Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ciki, bai Isa ya karyata ba tunda yasan Jaka tasa ce, haka kuma ba zai ce shine wanda ya aikata ba, saboda haka ne yasa ya kasa magana sai dai kawai ya sauke kansa kasa yana wasa da zoben hannunsa.........



Normal group #300
Special group #500


1499884120
Umma Salma Sani
Access bank


07033371851


YOUR YAR GABAN GOSHI ๐Ÿ˜‚


YAR LELEN ROYAL STAR......๐ŸŒน SHEIKH IMAM๐ŸŒน


By

YAR LELEN ROYAL STAR..



Normal group #300
Special group #500


1499884120
Umma Salma Sani
Access bank


07033371851

*๐ŸŒŸROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION๐ŸŒŸ*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fadโ€™akarwa, ilimantarwa da kuma nishadโ€™antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kadโ€™ai ke maganin kโ€™ishi_

*Alkโ€™alaminmu โ€˜yancinmu*

END OF FREE PAGES๐Ÿ’ƒ๐Ÿฝ๐Ÿ’ƒ๐Ÿฝ๐Ÿ’ƒ๐Ÿฝ๐Ÿ’ƒ๐Ÿฝ๐Ÿ’ƒ๐Ÿฝ๐Ÿ’ƒ๐Ÿฝ๐Ÿ’ƒ๐Ÿฝ


Page.....10



Da sauri Asrat ya shigo parlourn Ummie hannunsa rike da waya, har yana tuntube cikin fita hayyaci yake kwala Kiran sunan "Ummie!, Ummie!! Ummie!!!", Ya karasa fads da karfin gaske, cikin rud'ewa ta fito daga bedroom nata wuyanta sak'ale da hijab , a'lamar Sallar ta idar ko Kuma Sallar zata yi, cikin sauri da faduwar gaban da take riskarta da an yi magana Mai karfi, da wata tsinkewar zuciyar da take fama da shi tun tashin ta da safe, tace "wai mene kake kwada min kira haka ?", Ta fada tana dafe gefen kirjinta na haggu, tana Jin yarda zuciyarta take luguden bugu.


Kasa magana ya yi sai wayarsa da ya mika mata, da sauri ta karbi wayar tana Jin yarda buhun zuciyarta da tsinkewar zuciyar na dad'uwa, a hankali ta sauke Manyan idanunta akan fuskarsa, tare da bin headline din da idanu.



Kwakwalwarta ce taji tayi skipping na wasu Yan seconds kafin ta fara overworking, wani Abu ta ji ya tsirga mata tun daga k'asan zuciyarta har izuwa tafin kafarta, a Hankali ta sulale kan kafafunta tana furta "hasbunallahu wani'imal wakeen!, Innalillahi wa'inna ilaihi Raju'un", tana kai wa nan ta kifa kanta, a jikin ciniyoyinta, da sauri Asrat ya dafa kafadarta, tare da jawota baya, Jin ta taho gaba daya ne ya tabbatar masa da sumanta, cikin sauri ya mike tsaye, Yana Kiran sunanta, gurin fridge ya nufa, cikin sauri ya dauki ruwa mai sanyin gaske ya karasa gareta cikin sauri ya balle gorar ruwan tare da fara zuba mata, ya dauki lokaci Mai tsayi Yana zuba mata ruwan kafin ta ja doguwar ajiyar zuciya mai dauke da hadiyar Abu kamar wadda ta hadiyi zuciya, cikin sauri ya zube gabanta ya rike hannayenta, Yana Kiran sunanta, a hankali ta bude idanunta sai dai ta kasa magana sai kallonsa da take yi kamar wanda bata sani ba...cikin nasara su LAYLEERH Da BEERBAH suka fara samun SAUK'I abun da aka cire musu a jikinsu, da taimakon magungunan da likita ya Basu da Kuna shiga cikin ruwan zafin da suke.


Aizza ma an cire mata abun da yake cikinta.


Zaune suke cikin parlour, da wasu Manyan maza biyu, table din gabansu shake da Hodar ibilis da kudade irin kudaden Dubai.


Cinikin kaya ake, inda Aizza da bata son doguwar magana ta sallama kayanta akan kudin Nigeria million 35.


Su kuwa sai tayin wulakancin suke wa kayansu, duk kuwa da cewar kayansu sun fi yawa, amma nata aka fi Siya a mafi k'ololuwar daraja, Hakan yasa suka ki su siyar , suke ta Jan ran masu siyan, suma suna Jan nasu rayu kan.


Daga karshe dole suka sakar musu akan tsabar kudi naira million 30ยฒ, na AIZZA ya darar was na su da 5M, duk da yawan kayan ba daya ba, ga Kuma uwar wahalar da suka sha kafin kawo kayan.... bangaren Imam lamarin na ta tsamari , yak'i ya yi magana, gashi K'asar Dubai sun ki su kyalesa, sun ce zasu makasa a court, har sarkin Makkah ya yi magana da sarkin Dubai Amma suka murza gashin bakinsu suka ce inaa, su fa sai sun hukuntasa akan laifin son b'ata musu kasa da shigo musu da kayan maye.


Lamani daya sukawa Sarkin Makkah akan zasu iya tsayawa Imam madamar shi ke da gaskiya zasu wankesa tsab su sakesa, in Kuma bashi da gaskiya to ba makawa sai ya d'andana azabar hukuncinsu.


Zaune yake cikin wani dan guri da aka tanadar domin ajiye mutanen d ake tuhuma, sosai gurin ya yi kama da kurkuku, gaba daya gurin carpet ne aka baza, sai karamin gado mai dauke da babbar katifa, da taji zanin gado abun rufa a gefe, chan gefe kuma madaidaicin fridge ne Mai dauke da abubuwan ci da sha, danginsu Madara da kayan marmari irin su danino inibi da sauransu, daga dayan gefen Kuma kofa ce inda anan bathroom da komai yake.


Rayuwar gurin , rayuwar shiru ce kowa na gefensa bb Mai magana da wani, in ma da akwai shi dama ba gwanin magana bane da kowa musamman ma yanzu, bashi da wata damuwa sai ta kewar Yan uwa da rashin samun jam'in Sallah, don sai dai ya yi Sallah shi daya.


Haka babu abun da ya ragu na daga ibadarsa sai ma k'aruwa da ya yi, don yanzu ya kara adadin nafiloli, adadin tasbihi, adadin kadaituwa da Allah, karatun Al-qur'ani, azumin da sauransu.


Idan ka gansa zaka rantse bashi da wata mata saboda yarda jikinsa ya kara ginuwa, haiba da kamalarsa ta kara dad'uwa, fuskarsa ta kara annuri, ga jiki sa ya kara taushi da haske, gemu da kasummarsa sun kara cika, gashi ko yaushe tufafin jikinsa na baza kamshin turarensa na Viktor&Rolf Flowerbomb Haute couture , wanda ya kara zama sosai a jikinsa.



Watansa daya a cikin kurkukun kafin a yanke shawarar lokacin da za'a fara saurarar shari'arsa, k'afa da k'afa Abokinsa kwalli daya jal da ya kasance lawyer Mai suna Afaf yazo daga Germany, wanda yana daya daga cikin lawyers masu zaman kansu ko a cikin lauyoyin k'asar Germany, Amma aka Hana masa ganin Imam din sai dai aka yi connecting wata hanyar sadarwar da zasu ga nuna a zahiri su yi magana, duk kuwa da cewa basa kusa.


Tambayar Imam din ya fara yi akan abun da ake tuhumarsa da shi, sai dai ya kafesa da idanu bai iya ce masa komai ba sai dai Kallo, haka ya gama maganganunsu ya tafi ba tare da yace komai ba.


Ana gobe fara saurarar shari'arsa daga Makkah aka turo da manyan lauyoyin da zasu tsaya masa, Amma yak'i ya basu hadin kai.


RANAR DA ZA'A SHIGA COURT....



Tun da sassafe karfe 6 aka aiko wani guide Robert da kaya ya kawo masa, Bude kofar ya yi ya mika masa kayan, a hankali ya ajiye karatun Al-qur'anin da yake yi tare da mika hannayensa biyu ya karb'i kayan, har zai juya sai ya juyo ya kallesa, cikin girmamawa yace "da karfe 7 za'a zo a tafi da kai ka shirya kafin lokacin", bai Kara magana ba, shima da akawa maganar bai yi ba, sai tashi da ya yi ya shiga cikin bathroom din da yake can cikin room din.



Bai dauki lokaci Mai tsayi ba ya fito sanye da tufafin da aka kawo masa, ya daura farin maka-wuya, inda ya nanade bakar sumar kansa.



Lokaci na cika aka zo tafiya da shi, A hankali yake tafiya, cikin Kamala da dattaku, har suka fito daga cikin gurin da aka ajiyesa, wata mota ce kirar Bentley bak'a, aka karaso da ita gurin, sai wasu Manyan hilux biyu daya gaba daya baya, Bude masa kofar motar aka yi ya shiga, tare da kamewa guri daya.


Kansa ya jinginar da jikin kujera tare da lumshe idanu, a hankali yake shak'a tare da fesar da iska mai sanyi, har Allah yasa suka karasa babban court din k'asar, cikin natsuwa ya fito daga mota Yana gyara zaman hiramin kansa.


Tun fitowarsa a mota Yan jaridu suka fara daukarsa a photo da videos, har lokacin da suka shiga cikin court din....zaune take kan gadonta, tun da ta kwanta ta kasa barci sai juyi take, haka nan take Jin zuciyarta na tsinkewa tun bayan da suka dawo Nigeria, gaba daya bata cikin Yana yi Mai dadi mood dinta take ji Yana chanjawa, wata irin kasala na baibayeta, fargaba da tsinkewar zuciyar sun hanata kata6us.


A hankali ta zuro kafafunta daga kan gado, slippers nata ta sa, tare da fitowa parlourn k'asa, Nan ta samu Mahaifinta da matarsa suna tsaye, cikin shirin fita, Dan tsaresu da idanu tayi na Yan seconds kafin ta cire idanunta a kansu.


Da kansa ya karasa gareta tare da bata side hug, cikin kula ya shafa kanta, kafin yace "Aizza zaku yi tafiya ni da Mamaki zamu je Afghanistan, sai Allah ya yi mana dawowa", shiru tayi ba tare da ta kulasu ba.


"Aizza baki ji abun da nace ba ?", Birkitattun idanunta ta watsa masa, cikin juyewa tace "in naji Mai kakeson na ce ?, Tafiya zaka yi sai ka fada min ?, Kun dade baku je birnin Sin ba" , tana gama maganarta ta fice ranta a datace, bin bayanta ya yi da kallo yana murmushi, duk wannan abun da tayi Sam bai ji haushinta ko ganin ta aikata ba daiยฒ ba, sai ma ji da ya yi ya kara kaunarta, sai ma bin bayanta yay da kalmar "I love you Daughter", Hajiya dai na tsaye tana kallon wannan Abu na tsakanin uba da ya, Wanda shi a kullum da ki yaushe, a Kuma duk abun da zata yi daiยฒnta yake gani, ko zata zagesa ta masa cin mutunci baya tab'a ganin tayi ba daiยฒ ba....


Court tayi tsittt ana sauraro maganar da Mai girma Alk'ali yake cikin harshen larabci, bayan an gama Jin akan abun da ake tuhumar Sheikh a kai.



Bayan gabatar da shaidu da Dubai ta yi akan shaidunsu da sauran abubuwa, aka bawa Sheikh damar magana, sai dai ya zubawa yatsun hannayensa da suke kan kantar da ake zagaye Mai laifi da ita, ya kasa magana sai jujjuya harshensa da yake cikin bakinsa.



Karon farko da ya taba tsayawa a gaban k'ulliya da sunan Wanda ya aikata wani Abu maksmancin Wanda ake tuhumarsa, shi da ko police station bai tab'a ziyarta a sanadiyar wani Abu da ake zargin ya aikata tun yarinta ba, Amma yau gashi shine a gaban k'ulliya ana gabatar da case mai matukar daure kai.


"Kana da damar karyata tuhumar da ake maka, sannan ka kawo shaida domin wanke kan ka daga abun da ake tuhumarka da shi", muryar kamilin Alk'alin da yake zaune kan munbarinsa ya fada, Yana kallon Sheikh cike da mutuntawa da dattaku.


Har lokacin ya kasa dago da kansa balle har ya iya Amsa abun da ake son ya fada, daya daga cikin lawyers din da suke jere akan wani katon table ne ya tashi bayan an gama basa izinin tashi domin yi was Sheikh tambaya, cikin iya sarrafa harshe yace "Ya Imam muna son ka kalli jakar tsaf sannan ka shaida mana ko kasan wata jaka makamanciyar wannan ?", Ya fada tana nuna masa jakar da take ajiye kan table.


Kyawawan idanu sa ya d'ago daga saukesu k'asan da ya yi, jakar ya karewa kallo, cikin sanyin muryarsa Mai amo tamkar ana busa sarewa ya ce "Tawa ce", lawyer din ne ya kara kallonsa, kafin yace "ka natsu , ka Kuma ajiye hankalinka da natsuwarka a guri daya, sannan ka Kara duba jakar nan tabbas taka ce ?", Karon farko da tun shigowarsa gurin ya d'aga kai ya kalli lawyer da yake masa tambayoyin nan, a cikin zuciyarsa ya maimata "ka ajiye hankalinka da natsuwarka ?", mai hakan yake nufi.



Cikin sanyi da kaushin harshe yace "Ina tunanin daga lokacin da ka kalle ni zaka san cewar akwai hankali haษ—e da natsuwa a tattare da ni, ko ka ga wani alamu da ya nuna Maka bana tare da daya daga cikinsu ?", Ya fada cikin nuna rashin Jim dadin maganar da lawyer ya fada masa.


Kallon lawyer alkali ya yi, cikin natsuwa yace "a ringa sanin abun da za'a fada", sunkuyar da Kai lawyer ya yi kafin ya ce "za'a kiyaye in sha Allah". Kallon Sheikh da ya ji kansa ya Sara tun bayan maganar da ya yi Mai dan tsayi, "ko zaka iya fada mana abun da kake dauke da shi a cikin jakar tun bayan fitowarka gida ?", Jinjina kansa ya yi , kafin chan ciki yace "Apple laptop, files da documents, su kawai na sani a cikin kayan da ke ciki, bana da masaniya akan abun da aka samu a ciki", ya fada Yana lumshe idanunsa, Yana Kuma Jin kansa tamkar zai bare gida biyu.


Jinjina kai lawyer ya yi, kafin yace "kana nufin baka da masaniya akan abun da ake tuhumarka da shi kenan ?", Ya fada yana kallonsa, girgiza kai yay kafin yace "ko daya ni ban ma san abun da ake tuhumata da shi ba, don ba da ban fad'in sunansa da aka yi ba ban tab'a ganinsa ba", "kana nufin duk safararsa da kake baka san sunansa ba kenan ?", Wani Abu yaji ya saukar masa a tsakiyar kai, take ya ji wani nauyi ya fara mamayesa, Mai Hakan ke nufi, suna nufin kenan shi din safarar hodar ibilis yake kenan?, Ya tambayi kasan.


Wani d'aci yaji ya sauko masa a makogwaronsa, harshensa yasa ta laso lips nasa da suka gama bushewa tsabar k'ishi da zafin tambayoyin da ake afka masa, da yawan maganganun da suke sa masa, har wani zazzafan zazzab'i yake Jin ya fara sauko masa..Afaf ne ya tashi cikin sauri a Kuma face kamar zai daki lawyer da yake wa Imam zafaffan tambayoyi yace "ya Mai girma Mai shari'a, ya kamata lawyer masu Kara yasan kalar maganar da zai ringa fadawa Wanda ake tuhuma domin har zuwa yanzu tuhuma ce ba'a tabbatar da cewar shine y aikata ba, don mutum kamili kamar Imam ba zai iya aikata abun da ake tuhumarsa da shi ba", cikin fada shima dayan yace "ashe kuwa mutane da yawa da Basu aikata abun da suke aikatawa ba indai da ta fuska za'a gane mugu da ba mugu ba, babu ruwan mu da Kamala ko Mulunci abun da ake tuhumarka akai kawai zamu bincikeka, domin mutum nawa ne suke yaga rigar mulunta suyi fatali da ita, ya yin da suke aikata fasadi a ban kasa", a harzuke Afaf har Yana cin kwalar wannan dayan lawyer yace "karya kake, Imam ba haka yake ba, zan iya rantsuwa da Al-qur'ani kan cewa Imam ba zai iya safarar kwayoyi daga wata kasa zuwa wata ba, Kai na yo Imani da Allah Imam ko kwalin sigari bai tab'a, tab'awa ba balle har ya kai ga ya yi safarar Hodar ibilis ba,Kuma zan tabbatar maka da hakan", ya fada kamar zai duki lawyer da sauri Alkali ya buga gudumarsa, ganin yarda court ta dauki d'umi yasa alkali bada hutun rabin awa...


MU KOMA GIDA NIGERIA....



Ummie na zaune a gaban tv tana kallon yarda shari'a take gudanar, idanunta jargab da ruwan hawaye, sai faman goge mata Asrat yake, shima don dai dauriya irin ta Namiji Amma da yanzu ya fara kuka, sun so tafiya Dubai domin a gabatar da shari'ar tare da su. Sai dai wani Abu da ya faru, sai aka kullewar Sheikh gaba daya account nasa, aka Hana kudi fita aka hanasu shiga, dole tasa suka zauna tunda babu kudin da zasu yi booking flight daga Ninja zuwa Dubai ...


Tun da ta fita take Jin kanta na ssrawa, wani Yana yi mai kama dana kewa yana mamayeta, a mugun haukace take driving ga jikinta babu wani kwarin sosai.


Tana tafiya tayi zurfi a cikin Jin abun da yake damunta, ta ji mota ta kwace mata, tare da yin kan wani tsoho da ya zo wucewa, bata yi yunk'uri taka burki ko wani Abu ba, kawai ta bi ta kan tsohon nan, take kansa ya fashe, bata Kuma tsaya ba sai ta karawa motar wuta , kasantuwar babu mutane sosai a anguwar gata Yar wani sai babu matakin da aka dauka....


Court yana yi ta sau zafi inda dole aka d'aga shari'a zuwa biyar ga wata 12, Wanda a zaman ne za'a yanke hukuncin in ba'a kawo shaidu masu karfi da zata nuna cewa Imam bai aikata abun da ake zarginsa da shi ba ..



Hankali ta tashi barin ma na Ummie da ta gama sanin Idan ta rasa Imam yanzu ta rasa wani bango ne na rayuwa.


Haka mutane da yawa, ciki harda Asneeeh, da ta kasa samun sukuni, don tun ranar da Allah ya hadasu ta kasa samun kwanciyar hankali, barin ma da taji abun da yake faruwa, duk sati ciki azumi da sadaka take, ana haka ta nemi gidansu Imam , ba tayi k'asa a guiwa ba taje, anan ta musu jaje, tare da zama tare da Ummie ta ringa kwantar mata da hankali.


Da haka kullum ta auri zuwa gidan Ummie , har suka saba , don in tazo tun safe sai dare take tafiya...


Lamarin ya fara fin karfin Afaf , yana chan cikin tunanin yarda gobe zata kasance, gashi dai har ana gobe zaman court Amma bashi da shaidar zai Kai a matsayin abun da zai wanke Imam.


Bangaren Imam ma hankalinsa ya fara tashi har wata Yar kwaryaยฒn rama ya yi, saboda hankalinsa da ya fara tashi, barin ma da yasan cewar idan har ba'a samu wata kwakwarar shaida ba hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga ne saboda ana sa hakan ne a layin ta'addanci.


Sai dai ya zai yi ?, In Hakan ta kasance a garesa zai daukesa ne a matsayin kaddara, wadda dukkan muummuni nagari ya yarda da ita, domin daya ce daga cikin rukunnan musulumci, a cikin kunnansa ya fara Jin ana masa magana, Allah (S.W.T)Shi ne wanda ya yi halitta, kuma ya daiยฒta ta, kuma shi ne wanda ya qaddara abubuwa, kuma ya shiryar da su.

Kuma Allah yana cewa,

(ูˆูŽุฎูŽู„ูŽู‚ูŽ ูƒูู„ู‘ูŽ ุดูŽูŠู’ุกู ููŽู‚ูŽุฏู‘ูŽุฑูŽู‡ู ุชูŽู‚ู’ุฏููŠุฑู‹ุง2) [ุงู„ูุฑู‚ุงู†: 2]

โ€œKuma ya halicci kowane abu, kuma ya qaddara shi, da qaddarawa.

Ayoyi da suke tabbatar da wannan rukuni, sun fi a qirga, kuma a cikin sunnar Manzon Allah (๏ทบ) ma wuri daban-daban, ya tabbatar da wannan rukuni mai girma. Misali, a cikin hadisin da malaโ€™ika Jibrilu ya zo wajen Annabi (๏ทบ), yana tambayar sa, da ya tambaye shi kan imani, sai ya ce, โ€œImani shi ne, ka bayar da gaskiya da Allah, da malaโ€™ikunsa, da littattafansa, da Manzanninsa, da ranar qarshe, da yarda da qaddara, mai kyau da marar kyau .Sai Jibrilu ya ce, โ€œKa yi gaskiya!โ€ (Muslim ne ya ruwaito.)

Ya ku โ€˜yan uwa! Abin da ake nufi da qaddara, shi ne ilimin Allah Taโ€™ala, wanda ya rigaya tun fil-azal, da abubuwa kafin su auku, kuma Allah ya rubuta su daki-daki, kafin ya halicci sama da qasa, da shekara dubu hamsin, kuma babu abin da zai auku, face da ganin damarsa, kuma shi ya halicce shi. Wannan shi ne bayar da gaskiya da qaddara wajen sahabbai, kuma shi ne bayar da gaskiya a wajen ahlussunnah. Don haka, tilas ne ga duk wani musulmi, ya yarda cewa babu wani abu da zai faru cikin mulkin Allah, wanda sai daga baya Allah zai san shi. Aโ€™a, Allah ya rigaya, ya san komai, tun fil-azal, kuma ya rubuta shi a allon qaddara (lauhil mahfuuz), kamar yadda ya zo a hadisin, kuma kamar yadda Allah yake cewa,

(ุฅูู†ู‘ูŽ ุฐูŽู„ููƒูŽ ูููŠ ูƒูุชูŽุงุจู ุฅูู†ู‘ูŽ ุฐูŽู„ููƒูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ูŠูŽุณููŠุฑูŒ70) [ุงู„ุญุฌ: 70]

โ€œLallai hakan, yana cikin littafi, lallai hakan mai sauqi ne wurin Allah.โ€

Don haka, babu wani abu da zai auku, face sai Allah ya ga dama, kuma idan zai auku, zai auku ne, kamar yadda Allah ya zartar. Allah yana cewa,

(ูˆูŽู…ูŽุง ุชูŽุดูŽุงุกููˆู†ูŽ ุฅูู„ู‘ูŽุง ุฃูŽู†ู’ ูŠูŽุดูŽุงุกูŽ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุฅูู†ู‘ูŽ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูŽ ูƒูŽุงู†ูŽ ุนูŽู„ููŠู…ู‹ุง ุญูŽูƒููŠู…ู‹ุง30 ูŠูุฏู’ุฎูู„ู ู…ูŽู†ู’ ูŠูŽุดูŽุงุกู ูููŠ ุฑูŽุญู’ู…ูŽุชูู‡ู ูˆูŽุงู„ุธู‘ูŽุงู„ูู…ููŠู†ูŽ ุฃูŽุนูŽุฏู‘ูŽ ู„ูŽู‡ูู…ู’ ุนูŽุฐูŽุงุจู‹ุง ุฃูŽู„ููŠู…ู‹ุง31) [ุงู„ุฅู†ุณุงู†: ูฃู  - ูฃูก].

(Ba kwa nufin aikata wani abu, sai Allah ya yi nufi. Lallai Allah masani ne, mai azanci, yana shigar da wanda ya yi nufi cikin rahamarsa).

Ya dan uwa! Ka sani, babu tilas ga dan Adam kan ayyukansa, a aqida ta musulunci. Mutum yana da dama, da kuma zabi, na ya aikata abin da ya ga dama, kamar yadda yake cewa,

(ูˆูŽู‡ูŽุฏูŽูŠู’ู†ูŽุงู‡ู ุงู„ู†ู‘ูŽุฌู’ุฏูŽูŠู’ู†ู10) [ุงู„ุจู„ุฏ: ูกู ].

(Kuma mun shiryar da shi hanyoyi biyu).

Wato na alheri, da na sharri. Don haka, shi dan Adam, shi ne yake zabar abin da ya ga dama, kuma sanin Allah, ba ya nufin Allah ya yi masa tilas ba ne. Don ba daiยฒ ba ne, mutum ya kafa hujja da qaddara wajen sabon Allah, kamar yadda wasu mutane suke yi.

Ibni Taimiyya ya ce, ยซWannan maganar banza ce. Wato mutum ya kafa hujja da qaddara a kan sabawa Allah, saboda imma dai qaddara ta zama hujja ga kowa da kowa, ko kuma ba hujja ba ce ga kowa da kowa. To idan qaddara hujja ce ga kowa da kowa, to babu wanda yake da dama ya yi musu ko inkari ga wanda ya cuce shi, ya zage shi, kuma ya qwace masa dukiyarsa, ya bata masa matansa, ya sare da takobi a wuya, kuma ya lalata masa gonarsa da โ€˜yaโ€™yansa. domin ba zai cuce shi ba, sai da qaddara. Babu wanda zai yarda a cuce shi, a kafa masa hujja da qaddara. Abu na biyu, idan qaddara hujja ce, to da Iblis, da Firโ€™auna da mutane Annabi Nuhu da Adawa da sauran masu sabon Allah, wadanda Allah ya halakar da su, da sun sami hujja. Haka kuwa abu ne da babu wani mai bin wani addini da zai yarda da shi. Abu na uku, da qaddara hujja ce, to da babu bambanci tsakanin bayin Allah na qwarai da fajirai. Wanda ya saba ga tunani na qwarai, ya kuma saba da fadin Allah cewa,

(ูˆูŽู…ูŽุง ูŠูŽุณู’ุชูŽูˆููŠ ุงู„ู’ุฃูŽุนู’ู…ูŽู‰ ูˆูŽุงู„ู’ุจูŽุตููŠุฑู19 ูˆูŽู„ูŽุง ุงู„ุธู‘ูู„ูู…ูŽุงุชู ูˆูŽู„ูŽุง ุงู„ู†ู‘ููˆุฑู20 ูˆูŽู„ูŽุง ุงู„ุธู‘ูู„ู‘ู ูˆูŽู„ูŽุง ุงู„ู’ุญูŽุฑููˆุฑู21 ูˆูŽู…ูŽุง ูŠูŽุณู’ุชูŽูˆููŠ ุงู„ู’ุฃูŽุญู’ูŠูŽุงุกู ูˆูŽู„ูŽุง ุงู„ู’ุฃูŽู…ู’ูˆูŽุงุชู22) [ูุงุทุฑ: ูกูฉ โ€“ ูขูข].

โ€œMakaho ba zai daidaitu da mai gani ba, haka duhu ba zai yi daidai da haske ba, haka inuwa ba za ta yi daidai da zafi ba, haka matattu ba za su yi daidai da masu rai ba.โ€

Kuma yana cewa,

(ุฃูŽู…ู’ ู†ูŽุฌู’ุนูŽู„ู ุงู„ู‘ูŽุฐููŠู†ูŽ ุขูŽู…ูŽู†ููˆุง ูˆูŽุนูŽู…ูู„ููˆุง ุงู„ุตู‘ูŽุงู„ูุญูŽุงุชู ูƒูŽุงู„ู’ู…ููู’ุณูุฏููŠู†ูŽ ูููŠ ุงู„ู’ุฃูŽุฑู’ุถู ุฃูŽู…ู’ ู†ูŽุฌู’ุนูŽู„ู ุงู„ู’ู…ูุชู‘ูŽู‚ููŠู†ูŽ ูƒูŽุงู„ู’ููุฌู‘ูŽุงุฑู28) [ุต: 28]

(Ko za mu sanya wadanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na qwarai kamar masu barna a doron qasa, ko kuma za mu sanya masu taqawa su zama daidai da fajirai).

Abu na hudu: Ita qaddar imani aka ce mu yi da ita, ba kafa hujja ba. Duk wanda ya kafa hujja da qaddara to hujjarsa ta banza ce. Duk kuma wanda ya ba da hanzari da qaddara to hanzarinsa ba abin karba ba ne. Da ana karbar hujja da qaddara to da an karbi ta Iblis da sauran masu sabo. Da qaddara hujja ce ga bayi da babu wani da za a yi masa azaba a nan duniya ko a lahira. Da ana hujja da qaddara da ba yanke hannun barawo ba, ba a kashe wanda ya yi kisan kai ba, da ba wanda za a yi wa haddi don ya yi wani laifi. Kai da ma ba wanda za a yaqa, ko a yi umarni da wani abu na shariโ€™a ko hana wani mummunan abu.

Abu na biyar, an tambayi Manzon Allah (๏ทบ), โ€œIdan dai Allah ya rubuta komai, to meye amfanin aikin da bayi za su yi?โ€ Sai ya ce, โ€œAโ€™a! Ku yi aiki. Kowa abin horewa ne ga abin da aka halicce shi don shi.โ€ Abu na shida, idan dai rubutu da Allah ya yi, zai zamo hujja

Please Login or Register in order to submit comment