Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[12/10, 08:50] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*

*K'ADDARAR RAYUWARMU*


® *NAGARTA WRITERS ASOCIATION*

2019
Cweat novel

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


*Assalamu Alaikum Makarantana, ina me muku Barka da sallah, da fatan* *munyi sallah lafiya, Allah Ubangiji ya* *karb'i ibadunmu yasa muna cikin 'yantattun bayi Amin summa Amin*
*Ga novel nan na kaho muku a goron sallah, da fatan zaku ilmantu dashi ku nishad'antu, ku kuma ji dad'inshi, comment d'inku ne kawai zai nunan kuna biye dani, kuma kuna jin dad'inshi, duk group d'in da nayi post kamar biyar naji babu comment babu thanks babu ham ba d'aga hannu, to nima zan d'auke nawa hannun shi yafi sauk'i, zanyi post a inda ake mararinshi sosai, idan kuma kinsan zaki bini muyi tafiya d'aya ki bini muyi ta a lokaci d'aya kar sai nayi nisa sosai a biyoni PC ana dan Allah daga farko, gaskiya ba zan d'auka ba kamar sanda na d'auka ina typing d'in Rabee'ah, Rabee'ah short novel ne wannan kwa ban san iyakarsa ba sai inda alk'alamina ya tsaya, kuyi mana uzuri abubuwan da yawa wallahi wataran lokacin da zaka tsaya ka dubo littafin baka da lokaci, da fatan zaku fahimceni, ku bini muyi tafiya d'aya, idan kuma ba haka ba kya iya nemanshi a group, ko ki bari har sanda zan kammala ki nemi document, ina godiya ga wa 'yanda suka fuskanceni*

*Sharhinku gareni shi zai k'ara mini k'aimin antayo muku typing ba k'ak'k'autawa, ina sonku masoyana maza da mata da kuke bani aron lokacinku, Allah Ubangiji ya had'a fuskokinmu a Jannatul Fiddausi Allahuma Amin*

*Allah ina ro'kon ka yadda na fara rubuta shi lafiya, Allah kasa na gamashi lafiya cikin kwanciyar hankali ka rabamu da sharrin mutum da al Jan Allahuma Ameen*



Da sunan Allah mai rahama ,mai jin 'Kai

~GORON SALLAH~
____________________
*ONE EPISODE*

Tunda suke tsaye a kanta, suna zazzaga mata masifa, bata d'ago ta kallesu ba sai gunshe'kar kukanta take, Sumy ce tace "anya kwa kuna ganin ita ta d'au kud'innan? "caraf sai Sury cewa tayi "To da waye ya d'auka banda ita haka ta iya ai ,tayi sata kuma in an kamata taxo tana kukan banza da na hofi "hmmmm ,ajiyar xuciya suby tai tace "ai yaseen yau ko kukan jini zatayi sai ta futomun da kud'ina, na gaji kullum ita kenan yimin sata ina ha'kuri to wlh yau sai kin bani kud'ina "takai 'karshen maganar, gami da ran'kwashin ta aka, sai Sufy cewa tayi "Ni na gaji da cece kucen nan, tunda ta'ki ta bamu kud'innan kuxo muje mu gaya ta da ittale ,tunda da alama dukan da yai mata shekaran jiya bai shigeta ba "

Amincewa sukayi da shawarar Sufy, sukayii hanyar fita daga class, sun kusa fita daga class d'in suka ji muryar Rumana ta dakatar dasu.
"Ku tsaya.” tsayawa sukayi su basu fita ba,basu dawo ba.

Matsawa tayi kusa da ita, ta dafata tace. "Idan kinsan ke kika d'aukar musu kud'insu ki basu, ke bakya tausayin kanki? kiga fa irin dukan da Ittale yayi miki,kinsan ba imani ne dashi ba, dan Allah ki fito musu da kud'insu bana son naga ana dukanki ko kad'an. "

D'ago da kanta tayi tana matsar hawaye ta zira hannunta cikin rigarta ta d'auko sabuwar 1000 ta mi'kowa Rumana, karb'a Rumana tayi taje ta kai musu, cike da takaici da ba'kin ciki Suby ta saka hannu ta kar'ba gami da jan tsaki,ta taka a hankula ta isa inda take.

Ta mayar da kanta kan guiwa tana kuka sosai, Allah ne kad'ai yasan halin da zuciyarta take ciki.

Ran'kwashi Suby ta sakar mata tace. "kinyi asara wallahi, na gaji da bani kunyar da kikeyi, wannan wata irin rayuwa ce?ke baki rasa ci ba,baki rasa shaba, baki rasa sitira ba, kina da gatanki amma kika d'aukarwa kanki wannan rayuwar, meye riba a cikinta? bata da wata riba, illa toxar ci da 'kas'kanci da take kawowa, kar ki tunanin don kin fitomun da kud'ina bazan gaya ki da Abba ba, to wlh sai na fad'a mishi ,yasan har yanzu kina nan kina jaho masa abin kunya. " Daga haka taja 'kawayenta suka fice.


Fashewa tayi da kuka sosai mai cin rai, don tasan gamuwar ta da Abba baza tayi kyau ba, Rumana ta xuba mata ido, cike da tausayawa irin Rayuwar da take ciki .



*
'Karfe 1:00pm a ko wace 'kaida ake tashin su daga makaranta, tana tsaye a bakin get a kazo aka d'auki Suby da 'kawayen ta a mota, haka ta mi'ke sayyadar ta ,ta nufi gida,don ba wani nisan kirki ne dasu da makaran tarba,

tazo shiga gidan shi kuma Hamid zai fito, ja da baya tayi ,ta bashi guri ya huce, kallon ta yayi na d'an second yace *HANAH* kuka kikayi ko ?ba na hanaki zubar da hawayenki ba, murmushi mai kama da yak'e tayi tace "Haba Yaya, ai zubar hawaye ya zame mun JININ JIKINA, shi kad'aine zanyi naji sanyi a zuciya ta, kaidai kawai yaya addu'ar ka nake buk'ata.” Bata saurari abinda xaice ba, tai sauri ta shige gida, don shima in aka ganta dashi kashin ta ne xai bushe, girgixa kanshi yayi cike da tausayin ta fal xuciya ya shige gidan su.


Tana shiga ciki, ta tadda Ammi da su Janah da Jabir a main ferlow suna kan deining sallamarta kawai suka amsa, suka ci gaba da cin abincinsu, in da sabo ta saba, don haka kawai sai ta nufi hanyar d'akinta, tana shiga d'akin ta fad'a kan gado, taci kukan ta ta gode Allah, daga bisani ta mi'k'e ta shiga toilet.




______________

Tsaye yake a bakin window d'in d'akin shi sai sintiri yake yaje nan ya dawo, momy ce ta d'an tab'a kafad'arshi, a d'an tsorace ya juyo yana kallon ta, alamun ta bashi tsoro, don baiyi tsammaninta cikin wannan silisin dare ba, girgixa masa kai tayi tace "Haba Alhaji ya zaka dinga hana idanuwanka bacci, akan yaron da bai damu da muba, ina jiye maka karfa ciwo ya kama ka. "

D'an yak'e yayi, yace "Kema kanki Hajiya abinda ya dame ki kenan ya hanaki bacci, kawai dauriya kika fini, shi kad'aine fa d'anmu in bamu damu dashi ba, wa zai damu dashi? babu iyayen da zasu kwanta bacci, ba tare da sun san halin da yaransu ke ciki ba, bare mu da shi kad'ai Allah ya mallaka mana, tunda yake dad'ewa bai tab'a kaiwa kamar yauba, ki gayan taya zamu iya bacci"?

Kan takai ga magana, suka ji wani wawan horn da ake saki, ko ba'a gaya musu ba, sun san *HAISAM* ne, a gigice Baba mai gadi ya futo yana bud'e mishi get d'in, kafin yakai ga k'arasa wangale get d'in, Haisam ya danno motarshi a guje,wani wawan tsalle Baba mai gadi yayi sai gashi a bakin k'ofar d'akin shi. Lol

A yadda ya bud'e motar ya fito ya banka ta, da ji kasan ba a hayyacin shi yake ba, tangad'i yake yi sosai, ya nufi phart d'inshi yana harhad'a hanya,
Momy da Daddy kwa kawai girgixa kai suke cikin tarin bak'in ciki, Daddy bai iya dauriya ba, har sai da ya xubda k'walla, kamar yaune ya fara ganinshi cikin wannan hali.
[12/10, 08:51] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


~GORON SALLAH~
____________________
*TWO EPISODE*

Fitowar ta daga wanka kenan, ta hau tsatstsane jikinta, tana gamawa, ta d'aukko man shafawarta ta shafa, uniform d'inta ta d'aukko light blue a wanke a goge, duguwar Riga ce da hijabi, sakawa tayi, ta d'aura pink d'in d'ankwali na prifect,
duk da ba abinda tasawa fuskarta tayi masifar kyau.

Inda take ajiye jakar makaran tarta ta isa ta d'auka, suwaga ce pink colour, ta rataya, ta xira plate shoe mai taushi shima pink, kana ta 'karasa gaban dressing miror ta feffeshe jikinta da turaruka masu 'kamshi, ta fito taja 'kofar d'akin nata.

A falow ta tadda Ammi ita kad'ai tana kishingid'e jikin kujera, cikin muryar ta mai matu'kar sanyi tace "Ammi na tafi"

sai da ta fara jifanta da harara, kana tace "Saura in kinje canma kiyi d'an halin naki da kika saba, kuma gamuwar ki da Abbanku tana nan ta satar da kikayiwa Suby."

Jitayi hawaye ya tarar mata a ido, da sauri ta fita daga d'akin, tana xuwa bakin get, ta tadda su Suby, gaba d'ayansu harara suka jefeta dashi.

Sufy tace "Mtsss kyahu har kyau amma kyahun d'an miciji "

Sury tace "Kinsan Allah ina ba'kin cikin kyahunnan na Suhanah ji nake dama nice dashi "
tsaki Suby taja tace "Kunga kuzo mu tafi ku waccen B'arauniyar ta dama.”

Bata tanka musu ba ta hucesu, tana fita sukayi ido hud'u da Hamid yana zaune kan mota, binta yake da kallo cike da tsantsar 'kauna sakkowa yayi daga kan motar ya nufo gurinta,
tunda ya taho 'kirjinta ke dukan uku² ta 'kara sauri a kan wanda take,
sauri yayi ya taddata yasha gabanta, k'asa tayi da fuskarta, ya rank'wafo da tasa fuskar yana le'kenta so yake yaga 'kwayar idonta amma ta'ki yarda yace "Hanah me yasa kike son ki dinga azabtar da nine da rashin ganinki ?kinkwa san irin halin da zuciya ta ke shiga in .......bai kai 'karshen maganar ba sakamakon Suby da ta funcuko hijabin Hanah ta kintsa mata mari, rintse idonta tayi, dama zuciya a kusa, tuni ta fara d'igar hawaye, binta Hamid yayi da kallo gashin idonta ya ji'ke sharkaf da hawaye, bai wata² ba ya juya kan Suby da keta huci kamar zakanya ya kintsa mata kyawawan maruka biyu wani irin ihu ta saki ta nufi hanyar gidansu Hamid.


"Kiyi ha'kuri Hanah ni nake jaza miki, ba laifina bane nima zuciya tace da ta'ki amincewa da rashinki, Allah ne ya K'ADDARA mini sonki Hanah, ina sonki, ina 'kaunarki My Hanah, kamar an hankad'a ta tayi sauri tabar gurin da azama don yana shirin wargaza mata zuciya, kuma bata shiryawa hakan ba.




Tana shiga gidan, ta tadda Mamanshi a tsakar gida, 'kara sakin wani ihun tayi iya k'arfinta, da azama Mama tazo ta tareta, tana "D'iyata ke dawa ?”

Cikin kuka tace "Yaya Hamid ne ya mareni, wai don na mari Suhanah, na ganta ita dashi kuma ita ta fara tararshi tayi masa magana.”
Salati Mama ta fara yi tana tafa hannu "Yanzu akan B'arauniyar nan ya dakeki? duk kashedin da Baffanshi suke masa baiji suba kenan, bar ni dashi a yau d'innan wlh zaibar garinnan kuma yana 'kare karatunshi za'ayi bikinku, share hawayenki kinji ki tafiyarki makaranta kar ki 'bata lokacin ki a banza.” Murmushi tayi tace "Tom Mama na gode "

Ta fita, tana rakata da a dawo lafiya,
tana fita ta tadda su Sufy suna jiranta, suka rankaya suka tafi, tana basu labarin abinda Mama tace ......





____________________

'Dago da kyawawan idonshi yayi ya d'ora a kanta, hakan ba 'karamin k'ara jefata cikin shau'kin sonshi yayi ba, narkar da idonta tayi, wanda ita kanta bata son tayi ba, tace "Yaya Haisam zuciyata ta rayu da sonka, ka taimakeni ka amshi soyayyata.”
D'an tsaki yaja, ya zagayeta ya huce cikin motarshi ya bud'e ya shiga, jinginar da kanshi yayi jikin kujera yana busar da iska mai zafi.

Juyowa Hisham yayi yana kallonsa yace "Abokina kana wahalar da Hindu, ina laifin wanda yake sonka ?"

Maimakon ya bashi amsa tsaki yaja, ya d'auki kwalbar giya ya kafa a baki yana kwankwad'a kamar mai shan lemo, kana ya d'ago da idanuwanshi da suka fara canja colour yace. "Dukkaninsu ji nake na tsanesu har mahaifanta, in kana sonta na bar maka ja mota muje, "yaci gaba da kwankwad'ar abarsa.



Dur'kushewa tayi a gurin da ya barta tana kuka, Haris ne ya taddata a gurin yasa hannu ya d'ago ta "Haba 'kanwata da kyanki da wayonki kidinga wahalar da kanki akan wancan d'an shaye-shayen me neman mata.”


"Yaya wallahi baya neman mata shaye-shaye ne kawai kuma shima zai daina tunda giya ce ka....”
bata 'karasa ba ya wanke ta da mari "Kinfini saninshi ne? ke duk abinda ake gaya miki bakya ganewa, to kisan da cewa wlh baza ki auri Haisam ba” daga haka ya zagayeta yabar gurin.

Zubewa tayi a gurin tana gurshe'kan kuka, zuciyarta tana gaya mata yanzu ta fara nutso cikin soyayyar Haisam......
[12/10, 08:52] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*


® *NAGARTA WRITERS ASOCIATION*

*2019*
*Cweat novel*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise.)


~GORON SALLAH~
____________________
*THREE EPISODE*
Ta kawo kanta zata shiga ajin, taji wata daga cikin d'aliban tana cewa.
"To ga b'arau² nan kowa yayi hankali da kayansa. ”
K'walla ce ta biyo idonta tayi saurin d'auketa da hannunta, ta shiga ajin da sallama, babu wanda ya amsa mata sai kallon wulak'anci da kowa yake binta da shi, gurin zamanta da ya zame mata permanent ta nema ta rakub'e a gurin, babu me zama kusa da ita, kullum itace a rakub'e a gefe, bata da k'awa bare aminiya, wata Shukhurah ce ta so suyi k'awance, saboda k'ok'arin Hanah, amma a gidan su Shukuran aka raba su da ita suka ce ta rasa da wa zata yi k'awance sai da B'arauniya.

Bayan an tashesu daga makarantar ta kusa kaiwa gida taga wani saurayi a tsaye a jikin babur d'insa, wayarsa a kan babur d'in ya juya baya ko me yake oho, ita dai ba tace ga sanda taje har ta d'auki wayarba, ita dai kawai ta tsinci wayane a hannunta.

Saurayi yana gama abinda yake ya juyo zai d'auki waya, waya tace d'aukeni inda ka ajiye, mamaki ne da al'ajabi suka kamashi, da yaushe har aka zo kusa da shi aka d'auke wayar amma bai jiba, cigaba yayi da duddubawa harda k'ara fito da aljihunsa ko ya manta bai fito da ita ba amma wayam, duk inda yake tunanin ya ajiyeta ya duba bai gani ba.”

D'ora hannu yayi a ka kamar ya fashe da ihu, "Wayyo na shiga tara ni Saifu, wayar dubu d'ari biyar shi kenan ta tafi baza ta dawoba”
Ji yayi an dafa shi ya juyo yaga waye, wani mutum ya gani, yana cemasa.
"Bawan Allah me kake nema ne? ”

"Wai wayata ce na d'orata kan babur ina gyara wani noti kafin na juyo kamar walk'iya na nemeta na rasa. ”

"Aikwa naga hucewar Suhanah B'arauniya duk yadda akayi ita ta d'au wayar nan, taho muje gidan nasu. ”

Ba musu Saifu yabi bayan mutumin, dan shi burinshi bai huce yaga wayarshi a hannunsa ba .


Tana shiga a falo ta tadda Abba, wani mugun kallo yake jifanta da shi wanda yasa hanjin cikinta da 'yar autar hantar cikinta kad'awa.

"Me ya kaiki satarwa Subai'a kud'in makaran tarta kuma kika hana ta?” Ta jiyo muryar Abba cikin dodon kunnenta yana tambayarta.

Kasa magana tayi sai ruwan hawaye da ya fara wanke mata fuska, mik'ewa yayi a fusace yayo kanta da belt a hannunsa, ja da baya ta soma yi cike da tsoro, ya kusa cimmata yaji ana sallama a waje.

Fita yayi don yaga su waye, ya tadda su Saifu, abinda yake tafe dasu suka sanar mishi, yace.
"Bazan muku musu ba zata iya d'auka ku shigo daga ciki.” Ya basu guri suka shige, "Umaima” Ya k'wallawa Ammi kira, tana daga cikin d'akinta ta amsa. "Hadiza” Ya kuma k'wallawa Amma Kira, itama tana daga d'akinta ta amsa, a kusan tare suka iso, zuciyarsu dama ta sanar musu wannan kiran bazai huce halin Suhanah tayo ba.

Guri suka nema suka zauna, Abba yace.
"Wai wannan mutumin ne ya ajiye wayarsa kan babur bai ganta ba, kuma sunga hucewar Suhanah shine suka biyo baya ko ita ta d'auka. ”

Jinjina kai dukkaninsu suka yi, Ammi ta kasa magana, sai Amma ce tace. "Tun muna shai da juna da ke in kinsan ke kika d'au musu waya ki fito musu da ita. ”

Tana durk'ushe tana ta shashshek'ar kuka, tasan halin Amma ciki da bai, tana iya yimata tsirara a gaban mutanen nan, dan haka ba musu ta sanya hannu cikin jakarta ta d'auko wayar ta mik'o.
Mamaki ne ya kusan kashe Saifu, don duk ciki shine bak'on sanin halin Hanah, mutumin ne yace "D'auki wayar mu tafi wannan ma kad'an ka gani wallahi, kaidai tunda wayarka ta fito ka gode Allah kawai. ”

Mik'ewa yayi ya d'au wayar suka yi godiya suka fita, ziciyar Saifu cike da tarad dadi, Ammi fashewa tayi da kuka, ta mik'e ta nufi d'akinta, daga Abba har Amma tab'e baki sukayi suka bi bayanta da harara.

Wasu munanan maruka Amma ta zabga mata, tayi boll da ita, Abba yasa belt ya shiga zuba mata ko ta ina, yana kuma haushinta da k'afa, tun tana ihu yana fita har ya zamo ba ta iya yi domin muryarta ta dashe sosai da sosai, amma hakan baisa sunji tausayinta sun k'yaleta ba, Abba fad'i yake a zuciyarsa. "Ai gara ki mutu kibi bayan Ubanki butulu maci Amana, ai daga ke har uwar taki ba wanda zan bari, jira kawai nake lokaci yayi. ”

Hamid ne ya shigo kamar an jefoshi, tsakiyarsu ya shiga ya janyota jikinsa ya rungume, ya rasa abinda zaiyi kawai sai ya saki kuka me ciwo...........
[12/10, 08:57] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*


® *NAGARTA WRITERS ASOCIATION*

*2019*
*Cweat novel*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise.)


~GORON SALLAH~
____________________
*FOUR EPISODE*
Shek'e² suka tsaya suna kallonshi cike da takaici, a fusace Abba yasa hannu ya fisgeta daga jikinshi yayi cilli da ita goshinta ya k'umu da k'asa, rintse idonta tayi saboda jin wata sabuwar azaba da tayi, saka hannu tayi a gurin taji danshi, duba hannunta tayi sai taga jini kawai sai ta kuma fashewa da wani irin kuka me ban tausayi.

Maruka har biyu Abba ya sakarwa Hamid, yana harararsa. ”Ai naji abinda ka aikata, akan wannan shegiyar yarinyar ka mararmun yarinya, shine yanzu don an koreka ka shigo kuyi sallama ko, to bari kaji na gaya maka, Subai'a tana yin candy zan d'aura muku aure ta biyoka, kai da Suhana kam sai a lahira in kuna da raban aure. ”

Idanshi yayi jajir, jijiyonyinsa duka sun mik'e, tashi yayi ya k'arasa gurin da Hanah take tana sharb'ar kuka, hannu yasa ya d'ago ta yace."Kici gaba da hak'uri, Allah yana sane dake, zakici riba wata rana, a sannu duk k'ullin da aka k'ulla zai warware, komai na duniya me k'arewa ne kamar ba'a tab'a yinshi ba, ni zan tafi, na barki a hannun Allah domin shi kad'ai ne gatanki, amma duk inda nake zuciyata na manne da taki babu wanda ya isa ya ciremun soyayyarki sai Allahn da ya dasa mini ita. ”

Jakarsa da ke bakin k'ofa ya d'auka, hawaye yana wanke masa fuska, ya rataya jakar ya juyo da jan idonshi yana kallon Abba da Amma yace.
"Kubi a sannu domin Allah baya barin hak'k'in mutum, bare kuma *HAKK'IN MARAINIYA* kunsa zan bar garin amma ba ku isa ku cireta daga zuciyata ba, ina me tabbatar muku idan na dawo babu wanda ya isa yamun shamaki da auranta, a lokacin kuma zan kunce k'ullin da aka k'ulla insha Allahu, sai na dawo.”Yasa kai ya fita.

"Yaronnan tabbas sai nayi maganinka, zaka tab'o inda bazan tab'a k'yaleka ba, dole sai nayi maganinka da gaggawa. ” Abinda Amma ke sak'awa kenan a zuciyarta.

Abba kuwa wani tiriri ne ke tashi a zuciyarsa saboda b'acin rai, a ransa yace. "Yaro kenan aikwa nine nan da zan zamo babban shamakin da zan hana auranka da Hanah, mu zuba ni da kai. ”


(Tofa ni 'yasu wai ya al'amarin yake ne?)
Muje dai zuwa.

______________
Juyowa yayi ya kalleshi sai d'ad'd'akar giyarsa yake kamar lemo, girgiza kanshi yayi cike da tausayin abokin nasa yace.
"Ina muka nufa ne? ”
"Muje gidanku kawai, ina son na huta. ”

Bai k'ara magana ba ya d'auki hanyar gidansu, yana yin parking ya fito ya daho gefen da Haisam yake ya bud'e ya rik'oshi suka fito, ido hud'u sukayi da Aunty ta jefesu da muguwar harara taja tsuka.
"Aikin banza haka dai rayuwar zata k'are, shi mashayi kai kuma mazinaci, tir da wannan rayuwa taku. ”
Ko kallon inuwarta baiyiba, bare ya nuna mata yaji abinda tace, yaja Haisam suka nufi phart d'inshi.

A kan gado ya kwantar dashi ya cire masa takalma, ya cire masa shirt d'in jikinsa, fitowa falo yayi ya bud'e fridge ya d'auki ruwa me d'an karan sanyi ya kafa a baki, sai da yasha kusan rabi sannan ya ajiye, ya zauna a kan kujera yana maida numfashi.
Wayarsa ya d'auka ya kira Rumana.
"Hello Yaya ”
"Ina d'aki ki kahomun abinci. ”

"Tom” Tace shi kuma ya kashe wayar, ko mintina biyar ba'a rufa ba sai gata ta shigo d'akin da tiren abinci, ajiyewa tayi ta d'ago tana kallon yayan nata tace.
"Yaya dan Allah kayi aure kafin na bar gidannan nima. ”
"Saboda me kike so nayi aure Rumana? ”

"Saboda Aunty, idan na bar gidannan na tabbata baka da rabon abinci a gidannan ko kad'an, da badan nima ba raga mata nake ba wallahi ko ruwa baza musha a gidan nanba,

Please Login or Register in order to submit comment