Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kunsa sune ,bayan aikin harshe da kuma na zuciya akwai ayyukan gabbai, irin su sallah, azumi, da dai sauran rukunan musulunci, da jihadi saboda daukaka kalmar Allah, neman ilimi da makamantansu.
Allah madaukakin Sarki yana cewa, 'Idan aka karanta musu ayoyin Allah sai su ara musu imani.
A wani wajen kuma Allah cewa ya yi Allah shi ne wanda ya saukar da nutsuwa a cikin zukatan Muminai domin su kara imani tare da imanin da suke da shi.
Imani yana dad'uwa a duk lokacin da bawa ya kara ayyukan da’a ga Allah ya yawaita ibada, yana kuma raguwa a duk lokacin da da’arsa da ibadarsa suka ragu, kamar yadda aikata sabo ma yake tasiri a kan imani, har ma idan sabon ya kai babbar shirka ko babban kafirci to sai ya warware asalin imani ya bata shi, idan kuma bai kai haka ba to sai ya hana imanin kai wa matakin da yake wajibi ne ya kai shi, ko kuma ya bata shi ya raunana shi,"numfashi Mai sanyi da natsar da zuciya ya saki, cikin wani irin Yana na kad'aita Allah da son Manzon tsira , tare da wani shauk'i da masu wadataccen Imani ne kawai suke jinsa a lokacin da aka fada musu Allah sannan aka karantar da su wani abu game da shi.



Cikin natsuwa da gyara zama tare da karya harshen domin jin dadin kallon jama'ar da yake wa karatu , dama Wanda suke saurarensa na gida da na wasu shiyoyin ta hanyar wasu kamarori da aka Ajiye a gabansa domin nadar sauti da dau daukar karatunsa, da kuma loudspeaker da take karade gaba daya anguwar har da makwabta.



"Allah madaukaki yana cewa,Hakika Allah baya yafe (laifin) shirka da shi, amma kuma yana yafe duk abin da bai kai haka ba ga wanda ya so yafewa . Nisa’i 48.

Allah Ta’ala ya kara cewa
,Suna rantsewa da Allah cewa ba su fad'i komai ba, alhali sun fadi kalmar kafirci, kuma saboda haka sun kafirce bayan a da sun musulunta .Tauba: 74
Annabi (S.A.W) kuma ya ce.Mazinaci baya yin zina a lokacin da yake cikin yin zinar- alhali yana tare da imani, haka nan shi ma barawo baya yin sata tare da imani a dai² lokacin da yake yin satar, shi ma mai shan giya ba ya shanta a dai² lokacin da yake shanta alhali yana da imani. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi".kadan ya rage muryarsa, yana jin dan agajin yake bayansa da yake fada masa lokacin Issha ya yi,duba Rolex watch na sa yay, cikin dan kad'a kai, da Jin yarda muryoyin mutane suke ta faman kabbara .


Cikin natsuwa ya had'a hannayensa biyu tare da cewa ,
gyara abun maganar yay, tare da sa yatsarsa ya dan bubbuga kad'an wani sauri ne ya fito daga cikin abun maganar kai tsaye ya dira cikin kunnan jama'a, take kowa ya natsu, sun yi zaton wata madarar ilimin ce zai kara zubar musu a gurin, Dan murmushi kadan yay don ya lura da yarda hankullansu gaba daya ya dawo garesa ba zato suka ji ya ce "Subhanakal-lahumma wabihamdik, asshadu an la'ilaha illa ant,astaghfiruka wa-atoobu ilayk......



Comments
Share


YOUR YAR GABAN GOSHI😂



YAR LELEN ROYAL STAR........🌹 SHEIKH IMAM🌹


By

YAR LELEN ROYAL STAR


Page.....3



Nan guri ya rude ana ta kabbara, da godewa Malam cikin wata dauwamammiyar kaunar Allah da Manzonsa da ya kara dasa musu a zuciyoyinsu.
Anan aka gabatar da Sallar issha , bayan nan suka gaisa da mutane kafin suka fito a Masallacin shi da Asrat da yana gefensa kullum da ko yaushe, cikin natsuwa suka sa Kai cikin parlour gidan da Sallama dauke a bakunansu, cikin murmushinta marar yankewa ta Amsa musu, tana mayar da hankalinta a kansu, TVn da take kallo ya dan tsurawa ido , sai kuma ya dawo da dubansa gareta, cikin harshen larabci Asrat ya ce "Ummie ga shi a zahiri kallon mai kike masa kuma a TV ?", Ya fada yana dan dariya cikin suffar zaulaya.


Rausayar da kanta ta Dan yi har lokacin fuskarta da murmushi tace "Uhmmm ba zaka gane ba Asrat, ni kad'ai nake iya gane abun da nake ji idan Ina kallon karatuttukan Imam , Ina ji duk duniya bb macen da ta Kai ji sa'ar samun D'a nagari kamarsa, shi yasa kullum nake dad'a godiya ga Allah don ya kin baiwar da ba kowa ne yake da ita ba, Ubangiji dai yay Albarka", ta fada tana k'ara yalwata fuskarta da tausassan murmushi, tsura mata idanu ya Dan yi kafin yay murmushi cikin ransa ya furta "Ameen" shi kuwa Asrat zama yay yana tsokanarta.


Gyara zamansa yay, tare da fara dan danna wayarsa, seconds kadan Asrat ya ji karar shigowar sak'o a wayarsa, dubawa yay ganin Number Imam yasa sa dubawa cikin sauri don yasan wata killa wani abu yake so , don mafi yawan lokutta in yana son abu ko zai ce a masa in baya Jin Yan maganar sai dai ya tura maka sak'o ko da kuwa kuna kusa da juna ne, "laptop na", abun da aka rubuta a sak'on kenan.


Mik'ewa yay zuwa saman, yana cewa Ummie "Ummie bara na daukowa Imam Laptop nasa na dawo", ya fada yana hayewa sama, bai jima ba ya dawo dauke da jakar laptop, cikin girmamawa ya ajiye masa a gabansa tare da matsa masa da center table din , sai da ya zauna har sun ci gaba da fira sai wani sak'on ya kara shigowa wayarsa, dubawa yay shima daga gurinsa sak'on ya fito "Brief-case" ya gani an sa masa, daukowa yay ya kawo masa, ci gaba yay da aikinsa su kuma suna zaune suna firarsu, har goma ta wuce sha daya ta yi, hamma Asrat da kuma Unmie suka yi kusan a tare, kallonsu yay da gefen idanu, su kuma a tare suka mike tsaye, Ummie ce ta ce "Imam Abin cinka na dining naka, sai da safe", jinjina mata kai yay tare da cewa "Allah ya bamu Alkhairi", daga haka bai kara ce wa komai ba, shi kuwa Asrat ce masa yay "sai da safe"."ka kula, sannan ka tabbatar ka yi addu'a kafin ka kwanta", ya fada ba tare da ya d'ago idanunsa daga kan laptop nasa ba, "tom Ya Sheikh Muhammad Imam Aleeyou", y fada yana murmushi, shi kuma bai kallesa duk kuwa da cewar yasan zaulayarsa yake, anan ta tafi ya barsa.


1pm ya tashi daga gurin da yake, kofar parlourn ya k'ulle da addu'o'i a bakinsa, dawowa yay ya saki duka labulayen parlourn ya gyarasu, gaba daya kayan wutar cikin parlour ya kashesu, kafin ya tarkata gaba daya tarkacensa ya bar cikin parlourn....Kwance take cikin ruwan dumin da ta gani haɗe cikin bathtub Wanda yake fitar da kamshi Mai dadin gaske, ga Kuma wasu reds flowers masu kyau da kamshi, idanunta da suke lumshe ta ware , a hankali ta bude shower ta wanke jikinta da yake dauke da kumfa, kanta ta fara nadewa da karamin towel sai kuma ta lulubawa jikinta rigar wanka mai taushi gaske, bathroom slippers ta sawa kafafunta, tare da shiga gurin d'azun inda kaya suke har ma da kayan kwalliya, shiryawa ta shiga yi cikin kuzari , anan ne na gane ashe kayan kwaliyyar da suke chan bedroom da ma kayan da suke cikin wardrobe an sa su ne kawai don kwalliya, anan Kuma na ga karshen kwalliyar, don gurin ajiye takalma ma da ban ne, bangaren slippers daban , boot da ban , heels shoes ma daban, jakunkunan kwa yarda kasan shago, babu kalar da babu, ga sunan masu kyau da tsada.


Chan gefe kuma katon guri ne da aka k'awatasa da turaruka da maya²i masu kyau da tsada, sosai ta b'ata lokaci a gun shafe²nta ta, ba wata kwaliyya Mai yawa' tayi ba amma tayi kyau sosai.
Wardrobe nata ta bude,kaya ne kala² suka bayyana, kallo daya ta musu zaro daya a cikinsu , dar suke cikin ledarsu , b'arewa tayi nan wasu kaya suka bayyana, riga ce iya cibiya sai kuma crazy jeans , ga wasu uwayen kacoci a jikinsa, rigar kuma fara ce an mata zanen heart yana d'igar da jar kala a jikinsa, kayan ta sa a jikinta ba tare da damu da sa underwears ba.


P-cap ta sawa kanta tare da daukar slippers Mai taushi da tudu, jacket din wayarta ta chanja zuwa kalar kayan da tasa, fitowa tayi cikin tak'ama tana tauna chewing gum , cikin wani kalar sauti.


kwance suke akan makeken bed din da ke cikin bedroom din, cikin fita hayyaci da nuna zalamawa junansu, suke lasar jikin junansu, tab'a junansu suke ta ki ina,
Suna lasar jikin juna da harshe,shafa Jikin Layleerh , Beerbah take tana kissing dinta, dai² kan nipples dinta ta daura bakinta tana zagayewa tana dan tsotsa, nishi kawai suke yi duk sun fita hayyacinsu Kamar su cinye juna.Aizza ce ta fito daga bathroom ganin su a haka yasa ta dauke kanta tana Murmushi, komawa tayi gefin sofa ta zauna, ga mamakinsa wayarta ta dauka tana latsawa, Jin abun na na kare bane, sai ta tashi daga bedroom din zuwa parlour.
nishin su Layleerh ba karamin kara daga hankullansu yake ba.(kafin ki/ka zageni ko muzantani, ka tsaya ka karanta , domin gane abun da ake son fitarwa)...ta fi 30 minutes a gurin kafin suka fito, sai da suka zauna kafin ta daga kai ta kallesu, "Ina bedsheets din ?", Layleerh ce ta shiga sai gata da bed din da suka gama tsula tsiyarsu a kai, "kirata ki bata", tana gama fada ta shige ciki.


Bathroom ta shiga, daga chan gurin da clothes yake ta bude wata kofar, fadawa kan bed din tayi tare da lumshe idanunta, wasu abubuwa ne masu kama da feels ta ji suna bijiro mata tun daga tafin kafarta har izuwa cikin kwakwalwar kanta, kad'a yatsun kafarta take, tana dan sauke numfashi a dan zafafe...Agogon da take manne da jikin bed din ce tai kara tare da buga karfe 3.
Cikin natsuwa ya yaye duvet din da yake jikinsa, tare da ziro k'afafunsa kasa, a hankali ya tashi, slippers nasa da suke gefen bed din ya sa, tare da mik'ewa, bathroom ya bude ya shiga, bai jima sosai ba ya fito sanye da wata ash din jallabiya mai santsi da taushi, ya daura hula irin ta Yan Makkah a kansa, gashin kansa ya kwanta sosai a bayan k'eyarsa wanda ke nuni da cewa wanka ya yi.


Kan mirror ya karasa, cikin natsuwarsa Mai burge mutane, da Kara sanya masu natsuwarsa a zukatansu ya dauki kwalbar turaren Viktor &Rolf Flowerbomb Haute couture, a jikinsa ya shiga fesawa, har sai da ya ji ya fara hawar masa kai kafin ya ajiye, cikin takunasa da natsuwarsa ya karasa gurin da aka kiillacesa musamman domin yin Sallah, gurin linkif yake da wani irin carpet mai taushi gaske, ga wani kamshi na musamman Mai kwantar da rai da sa natsuwa da yake fita a gurin, dai-daita sawunsa yay tare da kabbara, karatu ya fara yi cikin natsuwa dai²tuwa tare kara fitar da ainahi muryarsa Mai dadin sauraro, cikin suratul Nisa'i ya nutsa, yana mai jin dadi karatun da wata iriyar natsuwa, kasancewar shi daya ne yake Sallah, don zai fi sakewa yay karatunsa sosai, amma in da wani ne dole ya tsagaita domin bai san yanayin wanchan din ba zai iya juriyar tsayuwar ko ba zai iya ba ?, da kuma ya lafiyarsa da uzurinsa kamar yarda Manzon tsira ya fada, 'in kana limancin mutane ka ringa takaita karatu yarda kowa ba zai cutu ba, don baka san da yana yin da mutum yake ba, wasu mata ne, wasu Yara har da ma tsofaffi'...JAMVALY HOTEL & RESORT KATSINA...


Sautin kid'a mai karar gaske da dukan zuciya ne yake tashi, ta cikin wani dan madaidaicin guri mai kama da club, gurine karami a ta waje, sai ka shiga ciki zaka ga asalin girman gurin, Yan mata ne da samari masu aji da kud'i, duk da ka kallesu kasan su din Yaran manya ne, duba da yana yin shigarsu, da yarda suke mu'amullantar junansu, gungu² ne na mutane, a kusan ko wane gungu zaka samu mutum sama da goma, gasu nan mata da Maza ba banbanci, kowa da harkar da yake.


Hayaki ne yake tashi kamar gurin da aka hada wutar danyen icce, baka ki iya ganin wanda suke gurin, sai ka matsa kusa sosai.
Su ukku ne , cikin shigarsu kala daya, riga t-shirt da jeans, sai wata jar p-cap, da suka sa a kansu, randunan shisha ne a gabansu, ga tulin favours kala², su biyu suna ta shan shisharsu, ita kuma ta kame a gefe, ta zuba wani farin abu a kan wani dan karamin plate din glass, tana gogawa a hancinta , ko ta diba a hannunta ta shak'a a hancinta......Sai da lokacin Asuba ya yi kafin ya sauka akan Daddumar da yake, komawa yay cikin bathroom din ya sake sabon wanka, da dauro sabuwar Al'wala ya fito, wannan karon captain Jallabiya fara yasa, sai hularsa tashi da kwakwa, fitowa yay yana baza kamshinsa mai dadi, ga wani annuri da yake, fuskarsa sai k'yalli take.
K'asa ya sauko, cikin natsuwa ya masa jikin wata kofa, fara knocking yay, bai jima da farawa ba aka yi magana daga ciki, Ummie ce ta leqo , tana sanye da hijab black wadda ta kara fito tsantsar farin da kyan fuskarta, cikin sanyinsa yace "Ummie lokacin Sallah", ya fada kansa a kasa, yana jin lokacin da ta saki murmushi tare da cewa "na tashi tuni SHEIKH", jinjina kansa yay tare da matsawa Kofar Asrat, a hankali ya fara kwankwasa kamar Mai jin tsoro , cikin magagin barci ya bude kofar idanunsa a rufe.


Rankwashi ya sakar masa a kansa, cikin sauri ya bude idanunsa mai cike barci yace "barka da Asuba SHEIKH", bai Amsa masa ba sai kallonsa da yake, dan turo baki yay yana kallon k'asa, ya lura magana SHEIKH din yake son yi amma ya rasa mai zai ce ta kuma Ina zai fara, chan kasan mak'oshi kamar an masa tilas yace "kana sakaci da ibadarka ko ?", Cikin sauri ya girgiza masa kai tare da cewa, "aa SHEIKH", bai kulasa ba ya fice, shi kam sauke numfashi ya yi, yana bin bayansa da kallo, shi kam ya rasa wannan wani irin kwarjini ne da cikar zati mutumin nan yake da shi, duk yarda kaso ka yi magana da shi har in ka ganka a gabansa to maganar b'ace ma take karasa Mai zaka ce, gashi dai shi ba gwanin magana ba balle ace ko fada ko masifarsa ce tasa ake shakka da tsoronsa, ko kad'an shi tun yana Yaro bashi daya daga cikin yara masu fitina ko fada, haka ya tashi bashi da son hayaniya.



YOUR YAR GABAN GOSHI 😂


YAR LELEN ROYAL STAR......🌹 SHEIKH IMAM🌹


By

YAR LELEN ROYAL STAR


Page....4


... Sheikh Muhammad Aleeyou Imam shi ne cikakken sunansa, Amma ana masa lakabi da (Sheikh Imam)....



SHEIKH IMAM D'a ne ga Aleeyou, wanda ya kasance hamshakin Dan kasuwa da duk fadin duniya babu kamarsa, yana simogarin kaya daga wata kasa zuwa wata kasa, a takaice dai shi babban dila ne na kaya kama daga kayan Abin ci kayan sawa da sauran ababen Amfani, haka yana siyan kayayyakinmu na gida Nigeria kamar su Auduga , zobo , fata d.s yana aikawa da su k'asashen waje domin a safartasu su koma wani abun amfanin, bugu da kari kuma yana da kamfani nasa ba kansa da ake buga takalman fata da kuma kamfanin robobi, sosai ya shahara yake kuma amsa sunansa.
Sun haifi SHEIKH cikin gata da kulawa, in da tun yana da shekara biyu Mahaifinsa ya daukesa ya kai sa chan wata makaranta da take Madina wadda ake kai yara tun kafin su fara magana domin su tashi da larabci da kuma karatun Al-qur'ani a bakinsu...


Bai dawo k'asar haihuwarsa ba sai bayan da ya cika shekara Ashirin da biyar cib, shima a sanadiyar rasuwar mahaifinsa, mutuwar nan ta girgiza dubbsn mutane musamman ma na jikinsa sosai, sanan mutuwar tazo da abubuwa daban² na abun mamaki wanda har mutane da yawa suke zargi da tunanin cewar ba mutuwar Allah yay ba akwai sa hannun Yan uwa ko wasu na jikinsa, haka aka zo rabon gado, duk da Yana da Yara har biyu ga mata, amma hakan bai yan uwansa wawure dukiyarsa ba, dan abun da aka bar musu ba wani abun azo gani bane.



Babu wanda yay wa dangin mahaifinsu magana don su ko da aka ce su kai kara kotu sun wawurewa Yara arzikinsu, sai cewa su kai Arzikin bawa ai na jikinsa, in Allah yawa bawa arziki to bb wanda ya isa ya karbesa, idan kuma yay ka wanda bashi da shi to fa tabbas ko duniya zasu taru don su azurtaka, ba zaka tashi daga abun da ya tsaga na arzikinka ba , da haka ta ci gaba da kula da Ahlinta, tana kokarin ganin ta zauna da su don debe musu kewar mahaifinsu, amma IMAM ko da na second daya mutuwar mahaifinsu bai tab'a fita a ransa ba, ya kara wani irin shiru², bb ruwansa da kowa, harkokin da yasa gaba kawai yake yi, da haka ya koma gurin karatunsa, wanda daga wannan zuwan ne bai kara zuwa ba sai da yana da shekara 30 cif, lokacin ya gama karatunsa tsaf, sai dai fa jami'atul Madina ta rik'esa domin ya yi musu aiki, domin shi din babban likitan kwakwalwa ne bangaren daya kuma yana koyarwa a jami'a, kyautar 'Ya sukutukun Baba Hameed da ya kasance Yaya wa Babansu Imam, ya bawa Ummie kasantuwar tana matukar son 'ya mace saboda bata da ita, sai ta karb'a da hannu bibbiyu.



Wanda dalilin yasa bai fiye samun zama ba sosai, amma duk da haka yakan yi kokarin ziyarta mahaifiyarsa a ko wane karshen wata daya ko biyu, domin duba halin da take ciki da kuma kaninsa, daga nan ya bada karatu a masallatai da aka gayyacesa, sannan Kuma baya kasa a guiwa gurin amsa gayyatar k'asashen duniya da yake samu, ya iya karantar da Mutane da natsar da zuciyoyinsu, zai yi wuya ya je jami'o'i bayar da lectures ba'a samu wanda ya musulumta ba, hakan yasa ake matukar Alfahari da shi domin yana matukar kawowa Musulumci ci gaba.


A cikin lokaci kadan yay kudi na ban mamaki, wanda ki a iya aikin zuwa jami'o'i ya tsaya to ya taka babbar nasara balle kuma har da aikin Asibiti a sashen mafi daukaka da ba kowa ne kan iya jurar karatu a sashen ba sai wanda ya mayar da hankali , sannan yake da natsuwa....



Wacece Aizza....

Cikakken sunanta shine Khadija Ahmed, kuma ita haifaffiyar garin Katsina ce , mahaifinta shahararren mai kudi ne sannan dan siyasar da ake ji da shi, ta wani fannin kuma Yana dan tab'a black market, Mahaifiyarta bafulatanar Adamawa ce , sun hadu da mahaifinta a wani taron karawa juna sani (Samina) ita ma Mahaifinta Mai kudi ne sosai a Adamawa , basu jima da haduwa ba su kai gaggarumin biki sosai aka hada, kasantuwar kudi da kud'i an hadu, sun jima sosai kafin Allah ya basa haihuwa, mahaifiyar tana haihuwa bata ko juya ta ga abun da ta haifa ba Allah y karb'i abun sa, hakan yasa mahaifinta ya dauki son duniya ya daura mata ya nuna mata gata da wata soyayya na ta tab'a kowa ba komai , tayi duk abun da take so ba tare da sha yi ko Jin dar ba, tun tana karama ta tashi da wannan izzar da kuma karfin da mahaifinta ya bata, ta sha raina manya a gabansa sai dai yay dariya, duk abun da zatai baya daukarsa a matsayin laifi, shi koma mai tai dai² ne ko da kuwa ba dai² bane, hakan yasa suka ringa samun sab'ani da mutane a kanta, hatta da makaranta kusan a gida tayi ta, don kar a b'ata mata, sannan kuma kar a doketa, don haka special teacher ya daukar mata, don ta samu ingantaccen ilimi, ya ginata sosai akan boko, bb Addini sam a cikin rayuwata, sunan Allah ma tana ji dai ana fada ita ma take fada, amma bata san komai ba, hatta da Sallah yinta kawai take ba don tasan sharadodi da ka'idojinta ba , ba ma ki yaushe take yi ba,mahaifinta y kara aure, inda matar take tsananin kula da ita,sai dai duk da haka bai mata ba, hakan yasa bata ko shiga harkar matar, tai mata rashin kunya a gaban Baban amma baya cewa komai, in kuma matar tai mishi mgnr sai ya hau ta da masifa ita bata son yarsa, ita bata me ne ne haka zai ta mata mita.




Mafarin kara lalacewarta lokacin da ta shiga higher level ne ta hadu da Layleerh da Beerbah, wanda anan abubuwan suka kara ta6ar6arewa, suma yaran masu kudi ne sosai, wanda aka nuna musu gata makamanciyar tata, an rainesu akan suyi komai ba komai, su tab'a kowa bb abun da zai faru domin sune masu k'asa.


Fadawa harkar shaye² shine babban abun da suka fara jefa kansu a ciki, dagan an kuma sai lesbian, bayan kuma mugayen aiyuka suke aikatawa a b'oye....




Tafiya yake a hankali yana tasbihi da yatsunsa har ya karasa masallacin, cikin natsuwa ya kwada kiran Sallah a babbar masallacin Anguwar, Kai tsaye ya sauka a kunnuwan Al'umma da dama. Cikin sauri mutane suke ta zuwa ga Sallah , Cikin kasalar da yaji ya saukar masa suka gabatar da Sallah, ko da suka idar, zama ya yi yay karatu sosai sai guraren 6 ya tashi zuwa gida.


A parlour ya tarar da Ummie zaune kan Sallayarta tana jan chasbaha, zama ya yi kusa da Ummie, cikin natsuwa da girmamawa yace "Barka da safiyya Ummie", ya fada cikin sanyin harshe , hannunta ta sa a kansa cikin Jin sanyi a ranta tace "barka dai Muhammad", cikin sanyi ya kara yin k'asa da kansa, yana mai jin matukar dadi idan ta kirasa da sunansa na gaskiya, har ya kan ji kamar ta fi kowa iya fad'ar sunan saboda yarda take fitar da ko wacce kalma , "Allah ya maka Albarka Muhammad, ubangiji y kareka daga sharrin mutum da Aljan, Allah ya tsare gabanka da bayanka, ubangiji ya rabaka duk wani abun cutarwa ya azurta min Kai da mace ta gari da zata tarairaya min kai, ta adana min kai , ta tallafi maraicinka", wani rauni ya ji ya zo masa a ransa, cikin kara yin kasa Kai da wani sanyi da ya mamayesa yace "Ameeen yah Ummie", daga haka ya tsuke bakinsa ba tare da ya kara cewa komai ba, sai wasa da hannunsa da yake, magana yake son yi, ko wani abu yake so, amma kuma bakinsa yay nauyi ya kasa fada.



Cikin so da kauna ta ce "Coffee ?", Bai yi magana ba sai zuba mata idanu da yay, hakan kuma ne ya alkalanta mata cewar lallai fa coffee yake so, mikewa tai don had'o masa, tana kara jinjina miskilanci da rashin son magana irin nasa, tunani tai sai kuma ta ga da yawan surutu marar amfani gwara shiru mai amfani .


Don shi mutum ne da bazai tab'a bude bakinsa yay magana ba tare da ka dauki wani darasin rayuwa, ko na zamantakewa ba, sau da dama wani Abokinsa da shine kawai Abokinsa a duk duniya ya sha ce masa "kai din Allon duba ne, sannan Kuma baka maganar banza, dukkan maganar da zaka yi tana da amfani, ko ba'aga amfaninta yanzu ba, gaba za'a gani, Ina matukar Jin dadin tarayya da kai", sai dai ya d'aga kai ya kallesa kawai.



Bata

Please Login or Register in order to submit comment