Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Habiba, kuma duk da haka bai isheta ba, ta ɗauko yayanta suka biyo Sani gida shima suka daka, haka ake yi fisabilillahi wallahi sai da na biya na kai ta chemist aka yi mata allura.
Dawowata gida kenan bana nan kawai na tarar da yarinya baki ya haye, ya fashe ta riƙe kai sai kuka take, shima Sani kalli fuskarsa duk shatin mari tsakani da Allah Wannan adalci ne?" Ta ƙarasa maganar tana haska fuskar Habiba. Fuska ta kumbura suntum, bakin ko rufuwa baya yi, leɓen sama ya ɗage ya kusa danganawa da hancinta, duk dadashi a waje.
Duk da halin da Rumaisa take ciki na fargaba, amma sai da ta ƙunshe baki tayi dariya ƙasa-ƙasa, saboda yadda fuskar Habiba ta koma kamar an naushi fura.

Jiki a sanyaye Mama ta ce "Dan Allah dan annabi kiyi haƙuri, yaran yanzu ne sai addu'a kawai, kin ga ni ban ma san tayi ba, daga ita har yayan nata babu wanda ya zo ya gaya mini, ban ma san waye ba a cikin yayyan nata ba, amma kiyi haƙuri".

Haidar yayi gyaran murya ya ce "Mama nine, su meyasa yaran ba a tambayesu me suka yi mata ba, hijjabi a hannu suka biyota da bulalai zasu daka.....

"Rufe mini baki ban tambayeka ba" Mama ta dakatar da haidar cikin tsawa.

Mama tayi ta bawa Babar su Habiba haƙuri, amma ba kunya babarsu Habiba ta ce "An bar yara babu tarbiyya su yi ta abin da suka ga dama, saboda tana taƙamar ita ƙanwar maza ce, sai tayi ta isakancin da ta ga dama, sai ta kashewa yarinyar fuska ta cuceni, wallahi ban da ana maƙota da sai na kai maganar wurin hukuma, dan ba zan yadda ba, ita ta dakar mini 'ya, shi kuma ya zo ya zage ƙwanji a kan ɗana".

Cikin muryarsa mai ban tsoro da babu alamar wasa a cikinta ya ce "Ke ya isheki haka malama, ke kamar ba uwa ba, kawai ki zo gaban mace kina cewa 'ya'yanta basu da tarbiyya, tana baki haƙuri kina cigaba da ƙanan maganganu, kar Allah ya sanya ki haƙura ɗin, ki kai duk in da zaki kai ki je ki faɗa, kuma ko yau wani ya kuma yinƙurin taɓa Rumaisa a unguwar nan, sai mun nuna wa duniya ƙanwar maza ce, fice ki bawa mutane wuri"
Mama zata yi magana, amma mai sunan Baba ya haɗe rai, ya girgiza mata kai, tare da nunawa Babarsu Habiba hanyar fita.

Jiki na rawa ta saka su Sani a gaba suka fice, duk girma da ƙanƙantar mutum, babu wanda Umar baya yi masa kwarjini.

Sai da ya tabattar sun tafi, sannan ya dubi ƙofar Kitchen ɗin ya ce "Ke kuma fito nan munafuka" aikuwa kamar munafukar ta fito tana sunkuyar da kai ƙasa.

Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Muna zaman zamanmu lafiya aka haifeki, shegiya kamar rainon iblis, duk gidan nan babu mai fita ya ɗauko magana sai ke, tana zaman zamanta kin saka an zo har cikin gida ana gaya mata maganganun banza saboda ke, kai ma saboda hauka dan me zaka biye mata ku je kuna dukan 'ya'yan mutane? Waye ya aiketa ta tsokane su?".

Ran Aliyu ya ɓaci, ya harzuƙa ya ce "Bafa maganar hauka a nan, yarinyar nan hijjabi a hannu suka biyota, ba dan filin ball ɗin mu na hanya ba, haka zasu haɗu su yi mata duka, yara maza ba mata ba, har sun fara dukanta baiwarsu ce ita, ko kuma ce musu aka yi ba ta da gata?.

"Shut up! Ita ka san me tayi musu, wannan Yarinyar da rashin jin tsiya, ai gara su zane ta gobe ba ta kuma ba, ki cigaba da zuwa ki na janyo mata magana, wallahi ba zaki ɗora mata hawan jini a banza ba, da ki cigaba da ɗauko mata magana ana zuwa ana gaya mata maganar banza, gara na takeki na murɗe miki wuya ki mutu kowa ma ya huta".

Tun da Mai sunan Baba ya fara sababi, Sentence ɗinsa na ƙarshe ne ya baƙanta mata rai, wai ya murɗe mata wuya ta mutu su huta. Ta yi shiru ya gama bala'insa ya ce ta wuce ta cigaba da yi masa aikinsa, ya fice.

Rumaisa tana aikin tana kuka, wato ma ba'a sonta, wai da suna zaman zamansu aka haifeta, ta hana mahaifiyarsu kwanciyar hankali.

Usman ne yayi tsaki ya ce "Wallahi Mama ɗan nan naki yana da matsala, na yi shiru ne kar na tanka masa yayi mini tijara, amma ba damar yarinya ta motsa sai faɗa, ke Ruma" ya kirata.
Ta goge hawayenta, ta fito daga Kitchen ɗin.

Ya kalleta ya ce "Duk shegen da ya takaleki kar ki raga masa, ki ci uabnsa idan yafi ƙarfin ki muna nan, yaran unguwar nan marasa mutunci, ki ka zama nusara raina ki zasu yi, duk ɗan da ya miki ki ci ubansa ko mace ko namiji mun tsaya miki".

Mama ta ce "Zinnuraini, kai ne kake zigata ta ɗauko magana?".

"A'a Mama bance ta ɗauko magana ba, amma duk wanda yayi mata, ta rama babu nusari a cikinmu, ƙanwarmu ba zata zama nusara ba, mu ci uban mutum ya zo kawo ƙara mu ƙara masa"

Martanin Yaya Usman ne ya ɗan sanya hankalin Rumaisa ya kwanta, ta kammala yiwa Yaya Umar aikinsa ta je ta nemi wuri ta kwanta, ko gurasar da Yasir ya bata ba ta ci ba.
Tana kwance lamo a kan katifarta, ta ji muryar Huzaifa a kanta yana cewa ki cigaba da ɗauko magana, ai gara ya murɗe miki wuyan ki mutu kowa ma ya huta da tijararki da rashin hankali.
Banza ta yi masa, kamar ba da ita yake ba, dan idan ta ce zata biyewa Huzaifa faɗa za suyi, kuma a kowane lokaci mai sunan Baba na iya shigowa, yadda yake a ƙule da ita ta san sai jikinta ya gaya mata, idan ya dawo ya tarar suna faɗa da Huzaifa.

Da safe bayan gaisuwa ba abin da ya haɗata da mutan gidan, tana kwamce a ɗaki, 'yan mazan suka gyara komai na gidan, suka ɗora abin kari. Ko ta kan abincin safen ba ta bi ba, ta saye gurasarta a hijjabi, ta ɗau allonta ta tafi makarantar allo.

Sai dai ashe tuni labari ya iske shugaban makarantar su, a kan faɗan da suka yi jiya, malam babba ya tara su ya ce sai ya zane su.
Idon Rumaisa yayi tsilli-tsilli, dan kusa bulalar malam Babba akwai ɗan karen zafi.
Kan Malam Babba ya kai ga zuwa ya yanke musu hukunci, ta zari allonta ta kwasa da gudu, ya tsaya yana ƙwala mata kira, amma tayi burus ta bar makarantar ta kama hanyar komawa gida, dan a rayuwar Rumaisa ba ta ƙaunar duka ko kaɗan.

A soro suka yi karo da Yaya Usman zai fita, ya tsaya yana kallonta, har zata wuce ya ce "Wai me kika dawo yi ne gidan nan yanzu, ina Makarantar kuma?"

Ta tura baki ta ce "Kashi nake ji shine na dawo gida"

Tsaki yayi ya ce "Haka dai kika iya, wannan uban cin da kike yi, ba dole kullum ki kasance cikin zawo ba, baki da aiki sai kashi da tusar tsiya" banza tayi masa ta raɓe shi ta wuce tana murguɗa masa baki, ba tare da ya sani ba.

Ta shiga cikin gidan tana ciccin  magani, ihuu tayi, tare da tsalle ta nufi in da wani dogon matashi ke zaune, mai tsananin kama da Yaya Umar, sai dai banbancinsu, Yaya Umar fari ne shi kuma bai kai shi haske ba, sannan shi wannan fuskarsa ɗauke take da murmushi saɓanin fuskar Yaya Umar.

Babu tunanin komai, ta faɗa jikinsa tana murmushi.
Shima rungumeta yayi yana murmushi ya ce "Autar Mama, tun ɗazu zaman jiran dawowarki nake yi".

"Babban Yaya, yaushe ka dawo?"

"Tun ɗazu na dawo, nace kina ina aka ce kin tafi makarantar allo".

"Wayyo daɗi, yaushe rabon da na ganka, gaba ɗaya gidan babu daɗi, kowa ya tsane ni, har da cewa na ishesu wai kamar su murɗe mini kai su huta".

Waro ido yayi ya ce "Wane mara ta idon ne yayi wannan iƙrarin a gidan nan?" Ta waiwaya sannan a hankali cikin raɗa ta ce "Waye banda ƙaninka, ya tsaneni wallahi".

Yayi murmushi ya ce "Ai ba wanda ya isa ya taɓa mini auta ina raye, ai gani a gidan na dawo".

Wani matashin ne ya sake fitowa, yana faɗin "Iya rigima, ya halinki?"

Sake waro ido ta yi ta ce "Yaya Abdallah".

Ya amsa da "Na'am uwar rikici".

"Haɗa baki kuka yi duk kuka dawo yau kenan?"

Abdallah ya ce "Eh haka ne, su Baba Atine suna ta gaisheki, sun ce ke ba kya zumunci"

Ta taɓe baki ta ce "Waye zai barni na je garin, ai ni ina son zumunci kai ni ne ba ayi" Gaba ɗaya sai ta manta da damuwarta, ta shantake suna hira.
Sai da aka jima sannan ta shiga ɗaki ta ajiye allonta.

Sabgoginta ta shiga yi, ta zage ta ce ita zata yi wa su Babban Yaya girki, abincinta zasu ci.
Aikuwa faɗa ya kaure, Huzaifa ya ce ba zasu ci jagwalgwalonta ba su zasu yi girkinsu, ƙarshe Yaya Sadik ya ce na Rumaisa zai ci.

Zuwa Azahar gida ya ɗinke kowa ya hallara a falon Mama suna cin Abincin rana, Sadik sai jinjinawa ƙoƙarin Rumaisa yake ta yadda ta iya girki mai yawa haka, Huzaifa da Yasir kuwa sai kushewa suke yi.

Zaratan maza ne su bakwai sai Rumaisa, Mama a hankali take binsu ɗaya bayan ɗaya da kallo, tana tuna baya.

Hadiza shine sunan Mama na gaskiya, haifaffiyar garin Kano ce, unguwar mandawari. A nan ta taso tayi karatun boko da islamiyya, sai dai tana aji uku na Sakandire, ta haɗu da mahaifinsu Rumaisa, Muhammad Aminu a nan unguwar sabon sara, amma asalinsa ɗan garin Katsina ne, yana zuwa gidan wan mahaifinsa ne a Kano yana koyan harkar kasuwanci, a nan suka haɗu suka yi aure, kan Hadiza ta gama makarantar sakandare.

Haihuwar fari Mama ta haifi tagwaye Abubakar Sadik da Umar faruk sune 'ya'yanta na fari, Sai ta kuma haihuwar Usman, sai Aliyu, Abdallah da Huzaifa, Yasir ne kawai ba ɗan ta ba, ɗan ƙanwar mahaifinsu Rumaisa ne, ta haife shi da kwana kaɗan Allah ya yi mata rasuwa, a lokacin Mama tana shayar da Huzaifa sai ta haɗa su ta shayar da su tare, ba zaka taɓa cewa ba 'yan biyu bane ba, ko ba ita ce ta haifesu ba.
Mama gaba ɗaya tayi tunanin ta daina haihuwa, saboda galibi bai fin shekara biyu uku a tsakanin yaran take haihuwa, amma bayan haihuwar Huzaifa sai da ya shekara takwas, kawai ta daina ganin al'ada, sai ga cikin Rumaisa.
Tun da Allah ya sa ta haifi Rumaisa, kowa ya ɗauki soyayya ya ɗora mata, kasancewarta kallabi a tsakanin rawuna, kowa babban burinsa ya faranta mata.
Mahaifinsu Rumaisa, mutum ne mai matuƙar kulawa da son iyalinsa, kasancewar Ruma ce kaɗai 'yar sa mace yafi kowa ji da ita, ba shi da magana sai ta Rumaisa, Akwai tsananin ƙauna da shaƙuwa a tsakanin Ruma da mahaifinsu, dan kusan tafi son sa a kan Mama, saboda Mama akwai faɗa, Abba kuwa lallaɓata yake. kwatsam Allah ya yi masa rasuwa tana da shekaru uku kacal a duniya, bayan yayi gajeriyar rashin lafiya.
Bayan rasuwar sa sai da Rumaisa tayi cuta kamar ba zata rayu ba, saboda alhini. Dangin mahaifin su Rumaisa suna da zumunci sosai, sun so a rarraba musu yaran su riƙe su, amma Mama ta ce ba ta son a raba nata kan yaranta, dan haka ta ce su ƙyale mata su.
Haka tayi ta ɗawainiya, 'yan uwa da abokan arziki suna taimaka mata da abin da zasu iya
Tasowar Rumaisa a cikin 'yan mazan nan, wannan ya ɗauka wannan ya sauke ya sanya ta taso tamkar namijin ita ma. Ba ta jin magana ga rashin tsoro, ga tsiwa da ɗan karen surutu da iyayi, gashi lokacin da take tasowa girma ya fara kama Mama duk tayi sanyi, dan haka ta mayar da Mama kamar wata kakarta ba uwa ba.
Mutum ɗaya take tsoro shi ne Baban Mama, Yaya umar mai sunan baban Mama, Allah yayi masa kwarjini shi ko irin wasan nan na yarinta baya yi, ba shi da abokai, ga tsare gida ba shi da fara'a ko walwala baya son shiga mutane sam, idan kaga an taka masa burki kai tsaye to Yaya Sadik ne. Mama tana matukar girmama shi saboda sunan mahaifinta da yake da shi.
Yanzu Rumaisa tana aji huɗu na Firamare, Abubakar yana Dutse yana karatu,  babu wanda yake da cikakken ƙarfin ɗaukar ɗawainiyar gidan gaba ɗaya, amma kowa babban burinsa ya nemo ya kai gida, komai suka samu mahaifiyarsu da ƙanwarsu kawai suke tunani.

"Hajiya Mama, ya naga kina ta kallonmu ne kamar da baƙo a cikinmu".

Mama tayi murmushi ta ce "Allah nake yiwa godiya, da ya sanya duk ku ɗin nan nawa ne, Allah ya dafa muku ya ƙara haɗa mini kanku"

Suka amsa da "Amin"
Yasir ya ce "Mamanmu, maganin kukanmu Allah ya ƙara hore mana, mu gantataki fiye da kowace irin uwa a duniya"

Huzaifa ya ce "Hmm kamar gaske, nan fa kake zuwa da abin duniyarka ka hanata, ka hana kowa ka bawa waccan  yarinyar mai kama da Akushin"

Murguɗa baki tayi tana fari da ido ta ce "Tubarkallah zuƙul-zuƙul maye ya ci kansa da kansa, wallahi ni bana kama da Akushi, son kowa ƙin wanda ya rasa"

"Ke dalla ware, meye son kowa ƙin wanda ya rasa, aba Kamar gurguwar akuya" Yasir yayi maganar yana dariya.

Haushi ne ya kamata ta buɗe baki za tayi rashin mutunci, ta sanya idonta a cikin na Umar, ta haɗa maganar da zata yi, da lomar abincin ta haɗiye.

Suka gama cin abincin, Yasir ya kwashe kwanuka, ya fara ƙoƙarin wankewa, Huzaifa ya shigo da tsintsiya zai share ɗakin, Umar ya ce ya ajiye tsintsiyar ya bawa Rumaisa ta share.
Haushi ne Yakamata ta lura tun da aka kawo ƙararta ya tsaneta, dama can ba wani shiga shirginta yake yi ba.
Bayan ta kammala sharar ta nemi wuri za ta kwanta Mama ta kalli kan Rumaisa, da ta fara tsifa, tayi rabi ta bar rabi ta ce "Fita ki bar mini ɗaki, karki sake shigowa sai kin gama wannan tsifar.

Fitowa ta yi ta na tura baki, tana nema ta yi kuka.
"Autar Mama, meya ɓata miki rai ne?" Cewar Yaya Abubakar da yake ƙoƙarin shiga ɗaki.
Dama ƙiris ta ke jira, dan haka ta fara kuka "Ba mama ce ta koreni daga ɗakinta ba, wai sai na gama tsefe kaina ba, ni mama ta tsaneni".

Girgiza kai ya yi ya ce "Yi haƙuri ki daina kukan, bari na zo na tayaki tsifar"
Haka suka zauna ya samu kibiya ya tsefe mata kan tsaf, suka wanke gashin, ya ce da safe zai bata kuɗin kitso.
Mama ta na kallonsu ba ta kula su ba, ta cigaba da sabgoginta.

Abdallah yana ta dube-dube a kitchen, ya ci karo da allon Rumaisa, duk gefensa ya karye, ga rubutun jiki yayi baƙi ƙirin, ba ta sake wani ba.
Ya fito da allon a hannunsa ya ce "Ruma, wannan allon naki yaushe zaki yi wani rubutun?" Ta haɗe rai ta ce "To ban iya ba, sai na iya zan wanke".

"Haka dai, ba kya ja a ko ina, daga arabin har bokon, Allah ya sa su zaneki idan ki ka je sati mai zuwa, baki wanke allon kin yi wani rubutun ba, gandamemiya da ke amma haryanzu a izifi biyu ki ke"
Sai da yayi wannan maganar ta tuna yadda malam Babba ya dinga ƙwala mata kira amma ta gudo gida, yanzu sati mai zuwa ta yaya zata je makarantar allon? Kuma muddin abin da ta yiwa malam ya zo gidan nan, ta san ta kaɗe".

"Astagfrillah, ni 'ya su meyasa haka ne, garin in gujewa wani hukuncin sai na faɗa wani tarkon, ya zan yi da raina?.

Ayshercool
08081012143

Kar a manta ayi subscribing YouTube channel ɗina na Cool hausa tv
[18/06, 2:35 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA

      BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION


      p 4



Ko da sati ya zagayo, Mama tana sa ran ta ga Ruma ta shirya ta tafi makarantar allo, amma ta ga bata da niyyar yin hakan.
Sai ma aiki take a tsakar gida, wanda ba ta saba ba, tana naɗe yayyenta je komai.
Aliyu ne ya fito daga banɗaki, hannunsa riƙe da buta ya kalli Ruma ya ce "Ke ina makarantar allon?"
Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Ni na cire kaina na daina zuwa".

"Saboda ke ki ka saka kanki, shine sama ta ka ki ka cire kan ki ko? Da alama baki da gaskiya"

Mama ta fito tsakar gida ta ce "Ali ajiye butar nan ka je mini makarantar allon ka ji me ta aikata, dan ban yadda da ita ba"  dan jikinta ya bata Ruma wani laifin tayi.

"Wallahi Mama ba abin da na yi, ba sai ya je makarantar ba, idan ya je ma sharri za su yi mini, ba sa sona malaman"

Mama ta ce "Au malaman ne suke miki ƙarya Rumaisa, ai ko me za ace mini kin aikata ba zan musa ba"

Huzaifa daga cikin ɗaki ya ce "Dama saboda ƙawayenta ya sa ta ce ita ma a sakata a makarantar, ba dan Allah take zuwa makarantar ba ".

Aliyu ya saka jallabiyarsa ya tafi makarantar allon.

Bayan fitarsa rantse-rantse take ta yiwa Mama, akan ita fa ba abin da ta aikata a makarantar nan, amma Mama ta shareta.

"Ruma!"

"Na'am Yaya Sadik "

"Zo ki sayo mana ƙwai ki soya mana mu karya"
Kasancewar Ruma akwai kwaɗayi, ya sanya ta daina fargabar zuwan Aliyu makarantar su, ta karɓi kuɗi ta tafi aiken da Abubakar ya yi mata.

**********

A kashingiɗe take a kan kujera, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta tattara dukkan wata nutsuwarta a kan ƙatuwar wayar hannunta, da alama ko me take kallo mai muhimmanci ne.
"Samha me ki ke wa wannan kallon ƙurillar ne?"

Wadda aka kira da Samhan ba ta motsa ba, balle ta daina abin da take yi.

Hannu ɗayar ta saka, ta zare wayar daga hannun Samhan, tana dubawa.
Har a wannan karon, Samha ba ta yi motsi ba, balle ta karɓi wayarta ta ba.

"Samha kina da hankali kuwa? Wai dan Allah da gaske ki ke dama?"

Samha ta ja ajiyar zuciya ta ce "Nusaiba, ke da kin ɗauka da wasa nake yi dama?"

Nusaiba ta jinjina kai ta ce "Eh, ni ban san abin da ki ke faɗa har zuciyarki ba"

Samha ta gyara zamanta ta kalli Nusaiba, cike da son tabattar mata abin da take faɗa ta ce "Nusaiba, ban fara dan na daina ba, ko zan tafi tsirara zan mallaki abin da zuciyata take muradi"

Nusaiba ta ɗan jinjina kai ta ce "Amma ya batun alaƙa fa, ko kin manta?".

"Alaƙa bata gabana, na san a yadda zan yi wasana. Kar ki manta anjima akwai walima a gidan Shamaki"

"Hmmm Allah ya kaimu, Allah ya sa ba wani banzan abun zaki yi ba".

Wani ɗan guntun murmushi Samha tayi, ta ce "Koma dai menene, we should see"

********

Ko da Runaisa ta dawo gida daga aiken Yaya Sadik, tana daga tsakar 6 tarar da Yaya Aliyu a falo yana wassafawa Mama abin da aka gaya masa a makarantar allonsu, ga Yaya Umar a zaune.

"Wallahi mama ba ki ji yadda ake complain a kan yarinyar nan ba, malaminsu ya ce dama ko ta dawo korarta za su yi, ba karatun take yi ba, sai tsokana da fitsara, da damben da yaran mutane, wai sam ba ta da nutsuwa da ɗa'a, malam Babba ya tara su zai hukunta su sun yi laifi ta ɗau allonta ta gudu, yana kiranta amma tayi masa banza".

Cike da fushi Umar ya ce "Ba kune kuke goya mata baya take wani rashin mutuncin ba, tun da ta san ko me ta ɗauko zaku tare mata ba, ku bari ta tsokano waɗanda zasu nakasata yadda gobe ba zata ƙara ba. Babu wanda yake faɗar alkhairi a kan ta sai sharri" ya ƙarasa maganar yana fitowa tsakar gida cike da fushi.suna yin ido huɗu da Rumaisa ta saki ƙwan hannunta a ƙasa ta na ja da baya, saboda tsoro da fargaba.

Taku biyu ya yi ya danƙota, ya sanya hannunsa ya riƙe kunnenta ɗaya da ƙarfi.
Wani irin ihu ta kurma tana riƙe hannunsa, saboda ji tayi kamar zata ɗaga kai ta ga kunnen a hannunsa, saboda azabar zafi.

"Dan ubanki idan har ba zaki canza hali ba, makarantar kwana zan kai ki, tunda ba ki in da yake miki ciwo ba, ko mu mayar da ke can ƙauye, su miki aure"
Usman ya ce 'Ai Rumaisa sai ka ce wadda ta sha nonon aljana, hatsabibancin ta yayi yawa, ba ta jin magana sam"

Abubakar ne ya fito daga ɗakinsu a fusace, ya ƙaraso ya riƙe hannun Rumaisa, ya kalli Yaya Umar ya ce "Sakar mata kunne" Umar ya ɗan yi turus yana kallon Sadik.

"Baka ji bane?"

Sadik ya maimaita masa. Yaya Faruk ya saki kunnen Rumaisa, da idanunta tuni suka yi ja saboda kuka.

Ya janyota ya zaunar da ita a kan tabarma, ya dinga share mata hawayen fuskarta.

Cikin ɓacin rai ya ce "Yakamata ku dinga yiwa kan ku adalci a kan yarinyar nan, ita kaɗai ta tashi a cikinmu mace, tayaya zaku ce sai kun tanƙwarata yadda ku ke so? Tayi laifi kowa yayo kanta, ba mai yi mata nasiha, daga mai ce mata munafuka sai me ce mata aljana haka ake rayuwa?"

Yasir ya ce "Wallahi Yaya Sadik, duk ranar da yarinyar nan ta kwaikwaya maka rashin mutuncin da take aikatawa zaka gane ba tsanarta aka yi ba"

"Koma dai yane, a dinga barin yarinya ta huta a daina takura mata haka "

Guntun tsaki Umar ya ja, ya fice daga gidan gaba daya, suna zaman zamansu Mama ta haifo wannan 'yar kalen hanjin da ta gallabi rayuwarsu.

Yau cikin dare, Mama ta tashi tana ibada, kamar yadda ta saba domin a cewarta wanda duk ya tara zuriya yake neman kuma dacewa, bai ga ta bacci ba.
Fitilar ɗakinta ta kunna, haske ya gauraye ko ina, Rumaisa tayi rashe-rashe a kan katifa, zaninta daban ita daban daga ita sai wando, kanta ko ɗan kwali babu.
Mama ta girgiza kai, ta janyo zanin ta ɗaura mata, ta saka mata hula ta lulluɓeta, sannan ta fice ta ɗauro alwala ta zo ta tayar da salla. Sai dai sam Ruma ba ta san an yi bama, tana ta fama da bacci.

Can Mama ta kuma juyawa, amma ta ga Rumisa ta kuma yada zanin, ƙafafuwanta duk suna ƙasan katifar, ta kuma tumɓur tana bacci.
Haushi ne ya kama Mama, ta ƙarasa in da take, ta ɗala mata duka a cinya. Amma maimakon ta tashi, sai ta sake dunƙulewa tana bacci.
"Ke Ruma, ba zaki tashi ba sai na saka miki bulala?" Da ƙyar ta tashi tana murza ido tana kalle-kalle.

'tashi ki ɗauki rigarki ki saka, ki ɗaure kanki ki je ki yo alwala ki salla".

"Wai har asubar ta yi ne?"

Mama ta ce "Wato ke idan ba sallar farilla ba, baki san ki yi nafila ba, sai dai ki saki leɓe kina bacci. Ki je kiyi alwala ki zo ki yi salla ki roƙi Allah ya yaye miki wannan wautar da rashin hankali da kike fama da shi" kafin Mama ta gama maganar, Rumaisa ta sake ɓingirewa ta kwanta.
Aikuwa mama ta ƙule, ta janyo mafici ta shiga rafka mata a cinyoyinta, a razane ta miƙe tana sosh-soshe.
Mama ta bata riga da ɗan kwali ta ɗaura, ta korata tayo alwala.

Mama ta koma kan tata sallayar ta cigaba da salla.
Kusan mintuna arba'in, Mama ta manta ta tura Rumaisa tayi alwala, ta kalli shimfiɗarta taga bata wurin.
Da sauri ta tashi ta fita tsakar gida tana dubawa, sai dai babu Rumaisa babu dalilinta.
Lelleƙawa Mama ta hau yi, tana nemanta a cikin gidan amma bata nan.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina yarinyar nan ta shiga ne haka?" Tayi maganar lokacin da ta ƙarasa soro tana haska fitila, amma taga ƙofar gidan a rufe.

Ƙofar ɗakin samarin gidan ta tsaya tana bubbugawa da ɗan ƙarfi.
Usman ne ya taso cikin yanayi ya bacci, ya kalli Mama ya ce 'Mama lafiya kuwa?".

Cikin tashin hankali ta ce "Ruma na tasa tayi sallar dare, daga ta fito tayi alwala, na nemeta na rasa".

Ƙwalalo ido waje yayi, ya ce "Ruman? To ina ta tafi?"

Mama ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, na duba ƙofar gida tana rufe da sakata ba a buɗe ba"

Mamaki duk ya cika Usman ya ce "To in ta shiga a tsohon daren nan, bari na sako rigata a buɗe gidan a dudduba".

Ya shiga cikin ɗakin, ya kunna wutar lantarkin ɗakinsu, sai ga Ruma a tsakiyar su Yasir tana bacci.

Kunna fitilar

4 Comments On KANWAR MAZA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Anayi munajin dadi

avatar
maryam-2-7-4

11 months ago

Reply

Anayi munajin ddi

avatar
maryam-2-7-4

11 months ago

Reply

Yyu kyau

avatar
hauwau-8-4

8 months ago

Reply

Dan Allah qarashen fa

Please Login or Register in order to submit comment