Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gudu cikin gidan dai-dai lokacin kuma su Afaf suka fara daga baccin da suka fara domin duk da wuri suke bacci.
Car key ya ɗauka ya fito da sauri Mami tace "Ina zaka at this time?" Bai ko kalleta ba ya nufi wajan ɗaya daga cikin motocin sa ya shiga key yay mata ya fita da gudu tare da barin estate ɗin, kuka Didi tace "Bukari ka kawo masifar duniya gidanka" cikin damuwa Ummi tace "Didi Aljanu ne da Yarinyar wallahi kuma sune suka tashi" wani zaro ido waje Didi tayi tace "Muhammadur Rasulullah s.a.w shine ke kuwa kikai min shiru itana da surutu yau na shiga wallahi gidan zan bari" juyawa Mami tayi ta shige ciki Ummi ba haka da gudu Didi tabi bayansu har zaninta na faɗuwa.

Akeem kuwa yana fitowa kai tsaye motarsa ya nufa idanunsa a Lumshe ko ganin gabansa ba yayi, wani irin zafi da tafasa zcuiyarsa ke masa, yana shiga motar ya jata da gudu bayan ya danna wani hargitsastsan horn da dauri Isa ya tashi daga baccin da yake ya buɗe masa gate fita yay da motar yana ƙara gudun motar tafiya yay mai nisan gaske har yabar gaba ɗaya cikin Rail way ɗin kafin ya nemi hanya yay parking motar, kansa ya kifa akan string motar yana sauke wani zazzafan numfashi jikinsa duk rawa yake amma har kawo lokacin fuskarsa bata nuna damuwar da yake ciki ba sai idanunsa kawai da suka sauya kala.
Akeela kam gudu kawai take tana bin sahun motar Akeem tun tana gudu kaɗan har ta fara mai yawa, kasancewa gudun ba nata bane na Iskane yasa itama ta fice daga cikin Rail way ɗin,
Akeem na zaune cikin motar yana sauke numfashi a hankali ya ɗaga kansa dai-dai lokacin da Akeela tazo ta gaban motarsu ta shige, bayanta yabi da kallo yana ganin yadda take gudu tamkar mahaukaciya tun yana iya ganinta har ta ɓace masa da gani, taɓe bakinsa yay a hankali yay baya tare da kwanciya a jikin kujerar motar yana maida numfashi tare da dafe kansa wanda matsanancin harba masa.
Duk inda Abbu yake tunanin ganin Akeela ya duba amma babu ita tashin hankalin mara misaltuwa ya sauka akan fuskarsa, yasan Akeem tun inda yake sai kula da kansa Amma Akeela waye ta sani a wannan garin? Musamman Wannan hargitsastsiyar unguwar tasu, jiki babu ƙauri ya koma gida har wayewar gari basu runtsa ba,Didi data rufe idanunta zata buɗe da sauri tana faɗin "Muhammadur Rasulullah s.a.w" washe gari wajan ƙarfe 8 na safe lokacin tuni Abbu ya gama bada cigiyar Akeela both side t.v Redio, a hankali motar Akeem take shigowa cikin estate kai tsaye kuma gate ɗin gidan su ya nufa yana zuwa Isa ya buɗe mata gate ya shiga tun kafin ya fito daga motar cikin ɓacin rai da kuma tashin hankali Abbu ya nufi kan Akeem gadan gadan domin rashin Akeela dai-dai yake da rasa rayuwarsa....



Hhhhh Akeem you're too selfish baka da kirki ko kaɗan😒



*TSINTACCIYA*
NRML GRP ₦300
VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING
0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616

*NOTE*
NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾‍♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.


*FITATTU HUƊU🔥*

BAƘAR FATA
AutaR ManyA

DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo

SULTAAN
Mss flower

gaba ɗaya ₦800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218



*SARAUTAR MARUBUTA*
*🌈TSINTACCIYA🌈*

NIMCYLUV
FITATTU HUƊU🔥

Writer of
Abu Maleek
Sirrin mu
Uncle ne
Kwaila ce
The new emir
Jidda
Juyayi
Izzar so
Moon
Lamrat
Raino ne sila
Ranar Aure na
Ƙaddarar mace
Ashe ƴar babata ce
TSINTACCIYA


http://wa.me/+2348119237616
MASU SIYA SUYI MGN👆🏾

EPISODE1️⃣6️⃣-1️⃣7️⃣
Yana zuwa bakin ƙofar ya tsaya yana jiran fitowar Akeem, gently ya buɗe ƙofar ya fito idanunsa a lumshe ga yadda jijiyoyin kansa suke a mimmiƙewa fuskarsa tayi jajirrr da ita alamun har yanzu yana cikin ɓacin rai.
Ganin Akeem cikin wannan halin wanda bai taɓa ganinsa a ciki ba yay saurin faɗin "Dr" idanuna da suke a Lumshe ya buɗe tare da sauke ganinsa akan fuskar Abbu,wani irin bugawa zuciyar Abbu tayi saboda wani irin jaaa da idanun Akeem sukai har wani ruwa suke fitarwa. Muryar sa na rawa yace "what... what happened to Akeem?" Lumshe idanunsa yay kana ya buɗe kamar wanda baya son yin magana ya buɗe baki da ƙyar yace "noting" yana faɗin hakan ya nufi shiga cikin gidan da idanu kawai Abbu ya bisa yana mamakin baƙar zuciya irinta Akeem. Girgiza kai kawai yay tare da nufar cikin gidan kai tsaye part ɗinsa ya nufa, Akeem na shiga Amani na ganinsa ta miƙe tana faɗin "Abbie na" bai ko kalli inda take ba sai hannu daya sanya yama ture ta kai tsaye upstairs ya nufa yana dafe kansa yana jin yadda Amani ke kuka amma yau banza da ita, Didi dake zaune tayi saurin faɗin "Au! Yarinya ba sai dai kiyi tayiwa Ubanki istigifari ba, daɗin abin ko kashe ki yay shine ya haifa a toh" Aleema ce ta kama hannunta tana rarrashinta kasancewar weekend ne duk suna gida. Akeem na shiga side ɗinsa rest room ya nufa cire farar jallabiyar jikinsa yay tare da saƙale ta a hanger, fure fresh skin ɗinsa ta bayyana wani irin ƙwantaccen baƙin gashi ne a saman mararsa mai matuƙar ɗaukan hankali jikinsa a sanyaye ya nufi cikin tube tare da shigewa ciki, wani irin sauke numfashi yay a hankali kuma ya ƙara nutsewa cikin ruwan dake cike har bakin tube ɗin, zafin da zuciyarsa ke masa ya sanya gaba ɗaya yama mance a cikin ruwa yake, idan ya tuna irin faɗan da Ummi da Abbu sukai masa sai yaji wani abu ya tsaya masa a ƙirjin, cikin ficewar hayyaci da kuma zallar damuwar dake ransa ya ƙara nutsa kansa cikin ruwan a hankali kuma ruwan ya fara shige masa cikin baki da hanci.

A hankali wata baƙar mota mai ƙirar Audi RS5 ta fara shigowa ciki Nasarawa daga farko farkon Nasarawa harya gifta sai kuma ya dawo baya a hankali yana zare baƙin glasses ɗin dake idanunsa, saurayi ne ɗan kimanin shekaru 27 yana sanye da wani farin voyal wanda yay masa kyau sosai kasancewar sa farin bafulatani kana ganinsa Kasan cewar kuɗi sun zauna masa, a hankali yake tafiya da motar zuwa baya kasancewar shike driving ɗin ganin hakan yasa wanda ke kusa dashi yace "Ajmal me kake haka ne?"shiru Ajmal ɗin yay domin baya jin akwai abinda zai iya faɗa, a hankali ya gama tsayar da motar tare da buɗe murfin motar ya fito ganin hakan yasa Karim yay saurin fitowa yana faɗin "wallahi kaifa ba hankali gare ka ba, kana ganin aikin dake gabanmu dole ne a wannan satin mu samu mu shawo hankali duk raguwar jama'ar" ina Ajmal baya gane yaran domin tuni idanunsa suka sauka akan fuskar Akeela dake kwance a ƙasan wata bishiya wallahi wallahi a wannan lokacin duk wanda yaga Akeela dole zuciyarsa ta buga domin ba zaka taɓa cewa ƴar hausawa bace, tana kwance kanta na zubda jini saboda wata muguwar faɗuwa da tayi gaba ɗaya kayan baccin dake jikinta sunyi wani bala'in yin datti gashinta ya wargatse yay ɗai ɗai, tsaye Ajmal yay akan Akeela yana jin zuciyarsa na bugawa, a hankali kuma ya tsuguna a gabanta dai-dai lokacin da Karim yake ƙarasuwa wajan cikin sauri yace "wai Ajmal meke damunka ne? Baka tsoran abin cutarwa ne? Kilama ba mutum bace Aljana ce, ina ka taɓa ganin mace mai gashin wannan?" Banza Ajmal yay masa domin yadda idanunsa suka sauka akan fuskarta yasa baya fahimtar komai dukkan wani abu na kansa sai da ya kunce, hannunsa ya miƙa tare da tattare sumar data rufe mata fuska cikin sauri ya rufe idanunsa yana faɗin "Ohh God" Karim yay saurin faɗin "is she died?" Girgiza masa kai kawai Ajmal yay yana ƙoƙarin sanya hannunsa ya ɗauke ta Abbu dake ƙarasuwa wajan yace "Akeela! Allahamdulillah"
Da sauri ya sanya hannunsa ya ɗauke ta tare da kallon Ajmal yace "thank you son, wallahi tun jiya mukai missed nata yanzu na ƙara fitowa ne, kamar daga sama na hangeka ji nai kawai ina son ganin Meke faruwa cikin ikon Allah kuma naga Akeela thank you" jinjina kai kawai Ajmal yay yana shafa wuyansa sosai ya gane Abbu amma shi Abbu sam bai gane waye Ajmal ba, kamar bazai magana ba sai kuma yace "Dad! A nan kuke ne?" Kallon Ajmal Abbu yay yana karantarsa sai kuma yace "eh cikin Railway quarters no 112" idanunsa akan fuskar Akeela yace "ok Thank you" yana faɗin hakan ya nufi cikin motar tare da zama wajan driving ba ganin hakan yasa Karim shima ya shiga cikin motar da gudu Ajmal yaja suka bar wajan, mai makon yaje inda zashi sai kawai ya juya kan motar ya nufi hanyar gida da Mamaki Karim yace "wai Ajmal Meke damun ka ne?" Cikin ɓacin rai Ajmal yace "ban sani ba, banza shege munafuki kawai haba" ya faɗa cikin ɓacin rai yana ƙara sharara gudu.
Abbu shima cikin farin ciki ya nufi motarsa bai yadda ya ajjiye ta a back seat ba a nan saman jikinsa ya barta key yaywa motar ya juya zuwa gida tun a hanya ya kira number Ummi da sauri tai picking call ɗin tana faɗin "Something news?" Cikin ƙasa da murya yace "I've seen her Ummi on my way yanzu" Murmushi tayi tace "Allahamdulillah"

A wahala Akeem ya ɗago kansa daga cikin ruwan yana sauke wahalallan numfashi a hankali kuma ya buɗe idanunsa da sukai wani mahaukacin ja, ya jima cikin ruwan kafin ya fito ya ɗauki bathrobe ya sanya a jikinsa, ruwa na zuba a jikinsa ya fito kai tsaye ya nufi cikin wani special bedroom ɗinsa Yana zuwa ya rufe ƙofar da key, derect bed ya nufa yana zuwa ya faɗa tare da jan duvet ya rufe jikinsa tass domin wani mugun bacci ya keji, kamar yadda ya saba haka yanzu ma ya jawo pillow ya rungome a tsakanin ƙirjinsa yana sauke numfashi a haka bacci ya ɗauke sa da tunanin yadda zai rama abinda akai masa akan wannan yarinyar.

Ummi da Didi ne suka miƙe lokacin da Abbu ya shigo da Akeela a hannunsa, kai tsaye part ɗin su Aleema ya nufa da ita, Ummi na biye da shi Mami ko motsawa ba tayi ba idanunta akan cineme, yana zuwa su Afaf suka miƙe fuskarsu ɗauke da farin ciki, kwantar da ita yay cikin nutsuwa Ummi tace "bari na duba ta" gefe Abbu ya koma yana jin kamar ya kori kowa ya jata jikinsa ya rungome ya lallasheta da kansa amma no way ahlinsa na wajan dole yaja da baya da yaga yana neman zama wani uncontrol sai kawai ya fice daga part ɗin, a hankali Ummi ta zauna idanunta akan Akeela tace "Afaf jeki kawon warm water a bowl with towel" "ok Ummi" bathroom tayi ta shiga haɗa ruwan zafin kana ta fito ɗauke da towel ɗin "drop it and leave and you too Aleema" ficewa duk sukai gently Ummi ta zamewa Akeela rigar jikinta babu ko bra a jikinta cikin tausayin ta Ummi ta shiga goge mata Jikinta da ruwan zafin, sosai ta kasa mata Jikinta ta shafe ta da robe kana ta sauya mata kaya zuwa Sleeve Bodycon mai sauƙin nauyi saboda zafi ake da alama akwai ƙaramin hadari a ƙasa, kwantar da ita tayi ta rufe da duvet gudun a.c ta ƙaro mata ba mai cutarwa, fuskarta tabi da kallo ganin yadda take sauke ajjiyar zuciya a jajjere, fita tayi daga bedroom ɗin a Parlo ta samu su Afaf ɗin suna buga game ficewa tayi daga part ɗin nasu baki ɗaya.
Ummi na fita Akeela tai wani irin juyi tare da buɗe idanunta abinda basu sani ba idanunta biyu kawai har yanzu mutanan na kanta ne irin aljanun nan ne masu mugun abu wanda sai ansha wahala kafin suyi magana ma. Parlo Ummi ta dawo kusa da Mami ta zauna ba tare da tace komai ba, a hankali Abbu yake tafiya cikin tafkeken bedroom ɗinsa hannunsa goye a bayansa sai numfashi yake fitarwa, gaba ɗaya yama rasa yaya zai yi baya jin daɗin komai burinsa kawai yaga fuskar Akeela, wani murmushi yay yana jin daɗi domin sai yanzu ya tuna da Ƙofar dake bedroom ɗinsa wacce kai tsaye hanyar tayi har parlon su Aleema, jikinsa na rawa ya buɗe ƙofar tare da fita su Afaf na tsaka da buga game su kaga Abbu kamar daga sama kallonsu yay yace "bari na mata magani" jinjina kai kawai sukai, bedroom ɗinsu ya nufa jikinsa har wani tsuma yake tana zaune ta tura kanta cikin tsakiyar cinyoyinta, ƙarasawa yay tare da faɗin "Babyn Abbunta zo nan gani nazo rarrashin ki" shiru bata motsa ba hakan yasa ya ƙarasa inda take yana zuwa ya jawota jikinsa yana shafa kanta tare da faɗin "Babyna" jajayen idanunta ta ɗaga ta kallesa cikin wata kakkausar murya tace "Abbu Akeem" zuciyar Abbu ce ta buga da ƙarfi cikin damuwa yace "me Akeem zai maki" kuka ta sanya masa ko kuma aljanun suka sanya masa cikin wata iriyar Murya mara daɗin saurara tace "Akeem muke son gani Abbu" sai a lokacin Abbu ya fahimci ba ita take Maganar ba, shafa kanta kawai yay yana faɗin "sorry Babyna kina shan wahala ko? Dana aureki zan bar ƙasar dake" wani irin kallo tayi masa tace "kai ma baka da lafiya Abbu Meye Wannan a jikinka?" Bai tsaye jin zan canta ba ya ɗura bakinsa a kunnanta ya shiga yi mata addu'a, miƙa ta fara yi kafin kuma a hankali jikinta ya saki bacci mai nauyi ya ɗauke ta, Murmushi Yay yace "Babyna zaki sanya zuciyata bugawa idan kina kiran sunan Akeem, Tabbas ni kaɗai zaki so nasan Akeem bai taɓa cewa yana sonki amma yadda kike da mugun kyan nan masu kawo maki hari suna da yawa, ni kawai zaki so zaki zauna dashi, zan koyar dake zallar so da kuma ƙauna ta Akeem kuma duk yadda za'ai a watan nan sai na tura shi Germany zai nesa dake sai yay Shekaru masu yawa lokacin tuni kin zama tawa zai dawo" ya faɗa yana shafa kanta a hankali ya sumbaci goshinta..


*Singapore*
Khoo Teck Puat Hospital
A hankali motar tai parking Meema ce a gaba sai mahaifinta President Ahmad Adil yana Cikin Wata dakakkiyar shadda dark blue mai kyau sai sheƙi yake, yayinda ita kuma take cikin wata milk ɗin abaya da red ɗin Stones tayi rolling kanta da vail tayi kyau sosai, hannunta riƙe da waya ga wasu manyan guards kai tsaye cikin female sugical world suka nufa shiru asibitin saboda asibiti ne na masu kuɗi babu hayaniya ko kaɗan, cikin sauri Meema ta buɗe ƙofar office ɗin Dr ɗin ba tare dako permission ba, yana zaune yana duba wasu files Meema ta shiga tana faɗin "Dr what happened i saw your miss call" Murmushi yay yace "Na kira na faɗa maki yau za'a buɗe fuskar ƙaninki" wani daɗi taji da sauri ta rungome Dad tace "Dad bana faɗa maka ba" hannunta ya riƙe yace "ok be careful" Miƙewa Dr yay cikin so much respect ya shiga gaisar da Dad kafin yace "follow me" binsa sukai a baya har suka nufi wani room 11 buɗe ƙofar akai Dr na gaba Meema na baya sai Dad, cikin sauri ta zame hannunta ta nufi inda yake a kwance da kayan marasa lafiya Murmushi tayi tana riƙe hannunsa, ɗumin hannunta daya ratsa tafin hannunsa yasa yay sauri riƙe hannunta domin yau gaba ɗaya ba tazo hospital ɗin ba kamar yadda ta saba, kayan aiki Dr ya ɗauko Meema jikinta har rawa yake domin ta matso ta ganshi, cikin nutsuwa Dr ya fara ware masa bandejin fuskarsa yana cirewa, bakinsa ne ya fara bayyana mai ɗauke da jajayen laɓɓa, sai kuma hancinsa a haka har aka gama buɗe masa fuskar, idanunsa a rufe ruff fuskar Abbu kwance a saman nashi fuskar Dr ne yace "Congratulations now open your eyes" slowly ya shiga buɗe idanunsa kai tsaye ya sauke ganinsa akan fuskar Meema babu ko kifta idanu, cikin farin ciki Meema tace "Bro na" shiru yay mata bai ce mata komai ba ganin hakan yasa ta kwaɓe fuska tace "why baya magana?" "Ai sai ya koyi komai ba, kinga aiki ya sameki" Dad kam tunda aka buɗe fuskarsa yaji gabansa ya faɗi sosai ya san me fuskar amma mene haɗin Meema da wannan gske har ta sanya aka sawa wani ita? hannunsa Meema ta kama tace "I'm your sister" cikin kwaikwayon Abinda ta faɗa yace "I'm your sister" wani irin Murmushi Meema tayi tace "A'a ba haka za kace ba" kallon Dad tayi tace "Dad his name please" buɗe baki Abbu yay yace "Asheer" "Wow! Nice name" Meema ta faɗa tana faɗin "as from today sunanka Asheer amma zanna ce maka Bro ni kuma kace Sister" dry Dr yay yace "tab kina nufin a yanzu duk zaki koya masa komai? Mudai nan kafin ku tafi zamu kuya masa wanka,Sallah, cin abinci komai" Asheer kuwa tunda ya ɗura idanunsa akan Meema yaƙi ɗaukewa domin tsoran kallon mutanan wajan ma yake, miƙewa tayi zata ɗauko masa mirror da sauri ya riƙe hannunta yana juya idanunsa, da ƙyar dai ya sake ta lokacin da yaga kansa a madubi kansa ne yay wani irin sarawa da sauri ya saki madubin a ƙasa ji kake tasssss ya fashe a ƙasa cikin sauri kuma cike da tsoran abinda yayi ya ɓoye fuskarsa a bayan Meema..


Today is Monday yau Akeem ya tashi da azumin Litinin da Alhamis kamar yadda ya saba, rabonsa da ganin Akeela wajan sati guda kenan, domin ko zama yanzu ba yayi a Parlo, a hankali ya fito daga motarsa lokacin ana ta kiran sallar magrib kai tsaye pampo ya nufa tare da ɗaura alwala, ko cikin gida bai shiga ba ya nufi cikin masjid ɗin, lokacin daya isa ana jiran zuwan liman amma Shiru ganin an rasa wanda zai ja sallar sai kawai yay gaba tare da tada kabbara, nutsuwa kowa yay a hankali cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗin gaske ya fara fidda kira'a yana fidda makarijil huruf, a can gida kuma Akeela na zaune domin ita sosai azumin ya wahalar da ita kuma ta saba tana yinsa ne, idanunta ta buɗe jin sautin Muryarsa ya daki kunanta rabon da taji Muryarsa haka harta mance, Miƙewa tayi saboda wani sanyi da jikinta yay a hankali ta nufi bathroom ta ɗaura alwala kana ta dawo tayi sallah ji tayi jikinta babu daɗi sai kawai ta zame hijab ɗin ta nufi bathroom, cikin sanyin jikinta ta buɗe ƙofar ba tare data rufe ba ta fara kwaɓe kayan jikinta ruwan zafi ta sakarwa kanta tana sauke ajjiyar zuciya.
Bayan an idar da sallah Akeem ya fito Abbu na bayansa a haka suka nufi gida babu kowa Parlo duk Sallah suke, part ɗinsa ya nufa Akeem kuma ji yayi yau babu abinda ya keso sama da zuma yasan kuma Didi kawai ke Shanta, part ɗin ta ya nufa a hankali ya shiga lokacin tana Sallah, wani daɗi yaji domin baya son masifar ta a yanzu, fridge ɗinta ya nufa gaba ɗaya robar zumar ya ɗauko Didi kam banda zare ido babu abinda take da taga abin bana wasa bane sai ta fara "ehem! ehem!" Ko Kallonta bai ba ya nufi waje ai da sauri tace "Assalamu alaikum" miƙewa tayi tana faɗin "Muhammadur Rasulullah s.a.w Audil sata ƙiri ƙiri Ubangiji dai yau ya nuna min ɓarawon zumata" jin tana kiran sunansa kuma ya tabbatar part ɗinsa zata bisa cikin rashin makamar yi kawai ya faɗa part ɗin su Aleema ga mamakinsa sai yaji tana faɗin "Munafikin ai na ganka" da sauri ya juya yana duban inda zai ɓoye ganin ƙofar bathroom a buɗe ya wani faɗa ciki da sauri yana murzawa ƙofar key.....

*LAST FREE PAGE'S*

😂Akeem daga nan kawai ka ƙarasawa Akeela wanka ina sane na tsaya a nan mai son ci gaba ya biya a nan na kawo ƙarshen *FREE PAGE'S*

NA BADA FREE PAGE'S DAGA 1 ZUWA 17 IYA ADALCI NAYI LITTAFIN NAN BABU TSADA NRML GRP 300 VIP 500 SHINE KAWAI, DAN ALLAH IDAN BA SIYA ZAKI BA KADA KIYI MIN MAGANA PLEASE👏🏻.

1. WACECE AKEELA?
2. WACECE MEEMA?
3. IS HE FALL IN LOVE WITH AKEELA?
4. ABBU ZAI AURI AKEELA?
5. MEYE TSAKANIN MEEMA DA ABBU?
6. MENE MAKOMAR LAYAR DA BABA RABI TA SANYAWA AKEELA?
7. ADNAN WANDA YA ZAMA ASHEER ZAI DAWO WA FAMILYN SA?
YA BATUN MUTANAN WUDIL DA GONAKIN SU? KUNA GANIN ZA'A IYA HAƊUWA TSAKANIN ASHEER DA AKEEM A WORLD SICKLE CELL AWARENESS DAY?

8. WHO WIN BETWEEN ABBU, AKEEM, ASHEER, AJMAL WAYE ZAI SAMU AKEELA A CIKIN SU???
AKWAI DRAMER AKWAI LOVE UWA UBA ROMANCE BAZAN ƁOYE MAKU BA😂 ADDINI ILIMI BABU WANDA BABU KAWAI KO FARA BIYA KUƊIN KU AYI DAKU🤗.

ƳAN NIGER SUYI MIN MGN KAI TSAYE ZAN MUSU BAYANI.

*TSINTACCIYA*
NRML GRP ₦300
VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING
0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616

*NOTE*
NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾‍♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA, VIP MUTANAN AMANA HAJIYOYI POSTING BOTH SAFE YAMMA ZA KUSA KARATU💃🏻NASAN HAR KYAUTAR KUƊI SAI KUNYI MIN.


*FITATTU HUƊU🔥*

BAƘAR FATA
AutaR ManyA

DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo

SULTAAN
Mss flower

gaba ɗaya ₦800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218



*SARAUTAR MARUBUTA*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment