakfast be ba. Ya duƙufa sosai yana aiki tuƙuru kafin ya ɗauko wani Ƙaton Diarynsa ya fara rubutu ya daɗe sosai yana rubutun dan duk Acn da ke ɗakin zaufa na ɗan ɗiga daga goshinsa. Yana gamawa Ya miƙe ya fito hannunsa riƙe da mukullin mota ya fito Parking lot ɗin gidan daidai lokacin Su ma Suka fito Irfaan ya kalle sa ya yi masa murmushi Abdul ya kalle sa ya ɗauke kansa gefe, Shi ma Dr ya ɗauke nasa kan, ya buɗe motarsa Ya tada ta da mugun gudu ɓe gadi ya buɗe masa ya bar unguwar. Tun da ya ɗauki Hanyar rugar Yake jin zuciyarsa babu daɗi, Tafiyar Awanni huɗu ya yi, saboda gudun da yake shararawa, Ya fara shigowa cikin Rugar saboda titin da yake marar kyau sosai me kwazazzaɓe, ga kuma Rugogin da ya fara wucewa. Wuri ya samu gefe ɗaya ya Parker Motarsa. Tafiya ya fara a hankali cikin nutsuwar da ta zame masa jiki, Ya fara shiga cikin Rugar yana wuce Lambuna, Wani lambu me cike da ni'ima da sanyi ya zo wucewa ya ga wani tsohon Bafullatani Yarinya na zuƙunne gabansa shi kuma ya kafa ƙwaryar Nono a baki yana sha, Ya sauke ajiyar Zuciya yana gode ma Allah, Ya ƙarasa inda suke yana musu Sallama. Shiru suka masa ba su amsa shi sai kallon shi da suke yi kamar za su cinye shi, Ya sake maimaita sallamar Yana matso su, Bafullatanin ya amsa masa yana dire ma yarinyar ƙwaryarta. Ko kuɗi ba ta tsaya karɓa ba ta ɗauki ƙwaryar jikinta na kyarma sai kallon tsoro take wa Dr Ta kwasa da wani irin gudu sai da ta fara gudun ta buɗe murya tana ihu faɗin 'Aljani' shi dariya ma ta ba shi ya ɗan murmusa. Ya kalli tsoho da ke shirin barin wajen ya ce “Baba Dan Allah ɗan tsaya tambaya nake” Ya tsaya yana ƙare masa kallo sai ya ce,“Mutum ko aljani?” Ya sakemurmusawa, Hakan ya sa mutumin Matsawa, Dr. ya ce “Mutum!” Sai ya ɗan numfasa ya ce “Ina sauraronka yi tambayarka”. Dr ya ce “Baba ina neman Nafeesa 'yar gidan Baffa Iro”. Mutumin ya yi bala'in tsorata ya ɗan zaro idanuwa ya ce “Nann...Nafi kake nufi??” Ya ɗaga masa kai alamar E Mutumin ya ce “Amma miye haɗinka da ita kai din nan??” Ya Dan yi shiru kafin ya ce “Ina siyan Fura gun ta ne” “To maganar gaskiya ni ba zan iya faɗa maka komai game da ita ba” ‘’Dan me?’‘ ya tambaye sa cike da ƙuluwa, Ya ba shi amsa a hankali “Wataƙila tana saurarenmu yanzu haka ma, ni zan tafi” Ya Kalle sa cikin rashin fahimta ya ce “Ban gane ba” Mutumin ya yi shiru sai kuma ya ce “Ai ba mutum ba ce ita ɗin Mayya ce!” “MAYYA!!” ya faɗa zuciyarsa ta yi wani irin bugu, kafin ya samu zarafin magana Mutumin ya fara tafiya dan har ya fara kutsawa cikin daji, Ya bishi cikin sassarfa yana haɗa shi da girman Allah ya tsaya yana faɗin, “Ɗan Allah ɗan saurayi ka bar ni bana son ka ja mini fitina.” Ya ce “Baba dan Allah ka taimake ni, in sha Allahu babu abin da zai same ka, so na ke ka sada ni da wani makusancinta ko ka sanar da ni dangane da ita” Mutumin ya yi shiru sannan ya ce “Ba zan iya faɗa maka komai ba yanzu, Ka dawo gobe da safe nan Amma kai jinin Sarauta ne ko?” Ya yi Mamaki sosai Amma ya maze ya ce amsa masa, Sai kawai mutumin ya yi murmushi yai tafiyarsa. Dr Ya koma inda motarsa take jiki a sanyaye Yana ta tunani barkatai.....
“Waziri Cewa na yi ina son ganawa da Abdul'aziz!” Wani irin Kalllo Wazirin ya yiwa Gimbiyar Ya girgiza kansa ya ce “Kamar ya??” Ta ja masa tsoki wannan Karon rai ɓace ta ce “So nake ka kira shi yanzu” Ya yi mata kallon banza ya ce “A Matsayinki nawa??” A fusace ta nuna kanta da yatsa ta ce “Ni kake faɗawa haka Yusuf?” Be ba ta amsa ba ya miƙe ya fice daga ɗakin.....Gimbiya Zubaida Ɗiyar sarki me ci A yanzu ta miƙe ranta a ɓace ta fito daga Ɓangarenta ita ma, Ta fito, tun da ta nufo sashen Uwar Gida Masu hidima a bayi suke ta gaishe ta, Amma babu wanda ta kula, A bakin ƙofar shiga ma babu wanda ya yi mata iyaka ko ƙoƙarin yi mata iso ta shige ciki. Uwar gida na kishingiɗe Ba yi guda biyu suna mata fita da tausa sai murmushi take yi, Gimbiya Zubaida Ta shigo ɗakin fakam-fakam. Babu Sallama bare neman izini ta Iso Gaban uwar gida tana huci. Ganin a yanda ta shigo ne ya sanya Uwar gida sallamar dukan masu mata fidima ya rage da ita sai Gimbiyar. Ta kalle ta tana jawo ta jikinta ta ce “Wa ya taɓa min auta?” Ta ɓata fuska sosai cikin tsananin fushi ta ce, “Mammy Waziri ni zai..” Ta girgiza kai ta ce “Ya isa haba Auta Mi ya sa ba ki jin magana ne wai, taurin kanki ne ya janyo miki, ba sai da na faɗa miki kar ki saka kanki cikin Wannan wasan ba, Kin ƙi barina da su bare ki ga yanda ake buga ainahin wasan kin tsaya shirme, Yanzu ki haƙuri Ni zan ɗauki Tsattsauran mataki a kan al'amarin tashi ki je.” “Amma Mammy..” Ta girgiza kanta “Na ce ki bar komai a wajena tashi” Ta miƙe tana zumɓura baki cike da rashin tarbiyya ta nufi ƙofar fita. Sunfar da ke Laɓe ta bayan ɗakin ta yi gaggawar barin Inda take laɓen ta Nufi Ɓangaren Galadima kamar za ta kifa dan sauri.....
*📕K _ S H I T U*
*ZUCIYA. . .*
```Qalb```
PAID BOOK 200 VIP 500.

In sha Allahu Zan ci gaba da posting a kai- a kai ba ɓata lokaci. Idan kina jin daɗin littafin ko kana jin daɗi ka yi mini Addu'a.

Littafin kuɗi ne Naira ɗari biyu, Wanda ya shirya biyan kuɗinsa sai ya turo ta wannan Account ɗin *9117440993* Palmpay Bank, Khadija Muhammad Shitu.

```Kshitu@Arewabooks
09117440993```

*ZUCIYA...!!*
(Qalb).

*(18).*
Tuƙi yake amma sam tunaninsa na ga Nafi Kalamar ‘Mayya’ ta tsaya a ransa. Ƙarar wayarsa ce ta katse masa tunanin da yake, ya kalli mai kiran nasa ya ɗauke kai yana jan guntun tsaki. Ya ci gaba da tafiya har kiran ya tsinke bai ɗaga ba. Lokacin da ya shigo cikin Gari har an gama sallar la'asar, Ya yi Parking ɗin motarsa gefen titi ya sadda Kansa yana tunanin inda zai nufa. Ya tada motar ya ɗauki hanya, yana tafiya yana murmushi shi ɗaya, kawai haka nan yake jin faɗuwar gaba. Ya iso bakin wani ƙaton gida me dogayen katangu da girma sosai, masu tsaron ƙofar suka duba ganin Dr. ne ya sa aka buɗe masa ya shiga. Tun da ya shigo yake jin zuciyarsa tas tamkar babu abinda ke damunsa. Mutane maban-banta sukai ta gaishe da shi da yara yana amsawa kamilalliyar fuskarsa bayyane da murmushi me kyau. Ɓangaren da ya fi buƙatar zuwa ya yi tattaki, Ya ƙwanƙwasa ma tsohon ƙofa. Daga ciki tsohon na zaune ya ce “A buɗe take shigo” Ya shiga yana faɗin “Abokina na nan?” Tsohon ya harare shi ba tare da ya yi magana ba ya aje chazbahar da ke hannunsa ya ce, Amadu matso kusa da ni. Ahmad ya cire takalmansa ya matsa jikin taohon ya zauna cikin ladabi ya ce “Baba ina wuni, na same ku lafiya?” Ya shafa kansa yana faɗin “Lafiya ƙalau Alhamdulillahi, Kana lafiya?” ya murmusa be ce komai ba. Baban ya ce “Amadu ka ganka kuwa, ka yi haske sosai, amma ka faɗa sosai, anya lafiyarka lau??” Ya yi dariya marar sauti yana danne abin da je taso masa ya ba shi amsa cike da shaƙiyanci da son basar da zancen, “Sai dai in rikicin tsufa lafiya nake” Tsohon yai shiru kawai yana kallon shi da jin ƙaunarsa na ratsa shi ya sake faɗin “Ka ci abinci?”Ya ɗan ɓata fuska ya ce “No” Ya jawo Cooler da ke gefe ɗaya ya ajiye gabansu da ruwan wanke hannu ya ce Bismillah. Samun kanshi ya yi da son cin abincin ya wanke hannu da Baba ya buɗe Cooler Tuwan Shinkafa ne miyar kuka sai Nama yanka uku, amma abincin si ƙamshi me daɗi yake, Ya yi bismillah ya fara ci, ya ji daɗin abincin sosai amma bai wani ci da yawa ba ya tsame hannunsa ya ce ya ƙoshi. Baba ma ya cire hannunsa suka wanke tare. Ya ba shi ruwa ya sha ya ji sa daidai, dama har da yunwa ke cinsa. Ya yi Sallah ya daɗe yana addu'o'i da istigfari har barci ya ɗauke sa cikin barcin yake ta yi ma Baba maganganu da fira kala-kala, Duk jikin Baban ya yi sa yi yana buƙatar ƙarin bayani kan maganganun Ahmaad ɗin amma yana son ya bar sa ya ɗan huta tukuna....Sai da aka fara kiraye-kirayen sallamar Magrib kafin Baba ya soma tashinsa. A hankali ya fara buɗe idanuwansa, ya sauke numfashi ya miƙe zauna yana karanta addu'a yaɗan yi miƙa ya kalli Baba da yay tagumi yana kallonsa ya ce “Wai har lokaci ya ja haka ke nan, Bari na tsay na yi sallah sannan na wuce” Tare suka yi Alwala suka jera suka nufi Masallaci, suka dawo, Ya sake shan shayi sannan suka yi bankwana ya baro Gidan cike da nishaɗi. Maimakon ya yi gida sai ga nufi Masarauta ya ɗauki Hanyar ɓangaren Hajiya, Aka masa iso ya shiga, Tun kafin ya zauna take ta fara'a ta sallami Baiwar dake mata hidima shi kuma ya ƙaraso inda take ya zauna suka gaisa ta tambaye sa jikinsa saboda ganin da ta yi duka yaushe ya ɗan samu sauƙi Gabaɗaya ta ga ya yi wata muguwar rama ya yi haske sosai ta zuba masa idauwa ta ce “Wai meke damunka ne?” Ya girgiza mata kai alamun babu komai ta ce “Likita gabaɗaya ka chanza rayuwarka daga rayuwar farinciki zuwa rayuwar ƙunci me cece matsalarka, dan Allah, ko so kake ka farantawa maƙiya ne, Wai ban faɗa maka ba ka riƙe Allah ka kasance me yawan ibada da addu'o'i in sha Allahu za ka cin ma burikanka a rayuwa. Kar ka kasancewa me yawan Nuna rauninka a ko da yaushe, Tun da mahaifinka ya rasu har zuwa yau ciwon da ke zuciyata bai warke ba amma ban taɓa nuna Raunina ba a matsayina ma Macce sai kai haba kar ka ba jinin Lamiɗo kunya, Shekaru Huɗu ke nan amma har yau ban karaya ba kai ne fatana Ahmaad ina sa ran za ka kawo ƙarshen Azzalumai amm...” Ya lumshe idanuwansa a hankali jin ta yi shiru tana kallon sa ya buɗe baki da ƙyar ya fara magana, “Hajiya wannan shi ne Burina a rayuwa kuma mafarkin zuciyata, ban taɓa kwanciya ba tare da tunanin Abbi ba,sai dai Ƙaddara ba ta ba ni dama ba, Hajiya kwanakin da suka rage mini ba su da yawa Ina fata ace na samu salama! Akwai hisabi”. Ta yi shiru kawai amma kalamansa sun daki zuciyarta sosai Ya miƙe ya fice zuwa ɓangarensa. Ko mintuna goma bai yi da zama ba me martaba ya turo wani dogari ya ce a kira sa yana ɓanagaren Sarauniya ya miƙe yana jan ƙaramin tsoki. Ya nufi ɓanagaren ransa a ɓace Gimbiya Zubaida da ta ji Yarima na tafe ta yi saurin faɗawa ɗakinta, ta tsaya gaban madubi tana ƙare wa kanta kallo ta gyara jikinta ta fesa turaruka sannan ta fito, ta zauna ƙasana Carpet Sarki na bisa kujera. Yanda ya saba sallama A hankali haka yay ya shigo cikin ɗakin ya risina ya gaishe sa Sarki ya amsa yana sakin fuskarsa, Zubaida ta gaishe shi, ya amsa fuska a haɗe, Ya zauna bisa kujera shi ma, Bilkisu wacce ta kasance yayar Zubaida ta shigo cike da yauƙi da yanga ta yi kyau sosai ta ajiye Fruits tana gaishe da Dr. Lafiya kawai ya ce ko kallon ta bai yi ba Sarki ya kore su, Ya gyara zama ya fara yi ma Dr. magana “Ahmaad ya jikinka?” ya ba shi Amsa da “Alhamdulillah” ya sake faɗin “Ka tuna maganar da mu ka yi, Atleast ya kamata a ce ka ajiye iyali yanzu, amma na ji ka shiru, tun tuni nake ta sauraron ka” Ya ɗan yi shiru kafin ya ce “A yi haƙuri komai ma ya kusa zuwa ƙarshe in sha Allah” ya yi murmushi ya sanya mashi albarka sannan ya sallame shi, Ya koma Ɓangarensa ko zama bai yi ba wayarsa ta sra ringing, Sunan da ya gani ne ya sa gabansa faɗuwa Ya daure ya zauna tare da amsa kira, ya kara wayar a kunne. Wata irin dariya ake yi me cike da zallar ƙeta, da ka ji dariyar ka san ta kauce hanya irin dariyar rashin imani ce ake yi. Me dariyar ya ɗan tsagaita ya ce Dr “Ahmaad Abubakar Yusuf Lamiɗo! Congratulations.” Sai kuma aka sake fashewa da dariyar bai ce komai ba kirab ya katse, ya dafe kanshi yana jin wani irin tuƙuƙun ɓacin rai da baƙin ciki haɗe da Tsantsar damuwa. Yana cikin tunane-tunane wayar ta sake ƙara Sai da aka yi masa two miscalls sannan ya buɗe idanuwa a hankali ya kalli me kiran ganin sunan Ammi ne ya sa shi saurin ɗagawa ya kara a kunne be ce komi ba. Ta rufe ido ba ji ba gani tana zazzaga masa faɗa sosai, Ya yi shiru bai ce komai ba zuciyarsa har wani tururin ɓacin rai take yi saboda fushi da damuwa Cikin mintuna goma ta ce tana son ganinsa ko cewarsa ba ta jira ji ba ta kashe wayar. Ya dafe kansa yana runtse idanuwa da tunanin ya zai yi da rayuwarsa, Ya miƙe cikin rashin kuzari har wani jiri yake gani ya ɗauki mukullin mota ya fito, Masu tuƙa shi ya ba Key ɗin ya faɗa musu inda za su kai shi, ya shiga motar sannan motoci biyu ma suka saka motar da yake ciki tsakiya, suka ɗauki hanyar Gidan Ammi......
*©®K_shitu🦋*
09117440993.


https://whatsapp.com/channel/0029VaErT9RCsU9JpePsjA0Y

Khadija Muhammad Shitu.
09117440993.

*ZUCIYA...!!*

*(19).*
Ya yi kusan mintuna goma cikin motar bai fito ba, Kansa ne ke masa wani irin azababben ciwo, Ƙofar ma a buɗe take amma ba shi da Niyyar fitowa, Da ƙyar ya zuro ƙafafuwansa waje yana dafa motar, Ya fara tafiya yana jin jiri na ƙoƙarin kada shi, Ya ƙwanƙwasa ƙofar Parlourn, Imaan ta leƙa ta gan shi, cikin sauri ta buɗe tana kallon shi za ta fara surutu ta ga Ya dafa ta dan yana shirin faɗuwa. Ta riƙe hannunshi tana jera mashi tambayoyi, “Yaya me ke damunka, ko jikin ne ka yi tafiya a hankali??” Ammi na kallon su har Imaan ta taimaka masa ya zauna kan kujera. Ganin yanda idanuwansa suka yi ja sosai ya tsorata su, Imaan ta ci gaba da tambayar sa “Ka yi magana Please yaya what's wrong with you?” Ya yi mata murmushi kawai. Ya kalli ammi cikin daddaɗar muryarsa ya gaishe ta, ta kalle shi tana sake haɗe fuska ta ce “Lafiya! So nake ka kira Abdulrahim ka ba shi haƙuri ya amince Zai turo mana da maganinka”. Ya ɗan waro idanuwansa sannan ya lumshe su, Jikinsa sai wata irin Karkarwa yake ya zamo daga kan kujerar ya matsa gabanta, Cikin nutsattsiyar muryarsa wacce take ƙunshe da tsananin Tashin hankali da damuwa ya kamo hannayenta cikin dakiya yana magana “Ammi do Allah kar ka saka ni aiwatar da abu da zai yi silar barin duniyar nan, I can't! He's our enemy Please try to understand what i mean!!” Yanda ya ƙarashe maganar muryarsa na rawa yanayin hausarsa kuma da ta jagule saboda Tashin hankali ne ya sa jikin Ammi yin sanyi Imaan ma har ta fara hawaye. Cikin dakiya ammi ta sake faɗin “Umurni ne nake ba ka ba shawara ba!” Ya saisaita muryarsa Ya sake cewa “Please Ammi, ki rabu da shi.. nd he's Very dangerous more than..” ta katse shi cikin fushi “Ya isa tashi ka fita!” Irin tsawar da ta yi masa tana nuna masa ƙofa har cikin ƙwa-ƙwalwarsa, ya kalle ta irin kallon mamakin nan, Ya miƙe da ƙyar ya fice, bai kula kowa ba ya shige Parlournsa, kawai ya zube bisa kujera. Ya dafe kansa jikinsa sai wata irin karkarwa yake yi, ya abubuwa suke neman chaɓe masa ne haka gabaɗaya komai ya fita daga ransa abinda Ammi ke ƙoƙarin tursasasa shi ya aikata ba ta san yana iya zama ajalinsa ba, da a ce shi Ahmaad Abubakar Yusuf Lamiɗo ya kira Abdulrahim gwara a ce ya rasa rayuwarsa ya furzar da huci me zafi cikin tsananin baƙin ciki yana lumshe idanuwansa, gabaɗaya ba ya jin daɗin komai ya rasa me ke damunsa wani irin zafi yake jin Zuciyarsa na masa. Shi kam ya gama sarewa ya san ba shi da sa'a kwata-kwata a rayuwa, Amma da zarar ya tuna da cewa ba zai wani daɗe ba yana ƙunsar baƙin cikin duniya ba sai ya ɗan murmusa. Ya daɗe sosai a nan ga yunwa da yake ji ga kuma jikinsa da ya ɗau zafi sosai....
Tala me aikin hajiya Safee ta kalli Nafi a karo na biyu ta sake kecewa da wata dariyar ƙeta kamar za ta shiɗe tana riƙe ciki, Ta faɗa kan gadon gudun kar ta faɗi, sai da ta yi me isarta sannan ta yi shiru tana matse ƙwalla, Nafi ta yi zuru tana kallonta hawaye duk sun bushe a kan fuskarta. “ 'Yan'mata adon gari! Lallai Nafi kike ko? Yo idan kin san ba za ki iya wannan harkar ba tun farko uban me ya jawo ki cikin ƙungiyar, ni kin ba ni mamaki ma ina ganinki yarinya ɗanya shakaf amma ki ce rayuwar da kika zaɓa ke nan Chaɓ wallahi in dai Hajiya ce sai ta more ki son ranta kafin ki samu sassauci, in kin dace ta ɗan sa an ɗan koyar da ke ilimi to alhamdulillah amma babu abin da za ki samu sai wasu kuɗaɗen banza amma darjarki za ta ragu kuma kin ɗauko hanyar kashe rayuwarki ne bakiɗaya, ni dai iyakacina da ke kallo.” Nafi ta ruɗe sosai Tana magana saboda tsananin tsoro har fullanci take mata. “Ka taimake ni, hanɗi jam`im wayyo Baffana”. Ta sake sheƙewa da dariya “Hahhhaha! Ai idan taimako kike buƙata tun farko ke za ki taimaki kanki da kanki, matsalata da Ƙauyawanmu ke nan ba sa kishin kansu wasu lokutan kwaɗayinmu na jayo mana masifa mu kasa fahimta tun farko sai lokaci ya ƙure mun ga bala'in duniya.” Cikin harshen fulatanci Nafi ke faɗin Dan Allah ta kai ta gun Baffanta. Tala ta yi saurin sanya yatsanta bisa baki tana faɗin Ssh! jin kamar motsi a Parlour. Ta yi shiru tana sauke numfashi. Gabaɗaya wani irin mugun tsoro ya gama kama ta, A halin yanzun babu abinda ta fi muradi irin ta buɗe ido ta gan ta gaban Baffanta, Tsoron Hajiya Safee take bala'in ji kamar mutuwarta Tun da ta fara ganin alamomin iskacinta sun bayyana. Nafi na sake tunanowa a yanayin da ta ga Hajiya Safeen lokacin da ta shiga wani ɗaki ba tare da sanin ta ba maimakon nasu, kuma da yunƙurin da ta yi na aikata mata wani abu sai ta sake ruɗewa, Ga tun da ta tashi daman take jin wata irin faɗuwar gaba da rashin jin daɗi. Hajiya Safee ce ta ƙwala wa Tala kira, ta miƙe da sauri ta fice. Sai ga ta tadawo Hannunta riƙe da Kofi. Ta dubi Nafi ta ce “Amshi ki sha in ji Hajiya” Ta yi mugun tsorata ta kasa amsa, sai kawai ta rushe da kuka, Tala ta zauna a

Please Login or Register in order to submit comment