Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadi sai zuba kamshi take, dayar kalar tasu Mai dan madaidaicin girma ya bude hanta ne da aka masa hadadden gashi Mai yarfe da ruwan tafasa hantar, shima ya yi kyau sai kamshi take, tunda ya ga gashin ya ji miyansa ya tsinke, a hankali ya jaa karamin plate , hantar ya zuba a ciki, wani karamin Abu Mai kama da bowl don dai shi Yana da murfi ya bude, romo ya ci karo da shi, dibar romon ya yi ya zuba a gasashiyar hantar.


Cukali Mai yatsu ya sa tare da fara sokar gasashiyar hantar yana sawa a baki , idanunshi a lumshe Yana Kara yabawa girkin Ummie'sa, don ta iya sarrafa abubuwa, musamman ma wanda tasan yana so....tun da Asneeeh ya koma gida sai ya zamans ta kasa natsuwa, duk Inda tai sai ta ringa ganin photon Sheikh na mata gizau, ta kasa zaune ta kasa tsaye sai jujjuya card din da ya bata take, tana tunanin ko ta kira, ko ma karta kira, yanke shawarar kira ta yi.


Tun bayan Magrib take Kiran wayar, har karfe goman dare, ba'a dauka ba ita Kuma bata gaji da kiransa ba, yanzun ma rike take da wayarta tana kokarin k'ara kira, haka ta kira ta gama ring har ta katse ba'a dauka ba, numfashi ya ja tare da cewa "mey be yana wani abun ne , ko baya kusa da wayar, bari na bari sai an jima na sake kira", ta fada tana ajiye kiran, ni Kuma na bita da kallo yana Mai tausaya mata, ganin yarda take ta wahalar banza, duk da dai a sani na shi din ba Mai share mutane bane, sai dai yana da murdadden hali....


Tattara gava dayaKayan amfaninsa ya yi ya shige ciki..



Karfe tara da rabi Asrat ya turo kofar parlourn ya shigo dauke da kayan breakfast nasa , a hankali ya Dan kallesa ta gefen idanu, a'lama ya masa da ya ajiye kayan ya zo.


Zaune yake cikin shigarsa ta yau da kullum , laptop nasa ne a gabansa, lokaci bayan lokaci yana Dan magana, in yay daya sai ya jima sosai bai kuma ba, ajiye tray din da aka jera kayan breakfast din ya yi, karasawa yay gefen Sheikh Yana zura kansa, da son ganin wanda yake magana da su, ganin yarda yake leqa kansa ne yasa, ya juya masa gaba daya fuskar laptop din, Yana Mai lumshe idanunsa, wanda hakan yay sanadiyar kwanciyar zara²n eyelashes nasa.


Gaba daya mutanen da suke cikin laptop din Mazan sanye da fararen kaya matan Kuma Abaya ce bak'ak'e Yar Saudi, daga dukkan alamu dai meeting suke, kuma dai kamar shine shugabansu duka, gashi sun saba da yana yinsa, basu damu da sai ya yi magana ba, sai duk suka zubawa Asrat idanu, shi ma sai ya zuba musu nashi, d'aga musu Hannu yay, suma suka d'aga masa.


Wasu daga cikinsu ya san su, wasu kuma suna dan haduwa wasu lokuta na musamman, ko in sun je Umrah ki Hajj, fira suka hau yi, labari ya fara basu, suna dariya don Asrat dai ba dai shafta ba , ya iya labaran ban dariya.


Juyar da fuskar laptop din ya yi garesa, yana kallonsu duka, cikin natsuwa ya fara juya labbansa yana son yin magana, dak'yar ya iya cewa ''In sha Allah gobe ina hanya", ya fada kamar wanda aka wa dole, cikin murna suka nasa fatan Isa lafiya, wani Abu ya danna a jikin laptop din tare da rufeta ya ajiye a gefe , zama Asrat ya yi a gefensa, tare da cewa "zaka wuce gobe ne ?", Ba tare da ya kallesa ba yace "kana da wata matsala ne ?",da sauri ya girgiza kansa a'lamar bashi da wata matsala.



A tare suka mike, shi ya yi dining room shi Kuma ya fice....zaune suke suna firar yarda tafiyarsu Dubai zata kasance, "Zaki tafi da kayan ne ?", Beerbah ta tambayi Layleerh, Yar harara ta balla mata kafin tace "Abu ga dole, ai Ina Jin wannan zuwan ma kayan da zani da su sun fi ki wanne," jinjina kanta tayi kafin tace, "na yi magana da mutanen nan fa sun ce yanzu an dad'a tsauri, har na dan fara jin tsoro, " dariya Layleerh ta yi kafin tace "chab, ai in sun san wata basu san wata ba, Ina da dubarar da Wallahi mutum ko ya fi kuturu kwakwa ba zai tab'a iya gani abun da na dauka ba", "wacce kalar dubara kenan ?", Beerbah ta Kara tambayarta tana kallonta,dariya ta karayi tare da cewa "ke dai In kina tare da ni kawai gobe Zaki ga yarda za'ayi, likita na musamman ke aikin , Kuma ya had'a ki da Likitocin da zasu cire Miki ba tare da kin sha wata wahala ba" , to tun da suka fara firarsu bata da musu baki ba, haka bata kallesu ba sai da suka zo karshen maganarsu ta dago da idanunta masu dauke da manya²n kwayar idanu ta zuba musu.


Beerbah ce ta kalleta kafin tace "ke dai kam nasan dan yau da kullum zaki yi, don ba zaki iya sabon da na zo.mana da shi ba", bata tanka ta ba sai ta Kara dauke idanunta, a'lamar bata son yin maganar.


Shafa cikinta ta Dan yi tana yamutsa fuska, cikin rashin son magana da fusgots tace "zan je restaurant", ta fada tana tattara gashin kanta da aka yaryara mata sabon kitson attachment din ta ya zauna ya yi kyau a kanta.


Duk mikewa suka yi suna kallonta, a tare suka fice, kowa motarsa ya shiga suka fita a gidan, direct ita Bilnaf ta nufa, yalwace gurin yake da kwayayen lantarki da suka haskaka gurin ya zama tamkar rana.


Zafafan motoci ne masu kyau da tsari, gaba daya an parker su a parking lot din da yake gurin, ajiye ta ta motar tayi, tare da daukar abun da zata buk'ata ta shiga ciki .



Tun da ta shiga mutane suke kallonta, har wanda hankalinsu bai kai kanta ba kamshin turaren da ta cika yake ta jawo hankullansu, da damar mutanen da suke gurin sun Santa, don kusan mutun dai² ne bai Santa ba da sanin halinta, chan special side ta nufa, inda babu yawaltar mutane, komai nasu a natse yake sai dai in ka zauna a gurin in Kai talaka ne zaka sha tsada.


Menu din da yake ajiye akan table din ta dauka, abubuwan da suke gurin ne rubuce a jikin menu din, Wanda zata ci ta zab'a tare da amfani da telephone din da take gurin ta kira ta shaida musu abun da take so da Kuma inda take, ba'a dauki lokaci Mai tsayi ba aka kawo mata abun da tace, card dinta ta bayar a cire kud'in, sai akwai aka dawo mata da shi wai an biya mata.


Cike da mamaki tace "karb'a ku cire kud'in ku", kara maimaita mata abun da aka ce aka yi, ranta ne ya fara baci da ganin an ma raina mata wayau da har zata zo siyan Abu kamar ita wai ace wani ya biya mata, tana ganin hakan kamar kaskanci ne a gareta.fada ta farawa wadda ta mayar mata da card din.


"Hi Maa. Tunda aka ce an biya miki kiyi hkr ki karb'a mana, ko bakya karb'ar abun a gun wanda baki sani ba ?", Ta ji an fada a bayanta,cikin hasala ta juya bayanta, kyakyawan saurayi ta gani Yana mata murmushi, fuskarta ta kara hadewa ba a'lamar wasa a kanta, duban Abin cin ta yi ta kara dubarsa, tsaki Mai tsayi ta ja kafin tace "Kai baka kai matsa yin da zaka Siya min abu ba,kana kaskantace , " zai yi mgn ta dauke gaba days Abin cin ta juye masa a kansa,cikin kaushin murya tace "wannan sai ya zamo izina a gareka", tana gama fad'ar hakan ta tattara komai nata ta fice, sumarsa da ta ci kudi ta yalyalo a kan fuskarsa ya tab'a, ransa ne ya b'aci ganin har da sumar tasa ta b'ata masa....sai da ya gama dukkan abun da zai yi kafin ya fito parlourn kasa gurin da mahaifiyarsa take, "gobe zaka koma?", Jinjina mata kai ya yi ba tare da tayi magana ba, "Allah ya kai ka lafiya, yanzu ya maganar mu ?", Ta fada tana kallonsa, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya daure yace "Ummie wacce magana ?", Harararsa tayi kafin tace "saboda maganar bata gabanka shi yasa ka mata ai", gemunsa ya dan shafa , kafin ya jujjuya kai a'lamar ba haka bane ", to ya ne?", Ta fada tana kallonsa, shiru ya yi yana kallon k'asa don shi Sam bai ma gane akan Mai take magana ba, "akan aure da na ke magana ", da sauri ya d'aga idanunsa ya kalleta, cikin son gasgata abun da ta fad'a din", Ea aure nake nufi", lumshe idanunsa ya yi, don shi kam bai san mai zace ba, "haba Imam ya kamata kawa kan ka fada fa, Abokanka babu wanda bai yi aure ba, wasu ma mata bibbiyu garesu, daga mai 'ya'ya ukku sai Mai sama da haka, kai hatta da sa'anin Asrat sun fara yin aure, kai kenan haka zaka yi ta zama babu mata babu komai ?", A hankali ya bude bakinsa, "Ummie aure , mutuwa da haihuwa duk na Allah ne, sannan kuma lokaci ne, idan suka zo bb makawa sai bawa ya yi su", murmushi ta yi don dama tasan abun da zai fada kenan, don shi kullum dan bada wannan uzurin ne, da ka matsa sai ya fara kawo maka hadissai da ayoyi.


"Na sani kuma na fahimta Hammad, Amma Kai abun ne naka kamar Wanda aljannu suka aura, k'wata² baka sha'awar auren baya kuma burgeka, kawai dai ga kanan² ne, "shiru ya mata don bai san mai zace da ita ba, zancen aure da wani ma nauyi yake masa baya iya ma,balle kuma da mahaifiyarsa .


Ranar yini suka yi parlourn suna Hira, don dama shi d'abi'arsa ce duk in ana gobe zai koma to ranar yini yake yana zaune s parlour, ta haka ne yake kara fahimtarsu, ko wani Abu in suna so.... Layleerh da Beerbah ne zaune suna bincikar ko zasu samu jirgin da zai Kai su Dubai jibi, sai dai basu samu ba sai dai na gobe, Hakan yasa suka ajiye zance cewa sai jibi zasu tafi, suka yanki ticket dinsu kwara ukku, sai kuma na daga Kt zuwa Lagos don ta chan jirgin zai d'aga , kiran Aizza suka yi suka fada mata , nan suka yanke shawarar , su tafi Asibiti su yi abun da zasu yi su ga kafin gobe.



Shirinsu suka yi suka tafi, ita Aizza dama already har ta kara chan, suna zuwa suka sameta, wani office suka nufa a tare, wani Matashin likita suka samu, cikin fara'a suka gaisa, dama sun saba kalar harkar da shi so bai wani tambayesu basu da suke so ba, ya nufi wani daki da su, sun jima sosai kafin suka fito.


Dak'yar Layleerh da Beerbah suke tafiya, fuskokindu duk sun hada zufa, Aizza kuwa, a hankali take tafiya, ga gefen cikinta manne da plaster, kudade masu yawa suka bawa likitan kafin su tafi..



Washe gari da sassafe jirginsu ya tashi daga KATSINA zuwa Lagos, lokacin da suka karasa bai fi saura 30 minutes jirginsu ya tashi ba, gurin awon kaya suka k'arasa, normal aka auna musu kayansu suka shige ciki, sai dai idanun Aizza na kan wata Jaka Yar madaidaiciya mai kyan gaske, da take bayan ta su.....



Mai kuke ganin wa'innan bayin Allah zasu aikata ?.
Ita da take kallon Jaka ki me ne a cikinta ?



Normal group#300
Special group #500


1499884120
Umma Salma Sani
Access bank


07033371851



YOUR YAR GABAN GOSHI 😂


YAR LELEN ROYAL STAR......🌹 SHEIKH IMAM🌹


By

YAR LELEN ROYAL STAR..



Normal group #300
Special group #500


1499884120
Umma Salma Sani
Access bank


07033371851

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Second 2 the last free page.


Page.....9


Lafiya Lau suka karaso cikin k'asar ta Dubai Mai cike da tsaro na musamman, a hankali matafiya suka shiga saukowa daga cikin jirgin, suma haka suka fara saukowa dukkansu sanye da bak'ar Abaya sun yi rolling kansu da mayafan abayar da suka musu kyau na gaske, barin ma Aizza, kayan sun mata kyau sosai kamar Balarabiya.


Ko da suka sauko idanunta na kan jakar da take bayan tasu, haka suka tafi gurin da ake screening mutum kafin bari ya shige, tsakaninsu duk sai da suka bada tazara ta a kalla mutane biyar², don haka Aizza ce a gaba, sai bayanta mutum biyar ne kafin Beerbah, tsakanin Beerbah da Layleerh kuma mutum biyar ne.


Ana zuwa kan Aizza aka sa mata wata na'ura, a jikinta, kuka na'urar ta shiga yi, kallonta mutumin ya yi itama ta kallesa, a'lama yay mata da ta bude handbag din da take rataye a kafadarta, zare handbag din tayi daga kafadarta ta cire tare da mika masa, Bincike aka fara ciki, sai dai babu komai na abun laifi a ciki don daga kudi sai phones nata kawai a ciki, mace aka sa ta bincika ta ba a samu komai a jikinta ba, hkr suka bata ganin ba'a samu komai a jikinta ba, Jakarta suka bats da Kara bats hkr kafin ta wuce, haka duk aka musu, amma ba'a samu komai a jikinsu ba, securities din sai mamakin wannan abu suke, su kuwa suka fuske tare da ci gaba da harkokinsu, gurin da za'a tantance jakunkunansu suka k'arasa.


Kamar wancan haka aka chaje jakunkunansu Amma ba'a samu komai a ciki ba, sai da suka dauki jakunkunansu suka fara tafiya, kafin suka ji, an ce "waye bai wannan jakar ?", Duk juyawa suka yi banda Aizza da ta ci gaba da tafiyarta, daga gefen da mutane suke, aka daga wani kyakyawan hannu sama, da sauri mutanen da suke gabansa suka matsa masa.


A hankali cikin natsuwa da Kamala ya fara tafiya zuwa gurin da ake tantance jakunkunan, cikin sanyi da Kuma harshen larabci yace "akwai wata matsala ne ?", Da sauri securities din suka juyo garesa, saboda muryar da suka ji, kallonsa suka yi suka kalli jakar.


Cikin larabci suma suka ce masa "zamu iya bude jakar?", Jinjina musu kai ya yi, a'lamar ba matsala.


Da sauri suka zuge jakar, fiffitar da kayan da suke ciki suka fara yi, ba wasu kaya bane sosai, laptop nasa ne sai wasu sai wasu abubuwan Amfani, daga chan kasa aka fara fitar da wasu yan madaidaitan robobi, bude robobin aka shiga yi, da sauri ya ja baya, yana k'ara kallon jakar, "innalillahi wa'inna ilaihi Raju'un!", Ya furta daga chan k'asan zuciyarsa ba tare da kowa ya ji ba.


Daya daga cikinsu ne ya matsa kusa da shi tare da cewa "Yallabai zamu tafi da kai Office, domin muna buk'atar bincike a kan ka", jinjina kansa ya yi, tare da bin bayansu, haka suka sa sa a tsakiya wasu na bayansa wasu na gabansa, lafiyayyiyar mota Mai kyan gaske aka shigar da shi, tare da wucewa da shi Chan headquarter din su.



Suna barin gurin ta saki sanyayyiyar ajiyar zuciya da murmushi a tare, duk kallonta suka yi, ganin irin kallon da suke mata ne yasa ta kawar da kanta gefe, tana gintse fuskarta .



Wata lafiyayyiyar mota ce Mai kyan gaske ta tsaya a gabansu, daga ciki aka bude musu, shiga suka yi, Mai motar kuma ya jaa ta da wani irin speed.


Basu tsaya ko Ina ba sai wata tsararriyar unguwa Mai kyau da tsari , anguwar da ko a k'asar Dubai din ma masu kudin k'asar ne suke zauna a cikinta


Gaban wani tamfatsetsen gidan mai kyau da girman na gaske, suka tsaya, bude musu get aka yi kafin motarsu ta sulala cikin gidan.


Gida ne Mai girma da fadi, wanda yake dauke da abubuwan more rayuwa, sun dan yi tafiya a cikin gidan kafin su karaso wani tankamemen kofar parlour, ana driver ya yi parking, firfitowa suka yi, Aizza na gaba Layleerh da Beerbah na bayanta suna tafiya a hankali kafafu a bubbude.


Suna shiga cikin gidan, suka tarar da wasu mutane da fararen kaya da a'lama Dr ne da nurses, sannu da zuwa suka musu, cikin yarfe hannu Beerbah tace "Dr we need your help, " ta fada cikin radadin azabar da take ji.


Gyada kansa ya yi yana kallonsu, wata kofa suka nufa, Aizza kuma ta zauna anan gurin da Dr din ya tashi.


Minti kadan da shigarsu dakin ta fara Jin ihu da kururuwarsu, a hankali ta tashi daga inda take ta nufi inda suka shiga, guri ne kamar Asibiti don da akwai komai na bukata, kama daga kan kayan aiki da komai dai da aka San ana samu a Asibiti, kwance lame² ta gansu, sun gwagwafe cinyoyi sun budewa Dr din kafafunsu, Abu yake kokarin ciro musu a cikin gabansu, Amma yak'i ciruwa dai faman ihu da kuka sosai.


Kallansu ta yi da kyau, fuskarta da jikinta bai nuna tsorata ko wani Abu a zahiri ba, sai dai a bad'ini tsorace take da yarda ta ga suna yi, sun wani gwagwafe kamar masu labour, jingina tayi da jikin Bango tana kallonsu.



An jima sosai ana kokarin fitar da abun da suka sa a gabansu Amma Abu ya faskara, tun suna ihu da karfindu har ya fara karewa, daga su har Dr din da nurses din cikin fargaba da tashin hankali suke, ga wata uwar zufa da take karyo.musu.


Cikin fads Dr din ya fara cewa "da hankalinku da tunaninku, zaku yarda ku aikata. Wannan aikin?, Shi likitan da ya muku bai fada muku ilolinsa ba ?, to ku sani babbar illa garesa, don ko Wanda kuke zuwa a fasa cikinku a sa muku, matukar illa ne da shi balle wannan da zaku Bude prevent part naku a sa muku, ku yanzu baka tsoron ma abun ya fashe muku a jiki, ko Kuma a nemesa sama ko k'asa ba'a gansa ba ?", Ya karasa fada da sigar tambaya.


Su dai ba baka sai kunne don bala'in da suke ciki ma kad'ai ya ishesu, jin su suke su ba k'asa ba su kuma ba sama ba, mika hannu Dr din ya yi, wata nurse ce ta mika masa Scissors, Mai kaifi irin Wanda ake Amfani da shi gurin k'ara mace ya yin haihu, gaban Layleerh ya koma, cikin rashin tausayi ya kama fatar da take jikin Prevent part nata ya tsarga, ihu Mai karfin gaske ta saki, tare da kankame farin bedsheets din da aka luluba akan gadon da yake tamkar na Asibiti.


Wani karfe ya dauka tare da zura mata shi cikin prevent part din nata, kara yankawa ya yi, sai da ya yanka mata gaba daya fata bakwan da take gurin, kafin ya sa mata hannunsa Mai dauke da safar hannu.


Tun tana kuka da kururuwar neman taimako har ta dai na sai dan nishin da take kamar akuyar da ta gagara haihuwa.


Da yatsu biyu ya kama abun tare da fara zarowa, ta sha bak'ar wahala kafin ya fito da abun, da mamaki yake bin robar da ya ciro da idanu, roba ce madaidaiciya mai murhi an rufeta rikif, girgiza kansa ya yi, Yana jinjina wannan lamarin, ashe akwai wanda zai iya salwantar da lafiyarsa saboda neman kudi, Neman kudin ma ba na Allah ba kudin Haram, bak'ak'e kudi da basu da albarka .


Ba tare da tausayawa ba ya fara dinketa kamar kwarya, sai da ya dinketa Ras, kafin ya koma kan Beerbah kamar yarda yawa LAYLEERH haka ita ma ya mata.


Juyawa ya yi gurin da Aizza take, gaba days ta sha jinin jikinta, ga kasa motsawa daga inda take , ta kafe Abokan cin mushenta da idanu, tana kallon irin bak'ar wahala da suka sha a gurin neman kudinsu, "you see ?,zan baki shawara ko watan wata rana, kar ki sake kice zaki yi abun nan don yana da side effects,"ita dai bata ce masa komai ba bata ma kallesa ba, balle yasa ran ta ji abun da ya fad'a.


Zuwa tayi zuwa chan ciki, sama ta haye, tare da fadawa wani room, kamar dai room din ta na gida wannan ma sak abun da yake chan shine anan, a gajiye take Hakan yasa bata zauna ba sai ta shiga band'akin, a hankali ta zare kayan jikinta, gefen cikinta daga dama inda yake manne da plaster ta tsurawa idanu tana kallo.


A hankali ta shafa gurin tana sauke ajiyar zuciya, wani Abu kamar leda tasa ta daure gurin, tare da sakarwa da kanta ruwa, numfashi ta shiga saukewa a hankali tana Kara baza gashin kanta , sai da ta ji ruwan ya daki tsakiyar kanta sosai kafin ta kashe shower din ta fito daga cikin bathroom din.


A hankali ta fito tana daure da towel tafiya take kamar Yana Jin tsoron taka k'asa, haka ta ci gaba da tafiyar har ta k'arasa gefen gado ta dan zauna, barci ne sosai a idanunta don jiya dadewa ta yi ba tayi barci ba, Hakan yasa ta kwanta tana dafe da gefen cikinta Mai dauke da plaster .


Lulube jikinta tayi da duvet tana lumshe idanunta...kafin wani lokaci gaba daya gidajen radio har na Nigeria sun samu labarin wai an kama babban Malamin Addini ya yi safarar cocaine daga Nigeria zuwa Dubai, take kasashe suka dauka, tun kafin su karasa chan headquarters din har an fara kiyaye² daga k'asashen duniya, akan San Jin ba'asi da gundarin bayani.


Kowa yasan yarda Dubai ke da tsauri, Basu kula ki wacce kasa ba, suka ce sai sun yi bincike sun gane asalin abun da yake faruwa.


Sun yi tafiya mai tsayi gaske kafin su karaso wata babbar headquarter , Mai abubuwan ban mamaki, jiragen da suke tashi da sauka a cikin headquarter'n kad'ai ma abun tsoro da Al'ajabi ne.


Wani babban gurin ajiye motoci suka ajiye motarsu, budewa Imam kofar motar aka yi tare da basa hanyar wucewa, cike da confidence, ta fito daga cikin motar, kamar ko yaushe fuskarsa bata dauke da murmushi sannan Kuma ba daure take tamau ba, don a halin yanzu fuskarsa ma tafi bayyanar da annurinsa.


Ciki aka wuce da shi, ko da suka shiga ciki, kasantuwar case din ya had'a da gurbata k'asa da son kawo musu bara gurbi, sai kawai aka wuce da shi gurin tuhuma kai tsaye.


Tuhumarsa aka shiga yi, da Jin abun da ake tuhumarsa da shi sai ya kasa magana, sai kawai ya sauke idanunsa kasa, bai nuna wata a'lama ta razani ko tsoro ba, haka zalika bai gusa da fargaba da mamakin abun da ake tuhumarsa da shi ba, har zuwa dare shi dai bai yi magana ba, tunda bai San Mai zai ce da su ba, jaka dai gata jakarsa ce aka ga kayan

Please Login or Register in order to submit comment