Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[11/15, 7:59 PM] KS.: *https://whatsapp.com/channel/0029VaErT9RCsU9JpePsjA0Y*
*@K_SHITU’S NOBLE WORLD CHANNEL*
*ArewaBooks@Kshitu.*
Copyright (c)K_shitu
Khadija Muhammad shitu
Reposted.

*ZUCIYA...!!*
(Qalb)

SHAFI NA ƊAYA.
*(1).*
Wani mahaukacin burki ya taka, har sai da gabanta ya faɗi, ta ɗago tana kallon sa, hankalinta a tashe, shi ma kallonta ya yi cikin wani irin yanayi. Cikin jin tsoro ta ce, “Hamma kana lafiya?” lumshe idanuwansa ya yi ya ce, “Akwai matsala Fulani..” A ruɗe ta ce, “Matsala kuma hamma?” Bata ankara ba ta ga hawaye na zuba daga idanunsa. A karo na farko ya ruƙo hannayenta ya ƙura mata idanuwa yana sauke ajiyar zuciya. Hankalinta ya kai ƙololuwar tashi ta shiga jero masa tambayoyi lokaci ɗaya. “Hamma meke faruwa ka faɗa min kar zuciyata ta fashe..” Murmushi ya yi me kyau, sannan ya sake ta ya jingina da kujera, ya lumshe idanuwa kamar ba zai yi magana ba cikin gur'batacciyar hausarsa ya ce, “Fulani zan mutu ne” Duk da ta san baya magana me tsayi da hayaniya amma ta rikice ta fashe da kuka tana faɗin “Hamma kar ka mutu do Allah idan ka mutu nima mutuwa zan yi” wani irin tausayinta ne ya kama shi ya rasa me zai yi, cikin murmushinsa ya ce, “Fulani me yasa kike min ihu a kunne? Ke matsoraci ce” Shesshekar kukata ci gaba da yi, ya sanya hannayensa yana goge mata fuska, sannan ya ɗauko ruwa masu sanyi ya bata ta sha ta ci gaba da ajiyar zuciya, sannan ya tada motar suka ci gaba da tafiya. Bai yi tafiya me nisa ba ya ƙaraso bayan lambun da yake aje ta, ta ɗauki ƙwaryarta duk jikinta babu kuzari har ta buɗe motar zata fita ya kira sunanta a hankali, “Nafisa” cikin jin kunya ta amsa, “Hamma”. Wani zobe ya ciro daga cikin aljihunsa ya mi‘ko mata ya ce, “You can leave, ki kula zoben ki boye”. Jinjina kanta ta yi, bata ce komai ba dan idan ta yi magana kuka zai iya ƙwace mata ta rufe masa motar, tana gani ya bar gurin. Ita ma cikin rashin kuzari ta juya ta ci gaba da tafiya haka nan take jin zuciyarta babu daɗi, har ta fara wuce bukkokin wasu fulani, tun kafin ta iso gidan ƙirjinta ke dukan tara-tara gabanta sai faɗuwa yake, tana ƙarasowa gidan ta yi sallama a hankali ta ɗaga asaberin da yake matsayin ƙofa ta shigo ciki.
Cikin sauri wata mata ta fito daga wata bukka, tana faɗin, “Sannunki da gantali” ta sunkuyar da kanta Ƙasa, cikin harshen fillanci ta gaida ta, maimakon ta amsa sai cewa ta yi, “Ina kuɗina kin siyar duka?” ɗaga kai ta yi, ta kwanto kudi daga zaninta ta mika mata. shewa ta yi, cike da masifa ta ce, “Nafi mutuwa kake so kenan, yanzu Nafi gidan uwarwa ka sami kuɗi sabo haka iye? Nafi anya ba maganar Jummai gaskiya ba ne ka faɗa min kafin na kashe ka.” Nafi ta tsorata dan ta san zalunci irin na Inna Hure ta ce, “Na rantse inna shinikin nono da fura ne kawai”. Ƙwafa kawai inna ta yi, bata ce komai ba ta nuna mata wanke-wanken da zata yi ta koma ɗakinta. Sai da duhu ya fara sannan ta gama wanke-wanken uwayen kwanonin, tana gamawa ko hutawa bata yi ba, inna hure ta miƙo mata tuwo da miyar da take talla, ta ɗauka ta fice tana hawaye. Bayanta sai ciwo yake yi saboda tsananin gajiya tun asuba idan ta tashi bata komawa sai dare ya raba.Haka ta iso inda take tsayawa siyar da tuwon, sai da dare ya raba sannan ta komo gida da sallamarta. Muryar Inna hure ta ji tana masifa, “Yo Malam idan ban tura ta talla ba ta samo kuɗi ba da me zan cida ka kai da ita? Ashe munafurcin da take kawo ma kenan tambadadden yarinya, Yauwa ga ta nan ma munafuka kika saya kina kallon mutane zo nan!” Hankali Tashe Nafi ta fara bata haƙuri cikin hausarta da bata fita sosai, “Inna na rantse ban faɗa komai komai ba”. Cikin fushi ta iso kusa da Nafi ta riƙe ƙugu tana faɗin, “Dan uwarki ni ke karya ko??Taimako ɗaya zan miki na ƙyale ki in kin sayar min da tuwona kin ƙaro da kuɗi, in ba haka ba....” Tana jim furucinta jikinta ya ƙara yin sanyi, ta san dole saita dake ta, matsalarta ɗaya cinyoyinta da har yanzu basu warke ba tun dukan da ta yi mata. Dukan da ta ji ne ya sa ta dawo duniyar mutane, cikin daka tsawa ta ce, “Karka bari na sake maimaita maka Nafi”. Cikin shesshekar kuka take fad'in, “Inna kiyi haƙuri, ba kashuwa tuwon bai kare ba, Kuma Baffa ya hana na kai dare”. Finciko wuyan Nafi ta yi cikin rashin imani ta janyo ta har gaban Malam Iro ta fara dukanta tana haɗa mata da zagiggika iri-iri da gori, “Dan uwarki ba zaki kashe min ciniki ba saboda nakasasshen ubanki Wanda zuciyarshi ta lalace, kema kina son zama kamar uwarki kenan, saina miki dukan yawon karuwancin da kike yi yau, an faɗa miki hauka nake bana gane inda kike sato kuɗin ba? da karuwancin da kike yi”. Saida ta jigatar da ita da ita sosai sannan ta ƙyale ta bayan ta ƙwaƙule kuɗaɗen da Nafin ta ɓoye cikin jikinta. Tun Nafin na kuka da ƙarfi har muryarta ta disashe, duk da irin wulaƙancin da Inna hure take yi Baffa be ce komai ba kuma yana nan zaune. Saidaata gaji da mita da masifar dan kanta sannan ta shige Bukkarta ta rufo ta bar Baffa da Nafi a waje. Da ƙyar Nafi ta miƙe jikinta babu kuzari sai ciwo kanta ke yi, ta ɗauko ragowar Tuwon ta ajiye, sannan ta gyarawa Baffa Shimfiɗarsa, ta yi masa jagora zuwa makwancinsa, Sannan ta dawo bakin 'yar bukkarta marar kyan gani ga ƙwari da datti ciki, haka nan ta kwanta kan wani yagaggen buhu. Ta daɗe tana kuka tana kiran sunan Babarta sannan barci ya ɗauke ta.....
#ZUCIYA
#K_SHITU
#REPOSTED
09117440993
09060584800
[11/15, 8:32 PM] KS.: *@K_shitu’s Noble World Channel.*
ArewaBooks@Kshitu


*ZUCIYA...!!*
(Qalb)

SHAFI NA BIYU.
*(2).*
Tana tsaka da wahalallen barcin da ya ɗauke ta ta ji saukar ruwa a jikinta. Cikin gigita ta farka tana sauke numfashi da ƙyar. Muryar Inna Hure ta ji tana faɗin, “Zaki tashi ne ko kuwa?” Ai bata San lokacin da ta wartsake ba, Ta tashi zaune tana hamma idanuwanta Jajir gwanin ban tausayi. Ƙwafa ta yi, ba tare da ta ce komai ba ta fice. Duk da har lokacin barci be bar idanunta ba haka ta miƙe da ƙyar jikinta sai ciwo yake yi kanta sai sarawa yake, ga mugun sanyin da ke ratsa ta, Ta fito tsakar gidan ɗan ƙarami, ta fara wanke-wanke, sannan ta fara ƙoƙarin haɗa wuta, lokaci ɗaya fuskarta ta yi face-face ta yi jajir, idanuwanta sai zubar da ruwan hawaye suke yi saboda hayaƙi, da ƙyar ta samu wutar ta kama saboda itacen ɗanyu ne. Ta ɗaura Ruwan Zafi sannan ta ɗauki tsintsiya ta fara sharar gidan, sai da ta share tsaf, ta dama koko, bata ɓata lokaci ba ta sauke Ruwan ta ɗumama tuwo, saida gari ya fara haske sannan ta kammala, ta ɗauki tuwo da kokon ta fito waje. Yanayin tafiyarta kaɗai zai iya tabbatar da bata da zubin cikkakkun mutane, tafiyar a lanƙwashe take yinta. Ɗai-ɗaikun mutanen da suka fara fitowa ne suka fara gulmarta, da chanza hanya idan sun ganta. Har wajen ƙarfe tara na safiya babu wanda ya siyi komai daga gurinta, kuma shiru-shiru Hammanta bai zo, damuwa ta ishe ta, jiki ba kuzari ta miƙe da ƙyar ta dawo cikin gidan. Sallama ta yi ta shiga gidan cikin shaƙaƙƙiyar muryarta, maimakon amsa sai wani mugun zagi da Hassatu ɗiyar Inna hure ta yanko da harshen fulatanci. Kamar tana jira ta fito daga Kewaye tana faɗin, “Ke da wa hassatu?” Zubda miyan barcin da ya tarar mata a baki ta yi, ta ce “Inna wai ke baki ga Nafi ba?” cikin sauri ta kalla inda Nafi take, bakinta har rawa yake ta ce, “Zancen banza kai Nafi! ni ba zan ɗauki iskancinka ba, bana tsoronka ni ba irin mutanen rugar nan bane, ko ba maye ba? babu ruwana da wani iskanci, ka kashe mana kasuwa hassatu ta dena sana'ar kai da ka fara kai ma kana son denawa to me kake nufi?” Jikin Nafi na rawa ta ce, “Na rantse inna mutanen rugar nan basa son siyan komai daga..” Hassatu bata bari ta ƙarasa faɗar abinda take son faɗa ba ta katse ta da faɗin, “Ƙarya kike munafuka, wallahi kece ke yin maitar har aka dena siya.” Ta buɗe baki zata yi magana cikin hanzari Inna hure ta hankaɗa ta, tana faɗin, “Duk inda zaki je ki tafi ka siyar da shi, ko yau na kashe ki Nafi” jin haka yasa Nafi ficewa cike da tsoro. Babban tashin Hankalinta yau da Hammanta bai zo ba, bai turo a kira ta ba. Ta fara tafiya tana hawaye ga rana ga yunwa da ke cinta, duk inda ta wuce sai an yi zunɗenta an aibanta ta. Ta je duk inda ta san suna haɗuwa amma bata ganshi ba. Lokacin ne ta fara jin jiri-jiri, ta nemi wata bishiya ta zauna ta ajiye tuwon da kokon da ƙudaje suka daddaɓe ba kyan gani. Ta daɗe nan zaune cikinta sai karta yake tsabar yunwa, ganin bata da mafita ya sanya ta tashi ta fara tafiya. Sai da rana ta buɗe sosai sannan ta iso babbar kasuwarsu, ta fara yawo, haka ta ƙarashe yawonta bata siyar da komai ba, yunwa ta jigatar da ita ta zauna ta ci tuwon sannan ta miƙe, ta ci gaba da tafiya. Wata Hamshaƙiyar mata Kyakkyawa ce ta zo wuce wa, ta sha ado me kyau, kwata-kwata bata yi kama da 'yan Rugar ba, da ganinta hutu ya zauna mata da arziƙi hanunta riƙe da jaka me kyau. Suka yi ido huɗu da Nafi, Har matar ta tafi sai kuma ta dawo Ta kalli Nafi a karo na biyu ta ce, “Y’an'mata dan Allah tsaya mana” Tsayawa Nafi ta yi, tana kallonta ba tare da ta ce komai ba, matar Ce ta sake fadin “Dan Allah Ina so ki kwatanta mini Inda mazaunin me garinku yake”. Jim ta yi, tana tunani cikin jin tsoro ta ce, “Ban san ina yake ba, ka tambayi wasu”. Tana gama faɗin haka ta juya da sauri zata tafi, matar ta ruk'o hannunta tana murmushi ta ce, “Kuma baki faɗa min sunanki ba?” kamar ba zata amsa ta ba, ta zame hannunta daga nata ta ce, “Nafi”. “Nafi!” matar ta maimata sunan a hankali, kafin ta yi wani yunkuri Nafi ta bar gurin, ta yi murmushi kawai ta juya ta bar gun itama. Tun da Nafi ta taho take jinta wani iri ta kasa fasalta yanayin da take ciki. Tana Tsallakowa Cikin Rukunin bukokinsu, wani Ƙaramin Yaro ya rugo da gudu, Karon da za suyi da Nafi Yaron ya faɗi itama haka Tuwonta da Kokon duk suka zube, Rintse idanuwanta ta yi, da ƙarfin cikin ruɗu, ta fara ƙoƙarin miƙewa. Ihun wata Macce ta ji tana faɗin, “Taimako! Taimako!! Mayya zata kashe min yarona” Kafin wani Abu matan da ke kusa wad'anda suka ji suka fara firfitowa. Ƙarasowa Uwar yaron ta yi, A kiɗime tana kiran sunan shi, amma sam babu alamun ma yana da rai sai jinin da ta gani yana fita ta hanncinsa. Ai Nafi na ganin Matar ta fara ihu da sambatu, matan kuma suna nufo ta, ta kwasa da wani irin mugun gudu. Suna ganin ta gudu suka dawo, aka fara ba wa Uwar Yaron baki, da ƙyar aka samu ta amince aka Nufi Gun Mai magani da Yaron. Tun a kallo ɗaya da me maganin ya yi wa yaron ya ce musu, Mayya ta yi abinda ta saba, yaro ya mutu.....
#ZUCIYA
#K_SHITU
#Paid book 200
09117440993.
[11/19, 7:21 PM] KS.: *@K_shitu’s Noble World Channel*
ArewaBooks@Kshitu.

*ZUCIYA...!!*
(Qalb)

SHAFI NA UKU.
*(3).*
Kafin Faɗuwar Rana maganar ta game Rugar Fulanin da suke Rayuwa a rugar duk sun san abinda ke faruwa. Hayaniya Ce kawai ke tashi ƙofar gidan, matasan Fulanin Maza faɗi suke, A fito da Nafi su ƙona ta. Inna Hure ce ta leƙo tana masifa, “Ku je Ku neme ta wani wuri bubu ita nan”. Ɗaya daga cikin matasan ya ce “A fito mana da ita ko mu shige mu duba da kanmu” Rigima Ce ta ‘barke tsakanin samarin da inna hure, ta kasa ta tsare ba wanda zai shiga, suna tsaka da rigima Uban yaron ya bangaje Inna hure ya shige gidan suma sauran matasan suka shigo, kaf sun duba ko'ina amma babu Nafi babu Dalilinta. Nan fa suka fara masifa suna faɗin an san inda aka ɓoye ta, inna hure ba haƙuri ta biye musu. Kamar abun arziƙi duka suka fice daga gidan. Inna Hure ta ci gaba da masifa faɗi take yi, Yau sai Nafi ta bar mata gidanta. Ba a wani jima ba gabannin Magrib sai ga su dawo da kalanzir me uban yawa, Suka fara watsawa zasu ƙona gidan. Hankalin Inna Hure da hassatu ya yi mugun tash ganin da gaske ƙona gidan za ayi. Ana cikin wannan yanayin sai ga Malam Iro mahaifin Nafi Da ƙyar ya kawo ƙofar gidan ya shigo kasancewar baya gani sosai bai zama makaho ba amma baya gani sosai. Haƙuri ya fara ba su, cikin tattausan lafazi, da ƙyar ya shawo kan matsalar suka fice zuwa Fada. Maigari ne ya soma magana, “Malam iro ka ji abinda suka fada ko? A karo na ba adadi yarinyar nan tana ta kashe fulanin rugar nan da mutanen gari amma ka kasa daukar mataki, a wannan karon gaskiya ka yi mata gargad'i na ƙarshe, mun Baku dama da yawa, Idan har ta sake aikata wannan laifin na kisan kai zamu Kore ta daga rugar nan gabad'aya ba zata sake dawo mana ba, wannan shine adalcin da zamu iya yi maka.” Amsawa ya yi ya ce, “Hakan ba zata sake faruwa ba”. Daga haka kowa ya kama gabansa duk da mahaifan yaron da sauran fulanin dam basu ji daɗin hukuncin me gari ba, hasalima Ransu ya sake ɓaci ne kawai, sun gaji da matsalar Nafi Bafullatanar Mayyar da ke kashe musu mutane amma an kasa ɗaukar tsattsauran mataki tamakar ana tsoronta. Ko da fulanin na tsoronta amma abun ya ishe su har sun fara bayyana fushinsu...Shesshekar kukanta ne ke tashi kawai cikin jejin Fuskarta ta yi, Jajir ta jigata sosai gabaɗaya ta gaji da Rayuwa, sai yaushe ne za a daina mata Kallon Mayya, yanzu ana nufin ita ce ta kashe Idi wace kalar mummunar ƙaddara ke bibiyar Rayuwarta haka? Tambayoyin da suka addabi zuciyarta kenan a kowane lokaci, musamman ma idan wani ya mutu aka ɗaura alhakin kanta. Ɗago kanta ta yi, tana kallon hannayenta da suke lafce da jini, ta sake mayar da kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka me taɓa zuciya, Tun tana kukan yana fitowa har muryarta ta disashe, ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya. Dariya ta fara ji me ban tsoro na tashi cikin dajin, lokaci ɗaya hankalinta ya tashi, wani mugun tsoro ya shige ta, ta ƙanƙame jikinta. Sunanta ta ji wata murya na kira da ƙarfi kamar kunnenta zai fashe, ta miƙe jikinta na kyarma ta fara gudu, da ta kusa fita da dajin sai a maido ta inda take. Cikin tsananin Ruɗu ta miƙe zata sake guduwa, ta ji wani irin abu, kan ƙafarta, Kallon da zata yi taga wani danƙareren Maciji Fari tas, yana nannaɗe ta, Irin yanda ta gigita ya sanya komai nata ya tsaya ta sume, macijin kuma ya nannaɗe ta har wuya.....
#Zuciya
#K_shitu
09117440993
Follow my Accounts please🙌🌝
*AREWABOOKS: Kshitu*
*WATTPAD Kshitu*

*Share, React, Vote nd Comment Please❤️.*
[11/19, 7:21 PM] KS.: *ArewaBooks@Kshitu*
*Wattpad@Kshitu*

*ZUCIYA...!!*
(Qalb)

SHAFI NA HUƊU.
*(4).*
Ciki-ciki ya yi sallama ya shigo ɗakin da suke, Ammi ce ta amsa masa tana murmushi, sai da ya zauna kusa da ita sannan ya ce, “Ammi zan koma masarauta”. Wata irin ƙwarewa ta yi, cikin sarƙewar murya ta ce, “Saboda me?” kamar ba zai yi magana ba ya yi shiru, sai da ya fesar da iskar bakinsa sannan ya ce “Haka”. Jinjina kai ta yi cikin damuwa ta ce, “To Allah ya tsare ka Dr ka kula da kanka sosai, bana son neman magana” jinjina kansa ya yi, Budurwar da ke kwance ce ta turɓune fuska tana faɗin, “Yah Please kar ka tafi” Hararta ya yi, ya fice be ce komai ba. Turo baki ta yi ta ce, “Ammi Please ki ce kar ya tafi” Ajiye Cup ɗin hannunta ta yi tana faɗin, “Auta kin cika rigima” Ta miƙe ta shige toilet ta bar ta tana ta mita. Bai ɓata lokaci ba ya fito hannunsa ɗaya riƙe da Mukullin mota ɗaya, ɗayan kuma ya kara waya a kunnensa, ya zauna bisa ɗaya daga cikin kujerun Parlourn, yana magana “Idan ka ɓata lokaci ba zaka same ni ba” yana gama faɗar haka ya kashe wayar. Bai fi 10mnts da gama wayar ba aka yi Knocking ɗin ƙofar Parlourn, “Yes,” kawai ya faɗa a daƙile Ya lumshe idanuwansa. Abdul da ke shigo ya fasa ihu yana faɗin, “Dan Allah Dr kai ne da gaske? Woaw wallahi ka yi kyau yau zaka haukata Babies, Please bari na maka photo ko guda biyu” Taɓe baki ya yi, a hankali kuma ya ce “Kar ka fasa min kunne da ihu tashi” Ɗaukar Apple ɗin da ke gaban Dr ya yi, sannan Suka jero, a tare suka fito har suka iso harabar bai sake magana ba, Abdul sai 'yan surutai yake shi ɗaya dan Ya yi amma ya yi banza ya ƙyale shi. Parking Lot suka ƙaraso ya miƙa wa Abdul key ɗin ba tare da ya yi magana ba, Buɗe wata Farar mota ƙarama suka yi me zubin machine suka shiga Abdul ya ja su. Har suka miƙo titi Bai yi magana ba, ƙaramin tsaki Abdul ya ja, ya ce “Dr A ni fa ba zan iya zama haka ban yi magana ba, a to kar ka ga laifina idan na yo ni kaɗai tun da kai bakinka ɗinkakke ne, Shi mutum ace kullum magana ta fi komi wahala gurinshi ba fara'a ba komi maganar ma babu haba mana” Still bai tanka masa ba, ya ƙulu ya sake faɗin, “Kai fa baka san daɗin magana ba wallahi...” zai ci gaba da surutu Dr ya yi tagumi da dukkan hannayensa ya zubo masa idanu “Surutunka ya yi yawa ka nemi magani” “Wane magana kenen?” ya tambaye shi cikin rainin wayo a hankali ya dago yatsansa ya nuna masa ya ce a hankali “Double two fucks”. Sheƙewa da dariya ya yi, ya kunna waƙa ya ci gaba da bi yana tuƙin. Har suka shigo babban gatre ɗin Ɓangaren Masarautar. Ɓangaren Ƙarshe da ya kasance na Dr suka nufa, ya yi Parking suka fito suka nufi ƙofar main Parlour, ya latsa Security Lock ɗin suka shige. Sai da suka nutsu sannan Abdul ya gyara zama ya fuskance sa sosai ya ce, “Ka ce kana son mu yi magana me muhimmanci ina sauraronka”. Ajiye wayar da ke hannunsa ya yi ya ce, “Good! Abdul kai ne kaɗai zan iya faɗawa mstsalana, bana son aikin da Akarsh ya ce dole sai an yi, Ammi zata shiga damuwa fiye da kowa and The king too...” sai da ya dafe saitin zuciyarsa ya numfasa, sannan ya ci gaba da magana, Abdul bana jin daɗin komai Please...take care of Ammi nd Imaan nd Fula..,” sai kuma ya yi shiru ya muryarsa ta sarƙe, `Ba a bina bashi sai dai company duk masu bashina na yafe musu, akwai kuɗo cikin bank ɗina na U.b.a, zamu fita da wuri gobe”. Sae Numfashi saboda magana me tsawon da ya yi, Cikin fargaba Abdul ya ce “Dole ne fa ayi maka aikin, sannan waɗannan maganganun fa ka ruɗar da ni, ka ce Fula waye haka??” ya goge zufa da hancky ɗinsa duk da Acn dake ɗakin. “Dan Allah ka min magana A ina cikin rud'u”. Sai ya yi wani tsadadden murmushi Wanda ya sake sanyaya jikin Abdul sannan ya ce a hankali, “Just Forget about it” “Please Ahmaad ina bukatar karin haske” Sai da ya ja numfashi sannan ya ce “Ohh Abdul! kana son sani surutu anyhow na gaji gobe zamu yi magana ko”. Ba haka Abdul ya so ba amma ya yi shiru yana ta saƙe-saƙe a ransa ga kuma tausayin Ahmad da ya cika zuciyarsa...
Kwance take ƙasa cikin ciyayi, sai a hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanuwanta saboda zafin rana da kuma yanda Ranar ta dalle ta sosai. Buɗe idanuwanta ta yi waɗanɗa suka mata nauyi sosai, ko gama ware su bata yi ba ta rufe saboda tsananin hasken ranar. Saida ta jima a haka da ƙyar ta miƙe zaune ta matsa gefe kaɗan sannan ta buɗe idanuwanta sosai. Wata irin karta

Please Login or Register in order to submit comment