Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bane , dasu da limam ɗin ya shigo yaga yana zabura yana ihu yaɗan mishi wasu addu'oi shine zakaga yasamu yayi Shuru , shine ya faɗamun yace idan ya fara ihun na dinga karanta mishi Ayatulkursiyu da fakali da Nasi, ko ɗazu ma da yayi ihun ina karanta mishi shine yasamu yayi barcin nan , kaga kuwa ai ba'a ce wanan ciwon na Asibiti bane , taƙarasa maganar kamar me shirin yin kuka .......

Hullar kanshi Abubakar ya cire , ya ja numfashi ya furzar da wata iska , cikin tsananin tausayawa yace," innalillahi wa'inna illaihir raju'un, kai Hajiya tabbas ciwon kam bana Asibiti bane , ni kam anma tafi ɗaurin auren kuwa! lokacin da ya faɗin? dan naga ko Lokacin da mukayi waya naga da sauran lokaci , Ina ba'a tafi ba ai ana shirin tafiya ne shine fa ya faɗi, ni gara ma daka tunamun , barin ƙara kiran gidan Amaryar naji ko Allah yasa an ganta , Tafaɗa tana shirin ƙoƙarin kira ......,

Subhanallahi ,ina Amaryar taje? Naji kina cewa ko an ganta,badai ɓata tayi ba? Abbbakar yafaɗa cikin tsantsar mamaki , dakatawa da kiran wayar Hajiya tayi ta mai da kallanta zuwa Abbakar tace," Au baka sani ba ko ai ita kuma Amaryar an nemeta an rasa wallahi , daidai lokacin Munawir ya fadi , shine suka kiramu a waya suke shaida mana halin da ake ciki , kuma mu bamu faɗa musu cewar ga halin da shi Munawir ɗin yake ciki ba kar abun ya taru yayi musu yawa ,sai daga baya nakira su , sai ce musu mukayi ai Munawir ɗin ya suma tsabar damuwa hakan yasa ma bazai iya zuwa gidan ba , kar suji shi bai zo bane yasa ma na faɗa musu haka ......

Hmmmm Lallai wanan shine ake kira da ɗaaa kwance uwa kwance Abbakar yafaɗa cikeda da damuwa, Shuru yayi kafin daga bisani yace" to yanzu Hajiya ya kike gani za'a ɓullo wa lamarin nan ? Ko mallamai za'a kira su duba shi ? Wai tukkunama banga Abban Munawir ɗin ba, ko baya gari ne? Hmmm Hajiya tace," murya a sanyaye tace," kasan tunda Munawir ya dage sai ya auri yarinyar nan , shine yace to ya cire hannu a lamarin shi , sanan yace duk abun da ya biyo baya babu ruwan shi ,amma gaskiya bai san abun dake faruwa ba saboda baya gari , tun bikin saura sati yayi tafiya , amma munyi waya yace zuwa jibi inshallahu zai dawo , ni tsoron faɗa mishi ma nake wallahi.... ta karasa maganar murya a sanyaye , kai ikon Allah , amma gaskiya Hajiya wannan ba'abun da za'ayi Shuru bane , kamata yayi ki kirashi ki shaida mishi halin da ake ciki , kafin ma ace yadawo , suma mutanen dasu ke zaune a gurin saka baki sukayi ta hanyar faɗin,' gaskiya kam dole a kirashi a faɗa mishi kam ,Shuru Hajiya tayi tana me tunanin ta'inda zata fara faɗa mishi , Shuru tayi naɗan lokaci kamar me tunanin wani abu kafin daga bisani ta ɗauki wayarta , ta kalli Abbakar da ya kura ma Munawir ido tace," barin kirashi din kawai, Ah to da yafi kam gaskiya ya faɗa a takaice .......

Ƙoƙarin dailing lambarshi ta farayi , bugu uku ya dauka , murya a sanyaye tafara faɗin," sannu Alhaji ina wuni ! Lafiya kalau ya kuke ya bata amsa , lafiya kalau Alhamdulillah , Shuru tayi na ɗan wani lokaci gamida ɗan jan guntun numfashi , jin shurun da tayi yasa , Alhaji faɗin," lafiya kuwa ! Naji muryarki a sanyaye , numfashi taja muryarta taɗan fara rawa tace," Alhaji dama Munawir.......Shuru tayi ta kasa ƙarasa maganar , cikin damuwa ,yafara faɗin," munawir me? Kin fara magana kuma kinyi Shuru , menene? Yafaɗa cikin faɗa da ɗaga murya .........

Miƙama Abbakar wayar tayi tace," Abbakar kayi mishi magana, karɓar Abbakar yayi yakara wayar a kunnenshi gamida yin sallam, yace," Assalamu Alaikum ! Alhaji ina wuni, ga mamaki Alhaji ya amsa yace," lafiya kalau dawa nake magana??Abbakar ɗin Hajiya salamatu ne , yafaɗa cikin girmamawa ,to to Abbakar ashe kana gidan ? Wai me ke faruwa da Munawir ɗin ne?eh wallahi ban dai daɗe da zuwa ba , nan Abbakar ya labarta ma Alhaji dukkan abun da ya faru da Munawir har zuwa yanzu da yake ta barcin Azaba , ya karasa maganar gamida faɗin," wallahi Alhaji jikin shi sam ba daɗi......

Shiru Alhaji ya furzar da iska irin tasu ta manya ,ya ɗan ja dogon numfashi kafin daga bisani yace," Hmmm wallahi tallahi ko kaffara bazanyi ba wannan abu akwai dalili , dalili kuwa shine auren wanan yarinyar da zaiyyi ne yasa haka , shiyasa tun farko na guda wanan auren , tunda ya fara neman yarinyar nan abubuwa da dama marasa kyau suke shigowa Cikin rayuwarshi , ko da yaushe cikin tashin hankali da firgice yake , shida mahaifiyarshi sun ƙi fahimta tane ,akwai binciken da nayi akanta , ba auren su bane bana so ,ba kuma talauci su bane nake gudu , A'a damuwar datake tattare da yarinyar ne itace Abunji amma sun gagara fahimta na , shi yana bin soyaiyya ita kuma mahaifiyarshi ita mai ɗàa tana son abun da yake so , wallahi daga yanda ka fasaltamun ciwon na riga na gano inda matsalar take , ai abubuwa masu irin yanayin haka sukan ɗan faru dashi , amma so ya rufe mishi ido ya kasa fahimta, ita Hajiya Maryam ɗin ai tasan komai , ta baka labarin abubuwa da suka dinga faruwa tun kafin yanzu , tunda ya sa kafa a neman yarinyar nan hankalinshi ba a kwance yake ba , to yanzu wa gari ya waye ??
Shiru Abbakar yayi yana sauraron maganganun Alhaji , yana nazari sossai akansu , nan fa shima ya fara yarda da abubuwan da Alhaji ke faɗi, duk da bai san wasu abubuwan da suka faru ba, buɗe baki yayi yace," gaskiya Alhaji na yarda daa maganar ka tabbas akwai lauje cikin naɗi, kuma kasan yanzu haka ma fa an nemi Amaryar an rasa fa , Hmmm Alhaji yace,"gamida da sakin murmishi irin masu na manya yace," Ahaf ai maganata zata fito ai , ana tafe , daka na garinan da kaga komai da idonka kuma kaji komai , cikin ƙan_ƙan dakai haɗe da lallami Abbakar yace," yanzu Alhaji miye abunyi , dan kaga gaskiya ba za'a zuba mishi ido haka ba , Hmmm Abbakar kenan to idan ma nazo ni me zanyi ? Kudaiyi abun da ya dace kawai , nidai gaskiya ina san ran dawo wata jibi ne, amma idan naga da yuyuwar dawo gobe inshallahu zan biyo jirgin safe in dawo , yafaɗa jiki a sanyaye , to Alhaji Allah dawo dakai lafiya , Allah tsare hanya , Ameen Ameen Alhaji ya faɗa a taƙaice ,bama Hajiya Maryam wayar , to ya faɗa cikin girmama gamida mikama Hajiyan wayar.....

Ƙara wayar tayi a kunnen ta murya ƙasa_ƙasa tace," gani Alhaji , Shuru yayi na ɗan lokuta daga bisani yace," wallahi duk abun da ya faru da yaranan laifinku ne kedashi, abun da ake gudu shi ya faru , kar ki zargi kowa ki zargi wanan yarinyar da kuka liƙema ke da shi , ni bansan abunyi ba yanzu , kuyi duk abun da ya dace kafin kujira dawowata , Shuru Hajiya tayi Itadai batace komai sai to da ta amsa mishi dashi , tace," to Allah dawo dakai lafiya, duk da itama yanzu ta tuna da abubuwan da suka faru ,hakan yasa ta fara tunanin maganganun mijin nata suna kan hanya, cikin girmama tace to Allah dawo dakai lafiya , Ameen ya faɗa a takaice gamida kashe wayar ......
Cire wayar tayi a kunnenta tamai da kallonta zuwa Abbakar da yayi Shuru kamar me nazarin wani abu , tace," Abbakar me yace maka ne ??
Nan Abbakar yafaɗa mata duk abun da suka tattauna dashi ya ƙara da cewa , Hajiya akwai kamshin gaskiya a maganar Alhaji , menene yake faruwa ???

Uhmmm kaidai Abbakar Allah dai shi yasan dai_dai, Allah ne ya bar wa kanshi sani, to Allah ubangiji dai ya bashi lafiya shine fatan mu kawai, nan suka fara tunanin yanda za'a fara mishi magani , haka dai suka tsaida matsaya kan cewa a nemo babban mallami ya dubashi...........


Kwance take a cikin wani ɗan ƙaramin ƙogo , banda kakkarwa ba abun da jikinta keyi , a hankali ta fara bude idonta , firgit ta mike a firgice ganin irin gurin da take kwance yasata tsorata matuƙa haɗe da mamakin yanda akayi tazo nan , tsoro ne ya mamaye dukkanin ilahirin gangar jikinta , wani irin sanyi taji mai shiga jiki yana ratsa mata ko ina , ganin duhu a ko ina yasa tsoro ya ƙara mamayeta , ga wani matsanancin ciwon jiki , kukan da take kokarin yi ma taji babu Alamar hawaye ko ɗigo da ya zuba , maƙogaronta ya bushe ga zafi dayake mata , ganin bata da zaɓi ne yasa ta ƙara komawa ta kwanta , cikin ranta tafara tunanin ina ma ace mutuwa tayi , ina ma ce batakai wannan lokacin a raye ba , domin yanzu kam da rayuwarta da mutuwarta duk ɗaya , tunawa da tayi da rayuwarta a cikin mutane da iyayen ta da kuma masoyinta yasa ta tsala wani irin ihun da ko fita batayi saboda tsananin dashewar da muryarta tayi nan tafara faɗin," Allah laifin me nayi maka ? Allah kadubeni , Allah kana kallona , Allah ka halliceni a cikin jinsin mutane ba na Alhajanu ba , amma Allah ka ƙadartomin zama a cikin duniyar da bata mutane masu irin jinsi na ba , Allah ka fitar dani , tafaɗa tana ihu da dashashiyar muryarta,ta ɓangare guda zuciyarta na sake tunano mata halin da Ango ta zai shiga ,ko wani hali yake ciki !! ganin bata da amsar tambayar ne yasa ta ƙara shiga cikin matsananciyar damuwa da tunanin shi fal cikin ranta , da Amminta dakuma Abbanta.............✍️✍️


*MUJE ZUWA*

*PLEASE KUDINGA SHARING MUN*

*IDAN BANGA RUWAN COMMENTS BA BAZA KU JINI GOBE BA GASKIYA*

*STORY AND WRITTEN BY*✍️✍️
*(MOM FU'AD)*


*SHARE PLS*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment