Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"ke ki gayamun a gidan ubanwa Almash ya zama yayanki?" abin dariya yaso bawa Rabee'ah amma ta maze, banza tai mata taci gaba da yiwa Iffa wasa, yarinyar kwa sai dariya take, takaici ya turnu'ke Hafsa ta zuciya ta fusge Iffa daga hannun ta, "bani 'yata tunda ba 'yarki bace ai" murmushi tayi "aikwa iffa 'yatace, tunda 'yar yayana ce" daga haka ta mi'ke ta shige d'akinta don tasan ta kuma 'kular daita, kuma yadda take a 'kufulen nan tasan zata iya kaho mata wawura, tasan kuma tsaf zaneta zatayi, shiyasa ta gudu, aikwa ta barta tana ta huci, takaici ya isheta fuuuuuuuu ta haye sama tana huci ta bar su Iffah anan.


*****
Yana zaune cikin office inshi yana latse-latse cikin computer, idanuwanshi 'boye cikin siririn glas yai masa matu'kar kyau, turo 'kofar akai aka shigo, ko kad'an bai d'ago da kanshi ba, don tuni 'kamshin ta yakai mishi ziyara 'kofofin hancinshi, kujerar da take facing inshi taja ta zauna ta zuba mishi mayun idanuwanta, zuciyarta na 'kara kwad'aita mata shi, " barr na rasa me kuma zanyi ma ka gane yadda zuciyata ta mato akan sonka, batun yauba nake sanar dakai, amma kake ta wahalar dani ,zuciyata ta jigata Barr tana neman agajinka pls" takai 'karshen maganar cikin raunan niyar murya."

"Barr Jiddah ya kamata ki tashi zuciyar ki daga mafarkin da take, ba tun yauba nake gaya mata bata da gurbi ko kad'an a zuciyar Almash, mace d'aya ce take da wannan gurbin, don haka ki sara ramun ki fita harkata, tunda ba'a so dole"

"Tabbas ba'a so dole Barr, zan bar takura maka ba don na daina sonka ba, don nasan bazan ta'ba daina sonka ba, ina sonka, ina sonka, ina sonka, kuma na tabbata son da nake maka watarana sai yaimaka RANA" daga haka ta fice daga ofis in tana d'gar hawaye, ranshi a 'bace ya mi'ke ya fara harhad'a takaddunshi don tafiya gida tunda yamma ta kawo kai ......





Author: Bebe'arth๐Ÿ˜˜
[4/15, 11:05 AM] BEBE'ARTH๐Ÿ˜˜: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_๐Ÿ’‹


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE SK MASHI


An kar'bo daga Abdullahi d'an Umar (R.A), wani mutum yace da Manzon Allah (S.A.W)

" _Zanyi ya'ki," sai Annabi yace "kana da iyaye? " sai yace "na'am ina da iyaye"sai yace_) " _yimusu ya'ki" (ma'ana kaje kayi musu biyayya._)


*Makaran tana sai kuna ha'kuri da yanayin typing ina, ni kaina ina son yin typing kullum, amma hakan yana gagarata, amma zan 'ko'karta insha Allah ko byan two days ne haka zakuna samunshi insha Allah,ina godiya ina kuma alfahari daku da kuke bani aron lokacinku, Allah yabar 'kauna*

~Sumy Abdoul, nd Nafisa Musa, 'yar gatan Hudah na cigiyarku ina kuka shige ne?~

( *9*)

Tsaye suke bakin titi suna jiran mota, byan fitowarsu daga gidan Auntyn su Meenah sunje nuna mata anko.

"Nababa wai har yanzu kina jin abinda kikeji game da ya Almash kuwa dukda ya Abuu yana sonki?"
Hmmmmm Rabee'ah ta numfasa, "me za'a fasa Meenah? ai sai abinda yaci gaba, har ila yau in na ganshi sai naji wani zugi tun daga 'yan 'yatsun 'kafata zuwa 'kwa'kwalwata, ga tarin 'kaunarshi da kullum take mun katutu a zuciya, Meenah tun kanfa nai wayo nake fama da soyayyarshi, tun bansan meye soba, ada nai tunanin burgeni yake, sbd yadda nake shagala da kallonshi idan yai dariya ko murmushi kumatunsa suka lotsa, sbd Allah yayini da 'kaunar dimple, sai gashi ni bana dashi, shiyasa duk yayin da naga maishi nakan shagala da kallonsa har naji yana burgeni, to shima nai tunanin hakanne nake ji game dashi, ashe soyayyace tamun tsiro mai girma, wanda da nasan sanda zuciyata zatamun haka da ban barta tayi ba, Amma na binne soyayyar ya Almash acan 'kasan zuciyata, bana fatan abinda zai tasomun daita ko kad'an, na d'aukko ya Abuu na na d'orashi a sama, sbd yaya Almash tuni ya dad'e da haramta gareni."Takai 'karshen maganar cikin raunanniyar murya.

Hmmmm, Meenah ta numfasa "in so cutane ha'kuri magani ne, dama ba duk abinda bawa yake so yakan samu ba, Allah yana jarabtar bawansa a duk sanda yaso, Allah ya tabbatar miki da alkhairi cikin rayuwarki"

"Allahuma Amin" dai-dai nan Almash da yazo hucewa ya hangosu yai parking a gabansu, dama tun d'azu take jin sauyin bugun zuciyarta yana sauyawa, ashe shine yake tunkaro su, d'ago idonta tai ya sauka cikin 'kwayar idonshi by an ya zuge glass in motar, a lokaci d'aya yanayin bugun zuciyarsu ya sauya, da sauri ta kawar da 'kwayar idonta taja hannun Meenah suka 'karasa gaban motar, gidan gaba ta shiga, Meenah ta shiga baya.

Ko kad'an baiji dad'in d'auke 'kwayar idonta da tayiba, saboda wani irin yanayi yajishi yayin da yake kallon k'wayar idonta, Meenah ce ta katse mishi tunani, "yaya ina wuni?"
"lfy qalau Amarsu, biki kuma ya 'karato Allah Ubangiji ya sanya alkhairi" murmushi tai ta sadda kanta 'kasa, Amma fa a zuciyarta tunkan yakai 'karshen furucinshi ta rigashi da "Amin ya Allah"

Kallonta yai ta sunkui da kanta 'kasa tana wasa da zoben azurfarta, 'kasa yai da muryarshi "sai yanzu kuka dawo kenan?"

"Eh" ta bashi amsa ba tare da ta kalleshi ba, shikwa so yake ya kuma kallon 'kwayar idonta, "amma dai kinsan bana son dawowar gab da magariba ko?" "Kayi ha'kuri bansan zamu kai haka ba" gyad'a kai kawai yai, yamai da hankalinshi ga titi don yaga alamun baza ta d'ago kanta ba.



Sai da suka tsaya a hanya yasai kayan fruit da fura, shiyasa ana kiraye-kirayen salla suka shiga unguwar, Meenah aka fara saukewa, tunda aka karyo layin ta hango Saudah da Ummi a ranta tace "Jarababbu yanzu zasu isheni da mitar ban jirasu ba" kamar tasan abinda Meenah take sa'kawa kenan tace mata "ko me zasu cemiki kar ki tanka, laifine dai mun riga munyi" sauka tayi tana yiwa ya Almash godiya.


Hafsa ganin har magariba Almash bai dawo ba hankalinta ya tashi ,fitowa tayi barandar gidan tana ta kaiwa ta komo, tsayawa tayi cur yayin da taga me gadi ya bud'e masa get yana shigowa, a ranta cewa take "shida wace shegiyar ne?" yana yin parking fuuuu ta isa gurin motar tana huci, Rabee'ah zuciyarta sai dukan tara-tara take, shi ya fara bud'e motar ya fito, tunda ya hangota ya kuma murtuke fuska. Cike da masifa take tambayarshi, "daga ina kuke na ganku tare da yarinyarnan?" takai 'karshen maganar tana nuna Rabee'ah da fitowarta kenan daga cikin motar. Ko kallon inuwarta baiyiba bare ta samu amsa ya kashe motar yabi ta gabanta ya huce.


Da sauri taje tasha gaban Rabee'ah da ta nufi cikin gidan, "ke dan ubanki ina kuka je da mijina?" ja da baya Rabee'ah tayi ganin yadda take neman gwabjeta, sai ji sukai ance, "gidan ubanki suka je."


A tare suka d'ago don ganin me maganar, Abu Zarrin ne, yana tsaye ya hard'e hannuwanshi a 'kirji ya zubawa Rabee'ah ido kamar bashi yai maganar ba.

Sanin halinshi da Hafsa tayi bai mata wasa, ga wani kwarjini da yake mata kamar ba 'kanin mijintaba,shiyasa bata tanka mishi ba tabi byan Almash"

'Karasawa yai gabanta, "gaskiya yau Mamina kin azabtar dani da rashin ganinki, tunfa jiya da daddare rabon da naga 'kwayar idonki"

"Uhmmm to ai duk Kaine kake jamana, ni kaina 'kwayar idona tayi kewarka ya Abuuna "

"Ya zanayi? yanayin aikine, amma ina addu'ar Allah ya matso mana da nesa kusa, ko ma huta da azabtuwar ZUCIYA DA RUHINMU"

Murmushi kawai tayi, tai 'kasa da kanta.

"Au ba zakice Amin ba mami? kunyarki tayi yawa, toni nace Amin, Amin, Amin, sau ba adadi" dariya sukai a tare.

"Abba yace "yana nemanmu byan sallar isha"

"Ok tom, bari na shiga ciki nai sallah"

"Nima Masallaci zani, in na dawo ma had'u."




*****
After isha
Tuni sun hallara gidan Abba, suna zaune a falonshi, Rabee'ah tana gefenshi,

"Abinda yasa nace ina son ganinku, dama gobe in Allah ya kaimu za'a d'aura aurena "

Dan zabura Rabee'ah tai ta juyo ta kalleshi. "Aure kuma Abba?"

"Eh Mamina ko na tsufa ne?"

A sanyaye ta girgid'a kanta,

Abu Zarrin da Almash a tare suka had'a baki.

"Allah ya kaimu goben, Allah kuma ya sanya alkhairi "

"Amin, Mamina lafiya naga kinyi shiru?"

"Ba komai Abba, wace wacce zaka aura?"

" A can Ilorin muka had'u, mijinta rasuwa yai, ya barta da yara biyu mace da namiji, namijin zaiyi yayunki, (Dawud) macen kuma zata yiki (Amirah), abinne yazo a 'kurarren lokaci"

"Gaskiyane Abba, Allah ya sanya alheri"

"Amin mamina,"

Almash da Abu Zarrin sallama sukaiwa Abba suka fita, juyowa yai ya kalli Rabee'ah,

"Naji wata magana gurin Abu Zarrin nayi matu'kar farin-ciki daita, Mami kalleni nan ki gayamun kina sonshi?, don bazan d'au lokaci ba, burina yanzu na aurar dake, in mijin naki yana son kiyi karatun kyayi a gidan shi"

Sunkui da kai Rabee'ah tayi tana wasa da flower center carfet in d'akin.

"Alhamdilillah! shirunki ya tabbatar mun kina sonshi dama ya gayamun, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, tashi kije suna jiranki, ga wannan ki ri'ke a gurinki "

Kud'ine masu yawa tasa hannu biyu ta amsa tana godiya, tai mishi sallama ta fita.



Lokacin da suka isa gida, har zata huce Almash ya kirata ya bata furar da ya siyo da fruit, "ki dama mun furar ki kahon d'aki, su kuma kisa a fridge"

"Tom" ta juya ta shiga ciki, sai da ta fara jera kyan fruit in a fridge sannan ta juye furar a roba mai d'an fad'i ,sbd furar tana da d'an yawa, damata tayi, ta damu sosai, kana ta nufi d'akinshi zuciyarta na tsananta bugu.

Yana zaune kan kafet ya tan'kwashe 'kafafuwanshi yana lallatsa computer, turo 'kofar d'akin tai da sallama a bakinta,

Bai d'ago ba, a yadda yake ya amsa mata, har saida ta ajiye jug mai matu'kar kyau a gabanshi da d'an 'karamin cup, "yayana gashi" yanayin yadda tai maganar saida yajishi can 'kasan zuciyarshi, d'ago da kanshi yai ya kalleta idanuwansu suka had'e, wani irin kallo yake jifanta dashi, wanda shi kansa baisan yana yiba, zuciyarta taji tana tsananta bugu da sauri ta kau da idonta, sbd ba zata iya jure kallon 'kwayar idonshi ba, tana jefata cikin wani yanayi mara misaltuwa, bata dawo da hayyacin taba taji muryarshi, wacce tai sanadiyar 'kara jefata cikin kogin shau'kinshi, wani abu takeji yar yana tsagawa ta cikin mararta.

" 'kanwata ke bazaki shaba? taya kike tunanin yayanki zai iya sha byan 'kanwarsa bata shaba"

tana can duniyar da ta tafi, sukaji alamun za'a bud'e d'akin, tuni Rabee'ah ta wartsake ta fara rarraba ido cike da tsoro........






Author: Bebe'arth๐Ÿ˜˜
[4/19, 2:48 PM] BEBE'ARTH๐Ÿ˜˜: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_๐Ÿ’‹


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE SK MASHI


Manzon Allah (S.A.W) yace;

_"Yardar Ubangiji tana cikin yardar Iyaye, kuma fushin Ubangiji yana cikin fushin Iyaye._"

Allah Ubangiji kasa mu gama da Iyayanmu lfy, Allahuma Amin.


( *10*)
Rintse idonta tayi tana kiran sunan Allah, don tasan had'uwarsu ta yanzu baza tayi kyauba da Hafsa.

Shikwa Almash mai da kanshi 'kasa yai yaci gaba da abinda yake, sai jin muryar Abu Zarrin sukayi.

"Naga alamun rowar furar za'amun, byan a gabana aka bayar a dama shiyasa na biyo byanta"

Sanyayyar ajiyar zuciya Rabee'ah ta saki, ta bud'e idonta tana murmushi, Almash yana kallonta ta gefen ido, murmushi shima yai a ranshi yace "matsoraciya"

"Amma broth anyi kwad'ayayye yanzu furar ka biyo? aikwa ba rabonka a ciki"

Nikwa nake da rabo, tunda dai mamina ce ta dama ko kuma a biyamu kud'in damawar mu"

"Ko d'aya bazanyi ba,tunda ai ba 'kanwarka ce kai kad'aiba, ba don halinka ba dai tsiyayi kasha, kaci darajar *RABEE'AH* "
Wani zir taji, sakamakon ambatar sunanta da yai, d'ago kanta tai idanuwanta suka sar'ke da nashi ya kashe mata ido d'aya, da sauri ta janye idonta, don wani narkakken dafi ya kusa watsa mata, wanda da ta bari ya shigeta gab take da rasa nutsuwarta a gurin.

Janyo jug in yai, ya tsiyayi furar ya kaita bakinshi ya kur'ba girgid'a kai yayi sbd tsabar gard'inta.

"Big broth wai a ina kake siyo furar nanne? gard'inta yana sakani nishad'i"

"Gama sha tukun sai na gaya maka, 'kanwata dad'o mana cup"

Kafin ta mi'ke sai da ta fara mi'ka musu kud'in da Abba ya bata, kusan tare suka had'a baki.

"Kud'in meye wannan?"

"Abba ne ya bani d'azu, na d'auki wanda zanyi amfani dasu"

"OK" Abu Zarrin yace, sbd yasan koda yace ta d'auke ba zata d'auka ba, dama sun saba 'yar haka, indai Abba ya bata kud'i iyakacinta ta d'auki wanda zatai amfani dashi ta bashi sauran, shi kuma sai yake tara mata su a Account inta.

"Jeki ki d'aukko cup in sai kizo muyi shirin bikin Abba na gobe." Cewar Abu Zarrin,

Batai magana ba sai turo baki da tayi ta fice.

Kallon Almash Abu Zarrin yai. "Big broth munfa gama magana da Baba, satin sama za'a kai kud'ina da saka rana."

Duk da yasan maganar sai da yaji fad'uwar gaba, ya rintse idonshi yana 'ko'karin saita nutsuwarshi, wanda lokaci d'aya taso kufce mishi.

"Ai munyi maganar d'azu da safe dashi, Ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi" yakai 'karshen maganar yana jin wani d'aci a ma'kogaron sa.

"Amin"

'Kara sukaji an saki, a lokaci d'aya ta kuma ziyartar musu kunnuwa, mi'kewa sukai a tare suka fice.

Rabee'ah zaune bakin kitchen ri'ke da 'kafarta, hawaye sha'be-shab'e duk ya wanke mata fuska, da sauri Abu Zarrin ya 'karasa gefenta yana tambayarta , "me ya faru"

Cikin kuka tace "fad'uwa nayi na gurd'e kuma 'kafata tana tamun zafi"

Almash ne ya 'karasa gurin yasa hannu ya fara danna mata 'kafar,

Wani iron shock da zafi a lokaci d'aya suka kai mata ziyara 'kwa'kwal warta, ta saki wata siririyar 'kara, Abu Zarrin sai sannu yake mata"

"Ina jin buguwa ce, gashi dare yayi da munje an duba miki, amma ki shafa camfo a gurin, da safe in yana miki zafi sai muje a duba miki,sannu Allah ya sawa'ke" daga haka ya juya yabar gurin.


Kallonta yai sai hawaye take d'igarwa, cike da tausayawa yace. "Sannu kinji mamina! tashi muje d'aki"

Hawaye ta matse. "Zafi take mun bazan iya tashi ba." Bai magana ba ya sunkuceta ya nufi d'akinta, akan gadonta ya ajiyeta, ya d'ago da kanshi yana mata sannu.

"Bari naje na zubo miki abinci kici kisha magani,sai ki shafa camfo in"
'Daga mishi kai tayi, yasa kai ya fice.


Bayan ya barsu a gurin, tafiya yake zuciyarshi tana mishi tu'ku'ki, wani irin abu yake ji wanda shi kanshi bazai iya fassarashi ba.
'Dakin Hafsa yasa kai, yana murd'a handle in 'kofar ya shiga, hangota yai mi'ke akan gado, fararen 'kafafunta santal a mi'ke, gefenta ya samu ya zauna ya rafka tagumi, tana jinshi amma tai likimo kamar bacci take,ganin yayi tagumi yasa ta mi'kewa, hannuwanshi duka biyun ta ri'ke ta zuba mishi ido, soyayyarshi tana ratsa duk wani sa'ko na zuciyarta gami da tarin zazzafan kishinsa.

'Dago da kanshi yai yana kallon farar kyakkyawar fuskarta, soyayyarta tana nan a ajiye a zuciyarshi, amma wani abu yake ji game da Rabee'ah wanda ya da'de da rufe babinshi amma yanzu yana neman fin 'karfinshi, abinda yake kuma rikita shi sa'kon da yake d'iba cikin 'kwayar idanuwanta. 'Dan girgiza shi tayi. "Honey me yake damunka na ganka cikin damuwa?" lasar le'benshi na sama yayi.

"Ba komai hafcyna, tarin gajiya ce da kuma yunwa, nayi tunanin bacci kike yine, bani abincin"

Karyar da kai tayi,
"Honey kana bani damuwa, idan zuciyata ta buga Kaine, kasan ina matu'kar kishinka, wani irin d'aci nake ji idan na ganka da wannan yarinyar, nakan ji zazzafan kishi a kanta, wlh Almash zan iya yin komai akan sonka"

"Nasan kina kishina, amma kishin da kike nunawa akan Rabee'ah yayi yawa, kina zubda mutuncin ki ne a gurinta da girmanki, in kin manta bari na tina miki, da Mahaifiyar Rabee'a da Mahaifiyata Uwa d'aya suke Uba d'aya, Mahaifiyarta ita ta ri'kemu tun muna yara, ita da mahaifinta suka maidamu tamkar 'ya'yan cikinsu, har byan ranta Mahaifin Rabee'ah ganinmu yake a 'ya'yanshi, don haka ya kamata ki taka burki, Rabee'ah 'kanwa tace ina da hurumin da zan d'auketa naje duk inda nake so daita ba tare da wani ya tambayan inda muka jeba, a gaban idonki ko Abu Zarrin bai tambayi inda muka jeba, saike saboda kin raina ni, to naga abun naki ba mai 'kare bane duk randa kika kuskura kika 'kara yimun wani abu akan Rabee'ah sai kin gane kuranki ,aini ba sakaran Namiji bane."

Tunda ya fara maganar take kallonshi, yana dasa aya, bata jira komai ba ta jefa bakinta cikin nashi, kising inshi take tana kallon 'kwayar idonshi tana watsa mishi sa'kunan ban ha'kuri, da ganin yanayin Almash nasan ha'kurin Hafsa ya kar'bu, don shi ya kar'beta yaci gaba da gashi.




*****

Washe gari sumul 'kalau ta tashi 'kafar bata mata zafi, dama raki ne irin na Rabee'ah.

Da sassafe Almash ya fita, sbd zasui zaman court. Abu Zarrin ne dai bai fita da wuri ba, sai wajen 12:00pm ya fito.
A palo ya tadda Hafsa tana bawa su Iffa priso, zama yai suka gaisa, d'aukan Irfan yayi da yake ta mi'ko mishi hannu, dubanshi tayi.
"Kayi ha'kurin abinda ya faru jiya"

"Ai ya huce, abinda nake so ki gane baki isa kin shiga tsakanin Almash da Mami ba, kamar yadda itama bata isa ta shiga tsakaninmu ba, yadda kike 'kanwa a garemu itama haka take, don haka a matsayinki na 'kanwata dole na gaya miki gaskiya, ba haka ake kishiba, kishin da kikema darect zan iya kiranshi da hauka, tunda taya kike tunanin Big Broth zai iya had'a soyayya dani? tun tana 'kan'kanuwa nake jigila da soyayyarta, ke koda yana sonta zai iya danne soyayyar don ya sanyamu farin-ciki"

"Ai na fahimta, dama sharrin shaid'an ne, hakan bazai sake faruwa ba." Bai magana ba ya mi'ke ya nufi d'akin Rabee'ah, 'kwan'kwasa 'kofar yayi, saida ya 'kan'kwasa sau uku, sannan yaji muryarta. "Shigo". Murd'a handle in ofar yai ya shiga.

'Dago da kanta tayi, ya sauka cikin 'kwayar idanunshi, ganin idanuwanta yayi jajir duk sun kumbura sun tattashi.
"Kukan me kike Mami?'kafarce har yanzu?"

"A'a ba 'kafata bace, Umma na tuno, yanzu wai yau za'a d'aura auran Abba don babu ran Umma."

"Ai Addu'a zaki mata ba ki zauna kina kuka ba, Aure kuma idan yana cikin 'kaddarar mutum to wajibi ne sai yayi, koda da ran Umma in ta kama Aure zaiyi, don haka ki daina damun kanki,kiyiwa Umma Addu'a, kinci abinci?"

Girgid'a mishi kai tayi, ya tashi ya fita domin had'o musu break in, don shima baiyiba.



'Karfe biyu da rabi na yamma aka d'aura auran Abba da Sakina (Ummi) Amma sai washe gari zata tare. Abba ya gyare gidan sosai, yayiwa Maminshi d'akinta daban, komai na ciki maroon colour ne, d'akin yayi matu'kar birgewa ainun, amma Rabee'ah tace "ba zata koma ba sai sun gama cin amarcinsu, hhhhhhh.......





Author: Bebe'arth๐Ÿ˜˜
[4/28, 2:34 PM] BEBE'ARTH๐Ÿ˜˜: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_๐Ÿ’‹


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE SK MASHI



Manzon Allah (S.A.W) yace.

" _Kabi Mahaifiyarka da Mahaifinka, kuma ka kyautatawa 'yar uwarka da d'an uwanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa._(Nisa'i, Abu Dawuda, Tirmuzi, Ahmad da Hakim suka rawaito shi.)



( *11*)

After two weaks.

Rabee'ah ta had'a komai nata ta koma gidan Abba, zuciyar Hafsa ta 'kara samun nutsuwa sosai da sosai.

Ummi tana da kirki sosai, lfy qalau suke zaune, jininsu yazo d'aya da Amira, yadda Ummi ta d'auki Amira haka take d'aukan Rabee'ah, hakanne yasa Abba shima baya bambanta su ko kad'an, shikwa Dawud ba mazaunin gidan bane, gidanshi da ban saidai yazo ya gaishesu ya tafi.



*****
Tu'ki yake cikin kasala, wani irin yanayi yake ji a jikinshi na kewa, wani abu ne yake fusgarshi tun daga 'kasan zuciyarshi, yau rabonsa da ya sanyata a idanunshi tun randa ta taho gida, koda yaje gaida Abba baya bari su had'u sbd gocewa abinda yake neman fin 'karfinshi, Amma yau kam yanayin da yake jinshi sam bazai iya jurewa ba.

Juya motar yai ya d'auki hanyar unguwarsu. Ummi ya tadda a palo ita kad'ai, byan sun gaisa ya tambayeta Rabee'ah, tace "Tun safe suka fita rabon invitation in Meenah, kaga yanzu Abu Zarrin ya mi'ke yana ta tsaki ya gaji da jiranta, sai cemasa take gasunan." Jiki a sanyaye ya mi'ke yai mata sallama ya fita.

A barandar gidan ya taddata a tsaye ita da Abu Zarrin, cakewa yayi daga bakin gurin yana binta da kallo, wani maganad'isun madarar 'kaunarta na 'kara shiga RUHINSHI.

"Haba yaya Abuna kar kai fushi dani, zan iya jure komai amma banda fushinka, pls kayi mun magana ko zanji sanyi a raina"

Still shiru ya kuma mata, d'aga idon da zatai ya sauka cikin na Almash, murmushi suka sakarwa juna a tare, ta narkar da idonta, wanda ita bama tasan sanda tayi ba.

"Yauwa yayana zo ka tayani bawa yaya Abuna ha'kuri, yayi fushi dani" matsowa yayi inda suke ya kalli Abu Zarrin. "Haba broth me ya had'aka da Mamin taka? koma dai meye ma ina nemawa 'kanwata afuwa."

" Wai tun safe suka fita rabo, sai yanzu suka daho, tasan bana iya cin abinci ba tare da ita ba, rabon ma duk wahalar banza ce, ka gamaiwa mutum wahala, wani in bikinka ma yazo ko ka gayyaceshi bai zama lallai yazo ba."

"Hakane yaya Abuna kayi ha'kuri pls muje kaci abinci"
Bai magana ba ya juya ya shiga ciki, juyowa tai ta kalli Almash da ya zubawa bakinta ido, yankan bakinta yana matu'kar birgeshi. "Yayana muje Kaima kaci abinci"

Matsowa yayi gab daita" 'Kanwata ba kya jin wani yanayi game dani a zuciyarki" dabarbarcewa tayi, bakinta na rawa tace "Ni ba abinda nakeji, da sauri tabar gurin.




****
Anyi bikin Meenah sunsha shagali sosai, aka

Please Login or Register in order to submit comment