Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dagudu tayi hanyar fita gabadaya batada kaya ajikinta zindir take

Kurajenta suna nan saidai basucigaba da girmaba gashin kanta duk ya cukuikuye jikinta duk raunine tana fita mutane suka dafa mata baya

Usman kansa yakauce hawaye masu zafi suna saukomasa shihar kunya zaiji idan akace wannan matar wai matarsace.........

Aisha✍🏼

☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



PART 2⃣
30
By gentle
lady💃🏽


Lubcy ko waigen kofar batasakeyiba take jama a sukabita wadansu Na kuwwa wadansu na sallal lami ragowar makotan wadanda dattawane sune suka soma tambayar Usman alakarshi dawannan matar kasace masu komai yayi"" ..


Kaleed yamatso kusa dashi yace dad muje gida,kaiya gyada masa suka wuce mutanen suka bishi da kallo muhd kam yabi tawagarda sukaje kamo lubabatu dakyar suka kamota

Aikuwa takama ihu wlh baxan koma gidan cenba sokuke su kasheni menaimasu kawai dannaje wajen boka sunce saisun halakani harda samirah danasa akashe saitafito tayita banie tsoro

Kasheni sukaso suyi nikuma baxan mutu yanxuba saina tonawa kaina asiri daganan tasoma fadin abubuwanda ta aikata ciki harda tagwayenda tasaka aka shanyewa Jinie duk dansaboda bukatar ta taduniya

Haukadai haykan takama lubcy "" gabadaya wadanda suke rikeda itah sakinta sukayi sukasoma la antarta

Ikon Allah mutanenda sukataru suna kallonta kamar ana nadin sarauta tuni wasu sukasoma Daukar video suna turawa yanar gizo Facebook whatsapp

Ina mamakin mutanenmu shikenan dazaran wani Abuyasa meka kafin akaimaka dauki za afara yadaka cikin net

Aikuwa cikin dakiku akasoma watsashi kaiharma abunda batayiba saida akace tayi

Kowa datashi kalar karyar idan wannan yaturawa wannan saishikuma yaturawa wanie

Usman yanakomawa gida sai zazzabi lubabatu kam tunda tasamu aka saketa saita ranta Ana kare yara sukabita suna kiran mahaukaciya

Duk unguwarda takai saita basu labarin abunda ta aikata kafin dare labari yagama baje duniya

Sajida tana zaune anisa takirata
Tadauka tanacewa shegiyar duniya saiyanxu kike nemana anisa tana kuka tace sajida ba maganar wasa nakiraki muyiba kinga yanda lubcy takoma???

Sajida tamere baki tace itace tajawa kanta ai "" meyasa tataka umurninda boka yabata nifa kokadan banajin tausayinta

Anisa tace sajida lubcy din??? Karfa kimanta acikin kawayenki bakida kamarta tace adako??? Nifa yanxu harmantawa nake dawata lubabatu itace tasiya dakudinta

Anisa tace sajida kinada imani kuwa kinga halinda takeciki lubcy takoma kamar ba itah ba hauka takeyi kamarme

Sajida tace bandashi idan kinsan gunda akesiyarwa kisiyomun na hamsin"' inaruwana inabadai nice nasakamata haukanba

Ko mutuwa zatayi ruwanta keni Abu indai ba akaina yakeba banadamuwa

Anisa taja majina tace naji sajida Amman dai kekindaina zuwa wajen bokan nan ko???

Sajida tamere baki tace yanxu nafara wlh banajin akwai abunda xaisakani gangancin daina mu amala da *hatsabibin boka* saifa idan bana numfashi Amman yanxu nafara wlh komai zakifada baxaisa inji wani tsoroba

Itama doka takarya doka tahau kanta Kuma"" anisa zatasake yin magana sajida tace kinga dagata inacikin nishadina kinzo kindameni Indai akan wannan zancenne karkisake kira na

Anisa tanisa tace shikenan Amman sajida ganie gawane ya ishi wane tsoron Allah inajiye maki fushin ubangiji yasauka akan......


Ke dakata ya isheni haka banason jin wannan surutun naki Mara amfanie yaushe kike dahar zakimun wa azi zuwanki na Islamiyya yaushe

Malamanda suka haifeki da karatu sunyi nasu wa axin baiyi tasiri akainaba saike damadai kece hawala takaremawa

Saikizauna kitare gindin kishiya taja tsaki takashe wayar anisa ta share hawayen takaici tunfarko heelin CE tajefasu cikin wannan masifar duk da itah zuwanta daya tunsanda sukaje tare batasake gigin komawaba

Dan bayan sungama makaranta datayi aure wani Dan uwanta ta Aura yasakata islamiyya damakuma tanada dansauran hankali danduk tafi su sajida kokarin sallah

Amakaranta akemasu wa azi illolan zuwa wajen boka dakuma azabarda akeyiwa wadanda suka kauce hanya aikoda anisa tadawo gida saizawo

Kunsanta dama akwai tsoro indai takaice maku labari Saida anisa tayi sati biyu batacin komai kullum sai kuka dayake ita Allah yanasonta da rahama saiya shiryarda ita cikin hikimarsa da ikonsa

Tun lokacin anisa tadaina hulda dasu sajida sosai dantayi masu wa azi lokacinda tawarke Amman sukai mata fata fata cikinsu rabi atu kawaice tace itama dagayanxu bazata sake zuwaba

Baran baran sukayi lokacin shiyasa basucika wani mu amalaba" anisa tun lokacin takoma Neman tuba tanata istigfari

Abunda yasamu lubcy batasaniba saiyanxu taga anturo video din ta whatsapp shine dalilinda yasaka takirah sajida yinin ranar sukuku anisa tawuni tsoron Allah yasake kamata

Lallai kukan kurciya ma jawabine maihankali yake ganewa""""



Sakon gaisuwa dafatan alkhari agareku ya[truncated by WhatsApp]

☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠



PART 2⃣
31
By gentle
lady💃🏽




Usman baisanarda su labila komaiba"" hardare bayan sallah babu abunda yake saukodashi abinci kansa kasa cinsa yayi Khadija tayi tambayar duniya meyake damunsa saidai yace bakomai

Gabadaya gidan yayi shiru kamar ba mutane kaleed ma yanayinda dadynsa yake ciki shiya haifarmasa da damuwa

Washe gari Usman yadanji dama dama azuciyarsa bawaima wannan ba yanxu mutanenda sukasan lubcy matarsace zaiji kunyar hada ido dasu

Bayan sunkarya suka fita tareda kaleed dansosai yatara aiki company tunda yarage zuwa sosai komai yanason dakushewa

Tunsanda yadawo yasamu lubabatu ba lafiya baisake zaman kirki acenba """ gashi hadin guiwarda sukayi baimaidamasu amsaba danshi Sam yama manta

Yau akwai aiki agabansa""" koda yaje office dinsa antara masa takardu ciki harda masu Neman aiki"" tare da kaleed suka soma cika takardun masu Neman aiki yazabi wadanda yaga zasu iyah yace saigobe aimasu interview""


Labila tana kwance daki haka kurum takejin gabanta yanata faduwa tunjiya wayarta tajawo tabude data danrabonta dahawa tajima gaskiya

Facebook tahau tasoma duba abubuwanda akaturo cikibis tayi da labari makamancin Na mamanta

Amman wannan aitahaukace akace tsaki taja mata sunajawa Kansu duk wannan fa akan danamijine

Kuma duk ta karkare saikin barshi koki mutu kokuma dubunki tacika kihaukace kokuma asakeki karshedai kinaji kinagani kibar mijin kuma kinakallo yayi wani auren kekuma dake dabanza duk daya

Comments da akayi kuwa yafi dubu kowa datashi kalar tsinuwar la antakuwa tashata yafi cikin kwando

Labila tun tana iyah Karantawa harta daina takara gaba mexata gani wani posting ne kuma irin Wanda tawuto

Saikawai tabuda video din ayya Allah sarki da labila tasan mugun ganinda zatayi Dabatayi gigin budawaba saidai anriga an gama

Bayan yabude tashiga video din saiga fuskar lubabatu tanarawa tana tonawa kanta asiri duk abunda tayi maxa sai ihu sukeyi suna jifanta da duwatsu wasu suna Daukarta hoto suna Daukar gaba gareta

Labila tun tana kuka ahankali hartasomayi kwarai dagudu tafita dakin tayi waje khadija waya takeyi tana murmushi tace kashigo mana wlh bakowa mune kawai agidan

Yace shikenan ganinan tana kashe wayar labila tana kawowa tafada jikinta nashiga uku sahiba yazanyi

Khadija tace menene yake faruwa labila??? Wayar hannunta takunnawa khadija tace kalli mom kalli abunda ta aikata irin wannan ranar nayita hangomata Amman batajiba duba kiganie

Tadanna play dasauri Khadija takauce kanta ta anshi wayar tagoge video din Sannan tace menene amfanin haka su mutane wlh basada hankali

Sunsan sarai kallon tsiraicin wani haramunne to akanme zasu dauki wannan suna yadawa Allah kadai yasan dub ban mutanenda sukaga wannan

Labila ta share hawaye tace nibanga laifinsuba sahiba itace tayi abun fadi meyasa su sauran mata ba ayimasu hakanma??? Aikuma ba ita ce kawai maceba

Khadija tace duk dahaka baidaceba wadanda sukai hakan aisuma sunada iyaye kuma itama tanada Yaya Sam wannan abun baikamata as amu musulmai sunayiba

Amman natabbata wadanda suka yadashi musulmaine"" kiyi hakuri labila wannan kaddarace haka Allah yarubuto za ayi kidaina kukan nan Dan Allah

Labila tace dole nayi kuka sahiba kukama aiyanzu nafarashi yanxu aganinki waye zai aureni alhalin yasan abunda mom dina ta aikata kifadamun waye zai aureni tasake fashewa dawani kukan maicin rai

Bakin kufar shigowa taji ance nine zan aureki"" dasauri tataso dagajikin khadija takalli kofar falon

Cikin mamaki tace ya mukty"" kaiyagyada mata yace kwarai labila karkiyi mamakin jin furucina inhar zanyi aure aduniya tobanida wata matar faceke

Dasauri tajuya takalli khadija itama murmushine akan fuskarta tagyada mata kai alamar hakane""

Kanta tasaukar kasa ahankali ya tako zuwa gabanta""yaciro hankicif dinsa yamika mata

Tadago ahankali takalleshi girah yadaga mata cikin murmushi alamar takarba"" takarba tashare hawayenda suke kan fuskarta


Duk da haryanzu ta gagara tsaida wadanda suke saukowa taja majina tana mikamasa hankicif din tace nagode ya muktar Amman nasan bazaka iyah aurenaba


Samun waje yayi yazauna yace kinada dalilin furta hakan??? Tagyada kai nasan bakasan abunda mom dina tayiwa kanwar kaba

Dakasani na tabbata kallon arxiiki baxansamu daga wajenkaba Bakowane zai iyah auren Yar matarda ta aikata laifuka masu tarin yawa


Ciki kuwa harda kisan kai"" tatushe bakinta saboda kukan da yazomata

Muktar yayi murmushi yace nasan komai labila tunsanda sapna tadawo tasanar Dani Dan lokacinda tafadamun saceta da akayi nayarda

Amman ranarda naganta nasan bagaskiya bane shaida namatsa mata da tambaya Sannan tasanar danie

Tayihakane saboda ke dankarnace bazan aurekiba abunda batasaniba narigada nayi Nisan kiwo babu abunda zaihanani auren ki saidai idan kece kikace bakyasona

Banakuma fatan hakan idanma kikace banyimakiba nasan zan tabbata agwaurona danmuddin kikace bakyasona babu wacce zatasoni

Cewa wai bazan iyah aurenkiba saboda wannan dalilin ba hujja bace dankawai mahaifiyarka ko iyayenka suna aikata barna sai ace baza a auri yayansuba???

Allah yana fitarda rayayye daga jikin matacce yanakuma fitarda matacce dagajikin rayayye zakasamu malami masani mai tsoron Allah Amman acikin yayansa saikasamu fandararre gagare Wanda Sam baiyi halin malam dinba

Sautari kuma zakasamu wasu yan iska lalatattu fandararru saikuma Allah ya azurtasu da Yaya kamilallu saikuma ace baza a auresuba aiwannan ba hujja bace

Kaima nangaba zaka iya Haifar yara kamarsu kaima ace baza a auri nakaba yakenan

Yanisa nidai magana tagaskiya labila banason kowace mata bayanke nadade dasanarda kawarki haka inajin tsoron sanardake dannalurah bakyasona ko kallona bakyayi

Shiyasa nake Dari Dari"" nazoda kokon barana ataimaka akarbi tayin soyayyata!! Yakai karshen maganar yana kallonta""

Shiru tayi batace komaiba yace bakice komaiba nayimaki kodasauran gyara dariya tayi taruga dagudu zuwa sama

Khadija tabita dakallo tana dariya muktar yabita dakallo yana murmushin wani sanyi yakeji aransa koba komai yaudai yasauke nauyinda yake addabar xuciyarsa yanzu yanaji acikin zuciyarsa kamar yawarke daga jinyar shekara daya

Aisha✍🏼

☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠

.


PART 2⃣
32
By gentle
lady💃🏽


Yasaukarda ajiyar zuciya yana kallon khadija yace akwai bukatar inga dad Dan dawuri nakeso ayi auren nan

Khadija tace kaiya muktar inkashirya mubamu shiryaba ai """yagyara zama wanne shiri kenan??? Ninadauke maku komai.

Tace munji Amman saimun shirya wlh yace waishirin me zakuyi kayan sakawane dakuma shirye shiryen buki cikin sati kungama komai

Tace mudai ah ah kuma so akeyi ayitareda na yayansu"" muktar yace tonidai karkiyimun tsiya idan akanemeki shawara kice sati biyu kinji Kanwata duk shirinda zakuyi aikun isah gamashi
..
Tace to yace kokefa inasu sapna banji duriyarsu ba"""??? Tace sunanan kuwa Bari nasa akawosu takwalawa Zaraha u kirah ta amsa tazo dasauri Khadija tace daukomasa sapna tace to tagaidashi sannan takoma daki

Yace Yar raino akasamo maki?? Tace um um daga Niger nazoda itah kaiyagyada daidai fitowarta taduka tabashi sannan takoma yace wai yanmatana tagirma sosai inasu anwar din Zahara u ce tasake fitowa tareda su anwar""

Yadorasu akan cinyarsa"" sai kallonsu " yakeyi Suna burgeshi jiyakeyi kamar yahadesu"" inama yayansane""" yanatayi masu wasa" khadija tana kallonsu saida akasoma kiran azahar yatashi"yamika matasu yayi alwala yawuce masallaci

Takira Zahara u tadaukesu tashiga kitchen tadorah girki"" sannan tahau sama dakin lubabatu" tashiga" labila tana kwance tarungume filo saijuyi take tana murmushi"'" tanaganin khadija tarufe fuskarta da tafin hannunta""

Duka khadija ta danamata abaya tasaki Yar kara

Tace haba sahiba menene haka daxafi wlh"" khadija tace ainasani dankiji zafin nadakeki banda iskanci Yayana yana tambayarki kinwani rugowa daki me kike nufi???

Murmushi tayi tace wlh kunyarsa nakeji sahiba mezance to??? Khadija tace ra ayinki zakifada akansa mana"" tace wanne ra ayi aikema kinsan inasonsa""

Khadija tace wa badai niba yaushe kikai danie kinasonsa"" labila tace kesahiba aibasai nafadaba daga fuskata dayanayina zaki gano tatashi zaune tana fuskantar khadija tace batun yauba nake fama dasoyayyar sa sainaga kamar shibana cikin tsarin matanda yakeso

Shiyasa banason zama guri inhar yana nan dankar xuciyata takarasa makancewa Amman sonda nakeyiwa ya mukty bazai faduba

Khadija tasaki murmushi tadafata tace nasan haka dagake harshi ainagano take takenku idanu kawai nazuba maku karshe saigashi yafito fili yasanar danie kinga kitashi kiyi wanka kishirya kafin yadawo sallah

Labila taturo idanu tace tome zanyimasa kina nufin akwai maganar dazamuyi????

Sosai sahiba akwai bukatar Ku tattauna ku fuskanci juna"" labila tace nidai ah ah"

Aikuwa baki isaba aini bahakan nayiwa dad ba 😕danhaka bazakiyiwa yayanaba"" tamike taja hanunta yauzan maidawa kurah aniyarta nima zanyimaki kwalliya kamar yanda kikamun

Babu yanda labila batayiba Amman saida khadija tasata gaba tashiga wanka itakuma tayi alwala tayi sallah

Takoma tadibo abincinta data Dora tana fitowa yanashigowa da sallama"" cikin fara a ta amsa harkadawo ya muktar

Yace ah wlh yana samun wajen zama yakirata tazo tazauna Murya kasa kasa yace yazanyi naganta inason nawuce

Khadija tace yanzun kuwa zan izomaka keyarta" tamike harzata wuce yace kidaiyi mata ahankali karki wahalarmun da itah

Tana dariya tawuce tashi yayi yafita saman kujerun dasuke harabar waje yazauna yana jiranta""

Khadija koda taje labila tashirya Amman tarasa kayanda zatasaka "saida khadija tazabomata wasu kayan kantine Riga da siket sunhadu sosai tasaka tasa farararen takalma da farin hijab"

Khadija tariko hannunta sukafito taduba bataganshiba tace nasan yafita saiki karasa Amman bari nabawa Zahara u abunsha takaimaku

Labila tawuce kamar wacce kwai yafashewa aciki tafiyarda takeyi saita bada wata ma anar daban kamar tafiyar yanga takeyi""
Tunda tatunkaro wajen yafara tasbihi ga Allah yakasa dauke idonsa akanta harta zauna fuskarta tana kallon kasa "tace inawuni yaja ajiyar zuciya yana fuskantarta yace lafiya qalau yagidan

Cen kasan makoshi ta amsa saikuma shiru yabiyo baya nayan dakiku muktar yakatse shirun tahanyar magana

Labila yakirah sunanta ta amsa batareda tadagoba"" yacigaba zansake gabatarda kaina awajenki magana tagaskiya maganar aure takawoni ba wasaba

Nadade ina jinyar sonki acikin zuciyata saiyau nasamu damar saukeshi Amman banji tabakinkiba shinnayi maki??? Shiru tayi """ yace eh ko ah ah yakamata ki amsamun tambayar nan

Dankarki cutarda kanki alkawarinda kuka daukarwa kanku kumanta dashi kifadamun ra ayinki nasan kumata kunada naku ra ayin tayiyu banacikin jerin mazajenda kikeso ki aurah

Naga mata wata zatace tafison fari wata baki wata maitsayi wata guntu wata maidogon hanci watakuma tafison mai gutsurarren hanci wata siriri watakuma tafison maikiba toke wanne kikeso aciki???

Cikin jinkunya tace Wanda yatara dukkanin abunda kakedasu"" bakinsa harkunne yace kenan ankarbi kokon barana???

Tace tunkafin makaroka akabaka"" yanxu shaidamaka nekawai akayi muktar baisan sanda yafurta alhamdulillah ba jiyakeyi kamar ana shawagi dashi saiwani kallo yake jifan labila dashi maikashe jiki

Zahara u ce tayimasu sallama ta ajemasu kayansha sannan takoma cikin gida "" labila haryanzun kunyar muktar takeji sunfara fira jefi Jefi Amman yawan maganar duk muktar keyi Dan batacewa komai

**-***---**---**---***-

Tafe suke cikin mota suna tafiya Wanda yake daya mazaunin yayi shiru yabuga tagumie daganinshi abun duniya yadameshi

Bayan motar wata matashiyar yarinyace zaune alamu sun nuna tana dauke dakaramin ciki danyadan taso yakara mata kyau farace Amman basosaiba

Mazaunin driver kuwa wani kyakkyawan saurayine mai kamada muktar yanayinsu iri dayane saidai shi yanada dan duhu sosai Sabanin muktar dayake fari

Amman dakagansu babu makawa zakace sunhada jini daya suna shiga garin kano dattijon dayabuga tagumi shiyasomayiwa maitukin kwatance

Harsuka kai unguwar saidai gabadaya komai yabace masa sukatsaya yafito yayita yandube dube Amman baigane komaiba

Matashinne yafito yace Abba idan bazaka ganeba muyi tambaya mana yasunan maigidan"??? Dattijon yayi shiru daga bisanie yace malam garba sunansa"

Inajin nan ne kawai sanadin gine gine da akai dahanyoyi wajen yabace mun" saurayin yace bari natambaya gawani cen zaishiga gida"

Dasauri yakarasa wajensa yana masa sallama hafis yawaigo yana kallonsa aransa yace wannan kamar muktar??? Saurayin yabashi hannu suka gaisa yace Dan Allah tambaya mukeyi

Hafiz yace Allah yasa nasani"" saurayi yanisa yace gidan wani malam garba"" Hafiz yayi shiru daga bisani yace akwai masu suna malam garba dayawa a unguwar nan saidai kafadamun sana arsa

Yace gaskiya bansan sana arsaba Amman yanada yaro muktar Hafiz yace haka kam naga kunyi kamada muktar sosai kamafi yanayi da Khadija""

Saurayin yayi murmushi yace yayanane ai nisunana faruq wancen mahaifin mune yayi nuni da dattijonda yake kishingide jikin mota yana jiransa

Hafiz yace Allah sarki kunbaro gidan baya kadan" faruq yace kozakadan taimaka kakaimu gidan??? Yace aibadamuwa bari nadauko mota Dan akwai Yar tafiya kadan wannan gidanane

Faruq yayita godiya Hafiz yace bakomai ai yashiga gidan yadauko motarsa yashiga gaba faruq yaja tashi yabi bayanshi

Aisha✍🏼

☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




PART 2⃣
33
By gentle
lady💃🏽



Yana tafe sunabiye dashi dattijonan Kuwa kirjinsa ya tsananta bugawa fatanshi daya yayi arba da matarsa fateema Allah yasa zata saurareshi tayarda da nadamarda yayi tunda ba laifinsa bane...

Hawaye suka zubomasa ya kaikaice idonsa yashare faruq yana lura dashi harsuka kai gidan"" Hafiz yatsaida motarsa sannan yafito suma suka fito yace ga gidan nan Amman bana tunanin Malam yana gida

Dattijon yace Dan samari kataimaka kayimana sallama dashi " Hafiz yace to sannan yakara kofar gidan yasoma sallama sulaiman ne yafito yana amsa sallamar

Yana ganinsa yasaki fara a yace Hafiz waidama Kaine shine katsaya waje kamar wani bako"" Hafiz yace aikamar shine yabashi hannu suka gaisa yana kallon bayansa yace tare kake dabaki

Amman wancen yayi kamada muktar"" Hafiz yace narigaka fadar haka wajen malam sukaxo akwai bukatar suganshi

Sulaiman yace yana kasuwa wlh kasan baicika zama gidaba Amman barinakirashi yayi maganar yana Ciro wayarsa cikin aljihu yakamo lanbar yadanna Kira

Ringing biyu tayi akadaga yagaidashi sannan yafadamashi yayi bakie"" yace suwaye??? Sulaiman yace gaskiya bansansuba Amman alamu sun nuna sunyi doguwar tafiya""

Yace shikenan gashinan zuwa"" yace shikenan yakashe wayar" yace kukarasa ciki bari na karbo key yakoma cikin gida yadauko key tareda tabarma yadawo"" zaibude dakin" dattijon yace kashnfida mana nan akwai inuwa"" yafi iska...

Sulaiman yashinfida masu suka zauna yadibo masuruwa Hafiz yayi masu sallama yawuce gidan hajiya

Baijima dawuce waba malam garba yadawo tunkafin yayi fkng din Babur dinsa yashaida Muhammad wani takaici yakamashi

Yasauko saman baburdin yayi hanyar gida Muhammad yataso dasauri yatareshi mugun kallo yawatsamasa yace lafiya malam

Muhammad yace Dan Allah kayi hakuri Yaya kasaurari abunda nazodashi malam garba yace mexan saurara mezaka fadamun???
.
Wlh Dana San Kaine dabazan zogidan nanba aikin banza aikin wofi mezakazo kaimana komun fadamaka munada bukatarka??/

Murya ya Marairaice yace kayi hakuri Yaya wlh duk abunda yafaru balaifina bane kasaurari mezan fadamaka idan harkaji inada laifi nayarda kayankemun duk hukuncinda kaga yadace danie..

Yakatse masa hanzari tahanyar dagamasa hannu yace babu amfanin saurarenka mezaka fadamun Wanda bansaniba ??? Babu amfanin jinkomai
Daga bakinka burinka yacika dama abunda yasa ka aureta kenan
.babu wata dangantaka atsakaninmu domin wacce tahada tabarmana duniyar danhaka ka gaggauta barin kofar gidan nan banason ganinka yakai karshen maganar hawaye yana saukowa daga idonsa yasa gefen hannunsa yashare yayi cikin gidan

Muhammad baya baya yayi yafadi dabas yadafe kansa wani kuka yafashe dashi kamar Karamin yaro sunan fateema kawai yake kirah fateema tatafi tabarshi.. Rukayya kin cuceni Allah ya isa tsakanina dake bazan taba yafemakiba .

Kinyimun cutarda harna mutu bazan mantaba Allah yawulakan taki kamar yanda kikamun"" faruq bayason ganin mahaifinsu cikin damuwa Dan sanadin haka yahadu dahawan Jinie yakalli matarsa yace tashi kishiga ciki ...

Bamusu tamike tashiga yakalli sulaiman yace kakaini wajen kawu kai yagyada masa sukashiga gidan Inna tana tsakar gida tunsanda malam yashigo gidan taga halinda yake ciki tayi tsaye sororo saiga matar faruq tashigo dasallama ta amsa jiki sanyaye saiga su faruq sunshigo

Inna saikallonsa take baki sake yaduka yagaida ita ta amsa murya sake yace Ina kawu yake ??? Dahannu tanuna masa dakin

Yamike yashiga da sallama malam yana zaune yajuyo daniyar magana bakinsa yakafe dasauri yamike tsaye yana kallonsa

Yaja hannunsa zuwa waje yana tattaba fuskarsa yace ikon Allah Amman kai Dan fateema neko??? Faruq hawaye suka saukomasa yarungume kawunsa yana kuka

Malam garba bakinsa harrawa yake yace dama fateema tanada wani yaron ayola Amman bata sanar daniba iko sai Allah sannu yaro.


Faruq yace kawu kayi hakuri kasaurari abunda abbana zaisanar dakai wlh babu karya aciki kuma bashida laifi kokadan sanadin rashin mom harciwon zuciya yakamashi

Tunsanda yasan gaskiyar abunda yayima mom yadaina cin komai kullum kuka likita yashaidamana muddin baiyi ahankaliba zuciyarsa gab take dabugawa nikuma banason murasa mahaifinmu shikadai muke dashi yanxu

Karshima murasashi kamar yanda mukarasa mom malam garba yayi shiru daga bisani yace muje suka koma wajen koda suka fita harya suma faruq dagudu yayi kansa yana jijjigarsa malam garba Yakoma gidan dasauri yadibo ruwa yadawo yashafa masa"" Amman ko gezau dole aka kwasa sai asiviti .

Suna cikin mota anashafa masa ruwa cikin sa a shedarsa tadawo yabude idonsa ahankali malam garbane kusa dashi cikin kuka yace malam Dan Allah kasaurareni kayafemun nasan laifinane wannan

Hannunsa yarike yace kakwantarda hankalinka kaga bakada lafiya "" Muhammad yace ina Dana muktar??/

Malam yace baya nan Amman yanxun zankirashi "" yace kataimaka kakiramunshi koshi naganie naji sauki araina

Suna kaiwa hospital akabashi gado akajonamasa Karin ruwa""da allurar barci bawani jimawa barci yadaukeshi

Malam yace Suleiman yakira muktar danshi yabar wayar agida yace to yakamo lambar yadanna kirah

Muktar suna tsaka dafiransu ta soyayya kirah yashigo wayarsa kamar baxai daukaba saida labila taimasa magana """ bayason yakatse firar tasu tanayimashi dadi

Badan yasoba yadaga saiyaga sulaiman yadauka da sallama sulaiman ya amsa yace malam nezaiyi magana dakai

Muktar yace tobashi yamikawa malam yakarba yace kana ina muktar?? Kansa yadan Sosa yace kawu bana gari inagidan sapna

Malam yace ayya lafiya daiko??? Yace kalau"" malam yace muktar" ya amsa yace kayisauri kazo ga mahaifinku yazo

Gabansane yabada rasss nan take idanuwansa suka rikide saboda bacin rai yace mezanzo inyimasa kawu yayi abunda yakawoshi yakoma kafadamasa bamuda bukatarsa acikin ruwarmu

Malam yace karkayi hka Mahaifinkane musaurari abunda yazodashi gamunan asiviti sanadin Sanar da shi rasuwar mahaifiyarku yahaifarmasa datashin ciwonsa

Muktar yace Allah yasauwake kawu Amman babu inda zanje banason ganinsa shekara nawa bainememuba saiyanzu akan me

Malam yace naji bazaici darajar mahaifiba kazo Amman aikazo kodan saboda kaninka yamikawa faruq wayar

Murya narawa yace ya muktar" cikin farinciki yace faruq Kaine??? Kaiyagyada yace nine Yaya Dan Allah kazo" baima karasa fadaba yace ganinan zuwa yakashe wayar yana kallon labila da murmushi yace Dan uwanane yaxo tareda mahaifinmu zanwuce bari nafadawa sapna

Taresuka shiga gidan khadija hartagama abinci tasheka wanka tana jerah abincin sukashigo"" tace harkayi me ya muktar???

Yana murmushi yace kano zantafi faruq dinmune yaxo tareda Abba khadija tace dagaske Dan Allah nima zanbika

Yace ah ah taya zakibini alhalin bakisanar da dady ba" ta marairaice fuska tace sainakirashi awaya ai

Yace karkifara haka kibarsa saiyadawo hankali kwance kisanar dashi saigobe kije Amman badadi kikirashi kilanta aikima yayimasa yawa kisake jagula masa lissafi fita indai bata dole bace karkigwada tambayarsa tawaya kinji maza basason haka Kaita gyada tace nagode Yayana kagaidashi to

Murmushi yayi yace kokefa kinga gobe saikizo ta gyada kai yakalli labila wacce shikawai take kallo suka hada ido tasanne kanta kasa tana murda yan yatsunta yace saina dawo ko takasan ido take kallonsa yayimasu sallama yawuce yashiga motarsa yana kallon labila tajikin madubi tana dagamasa hannu yasaki murmushi akabude masa kofar gidan yawuce

Aisha✍🏼

☠ *HATSABIBIN BOKA!!.*☠




PART 2⃣
34-35
By gentle
Lady💃🏽



Gudu yakeyi kamar Wanda zaitashi sama farinciki fal ransa Dan uwa maidadi kusan kullum saiyayi mafarkin faruq dinsu cikin mintunan da basuwuce arba in ba yakai kano kaitsaye khalifa hospital yawuce danyasan sunacen saida ya isah yakirah sulaiman yace gashima yana ganinsa danshi yana waje

Muktar yatsaida motar sannan yafito yabawa sulaiman hannu suka gaisa sannan suka wuce dakin"" dasallama sukashiga faruq dasauri yamike bakinsa harkunne

Muktar yakarasa wajensa suka rungume juna saisuka fashe dakuka maiban tausayi " malam shima hawayen yaji suna saukomasa.

Sunjima suna kuka daga bisanie muktar yashare hawayensa yadago faruq yana murmushi yace ya isa haka kar kanka yayi ciwo yahau share masa hawaye jisukeyi kamar suhade junansu.

Hannunsa muktar yaja suka fita waje saman wani dakali suka zauna"" muktar yace ya hanya??? Faruq yace alhamdulillah""

Amman kunsha tafiya faruq"" nidanaje garinku aikoda nakai kasa zuwa ko ina nayi"" faruq yace kana nufin kaje yola bayan Barin Ku cen??

Gira yadaga alamar ah " kawu dasauran yan uwan mom basusan tanada wani yaron acenba saini kawai nasani bayan nagirma nakoma yola datambaya harnagane gidan

Saidai duk wanda natambaya kai saiyace baisaniba danaje wajen dad cemun yai bashida yaro kodaya aduniya matarsa bata taba haihuwaba taya zance ina Neman dansa faruq

Yanisa kwanana hudu yola ina yawon nemanka karshe dole nahakura nadawo Amman bantaba fadawa kowaba sai sapna

Faruq yace wayekuma sapna ko matarka??? Kaiyagirgiza yace nibanyi aureba" yace toya kakeda itah??? Yana murmushi yace kanwatace

Nasan bazaka taba iyah tuna kamannin mahaifiyarmuba kasani khadija babu abunda tarago nakamanninta dazaran kaganta kaga mom yanxun ma daga gidanta nafito

Faruq yayi shiru daga bisanie yace nisam bangane me kake fadaba kace kanwarka kuma tana kama da Mamana to taya hakan taka sance!!!!!!
Muktar yace kanwar kace bayan munbaro yola akahaifeta" yanxu tayi aure yayanta biyar tayi tagwaye yanzu yan uku ne da itah

Hawayen farin ciki suka saukomasa yace kenan maman

Please Login or Register in order to submit comment