Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

BUSA A MUTU
Littafi Na Biyar (5)
Part A

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Barkanmu da wannan lokacin Dafatan Muna lafiya
Ina Ma'abotA son cigaban littafin Rijiya Gaba Dubu to Albishirinku ranar Asabar Zamu dora daga inda aka tsaya Insha Allah

Marubucin yaci gaba da cewa....
LOKACIN da Sarkii Jamal wanda ke
nulkin binin yazo karshe a bayaninsa
bisa shawarar da za abi domin a ga karsher
jarumi maí kahon BUSA A MUTU sai geha dayan
Saraakunan da ke cikin dakin taron suka yi tsuruu-tsuru
suka kama kallon junansu.
Duk wanda ka kalla sai ka ga aiarmua tsananin
Tsoro a cikin fuskarsa.
tsawon yan dakiku ba a sami wanda ya kara
ce wa komai ba.
Daga can sai Sarkı Imras yai gyaraa murya ya ce,
Ya ku yan uwana- Sarakai, ku y sani cewa nayı
iyakar bincikena a cikin hallarar tsafi domin gano
hanyar dà zamu iya magance wannan matsala.
Mafitar da na samo tana da tsananin wuya kuma
na jarrabata ma amma abu ya faskara.
Ina so ku sani cewa shi ilimin tsafi :kogine mai
Tsnanin zurfin da bashi da karshe saboda haka ga
wata sabuwar shawarar da zan bamu
Wannan shawara ita ce, mu tara gaba dayan bokayennu su dukufa aikin bincike a tare
Tsawon kwana bakwai ma'ana su hada KARFI DA
KARFE wajen aikin binciken, idan aka yi hakan
tabbas za a gano wata hanya ta biyu wacce za ta fiye mana sauki
Koda Sarki Imsar yazo nan a zancensa sai fiye da
rabin sarakai da ke cikin fadar suka kamu da matukar
farin ciki, sauran
kuwa sai hankalinsu ya kara
dugunzuma fiye da ko yaushe.
Musamman ma-Sarki Huraisu wanda tunda aka
fara magana bai ce uffan ba, amma ya sunkui da kansa
kas yana tunani.
Nan take dakin ya sake hargitsewa da hayaniya
gami da musu da kace-nace tsakanin 6angaren da suka
gamsu da shawarar Sarki Imras da wWadanda basu
gamsu ba.
Ana cikin wannan hayaniya ne kawai aka ga
wani bakon boka ya shigo cikin fadar.
Shi dai wannan boka ya yi shiga ne irin ta
mutanen kasar Hindu kuma kallo daya za ka yi masa
ka san cewa jinin Hindu ne.
Ya kasance tsoho tukuf mai shekarun da lallai
sun haura dari, kuma gaba dayan gashin da ke jikinsa
fari ne sol.
Gemunsa dogo ne ya zuba har kasan cibiyarsa.
Gashin bakinsa kuma murtukeke ne ya cika fuskarsa.
Launin kayan jikin nasa koraye ne shatar kuma yana
dogara wata koriyar sanda.
Koda Sarakunan suka yi arba da wannan bakon
boka sai kowa ya cika da tsananin mamaki
da suka ga wani irin farin haske da ke tashi a jikin
musamman
bokan tamkar bai kasance mutum ba.
Da shigowar bokan cikin dakin taron sai komai
na dakin ya sauya launi ya koma kore kuma dakin ya
haskake gaba daya yadda ko allura ce ta fadi sai an
ganta.
Hatta iskar da ke kadawa a cikin dakin wacce ke
shigowa ta cikin tagogi da kofofí saida ta sauya yanayi
ya zamana cewa gaba dayar dakin ya dauki wani ifin
sanyi madaidaici mai dankaren dadi.
Take kowa ya firgita da ganin wannan boka hatta
Sarki Imsar kuwa wanda yake ganin ya kai wani
babban matsayi a harkar bokanci.
Cikin tsananin girmamawa dukkanin Sarakunan
suka mike tsaye don girmama bakon bokan kuma suka
dare aka samar masa da hanya ya wuce ta tsakiyarsu.
Tun kafin ya karaso inda karagar mulkin take
Sarki Huraisu ya mike tsaye daga kan karagarsa ya
koma gefe daya yana mai yiwa bokan nuni da ya
zauna alkan karagar tasa.
Koda ganin haka sai bakon bokan ya dubi Sarki
Huraisu ya yi murmushi ya ce, "Ya kai mai birnin
Lairuf ai babu mai zama akan wannan karaga taka face
wanda ke da gadonta. Na gode bisa wannan
girmamawa da ka bani".
Koda gama fadin hakan sai bokan ya koma gefe
daya kusa da Sarki Huraisu ya tsaya sannan ya
fuskanci gaba dayan sarakunan da ke cikin dakin ya
ce, "YA
Sarakunan wannan nahiya ku yi sani cewa
ni sunan a BOKA KIRISHNA BIN URAD.
A halin yanzu duk fadin duniya babu wani boka
mai yawan shekaruna da yawan sirrikan tsafina kuma
ina zaune ne a cikin wani kogo da ke can bayan birnin
Hindu wanda ake kira KOGON HAREMA.
Shekafata dari da sittin da uku a cikin wannan
kogo, kuma a cikinsa uwata ta haifeni. Ina fadowa
duniya mahaifiyar tawa ta mutu. Aljanu ne suka reneni
har na girma.
Tsawon shekaru dari da sittin din nan ban taba
fitowa ba daga cikin kogon Harema ba sai yau kuma
idanuna kawai na rufe, ina budewa na tsinci kaina a
gaban wannan daki da kuke wannan taro.
Ku yi sani cewa duk halin da kuke ciki bisa
fargabar mutuwar ya'yayenku duk na sani kuma idan
ba a dauki matakin gaggawa ba wannan masifa sai ta
yadu ko ina a cunya ia žamo sanadin da gaha dayan
ya'yayen sarakan duniya za su rasa rayuwarsu.
Ni kaina asalina d'an Sarki ne don haka wannan
masifa sai ta shafeni. Yanzu haka na zo mana da
mafita ne guda daya wacce ita ce kadai hanyar da
zamu bi mu tserar da duniya daga cikin wannan
mummunan tashin hankali ".
Koda boka Kirishna yazo nan a jawabinsa sai
gaba dayan Sarakunan suka kamu da tsananin farinciki
kuma kowa ya nutsu aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta
aka zubawa boka Kirishna idanu domin aji bayanin da
zai yi a kan wannan mafita da yazo da ita, musamman
Sarki Imras da Sarki Huraisu.
Boka Kirishna yai gyaran, murya sannan ya ce,
"Ya ku wadannan Sarakai ku yi sani cewa'a halin
yanzu duk duniya babu wani mahaluki da zai iya yi
mana maganin wannan masifa face wani jarumi guda
daya wanda ya kasance ma'abo cin addinin Musuiunci
ana kiransa da suna IMRAN IBN HÚZEIR.
Jarumi Imran ya kasance kyakkyawan saurayi
kuma mai matukar jarumtaka ta gaban kwatance
anan kuma yana da launin fata na wankan tarwada,
ma'ana shi ba fari bane, kuma ba baki bane kumay na
da tsawo dai-dai misali gami da kaurin jiki.
Mutum ne shi wanda baya zama a waje daya
kuma rayuwarsa gaba daya a cikin daji take fiye da
shekaru goma sha biyu da suka shude. Bai ta6a cin
nama ba ko wani abinci.dabam wanda bai kasance dan
itaciya ba ko ganye.
Kullum dare da rana a cikin farauta yake gami da
bautar Ubangijinsa.
Baya farauto kananan dabbobin daji sai manya
kuma a shekara sau uku kacal yake shiga cikin gari
daga lokacin zafi sai lokacin sanyi sai kuma lokacin
damina.
Bai damu da komai na jin dadin duniya ba. Baya
sa sutura mai kyau, baya cin abinci mai dadi, kuma
baya kwanciya akan shimfida mai taushi. Babu abinda
ya tsana sama da zalunci sannan kuma baya taimakon
mutum face ya jarrabashi ya tabbatar da cewa yana da
abubuwa uku.
Abu na farko shi ne, dole ne ya tabbatar da cewa
mutum yana da gaskiya, amana da jin kai. Babbar
matsalarmu anan ita ce bamu san a inda jaurmi Inran
yake ba a halin yanzu bare muje my riskeshi tunda ya
kasance matafiyi wanda baya žama a waje daya.
Na yi iya bincikena na kasa gano inda yake a
yanzu saboda shi tsafi baya tasiri a kansa. Shi ac kadai
wanda zai iya shiga cikin dajin Kirzufa ya kamo
Muraisu kuma ya fito a raye."
Sa'adda boka Kirishna yazo dai-dai nan a
zancensa sai kankalin kowa ya dugunzuma aka yi shiru
ana tunani da zullumi.
Daga can sai Sarki Huraisu ya dago kai ya dubi
boka Kirishna cikin tsananin mamaki ya ce, "To yanzu
ta ya ya ke nan za mu ga jarumi Imran har mu nemi
taimakonsa alhalin bamu san inda zamu je mu ganshi
ba. Sannan kuma abu ne mawuyaci mu iya kiyaye
jarrabawar da zai yi mana?"
Koda jin wannan batu sai boka Kirishna yai
ajiyar zuciya sannan ya ce, "Akwai hanyar da za a bi a
tafi farautar jarumi. Hanyar ita ce kowanne Sarki da
yake nan ya yi tunani a cikin mutanensa ya zabo
mutane hudu wadanda ya yarda da jarumtakarsu da
AA Misau ke Magana
kuma gaskiyarsu dole ne ya zamana cewa akwai mace
guda daya a cikinsu.
Bayan kowanne Sarki ya kawo mutane hudu sai a
hada mutanen duka a, sake rabasu izuwa kaso hudu.
Kason farko su nufi gabas su shiga duniya farautar.
jarumi Imran, kaso na biyu su nufi yamma, kaso na
uku su yi kudu, su kuma kaso na hudu su nufi arewa.
Babu shakka kafin shekara ta zagayo sai daya
daga cikin wadannan rukuni hudu sun hadu da jarumi
Imran sun gabatar masa da bukatarmu. Idan har suka
ci jarrabawarsa lallai zai taimaka mana ya fitar damu
daga cikin wannan mummunan tashin hankali.
Wannan shi ne iyakar taimakon da ni boka
Kirishna zan iya yi à matsayina na bokan da babu
kamarsa a doron kasa. Sauran aiki kuma ya rage a
garcku yaku wadannan sarakuna.
Wannan shi ne furucina na karshe a gareku kumna
ba za ku sake. ganina ba ko jin muryata sai bayan na
samí nasara bisa abinda za a tafi nema.
Koda gama wannan jawabi sai boka Kirishna ya
bace bat daga cikin dakin taron tamkar bai taba
Wanzuvwa ba.
Al'amarin daya kara dugunzuma hankalin
sarakan ke nan kuma suka kamu da tsananin al'ajabin
duk abubuwan da boka Kirishna ya zaiyanc.
Sai da aka sami lokaci mai dan tsawo dayansu
bai ce uffan ba daga can sai Sarki Huraisu ya koma
kan karagar maulki ya zauna ya kawo gwauron
numfashı ya ajiye kuma ya dubi gaba dayan surakunan
da ke cikin fadar ya ce, '"Ya ku yan uwana srrakei ku
yi sani cewa yau D na dada tabbatar da karin maganar
nan wacce masu iya magana ke cewa; "Komai nisan
gari akwai wani gari a gabansa" Ban taba zaton cewa a
halin yanzu akwai wani boka mai đaraja ba wanda yafi
su Sarki Imras karfin sihirin tsafi ba sai yanzu.
Shawarar da zan bamu ita ce, lallai mu yi amfani
da wannan umarni wanda boka Kirishna ya yi mana.
Yanzu na sallami kowa ku je ku zauna ku yi
tunanin mutum hudun da za ku zabo daga cikin
mutancnku wadanda za su yi wannan gagarumar taliya
domin bamu da wani zabi wanda yafi mu yi hakan."
Koda Sarki Huraisu yazo nana zancensa sai gaba
đayan Sarakunan jikinsu ya yi sanyi suka kasa cewa
komai kuma suka kasa mikewa tsaye domin su tafi.
Daga can sai Sarki Jamal ibini Ihisar ya numfasa
va dubi Sarki Huraisu cikin nutsuwa ya ce, "Ya kai
wannan'Sarki mai daraja ka yi sani cewa shekara guda
fa ba kwanaki kadanbane.
Shin baka zaton cewa kafin mu ga jarumni Imran
gaba dayanmu zanmu iya rasa dukkanin 'ya'yayenmu?
Ka ga ke nan idan hakan za ta iya faruwa tafiya
neman jarumi Imran bata da wani amfani.."
Kafin Sarki Huraisu ya baiwa Sarki Jamal amsa
sai Sarki Imras yai sauri ya tari numfashinsa ya ce, "Ai
koda mun rasa 'ya'yanmu gaba Gaya dole ne muyi iya
kokarimu wajen dakatar da wennan masifa tunda
bamu san saadda karshenta zai zo ba ko don saboda
mu tsirar da iyalannu da jama'armu daga cikin tashin
hankali da fargabar da suke ciki".
Dajin haka sai gaba dayan sarakunan suka kama
hayaniva kowa na fadin cewa, "Ya amince da wannan
shawara ta Sarki Imras."
Nn take fadar ta watse aka bar Sarki Imnras da
Sarki Hurainu su biyu rrak a zaune cikin tagumi da
Tunani
Sai da suka shafe kusan dakika dari da ashirin a
zaune dayansu bai ce uflan ba sannan yai
ajiyar zuciya ya dubi Sarki Huraisu y. ce, "Hakika
gaba da gabanta aljani ya take wuta.
Ya kai bokina yanzu ashe akwai Goyayyen
mashahurin boka a duniya kamar Kirishna amma bak
sani ba?
To wai shin ma mene ne dalilin da ya hana boka
Kirishna neman wannan silin sibirin gashi da ke jikin
Sarki furaisu dan vvana tunda yana da karfin sihiin
da kai baka da shi"
Kodajin wannan batu sai Sarki Imras yai ajiya
numfashi ya ce "Ya kai abokina ka yi sani cewa
kamar yadda kaima ka yi mamakin wannan al'amari
haka inma na yi, to amma ni yanzu tashin hankalin da
muke ciki yasa ma ban damu da batunsa ba.
Ina mai sanar da kai cewa ina matukar son dana
yarima Hasnalu fiye da komai a wannan duniya, da dai
mutuwa ta daukeshi gwara ni ta fara daukata".
Sa'adda Sarki Huraisu yaji wannan batu sai ya
cika. da tsananin mamaki ya ce, "Ya kai abokina ai
ya'yanka guda biyu ne me yasa ban ji kayi batun 'yarsa
Lushaira ba?"
Koda jin haka sai fuskar Sarki Imras ta sauya
yanayi izuwa tsananin fishi ya ce, "Ai kaima ka san
cewa har abada ba zan taba son Lushaira ba
musamman da kamanninta suka zo iri daya sak da na
yar uwata Husnaila.
Har abada ba zan taba kaunarta ba musamman
idan na tuno da iin tsantsar kiyayyar da ta nuna mini
ta guje ta bi Sarki Muraisu izuwa cikin dajin Kirzufa
har ta aureshi suka haife mana jaraba a yanzu. Ina
tabbatar maka da cewa inda zan sami ikon ganin
Husnaila a fili yanzu nan da nan take zan sareta da
hannuna."
Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu yaja
dogon numfashi ya ce, "Ya kai abokina ka yi sani
cewa kai bacin rai ne ya saka duk kake wannan batu
amma ina so ka gane cewa ni fa na fika shiga cikin
tsananin tashin hankali.
Abu na farko shi ne, a halin yanzu 'yata gimbiya
Husnaila ba ta san yadda aka yi na sami wannan mulki
AA Misau ke Magana
ba duk ranar da ta sani na san za ta tsaneni ne ta kawar
da 'duk kaunár da ke tsakanina da Ita
Abu na biyu kuma shine duk ranar da wannan
yaro ya gama busa kahon busa a imutu to babu inda zai
dürfafa fa cẻ nan birnina domin yazó ya kasheni ya
karbi mulkin mahaifinsa.
Bani dawanda zai iya kareni face Suzaila, idan ta
ji abinda ke tsakahina da mahaifinsa kuwa ba za ta
taimakeni ba taje ta ciro wannan gashin sihiri da ke
wajenkaa cikin kwalba a ajiye ta bani ba.
Wai shin ma har yanzu kaima baka sami damar
ciro gashin bane? Ina fatan dai ka yiwa wannan
Kwalba cikkaken adani
Lokacin da Imras yaji wannan tambaya sail ya
takarkane ya bushe da dariyar mugunta sannan ya hade
faska ya dubi Sarki Huraisu ya ce, "Shin ka ta6a ganin
wanda ya yi wasa da rayuwarsa?
To ka sani cowa na dauki wannan gashin sihiri
tarnkarishi ne ruhina a cikin wannan abu. yadda nake
bashí tsaro da kulawa, bana bảiwa raina da: lafiyata
Waishin kaima na tarmbaycka mana, me yasa har
yanzu baka labartawa gimbiya Husnaila labarin
wannan gashin sihiri bạ da ke wajena domin taje ta
fiddo maka shi ta ceci rayuwarka tunda bokaye. sun
gaya maka cewa ita ce kadai za ta iya ciro gashin?"
Koda jin wannan tambaya sai shima Sarki
Huraisu ya kyalkyale da dariya tarmkar babu wani abu
da yake damunsa a rayuwa.
Lokaci guda kuma ya hade fuskarsa ya ce, "lHaba
ya kai abokina shịn ka manta ne cewa ni da kai KAR
TA SAN KAR. Ana sani cewa yadda nake mutuwar
Son wannan gašhin sihiri domin na cika babban burina
nà duniya kaima kake sonsa don haka bazaka ta6a
yarda ba na mallakeshi.
Abu na biyu kuma ai idan na nunawa 'yata
Husnaila muhimmancin wannan gashin sihiri zan
jefata cikin tunani da wasi-wasi wanda zai sa ta tayi
bincike har ta gano sirin da na boye ma ta tsawon
"shekaru.
Ni yanzu abinda nake so da kai shi ne, mu ajiye
maganar gashin sihiri a gefe guda mu tunkaru wannan
babbar masifa da kegabanmu".
Kafin Sarki Huraisu ya gama rufe bakinsa tuni
karar kahon BUSAA MUTU ta cika birnin gaba daya.
Al'amarin da ya haddasa girgizar kasa, nan take
Sarki Huraisu da Sarki Imras suka zube kasa suna
masu yin rub da ciki cikin tsananin razana da
đimaucewa.
Gaba daya birnin sai da ya hautsine, gidaje suka
rinka rushewa.
Gaba daya birnin sai da ya hautsine, gidaje suka
rinka rushewa suna zubewa A kasa
Ba a sami nutsuwa da kwanciyar hankali ba sai
bayan shudawar sa'a guda da faruwar al'anmarin
Asanman ne wani Sarki
bokansa da ya baro can
wacce ya tafi ya barta a
Kwance ya sami sako daga
birnin cewar babbar 'yarsa
wance babu Iafiya ta mutu
Wani tsutsun tsefi ne ya kavo wannan sako a
rubuce a ci'kin wasika.
Kode Sarki Raukib ya karanta Wannan
wasika sai ya fashe da matsanancin kuka na bakin ciki
Nan take ya kama kiran sunan 'yarsa yana begonta
kuma yana ihu áa guje-guje tamkar nahaukaci sahon
shiga.
Koda sauran Sarakunan suka ga halin da Sarki
Raukib ya shiga sai duk suka kamu da tsananin
Tausayinsa wasu suka tayashi kukan bakin ciki, wasu
kuwa sai tai ka ga kawai idanunsa Sun kada sun yi
jawur saboda fishi da takaici.
Koda aka fahimci. cewar idan aka kyale Sarki
yaci gaba da wannn kuka da sambatu zai iya
haukacewa sai aka yi sauri aka kamashi aka shigar da
shi cikin gidan
gidan sarautar aka kaishi har cikin
masaukin a aka bashi giya mai dadi da banju ya sha....

Zan dakata A saikuma wani lokaci idan Allah ya kaimu
Dafatan Kuna lafiya
AA Misau ke Magana
Domin shiga WhatsApp group dinmu danna blue din rubutun nan

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU
Littafi Na Biyar (5)
Part B
Na Abdulaziz Sani M Gino
AA Misau Ke Magana

Ina yima Daukacin jama ar wannan gida barka da wannan lokaci tare da fatan Alkhairi

YA YI TATIL, NAN TAKE BARCI MAI NAUYI YA SACESHI BAI SAni
.
AL'AMARIN yarima Hasnalu kuwa, tun bayan
ganawar da ya yi da gimbiya Husnaila a cikin lambu ta
kafa masa sharadi na cewar sai yaje dajin Kirzufa ya
kamo yaro mai kahon busa a mutu ya zo da shi
sannan za ta karbi soyayyarsa- sai hankalinsa ya
dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi a
duniya duk da cewa ya yi alkawari a cikin zuciyarsa
cewar ya yarda ya rasa rayuwarsa a kokarin cika
wannan buri.
Cikin shigar yaki yarima Hasnalu ya shiga gidan
sarautar bangaren da aka bashi masauki.
Duk inda ya wuce sai ya ga dakarun gidan suna
risinawa suna gaisheshi cikin girmamawa saboda
matsayinsa. Haka dai ya ci gaba da tafiya har ya isa
cikin dakin da aka bashi.
Koda ya tura kofar ya shiga ya yi arba da wanda
ke ciki sai ya cika da tsananin mamaki. Ba wata bace
zaune a cikin dakin face 'yar uwarsa gimbiya Lushaira.
Hasnalu ya tura kofar ta rufe sannan ya dubi
Lushaira ya ce, "Ya ke 'yar uwata mene ne ya kawoki
nan dakina har kika zauna ina jiran dawowata?"
Koda jin wannan tambaya sai Lushaira ta dubi
Hasnalu a cikin alamun tausayawa ta mike tsaye ta
kama hannunsa ta zaunar da shi suka fuskanci juna
Sannan ta dubeshi cikin nutsuwa ta ce, "Ya kai dan
uwana ka yi sani cewa duk abinda ya dancka ai nima
ya dameni.
Ka gafarceni na yi maka laifi domin dđazu
sa'adda ka tafi lambu domin ka gana da gimbiya
Husnaila na bika a baya baka sani bã, kuma na labe na
saurari duk irin hirar da kuka yi inda a karshe ta kafa
maka sharadin sai ka yi gagarumar jarumtaka wacce
tafi wadda tayi kuma ka shiga dajin Kirzufa ka karno
mai kahon BUSA A MUTU sannan za ta aurcka.
Ina mai tabbatar maka da cewa duk wuya duk
rintsi sai ka ci wannan jarrabawa da ta baka kuna sai
ka cika burinka ka mallaketa".
Koda jin wannan batu sai yarima Hasnalu ya cika
da mamaki ya ce, Haba ya ke 'yar uwata kada ki zama
'yar abi yarima a sha kida mana. Ni kaina da na
kudurce a zuciyata da zahiri cewar zan iya cika
wannan sharadi ai na san cewa abu ne wanda ba zai
taba yiyuwa ba, kawai dai na gwammace na rasa
rayuwata da dai na dawo gida ba tare da na cika
ka'idar da masoyiyata ta gindaya mini ba.
Ina so ki sani cewa na kamu da tsananin son
gimbiya Husnaila irin son da in ban mallaketa ba
bakin ciki ne zai zamo ajalina".
Koda hasnalu yazo nan a Zancensa sai
idanunsa suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo
masa.
Al'amarin da ya sa zuciyar Lushaita ta karaya kenan
Ta sake kamuwa da tsananin tausayinsa ta
rungumeshi a loakcin da itama hawaye ya fara sartu
akan kyawawan kumatunta ta ce, "Ka kwantar da
hankalinka ya kai dan uwaná na yí malka alkawarin
zan taimakeka ta kowanne hali har burinka ya cika."
Koda jin wannan batu sai yarima Hasnalu ya
janye jikinsa daga cikin na ta suka sake fuskantar juna
sannan ya share hawaycnsa ya ce, "Haba ya yar uwata
ta ya ya zan iya cika wannan buri nawa alhalin ban
kasance jarumi ba?"
Lushaira ta ce, Ai ba jarumtaka ba ce take baiwa
mutum komai ba.
Akwai sa'a da rabo a rayuwa wadanda za su iya
kai mutum matsayin da bai taba tsammani ba.
Ni na san hanyar da zan bi na taimakeka ka cika
sharadin da gimbiya Husnaila ta gindaya maka.
Abinda nake bukata da kai kawai shi ne, ka kara
hakuri domin komai yana da lokacinsa sannan kuma
ina son ka yi kokari ka sarrafa zuciyarka akan yawan
begen gimbiya Husnaila.
Ma'ana ka tursasa zuciyar taka ta danne soyayyar
don gudun kada ciwon So ya jefaka a cikin mugun
hali"
Koda gama fadin hakan sai gimbiya Luzaila ta
mike tsaye ta fice daga cikin daki gabadaya
Hasnalu na zaune yana mai binta da kallo cikin tsananin
Mamakin yadda za ta iya tainakosa har ya mallaki
gimbiya Husnaila wanda shi a ganınsa inda duniya zata taru tayi masa agaji ba za a iya cika wannan buri ba
AL'AMARIN gimbiya sulaiza kuwa, bayan ta
rabu da yarima Hasnalu sai ta wuce kai tsaye izuwa
Turakar mahaifiyarta Sabirat.
Tana siiga cikin turakar ta iske Sarki Huraioa
tare da Sabsrat a zaUne suna tatfauun wa.
Kallo daya ta yi musu ta fuskanci cewar suna
cikin matukar damuwa domin akan fuskokinsu ta ga
damuwar karara.
Suzaila ta karasa gabansu da sauri sannan ta
zauna a gefe daya tana mai fuskantarsu ta dubi Sarkı
Huraisu cilkin damuwa ta ce, "Ya kai Abbana wacce
irin shawar a kuka yanke yanzu kai da sauran Sarakuna
bisa wannaa matsala da kc gabanmu?"
Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu ya yi
ajiyar zuciya sanann ya kwashe labarin duk abinda ya
faru a faia ya zaiyane sna ta har da batun bakon boka
Kirishna kuma mafitar da ya kawo
Koda jin wannan batu sai gimbiya Süzaila ta cika
da tsananin murna ta ce, "Ya kai Abbana ka yi sani
cewa iin wannan dama nake nema a rayuwata wacce
zan yi gagarumar tafiya ta yin abin al'ajabi wanda in na
yi shi zan bar abin tarihi wanda ba za a taba mantawa
da shi ba har bayan raina.
Ba zan yabi kaina bả tunda an ce yabon kai
jahilci amma kai kanka ka san cewa nacancanta ka
zabeni a cikin mutum hudu da za ka ware a cikin
mutanenka wadanda za su yi wannan tafiya tunda ina
da jarumtaka, ina da amana dai-dai gwargwado haka
kuma ina da tausayi da kamanta gaskiya."
Lokacin da Suzaila ta zo nan a zancenta sai
hankalin Sarki Huraisu ya dugunzuma ainun ya dubi
Suzaila cikin tsananin damuwa ya.ce, "Ya ke 'yata kin
sani cewa ke kadai gareni a duniya don haka bana son
ki yi nisa da ni kuma bana son rayuwarki ta shiga cikin
hadari.
Kin ga kuwa wannan tafiya da za a yi itace tafiya
mafi hadari da za ki yi a rayuwarka domin
jarumtakarki ba za ta ceci rayuwarki ba tunda karshen
tafiyar za a durfafi dajin Kirzufa ne bay an kun sadu da
jarumi Imran ya aminta da ku ya yi muku jagora."
Suzaila ta kyalkyale da dariya ta ce, "Ya kai
Abbana ka yi sani cewa a rayuwata yanzu babu
mahalukin da yake burgeni sama da jaurmi.
Yanzu da naji labarin wannan sadauki mai suna
Imran kuma na ji

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment