Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta matso ta jikinta tana wani murmushi tana taɓa jikinta, Ita dai Nafi duk abin da take mata ta yi shiru ta kasa magana ba za ta ce tana jin daɗi ba kuma ba za ta ce ba ta ji ba. Jin hannu da ta yi cikin Rigarta ya sanya ta zabura ta fara tuna maganganun da mahaifiyarta ke yawan yi mata da gargaɗi. Ta yi saurin ƙwace jikinta, Hajjaju da ke Rage kayan jikinta ta Kalle ta, tana faɗin “Lafiyarki?” Ta ɗaga mata kai jikinta na wata irin karkarwa lokaci ɗaya, ga zufar da ta fara jiƙa ta, sai ji take yi jikinta na chanzawa. “Hajjaju Ba ki mata bayani ba ne ta ya na fara ɗaukar chaji za ta kwafsa min”. Shiru Hajjaju ta yi, kuma ta fara mata magana cikin Harshen turanci “Baturiya ni fa ban shirya yin komai da yarinyar nan ba, kin ga duka-duka yaushe ta zo, akwai rashin wayau sosai tattare da ita sannan ba ta san komai ba, ina so na fara gyara ta sosai na fi son na ɗan fara Gyara tukun, amma za ki iya nuna mata abin da za ta miki” Ta jinjina kai kawai, Sai ta koma kan gado ta zauna tana sauke numfashi, Ta janyo Nafi da ta yi tsaye tana mata raɗa a kunne, Duk sai Nafin Ta ji tsigar jikinta ta tashi, ta daure ta yi abin da ta ce yanda ta ga tana nuna mata. Hannunta ta sanya yana kyarma kamar yanda tace ta fara taɓa zip ɗin irin yanda ta ce ta yi, ta zuge ƙasa, sannan ta fara ƙoƙarin cire mata rigar Ta kwanta ta juyo tana kallon Nafin ta miƙo mata hannu ta matsa dab ita. A hankali ta sanya hannu ta fara warware mata mayafin jikinta, Sannan ta kai hannu kan doguwar rigarta ta fara ƙoƙarin taɓawa, tana kai hannunta kan ƙirjinta ta ji wani mahaukacin Shock har cikin ƙwa-ƙwalwarta, ta yi ƙara tana ja da baya, hakan kuma ya bawa rigarta damar saɓulewa ta ida yin ƙasa. Ɗago idanun da za ta yi suka haɗa ido da Nafin ta ga Idanuwanta suna kamar wuta kamar tartsatsi, ta yi wata irin zabura dan gabaɗaya ƙwayar idonta ta chanza launi, Hajjaju da ta shiga toilet ta fito da ɗan Towel tana kallon su fuskarta da Alamun mamaki. ta ce ‘Lafiya B?.’ Ta yi saurin saukowa daga gadon tana girgiza kai “Ki ce ta tafi..”. Hajjaju ta ce “Wai me ya faru ne?” ba ta saurare ta ba, ta yi saurin faɗawa Toilet, Hajjaju ta ce Nafi ta fice, ita dai ba ta lura da irin yanda launin ƙwayar idonta ta yi ba. Tana jin an ce ta tafi ta yi saurin ɗaukar mayafinta ta chukurkuɗa ta fice tana ta kyarma.....
_Washe Gari_ Da wuri aka kawo Allurar da za a yi wa Dr. Babban likita ya yi masa. Mintuna Talatin da yi masa Allurar abubuwan suka fara sauƙi, numfashinsa da bugun zuciyarsa ya ɗan fara daidaita. Hakan ya sa hankalinsu ya ɗan kwanta, Ammi ta koma gida su kimtsa su dawo ita da Imaan daga masarauta ma an ɗan rage doctor ya ce nan da ko awa biyu zai iya tashi. Hajiya ce kawai ta ƙi tafiya tana masarautar ita dai. Abdul ya sa aka gyara wani room me kyau kusa da Office ɗinsa Tsaf aka maido shi nan.......
*#K_shitu.*
_-2023_
_Qalb_
Paid book, 200 VIP 500
*09117440993*
*09060584800*


_*K _ S H I T U 🦋*_

*ZUCIYA...!!*
(Qalb).

*(14).*
Ƙafafunsa ne suka fara motsi sai idanuwansa da ya fara ƙoƙarin buɗewa, Daidai lokacin Abdul ya buɗe ƙofa ya shigo Ammi da Imaan suna bayanshi. Farin ciki ya kama su ganin ya buɗe idanuwansa ya kuma rufe, Imaan ta yi saurin ƙarasowa bakin gadon tana mishi magana “Yaya ka tashi ya jikinka?” Hararar ta Abdul ya yi ya ce “Za ki fara ko Imaan wa ya ce miki ana wa marar lafiya ihu, idan kika yi wasa gida za ki koma” baya ta yo inda Ammi ke tsaye tana kallon sa tana murmushi, Ta marairaice fuska ta ce “Sorry Yaya ba zan sake ba fa” Ahmaad da ke jin su sama-sama ya buɗe idanuwansa da ƙyar, sai kuma ya yi saurin rufe su saboda dishi-dishin da ya gani, ya sake buɗe su kan Ammi. A nutse ya fara ƙare wa ɗakin kallo, yana tuna abubuwan da suka faru sai yai saurin kallon hannumsa, ya kuma maida kallon sa gare su Yanda suka yi tsaye suka kafe sa da idanu, Ya lumshe idanuwa yana jin Zuciyarsa na masa nauyi da kuma wani ƙunci da yake ji da ɗaci a ransa, kwata-kwata bai san lokacin da hawaye suka zubo daga idanuwansa ba, Ya musu alama ta ido su ƙaraso, Har rige-rigen tambayar sa ya jiki suke yi me ke masa ciwo, sai murmushi yake yi, Kafin da ƙyar ya ɗaga hannunsa ya dunguri kan Imaan a hankali. Cikin sauri Abdul ya fita,sai kuma ga shi ya dawo shi da Hajiya, ta shigo da sallama tana takowa riƙe da 'yar sanda Ta iso gaban gadon tana kallonsa fuskarta cike da fara'a Imaan ta tashi daga kujerarta ta ba ta gurin ta zauna. Cike da son ƙarfafa kansa ya fara ƙoƙarin jingina da gadon cikin ransa sai addu'a yake yi Ubangiji ya sanya Abdul be faɗa wa Ammi halin da yake ciki ba. Ya ƙawata fuskarsa da sassanyan murmushi ya ce, “Hajiya, Ammi good moirning” Tare suka amsa masa Sai Hajiya ta dubi Abdul tana faɗin, “Wai dan Allah me ke damun abokinka ne ko dai wani abu ya ci ne?. Gaskiya ya tada mini hankali ban sanya rai zai sake shaƙar iskar duniya ba, Aman jini fa ba wasa ba ne, Yayata da mu ke uwa ɗaya uba ɗaya da ita tun da ta yi aman jini aka kaita asibiti Allah ya amshe ta, Ni fa ban taɓa ganin wani ya yi Aman jini irin wannan ba ya rayu, jini ba kaɗan ba kuma kai, Allah me iko, Ina roƙon Allah ya kare ka Ahmaad Allah ya tsare ka.” Dukansu shiru suka yi Har Abdul ɗin dan ba shi da abin faɗa, Jikin Ammi ya ƙara yin sanyi, Ita Kanta Hajiya da ka kalle ta za ka fahimci tana cikin damuwa. Cikin rashin sanin Abin faɗa Abdul ya buɗi baki zai yi magana, Amma Dr A ya yi saurin katse sa yana faɗin, “Kai Hajiya fa. kin san ana samun ɗan kuskure wani taste na je na yi shi ya sa, Amma mutane da dama sun yi aman sun rayu kin san ni yanzu garau nake jina zan iya faɗa da kowa.” Duk sai suka yi murmushi lokaci ɗaya, Abdul ya harare sa “Ka san dai ba za ka fara tunanin had’a ƙarfinka da nawa ba ko?” “Kana tantama kenan, Matso ka gani” Ya yi dariya ya ce”Zan kyale ka ne kawai saboda Ammi”. Yana masa magana yana cire ƙarin ruwan da aka saka masa. Umurni Hajiya ta ba Abdul ya sanya hadimanta su shigo da Abinci, Ya amsa yana ficewa daga Room ɗin. Su uku suka shigo sanye da Unifoarm ɗin Masarautar Suka ajiye Wani ƙaton tray da Flask da cup da sai breakfast suka fice. Abdul ne ya haɗa masa Tea me kauri marar zafi sosai miƙo masa, bai wani sha da yawa ba ya ce ya ƙoshi sai da Su Ammi suka matsa masa sannan ya ɗan ƙara, Abdul ya ba shi magani. Alhamdulillahi ya samu ɗan kuzari da ƙarfin jiki, tun da har ya tashi ya yi Sallah. Daga Masarauta Aka shiga zo masa ya jiki, Sai wajen Seven na dare sannan ya samu kansa, ya matsa wa Abdul a sallame sa, Abdul ɗin ya ce “An ƙi ɗin” ya yi murmushin mugunta ya ɗaga kafaɗu, ya ce “Idan ka gama komai zan koma masarauta”. Yana gama faɗar haka Ya miƙe ya sanya Takalman da aka ajiye masa, ya buɗe ƙofar ya kashe ma Abdul ido ya fice.......
*#K_shitu.*
09117440993

ArewaBooks@Kshitu.
09117440993

*ZUCIYA...!!*
(Qalb).

*(15).*
Nafi na kwance kan gado ita kaɗai ta yi ɗaiɗaya Sai dariya take yi kamar me matsalar ƙwaƙwalwa. Da ta tuna irin taɓargazar da ta danƙara a rugarsu sai ta kuma fashewa da dariyar, Da kuma irin yanda Inna Hure ta saita ta lokaci ɗaya ta nutsu ta sha wahala. Ta wani cije leɓe cike da zallar mugunta Tana hararo irin rashin mutuncin da za ta shuka musu idan ta samu dama. Hinde da ke shigowa ta tsaya tana kallon ta, cikin zuciyarta tana ayyana irin Yarintar da ke ɗawainiya da Nafin da rashin sanin ciwon kai. Ta ƙarasa cikin ɗakin tana girgiza kai, Sai lokacin ma Nafin ta lura da ita, ta ɗan tsagaita da dariyar tana toshe baki. “Nafi anya ba ki da Taɓin ƙwaƙwalwa ko dai kin zare ne?”. Cewar Hinde tana kallon ta. Ta yi shiru tana sunkuyar da kai ƙasa cikin jin kunya. Matsowa ta yi kusa da ita ta zauna ta fara mata magana, “Wai Nafi anya ba ki da Aljannu? ɗazun nan kika dawo ba ki min magana ba kika shige kewaye kika fito ina ta tambayarki yanda kuka ƙare da su Hajiya baturiya, Allah ya sa ba ki musu sakarci ba, ina ta miki magana kin yi banza kin ƙyale ni, na fita Unguwa na dawo yanzu kuma kina dariya, me suka ce miki ne wai?” Cike da zallar mamaki Nafi ta ɗago tana Kallon ta. Ta ɗan yi jim sai kuma ta ce “Wace ne Baturiya ni kuma gaskiya ni dai ban hita ba ina nan tin shahe ban tashi ba”. Ta yi mata wani kallo a harzuƙe ta ce, “Uwarki Nafi! ni za ki maida sokuwa, idan ba ki fita ba tun safe har yanzu da duhu ya fara gidan uban wa kika ci abinci kika chanza kaya ke fa munafuka ce.?” Ta yi Narai-narai da idanuwa ta ce, “Na ranse fa..” Katse ta Hinde ta yi tana tsaki ta ce “Yi min shiru zararriya, lallai ta tabbata Maganar Hure ba ki da Hankali sam Mts! in ban da iskanci Mahaukaciya kike son maida ni ko me?” Sai kawai Ta ga hawaye na zuba daga idanun Nafin ta zabga mata harara ta miƙe ta shige toilet cike da jin Haushin ta. Tagumi Nafi ta yi har ta rufe ƙofar Toilet ɗin, ita dai Allah ya sani yau tun safe ba ta je ko ina ba tana nan zaune. Matsalarta ɗaya ta kasa tunanin Abinda ya faru bayan idonta, dan duk wani abu da ya faru da ta yi tunani sai ta riƙa ganin komai kan idonta, Amma sam ita ba ta ga Hinde ta fita ba ko wani ya yi wani abu, Ga shi kuma Tun da ta zo Ta yi tunanin Baffanta amma ta kasa ganin komai da ya dangance sa, Saɓanin da tana rugarsu komai ya faru A bayan idonta ko da bai shafe ta ba da ta yi tunanin abun sai ta dinga gani kan idonta tamkar a lokacin abu ke faruwa. Ta buga uban tagumi tana ƙoƙarin tunani har da rufe idanuwa amma ba abinda ta gani. Ita dai wasu lokuta ta sha tambayar kanta ko dai Mayyar ce kamar yanda Fulanin Rugarsu ke faɗi, Sai kuma ta yi dariya kawai ta tuna maganganun Mahaifiyarta. Ita kaɗai ta fara surutu cikin harshen fulatanci Babata wai kina ina ne ina buƙatarki, “Wayyo hammana Baffana, ni fa ban tahi ko ina ba ku hiɗi ma Hinde”. Hinde da fitowar ta kenan ta ji abinda Nafin ke faɗi har da hawayenta, sai kawai tai dariya cike da shirme ita ma ta fara tunanin me ma ya sa za ta biye ma Nafin Dan ta san ko chan ba hankali ya ishe ta ba idan tana abubuwa wasu lokutan kamar aljana. “Hum! Nafi ke dai wallahi ba ki gajiya da shiririta yarinta na damunki. Ke ma da laifinki fa ai ba abun da hankali zai ɗauka ba ne, ɗazu ki dawo daga Wajen su hajjaju yanzu kuma ki kawo man wani busasshen rainin wayaunki wai ke kina nan tun da sahe, wallahi ba 'yar rainin wayau irinki, kin ga dole raina ya ɓaci ai ba wasa nake maki ba ah to, ni ta shi in shirya ki mu je ayi maki kwalliya” Sumi-sumi ta miƙe Hinde ta buɗe Trollyn da Hajjaju ta ba ta, ta duba Riga da wandon da ta ce Nafin ta sanya ta fiddo su wando baƙi sai rigar fara da kaɗan ta wuce cibi sai bazarta da ta ƙawata rigar. Wandon kuma ya yi kyau me yanka Crazy da kuma High-hills takalma 'yan daidai. Ta tsare ta ta shirya ta, sai wani sussune kai take cikin jin kunya. Ita kanta Hinden sai da ta ce Wai dan tsananin kyan da Nafin ta yi, kayan sun zauna ɗas kan fatarta me haske, duk da har lokacin da ka kalle ta za ka fahimci Rashin wayewa Tattare da ita, da kuma fatarta da ba ta ida washewa ba. Ta kama hannunta tana nuna mata yanda za ta yi tafiya da takalmin da gargaɗin da ta yi mata kan nutsuwa, Sannan suka fice Nafi ma tafiya da ƙyar da Wandon da rigar sun bayyana Ƙirar jikinta ga kuma kayan da Hinden ta ba ta ta sanya sun sake ƙara mata girma da na jiki, Suka fito zuwa ɗakin da Dee me Makeup ɗin take, suka shiga Nafi sai gurɗewa take dan takalman sun fi ƙarfinta, saboda ita tun da take a rayuwarta ba ta taɓa ganinsu ba sai Yau ɗin. 'Yan matan wurin sai chaɓa mata maganganu suke yi, A kaikaice abun kuma ya ƙona mata rai musamman yanda suke kushe gashinta saboda hassada da baƙin ciki, ita dai ta yi shiru ranta a ɓace. Dee ta matso ta fara mata light makeup me nutsattsen kyau. Nan fa ido ya sake yi mata yawa duk ta yi bala'in tsarguwa har aka gama kwalliyar zuciyar 'yan matan da yawansu baƙiƙƙirin saboda jarababben kishin tsiya. Sai yatsina suke suna abubuwa. Ta yi matsanancin kyau sosai fiye da tunani Ga idanuwanta da suka sha eyeliner da light eyeshow sun yi kyau me zautarwa da rikita ɗanAdam sam ba ta yi kama da bil'adama ba, Ga ƙaramin madaidaicin bakinta da aka saka lipstick sai sheƙi yake da maiƙo kamar wata aljana. Tana ɗabo idanuwa 'Yanmatan da suka santa suka tsorata sosai a sace duk suka fice cike da fargaba dan ta yi wani irin kyau sosai kamar ba ita ba dan dama Dee ta iya kwalliya kamar hauka, ba ta yi ma ƙananu sai jiga-jigai yarinyar Hajjaju ce ita kanta me kuɗi ce sosai. Aka sake gyara mata Gashi aka saka Ribborn me ƙyalƙyali aka yi packing gashin ta fito gwanin ban sha'awa ita kanta Sai da ta ɗan tsorata da irin kyan da Nafin ta yi shi ya sa ko Photo ma ba ta yi mata ba. Hinde sai washe haƙora take yi, Saboda farinciki, Suka miƙe tana ma Dee godiya suka koma Nasu ɗakin. Gaban madubi ta tsaya da ita, Nafi tun da ta fara kallon kanta ta ruɗe sosai sai zare idanuwa take cike da jin tsoron kanta, sai ta nuna ta cikin mirror ɗin ta tambayi Hinde wacece ta ba ta amsa ita ce, amma sai ta shiga girgiza kai. Faɗi take Wai duk abinda ta yi sai wannan Aljanar ta yi, Ta fiddo harshe sai kawai ta ga ita ma Ta cikin mirrorn wacce take faɗi a matsayin ba ita ba wata ta yi. Sai da Hinde ta yi mata bayanin yanda Mirror yake da yanda za ta ga kanta sai kuma ta ƙara ma da faɗi mata to mi ya sa ɗazu ba ta ƙi yarda ita ba ce sannan ta ɗan nutsu, amma ta yi zuru sai Kallon kanta take yi cike fa tantama. Ba maganar salla daga Hinden har Nafi..Ƙarfe 7:20 Ƙarar shigowar motoci ta cika gidan har cikin Ɗaki su Nafi ma na ji......
*#Khadija Muhammad Shitu.*
*#ZUCIYA🦋*
*#Paid book*
*#AhNaf#.*

Littafin kuɗi ne Naira ɗari biyu ki biya ta wannan account ɗin, *9117440993* Palmpay Bank. Khadija Muhammad Shitu.


_Wattpad@Kshitu_
09117440993

*ZUCIYA...!!*
(Qalb).

*(16).*
Kafin ka ce wani abu gidan ya cike da motoci, babu abinda ke tashi a harabar gidan da aka ƙawata sai kiɗa 'Yan'matan sun yi gayu na gani na faɗa.Manyan mutane me masu muƙami da Arziƙi suka kawo ziyara Mata da maza, an ƙawata inda za su zauna sosai. “Dalla Nafi ki yi sauri ki fito wannan wane irin abu ne Mts! kin san kowa ya taru amma kin tsaida mu dan tsabar rainin wayau, in kin ga dama ki ɓata kwalliyar” Hinde da ke tsaya tuntuni ta gama shirinta Nafi kawai take jira ta fito daga Bayi amma shiru ta faɗa cike da Masifa tana jan guntun tsaki.Ba ta ƙara jimawa ba ta fito tana ba ta haƙuri, ta sake fesa mata tsadaddun turaruka suka fito A tare. Yanda Nafin ke tafiya a hankali saboda takalman da ke ƙafarta ba ƙaramin ba da chitta ya yi ba, Hinde ma ta yi kyau ita ce ta ruƙo hannunta, Har suka fito harabar gidan, Idanuwa suka dawo kansu sai Kallon Nafin ake yi kamar za a cinye ta, ga gashinta a waje parking ɗin shi kawai aka yi ya bazo har kafaɗunta, ga wadataccen hasken da ya haska su Gabanta sai faɗuwa yake yi, Hinde ta sake damƙar Hannunta suka nufi Wani Teburi suka zauna, Me zuba abinci ya kawo musu abinci da snacks da Lemu sai ruwa. “Nafi dan Allah kar ki kunyata mu, kuma ki saki jikinki” Hinde ta raɗa mata a kunne. Kaɗan suka ci snaks ɗin masu rawa suka fara sai liƙi ake musu, suna sake dagewa. Wata Hamshaƙiyar Macce ce ta matso kusa da teburin su Nafi ta zauna tana ƙare mata kallo, Ta matso da kujerarta dab da ta Nafi tana murmushi ta ce, Beauty “Sunanki fa” Cikin jin tsoro ta ba ta amsa “Nafi”. Ta kamo hannayen Nafi ta ɗan matsa cikin nata tana aika mata da wani shu'umin kallo. Sai kuma ta miƙe ta fara Tafiya ta ƙarisa inda Hajjaju da Hajiya Baturiya suke ta yi ma Hajjaju raɗa a kunne, sannan ta koma ta zauna ta kasa ta tsare ta sa ido kan duk wani motsin Nafin....
Cikin jin haushi Abdul ya biyo bayanshi Ya fiddo Key ɗin Mota daga Aljihu ya shiga ya buɗe motar Dr A na nan tsaye, ya tada motar ya yi banza ya ƙyale shi, Ya shigo Ya zauna seat ɗin me zaman banza shi ma bai kula shi ba, ya ja motar Har suka Iso gidan ya yi Parking bai tanka masa ba, Ya buɗe motar ya fice shi ma bai tanka masa ba Ya ja motar Ya bar Gidan. Har zai shiga Sashensa sai kuma ya fasa Ya nufi Parlourn Ammi da sallamarsa ciki-ciki Ammi da ke riƙe da Kofi ta ɗebo ruwa ta sake shi ƙasa saboda mamaki, ta zaro idanuwanta duka waje tana kallonsa, Shi ma ita yake kallo ya kasa ƙarasowa ciki sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta nuna shi da yatsa “Ahmaad kai ne Abdul ɗin ne ya kawo ka wai me ya sa kake son ɓata mini rai ne??” Ya yi shiru bai ce komai ba, Ya ƙaraso inda take Yana ba ta haƙuri “Sorry Ammi shi ne ya kawo ni” Ta sauke ajiyar zuciya dan sai lokacin Hankalinta ya kwanta, Ta nuna mishi kujera tana faɗin “Shi kenan da asibitin za mu zo yanzu ya kake jin jikinka.” Zai yi magana Wayarsa ta fara ringing Ya duba sunan me kiran sai kawai ya kashe ƙara ya mayar aljihu. Kiran ya katse Still me kiran bai bari har kira uku, ya ja ƙaramin tsaki, Ammj ta ce “Waye ne ka ɗaga mana” “Akarsh ne” Ta harare sa ta ce “Idan ba zaka ɗaga ba bani wayar”. Bai iya musu ba sai kawai ya miƙa mata wayar. “Wato Doctor tsabar ba ka so na maka magana ba za ka iya picking call ɗina ba ko? to ai shi ke nan da ma na kira ka ne na maka ya jiki. Doctor ina faɗa maka babu lokaci ka amince a yi komai kafin mu rasa damar nan, Kwanaki uku kawai suka rage mana Please doctor muna buƙatar rayuwarka Ka kai mataki na ƙarshe fa, zaka iya rasa rayuwarka bakiɗaya, A yi magana a samu magana da Companyn da suke haɗa maganin nan ka ga kai ɗan sarki ne ko ba komai za su yi komai saboda Familynka kuma ka san suna ji da kai sosai...” Jin tun da ya fara magana be katse shi ba ya sa shi sauke numfashi ya ce “Hello kana tare da ni?” Hawaye kawai Dr A ya gani na zuba daga fuskar Ammi ta saki wayar ta faɗi ƙasa. Sai lokacin zuciyarsa ta shiga bugawa da wani irin mugun ƙarfi ranshi ya ɓaci ya fara jin haushin kansa dan me zai ba ta wayar yanzu shi kenan ta ji komai. Jikinsa ya kai ƙololuwa wajen yin sanyi Ya biɗe baki da ƙyar ya fara magana “Please Ammi ki tsaya na miki bayani, Bana so a yi aikin saboda ko da an yi ba za a dace ba, kawai za mu zubar da ƙimarmu ne mu nemi alfarma wajen ma'kiyanmu kum...”. Ta daka masa wata irin fusatacciyar Tsawa lokaci ɗaya idanuwanta Sun yi ja ta nuna shi da yatsa hawaye na bin idanunta. “Kai Ahmaad Ashe ba ka da tunani! Me kake sha ne haka da ke ruɗa maka ƙwa-ƙwalwa wai so kake baƙin ciki ya kashe ni ne, Ni da Ƙanwarka, wai me yake damunka ne haka, anya kai ne Ahmaad ɗina me sadaukarwa gare mu??” Sai matsanancin Kuka ya ƙwace mata, ta yi ƙarfin halin ci gaba magana Cikin muryar Kuka, “Yanda Mahaifinka ya mutu ya bar mu, haka kai ma kake so ka mutu a banza, Ka san ZUCIYA kuwa ka san irin gaban raɗaɗin da nake ji, Ka san tsawon lokacin da na daɗe ina burin haihuwar Mai share mini Hawaye?? Kana wasa da abubuwa, Komai da ka ga ina yi don Farincikinku Nake yi, Ahmaad Ciwon Zuciya me muni fa, ZUCIYA! ZUCIYA!! kana wasa da ZUCIYArka kana sakaci sosai Mahaifinka ZUCI...”. Ta kasa ci gaba da magana Tari ya sarƙe ta. Hankalin Ahmaad ya tashi sosai, Gabaɗaya ya rasa inda zai tsoma ransa. Zuciyarsa sai ƙuna take idanuwansa sun rine saboda Tsananin ɓacin rai ya kasa magana. Yai shiru ya sunkuyar da Kansa ƙasa. Ta miƙe da ƙyar ta ɗauki ruwa ta sha Ta Haye saman bene ta bar shi nan Zaune. Ya daɗe nan zaune da ƙyar ya iya miƙewa ya ɗauki wayarsa yana dafa bango ya isa ɗakinsa. Numbern Abdul ya shiga Kira dan ya san wajen sa kawai zai iya samun mafita a wannan lokacin, Ya yi masa 3miscalls amma bai ɗaga ba, ya yi wurgi da wayar cike da baƙin ciki, zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama. Ke nan shi ma Ahmaad ya yi fushi da shi, dan ya san duk irin fushin da ya yi masa ba ya ƙin ɗaga kiransa. Har Ƙarfe Goman dare bai kira sa ba ya sake kiransa bai ɗaga ba yana ƙoƙarin sake kiran ya ji wayar A kashe. Ya lumshe idanuwa kawai yana wani murmushime ciwo.......
*K_shitu.*
#Qalb
09117440993


Wattpad@Kshitu
09117440993.

*ZUCIYA...!!*

*(17).*
Har dare ya ratsa sosai ba su Tashi ba sai ma gaba da abun nasu ya sake yi, ganin Nafi na gyangyaɗi ne ya sa Hinde ta zame ta bar ta ita kaɗai,Ta sadda kanta bisa teburin barci ya ɗauke ta. A hankali Nafi ta fara buɗe idanuwanta da sukai mata nauyi, Cikin Rashin Kuzari ta miƙe zaune tana hamma saboda yunwar da ke kartar mata 'yan hanji,Sai lokaci ma ta fara ƙarewa ɗakin da take kallo, Ta yi Saurin dirowa daga kan gadon tana 'yan leƙe-leƙe gadon da tsarin ɗakin ma kwata-kwata ba nasu ba ne wanda suka saba Kwanciya ba ita da Hinde, Wannan ya zarce wancan kyau fiye da misali ya haɗu An baza kayan kwalliya da na

Please Login or Register in order to submit comment