Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mi'kata gidan angonta, a satin aka kawo kud'in Rabee'ah da saka rana, wata bakwai aka saka , A ranar Almash ya shiga tashin hankali ainun,kullum 'ko'karinsa ya danne soyayyarta kamar yadda yayi a baya tun sanda yaga take-taken Abu Zarrin yana sonta, amma yanzu ya rasa me yake 'ko'karin hanashi, da zai iya cire zuciyarsa ya cire sonta sannan ya mayar da yayi hakan amma kashh hakan bazai ta'ba faruwa ba.


Rabee'ah kwa ta kwantar da hankalinta sosai, takai soyayyar Almash can 'kasan zuciyarta, yanzu soyayyar Abu Zarrin ce take tashe a zuciyarta, kunsan zuciya akwai son me kyautata mata, musamman Abu Zarrin da kullum burinshi ya farantawa Mamin shi,hakan yasa ta 'kara d'ebo dukkanin kulawa ta azata bisa yaya Abu inta, sosai take nuna mishi soyayya ta rufe babin Almash a zuciyarta musamman yanzu da ba ganinshi take sosai ba.




*****
Iya dauriya yanayi, a kullum burin idaniyarshi taga mahad'inta, amma hakan yana mishi matu'kar wuya sbda aikin da ya kacame mishi, ko gidan baya samun zuwa saidai yaiwa Abba waya su gaisa, 'kara tarin damuwarsa tafiya da ta kamashi zuwa cairo kuma zai ibi watanni acan, zuciyarshi ta had'u da 'kunci mai tarin yawa har ya rasa ya zaiyi control inta.

"Honey tunanin me kake tayine? tun d'azu nake tsaye a kanka amma baka san nazo ba, kaida ko giftawa a kayi kana ji a jikinka." Hafsa ta tambayeshi byan ta jijjigashi.


"Hmmmmmm" ya numfasa, " babu komai, kawai ina tunanin yadda zan tafi na barki har tsawon watanni"


" Kai Honey ka gayan gaskiya, kodai ka fad'a soyayyane?"


Maimakon ya bata amsa sai ya mi'ke zai shiga toilet, da sauri ta rungumoshi ta baya ta kwantar da kanta a bayanshi.

"Tom Honey me zai hana mu tafi tare kawai, tunda hakan zai baka wahala."

"Ai hakan bazai yihuba shiyasa, aiki zamuje ba zama ba" daga haka ya zame hannuwanta daga jikinshi ya shige toilet.



**
da yamma ya shirya cikin jus nd t-shirt black nd red, rigar tayi masa matu'kar kyau, ainihin kyahunshi da cikar kamalarshi ta 'kara bayyana, gidan Abba yake son zuwa yayi musu sallama don gobe ne tafiyar tasu, daga nan sai ya huce gun mahaifinsu shima yayi musu sallama.


A falo ya tadda Hafsa, ta marairaice mishi zata bishi, don har tayi shirin ta ma ta goya Iffa, kar'bar Irfan yai, yayi gaba tabishi a baya.



Tana kichen tana had'awa yaya Abu inta kayan bud'e baki taji sallamar su sun shigo, jitai zuciyarta ta fara gudu, danne 'kirjinta tayi ta rintse ido tana sauke ajiyar zuciya a hankula.

Tana jiyo sanda suke gaisawa da Ummi, juyawa tayi taci gaba da aikinta, jitai zuciyarta ta 'kara gudu, bugawa takeyi da sauri-sauri, irin yanayin da take ciki, tana kasancewa ne idan Almash yana kusa daita, juyawa tayi ta kalli 'kofa, tsintar idanuwanta tayi cikin lumsassun idaniyanshi, Lumshe idonta tayi ta kau da fuskarta, murya a sanyaye tace. "Yayana ina huni?"

Har lokacin bai janye idonshi daga kanta ba, maimakon ya amsa gaisuwar sai ya tako zuwa gurin da take, hannu yasa ya juyo daita, ha'barta ya d'ago yadda zaifi kallon 'kwayar idonta sosai , 'kasa tai da idanuwanta zuciyarta tana bugawa da sauri_sauri, wani irin gudu take a 360.


"Ki barni na kalli 'kwayar idanunki, wasu sa'konni nake d'iba cikinsu"

Jin saukar muryarshi cikin kunnuwanta suka 'kara haifar mata da mutuwar jiki, 'kara yin 'kasa tayi da idanuwanta.

"Ko da zuciya ta 'boye soyayya, to 'kwayar ido bata 'boyewa, ban ta'ba lura da hakanba sai byan kinyi candy, Rabee'ah kina sona, na karanci haka cikin 'kwayar idonki."


Zazzaro idanuwa tayi cike da firgici, zuciyarta ta 'kara tsananta bugu, jinin jikinta kanshi tsere yadinga yi da gudu, kan takai ga magana sukaji alamun za'a shigo, da sauri ta juya bayanta don hawayene yake son zubo mata, shi kuma yayi gurin fridge.

Hafsace da ta gaji da jiranshi, tun byan da suka gaisa da Ummi, yaji 'kamshin girki a kitchen, kuma yana kyautata zaton Rabee'ah ce a ciki, memakon ya nufi gurin Abba, sai ya nufi kitchen in, tunda ya shiga zuciyarta ta kasa samun nutsuwa, kuma tana jin nauyin ta tashi ta bishi Ummi na zaune, har saida Ummi ta tashi ta shiga ciki, sannan ta taso.

"Honey anfa kusa magariba, kuma ko gun Abban baka jeba me kake yi a kitchen in?"

Baida shirin bata amsa saima kafa baki da yayi a gorar swan in da ya d'aukko mai matu'kar sanyi yana sha.

Sauri tayi ta goge hawayen fuskarta, da fara'a ta juyo. "Aunty Hafsah sannu da zuwa, sauri nakeyi na 'karasawa yaya Abuna girki, na fito mu gaisa" takai 'karshen maganar tana kar'bar Irfan da yake hannunta.

'Dan ya'ke tayi, don sam bata yarda da yanayin suba. "Babu komai Mami, ya gida?"

"Lfy lau, yasu Iffah?"

"Suna nan qalau" tamai da hankalinta ga Almash da idanuwansa suka canja colour, kafin takai ga cemasa wani abu ya fice daga kitchen in.



Gurin Abba yaje yai masa sallama, shikuma yabishi da addu'ah.
A falo ya taddasu, Iffah na hannun Rabee'ah, Irfan na hannun Amirah suna basu dankalin turawa sai mamula suke yi, Hafsa kwa ta zabga tagumi, a ranshi yace "wahalalliya."
Tunkan yace su taso su tafi har ta mi'ke.

Ko kad'an Rabee'ah bata bari sun had'a ido ba, har suka rakasu gurin mota, har ya tashi motar ya kirata.

" 'Kanwata"

Juyowa tayi tare da amsawa aikwa 'kwayar idonta ta samu kyakkyawan masauki cikin tasa, dukkaninsu saida suka samu hutu na d'an seconds, domin dawowa daga yanayin da suka tafi.

"In Broth ya daho kice yazo ina son ganinshi"

A sanyaye tace "tom" yaja motar suka tafi, daga nan gidansu yaje yaiwa Baba sallama, sannan sukaje gidan su Hafsah ta taho da 'kanwarta domin ta tayata zama.



Tayi matu'kar 'ko'karin danne zuciyarta da bata fallasa yanayin da take ciki ba, har saida Abu Zarrin ya gama shan ruwa, yayi mata sallama ya tafi amsa kiran Almash.

'Daki ta shiga ta fashe da kuka ko ta samu zuciyarta tayi sanyi, "meyasa, meyasa tun tuni baka karanci ina sonka ba sai yanzu? saida lokaci ya 'kure mana na rufe babin sonka a zuciyata sannan kake son tasomun da tsimun sonka wanda ya dad'e da si'kewa, me yasa zaka bijirowa da zuciyata abinda ba zata iya d'auka ba? tun wurima gara ka canja akalarka yaya Abuna zan aura shi nake so ni bakai nake soba."

Ita kad'ai take ta sambatun ta tana kuka mai cin rai.








****

Tayi matu'kar farin-ciki da tafiyar Almash, ko ba komai zai bar zuciyarta ta zauna lafiya, amma duk da haka yana mata tex a waya na soyayya kullum da kalar wanda zai turo mata, harda wanda yake cewa.....

"Tun kina 'kan'kanuwarki zuciyata take jigila da soyayyarki, zan iya cewa na riga Broth kamuwa da soyayyarki, ganin kinfi nuna 'kaunarki ga Broth yasa nikuma naja baya da ke, da kuma shima ganin yadda yake sonki sai na danne tawa zuciyar, ashe kema kina sona, dan Allah karki raba DANGANTAKAR ZUCINMU (Huguma) na tabbata kika gayawa Broth ni kike so, zai baki abinda kike so pls my everything."

tana zubda ruwan hawaye ta gama karantawa tayi masa reply da "'Ha'ki'kanin gaskiya baka karanci 'kwayar idona dai-dai ba, ko kad'an babu d'igon sonka cikin raina yaya Abuna nake so tun ina 'kan'kanuwa ta." tai masa send.

Tun daga ranar bai kuma mata tex ba.







******


Kwanaki suna ta tafiya, rayuwa tana juyawa a hankula cikin ni'imar Ubangiji. Gashi dai yau saura kwana biyu d'aurin auran Abu Zarrin da Rabee'ah, a ranar Almash ya dira 'kasar, yayi fresh dashi, cikar haibarshi da kwarjininshi ta kuma cika, saidai zuciyarsa da bata da ishashshen lafiya, yanaji a jikinshi in ya rasa Rabee'ah yayi babbar asara, soyayyarta 'kara azalzalar zuciyarsa take, ashe haka so yake? ashe haka Barr Jiddah takeji game dashi, babu makawa ha'k'kinta ne ya kamashi, sak'e sak'en da yakanyi a wasu lokuta kenan.



Ana ya gobe d'aurin aure da daddare, tana zaune cikin k'awayenta kamar an tsikareta ta mi'ke ta fice, jitai kawai tana son ganin Abu inta, kuma basu dad'e da rabuwa ba, har ta fita daga get in gidan ta tuna dare yayi dak'ar in zata samu mota, wayarta ta d'aga ta kira Amira.

"Hello, ki fito da key in mota ina bakin get ina jiranki." Bata jira cewarta ba ta kashe wayar.

Cikin mintina 'kalilan sai gata ta fito.

"Ina zamu?"

"Gidan ya Almash"

daga haka ba wanda ya kuma magana har suka k'arasa gidan.


A mota Amirah ta zauna ita kuma ta shiga ciki. Ta kutsa kai bedroom in nashi, shima zai fito, zuciyarshi ta azalzaleshi da son ganinta, baya yayi ya bata guri ta shigo , kallon juna sukai na 'yan seconds daga bisani suka d'an murmusa.

"Lfy na ganki da tsohon darennan?"

"Ba lafiya ba"

cike da tsoro yace. "Me ya faru?"

"Zuciyata ce ba lafiyaba, sonkane yayi mata yawa yake neman fasata, ga tarin kewarka da taimun dabaibayi, ji nake idan banzo na ganka ba kamar wani abu zai samemu."


"Nima haka nakeji Mamina, fitowarnan da nayi gurinki zan taho"

Bakin gado suka samu suka zauna, hira suka d'an ta'ba kad'an, ta mi'ke don ganin dare yayi sosai, ji sukeyi kamar kar su rabu, abinda bai tab'a faruwa tsakaninsu ba, hannu yasa ya janyota ya rungumeta, maimakon ta hanashi sai ta tsinci kanta da kwantar da kanta a k'irjinshi, duka hannuwa biyu yasa ya k'ank'ameta. "Duniya ba gaskiya Mamina kowa kanshi kad'ai ya sani, koda yake saima gobe zan baki labari in an kahoki gidana"

Janyewa tayi daga jikinshi,
"Amirah ta gaji da jira bari na tafi."

'Dago da kanta yayi, hannu yasa yana zagaye le'benta, daga bisani yakai bakinshi kan nata yana tsotsar le'benta, dukkaninsu ji suke kamar suyi dauwamammiyar rayuwa a haka, saidai wani 'barin na zuciyarsu yana sanar dasu kamar daga yau shikenan, bankwana sukeyi na har abada.


Saida ya rakata har bakin mota, yaga tafiyarsu ya juyo jiki a matuk'ar sanyaye.




****
Tun yamma ranar zuciyarshi take mishi ciwo, har ya rasa yadda zaiyi, yinin ranar a kwance yayishi ba inda yaje, tambayar duniya Hafsa tayi masa ya'ki tanka mata, wayarshi ya d'auka yaiwa Rabee'ah tex.

"Ki taimaki zuciyata, ki sami broth ki gayamishi muna son juna, idan baki haka ba zan iya aikata komai don ganin kin zama mallakina."

Yana tura mata, ya tashi ya shiga toilet.

Da sauri Hafsa ta d'auki wayar tana bincikawa, zuciyarta ta kusan hargitsewa sanda taga tex in, tashi tayi tabar d'akin don zuciyarta baza ta iya 'boye moment in da take ciki ba.



Saida tazo kwanciya ta kula da TeX in da yayi mata, shareshi tayi, suka shiga waya da yaya Abuu inta, kusan raba dare sukai suna waya da k'yar suka rabu.






*****

Washe gari da safe har Almash yayi shirin d'aurin aure baiji motsin Abuu Zarrin ba, part d'inshi ya nufa don ya duba lafiyarshi.

Hafsa tana ganin yayi phart inshi tabi bayanshi.


Yana shiga d'akinsa da d'ige d'igen jini ya fara karo, take zuciyarshi ta fara bugawa, da gudu ya 'karasa shiga, a tsakiyar d'akin ya taddashi an mishi yankan rago, wu'kar ma ba a gama cireta daga wuyanba, a gigice ya 'karasa gareshi, wuk'ar yake k'ok'arin cirewa Hafsa ta kawo kai d'akin, wata gigitacciyar 'kara ta saki ta fice daga d'akin da gudu........



Sai kuma Allah yaimana yawan rai zuwa bayan sallah, insha Allah zakuji yadda zata kaya.






Author: Bebe'arth๐Ÿ˜˜
[4/28, 8:01 PM] BEBE'ARTH๐Ÿ˜˜: [4/15, 11:05 AM] BEBE'ARTH๐Ÿ˜˜: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_๐Ÿ’‹


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE SK MASHI


An kar'bo daga Abdullahi d'an Umar (R.A), wani mutum yace da Manzon Allah (S.A.W)

" _Zanyi ya'ki," sai Annabi yace "kana da iyaye? " sai yace "na'am ina da iyaye"sai yace_) " _yimusu ya'ki" (ma'ana kaje kayi musu biyayya._)


*Makaran tana sai kuna ha'kuri da yanayin typing ina, ni kaina ina son yin typing kullum, amma hakan yana gagarata, amma zan 'ko'karta insha Allah ko byan two days ne haka zakuna samunshi insha Allah,ina godiya ina kuma alfahari daku da kuke bani aron lokacinku, Allah yabar 'kauna*

~Sumy Abdoul, nd Nafisa Musa, 'yar gatan Hudah na cigiyarku ina kuka shige ne?~

( *9*)

Tsaye suke bakin titi suna jiran mota, byan fitowarsu daga gidan Auntyn su Meenah sunje nuna mata anko.

"Nababa wai har yanzu kina jin abinda kikeji game da ya Almash kuwa dukda ya Abuu yana sonki?"
Hmmmmm Rabee'ah ta numfasa, "me za'a fasa Meenah? ai sai abinda yaci gaba, har ila yau in na ganshi sai naji wani zugi tun daga 'yan 'yatsun 'kafata zuwa 'kwa'kwalwata, ga tarin 'kaunarshi da kullum take mun katutu a zuciya, Meenah tun kanfa nai wayo nake fama da soyayyarshi, tun bansan meye soba, ada nai tunanin burgeni yake, sbd yadda nake shagala da kallonshi idan yai dariya ko murmushi kumatunsa suka lotsa, sbd Allah yayini da 'kaunar dimple, sai gashi ni bana dashi, shiyasa duk yayin da naga maishi nakan shagala da kallonsa har naji yana burgeni, to shima nai tunanin hakanne nake ji game dashi, ashe soyayyace tamun tsiro mai girma, wanda da nasan sanda zuciyata zatamun haka da ban barta tayi ba, Amma na binne soyayyar ya Almash acan 'kasan zuciyata, bana fatan abinda zai tasomun daita ko kad'an, na d'aukko ya Abuu na na d'orashi a sama, sbd yaya Almash tuni ya dad'e da haramta gareni."Takai 'karshen maganar cikin raunanniyar murya.

Hmmmm, Meenah ta numfasa "in so cutane ha'kuri magani ne, dama ba duk abinda bawa yake so yakan samu ba, Allah yana jarabtar bawansa a duk sanda yaso, Allah ya tabbatar miki da alkhairi cikin rayuwarki"

"Allahuma Amin" dai-dai nan Almash da yazo hucewa ya hangosu yai parking a gabansu, dama tun d'azu take jin sauyin bugun zuciyarta yana sauyawa, ashe shine yake tunkaro su, d'ago idonta tai ya sauka cikin 'kwayar idonshi by an ya zuge glass in motar, a lokaci d'aya yanayin bugun zuciyarsu ya sauya, da sauri ta kawar da 'kwayar idonta taja hannun Meenah suka 'karasa gaban motar, gidan gaba ta shiga, Meenah ta shiga baya.

Ko kad'an baiji dad'in d'auke 'kwayar idonta da tayiba, saboda wani irin yanayi yajishi yayin da yake kallon k'wayar idonta, Meenah ce ta katse mishi tunani, "yaya ina wuni?"
"lfy qalau Amarsu, biki kuma ya 'karato Allah Ubangiji ya sanya alkhairi" murmushi tai ta sadda kanta 'kasa, Amma fa a zuciyarta tunkan yakai 'karshen furucinshi ta rigashi da "Amin ya Allah"

Kallonta yai ta sunkui da kanta 'kasa tana wasa da zoben azurfarta, 'kasa yai da muryarshi "sai yanzu kuka dawo kenan?"

"Eh" ta bashi amsa ba tare da ta kalleshi ba, shikwa so yake ya kuma kallon 'kwayar idonta, "amma dai kinsan bana son dawowar gab da magariba ko?" "Kayi ha'kuri bansan zamu kai haka ba" gyad'a kai kawai yai, yamai da hankalinshi ga titi don yaga alamun baza ta d'ago kanta ba.



Sai da suka tsaya a hanya yasai kayan fruit da fura, shiyasa ana kiraye-kirayen salla suka shiga unguwar, Meenah aka fara saukewa, tunda aka karyo layin ta hango Saudah da Ummi a ranta tace "Jarababbu yanzu zasu isheni da mitar ban jirasu ba" kamar tasan abinda Meenah take sa'kawa kenan tace mata "ko me zasu cemiki kar ki tanka, laifine dai mun riga munyi" sauka tayi tana yiwa ya Almash godiya.


Hafsa ganin har magariba Almash bai dawo ba hankalinta ya tashi ,fitowa tayi barandar gidan tana ta kaiwa ta komo, tsayawa tayi cur yayin da taga me gadi ya bud'e masa get yana shigowa, a ranta cewa take "shida wace shegiyar ne?" yana yin parking fuuuu ta isa gurin motar tana huci, Rabee'ah zuciyarta sai dukan tara-tara take, shi ya fara bud'e motar ya fito, tunda ya hangota ya kuma murtuke fuska. Cike da masifa take tambayarshi, "daga ina kuke na ganku tare da yarinyarnan?" takai 'karshen maganar tana nuna Rabee'ah da fitowarta kenan daga cikin motar. Ko kallon inuwarta baiyiba bare ta samu amsa ya kashe motar yabi ta gabanta ya huce.


Da sauri taje tasha gaban Rabee'ah da ta nufi cikin gidan, "ke dan ubanki ina kuka je da mijina?" ja da baya Rabee'ah tayi ganin yadda take neman gwabjeta, sai ji sukai ance, "gidan ubanki suka je."


A tare suka d'ago don ganin me maganar, Abu Zarrin ne, yana tsaye ya hard'e hannuwanshi a 'kirji ya zubawa Rabee'ah ido kamar bashi yai maganar ba.

Sanin halinshi da Hafsa tayi bai mata wasa, ga wani kwarjini da yake mata kamar ba 'kanin mijintaba,shiyasa bata tanka mishi ba tabi byan Almash"

'Karasawa yai gabanta, "gaskiya yau Mamina kin azabtar dani da rashin ganinki, tunfa jiya da daddare rabon da naga 'kwayar idonki"

"Uhmmm to ai duk Kaine kake jamana, ni kaina 'kwayar idona tayi kewarka ya Abuuna "

"Ya zanayi? yanayin aikine, amma ina addu'ar Allah ya matso mana da nesa kusa, ko ma huta da azabtuwar ZUCIYA DA RUHINMU"

Murmushi kawai tayi, tai 'kasa da kanta.

"Au ba zakice Amin ba mami? kunyarki tayi yawa, toni nace Amin, Amin, Amin, sau ba adadi" dariya sukai a tare.

"Abba yace "yana nemanmu byan sallar isha"

"Ok tom, bari na shiga ciki nai sallah"

"Nima Masallaci zani, in na dawo ma had'u."




*****
After isha
Tuni sun hallara gidan Abba, suna zaune a falonshi, Rabee'ah tana gefenshi,

"Abinda yasa nace ina son ganinku, dama gobe in Allah ya kaimu za'a d'aura aurena "

Dan zabura Rabee'ah tai ta juyo ta kalleshi. "Aure kuma Abba?"

"Eh Mamina ko na tsufa ne?"

A sanyaye ta girgid'a kanta,

Abu Zarrin da Almash a tare suka had'a baki.

"Allah ya kaimu goben, Allah kuma ya sanya alkhairi "

"Amin, Mamina lafiya naga kinyi shiru?"

"Ba komai Abba, wace wacce zaka aura?"

" A can Ilorin muka had'u, mijinta rasuwa yai, ya barta da yara biyu mace da namiji, namijin zaiyi yayunki, (Dawud) macen kuma zata yiki (Amirah), abinne yazo a 'kurarren lokaci"

"Gaskiyane Abba, Allah ya sanya alheri"

"Amin mamina,"

Almash da Abu Zarrin sallama sukaiwa Abba suka fita, juyowa yai ya kalli Rabee'ah,

"Naji wata magana gurin Abu Zarrin nayi matu'kar farin-ciki daita, Mami kalleni nan ki gayamun kina sonshi?, don bazan d'au lokaci ba, burina yanzu na aurar dake, in mijin naki yana son kiyi karatun kyayi a gidan shi"

Sunkui da kai Rabee'ah tayi tana wasa da flower center carfet in d'akin.

"Alhamdilillah! shirunki ya tabbatar mun kina sonshi dama ya gayamun, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, tashi kije suna jiranki, ga wannan ki ri'ke a gurinki "

Kud'ine masu yawa tasa hannu biyu ta amsa tana godiya, tai mishi sallama ta fita.



Lokacin da suka isa gida, har zata huce Almash ya kirata ya bata furar da ya siyo da fruit, "ki dama mun furar ki kahon d'aki, su kuma kisa a fridge"

"Tom" ta juya ta shiga ciki, sai da ta fara jera kyan fruit in a fridge sannan ta juye furar a roba mai d'an fad'i ,sbd furar tana da d'an yawa, damata tayi, ta damu sosai, kana ta nufi d'akinshi zuciyarta na tsananta bugu.

Yana zaune kan kafet ya tan'kwashe 'kafafuwanshi yana lallatsa computer, turo 'kofar d'akin tai da sallama a bakinta,

Bai d'ago ba, a yadda yake ya amsa mata, har saida ta ajiye jug mai matu'kar kyau a gabanshi da d'an 'karamin cup, "yayana gashi" yanayin yadda tai maganar saida yajishi can 'kasan zuciyarshi, d'ago da kanshi yai ya kalleta idanuwansu suka had'e, wani irin kallo yake jifanta dashi, wanda shi kansa baisan yana yiba, zuciyarta taji tana tsananta bugu da sauri ta kau da idonta, sbd ba zata iya jure kallon 'kwayar idonshi ba, tana jefata cikin wani yanayi mara misaltuwa, bata dawo da hayyacin taba taji muryarshi, wacce tai sanadiyar 'kara jefata cikin kogin shau'kinshi, wani abu takeji yar yana tsagawa ta cikin mararta.

" 'kanwata ke bazaki shaba? taya kike tunanin yayanki zai iya sha byan 'kanwarsa bata shaba"

tana can duniyar da ta tafi, sukaji alamun za'a bud'e d'akin, tuni Rabee'ah ta wartsake ta fara rarraba ido cike da tsoro........






Author: Bebe'arth๐Ÿ˜˜
[4/19, 2:48 PM] BEBE'ARTH๐Ÿ˜˜: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_๐Ÿ’‹


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE SK MASHI


Manzon Allah (S.A.W) yace;

_"Yardar Ubangiji tana cikin yardar Iyaye, kuma fushin Ubangiji yana cikin fushin Iyaye._"

Allah Ubangiji kasa mu gama da Iyayanmu lfy, Allahuma Amin.


( *10*)
Rintse idonta tayi tana kiran sunan Allah, don tasan had'uwarsu ta yanzu baza tayi kyauba da Hafsa.

Shikwa Almash mai da kanshi 'kasa yai yaci gaba da abinda yake, sai jin muryar Abu Zarrin sukayi.

"Naga alamun rowar furar za'amun, byan a gabana aka bayar a dama shiyasa na biyo byanta"

Sanyayyar ajiyar zuciya Rabee'ah ta saki, ta bud'e idonta tana murmushi, Almash yana kallonta ta gefen ido, murmushi shima yai a ranshi yace "matsoraciya"

"Amma broth anyi kwad'ayayye yanzu furar ka biyo? aikwa ba rabonka a ciki"

Nikwa nake da rabo, tunda dai mamina ce ta dama ko kuma a biyamu kud'in damawar mu"

"Ko d'aya bazanyi ba,tunda ai ba 'kanwarka ce kai kad'aiba, ba don halinka ba dai tsiyayi kasha, kaci darajar *RABEE'AH* "
Wani zir taji, sakamakon ambatar sunanta da yai, d'ago kanta tai idanuwanta suka sar'ke da nashi ya kashe mata ido d'aya, da sauri ta janye idonta, don wani narkakken dafi ya kusa watsa mata, wanda da ta bari ya shigeta gab take da rasa nutsuwarta a gurin.

Janyo jug in yai, ya tsiyayi furar ya kaita bakinshi ya kur'ba girgid'a kai yayi sbd tsabar gard'inta.

"Big broth wai a ina kake siyo furar nanne? gard'inta yana sakani nishad'i"

"Gama sha tukun sai na gaya maka, 'kanwata dad'o mana cup"

Kafin ta mi'ke sai da ta fara mi'ka musu kud'in da Abba ya bata, kusan tare suka had'a baki.

"Kud'in meye wannan?"

"Abba ne ya bani d'azu, na d'auki wanda zanyi amfani dasu"

"OK" Abu Zarrin yace, sbd yasan koda yace ta d'auke ba zata d'auka ba, dama sun saba 'yar haka, indai

Please Login or Register in order to submit comment