Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi musu ƙari, ta buɗe Alqur'anin ta ajiye, ta cigaba da gyangyaɗinta.

Tun da Ruma ta shigo ajin ɗazu yake kallonta, sam ya lura babu alamar son karatun a tare da Ruma, daga hamma sai bacci take yi.
Ƙarshe ta haɗa jakarta ta cewa malamin fitsari take ji, ya ce taje tayi, ta ɗau jakarta ta bar ajin.
Zagayawa take tana lelleƙa azuzuwa ko Allah zai sa taga mutum ɗaya a tsakanin yayyenta, dan har wani irin jiri take ji, dan a duniya ba ta wuce ƙarfe ɗaya ba ta ci abincin rana ba, yau sai ga ta har azahar babu ko karin kumallo.

Ajinsu yayi tsit, sun tattara hankalinsu a kan ƙarin karatun da ake yi musu, kamar daga sama ya jiyo muryarta "Huzaifa, dama nan ne ajinki tun ɗazu nake neman ku" gaba ɗaya ajin aka waiwaya don ganin waye yake wannan wautar.

Kallon da ake yi mata bai sanya ta nutsu ta daina maganar ba "ka ganni a makarantar ku ko? Hmm ɗan zo ka ji wata magana mana".

"Ke wacece haka, baki ga karatu muke yi ba?" Malamin yayi maganar yana kallon tagar da Ruma ke tsaye.

"Yunwa nake ji, shiyasa nake nemansa" ta faɗa tana sake leƙo cikin ajin.

Shi Huzaifa mamaki ne ya cika shi, yaushe aka saka Ruma a makarantar nan bai sani ba?.
Ganin babu komai a kan Ruma sai wauta ya sanya malamin ya kalli Huzaifa ya ce "Je ka ka sallameta"

Cike da jin kunya ya tashi ya fita, yana fitowa ta tare shi da murmushi, shi kuma ya haɗe rai ya ce "Uban waye ya kawo ki makarantar mu?"

Kallonsa tayi ta kalli harabar da suke ta ce "Sai ka ce wata makarantar arziki, nima ban ce a kawoni ba, wayewar garin Allah kawai mai sunan Baba ya bani uniform ya kawoni, ni wallahi gara na koma na bawa malam babba haƙuri, in koma makarantar allon mu ba zan iya wannan jidalin ba".

"Ke dalla rufewa mutane baki, daga zuwanki kin fara nuna hali, kawai ki zo ta window kina kirana saboda hauka, maimakon ki yi sallama ki tambayi malamin, ke Allah sai kin bar makarantar nan, dan ba zaki zubar mana da mutunci ba".

"Saboda gani annoba ko?" Tayi maganar tana hararasa.

"To ba gara annoba ba, idan aka samo maganin ta shikenan ba, ke kuma maganinki sai Allah, yanzu uban me zan miki?"

Ta yatsuna fuska ta ce "Ni yunwa nake ji, kuma wallahi sonake na tafi gida"
Huzaifa ya ce "Lallai baki da hankali, to ke da gida sai ƙarfe biyar, wuce muje ajin su Yasir gara mu raba abin, da ki dinga yi mini ni kaɗai"tura baki tayi, ta rungume jakarta, Huzaifa ya sanyata a gaba yana mita suka nufi ajinsu Yasir.
Ita kuma sai mita take, a kan daga yau ba zata sake zuwa wannan makarantar ba da ake uzzurawa mutane.

Yasir kansa salati ya dinga yi da salallami "Dan girman Allah meyasa mai sunan Baba zai yi mana haka, ya saka yarinyar nan a makarantar nan ba a shawarce mu ba, wallahi mun kaɗe"

"Oho muku, ku kwantar da hankalin ku, ni ba kuma zuwa zan yi ba, kawai ku bani Abinci"
Yasir ya dungure mata kai ya ce "Shegen ci kamar kazar hausa" suka sakata a tsakiya suna tafe suna zaginta, suka saya mata awara da ruwa ta cinye tsaf, sannan suka korata aji.

Ko da ta isa aji, tuni an gama karatun Alqur'ani, ana jiran wani malamin ya shigo.

"Ya aka yi daga zuwa fitsari ki ka daɗe, gashi an gama ƙarin Alqur'ani, sati mai zuwa idan Allah ya kaimu zamu bayar da hadda" cewar yarinyar dake kusa da Ruma.
Ruma ta kalleta ta ce "Ina aka biya ɗin?".
Yarinyar ta buɗe Alqur'anin tana nunawa Ruma ta ce "Rabin shafi aka ƙara, gobe in Allah ya kaimu ma za a ƙara rabi, feji ɗaya kenan sati mai zuwa idan Allah ya kaimu sai ki kawo haddar".

Cikin ko in kula Ruma ta kawar da kanta gefe, alamar zancen yarinyar ma bai shigeta ba.

"Ya na ji kin yi shiru ne? Ki buɗe sai na koya miki, idan fa baki iya ba babu ruwan ya sayyadi da sabuwar zuwa ce ke, zaneki zai yi".

Rumaisa da shishshigin yarinyar ya fara ƙular da ita ta ce "To a kasheni mana kar a barni da rai, ba cewa aka yi nan aji ɗaya bane ba, kuma sai a ƙara mini rabin shafi, kuma wai na haddace yo ta ina zan iya ni, nifa a makarantar da na baro sai nayi wata ina nanata aya biyu nake iyawa, wannan karatun ma na san ba zan iya ba sai dai ayi kwaɗona da mai da yaji a cinye" galala yarinyar ta bi Ruma da kallo ta jinjina kai ba ta sake cewa komai ba.

Bayan an kaɗa ƙararrawar tashi, malamin da ya yi mata interview ya kirata ya gaya mata cewar za'a fara karɓar haddarta daga tushe, sannan za ta dinga yi tana haɗawa da wanda ake yi musu a aji.
Da yake ma bata fahimci bayanin da yayi mata ba, hankalinta na kan ta tafi gida, dan ta san ba iyawa za ta yi ba, kuma ta gama yanke shawarar daga ranar ba zata sake zuwa ba sai dai Yaya Umar yayi mata abin da ya ga dama.

Ko su Huzaifa ba ta nema ba, ta nufi gida.
Ɗa da uwa sai Allah, wuni gudan da mama tayi babu Ruma a kusa da ita duk sai ta damu, ta ji gidan babu daɗi, gashi tana ta tunanin ko abinci Ruma bata tafi da shi ba, balle ta samu ta ci haka mama ta wuni sukuku.
Tana tsaka da tunanin Ruman ne, ta ɗaga kai taga Ruman a tsakar gida.

"Meye haka, babu sallama ki shigo ki tsaya?"

Ruma bata amsawa mama ba, sai kumbura baki da take yi, ta cire hijjabinta da jakar makarantar ta dungurar a wurin ta tafi kitchen tana dube-dube.

Ba ta saurari mama ba sai da ta ci ta ƙoshi, Sannan ta dubi mama ta ce "Ni fa mama gaskiya ba zan sake zuwa makarantar nan ba".

"To ai ba ni zaki gayawa ba, wanda ya saka ki a makarantar zaki gayawa".

"Mama kin ga uban dukan da ake yi a makarantar nan kamar an samu bayi, kuma dan rainin hankali wai aka kai ni aji ɗaya ni za a kai aji ɗaya saboda raini, to wallahi makarantar malam babba zan koma ba zan iya ba"

Mama ta girgiza kai kawai, ta cigaba da aikin da take yi, Ruma ta saki baki ta dinga zuba tana cin alwashin ba zata sake zuwa ba.
Huzaifa ne suka yi sallama shi da Yasir, mama ta amsa musu. Basu kai ga zama ba suka hau mita.

"Mama dan Allah meyasa aka saka yarinyar nan a makarantar nan ba tare da shawarar mu ba? Kin san halin yarinyar nan tun a yau ta fara nuna halinta".

Ruma ta ce "Sha kuruminka ni ba komawa zan ba, daga yau ko za ayi ƙuli-ƙulina ba zan koma ba, wai saboda tsabar abu wai ƙari shafi guda, kuma wani satin ka kawo hadda, ni aya biyu nake iyawa waye zai yi wannan karatun taɓ ga uban duka wallahi ba zan sake zuwa ba

Yasir ya ce "Ai makarantar mu ba ta daƙiƙai ba ce ba, ki koma inda ki ka fito ba zaki zubar mana da mutunci a makarantar nan ba".

Ba tare da sun san Umar yana gidan ba, yana ɗaki a kwance suke ta wannan zubar.

Tsuru-tsuru suka yi, musamman ruma da ta fi zaƙewa, sai ganinsa suka yi ya fito tsakar gida.

"To dan ubanki ki daina zuwan kin ji ko, daga yau kar ki sake zuwa ki ga yadda zan yi da ke, kuma na gaya musu ba kya jin magana, idan har ba ki yi karatu ba su kama ki su zane ki"

Ruma a ranta ta ce "Ai wallahi sai na yi abin da za a koreni waye zai zauna ana jibgarsa kamar jaki"

Ya kalli su Yasir ya ce "Ku kuma, kune zaku dinga tsayawa a kan karatunta, ku zaku dinga koya mata dan daƙiƙiya ce, duk daɗewar da ta yi tana zuwa makarantar allo ta kasa kawo izu biyu, sai karatun wani ta je tana iyawa, daƙiƙiya ki yi musu shirme na bayar da damar a zaneki"

Kawar da kai Ruma tayi gefe, Umar ya gama bala'insa ya bar gidan.

Yana ficewa daga gidan, Ruma ta dasa wa mama kuka, a kan lallai sai ta saka Yaya Umar ya cireta daga makarantar, mama ta ce babu ruwanta.

Ko da wasa Ruma ba ta sanya a ranta za ta yi wannan karatu ba, dan idan za a kasheta ba ta ma san in da aka ƙara musu ɗin ba, ta cigaba da sabgoginta.

Da sati ya zagayo zata koma makaranta, sai da a ka kai ruwa rana, tana kuka su Huzaifa suka sanyata a gaba zuwa makaranta, suna tafe suna zaginta suna mita an haɗasu da alaƙaƙai.

Yau mama ta bata kuɗin makaranta, dan haka ta tsaya ta sayi goriba a ƙofar shiga makarantar.
Duk da babu malami a ajinsu, amma kowane ɗalibi ya nutsu sun haɗa baki suna ta tilawa.

Taɓe baki tayi, ta samu lungu ta zauna, ta kashingiɗa tana cin goribar ta a nutse.
Shigowar malamin bai hanata cigaba da hangale baki tana gwaigwayar goribarta ba.
Ba ƙaramin ƙulewa malamin yayi ba, tun a wancan satin ya lura ba ƙaramar gaɓuwa ce ba yarinyar.

Yayi mata alama da hannunsa ta je, ta tashi ta fito da jakarta da goribarta a hannu ta ce "gani"

Ya ce "Yauwwa, ta kan ki zan fara jin karatu yau, ɗauko Alqur'anin ki ki karanta ƙarin da na yi muku, sannan ki bani hadda" ɗan waro masa idanuwanta tayi sannan ta ce "Gaskiya ban iya ba wallahi, karatun yayi yawa ina laifin aya ɗaya ko biyu"

"Koma gefe ki tsaya" babu ban haƙuri babu komai ta koma gefe ta ja ta tsaya.

Ya cigaba da sauraron tilawar 'yan aji, Ruma kuma ta mayar da hankali a kan cin goribarta, ya ɗaga kai ya kalli Ruma, wani irin takaici ya ƙule shi ko a jikinta abin da ya dameta kawai take yi, ya ce "Ke zo nan"

Ta ƙaraso ta tsaya, miƙewa yayi ya ɗaga bulala zai daketa.
Ta ƙwalalo ido ta ce "Kar ka dakeni ba a dukana" bai saurari ruma ba, ya zuba mata a ƙafarta har sau biyu.

Wani uban ihu ta ƙwala, ta zube a kan ƙafarta tana jujjuya kai.
Gaba ɗaya 'yan ajin suka yi shiru suna kallonta, sai a lokacin da ya daketa ya huce sai kuma ya sha jinin jikinsa ganin uban kukan da take yi.

"Wallahi ni sikila ce ba a dukana, shikenan ba zan iya tafiya ba" gaban malamin ne ya faɗi, amma ya maze ya cewa 'yan ajin su cigaba da karatu.
A ƙalla ruma ta shafe awa guda tana kuka babu ƙaƙƙautawa kuma taƙi tashi daga wurin, wai sikilarta ta tashi.

Abu kamar wasa magana har kunnen malamai, kasancewar malamin nasu, ɗan ajin da suka yi sauka ne yake koyar da su, ba cikakken malami bane a makarantar.
Malamai suka taru a kan ruma, amma taƙi tashi wai sikila ce da ita, ba zata iya tashi tsaye ba.
Malamin nasu jikinsa sai rawa yake yana cewa "Wallahi bai san ba ta da lafiya ba"

Malamin da yayi mata interview ya ce "Kuma ni a form ɗinta yayanta bai rubuta tana da wani ciwo ba, ina ne gidanku?"

"Ni ba zan gane hanyar gidan ba, akwai yayyena a makarantar nan ku kira mini su su kai ni gida in ga mama zan mutu"

"Su waye yayyen naki?" Nan gaya musu ajinsu Huzaifa.
Huzaifa yana can yana karatu aka kirashi, yana zuwa ajinsu ruma ya ganta zaman dirshan malamai sun kewayeta.
Nan suka yi masa bayani, turus yayi yana kallon ruma yana son gano ko makircinta ne, dan shi a iya saninsa ruma ba ga da wata sikila, ban da zazzaɓi ba ta ciwon uban komai, amma a ina ta samo wata sikila?.
Ya miƙa mata hannu ya ce "Taso in mayar da ke gida"

"Ni na kasa motss ƙafata ciwo take mini" tayi maganar cikin kuka.

Huzaifa ya durƙusa ya ce "To hau bayana na mayar da ke" aikuwa ta ja jiki, ta hau bayansa ya ɗau jakarta ya ce bari ya kai ta gida.


Sai da suka yi nisa sosai da makarantar sannan ya sauketa, aikuwa ta tsaya cak a kan ƙafafuwanta.

Ya kalleta ya ce "A gidan uban wa ki ke da sikila?"

"To gani nayi za a kasheni da duka, naga a makarantar bokonmu ba a dukan wata me sikila, da na ji zafin dukan sai na ji kamar nima ina da sikilar".

Galala ya bi ruma da kallo, 'yar mitsila da ita amma ta iya makirci haka.

"To mu je ki yiwa Yaya umar abin da ki ka aikata"

Marairaicewa tayi ta ce "Dan Allah kayi haƙuri"

"Wallahi ba zan goyo ki a banza ba, ko ni sai na miki shegen duka yau" yana gama maganar ya danƙeta ya saɓata a kafaɗarsa dan zata iya ƙwacewa ta gudu.






Ayshercool
08081012243
[22/06, 9:49 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES


https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.



*AFUWAN BAN EDITING BA*


P6

Iya ƙarfinta take ihu, tana kiciniyar sai ya sauketa, amma yayi burus da ita, sai da ya je soron gida, sannan ya sauketa ya ja hannunta zuwa cikin gidan.

Aliyu ne a tsakar gida yana yiwa mama wanki, ya ɗago ya kallesu ya ce "Ya dai, ya kake jan ta tana ihu, makarantar fa?"

Hauzaifa bai amsa masa ya tambaye shi"Mama tana nan?"

"Eh tana nan" Aliyu ya bashi amsa.

Jin ihun ruma ne ya sanya mama katse sallar walahar da take yi, ta fito tana tambayar lafiya.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Yaya Umar, shi ma ya yi shirin fita. Duk suka zubo musu ido suna jiran jin ba'asi.

"Mama wallahi yarinyar nan ba ta da mutunci, daga sakata a makarantar nan ta fara tayar mana da hankali, yaushe yarinyar take da sikila ban sani ba?".

Mama ta ɗan yi sororo ta ce "Wace irin sikila kuma?"

"To haka ta je ta ce wai sikila ce da ita, ta tashi tsaye ma ta ƙi sai a bayana na goyota"

Yaya Umar ya kalleta ya ce "Ke meya sameki?"

Cikin in da in da ta ce "Dukana aka yi, kuma wallahi na ji zafi sosai shi ne na ce musu sikila ce da ni, na ga wata 'yar makarantar bokonmu ba a dukanta saboda sikila ce ita".

"Shi ne ki ke yiwa kan ki fatan ciwo saboda baki da hankali, ke dama za a zauna da ke baki yi abin da za a dake ki bane ba, me ki ka yi aka dake ki?" Yayi maganar cikin tsare gida.

Cikin kuka ta ɗage ƙafar wandonta, shatin bulala ya kwanta a kan fatarta, ta kalli mama ta ce "Mama kin ga fa, dan Allah a cireni wallahi ni ba zan iya makarantar nan ba, wai ban iya karatu ba shi ne aka yi mini wannan dukan, ni wallahi ba zan iya karatun nan ba, ga duka ga karatu mai yawa, da wanne zan ji?"

Cikin tsawa Yaya Umar ya ce "Wuce mu je makarantar, sai kin ci ubanki yau, ai dama karatu aka turaki ba wasa ba"
A karo na farko ta yi wa yaya Umar gardama tana kuka, ta riƙe hannun Huzaifa, ta ɓuya a bayansa.

"Ni nake miki magana ki ke ɓuya a bayansa, ba zaki fito ki wuce ba"

"Dan girman Allah kayi haƙuri, wallahi idan suka san ƙarya nake, sai sun kusa kashe ni, wallahi duka ake na tashin hankali a makarantar nan" kuka take wiwi kamar wadda aka yiwa mutuwa, mama dai ta kasa magana.
Huzaifa kuwa janyota ya yi daga bayansa, ya ce Wallahi ba zai kareta ba sai dai ayi mata duk abin da za ayi mata.

Yaya Sadik ne ya fito daga ɗakinsu, yana zuwa ya ture Umar, ya kamo hannun Rumaisa, ya wuce da ita ɗakin su.

Suna shiga ya zaunar da ita, shima ya zauna ya ɗan ƙura mata ido sannan ya ce "Auta, meke damunki ne, kullum sai an yi rigima dake an ce ba kya ji, ke ko haushi ba kya ji?"

Ta girgiza kai ta ce "Wallahi ina jin haushin yadda aka tsane ni kullum ace bana ji"

"To yanzu meyafaru, har aka dake ki ki ke cewa sikila ce dake? Kin san sikila kuwa meyasa ki ke fatan wannan ciwon?"

"Gani nayi za a kashe ni da duka, ni bana son a dake ni".

"Gaskiya ba ka kyautawa, dan me yarinya za ta yi laifi ka hana a hukunta ta, me kake ƙoƙarin koya mata ne?" Umar yayi maganar a mugun fusace.

Yaya Sadik ya waiwayo ya kalli Hussainin na sa, ya haɗa hannayensa alamar ban haƙuri ya ce "Tuba muke, zan wa tufkar hanci in sha Allah, on behalf of her, ayi haƙuri gobe in Allah ya kaimu da kaina zan mayar da ita makarantar in basu haƙuri" gajeren tsaki Umar yayi yai waje, babu wanda yake masa katsalandan kamar yadda Abubakar yake yi masa, ya fuskanci idan aka biyewa Yayan nasa ruma tsiyarta zata tsula ba tare da an kwaɓeta ba, da tayi laifi sai ya ce ƙuruciya ce.

Wunin ranar kowa share ruma yayi, yaya Sadik ne kawai yake kulata, Huzaifa da yasir suka ƙare mata zagi tsaf suka tsangwameta.
Ko a jikinta, tun da Allah ya sa ba a mayar da ita makarantar an ce ƙarya take ba, hankalinta ya kwanta.
Washegari Yaya Abubakar da kansa ya rakata makarantar, aka dinga yi mata sannu ana mata ya jiki, ta basar ta dinga amsawa.

************

Sanye yake da fararen kaya ƙal, fuskarsa sanye da fari siririn glashi, taku yake cike da ƙasaita ya biyo wata doguwar baranda.
Sannu a hankali ya ƙarasa gaban wata ƙatuwar ƙofa, ya sa hannu ya murɗata a hankali. A take ta buɗe wani sassanyan ƙamshi ya daki hancinsa.
Da sallama ya shiga ya mayar da ƙofar ya kulle, babu kowa a falon sai wata matashiyar budurwa tana saka turaren wuta.
Amsa masa tayi tare da faɗin "Sannu da zuwa".

"Yauwwa 'yar aikin Ammi, ina ma'aikatan ne ki ke aikin da kan ki?"

Ta ɗan kalle shi sannan ta ce "Nima 'yar aikin ce ai" yayi murmushi ya ce "Sorry idan haushi ki ka ji, ina Ammi?".

"Bacci take" ta bashi amsa lokacin da take cigaba da saka turaren wuta.

"Ba kowa kenan?"
Cikin ƙosawa da tambayoyinsa ta ce "Duk sun tafi makaranta".

"Ke me ya hana ki je makarantar?"

"Ohh God, uncle J am sick shi ya sa ban je ba, Ammi idan kana son ganinta ka dawo an jima, ina fatan zan iya tafiya na gama amsa tambayoyin ka?"

Ya girgiza kai ya ce "No, saura ɗaya ina yayan ku?"

Tayi murmushi ta ce"Wannan tambayar ai kai yakamata a yiwa, i don't know " daga haka ta bi wata hanya ta bar falon.

Ya girgiza kai a hankali ya ce "Wannan yarinyar ta fi mai kora shafawa, izzarki tayi yawa"
Wayarsa ce ta fara ringing, ya zura hannu a aljihunsa ya ciro wayar.

"Ke nifa kin isheni, ni kaina ban san in da yake ba, anjima kuma kilisa zan fita, zan neme ki amma" daga haka ya kashe wayar, ya saka a aljihunsa ya fice.

*********
Ruma ta sha kashedi a wurin su Huzaifa, a kan ta shiga hankalinta a makarantar nan, dan ba ƙaramin girmansu ake gani ba, halinta ba zai sa mutuncinsu ya zube ba.
Ta cigaba da zuwa makaranta, amma ba ta gane komai, idan Yasir ya zaunar da ita zai koya mata kuma, sai ta ce ita ta gaji ba ta so.

Ranar wata juma'a da yamma, Abdallah yana ta haɗa kayan miya, za a kai markaɗe, Yasir ya kalleshi ya ce "Abdallah kyanta na ɗau hotonka kana haɗa kayan miyar nan, na je na nunawa yarinyar nan mai awara".

Haɗe rai Abdallah ya yi ya ce "A'a mai wake zaka nunawa ba mai awara ba"

Yasir ya yi dariya ya ce "Zaka ga mai wake, wallahi yarinyar nan ta mato a kan ka, kawai ka nutsu ku daidaita, wallahi shar da kai awararka zaka yi ta ci"

"Na rantse idan ba ka yi mini shiru ba sai na ɓarar da kai"

Yasir ya ce "Yaya ba zan ƙoƙari na tayata kafa gwamnatin ta ba, kullum sai ta kyauta mini".

Buut Ruma ta fito daga ɗaki ta ce "Yasir yakamata muje ka gabatar mata da ni, na dinga biyawa idan zan je makaranta".

Tsaki Yasir ya yi "To munafuka waye ya sako dake, na zaci ma bacci take wallahi "

Abdallah ya ce "Wallahi ko da wasa ki ka je, sai na kakkarya ki".

"To ni ce maka ma nayi zan je?"

"Ke dai ki ka sani gulayya" Yasir yayi maganar yana hararta.

"Wallahi ni ba gulayya ba ce" shareta suka yi suka cigaba da hirarsu, yayin da Ruma ta koma gefe tana naɗar abin da suke faɗa.

Kamar yadda a islamiyya ruma ba wani ja take ba, haka ma makarantar boko ba uwar da take ganewa sai wasa.
Ta na cikin top 10 na marasa ganewa a aji, sannan ta farko a sahun marasa ji.
Yau bayan an taso daga makarantar boko, ta biyo ta hanyar da lambun mai unguwa yake. Ƙaton lambu ne da ya kasance mallakin wani a babba masarautar Kano, wanda yake ƙarƙashin kulawar mai unguwa, ba kowa ya san da hakan ba sai ɗaiɗaikun mutane.
Gaba ɗaya hanyar ba ta cikin jerin hanyoyin da zata bi su sada ta da gida, amma tun da ta ji 'yan ajinsu suna labarin mangwaron lambun ya fito yayi kyau, tayi alwashin bi ta hanyar dan ganewa idonta abin da suka gaya mata.
Aikuwa babu ƙarya, lambun ƙato ne na gaske, wani wurin an kewaye shi da katangar bulo, wanu wurin kuma aka ƙarasa kewaye shi da waya.
Akwai bishiyoyi kala-kala a ciki, wasu duk sun yi 'ya'ya kasancewar lokaci ne na damuna.
Mangwaron nan yayi 'ya'ya sosai gwanin ban sha'awa.
Ƙatuwar ƙofar shiga wurin ta gani, babu kowa a wurin, dan haka kai tsaye ta kutsa a gaban wata ƙatuwar bishiyar mangwaro ta tsaya, yanayin wurin yayi mata kyau sosai da sosai.

Ta samu dutse, ta dinga jifan bishiyar, suna faɗowa tana ɗiba, ta tara ta cika jakarta, sannan ta nufo hanyar fitowa.
Tana fitowa wani matashi yayi caraf ya danƙeta yana faɗin "Alhamdilillah, shegiya ɓarauniya ashe ku ne masu shiga lambun nan suna ƙurguma mana sata".

"Ban gane ba wace iri ɓarauniya me nayi maka?"

"Zaki ga me ki ka yi mini, gidan mai unguwa zan kai ki, ke saboda ƙwarewa ma, da ki ka sata sai ki ka biyo ta ƙofa zaki fita, kina 'ya mace kina sata"

Cikin rashin kunya Ruma ta ce "Wallahi ni ba ɓarauniya bace ba, ta ƙofar nan fa na shiga, ba wanda ya haura gida ne ɓarawo ba?"

"To da ki ka bi ta ƙofar, wa ki ka tambaya ki ka shiga ki ka ɗebo abibda ba naki ba?"

"A'a, to ni wa na gani a wurin, kuma ma naga ai bishiyar ta Allah ce, Allah ne ya fito da ita, kuma sai ace sai an tambayi wani sannan za a ɗau abin da Allah ne ya fito da shi, kai iskar da ka ke shaƙa wa ka tambaya ka ke shaƙarta?" Saroro ya bi ruma da kallo, wata 'yar cukul da ita sai shegen surutun tsiya.

"Zaki yi bayani, sai na kai ki gaban mai unguwa"

"Daɗinta shi mai unguwar ba shi da wutar da zai sakani, kuma duk in da za a je ai bishiyar Allah ce, kuma ka sakar mini hijjabi dan ni ba 'yar iska bace ba.
Bai ko saurareta ba, ya figi hijjabinta ya fara janta.
"Ka dai na ja na haka kamar wata akuya, ba ƙaramin aikina bane na cire maka hijjabin nan na ƙara gaba.




Mama sai kallon agogo take yi, tana kallon hanyar shigowa, amma babu ruma babu alamunta.
Tsakar gida ta fito tana kiran Usman, kasancewar shikaɗai ne a gidan, ya dawo da wuri bashi da lectures.
"Ka ga haryanzu yarinyar nan shiru ba ta dawo ba"

Usman Ya ce "wataƙila tana can tana rashin hankali a titi da ƙawayenta, amma maybe ki ganta yanzu".

"A'a zunnuraini, shi biyu da rabi fa take dawowa amma kalli yanzu ƙarfe ɗaya da rabi, hankalina ya kasa kwanciya"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Kuma fa kamar ma ga 'yan makarantar su lokacin da nake hanyar dawowa, amma bari na je makarantar ta su" yana rufe bakinsa, suka ji ana ƙwala sallama a waje.

Usman ya amsa, ya nufi ƙofar gidan, aikuwa yana zuwa ya

4 Comments On KANWAR MAZA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Anayi munajin dadi

avatar
maryam-2-7-4

11 months ago

Reply

Anayi munajin ddi

avatar
maryam-2-7-4

11 months ago

Reply

Yyu kyau

avatar
hauwau-8-4

8 months ago

Reply

Dan Allah qarashen fa

Please Login or Register in order to submit comment