Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikinta yake na yunwa ta miƙe tana layi kamar ta yi maye saboda yanda sassan jikinta ke kwankwatsa, Abubuwan da suka faru ne suka shiga dawo mata take wasu hawayen baƙin ciki suka shiga zubowa da idanunta, tana tambayar kanta 'Da gaske ita ɗin Mayya ce?' da ƙyar ta iya takowa ta fito daga dajin Zuciyarta ta yi wani irin nauyi fargaba ta cika ta. Ta yi sallama a hankali ta shigo zuciyarta sai bugu take cike da tsoron Fitina da masifar inna Hure. kamar jira Inna hure take ta miƙe tsaya ta karkace baki ta fara bala'i, “Lalataccen yaro ka dawo daga Findahon (Isakanci/Lalatar) to ka fita yanzu ba zaka sake zama ba, Hauwa ta bar min Bala'i, ki fice ni bana tsoron iskacinka fa!” tsabar bala'in hausar ma bata fita sosai. Hinde ce ta taso cike da munafurci Tana faɗin, “Haba Hure daɗina da ke rashin hakuri fa matso ki ji” kamar ba zata bita ba sai kuma suka ja gefe, ta janyo inna hure ta fara mata raɗa, tun kafin ta kai aya Inna hure ta yi shewa cikin harshen fulatanci Take faɗin, “Kudi fa Hinde, na zata kwana yau ba Ku tafi tun yanzu”. Jan ta ta yi, suka sake magana “Ke Hure da Allah ba wannan ba yanzu ba ta abinci ta ci, sai ta yi wanka dan Muji daɗin more kuɗi wallahi Hajiyar Birnin nan bata harkar tsiya kuɗi zamu samu, qur'anin Allah gidanta kamar a lahira” “Qur'an na yarda ke hinde na kusa zama maikudin rugar nan kamar ki fa huuuu j`anniha(shagali babba) amma fa sai na daki tuwona da kununa ba zan bar ta haka ba ehe” “Ba wannan ba, baki so a ganta da kirki yanda zamu wafci arxiki, ki barta kawai ke da zaki mori kudi kawai ki yi yanda na ce, mu tafi da ita da kuzari”. “haka ne fa bari in kira ta, Ke Nafi zo nan” ta kwala wa Nafi kira. Cikin Nafi na kyarma ta amsa ta zo ta tsaya, Sai da ta harare ta, ta jaɗa mata da zagika da tsinuwa sannan ta ce, ta je ta ɗauki abinci na nan madahwa ta ci ta yi wanka. Kamar a mafarki ta ɗago daga zuƙunnen da take ta kalle ta bakinta ya kasa rufuwa saboda tsananin mamaki. Tsawa ta daka mata “Zaki tashi ki yi abinda na ce ne ko kuwa??” cikin sauri ta miƙe, duk jikinta a sanyaye tunani fal a ranta ta ɗauki abincin da yake rufe fai-fai da kindirmon da aka haɗa, kamar kar ta ci saboda tsoro kar a ace inna Hure kashe ta zata yi, amma saboda mahaukaciyar yunwar da ke cinta ta manta da wani zargi ta ci ta yi nak. Ta yi wanka ta shiryo cikin kayanta na fulani ta dawo ta tsaya gaban Inna Hure, ta ce “Inna na gama.” sai sannan Hinde ta tanka mata, “Yauwa Nafi, So nake na tafi da ke Birni yau Aikatau Ki saki jikinki karki nuna ƙauyanci kin ji ki dangwali arziki.” Hawaye ne suka cika idonta, ta san dama ba banza ba, ta ɗago cikin sanyin jiki ta san bata da zaɓin da ya wuce haka, Amma baffanta shi ne damuwarta. “Baki ji bane??” Inna ta faɗa cikin fad’a, a sanyaye ta amsa da “To”. Umurni Inna ta bata da taje ta haɗa kayanta, ta miƙe jiki ba kuzari ta nufi 'yar bukkarta....
#K_SHITU
#PAID BOOK 200
9117440993 PALMPAY BANK.
[11/19, 10:27 PM] KS.: K_shitu’s Noble World
Wattpad@Kshitu

*ZUCIYA...!!*

*(5).*
Tana daga cikin ɗakin Ta ji yo sallamar Baffanta, Wani irin kuka ne ya kufce mata ta yi, saurin toshe bakinta, tana jin zuciyarta babu daɗi kwata-kwata. ta share hawaye ta kwashi 'yan tsummokaranta ta ƙulle sannan ta fito. Kallon Baffa ta yi cike da tausayawa ta ce “Ina yini Baffa.’’ Murmushi kwance kan fuskarsa ya amsa mata, “Lafiya lau Nafisatu kece?” cikin sanyin jiki ta amsa saboda hararar da Inna Hure ke banka mata. “Eh Baffa ni ce”. Baffan zai sake magana inna hure ta huro hanci ta ce, “To me ɗiya! kar ka ɓata mini lokaci gwara da ka zo ku yi sallama da ita, dan Binni Hinde zata tafi da ita Aikatau.” Cike da mamaki ya ce “Hure Aikatau hwa kika ce?” a masifance ta bashi amsa “Malam ina tunanin kai ba kuma ne ba, ka ji na ce aikatau ai ba wasa nike ba, dan ni ba zan iya zama da ita ba baƙin jininta ya shafe mu ni da hassatu, ko kuma ta ci gaba da janyo mini Bala'in Fillon rugar nan ba, idan kuma ka ce sai ta zauna billahillazi sai na cikin maciji ya fita 'yanci da komi”. Shiru Baffa ya yi yana tunani, Zuciyarsa ce ta dinga ayyana masa gwara Nafi ta nisanta da fulanin rugar ko ta samu 'yanci a matsayinta na 'yarAdam, ta kuma huta da Fitina da masifar Inna hure da hassatu. Bashi da zaɓi da kuma ɓulalliyar mafitar da ta wuce ya bita da fatan alkhairi da addu'ar tsari hakan ya sa shi faɗin, “Nafi ki kula sosai Allah ya tsare ki a duk inda kike Allah ya zama gatanki, Ubangiji ya albarkaci rayuwarki”. Hawaye ne suka shiga zubowa daga idanunta jiki a mace ta amsa “Amun Baffana na gode”. Yanda ta yi magana murya a matuƙar sanyaye ne ya ƙara dagula lisaafin Baffanta, zuciyarsa ta raunata, kukan zuci kawai yake yi, A duniya babu wanda yake tsananin so da ƙauna da kuma tsantsar tausayawa irin Nafi. Maganar da hinde ta yi mata ce ta sanya kuka taho mata, 'Nafi lokaci na ƙurewa ya kamata mu tafi' kuka ne ya ƙwace mata, Baffa ma duk dauriyarsa sai da hawaye suka zubo masa. Tana kuka Hinde ta tasa ta gaba Inna hure na bayanta suke fice daga gidan, Sai da Inna hure ta yi mata gargaɗi sosai, sannan ta dawo, ita kuma Hinde ta umurce ta da ta chanza kaya bayan sun ƙaraso gidan ta chanza kayan sannan Hinde ta ɗauki abun da zata buƙata suka fito da datse gidan. Tafiya suka fara Har suka ƙaraso cikin Kasuwa nan ne suka hau babur su biyun dan a kaisu tasha. Bisa babur ɗin me masifar ƙara suka taho, ga su biyu ne kuma akwai nisa sosai da inda ake hawan motar. Tun da me babur ɗin ya taho da su Nafita lula duniyar tunani, ita kaɗai take magana cikin ranta. 'Yanzu kuma wacce ƙaddarar ke jiranta, Wace irin masifar zata tarar a birnin, ya rayuwarta zata kasance me ya sanya take rayuwa kamar ba 'yarAdam ba komai yana zo mata banbaraƙwai Yanzu kuma ita ce da Ina mahaifiyarta take, Wace irin rayuwar maraici da rashin gata da ƙunci take yi haka, Allah sarki Baffanta abun alfaharinta sai yaushe zasu sake ganawa da shi???.' Waɗannan sune tambayoyin da ke danƙare a zuciyarta. Tafiyar Kusan Mintuna Arba'in suka yi, suka ƙaraso Inda ake hawan motar da za a fice daga Rugar ta su. Sallamar me babur ɗin Hinde ta yi, suka matso inda yagwalgwalun motocin suke, an yi sa'a mutum biyu ake jira, suna biyan kuɗi suka shiga mota ta tashi zuwa garin Katsina.....
#K_shitu
#Zuciya (Qalb)
#Reposted
#Paid book 200.

Na fara karɓar kuɗi, 200 ɗari biyu. ki/ka biya naka ta wannan account ɗin,
9117440993 Palmpay Bank.
Shedar biya 09117440993.

Masu ƙorafi akan hausar Inna Hure, su fa fulani ne na asali, so hausarsu ba me kyau bace sometimes ina rubutawa yanda suke faɗa su sometimes kuma ni ce nake gyara a daidaitacciyar hausa yanda zaku fahimta.
*Arewabooks@Kshitu*

Share Please.
[11/21, 7:48 PM] KS.: Khadija Muhammad Shitu
Arewabooks:Kshitu
Wattpad:Kshitu
BakandamiyaHikaya:Kshitu.

*ZUCIYA...!!*

*(6).*
Ƙarfe 5:37 Dr A ya fito daga wanka ya shirya tsaf, sannan ya dawo Parlour inda ya bar Abdul shi ma ya zauna. Miƙa Abdul ya yi yana aje wayarsa ya ce, “Mutuniyar nake ji fa.” ta'be baki ya yi, ya dauki wayar da ke gefensa karama ya dannawa wata number kira tana ringing ya miƙa masa ba tare da ya yi magana ba. Ya karɓa ya kara a kunne, jin muryar Sale Kukun Dr ya sanya shi faɗin, “Hello Sale nine ba Yarima ba, kana ji na, ina son a kawo mini abinci yanzu ko ma wane kala ne ina jin yunwa”. Daga chan bangaren Sale ya amsa, “Ai ho ranka shi daɗe Ashe kai ne, yanzu kuwa zaka ganni” ko amsar Abdul be tsaya ji ba ya yanke wayar. Girgiza kai kawai Abdul ya yi, dan shi Tsakaninsa da Allah dariya Salen ke bashi. Ya juyo ya kalli yarima kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, mintuna bakwai tsakani, sai ga knocking ɗin ƙofar ana yi, Abdul ya miƙe yana hamma ya doshi ƙofar ya buɗe ɗaya daga cikin masu tsaron ƙofar ne ya faɗa masa Sale na waje, umurni ya basu da su bar shi ya shigo ya dawo aikinsa ne. Shigowa Salen ya yi yana 'yar mita ƙasa-ƙasa. Ya jera masa abincin da ya kawo a dinning, yan gashe da su, amma Yarima ko kallon inda yake ma bai yi ba kawai dai ya ɗaga masa hannu. Har zai yi saving ɗinsu Abdul ya dakatar da shi ya ce, “Bar shi ma zuba ka ji Sale mun gode haka ma.” cike da walwala kan fuskarsa ya amsa masa ya fice. Zuba tuwon shinkafa da miyar Kuka da ta ji tsoka dafaffiya Abdul ya yi, ya ci sosai yana ta rausaya kai saboda yanda abincin ya daɗi sosai, Ya kalli Dr ya ce, “Gaskiya girkin ya yi dadi ya kamata ka ci fa”. Girgiza kansa ya yi kaɗan Alamun baya jin yunwa, bai takura sa saboda kar ya sa mishi gajiya ya kammala ya dawo ya zauna, Tun ɗazun yake son ya yi masa maganar da ke cinsa, ya daure dai ya ce “Dr Please ina so mu yi magana”. “Umhum” ya bashi amsa a takaice. Cikin lalama Abdul ya fara masa magana, “Ahmaad na roƙe ka dan Allah ka amince ayi aikin nan ka ga Akarsh 1week ya bamu kuma yanzu sauran six days idan kuma ba a yi ba akwai matsala sosai fa, Please Ahmad muna buƙatar Rayuwarka.” Murmushi ya yi me matuƙar kyau, wanda Abdul ya daɗe bai ga ya yi irinsa ba sannan ya fesar da Numfashi ya ce, “Oh Abdul!! Da ace hakan zata kasance da zan fi kowa farinciki yanda zan kama enemies buh Zuciyata bata yin aiki an riga da an chanza ta, ina tabbatar maka asarar Lokaci ne da dama kawai za ayi, idan ta kasance Akarsh ya matsa zasu yi aikin ko da anyi babu Nasara”. A wannan karon har hawaye sun fara taruwa a idanun Abdul jikinsa ya yi sanyi laƙwas gani yake yi ma yarima ya mutu ne, ya yi ƙarfin halin faɗar “Me fada ba za a yi nasara ba ka manta da ubangiji ne??” Silently ya haɗa hannayensa guri ɗaya kamar yanda ya saba cikin nutsuwa ya ce, “Please mana Abdul try to understand ka bari gobe zamu yi magana zuciyata tana ciwo yau na yi surtutu da yawa”. ɗaga masa kai kawai ya yi yana kallonsa, Allah ya sani a duniya yana yiwa Ahmaad ƙauna ta tsakani da Allah ne kuma yana tausayinsa sosai. Hancky ya miƙo masa yana ɗaga masa gira ɗaya, Karɓa ya yi ya goge hawayensa, still bai daina kallonsa ba, sai da ya ɗan Harare sa sannan ya yi murmushi ya kawar da kansa dan ya san saboda kallonsa da yake ta yi ne. Miƙewa ya yi Ya shiga ya yo alwalla ya dawo, shima Abdul ya shiga ya yi, Saboda lokacin sallar magrib ya kusa bai fi 20mnts ba....
Tun da suka fara wuce Rugar ta su, Nafi ke kalle-kalle har tafiyar ta su ta miƙa sosai sun yi kusan Awanni Uku suna tafiya, har barcin wahala ya ɗauke ta. Tashinta Hinde ta fara yi, “Nafi fito muyi sallah mu ci abinci”. Ta watsake sannan ta amsa mata da 'To'. Ita Nafi sai a lokacin ta tuna da rabonta da sallah tun jiya da Mutuwar yaron, da kuma rigimar da aka yi, duk da bata nan. Ta fito daga motar suka yi Sallah sannan Hinde ta siya musu Wainar tsala suka ci suka sha ruwa sannan suka komo cikin mota sauran mutanen ma haka, aka ci gaba da tafiya. Tafiyar awanni Biyu da 'yan mintuna suka ƙara duk saboda motar da ba mai kyau bace, Cikin Birnin Katsina suka shigo, me mota ya nufi tasha da su, Nan ne fa Nafi ta saki baki da hanci ta baza idanu tana kalle-kalle kamar idanuwanta zasu faɗo, Ta wani lambu mai kyau suka zo wucewa mai ni'ima da sanyi, Nafi Ta lumshe idanuwanta ta buɗe zuciyarta ta buga, tunanin hammanta ya bijiro a zuciyarta. 'Shin dama nan ɗin ne birnin da yake faɗi mata, yana ina lafiyarsa ƙalau rabon ta da shi tun ranar lahadi yau gasu talata??' Tasha me motar ya ƙaraso ya yi Parking fasinjojin suka fara fitowa, Saida Hinde ta yiwa Nafi magana Sannan ta ɗauko 'yan tsumman kayanta ta fito itama. Hinde ta ruƙo hannayenta suka fito suna tafiya, Kallon da wasu daga cikin Mutanen da ke tashar ke bin Nafi da shi ne, ya Hanata sakewa ta ci gaba da kalle-kallen duk inda suka yi sai an bita da idanuwa ri.. Bakin titi suka tsaya suka tsayar da Napep Hinde ta kwatanta masa unguwar da za a kaisu suka shiga.....
*#K_shitu.*
09117440993.

'Yar'uwa an fara biyan kuɗi fa, wannan littafin ba free ba ne, ki biya 200 a sauƙaƙe ki karanta.

*9117440993*
*Palmpay Bank.*
[11/21, 8:09 PM] KS.: *Arewabooks@Kshitu*

*ZUCIYA...!!*


Wannan Shafin Na Sadaukar da shi ga *AUNTY HAJJO*❤️Ina miki fatan Alkhairi.

*(7).*
Yanayin Unguwar shiru-shiru ba hayaniya, kuma unguwar da ka shigo zaka fahimci ta masu matsakaicin ƙarfi ce. Bakin wani Shago Hinde ta ce wa Mai Adaidaita sahun ya tsaya suka sauko, ta bashi kuɗinsa, suka ci gaba da Tafiya Nafi sai kalle-kalle take yi, 'yan tsirarun mutanen da ke wuce da waɗanda ke zama bakin shaguna Sai binta suke da kallo, har suka ƙaraso wani ɗan lungu, Gida na biyu me dakali da bulan fenti suka tsaya, Hinde ta fiddo mukulli ta buɗe, ita dai Nafi cike da ƙauyanci take kallon komai da Hinden ke yi, har ta cire kwaɗɗon suka shiga, Nafi bata rufe baki ba ta ci gaba da kallo ta tsaya ƙiƙam ta ƙi ci gaba da tafiyar. Da ƙyar ta ci gaba da takowa kamar me tsoron wani abu, Suna tsayawa ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan ta tsaya, Hinde ta sake buɗewa, still tana ta kalle-kalle na ƙauyanci, ga tsoro da ya bayyana ƙarara kan fuskarta kamar a ce tak ta arce. Sai da Hinde ta ce mata “Ki saki jikinki kinji yanzu wanka zan sake miki kiyi fes ki saka kaya irin na 'yan Birni sai muje gidan Hajjaju wacce zaki wa aiki amma dan Allah Nafi ki bada haɗin kai komai aka ce kiyi kar kiyi musu, idan har kika kuskura kika yi musu mutuwa zaki yi babu ruwana.” Tsoro ne ya kama ta gyaɗa mata kai suka shiga ɗakin. Akwati ta buɗe ta fiddo wasu riga da skirt masu kyau ba laifi, waɗanda zasu yi wa Nafi daidai. Ta fiddo sabulu da soso ƙarƙashin ɗan gadonta ta kai ruwa bayi Sannan ta dawo ta bata zane ta tuɓe kayan ta nuna mata yanda zata yi wankan ta bar ta. Ta dirje jikinta sosai fatar ta yi haske sosai, sannan ta dawo ɗakin hinde ta bata man shafawa ta shafa, ta sanya kayan Hinde ta ɗaura mata ɗan kwali ta yi kyau tsaf hasken fatarta ya ɗan dawo. Sai Ƙarfe bakwai na dare sannan suka fito daga gidan suka rufo ƙofar jikin Nafi duk ya yi sanyi hankalinta ya tashi zuciyarta sai harbawa take, suka tsaya bakin titi, ta tare musu me Adaidaita sahu suka shiga. Duk da dare ne amma akwai wadataccen haske wanda ya ba Nafi damar yin kalle-kallenta, Sosai garin ya bata sha'awa da mutanen kowa na ta harkar gabansa, sun wuwwuce masu gashin nama da shagunan aski da sauransu Nafi sai al'ajabi take ta yi, Yanayin Garin kaɗai da ka gani ka san cikin ƙayataccen Birni kake me cike da Wayayyun mutane masu ilimi. Tsoro ne ya fara shigarta lokacin da suka Fara kusanto manya-manyan gine-gine da fitilu masu matsanancin haske suka ƙayata layin kamar rana ga kuma gidajen masu mugun kyau da girma. Sosai Nafi ta sake karaya zuciyarta ta shiga Raya mata da ƙyar idan suna cikin duniyar mutane ma, ga kuma manyar motoci zuƙa-zuƙan da ke shige da fice daga wani danƙareren gida, muryar Hinde ce ta katse ta, ta kuma sake tsorata ta, “Ki fito mana Nafi” jiki a mace ta fito tana ƙanƙame jikinta, suka nufi bakin wani ƙaton gida Hinde ta ƙwanƙwasa. Me gadin ne ya buɗe yana ganin ta ya washe jajjayen haƙoransa yana faɗin, “Hinde ke ce tafe sannu” Cike da kwarkwasa ta amsa “E nice an wuni lahiya?” zai yi magana Aka yi horn ya yi saurin buɗe gate ɗin suka shige motar ma ta samu Nasarar shigowa ya maida Gate ɗin ya rufe.Tsayawa Nafi ta yi, taƙi ci gaba da tafiya saboda tsananin tsoro gani take gidan ƴan Kashe mutane ne aka kawo ta. Cikin faɗa Hinde ta ce, “Miye haka Nafi Mts! na ce ki saki jikinki kar ki yi ƙauyanci ana kallon mu fa”. Bata jira cewar ta ba ta janyo ta suka ci gaba da tafiya Tsirarun mutanen dake wangalelen Farfajiyan suka bisu da kallo, wasu suna zazzaune a Parking lot, bisa kujeru maza da mata. Tafiya suka ɗan yi suka ƙaraso Sashe na biyu wata babbar ƙofar main Parlour suka isa ta buɗe suka shigo, duk da ta riƙe Nafi amma jikinta sai kerma yake saboda tsananin tsoro ta ma kasa yin kalle-kallen ga uban hasken da ya dalle su. Wani sassanyan ƙamshi ne me daɗi da sanyin Ac ne ya daki hancinansu suka shigo cikin ƙaton parlourn da ya ji kayan more rayuwa. 'yan matan da ke zazzaune ne suka kwalliya suka fara binsu da kallo wasu sai harara suka bin su da shi wasu kuma ba yabo ba fallasa. Wani Ma'aikacin Hajjaju ne me kama da ɗan daudu ya matso yana rangwaɗa ya ce “Hinde sabuwar kaya aka kawo ne?”, “E Gaye ina Hajjaju ne?” Tana sama bari a muku iso. ya haye sama, bai jima ba sai gashi ya dawo, duk kallon banzan 'yanmatan ke wa Nafi ya sa ta tsargu. suka fara taka mattattakalar benen Nafi ta gurɗe zata faɗi Hinde ta riƙe ta sosai, 'Yanmatan suka kwashe da dariyar rashin mutunci, Har suka buɗe ƙofar suka shiga kan Nafi na ƙasa saboda tsoro da jin kunya. Tun da suka shigo Hajjaju ta ƙurawa Nafi idanu tana kallonta, ita kuwa ta sake tsarguwa gabanta sai faɗuwa yake yi.....
#K_shitu.
Paid book 200
09117440993.
[11/23, 7:50 PM] KS.: Wattpad@Kshitu

*ZUCIYA...!!*

*(8).*
Har suka shigo tsakiyar ɗakin jikin Nafi bai bar rawa ba, Hajjaju sai wani irin Kallo take mata irin na ƙurilla wanda ya sake tsorata ta. Tsaye suka yi ita da Hinden ba su zauna ba, saboda ƙa'idar Hajjaju sai ta bada izinin zama ake zama. Ta ɗan yamutse fuska ta ce, “Hinde wannan ce yarinyar?” Jiki na ɓari Hinde ta amsa mata “Eh ita ce”. Bata sake magana ba sai kujera da ta Nuna musu Hinde ta mintsine ta suka zauna duk da Nafi a ɗosane take dan ƙiris ya rage ta fashe da kuka tsabar tsorata. Hannunta ta miƙowa Nafi wanda yasha Jan lalle ya yi kyau aka yi mishi ado da zobunan zinare, Nafi ta ɗago suka haɗa ido da ita saboda mintsininta da Hinde ta yi. Cikin sa'a suka yi ido huɗu da Hajjaju hamshaƙiyar macce wacce a kallo ɗaya idan ka yi mata zaka fahimci arziƙi da wadata, hutu, gayu, jindaɗi, wayewa, isa, sun yi biyayya a wurin. Ta juya idanuwanta da suka sha kwalli blue kan na Nafi. Irin yanda Nafi ta zaro nata idanuwan ya sa dukkansu Zuciyonsu suka buga, Nafi ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa. Gyaran murya da kuma mintsininta da Hinde ta yi ne suka sake bala'in tsorata ta kamar ta ruga da gudu sai lokacin Kewar Baffanta ta bijiro mata ƙwalla ta cika idanunta. Cikin kunnenta hinde ta raɗa mata, “Ke Nafi wannan wane irin busasshen iskanci ne haka? dan ubanki tashi kije shegiya kar ki ja min asara dan wallahi na rasa wannan damar sai kin ci uwarki tashi ki je tana kiranki!” da fullanci take mata maganar ma saboda masifa ta turata, ta isa gaban Hajjaju. Hajajju ta kamo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita sosai cikin wani irin salo ta ce, “Miye sunanki?” Bakinta na kyarma halshenta na datsewa da haƙoranta ta ce “Nafi”. Ta yi murmushi “You mean Nafeesa ko??” Ta ɗaga kai duk da bata san me take nufi ba ita dai a tsorace take, saboda bata taɓa barin Yankin Rugarsu ba. Miƙewa Hajjajun ta yi, ta sake ta.Ta shige Bedroom ɗin da ke cikin Parlourn Ba ta wani daɗe ba sai ga Gaye ya shigo shi da wata macce da Trayn Abinci, su ka shigo Gaye ya kalli Hinde ya ce, “Hinde Hajjaju ta ce a kawo muku abinci ku ci da baƙuwa”. Washe haƙora ta yi ta ce “Godiya muke”. Maccen da ta riƙo ƙaton tire ɗin ta ajiye tana musu sannu sannan suka fice, suka bar su yanda zasu sake sosai. Kamar jira Hinde take ta fara ɓa Nafi bala'i kamar zata cinye ta. “Nafi kina son ja muna asara ko? wai wacce kalar ƙwa-ƙwalwa ce da ke? Mts! sai da na roƙo ki, ki natsu amma kina abubuwa kamar wacce ta ga Namun dawa, wallahi idan ba ki saki jikinki ba kika yi duk abin da aka saka ki ba ke zaki sha wahalar banza, Komai fa dan ke nake yi...” Sai kuma ta sassauta murya ta ci gaba da mata faɗan, “Ki yi taka tsan-tsan fa, Hajjaju da kike gani mutuniyar arziƙi ce me ƙwatowa mata 'yancinsu, me share wa kowace macce kukanta da Marayu, idan kika fahimce ta zaki ji daɗi amma idan kika ce haka zaki ci gaba da abubuwa wahala zaki sha, Dan Allah Nafi ki cire tsoro da ƙauyanci. Yanzu mu ci abinci zan sake miki bayani anjima.” Ɗaga kai kwai Nafi ta yi jiki a sanyaye. Hinde ce ta sake faɗin, “Babu Wanda zai cutar da ke a nan ko dukanki, kar ki saka shakku a ranki ba wata matsala sai alheri dan suma mutane ne kamar kowa da kika sani”. Sai lokacin hankalinta ya ɗan kwanta, ta ce “To zan kiyaye”. Zamowa ƙasa Hinde ta yi, ita ma Nafi haka suka buɗe Abincin da aka kawo Soyayyun kaji ne daƙwa-daƙwa sai Maiƙon suke yi, sai kuma Furar Maidabino da aka ajiye ƙasa da cups, da kuma tuwon Masara miyar ɗanyar kuɓewar da ta ji kifi da Ganda. Sai kuma Ruwa sha. Cikin Nafi ne ya hargitsa ta manta wane yanayi take ciki, Yawunta ya tsinke burinta kawai ta kai wa bakinta. Fidda plates da Chokulan Hinde ta yi, ta sa hannu ita ma Nafin haka suka fara kai wa bakunansu, Wani ɗanɗano ne na zallar madarar daɗi ya ziyarci Nafi har cikin kwanyarta, ta tauna kazar da ke da ɗan yaji ga ta yi luɓus ta kuma ji suyar mutunci,Ita kanta bata san lokacin da ta gyara zama ba ta duma hannayenta duka biyun cikin abincin ta ci gaba da nausa ma cikinta, Cikin 'yan mintuna suka gama fatattakar naman suka dawo kan tuwon shima, Nafi ta ji daɗi zai zauta ta, ta ce “Ruwa”. tana suɗe yatsunta hada hannuwanta. Furar Hinde ta zuba musu a cup sannan ta buɗe mata Bottle water ta ajiye mata. Ta ɗauki Furar ta kai baki ta sha ta ji zumar daɗi da garɗi, ta fara santi tana faɗin, “Hinde dama haka ake a binni jandi``ilso (Dad’n duniya na nan)”. Suɗe yatsu ta yi ta bata amsa ita ma daɗin girkin na ɗibarta“Hum! ai baki ji komi ba, ni kaina duk daɗewata ko da yaushe aka min haɗin ruɗewa nake saboda komi na Birni ya yi zarra.” Ta kasa bata amsa saboda

Please Login or Register in order to submit comment