Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsere. Da k'yar ya samu harshensa, yana mai jin d'aci a ransa.

"Ehmm, a cikin garin Maiduguri wannan abu ya afku, na fito daga gida kenan na iso anguwar Gwange. Ina sanye da jakar baya bak'i cike da littafan makaranta kasancewar ni d'an makaranta ne, fitowar ma da nayi na fito ne dan kammala aikin gida da aka bani.

Lokaci guda naji k'arar harbi daf dani, ga motar sojoji d'aya da ke fake, ban kula da inda harbin ke fitowa ba, kamar yanda sauran mutane ke gudun tsira nima haka na yi ba tare da nasan inda na nufa ba.

Inda mutane suka nufa nake bi, dan anguwar Gwange anguwa ne da ke rud'ani, k'arar harbi tun ina iya k'idaya nawa naji har ya zama na kid'ime na rasa duniyar da nake ciki.

Lungu na samu na fake, ina lek'en inda ya dace insa k'afa in tsere zuwa ga mahaifiyata.

Mintuna biyar nayi ina lek'e, har a lokacin ina sak'ale da jakan bayana. Jin k'arar harbin ya lafa, sahun mutane ya kau, naji a raina wannan lokacin ya dace in fice daga wannan anguwa, na fasa yin wannan assignment d'in har sai lokacin da gari yayi lafiya.

Cikin sand'a nake taku, ina rik'e da jakana dan in gudu ya kama kar ya fad'i in rasa muhimman littafaina.

Ina tsaka da sassarfa naji dirin motar sojoji, kafin in ankara sun zo daf dani ba halin gudu.

Zuciyana ya tsinke, na tsaya cak had'e da d'aga hannuna dan nuni da na karaya, ba dan komai ba sai don in tabbatar musu cewa babu ruwana cikin abunda ya faru.

Ban samu damar waigowa ba, naji an buge kaina da wani abu mai k'arfi, ina da tabbacin bakin bindiga ne, hankalina bai gama gushewa ba naji furucin d'aya daga cikinsu.

"Shine! Banza! Baka ga gemunsa ba!"

Ban sake jin komai ba, sai lokacin da na farka na ganni cikin wasu samari sa'annina, duk sun galabaita.

Wasu na kwance cikin rashin kuzari, wasu na zaune sun d'aura kansu a k'afafunsu, wasu kuwa na rasa gane suna raye ne ko suna mace.

Bansan inda nake ba, sai lokacin da aka fito damu mu goma sha-biyar, aka shigar damu wani d'aki mai matuk'ar duhu, aka hau mu da duka ta ko ina.

Ana mana tambayoyin da har ga Allah ban san amsoshinsu ba.

"Wa ya turo mu? Ina bindigoginmu? Su waye ke d'aukar nauyinmu"

Da sauran tambayoyin masu yawa".

Hawayen idanunsa ya share, zuciyarsa ya karye, yana tuno azabar da ya sha a wannan lokaci, yana ganin duk wani abunda ya wakana cikin idanunsa.

Daurewa yayi, ya tsayar da k'wallarsa, ya d'ago idanunsa ya kalli Alk'alin da ya zuba masa ido yana jin k'arashen labarinsa.

"Tun muna iya amsa su akan bamu san komai ba, har wasu daga cikinmu suka kasa magana, suka fara amsa laifin da ba nasu ba dan azabar ta yi yawa.

Mu hud'u ne muka k'i amsar wannan laifi, hakan yasa suka cigaba da gallaza mana azaba, a cewar su mun zama rik'akk'u masu taurin kai, shiyasa muka k'i karb'an laifinmu.

Wasa-wasa sai da muka yi sati a wannan wuri, wanda d'aya daga cikinmu ya tabbatar mana barikin soja ne.

Mahaifiyata da 'yan uwana sunyi iya k'ok'arinsu dan kub'utar dani daga hannunsu, amma abun ya ci tura, sunce ni d'an ta'adda ne, ina d'aya daga cikin mutanen da suka kai wa sojoji hari a wannan rana, wanda yayi sanadiyyar mutuwar sojoji biyu.

Iya abunda na sani kenan".

Idanunsa take kallo, nata idanun na kawo ruwa kaman yanda nashi ya kawo.

Waigowa ta yi dan kada ta zube a gaban kotu tana sharara kuka a matsayinta na lauya.

"Ya mai shari'a! Wad'an nan sune bayanan Hamza, shin da me ake tuhumarsa da ta'addanci bayan ganinsa kawai aka yi yana gudun ceton ransa? Shin haka kawai aka bawa hukuma daman cafke mutum ta gallaza masa ba tare da dalili ba?

Ina rok'on kotu mai daraja, da ta duba halin da aka sa wannan bawan Allah, ba tare da laifin komai ba aka k'wace masa 'yancinsa na d'an Adam, a bi masa hakk'insa yayi cikakken rayuwa kamar yanda ko wani d'an k'asa yake da wannan 'yancin. Nagode"

Tana gama fad'in haka ta koma mazauninta, tana kallon yanayin Anthony da ya had'e fuska.

Wasai ta ji zuciyarta, duk da ta san baza ta samu damar kub'utar da Hamza cikin wannan sauk'in ba.
[8/15, 5:15 PM] BEBE'ARTH😘: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_💋


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE'ATU SK MASHI


_An karb'o daga Nana Aisha, Allah ya k'ara yarda a gareta, tace._
" _Wani mutum ya saki matarsa saki uku, sai ta auri wani, sannan ya saketa kafin ya tara da ita, sai mijinta na farko ya dawo ya aureta._Sai ta tambayi Manzon Allah (S.A.W) akan haka, sai yace._" " _bai halatta ba, har sai na biyun ya d'and'ani zumarta kamar yadda na farkon ya d'and'ana."_( *Musulumu ne ya rawaito*)


( *15*)

Cikin sauri ta kammala shirinta, dukda simple make up tayi ba k'aramin kyau tayi ba, Jakarta ta d'auka ta rataya ta fita sai zuba k'amshi take mai k'ayatarwa.
Gurin motarta ta nufa fara k'al sai shek'i take da d'aukar ido, sai da ta shiga cikin motar ta zauna sai ta fara tunanin ina ya kamata ta fara zuwa, a take zuciyarta ta sanar da ita gurin BR Mak'ari, don haka ba wani kwane-kwane taja motarta ta nufu Akcils don a yanzu dai tasan anan zata sameshi.

Tana shiga makarantar ofis d'in MB ta fara zuwa, yana dariya yana komai ya tareta, ita kuma ta d'aure fuska.

"Yau kuma me ya samu Jiddah sarkin fara'a? gaskiya kinfi kyau da fara'a jidda na"

Mur ta kuma sha, kana tace. "Kaban mamaki ne MB, kasan halin BA ciki dabai ko k'waro bazai iya kashewa ba, amma kabi ka hak'ik'ance shine yayi kisan, akan ma me ka k'arb'i k'aran?" ta d'an fad'a da d'aga murya.

Shima cikin d'aga murya yace "A kan kud'i na karb'a, kinsan ni da kud'i jiddah, ko a gabana akayi kisa wanda yayi kisan ya d'auki kud'i yaban yace na tsaya masa sai na tsaya masa, kuma nine nan zanyi nasara." yakai k'arshen maganar gami da dukan bencin gabansa.

Itama a zafafe ta daki bencin "Haka kace ko? to mu zuba." Bata saurari me zaice ba tai ficewarta.


Cike da damuwa ta tadda Mak'ari, yana ganinta ya saki kyakkyawan murmushi. "Yaushe kika dawo k'asar? tun last weak naje nemanki bagauda aka cemun kin tafiya"

Murmushi tayi, kana tace. "Jiyannan na dawo wlh, nazo kuma na tadda abinda ya d'agan hankali."

"Eh wlh, akan case d'inma nake ta nemanki, tafiya ce ta kamani tun last weak amma haka na hak'ura saboda case d'in, yanzu ma tunanin wanda zan mik'awa case d'in nake sai gaki kuma kinzo."

"Nima dai akan zancen nazo maka, na kuma ji ta ya zamu b'ullowa al'amarin"

"Yanzu kuma ai saidai nabar case d'in a hannunki, sbd gobe ne jirginmu zai d'aga, kiyi duk wani k'ok'ari da zaki kiga kin fitar da BA daga wannan sark'ak'iya da ya shiga, kar ki bari a kuma d'aga k'ara, ki had'a duk wani shaidunki kafin ranar komawa kotu, Allah Ubangiji ya dafa mana."

"Amin BR, insha Allah ba zamu ji kunya ba mu zamuyi nasara, na kuma yi matuk'ar far in ciki da case d'innan ya dawo hannu na ko dan na nuna wa MB nasara a gurin Allah take, kuma insha Allah ba za'a d'aga shari'ar ba, tunda muna da sauran lokaci zanyi duk wani k'ok'ari naga na had'a shaiduna gaba d'aya kafin lokacin."

"Toh Allah ya taimaka mana BR Jiddah."

"Amin ya Allah."

Anan dai BR Mak'ari ya mik'a mata komai, harda wasu bayanai da ya fara samowa, tai masa sallama ta tafi.

Daga nan police station d'in da Almash yake ta nufa, tana zuwa ba wani jan lokaci aka fito mata dashi, kallonshi take tsagwaran k'aunarshi na ninkuwa a zuciyarta, hawayen tausayinsa ne ya fara sintiri a kumatun ta.

"Nasan Almash d'ina bazai iya kashe mutum ba, nasan Almash d'ina da tausayi ko wani can bazai iya kashewa ba bare d'an uwansa na jini, nai maka alk'awarin a ranar da aka koma kotu, a ranar kotu zata wankeka daga zargin da akema"

Murmushi me kama da yak'e yayi, "dama rabuwa kikayi dani BR, bani da wata mafita, mahaifina ya amince ni na kasheshi, Rabee'ah kallon tuhuma take mun, matata da na bata dukkanin wata yarda ta itace tamun wannan k'azafin, mutum d'aya ne nake jin dad'inshi, Abbana shi kad'ai nake ganin tausayina a idonshi, da Umma na nan itama na tabbata baza ta amince ni na kashe shiba, ina son d'an uwana bani da kamar sa, zan iya yin komai a kansa taya za'ayi na iya kasheshi da wannan hannun? ki gayamun BR" yakai k'arshen maganar yana kuka mai cin rai.

Tausayinshi gami da soyayyarshi su suke azalzalar jiddah, ji take kamar ta rungumoshi jikinta ta rarra sheshi amma ba damar hakan, k'arfafa zuciyarta tayi gurin lalla shin shi. "Dukkan tsanani yana tare da sauk'i, kuma ko wani bawa sai Allah ya jarabce shi, don haka kaci gaba da hak'uri, insha Allah komai yazo k'arshe kuma......." Bata fad'i k'arshen maganarta ba ta dalilin hankad'a k'eyar Almash zuwa ciki. "Hajiya lokacin ki ya cika." Taji muryar d'an sandan yana gaya mata.


Tana sharar hawaye ta fito daga police station d'in, tana shiga cikin motar ta tadda miss call d'in daddynta, batai k'asa a guiwa ba ta kirashi.

"Hello,shalelena ina kika shiga ne, yau kin manta dani ko kizo mu gaisa kikai ficewar ki?"

"Afuwan my DAD, wlh Dad ina solving d'in wani case ne that is way, i'm sorry kaina bisa wuya"

"Lallai shalele wannan case d'in yana da muhimmanci, tunda aka fita ba'a gaisa da daddy ba, ai kinsan bana fushi da shalele na, afuwa tuni nayi miki ita, amma kizo gida yanzu ina son ganinki."

"Thank u cweat Dad, ka bani five minute yanzu zan k'araso" takai k'arshen maganar gami da tada motar, ta kashe wayar ta ajiye a gefe, tabarwa sauran aikin zuwa gobe in me duka ya kaimu.



*JIDDAH*

Hauwa Isa Hashim shine asalin sunanta, wanda ta maidashi (Jiddah Isah Hashim) tun a haihuwarta Allah yaiwa Mahaifiyarta rasuwa, ta taso bata san kowa ba sai mahaifinta,sai kuma mai rainonta, dukkanin wani gata da kulawa mahaifinta yana bata shi. Tana shekara 6 mahaifinta yayi aure, don tsoron halin matan uba bai kori mai rainanta ba yabarta a phart d'insu da ban, komai na jin dad'in rayuwa yana yimata, akwai k'auna da tausayi sosai tsakaninta da mahaifinta, dukkan wani burinsa yana kan Jiddah. Kasancewar ya sanya ta a makaranta da wuri, hakanne yasa ta yin candy tana 15years, ba b'ata lokaci mahaifinta ya turata k'asar waje taje tayo karatunta na law.

Tana shekara 21 ta zama cikakkiyar Barrister, a yanzu dai lauya ce mai zaman kanta, kuma tana koyarwa a law school ta bagauda. Tana da samari wa'yanda suke sonta, amma har wala yau ita bata ga wanda take soba, Almash kad'ai zuciyarta ta aminta dashi, dashi kad'ai take son ta rayu.




*******

Washe gari kuma gidan su Rabee'ah taiwa tsinkayi, a kwance ta tadda Rabee'ah zazzab'i ya rufeta don har karkarwa take, dak'yar take iya amsawa Jiddah 'yan tambayoyin da take mata, a k'arshe da taga tana matsa mata sai ta rabu da ita, ta buk'aci Amira ta rakata gidan Almash, tana son shiga d'akin Abu Zarrin ko zata samu wani abin.

Kasancewar Amirah a shiryanta take futowa kawai sukai Ummi tanai musu Allah ya kiyaye. Amira motarta ta hau itama, jiddan na biye da ita a baya.

Phart d'in Abu Zarrin kawai suka nufa basu bi takan Hafsa ba, don gaba d'aya haushinta suke ji. Komai yana nan yarda aka tsarashi, babu abinda aka tab'a, saida Amira taji hawaye ya zubo mata na tausayin Rabee'ah da tuni tana nan suna rayuwa da masoyinta.

Bedroom d'inshi Amira ta nuna mata ta shiga ciki, tsayawa tayi tana k'arewa d'akin kallo, tunanin abin yi take kawai, jikin mudubi taje ta janyo drower, wani kyakkyawan littafi tai to zali dashi, kawai sai ta tsinci kanta da bud'o k'arshen littafin, wani kyakkyawan murmushi naga tana fitarwa a fuskarta.........
[8/19, 11:33 PM] BEBE'ARTH😘: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_💋


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE'ATU SK MASHI

Daga Manzon Allah (S.A.W) yace.
_Hak'ik'a Allah ya rubuta kyautayi akan dukkan komai, idan zakui kisa, Ku kyautata abinda zaku kashe, idan zakui yanka Ku kyautatawa abinda zaku yanka, d'ayanku ya wasa wuk'arsa, don ya hutar da abinda zai yanka._( *Musulumu ne ya rawaito*)


( *16*)
Bud'e page d'in baya tayi daga farkon gurin da ya d'auki hankalinta ta fara karantawa kamar haka.....

Ina zaune cikin offis d'ina, Alh Tasi'u Sabon Kud'i yazo ya samen, wani akwati ya d'oran a gabana ya bud'emun, damun kud'ine a ciki da bansan iya adadinsu ba, d'agowa nayi na kalleshi da alamar tambaya a fuskata, murmushi ne kwance akan fuskarshi yace.

"Abu Zarrin sunanka ko?" Bai jira amsata ba yaci gaba. "Wannan kud'i da kake gani naka ne idan har ka bani had'in kai, address d'inka aka bani, an sanar mun k'warewar ka akan aikinka, sai ka tabbatar da magana kake buga jarida hakanne yasa nazo gareka." Photon wani mutumi ya d'aukko ya mik'on, da wasu takaddu sannan yaci gaba. "Wannan mutumin nake so ka bugan jarida a kansa, sbd nasan idan ka rubuta tabbas mutane zasu yarda, dukkanin wasu bayanai suna cikin takaddun nan."


Gani nayi yana k'ok'arin tashi da sauri na dakatar dashi, byan na duba abinda ke cikin takaddun, b'atanci ne gaba d'aya a cikin takaddun akan mutumin, ajiye mishi takaddun nayi kan akwatin nace. "Ni bana yin irin aikinnan, ba kuma zan fara yanzu ba, don Allah kayi hak'uri ka d'auki kayanka ka tafi."

Wata iriyar tsawa yamun "Baka isa ba, kayi kad'an, bana bada aiki ace mun baza'ayi ba, yaro babu gaskiya yanzu a duniyar nan, ka d'auki kud'i kamun aiki idan kuma kak'i yi baka k'i gani ba." Daga haka yasa kai yabar ofis d'in, da Sauri na d'auki akwatin da takaddun nabi bayanshi, sanda na k'arasa a sannan yashiga cikin motar, kan yakai ga rufe motar nai sauri na saka mishi akwatin kan cinyarshi. "Idan babu gaskiya a duniya ni akwai gaskiya a zuciyata, meye ribata idan na rubuta b'atanci akan wani? Ni ba haka nake ba, d'abi'ata tasha ban-ban da taku, kaje ka nemi irinka maha'inta ba Abu Zarrin ba." Ban saurari abinda zaice ba, nai sauri nabar gurin, nadai lura sai huci yake.

Iska Jiddah ta busar yayin da takai k'arshen rubutun Abu Zarrin, taso da cigaba taji ya k'arshensu ya kaya, amma duk da haka tayi murna da samun wannan ma, dole ne yanzu tayi bincike akan Alh Sabon Kud'i, mik'ewa tayi taci gaba da bincika d'aki, bata samu komai ba, bayan wannan littafi, don haka ta k'ullo d'akin ta fito, bata ga Amira ba.

Amira kwa tunda Jiddah ta shiga d'akin ta fito barandar gidan ,tana nan zaune Hafsa ta fito tayowa k'awarta rakiya, basu kula da ita ba, don haka suka cigaba da hirar da suke yi, jin akan mutuwar Abu Zarrin suke maganar da sauri ta kamo record ta kunna, dai² nan Hafsa ke cewa k'awarta "Wlh Allah bani da tabbacin Almash shi yayi kisan nan, kawai dai zargi nake, da kuma tunanin da nayi yanzu fa shi zai auri Mami, nikwa da ya aureta gwara ya k'are rayuwar sa a prison, don wlh son da nakewa Almash bazan iya jure ganinshi da wata mace ba, na dad'e ina gaya mishi muddin ya sake yaso Mami zan iya aikata komai"

Dai² lokacin Jiddah ta fito tana neman Amira, ganinta da Hafsa tayi ne, yasa ta d'inke bakinta tai shiru , da sauri ta k'arasa gurin da Jiddah take. "Ke wace, me kika zo yi gidana, wama ya baki key d'in gurin?"

Wani kallo Jiddah take watsa mata na baki isa na baki amsa ba.

"Tare muke daita"

Da sauri ta juya don ganin me maganar , Amira ta gani a tsaye tana sakar mata murmushi, yak'e tayi. "Au Amira tare kuke kenan, me kuka zo yi?"

"Ummi ce ta aikomu" ta bata amsa gami da cewa Jiddah. "Mu tafi"


Bayan fitar su, a tsorace Hafsa ta juyo ta kalli k'awarta. "Allah dai yasa yarinyar can bata jimu ba"

"Aikam dai, da k'yar in bata jiba" cewar k'awarta ta nan take cikin Hafsa ya d'uru ruwa,sukai sallama da k'awar ta koma ciki.


Har Jiddah zata shiga mota, Amira ta tsaidata, recording d'in maganar Hafsa da tayi ta kunna mata, sai da ta gama sauraro tayi kyakkyawan murmushi, nan take ta shiga xender ta tura kana ta bawa Amira wayarta sukayi sallama kowa ya tafi gida.


A hanya traffic light ta tsaidata taga me tallan jarida, da hannu tamai alama yazo ta siya. Dubawa ta soma kafin a basu hannu, wani page take dubawa inda gaba d'aya b'atanci ne akan Alhj Mai Tangaran, murmushi ne kwance kan fuskarta, tsabar komai yana tafi mata dai².


Sanda ta k'arasa gida ta tadda zazzab'in ya saki Rabee'ah, tana zaune ta k'urawa photon su ido,hawaye na bimata kumatu, wanda suke su uku, da ita da yaya Abunta da Almash, sunyi kyau sosai, zama tayi kusa da ita ta dafata. "Haba Mami wai sai yaushe zaki cire damuwa a ranki ne? kika rasa Umma kika hak'ura ma bare wannan"

"Wannan daban Amirah, abu biyune suka had'u suka mun yawa, aduk sanda na tuno ya Abuna ya tafi shikenan bazan kuma ganinshi ba, nakan ji duniyar taimun zafi, komai bayamun dad'i, idan na tuna yaya Almash yana prison nakan ji ciwo a cikin zuciyata mara misaltuwa, Amirah ni kad'ai na San irin halin da nake ciki, duk yarda zan misalta miki baza ki ganeba."

"To ai komai ya kusa zuwa k'arshe insha Allah, bari kiji wani abu.". Ta kunna mata recording d'in da tayi.


A zaune yake, ya jinginar da kanshi jikin bango hawaye sai ambaliya suke a fuskarshi, ji yayi an dafashi, d'agowa yayi yaga waye.

A tsayi zaiyishi a shekaru ma bazai d'arashi ba, sanye yake da uniform d'in prison "nima sanda aka kawoni cikin gidannan haka na kasance kullum cikin k'unci, gani nake kamar bazan sukuni ba, amma yanzu kalleni har na ware, ka kwantar da hankalinka komai me wucewa ne, bare kai da ba wukunci aka yankema ba kana saka ran fita, nikwa dole sai na k'aide kwanakin da aka d'ibarmun, ka kwantar da hankalinka ka daina saka damuwa, kaci gaba da kaiwa Allah kukan ka."

"Ina k'ok'arin ganin na cire damuwa amma na kasa, sharri da k'azafi suna da ciwo d'an uwa baka sanin haka sai abun ya faru da kai, ko da d'an uwanka, kai ina jin ba irin abinda ya kawoni ne ya kawoka ba."

Gaskiya kam ni ba sharri aka munba na aikata, ba komai ne yaja munba sai halin rayuwa, a gidanmu nine babba, sai k'anne na biyu, mahaifinmu ya rasu, muna cikin halin talauci, sai mu kwan nawa bamu kai abinci bakinmu ba, rannan naga k'annena da mahaifiyata suna k'ok'arin mutuwa tsabar yunwa, kuma nayi fafutukar ban samu ba, shine naje na sato kwaki gwangwani uku na jik'a musu ba sikari haka na basu suke sha, suna tsaka da sha, 'yan sanda suka dira gidanmu, kasan 'yan sanda babu imani babu tausayi, indai za'a basu kud'i zasu iya komai, haka suka saka mun ankwa suka tafi dani, mahaifiyata na kuka k'annena na kuka, kaji silar zuwana gidannan."

Kuka Almash ya fashe dashi sosai, na tausayin mutumin nan, saida yayi kukanshi me isarshi, kana yace. "Idan har na fita daga nan gurin na yima alk'awarin futar da kai insha Allahu rabbi........

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment