Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin zubda hawaye.

Ummi salati take da sal'lallami, ta haura sama don ta gayowa Abba, kafin ta fito su Rabee'ah har sun rankaya sun tafi cikin motar Amira.


Koda Ummi tajewa da Abba zancan, tsaki yayi, "mtsss kiji wani sokon zance taya za'ayi Almash ya kashe Abu Zarrin?" Wayarshi ya lalubo yana neman layin Almash.


A bakin k'ofar get d'in suka tadda Hafsa tana kuka wiwi-wiwi, da gudu Rabee'ah ta shige phart d'in Abu Zarrin, muryarshi taji yana. "Abba da gaske ne an kashe Abu Zarrin, amma Abba bansan wanda ya aikata haka ba." Yakai k'arshen maganar cikin matsanancin kuka, Abba gaba d'aya ya firgice ya mik'e yana salati, muk'ullin motar shi ya d'auka suka taho shi da Ummi.

Da gudu ta banka k'ofar d'akin ta shiga , a kwance akan gawar ta tadda Almash yana kuka me soya zuci,farar shaddar da ke jikinshi gaba d'aya tayi face-face da jini, dukkanin k'arfinta ta saka ta hankad'e shi , rungume gawar tayi tana wani irin kuka mara sauti, ita kad'ai tasan yadda take ji a k'irjinta, don numfashinta har k'ok'arin d'aukewa yake.

Tsabar tashin hankalin da suke ciki ko kad'an basu ji jiniyar 'yan sanda ba, sai ganin shigowar su sukai tare da Hafsa tana ta shash shek'ar kuka.
"Wlh shine ya kasheshi don yau za'a d'aura musu aure da wacce yake so."

Tashin hankali, firgici, fad'uwar gaba, a lokaci d'aya sukai mishi rubdugu yayin da yaji muryar Hafsa tana fad'awa 'yan sanda haka, tafiya gun da yake sukayi suna neman saka mishi ankwa, yana zubda hawaye cikin takaici yana girgid'a musu kai, tsabar rud'anin da ya shiga da tashin hankali su suka sashi ya kasa musu magana, girgid'a musu kai kawai yake.

Suna cikin saka mishi ankwar su Abba suka shigo, a rikice Abba yace. "A'a ya kuma kuke saka mishi ankwa?" D'aya daga cikin police d'inne ya nuna Hafsa yace. "Alhaji wannan ce ta kiramu akan anyi kisa a gidanta, kuma tace shine yayi kisan."

Kallon Hafsa Abba yayi. "Haba Hafsa taya za'ayi mutum ya kashe d'an uwanshi duk girman laifin da yayi mishi? bare kuma Almash, wanda nayi imanin komai girman laifin da wani yayi mishi ko ciwo bazai iya jimishi ba, bare kisa, taya kike zaton Almash zai iya d'aukan wuk'a ya kashe Abu Zarrin?" Yakai k'arshen maganar cikin jin d'acinta a mak'oga ronshi, hawaye na k'ok'arin zubo mishi.

"Wlh Abba shi ya kasheshi, shi kad'aine ya shigo d'akin, kuma dama yacewa Mami idan ta bari ranar auransu tazo bata sanar da Abu Zarrin yana santa ba zai iya d'aukar ko wani mataki" takai k'arshen maganar cikin gunshek'ar kuka.

Police d'in basu saurari cewar Abba ba suka tusa k'eyar Almash sukai waje dashi...........
[7/28, 4:17 PM] BEBE'ARTH😘: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_💋


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE'ARTH SK MASHI

Manzon Allah (S.A.W) yace;

" _Duk abinda ya sameka, to dama can Allah ya rubuta zai sameka._ _Duk abinda ya kub'uce maka to dama Allah ya rubuta bazai sameka ba._ _Ka sani nasara na tare da hak'uri, yayewa na tare da bak'in ciki, tsanani na tare da sauk'i._"



( *13*)

Abbane ya lura da Rabee'ah ba ta motsi , da sauri ya k'arasa kan gawar Abu Zarrin da tayi rub da ciki a kai ya d'agota, sam ba ta motsi idanuwanta sun k'ak'k'afe, ruwa Abba yace Amira ta mik'o masa, shash sha'fa mata yayi amma ko gezau bata yiba, wani sabon firgici ne ya kuma shigar Abba dama dukkanin wanda ke d'akin in ka cire Hafsa wacce a zuciyarta fad'i take. "Dama ki bishi na huta wallahi." 'Daukarta Abba yayi cike da azama ya fice da ita su Amirah suka bi bayanshi, Ummi ce kawai ta tsaya kan gawar Abu Zarrin tana d'igar hawaye.

Suna fita, police d'in suka dawo suka d'auki gawar Abu Zarrin, a cewarsu zasu k'ara bincikar ta don su k'ara tabbatar da zarginsu.
Anja lokaci sosai kafin su gama bincike akan gawar, bincike ya nuna musu Almash shine yayi wannan kisan, duba da yadda duk wani shatar jikin Abu Zarrin hannun Almash ne, hatta wuk'ar da ke mak'ale a wuyanshi, hakanne yasa suka gark'ame Almásh a cell, suka dawo
da gawar Abu Zarrin gida, domin amishi salla a sitirceshi.

Dubban mutane sun halarci janaizar Abu Zarrin, dukkanin 'yan jaridu mutuwar ta kad'asu, sunyi rashin gwarzo jarumi mai rik'on gaskiya da amana, sunyi kuka sosai daga k'arshe suka bishi da addu'a.

Mutuwar ta karad'e dukanin birnin kano dama wasu garuruwa da dama.


Yana zaune a k'awataccen falonsa yana kallon TV tashar ARTV aka sako sanarwar kisan Abu Zarrin kuma ana zargin d'an uwanshi da kisan, wata mahaukaciyar dariya ya fashe daita ya d'aukko wayarshi daga mazauninta yana lalibar number don ya kira.


Tunda Hafsa takai labari cikin gidansu kowa ya hargitse, ihu kike ji yana tashi ta koina hatta da yara k'anana, shi kanshi Baba kuka yake sosai, yana wadarai da haihuwar Almash, wata iriyar kunya yake ji, don babban abin kunya ne Almash ya tafka masa, zuciyarshi wani irin ciwo take masa tana mishi suya me k'auri, ga mutuwar yaronshi mafi soyuwa a gareshi, kuma ace d'anshi wanda yafi shak'uwa dashi yafi k'aunarsa sama da kowa shine ya kasheshi da hannunsa, kuka ya kuma fashewa dashi, dak'yar ya iya fita akayi janaiza dashi, bayan an kaishi makwancinshi ya siraro ya dawo gida, sbd a can k'ofar gidan Abba za'ai zaman makoki.


Rabee'ah bata san kanta ba sai da ta kwana biyu a asibiti, tunda ta farfad'o tak'i ci tak'i sha, kuka takeyi sosai, b'arin zuciyarta yana gasgata mata Almash ne ya kasheshi, d'aya b'arin zuciyar na gaya mata yaya Almash bazai iya kashe yaya Abuu d'inta ba. D'agowa tayi ta kalli Amira da take ta lallashinta tasha ko ruwan tea ne. "Amira da gaske ne yaya Almash ne ya kashe yaya Abuu?"takai k'arshen maganar cikin dashash shiyar muryarta da bata fita sosai.

Share k'walla Amira tayi tace "nidai gaskiya ban yadda shi yayi kisan nanba Mami, amma yana can an gark'ameshi a cell bayan bakwai za'a shiga court"
Ba tace komaiba tayi rub da ciki ta fashe da kuka me suya rai.




*****
BAYAN SADAKAR BAKWAN ABU ZARRIN.

Abbane da kanshi ya samarwa Almash lawyern da zai kareshi, dak'yar ya yarda da lawyern don yace "shi baya buk'atar wani lawyer kawai a yanke masa hukuncin da ya dace dashi, tunda mahaifinshi yake fushi dashi ya amunce zai iya kashe d'an uwanshi ai yasan ba wani sauk'i gareshi, ga Rabee'ah ma lokacin da suka zo da Abba bai gasgata kallon da take masa ba yana ganin kamar kallon tuhuma take masa."


*FEDERAL HIGH COURT*
Mon/ 25/72018
Cikin kotun cike yake da mutane mak'il maza da mata, sbd yau za'ayi shari'ah da dama, shari'ar su Almash itace ta biyu a ranar.

Byan an fito da Almash an sakashi inda aka tanada domin saka masu laifi, me karanta k'arar ya mik'e ya karanta, sannan ya mik'awa al'k'alin, kotu tayi tsit masu jimami nayi, masu Allah wadarai nayi, Almash kwa tunda ya sunkui da kanshi hawaye ne ke zuba a idonshi, tarin takaici da bak'in ciki sun had'u sunmai tarin yawa, tunda yake bai tab'a nadamar auran Hafsa ba sai yau, wani irin tsanarta ce take gudana a zuciyarshi, wai yau shine ake shari'ah dashi ya kashe d'an uwanshi mafi soyuwa a gareshi, wani irin kukane ya tawo mishi mai d'acin rai.

BR MB Shehu ne ya mik'e ya gabatar da kanshi, akan shine lawyern wanda aka kashe, byan ya zauna BR Mak'ari ya mik'e shima ya gabatar da kanshi akan shine lawyern wanda ake zargi (Accused person) BR MB ne ya mik'e yana takunshi na isa da k'asaita ya isa gaban Almash, "Ina so ka sanar mini dalilinka na kashe d'an uwanka na jini?........
[7/29, 10:56 PM] BEBE'ARTH😘: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_💋


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE'ATU SK MASHI

Hadisi yazo cewa;

" _Mutane uku wa'yanda zasu kasance cikin inuwar Al'arshi, suna zantawa, suna Amintattu, yayin da mutane suna cikin hisabi._
_Mutumin da zargin mai zargi bai dameshi ba cikin shaanin Ubangiji._
_Da mutumin da bai tab'a kai hannunshi zuwa ga abinda Allah bai halatta mishi ba._
_Da kuma mutumin da bai tab'a dube zuwa ga abinda Allah bai halatta mishi ba._" Asbahani ne ya rawaito.

*Makaranta na ina dad'a baku hak'uri na rashin samun novel d'innan akan lokaci, ku dad'a hak'uri akan wanda kuke na da, zan fara zana exxam next weak dan haka zan ajiye typing daga yau, in sha Allah byan na gama exxam zan cigaba dai muku akan lokaci har nakai muku k'arshensa da izinin Allah, tunda lokacin muna cikin hutu, ina neman addu'ar dukkanin wani d'an uwana musulmi akan Allah Ubangiji ya bamu sa'ar jarabawar nan da zamuyi, ya kuma saka mu fara ta a sa'a mu gama a sa'a Allahuma Amin.*



( *14*)

Tunda yayi maganar kan Almash yake a k'asa shi bai d'ago ba kuma shi bai maganaba, hakanne yasa BR. MB ya numfasa.
"Shirunka yana nuna mana baka da wata hujja, kuma kaine ka kashe Abu Zarrin uhumm" Ya fad'a gami da d'aga mishi gira d'aya.

'Dagowa yayi ya kalleshi da idanuwanshi da sukayi ja suka kumbura na ban mamaki, zuciyarshi gaya mishi take ya amsa kawai shine ya kasheshi shima a kasheshi ya huta, had'iyar yahu yayi ya bud'e baki zaiyi magana, karaf idanuwansa suka had'u da na Abba, girgid'a mishi kai Abba yake yana rok'onsa kar ya amsa laifi da bashi yayi ba, had'iyar yahu ya kuma yi yamai da maganarshi ciki.

"Ka daina b'atawa kotu lokaci, ka amsa laifinka kawai, domin dukkanin wasu alamu sun nuna kaine kayi kisan"

A zafafe BR. Mak'ari yace. "Ina da magana ya mai girma mai shari'ah."

'Dagowa alk'ali yayi ya kalleshi daga bisani ya d'aga mishi kai gami da cewa. "Kotu ta baka dama.". Bai kamatu BR MB yadinga tirsasa wanda ake zargi da sai ya amsa laifin da bashi ya aikata ba, tunda har yanzu Almash Accused person ne babu wanda ya ganshi k'uru-k'uru sanda yayi kisan, na gode ya mai girma mai shari'ah." Ya koma mazauninshi ya zauna.

"K'orafi ya karb'u, BR ka kiyaye"

"Na gode ya mai girma mai shari'ah, idan kotu ta bani dama zan gabatar da wasu shaiduna da suke nuna cewa Almash shine ya kashe d'an uwanshi saboda yana son matar da zai aura."

"Kotu ta baka dama"

"Kotu tana son ganin Hafsat Almash a gurin bada shaida" mai sanarwa ya fad'a, A hankula Hafsa ta ratso ta cikin mutane tazo ta tsaya gurin da masu bada shaida suke tsaiwa. "Malama Hafsah zamu so ki gayawa kotu sunanki."

"Suna na Hafsah Almash, nice matar wacce ake zargi"
"To malama Hafsah zaki d'aga hannunki sama ki rantsuwa da Allah zaki gaya mana gaskiyar abinda kika sani."

"Na rantse da Allah zan gayawa kotu gaskiyar abinda na sani." Sai da ta fad'i hakan sau uku sannan BR MB ya matsa gabanta "Malama Hafsa me kika sani game da mutuwar k'anin mijinki?"
Muryarta na rawa ta soma magana saboda wani kwarjini da taga yayi mata. "Tun ana ya gobe d'aurin auren Mami da Abu dukkanin wata walwala ta bar fuskar mijina, ya shiga cikin damuwa matuk'a nayi-nayi ya gayamun damuwarshi yak'i, ya ajiye wayar shi domin ya shiga toilet, yana ajiyewa nikuma na d'auka anan nayi katari da text d'in da yayiwa Mami na kad'u sosai da na gani amma ban nuna masa na gani ba saboda ya hanani tab'a mishi waya, washe gari da safe naga gilmawarshi ya nufi phart d'in Abuu haka kawai naji zuciyata bata yarda dashi ba, sai nabi bayanshi, ina shiga d'akin na ganshi yana zare wuk'a daga jikin wuyan Abuu." Takai k'arshen maganar tana zubda hawaye.

"Ya mai girma mai shari'a ko da wannan shaida ta Hafsa aka duba za'a ga cewa Almash shine yayi wannan kisan." Sunkui da kai alk'ali yai yayi rubuce-rubuce daga bisani ya d'ago da kanshi.

"Lauyan wanda ake k'ara yana da tambaya?"

"Ina da ita ya mai girma mai shari'ah " BR Mak'ari ya fad'a bayan ya mik'e ya rusunar da kanshi, k'arasawa yayi gurin da Hafsa take wacce tunda taga tahowarshi bakinta ke rawa saboda tsabar kwarjinin da yayi mata, sai da ya fara sakin murmushi daga bisani yace. "Malama Hafsa kenan, shin sanda kika shiga d'akin a wani yanayi kika tadda Almash sanda yake zare wuk'ar daga jikin Abu Zarrin?" Shiru tayi na d'an sakanni kana tace " na taddashi yana kuka yana jijjigashi". "Ya mai girma mai shari'a idan har Almash kashe Abu zarrin yayi bazai tsaya zare wuk'a ba haka zalika bazai zauna yana kuka yana jijjigashi ba, kishi ne irin nasu na mata ya rufewa Hafsa ido ta kasa ganin hakan, da wannan nake so kotu ta duba wannan shaida ta BR MB tayi watsi da ita na gode ya mai girma mai Shari'ah" ya koma gurinshi ya zauna.

Rubutu alk'ali ya kuma yi, ya d'ago "Shaida ta karb'u" Murmushi BR MB yayi ta nasara, yayin da yanayin fuskar BR Mak'ari ta sauya.

"Idan kotu ta bani dama zan kuma gabatar da shaida ta gaba?"
"Kotu ta baka dama"

Duban Hafsah ya kuma yi. "Zan so ki gabatarwa da kotu text message d'in da Almash ya yiwa Mami"

"Yana cikin wayar Mami"

"Kotu tana son ganin Mami"

Amira ce ta mik'e tace "ba ta samu damar zuwa ba, amma ga wayarta a hannuna"

Hafsa aka mik'awa ta nemo message d'in ta mik'awa BR MB, karb'a yayi ya karanta ya mik'a daga haka har ya isa ga alk'ali, karb'a yayi ya karanta yayi rubuce- rubucenshi.

"Lauyan wanda ake k'ara yana da magana?"

"A'a ya mai girma mai shari'ah" Aka sallami Hafsa ta koma gurin zamanta.

Wani irin murmushi BR MB ya kuma yi yace "Idan kotu ta kuma bani dama ina so zan gabatar da shaidata ta gaba?"

"Kotu ta baka dama"

Wuk'ar da aka kashe Abuu Zarrin ya d'aukko da wasu takaddu ya mik'awa alk'ali. "Ina so Mai shari'ah ya duba wannan wuk'a shaidar yatsun Almash ne a jiki (finger print) haka zalika jikin mamaci shatar hannunsane a jiki, hakan yana nuna mana shine mutum na k'arshe wanda yaje ga Abu Zarrin kafin ya rasu, idan kotu ta duba wa'yannan shaidu nawa zataga tabbacin cewa Almash shine ya kashe Abu Zarrin na gode ya mai girma mai shari'ah (My Lord)."

"Lauyan wanda ake k'ara yana da magana?"

"Eh ina da ita ya mai girma mai shari'ah"

"Kotu ta baka dama"

"Na gode mai shari'ah, ina so kotu ta duba wannan shaida ta BR MB, finger print ana samun haka a gurare da dama, idan aka kashe mutum d'an uwansa da ke fara zuwa gareshi finger print d'insa ake samu da wannan nake so kotu mai adalci ta duba tai fatali da wannan shaidar a d'aga shari'ah domin bani dama na kawo shaiduna masu k'arfi na gode ya mai shari'ah" Ya koma gurinshi ya zauna.

Saida alk'ali ya d'auki lokuta yana rubutu kana ya d'ago. "Kotu ta d'aga wannan shari'ah zuwa 16/8/2018" Daga haka ya mik'e ya daki bencin da gudumarsa nan kotu ta kauraye da hayaniya.





*****

Satinta biyu bata Nigrea sai jiya da daddare ta dawo, firowarta daga wanka kenan tana tsatstsane jikinta da tahul idonta ya sauka kan TV, a lokacin ake sanar da shari'ar su Abu Zarrin, idonta ne ya sauka kan Almash sanda ake fito dashi daga kotun 'yan jaridu sun zagaye su kowa yana k'ok'arin samun News, an d'ad'd'aureshi da ankwa duk ya fita hayyacinshi, banda taji an ambaci sunanshi da k'aryatawa zatayi ba Almash d'inta bane, ta tabbata Almash d'inta bazai iya kisa ba, tana da yak'inin Almash ko k'waro bazai iya kashewa ba bare d'an uwanshi na jini, dole ne tai uwa tai makarb'iya ta fitar da masoyinta daga k'angin rayuwar da ya shiga idan har soyayyar gaskiya take masa.

Murmushi BR Jiddah tayi ta furta. "A yanzu ne zaka gasgata soyayyar da nake maka.
A yanzune zaka gasgata maganar da na tab'a gaya maka.
A yanzune soyayyar da nake maka zata yimaka rana.
A yanzu ne zaka tabbatar da tarin k'aunar da nake maka." Tana kaiwa nan ta mik'e ta fara shiri da sauri da sauri............


To shin abinda Jiddah ta fad'a zai gasgata? Kudai kuci gaba da bin 'YAR GATAN HUDAH zata warware muku komai byan kammala exxam d'inta kudai Ku sakata cikin addu'arku.

Auntyna HUDAH nayi miss d'inki dan Allah ki dawo online😭😭😭😭😭
[8/4, 11:01 AM] BEBE'ARTH😘: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

*AKWAI ILLAH*

*Alk'alamin Maryamerhabdul*

*SADAUKARWA GA LUBBATU MAI TAFSEER*

PAGE 2

Hannunsa sanye da ankwa, doguwar kaca manne ta k'asa ya iso k'afarsa da ke zagaye da wata ankwar.

Da k'yar yake ajiye takunsa, idanunsa na lumshewa, leb'b'ansa ya bushe. Fatar jikinsa da ya kasance bak'i mai haske ya disashe, yayi fari.

Yawun bakinsa yake had'iya dan gusar da ishin da ke addabarsa.

A hankali yake takunsa cikin rashin kuzari. D'an sandan da ke biye masa na kallonsa ta wani siga, ba daman ya tunkud'esa yayi sauri.

Wurin da aka tanada dan tsayuwar wad'an da ake tuhuma d'an sandan ya sa shi, ya jawo k'ofar ya rufe.

Hannunsa Hamza ya d'aura a kan katakon da ke gabansa yana mayar da numfashi.

Kallonsa Alk'ali ya tsaya yi ta saman gilashinsa, yana duba yanayinsa.

Bai furta komai ba na tsawon sakanni goma muryar Barrister Anthony ya doki kunnuwarsa.

"Sunana Barrister Anthony, lauya da ke kare wanda ake k'ara ya mai shari'a".
Ya russuna kad'an alamar girmamawa.

"Sunana Barrister Fatima, lauyar da ke kare wanda ya kawo k'ara. Nagode"
Ita ma ta russuna sannan ta koma mazauninta.

Gilashin idanunsa ya gyara, yana kallonsu d'ai-d'ai.

Sai da ya nisa sannan ya gyad'a kansa alamar bismillah.

Mik'ewa Barrister Fatima ta yi, ta gyara rigarta, ta dai-daita tsayuwarta.

"Ya mai shari'a, ina neman a bani daman farawa da k'orafi akan yanayin da Hamza ya shigo."

Kad'a kai ya yi yana sauraranta.

"A yanayin da Hamza ya shigo wannan kotu, ba sai an tambayesa ko an bincikesa ba, yana cikin hali ne na yunwa, ya galabaita, ana azabtar dashi da yunwa tun kafin a tabbatar da zargin da aka d'aura masa, wanda hakan ya sab'a shari'a.

Ina neman alfarma wurin kotu, da ta hana wannan cin kashi da ake masa, na hana sa samun wadattaciyar cima da kuma ruwan sha.

Dan har a lokaci irin wannan zargin da ake d'aura masa bai tabbata akansa ba, kuma ko da ya tabbata, alhak'in hukuntasa na ga kotu, sai ta bada hukuncin da ya dace dashi dai-dai da laifinsa".

Ta russuna kad'an
"Nagode ya mai shari'a, a duba bayanaina".

Zamanta ke da wuya Barrister Anthony ya mik'e, fuskarsa a had'e tamau.

"Ya mai shari'a, a yanayin yanda aka kama Hamza, an kama sa ne a yanayi na ta'addanci, an kama sa ne a tare dasu 'yan ta'adda, wanda dukkaninsu sun bada kai sun amince da zargin da ake musu, Hamza wasa da kotu yake yi, wanda 'yan sanda suke son sauk'ak'a wa kotu wahala, azabtar dashi shine kad'ai hanya mafi sauk'i da zai sa shi amsa laifinsa duk taurin kansa".

Bai zauna ba, idanunsa na yawo akan Alk'ali da alk'alaminsa. Gyarar muryarsa ya sa shi komawa mazauninsa.

"Barrister Anthony! Kotu na buk'atar ka karanto shafin da k'undin shari'a yace d'an sanda ya azabtar da mai laifin da ba'a tabbatar da laifinsa ba?".

'Ya'yan hanjinsa tuni suka kad'a, ya kama zare idanu yana kallon Alk'ali.

Bai d'auka zai iya b'atar da kwanyarsa tun farkon tafiya ba.

Shirun da ya yi ya bawa Alk'ali daman cigaba da maganarsa.

"Malam Hamza!"

Muryar Alk'ali ya karad'e kotu, ya ajiye alk'alaminsa ya had'e hannayensa wuri guda.

"Akwai abunda yake damunka? Yunwa ko ishin ruwa?"

Lumshe idanunsa yayi, yana hamdala a zuciyarsa.

Kasa sarrafa harshensa yayi, ya kad'a kai murmushi na zagaye leb'b'ansa.

"Kotu na buk'atar a bawa Hamza abinci ya dawo hayyacinsa, ya sha ruwa yanda yake buk'ata sannan mu cigaba da sauraran k'ararmu."

D'an Sandan da ya shigo da Hamza ya basa hanyar fitowa dan bin umarnin kotu.

"A k'ira k'ara na gaba"
Cewar Alk'ali bayan ya d'ago daga rubutun da ya ke yi.

***

MAIDUGURI BORNO STATE 11:15

"Ban fa ganka ba Na'eem, na gaji kuma rana".

Bakinta ta tura take maganar, ta dakata inda take tana sauraransa.

"Na ganki, k'ara matsowa kusa da wannan bishiyar, ina cikin mota".

Waigawa ta yi wurin bishiyar, ta hango bayan motarsa.

Ajiyar zuciya ta sauk'e, tana hamdala a ranta.

Mintuna goma da fitowarta daga aji kenan tana nemansa.

Wurin motar ta nufa, ta bud'e mazaunin gefen direba ta shige.

"Wash!"
Ta furta bayan ta zauna, ta janyo k'ofar motar ta rufe.

Lumshe idanunta tayi, tana jin k'amshi da sanyin da ke fita jikin AC (masanyaya) na busata.

"Sorry Sweetheart (yi hak'uri Sweetheart)"
Murmushi na lullub'e leb'b'ansa, yana kallonta ta k'asa dan furucinsa ya samu nasarar shiga zuciyarta.

Kallonsa tayi dan gaskata kalamansa, a wani b'angaren kuma da niyyar yin fad'an ajiyeta a rana da yayi, sai dai idanunsa da ya sark'e cikin nata, yana mata wani kallon da take jinsa har cikin b'argonta ya hanata furta k'ala.

D'auke kai ta yi, ta tura baki dan galaban da ya ci a kanta.

"Kalleni Mana Fanne, Na'eem ne fa".

"Na sani ai".

Hannunta ta hard'e a k'irjinta, tana had'e rai ala dole tana son ya san ta ji haushin minti goman da tayi tana nemansa, wanda can zuciyarta kuwa wani dad'i ne ke ratsata.

Wannan sunan da ya k'irata dashi, ya mik'a zuciyarta, da dukkan duniyarta wani matsayi na farin ciki, ya tabbata Na'eem yana sonta kamar yanda ita ma take jin soyayyarsa a zuciyarta.

"Yi hak'uri mana, ki daina b'ata rai akan abu irin wannan, kinsan haka kawai bazan barki cikin rana ba".

"Shikenan Na'eem, ya aiki?"

Iska ya furzar, ya kashe ido d'aya yana kallonta.

"Guduwa nayi daga office dan in amsa k'iranki, yanzu haka nasan ba'a kula bana nan bane, da an k'irani a waya".

Wani dad'i ne ya ziyarceta, ta kallesa cikin so da k'auna, murmushi ya zagaye leb'b'anta.

Tayi sa'a, tayi dacen samun Na'eem a lokacin da ya dace, zuciyarta zai dauwama cikin farin ciki dan dukkan burinta na tabbata.

Ta tabbata rashin Kaltum shi ya bata wannan dama, lallai tayi wayau kuma ta cancanci a jinjina mata.

***

LAGOS NAJERIYA 11:32

Kowa yana muhallinsa, Hamza ya ci abinci yayi dam, yunwar da ya addabesa ya kau, zantukan Fatima lokacin da yake cin abinci na k'ara sa zuciyarsa aminta da dukkan k'addarar duniyarsa.

A yau ya k'ara sa wa a ransa zai amsa dukkan tambayoyin da za'a jefo masa da iya gaskiyarsa, ba wai dan ya kare kansa ba, sai dan ya tabbatar wa duniya cewa d'an ta'adda ba daga kamanni bane, in ma na halitta, addini ko wani abu na zahiri.

Takun Fatima da ke doso shi ya sa zuciyarsa tsananta bugu. Kwayar idanunta na mik'a masa sak'on da shi kad'ai yake iya karanta, bazai dakusar da gwiwarta ba, ta sadaukar da abubuwa masu yawa dan ta kub'utar dashi, zai bata had'in kai d'ari-bisa-d'ari.

"Malam Hamza, ko zaka iya sanar da kotu yanda aka yi aka cafkeka a ranar alhamis, sha-takwas ga watan Febrairu, shekara ta dubu biyu da goma sha-shida. Ina nufin ka sanar damu a wani wuri hakan ya faru, ta ya ya ka kasance d'aya daga cikin mutanen da aka kama a wannan ranar?"

Yawu mai tauri ya had'iye, ya damk'e hannunsa yana jin yanda zuciyarsa ke

Please Login or Register in order to submit comment