Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina ba ya fara jin wannan muryar a kunnensa tamkar ana yi masa raɗa "Sarki mai koriyar alkyabba" a hankali ya buɗe idonsa, ya hau dube-dube a ɗakin, amma babu kowa.
Kawai sai ya ji ba ya son kwanciyar, dan haka ya tashi da sauri ya fito daga ɗakin.

Iman kuwa sai da ta tsaya ta share hawayenta, sannan ta shiga sashen Ammi.

Ammi tana nan a in da suka bar ta a falo ba ta tashi ba, Iman ta ƙaraso cikin yaƙe ta ce "Ammi, kin ga Mummy ce ta kirani ta bani"

Cikin mamaki Ammi ta ce "Ke da ki ka fita kaiwa Jabir lemo, me kuma ya kai ki sashin su? Kin san bana son zuwanki in da suke"

Iman cikin dakiya da ƙoƙarin danne hawayenta ta ce "Yaya Mahmud ne ya kirani, ya ce Mummy na nemana shi ne ta bani, bari na je na gwada" ta na gama maganar ta yi gaba, dan kar Ammi ta fahimci wani abu.

Takawa na tsaye a falon, har Iman ta yi gaba, ta ji ya janyota ya dawo da ita, ya ɗan ƙura mata ido.

"Me suka yi miki?"

"Wai ni? Babu komai fa, kaya kawai ta bani"

"Me suka yi miki?" Ya kuma maimaitawa.

Tunanin ƙaryar da zata yi masa ta hau yi, amma kan ta kai ga furta komai ya daka mata tsawa, hakan ya sanya jikinta fara rawa. Cikin razani ta gaya masa abin da ya faru.

"Wuce ki tafi" ya faɗa yana nufar ƙofar fita daga falon.

Ammi ce ta tare shi ta ce "Ban lamunta ba, kar ka kuskura ka je in da suke, da gayya suka yi, ka ƙyale su kawai"

"Ammi, ba saboda Iman kawai nake wannan abun ba, na san a duk lokacin da aka taɓata, kai tsaye ka aka yiwa, Ammi ko tausayin yarinyar nan ba sa ji?"

Ita kanta Nusaiba da ke zaune tana cin abinci, al'amuran gidan sun fara isarta, tana tausayin Iman sosai da sosai.

Ammi ta ce "Na fahimce ka takawa, amma tun da ka ga ina kawar da kai, to kai ma ka dinga haɗawa da haƙuri, ka koyi kawaici ba a komai zaka yi magana ba, kar ka kula su".

Baba Uwani da ke 'yan kaye-kaye a falon ta ce "Ayi haƙuri uban gidana, ban san ka da yawan hasala ba, Allah ya huci zuciyar magajin Galadima, ayi haƙuri"

Da ƙyar Adam ya haƙura, ya nemi wuri ya zauna, ya na jin yadda zuciyarsa ke tafasa,  shi dama ba ta Mummy yake ba, Mahmud kawai yake son ya yiwa kashedi a kan rayuwarsu.

Nusaiba tsam ta miƙe, ta nufi ɗakin Iman, ta tarar da Iman ɗin zaune ta zuba uban tagumi, tana kallon kayan da aka yi amfani da damar bata, aka ci zarafinta, kayan da basu wuce ta yi kyauta da ninkin su ba.

Nusaiba ta dafata ta ce "Masoyiya"

Iman ta kalli Nusaiba ta ce "Na'am Anty Nusyna"

Kallon idon Iman Nusaiba ta yi, idonta ya nuna ta yi kuka sosai.

"Be brave iman, kiyi haƙuri, ban san yadda zan fasalta miki abin da nake ji ba, idan aka cutar da ke ba, muna sonki sosai Iman, kin san yanayin halin da ki ke ciki, dan Allah ki daina damuwa ko ɓata ranki"

Iman ta yi murmushi ta ce "Kar ki wani damu, yayata ai na ma riga na saba"

Nusaiba ta zauna sosai ta ɗora da cewa "And yakamata ki daina nuna ki na jin tsoron su, musamman yaya Mahmud kamar mara tunani, abin da aka gaya masa kawai da shi yake amfani, ai gara ma yayi ya koma in da yake karatu mu huta masifaffen banza"
Iman ta toshe baki ta ce "Sai na gaya masa abin da ki ka ce, babu ruwana" tayi maganar tana dariya.
Ajiyar zuciya Nusaiba tayi tana murmushi, ganin yadda murmushi ya bayyana a kyakkyawar fuskar Iman.

***

"Ohh ni rumaisa sai girma nake, mama, ta bakin naki kwanci tashi asarar mai rai, na shiga jss2 fa"

"Aikuwa dai, kina ta girma amma babu nutsuwa ba"

"Kai mama, Allah ya nuna mini lokacin da zaki yabeni, ke kullum bana abin arziki a wurinki mamancy"

Mama ta girgiza kai ta ce "Ai ke gaba ɗaya abin tsiyarki ya ninka na arzikin yawa"

"Mama"

"Ina jinki"

"To ɗan kalleni mana"

Mama ba ta kalli ruma ba ta ce "Sai kuma kiyi ai"

"Dan Allah ki sai mini shayi da indomie, kin san bana son tuwon nan "

"Rumaisa ai ni ce ma Indomien, zo ki gutsiri in da ki ke so ki ci, tuwo kuma ban yi miki dole ba, ki barni da kayana"

"Allah ya jiƙan matar da ta ƙirƙiro tuwo idan musulma ce, amma ta cuceni zuciyata tafi raya mini a zamanin tsunburbura ta zo"

Ruma ta ƙaraci soki burutsunta, da gwasalewa mama tuwo, mama taƙi kulata.

Hankalin ruma ne ya tsaya a kan rediyon da mama take ji, wata mata tura wasiƙa, tana son a bata maganin da zata sha, tun da tayi yaye ƙirjinta ya zube kullum mijinta cikin yi mata gori yake.

"Kan uba, amma wallahi maza basu da kai, dan Allah meye haɗinsa da kallonta?" Mama ta ja rediyon ta kashe.

"Mama ya zaki kashe, ki bari mu ji mana, nifa bana son harkar watsewa, wallahi ka gaya mini maganar banza sai na tafi gidanmu, wannan ai rashin tarbiyya ne, ya ya zai din ga yi mata kallon ƙurilla, kuma mama ba kin ce mini ɓoyewa ake yi ba? Ita ma har da ita"

Mama dai ta basar, tayi mata shiru, can ta kuma cewa "Hmm kin san Allah mama, nima na gani fa, 'yan ajinmu na islamiyya suka ce, wai idan mace tana tafiya ba ta saka hannu a hijjabinta, maza kallonta suke yi, haka ma idan ta juya bayanta, jiya da na je gidan Asabe ban samo gawayi ba na je titi, daga nan na tsaya sayen mai, kin san riga da skirt na saka, sai mayafin abayat, wani mutum ya tsurawa gurin zamana ido, ai ban sani ba, ina waiwayawa muka haɗa ido, na ce malam kalli gabanka mana, baki ganshi ba babba da shi na saka hannu na kare abina har na zo gida".

Abdallah ya ce "Sannu jikar faisal, duk 'yan matan da suke kaiwa suna komowa a wurin, ba wadda ya kalla sai ke ƙwaila, wani ɗan abu kamar falanki, saboda asara ke zai tsaya kallo"

"Wallahi ni ba ƙwaila bace ba, kuma ka je ka tambayi kowa na wurin ka ji, kallona yake yi, ni kuwa na saka hannu na rufe"

Mama ta ce "Ya isa haka, kuma saboda tsabar rashin sanin ciwon kai ki tafi har titi da ɗan ƙaramin mayafin da bai fi ayi kallabi da shi ba, duk ranar da Allah ya nuna mini, sai na zane ki. Kuma zan saka bababana ya je islamiyyar lallai a raba muku aji da wannan yaron, dan sun fi ƙarfin tunanin ki"

Da sauri ruma ta ce "Ki yiwa Allah da ma'aikinsa, kar ki aika mai sunan Baba, kin san yanzu ƙiris yake jira yayi mini aure".

"Aikuwa ina daf da gaya masan, idan har baki nutsu ba, kin daina wannan rashin kan gadon ba, gara ya aurar da ke na huta"

Ruma ta saka hannu ta kama laɓɓanta ta ce "Na daina da yardar Allah"

***

"Takawa, wai yaushe zaka je ka ɗauko yarinyar nan ne?"
Ya ɗan lumshe idonsa ya buɗe sannan ya ce "Zan ɗaukota ne, gara ta ɗan huta ta nutsu tukuna, visarta har yanzu da saura"

Ammi ta ce "To shikenan, yauwwa ya maganar tafiyar da na ji Jabir ya ce zaka yi? Meye gaskiyar maganar?"

"Ammi ki manta da shi kawai, ɗan rainin hankali ne a wurin aiki ne za a tura mu wani bincike".

Ammi ta numfasa sannan ta ce "To, Allah ya yi jagora, amma dai duk da haka kamar yadda ya ce ka din ga kula takawa, ka san currently a ƙadamin da kake, kar ka janyo mana wata wahalar wadda muke ciki ba ta ƙare ba, dan Allah ka dinga komai a sannu, sannan ka riƙe addu'a kamar yadda nake jaddada maka"

"In sha Allah Ammi, kar ki damu ina iya ƙoƙarina wurin yin Addu'a".

"Haka ake so, Allah ya yi maka jagora"

"Amin Ammi".

Daga haka ya ɗauko wayarsa yana duddubawa, yana tsaka da duba wayar, Ammi ta kuma cewa "Ko yaushe Mahmud zai koma makaranta, na ga kamar lokacin komawarsa yayi, kuma ance mini haryanzu ana ganin gilmawarsa a gidan nan"

Takawa ya sauke wayar, ya dubi Ammi ya ce "Ammi, ba babarsa tana kallo bai koma ɗin ba ta zira masa ido, dan Allah ki daina damuwa da abin da ya shafe su, ki din ga ɗagawa kan ki hankali".

Ammi ta girgiza kai ta ce "Da kai da su ni duk abu ɗaya ne a wurina, ba zan so rayuwar wani daga cikinku ta samu tangarɗa ba".

"To Ammi tun da ba sa yi da ke, ai mu mun isheki rayuwa, dan Allah ki manta da su"

Ajiyar zuciya Ammi ta yi, ba ta sake cewa komai ba.

***
Yau kamar korarriya haka ruma ta shigo gida, sai cika take tana batsewa, ba ta kula kowa ba ta cire uniform ta yi wanka, ta zubo abincin ta ta fara ci.

Kamar wadda aka tsikara ta ce "Yaya Aliyu, wai ina ce makarantar 'ya'yan gwamna ne?"

Yayi murmushi ya ce "Mai yafaru?"

"A'a tambaya kawai nake yi"

"A manyan makarantu suke, wasu a turai ma"

"Suna zama a ƙasa, ajinsu babu abin zama?"

Yayi dariya ya ce "Amma kin ci kai, 'ya'yan gwamna ne zasu zauna a ƙasa? Zama a ƙasa a makaranta wannan ai sai ɗan talaka"

"To meye banbancin mu da su? Dukkanin mu ba mutane bane, kuma muma ba 'ya'ya bane?"

"Kuna da bambanci mai tazarar gaske, dukkaninku mutane ne, kuma 'ya'ya ne, amma iyayensu ke riƙe da madafun iko, abin da zaku yi ku taimaki kanku a matsayin yaran talakawa shi ne, kuyi karatu komai wahala, idan ba haka ba kuwa ku ƙare a bayinsu da 'ya'yansu"

Tamkar ruma zata fashe da kuka ta ce "To wallahi zan yi Allah ya isa, aka ce duk 'yan ƙasa ɗaya muke, bencinmu ya karye, dama wasu a ƙasa suke zama, kullum sai kayana sun yi datti, uniform ɗina duk sun fara koɗewa. Ga malaman namu ma sai a hankali, wallahi malamin English ɗin mu bai iya turanci ba kame-kame yake yi, malamin math ɗin mu kuma Arabic yayi ba uwar da muke ganewa, ga ajinmu azababben zafi window ɗaya ce, bana gane komai a makarantar kamar na daina karatun. Kuma jiya nake ji a radion mama uban kuɗin da ake saiwa  wasu manyan motoci sai ka ce motar aljanna, ko meye sunansu oho na manta, to wallahi duk wanda aka raba da haƙƙina ya cinye ban yafe ba, zama a ƙasan da nake a matsayina na 'yar ƙasa"

Mama ta ce "Ruma wa ki ke yi wa Allah ya isa, ban hanaki wannan ɗabi'ar ba ruma?"

"Mama ba zaki gane halin da muke ciki ba, ga rashin abin zama, ga zafi ga rashin malamai ga duka kamar an samu jakai, har noma ake sakamu fatanya a makaranta, gaba ɗaya makarantar mu 'ya'yan talakawa ne, shikenan mu ba mutane bane".
Ruma kenan, gaba ɗaya tunaninta da maganganunta sun shallake shekarunta, wataƙila hakan yana da alaƙa da yawan jin radion da mama take yi, da yawan tattauna matsalolin da ƙasa ke ciki da yayyenta suke yi.

Babu wanda ya kuma tanka mata, tayi bambaminta ta gama, dan ta wani fannin tabbas Ruma tana da gaskiya, amma babu yadda za ayi a gaya mata tana da tazarar da waɗanda take hange take kamanta kanta da su ta gane.
Haka ta ƙare cin abincin tana mita, kuma bil haƙƙi har cikin ranta, take faɗar yadda abin yake yi mata ciwo.

Kasancewar yau Alhamis babu makarantar islamiyya, Huzaifa da Yasir duk suna gida.

Huzaifa ya nutsu yana ta kallon tiktok a wayarsa, ruma ta lallaɓa ta zira kanta tana kallo.
Huzaifa ya ɗauke wayarsa ya kalli ruma ya ce "sai ka ce mayya, mara zuciya kawai"

"Eh na ji, ni kunna dai mu gani"

"Ba zan kunna ba, ke ki ke saya mini data?"

"A'a, amma ɗan kunna gani kawai zan" ya haɗe rai ya ce "Ba zan kunna ba, bar nan wurin ko na dakeki"

Ta tashi tana zumɓura baki ta ce "Mutum dai idan tsiya tana bin sa, ko ka raɓeshi haushin ka yake ji?"

"Ni ne tsiya take bi ko? Wallahi ki ka bari na zo kanki, saina kwaɗa miki mari"

Cikin tsiwa da rashin kunya ta ce "To kar ka barni da rai ma mana, idan da rai nima zan yi wayar nan" Jin yadda take ɗaga murya ya san idan ya biye mata, faɗa za su yi, ran mama ya zo yana ɓaci, kawai ya shareta ya cigaba da danna wayarsa.
A hankali ta lallaɓa ta koma wurin Yasir, shi kuma Yasir Instagram yake kallo, dan haka sai ka ce dole ta ɗan maƙale tana leƙawa dan kar shi ma ya koreta.
Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Dawo ta nan ki kalla, madam no heart"

"Ai in dai zaka barni na kalla, to babu damuwa kafi wancan tsiyar muka rako duniya". Yasir ya yi murmushi bai ce komai ba.
Sai dai tamkar zata shige cikin wayar, ko ta ƙwace masa wayar.

Duk hoton ko videon da ta gani sai ta tsaya ta yi liking. Ƙarshe sai sakar mata wayar ya yi, ya tashi ya bata wuri.

Sai da mama ta tashi ruma ta aiketa, sannan ta tashi daga kallon wayar.

Ɗaukar niƙa mama ta aiketa a can titi, ta ɗauki kayan saƙarta ta tafi da su, tana tafe a hanya tana saƙa, ta ɗauko niƙa ta taho gida, sai dai niƙan da nauyi.

Ba tsammani ta ji an ce "Sannu ko" ta ɗaga kai ta kalli mai maganar, ba ta amsa masa ba ta cigaba da tafiya. Biyota ya yi ya ce "Daga ina haka?"

Ruma ta tsaya ta kalleshi ta ce "Ba dan ka kusa sa'an yaya Usy ba, da sai na ce maka kai ka aike ni da zaka tsareni da tambaya?"

Ya girgiza kai ya ce "No, yi haƙuri kawo na tayaki ɗaukar kayan"

Ruma ta ce "Yauwwa, kamar ka san na gaji kuwa" ta ajiye masa niƙan ya ɗaukar mata.

Suna tafe yana yi mata tambayoyi, ita kuma hankalinta yana kan saƙarta.

Babu zato babu tsammani sai ganin Yaya Aliyu ta yi a gabansu, gabanta ya faɗi ta ce "Yaya"

Rai a haɗe ya ce "Waye wannan?"

Ta kalli mutumin ta ce "Oho kawai ganinsa na yi"

Mutumin ya yi murmushi ya ce "Ashe yayanmu ne, barka da yamma"

Aliyu bai amsa ba ya ce "Malam meye haɗinka da ita?"

"A'a babu komai, kawai dai na tayata ɗaukar niƙan ne, sannan dan Allah idan babu damuwa, ni dai ina son ta ne, dama na biyo ta ne domin na ga.....

"Haba bawan Allah, ina kai ina wannan yarinyar 'yar cikinka, meye wani abin soyayya a wurinta ban da salon ɓata tarbiyyar yarinya"

Ruka kuwa ta buɗe baki ta ce "wai sona ka ke ka zama saurayina, taɓ to ai ni ba zan yi aure ba"

Yayi murmushi ya ce "Eh mana, yayanmu ni zan jirata ko nan da shekara nawa ne idan muna raye zan jirata"

Aliyu ya sake tsuke fuska ya kalli ruma ya ce "Wuce ki tafi gida"

Ruma tayi gaba tana ɓata rai, ya ce "Zo ki karɓi kayan naki"

Ruma ta ce "Ka ajiye wa Yaya Aliyu ya taho da su"

Aliyu ya ce "Ni ne zan taho miki da aiken"

Kwasa ta yi da gudu, ko waiwayowa ba ta yi ba, dan kar ma ya ce sai ta ɗauko niƙan dan ta gaji.

Kamar korarriya mama ta ga ruma a cikin gidan, tana ta sauke numfashi.

"Lafiya ina aiken? Ko faɗan ki ka je ki ka yi?"
Ta girgiza kai.

"To menene, ina aiken?" Ruma ta sake tura baki.

"Ke magana nake miki kin shareni"

Kan tayi magana Aliyu ya shigo, da niƙan Mama.
Ya dire niƙan yayo kan Ruma, ta zura da gudu ta shige bayan mama.

"Wai meyene, lafiya?"

Aliyu ya ce "Ita ta san me tayi ai, wani bagidajen gaye ne, da wani tattararren ƙafar wandonsa, wai wannan bagidajiyar yarinyar ya biyo wai yana son ta, sai da na kusa ɗuɗɗura masa ashar, banda son lalata tarbiyyar yarinya, uwar me yake nema a wurin wannan yarinyar mai rabi hankali rabi hauka?"

Mama ta ce "Aliyu, ba ina sukar matakin da ka ɗauka bane ba, amma wanda ya ce yana son naka ai ba maƙiyinka bane, duk abin ku fa ko kuna so, ko ba kwa so dole watarana sai kun aurawa wani ta bar gidan nan, ku daina wulaƙanta mutane Sabo sun ce suna son 'yar uwarku".

"Ni bana son shi, ƙafarsa busu-busu ko mai bai shafa ba, kuma sai warin rana yake"

Hannu mama ta saka, ta mako ruma daga bayanta, ta din ga yi mata faɗa.

Duk da ita ruma ko faɗan ka yi mata ba ganewa take yi ba.

***
Iman ce ta shiga sashen Ammi da sauri, sai dai Ammi ta ɗan razana ta ce "Lafiya kuwa?"

Iman ta ce "Ammi, ina ga yaya Mahmud ne zai koma makaranta, na gansu a haraba kamar airport Mummy za ta kai shi".
Da sauri Ammi ta tashi, ta zaga ta ventilation ɗin ta, ta leƙa ta window, ta hangi Mahmud ya buɗe bayan mota ya shiga, Mummy ma ta shiga an kunna motar sun yi gaba.

Jiki a sanyaye Ammi ta saki labulen, ta shiga ambaton sunan Allah, Iman ta rungumota ta na faɗin "Ammi kina lafiya? Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki fa, kar ciwonki ya tashi" sai dai kan Ammin ta yi wata magana numfashinta ya fara sama-sama.



(Book 1 free ne, book 2 paid ne).

Ayshercool
08081012143
[04/08, 9:06 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

P 20

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.







P20




*Page ɗin sukutum guda naki ne masoyiyya Zainab kumurya, idan kin ga dama ki yayyaga shi ki zubar ko ki kashe Ruma, tun da naki ne😂. Ke kuma marubuciyar mijin malama Nimcy ki ji tsoron Allah, wallahi ana ta ƙorafi kin sako jaruma da masifu amma kin yi burus da mutane, zan karɓe rubutun mijin malamar nan fa😂 wanda bai karanta ba ya garzaya mijin malama an gama book1 labari mai tsayawa a zuciya*



A gigice Iman ta riƙo Ammi tana jera mata sannu, jinjina mata kai kawai Ammin ke iya yi, amma ta kasa magana.
Iman ta rungumota ta zaunar da ita a kan gado, cikin damuwa ta ce "Ammina, dan Allah ki yi haƙuri, ban nuna miki dan na tayar miki da hankali ba"

"Kar ki damu Iman, ba ki tayar mini da hankali ba, kawai dai tari ne ya taso mini, kawo mini ruwa a fridge mai sanyi na sha.

Cikin rawar jiki Iman ta tafi ta kawowa Ammi ruwa, ta karɓa ta sha, sannan ta ɗan kwanta ta lumshe idonta. A take ƙwaƙwalwaarta ta shiga tariyo mata abin da suka wakana a shekarun baya, daga kafuwar gidan zuwa yanzu, abubuwa da dama sun faru masu matuƙar wahalar mantawa da kuma ruɗani, wanda haryanzu a haka ake, komai sake dagulewa yake yi. A hankali ta gyara kwanciyarta tana son ta kawar da tunanin daga zuciyarta, amma sai kaiwa da komowa abubuwa suke a ƙwaƙwalwarta suka hanata sukuni.

***
Ruma kuwa a 'yan kwanakin nan ta addabawa Yasir, kusan kullum tana liƙe da shi tana kallon waya, idan anjima ta ɗau wayar Usman ta fara game, ya zo yayi ta zaginta ya ƙwace, sai ta koma gefe ta ɗau wayar mama, ta yi ta yi wa ƙawayenta fulashin, wasu su biyo wasu kuma suma su yi ta mata fulashin, babban abin da yake ƙonawa mama rai fulashin, wataran wayar haske kawai take yi, ko sai ta fara ringing ta zo ɗagawa ta katse, mama ta yi ta masifa ta ce "Idan baki kiyayeni ba, da ke da ƙawayen naki sai na saɓa muku, gayyar rashin hankali".

Yasir yana ɗan taɓa gyaran wayoyi, ya iya harkar jagwal, shine gyaran waya, system da sauran kayan electronics.
Wata waya ya samu, ta sha jiki, ya sayo layin data, ya saka a wayar, ya bawa ruma ya ce "Gashi nan, ki dinga kalle-kallen ki a wannan ki ƙyale mini wayata, kuma ki daina ɗaukar wayar mama kina fulashin, ki yi da wannan, saura ki lalata kuma akwai lokacin da zan dinga karɓa, dan ba bar miki na yi ba. Na buɗe miki account amma ban saka sunanki ba, ƙanwar maza na saka na ɗora miki hoton flower a dp kar a gano mu".

Ruma tamkar ta goya Yasir dan murna da farin ciki, ta gurfana ta dinga yi masa godiya, tare da sanya masa albarka.

"Amma ki ja bakinki ki yi shiru, kar ki gayawa kowa"

"In Allah ya yarda ba zan gaya wa kowa ba, bakina ƙanin ƙafata, amma me yasa ba zaka saka mini sunana ba da hotuna na nima?"

"Dan ubanki gidanku kuna da background ɗin da zaki dinga hoto ne? Kuma ni ban baki dan ki saka hotunanki ba, dan wallahi kin san idan suka gano kashinmu ya bushe, idan kin san ba zaki bi abin da nace ba, to tun wuri na karɓe kowa ma ya huta"

"A'a Allah ya baka haƙuri, da wasa nake maka nima, idan bana komai sai ka dinga bani ina ganin duniya nima, a daina hantarata dan na leƙa waya".

Tun da Yasir ya bata wayar nan, aka samu sauƙin neman magana a cikin gida, kusan koda yaushe tana kan wannan jagwal ɗin wayar, kuma Yasir abubuwan karatu yayi mata following, dan haka su tafi gani, kuma sosai suke ɗauke mata hankali, ya fi bata da daddare idan ya tabattar ta gama ayyukanta, da assignment, sai ya bata ta zauna a kusa da shi ta kalla, da lokacin kwanciya ya yi ya ƙwace wayar ya korata ta kwanta.

***
Zuwa la'asar Ammi ta ɗan samu nutsuwa, sai dai kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin damuwa.
Takawa ya fuskanci damuwa ƙarara a fuskar ta, sai dai ganin yadda take basarwa ba ta son magana, ya sanya shi yin shiru bai yi ƙoƙarin tilasta mata jin abin da yake damunta ba.

Wurin Jabir ya tafi, domin samun sauƙin wasu damuwoyin da suke damunsa, kasancewar sa ɗan uwa ɗaya tilo da ya fi yarda da shi.
Jabir na ganinsa ya ce "Sarkin matsala, tun kafin ka yi magana, fuskarka ta nuna akwai damuwa, yau kuma menene?"

Takawa ya ɗan yi shiru, sannan ya ce "Khalifa Usman wakili"

Jabir ya tsuke fuska ya ce "Ba zaka rabu da sabgar wannan yaron da ahalinsa ba ko?"

A hankali Adam ya ɗan lumshe idonsa, ba ya son yin dogon jawabi da ga Jabir, tun da shi jabir haryanzu ya kasa gane abin da yake nufi game da khalifa, dan haka kawai yayi shiru ya cigaba da tunani.

"Ina Ammi?"

Adam ya buɗe idonsa ya kalli jabir, amma bai yi magana ba, so yake yayi masa zancen muryar nan da yake ji, wadda haryanzu ya kasa daina jinta a kunnuwansa, amma ya san da ya ɗago zancen Jabir zai yi masa wata fassarar. Bai gama fahimtar mai Jabir ya cigaba da cewa ba, sai jin sunan Iman da yayi Jabir ya furta.

Ya ce "Me ka ce ne?"

"Ni fa matsalata da kai wulaƙanci, duk

4 Comments On KANWAR MAZA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Anayi munajin dadi

avatar
maryam-2-7-4

11 months ago

Reply

Anayi munajin ddi

avatar
maryam-2-7-4

11 months ago

Reply

Yyu kyau

avatar
hauwau-8-4

8 months ago

Reply

Dan Allah qarashen fa

Please Login or Register in order to submit comment