Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

MASHI


Ciwon ido

Man habbatus sauda ,a dinga kewaye idon dashi ,Ana kuma shanshi a shayi ko Kara's .


(5)

"Suna na Rahama, Ana kirana da reesy, mu biyar mahaifanmu suka haifa,zainab ce babba sannan ni, tun tasowar mu mahaifinmu sam baisan cinmu ba, shanmu ba, bare sitirarmu, hakama mahaifiyar mu, dai-dai da sabulun wanka in muka ta'ba mata sai tai mana Allah ya Isa, sun Riga sun sakar mana ragamar rayuwar mu ,tun muna 'kananu, da bin gidaje-gidaje muke samun d'an abinda xamu ya'fa'wa cikinmu, a haka har xainab tai saurayi, shine ya xamo komai namu, har mahaifanmu suna jin da'dinshi .


Bamuyi aune ba,sai ganin zainab mukai da ciki, hankalinmu yai matu'kar tashi,tun daga ranar zainab ta shiga matsin rayuwa, kullum baba cikin dukanta yake ga masifa da kullum sai ya'yita a filin tsakar gidanmu, sai kace ba shine ummul aba isin faruwar komai ba.

A haka zainab taci gaba da rayuwa har watan cikinta ya isa haihuwa, ranar da xata haihu baba cewa yai "a kaita ban d'aki ta haihu baza'a haifa mishi shege a tsakar gida ba."
Zainab tana haihuwa....Allah ya amshi ranta,tasha wuya sosai, tun daga kanta tsoro ya shiga raina na 'kudurta a raina baxan ta'ba yarda da namiji ba, don gudun irin wahalar da zainab taci.

Haka muka cigaba da rayuwa yau ba'ki gobe tsunma, domin har yanxu mahaifan mu basu saduda ba, har na had'u da hjy jamila itace sanadiyar fa'd'awa ta harkar nan ta dinga sakar mun kud'i sosai tad'au ragamar karatuna hakan yasa na sakar mata jikina nima nake faranta mata sosai,kud'in da take sakarmun dasu nake taimakon 'kannena domin gudun kar su fad'a rayuwa irin tamu ni da zainab, sosai nake kula dasu har taho wata makarantar nan, yaran da na 'batawa rayuwa a cikin makarantar nan Allah ne kad'ai yasan yawansu kuma ko wacce da amincewar ta ba fin 'karfinsu naiba, na tabbata xunuban da muka kwasa ni da zainab mahaifanmu suna da babban kamasho a ciki domin sune silar afkuwar komai, basu ri'ke amanar da Allah ya basu ba,


Rabee'ah naki iyayan da nawa iyayan na tabbata akwai ban-banci don haka ki ri'ke 'kimarki da mutuncin ki ,karki ci amanar iya'yanki ,ba Wanda zai jahoki ya la'la'ta miki rayuwa sai kin bada a'manna, ni kuma ki tayani da addu'a Allah ya kawo hanyar shiryuwa ta"


Daga haka ta share hawayen fuskarta ta juya xata tafi, sakamakon hjy jamila da tai mata horn,

Ta baya Rabee'ah tai sauri ta rungumeta tana kuka tace "xan tayaki da addu'a sosai aunty, amma kema sai kinyi ya'ki da xuciyarki da kuma shaid'an, Allah ya d'oraki a Kansu ya rabaki da wannan mugun abu ,xan taimiki addu'a a koda yaushe, kema ki dage sosai"

"Tom shikenan Rabee'ah na gode sosai, ki kula da rayuwarki ina jinki tamkar 'kanwa'ta, Allah ya kareki daga sharrin masu hali irin nawa" daga haka ta juya ta tafi domin hjy jamila sai doka mata horn take cike da 'bacin rai.




Tun barin aunty Reesy schl, Rabee'ah bata 'kara amicewa da kowa ba, bata da wasu 'kawaye na jiki da ya huce su meenah da saudah, kowa ya sansu tare, Abu zarrin yana yawan kawo mata ziyara amma banda Al'mash ko kad'an bai ta'ba xuwa ba.


Suna cikin xana jaraba'war qualified akai bikin Al'mash shi da hafsa, soyayya mai 'karfi ce tsakaninsu kuma 'yan uwane, 'yar 'kanwar mahaifinsu ce, Rabee'ah taso xuwa bikin sai gashi suna exam dukda indai ta tuno Al'mash xai aure,ta kanji xuciyarta a cunkushe kuma bata san dalilin hakan ba.


shikwa Abu zarrin, zuciyarshi ta cika da 'kaunar Rabee'ah jira yake kawai tai candy ya sanar mata, Amma dukkan wasu alamu na love yana nuna mata su.



Randa akai musu hutu, da huri Abu zarrin yazo d'aukar su ,tunda suke zuba kayansu cikin but yake binta da kallo, har suka kammala suka shige cikin motar, har ya fa'ra Jan motar ya juyo ya kalleta yace "nayi fa kewar ki mamina da yawa, don har nafi Umma da Abba kewarki."murmushi tai ta juyo ta kalleshi, kallon da yake matu'kar birgeshi tace "Anya kwa ka kai Abba na kewa'ta da dai Umma da ya Al'mash kace zan yadda don ita Umma ya Al'mash kad'ai take kewa."

Murmushi yai yace "Aikwa wannan karan Umma tayi kewar ki sosai tun safe take ta hidimar tararki"

"Da gaske kake ya abuu na?"

'Daga mata kai yayi, ta saki kyakkyawan murmushi Wanda yake nuna taji dad'in maganarsa.


Saida suka fa'ra sauke su sauda da meenah don gidansu ne a farko, sannan suka 'karasa gida, tun daga soro Rabee'ah take rangad'awa Umma Kira, "Umma na kina ina? Nayi kewarki irin da yawa d'in nan"

Suna xaune ita da Al'mash suna hira, taji muryar d'iyar ta'ta murmushi ne ya kubcewa fuskarta, ta mi'ke tana "gani nan ma'mina nima nayi kewarki, da gudu ta 'Karasa jikin Umma ta ru'kun 'kumeta tana dariya, Umma ta ja'ta sukai d'aki, tana kwance kan ka'fad'ar ta, Abu zarrin ne ya shigo, Umma ta shiga yimai sannu da xuwa, guri ya samu ya xauna yacewa Umma "ina ka'yan tar'bar ta'mu?"

Mi'kewa Umma tai tana "bari na kawo muku" Rabee'ah kwa ta shige can cikin d'aki don sauya uniform in jikinta,

Ala la ne, Umma taiwa Rabee'ah,don ta'san tana matu'kar 'kaunarshi, ita da Abu zarrin suka zage suna cin ala lansu, ko kad'an Al'mash bai d'ago ya kallesu ba, shi Sam baiji dad'in dawowar Rabee'ah ba, don a ganinshi a ta'kura ce, sunan da ya rad'a mata, don tana hanashi sakewa da Umma, duk da ba shiga harkar ta yake ba, halin ko in kular da ta nuna mishi ya 'kona mai rai ainun, d'agowa yai ya kalleta yace "ke watakan baki iya gaida mutane ba, bare ki kulasu, don kina ganin kin fara girma."

'Dan cin mur tai, ta kau da fuska, domin wani irin haushinsa take ji,

Umma ce tace "Au da'ma Baku gaisa ba? Aini nasha da na fita kun gaisa, Amma anyi ja'irar yarinya, mami ina zaki kai miskilan ci?"

"Tom ai shine Umma tunda muka shigo yake tasha mana kunu, ko kallon mu baiba, ko don yana ganin yayi aurene oho, yasha kurumunsa indai aure ne, muma mun kusa yi, ko ya abuu na?"

"Haka ne ma'mina gaya mishi dai, kamar yaune muma mun wuce gun"

'kwafa Al'mash yai kawai ya mi'ke ya fice,yana mitar yaushe rabee'ah ta raina shine, shi da ba sakar mata fuska yake ba.

Umma kwa ta rasa me zata ce musu, sai ido da ta zuba musu, suna ta cin abincin su, suna 'kya'kyata dariya.







Author:Bebe'arth😘
[4/11, 1:03 PM] BEBE'ARTH😘: *Bebe'arth*



*RABEE'AH*


RABEE'AH❤
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_💋


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE SK MASHI


Karyewar gashi

Garin habbatus sauda ,jurjur ,da cokali d'aya na kal ,da xaitun ,a had'a a dinga shafawa.

(6)

Har hutunsu ya kusa 'karewa, sannan taje gidan Al'mash ,kadaran kadhan hafsa ta tar'bi Rabee'ah, bata wani jima ba ta tashi zata tafi ,dai-dai nan Al'mash ke sakkowa daga bene, ya tsuke cikin cort ba'ki da fari, yai masa matu'kar kyau, murmushi ya sakar mata, Wanda ya haddasa mata buga'war xuciya, dimple in da take matu'kar so suka lo'ba a kumatunshi, 'ka'kalo murmushi itama tayi tai masa, ta dur'kusa tana gaisheshi, yace "yasu Umma da Abba, da abuu zarrin?"

"Duk suna nan 'kalau, suna gaisheku, ya abuu na kuma baya nan sun tafi Kaduna yin wani aikin .

"Af mantawa nai, Nima na tambayeki, badai tafiya xaki ba ?"

Lumshe idonta tai, saboda wani yanayi da take jin zuciyar ta a ciki, tace "Eh tafiya zan, Umma na can na jirana"

"OK tom muje, nima gidan na nufa"cewar Al'mash, ya kalli hafsa da ke ta jifansu da harara yace " sai na dawo"

Ta tafas, bata cemasa ba, har suka fice...





****

Hutun da akaiwa su Rabee'ah Wanda daga shi sai dai su zana weac, hutu ne da tayishi ba inda taje, kullum tana jikin Umman ta suna hira, yawanci cikin hirar takan yimata nasihu masu ratsa jiki.


Randa hutunsu ya 'kare, Abuu zarrin zai tafi kaita,har taje jikin motar, ta juya ciki da gudu, ta ru'kun'kume Umma tana kuka, itama Umma bata san dali liba sai jinta tai tana zubda hawaye, ta shiga 'karai mata wasu nasihun ,ta janyota, ta kawota har gaban motar, ta bud'e ta shiga, abinda Umma bata ta'ba yiba kenan sai ranar,

"Ki kula da Rayuwa Rabee'ah, kidinga tunawa in yau mune gobe ba mu bane, Rayuwar cikin DUNIYA takan sauya'wa a koda yaushe, ki ri'ki tarbiyar da na baki koda byan raina ne, kici gaba da ha'kurin zama da mutane, Allah yashi miki al'barka, ya al'barkaci dukkanin rayuwar ki, ya Kuma kaiku lafiya, Amin" daga haka ta koma tciki tana zubda hawaye,


Kuka Rabee'ah ta fashe dashi, Wanda har suka isa makarantar tana yinsa, Abu zarrin yna aikin rarrashi, bai baro makarantar ba ,har sai da yaga ta saki tukunna.




*****

*conteneau of the novel*

Zuciyarshi axalxalar shi take ya sanar mata da d'inbin soyayyar da yake mata, wata zuciyar kuma na yimishi hani, da ya 'kara ha'kuri, kamar yaune xatai candy, shawarar ha'kurin ya d'auka, har suka kammala cin abincin,suka rabu akan sai yaxo, don gobe sai ya rigasu fita.




***

Washe gari, da wuri Rabee'ah ta kammala shirinta, har ma sunyi sallama da Abban ta ya fita, fitowar Al'mash kawai take jira.

Tana nan zaune a falo suka fito shi da hafsa, sanye yake cikin dakakkiyar shadda marun colour, tayi masa kyau sosai, tsayawa yai yana jiran hafsa ta 'karasa karya mishi hula, ganin haka yasa Rabee'ah mi'kewa ta fara fita da kayanta bakin mota, tsayawa tai tana jiranshi ya fito, can sai gashinan, hafsa biye dashi, key yasa ya bud'e motar, ya bud'e mata but in ta zuba kayanta a ciki, ko kallon inda hafsa take batai ba, ta bud'e murfin motar ta shiga.

Hafsa ce ta kalleshi tace, "Honey bansan me naiwa mami ba, sam bata kula ni "

Baice mata komai ba, ya kira Rabee'ah, fitowa tai daga cikin motar, taje gurin da suke a tsaye, kallonta yai, ta sadda kanta 'kasa tana wasa da zoben azurfar hannunta, yace "mami me yasa bakya kula hafsa?"

Bata san dalili ba, kawai sai jitai 'kwalla ta tarar mata a ido, 'kara 'kasa tai da kanta tace "ba komai yaya"

"Amma kinsan abinda kike ba dai-dai bane, kuna zaune gida d'aya ace bakya kulata, ai daraja ta zaki duba, kuma kinsan da Umma tana nan baxa taji dad'i ba"

"Hakane yaya, kayi ha'kuri bazan kuma ba, kema aunty hafsa kiyi ha'kuri hakan bazai sake faruwa ba"

Murmushi hafsa tai tace "babu komai mami, in dama ga'bar ce bana so, tom honey sai ka daho, bari na shiga ciki, naji bayana yana mun ciwo, may be kan ka daho babynka ya sauka"

Saurin ri'kota yai yana shafa cikinta yace, "Da gaske kike cwt? Ko mu tafi asibiti?"

Dariya tai tana fisgewa daga ri'kon da yai mata, tace "Da wasa nake honey, sai ka daho" daga haka tai saurin shigewa ciki, shikuma yabi ta da kallon love.

Rabee'ah da tuni ta koma cikin mota, taji hawaye suna tinsiri bisa kuncinta, wanda bata san dalilin xuwansu ba, ga zuciyarta sai tiri ri take mata, ganin ya taho ne yasa ta saurin goge fuskar ta ta janyo hular hijabinta ta rufe fuskarta, baice mata uffan ba, ya shigo yaja motar suka tafi.


Suna tsaka da tafiya, dukkaninsu sunyi shiru, tamkar ruwa ya cinyesu, ko wanne da irin tunanin da yake a zuciyarshi, wayar Al'mash ce ta hau ringing, da axama ya sanya hannu ya d'auka don ganin me kiran nasa , cwt broth yagani rubuce kan sicring in wayar, d'agawa yai had'e da sallama, Amsa mishi sallamar Abuu yayi kana yace "broth kun isa ne?"

"A'a muna hanya"

"Ok tom, bani mami"

"Ok gata" ya mi'ka mata wayar ansa tayi, cikin sanyin muryar ta tace, "Hello yaya abuu na "
"Uhmmm mami na ykk?"

"lfy 'kalau, ya aikin?"

"Alhamdlillh, sai tarin kewar ki da ya daman"

Dariya tai tace "kai yaya abuu na, sai kace ba d'azu muka rabu ba"

"Ke a gurinki ne 'daxu, nikwa a guna kamar shekaru ne, gashi zaki kuma yimin nisa, amma gobe insha Allah zaki ganni"

"Tom shikenan ya abuu ina nan ina tsimayinka "


"Ok sai naxo, Allah yakaiku lafiya"

"Amin" kana suka ajiye wayar"

Mi'kawa Al'mash wayar tai, kar'ba yai ya ajiye ko kallon inda take baiba, sbd wani irin tu'ku'ki yadinga ji a ransa, wanda baisan dalilin haka ba ......






Author:Bebe'arth😘
[4/11, 1:10 PM] BEBE'ARTH😘: *Bebe'arth*



*RABEE'AH*


RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_💋


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE SK MASHI


Manxon Allah (S.A.W) yace

"Habbatul baraka ,ta isheku maganin komai ,banda tsufa da mutuwa ."


(7)

****

Filin makarantar yalwa bording school cike yake da d'alibai wa'yanda sukai candy, ko wanne ka gani zuciyarshi cike take da farin ciki, wanda hakan ya'ki 'boyuwa har sai da ya fito kan fuskar su.


Tsaye suke jikin motar su Almash, bakin Rabee'ah ya'ki rufuwa, tana taiwa Iffah da Irfan wasa, (yaran da Hafsa ta Haifa, twince, sunyi wayo sosai.)

"Ki rabu da su iffah, kije Ku gama bankwana mu tafi, ki had'o kan su Meenah ma."cewar Abu zarrin.Kan ta bashi amsa, taji muryar Zuhairah tana cewa "Nababa tun 'dazu nake nemanki, muna ta d'aukar picture's da su Sauda babu ke."

Jan hannunta Rabee'ah tai tana "taho muje"

'Daukar picture's suke tayi na tarihi, zuba selfie suke abinsu, ji suke tamkar karsu rabu, don bai zama lalle su 'kara ganin juna ba, may be in zasu had'u ma sai an d'au shekaru aru-aru, bankwana suke tayi, wa'yansu harda kukan su.

Sai da suka gama bankwana da 'kawayen su, kana suka taho, ko a mota ma hirarsu suka cigaba da yi, da su Ummi, suna dariya, Saudah tace "oh ikon Allah kamar yau muka fara karatun nan, gashi har mun 'kare, Mami kamar baki ci zalina a primary ba, in na d'aukko miki jakar nan ban isa nace ki kar'ba ba har sai munzo 'kofar gidanku " dukkaninsu dariya suka kwashe daita, Ummi tace " to aini nice mai zuwar mata break, amma yanzu yarinya baki isa ba"

"Hhhhhhh ai ko yanzu kasuwa ta tashi d'an koli yaci riba, da dai anjemun aike ehe"

"Da kika ce ai, yanzun ki gwada ki gani, in ban lillisa ki ba "

"Hhhhh to aini ko kud'i aka ban bazan had'a jiki da keba, ke da jikinki yake kamar 'karfe "

"Mur tasha"

Dariya Meenah tai tace "kinga kinsa tasha kunu, byan yau muna cikin farin ciki, yi ha'kuri 'kawalliya share Nababa, ke da kika gama secondary sai kuma technology in Allah ya yarda"
dariya suka saka dukkaninsu, sbd sun san fushi kuma ya 'kare tunda an ta'bo mata makarantar da take bala'in so. Duk hirar da suke suna jinsu ,idanuwan Abu zarrin suna kan Rabee'ah ta mudubi, yana ta more kallonta san ranshi, yana jin soyayyarta tana 'kara shiga cikin kogon zuciyarshi, Almash yana lura dashi, baisan dalili ba, kawai shidai yaji yana jin zafin kallon da Abu zarrin ke jifar Rabee'ah da shi.



****
Gidan Al'mash suka nufa, sbd Abba baya gari, yai tafiya, don tun mutuwar umma, yamai da hankali sosai kan kasuwancinshi.


Sanda suka 'karasa gida, Hafsa ta kammala girkin, ta Jere musu kan deaning, Abu zarrin part d'inshi ya nufa, wanda zai tare in yai aure, jin Rabee'ah zata koma gidan Al'mash, shine shima ya had'o kayanshi ya daho,
Tare da Al'mash suka shiga falon, hafsa cike da fara'a ta taso ta amshi iffah, da ke hannun Rabee'ah tai bacci, ta kwantar da ita, ta 'karasa gurin Al'mash ta shige jikinshi tana dariya, had'ata yai da irfan da ke hannunshi ya rungumesu, da sauri Rabee'ah ta kau da kanta, zuciyarta na mata zafi, hafsa 'ko'karin janshi take ciki, yace "cwt fara kai mami d'aki, ina nan ina jiranki" "tom Honey" ta juya ga Rabee'ah da ta sadda kanta 'kasa acan gefe da su, tace "muje na kaiki d'aki."


Tana gaba, ita kuma na binta a baya, har suka isa madai daicin d'aki, Wanda yasha kayan alatu dai-dai gwar gwado, tana nuna mata d'akin tai sauri ta fice, ita kuma Rabee'ah ta fa'd'a toilet.


'Balle mishi ma'ballin riga take, ta kalleshi, tace "Ni dai honey zuwan yarinyar nan gidan nan, hankalina bai kwanta dashi ba, sbd kasan ba muharramar ka bace, sam bana son tarayyarka da wata mace Abban iffah, kaima kasan da hakan " ta marairece fuska, tana jifanshi da shu'umin kallo,
"Nasan da haka hafsa, amma sau nawa zan gaya miki? Mami ina jinta tamkar ciki d'aya muka fito, ban ta'ba kawo zargin da kike ba tsakaninmu, ni kallon 'kanwa nake mata"

"Hakane kasha gaya mun, amma yarinyar ce duk sanda na ganta, zuciya'ta na shiga shakku, ta kan ji kamar wani AL'AMARI zai faru, byan zuwanta gidannan"

"Ki cire wannan a zuciyarki hafsa, ko kya huta, ni sam bata cikin tsarina, bakisan wani abu ba, na lura broth santa yake fa"duk da shi da kanshi ya fad'i Kalmar sai yaji zuciyarshi na mishi zafi, zafin da baisan na meye ba.
"Kai Allah ya tabbatar, wlh zanfi kowa farin ciki in hakan ta faru, honey kasan fa duk sanka ne yake jahomun kishin nan, ina kishinka sosai my love, tashi muje na maka wankan" taja dogon hancinshi.....







Author: Bebe'arth😘
[4/11, 1:13 PM] BEBE'ARTH😘: *Bebe'arth*




*RABEE'AH*



RABEE'AH
_rabee'ah means;.Beautiful ,she is filled with beauty and brains._
_Her eyes are the most admirable features_
_She is caring and sweat_💋


( *2018*)

( *Short novel*)


Dedicated to :.RABEE SK MASHI


Manzon Allah (S.A.W) yace,

" _Duk wanda ba ya jin tausayi, to baza aji tausayin saba."Abu Dauda, Bukhari, da Muslim ne suka rawaito shi._

( _Wato wanda ba ya jin tausayin bayin Allah, to Allah bazai tausaya masa ba._)


( *8*)

Tana fitowa daga wanka mai ta d'auka ta shafa, simple make up tayi tai d'aurin ta zagaye, daga bisani ta fita falo, don tun d'azu take jin Abuu inta na 'kwalo mata kira.

Tana fita ta hangi Hafsa na baiwa Almash abinci a baki, gefe kuma Abu zarrin ne shima yana ci, kujerar kusa dashi ta ja ta zauna, a zube ta tadda abincin cire murfin kan tayi tai bismillah ta soma ci, don Rabee'ah ba ta wasa da cikinta ko kad'an.


Sai da suka gama cin abincin suka d'an huta, kana Abuu zarrin ya ja Rabee'ah part in shi don ta kar'bi gift in ta na candy, suna shiga tsararren falonshi ya d'aukko wata 'katuwar leda ya mi'ka mata.

"Ungo ki je kikai d'aki ki daho muyi hira, ki bari sai da daddare kya duba"

"Tom na gode ya Abuu na, Allah ya ji'kan mahaifa ya 'kara bud'i, Amin." ta juya ta nufi waje cike da farin-ciki tsantsa.


*****
Sai dare ta bud'e ledar tai mata raga-raga a gado, ta d'auki wannan ta ajiye, ta kuma d'aukar wani ta ajiye murna tai mugun isar ta, can ta zalu'ko kwalin waya da hanzarin ta fara 'ko'karin bud'eta, murmushi ne ya kubcewa fuskar ta yayin da ta zaro wayar, fara ce 'kal 'yar shafal-shafal 'kirar Ivvi, tayi masifar kyau ainun, jujjuyata take bakinnan ya'ki rufuwa, don sosai wayar nan ta tafi da ita.

Can ta hango wani kyakkyawan kati mai kyau, anyi mishi ado da red in fulawoyi masu d'aukar ido, ga zanan heart a tsakiyarshi yai matuk'ar kyau, bud'ewa tayi don taga meye a ciki, wani kyakkyawan rubutu tai karo dashi mai matu'kar 'kayatarwa, kalmomi ne na love masu shiga zuci, maimakon taji sanyi a zuciyarta ganin sa'kon soyayya daga yaya Abu inta amma ina sai taji zuciyar ta tana mata zafi, batai aune ba taji ruwan hawaye na fita daga idonta, sufa tai ta kwanta a gado ta fara rera kuka sosai , ita dai zuciyarta ko kad'an bata ta'ba sha'awar soyayya da Abu Zarrin ba, ita dai tana mishi soyayya ta 'yan uwantaka, sai dai dama tuni ta riga da ta san Abu Zarrin
yana sonta sbd alamomin da yake nuna mata, amma ita zuciyarta ta rasa inda take son kaita.



Tayi al'kawari zata binne abinda ke damun zuciyarta, don ganin ta bawa Abu Zarrin kulawa a soyayya don ya can-canci sama da haka a gare ta, hakanne yasa ta saki jiki da shi suka fara soyayyarsu bisa tsari, ko kad'an bata ta'ba nuna masa zuciyarta ba shi take so ba. Hafsa kuwa ganin irin soyayyar da Rabee'ah da Abu Zarrin suke yi, sai ta samu kwanciyar hankali sosai, don ta lura da irin kulawar da suke wa junansu.




*****
Zaune suke a palo ita da su Iffah ta zube musu kayan wasa, suna ta wasan su tana binsu da ido cike da 'kauna, yaran sun shiga ranta sosai don tun dawo warta komai nasu ya dawo gareta, Hafsa tana jin dad'in yadda take kular mata da yaranta.

Wayarta ta janyo ta fara d'aukarsu photo, photo yana yin kyau sosai, kasan cewar camera wayar badai clear ba, tana wanke shi ainun, Hafsa da Almash ne suka fito, ta yo masa rakiya zai fita, murmushi dukkanin su suka sakarwa Rabee'ah don ganin hidimar da take da yaran su, dur'kusawa Rabee'ah tai tana gaisheshi,

"Ina kwana yaya?"

"Lfy qalau maman Iffa da irfan, kin tashi lfy?"

"Lfy qalau, yaya anjima zan raka Meenah nuna ankon bikinta in ka bani izini?"

"OK Allah ya kaimu anjiman, sai kun dawo, kidai kula sosai."
"Amin yayana na gode, a dawo lafiya"

Cike da kishi Hafsa ta galla mata harara jin furucin da tayi, shikwa Almash binta yai da kallon mamaki, yai murmushi ya fice, don kishin Hafsa ma ya fara bashi dariya, 'kwafa tayi ta bishi a baya, ita kwa Rabee'ah ko kallon inuwarta batai ba.

Har ya shiga cikin mota ya zauna ta 'karasa gurin tana huci, "Allah Honey wataran zan cirewa yarinyar nan ha'kori, har a gabana zata kiraka da yayanta a gidan ubanwa ka zama yayan nata?"
murmushin takaici yayi, yaja motarsa ya fice daga gidan yabar mata 'kura.

Huci takeyi kamar zakanya ta koma cikin falon, harara ta zabgawa Rabee'ah

Please Login or Register in order to submit comment