Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Uncle bai hauka ce ba? Ya gaya mini digirinsa ya yi shi ne kan sociology. (With first-class honour) Nima insha Allahu abin da zan karanta kenan".
Nabilah ta ce "Sai ki yi azama, me ake da abin da zai juyawa mutum tunaninsa zuwa na Yahudu da Nasara?"
Ta ce "Eh, idan kin amince da abin da suke fada ba? Ni dai ina so tunda Uncle shi ya karanta".
Nabilah ta kyabe baki ta ce "Kya karaci gulmarki dai, kina son mai abin kina cewa abin kike so".
Ta bude baki cikin mamakin Nabilah, ta suri bokiti ta yi waje tana yi mata dariya, tana cewa, "Ku gama kumbiya-kumbiyar taku a yi candy mu zo Galadanchi mu kawo amarya….".
Ta bi ta da duka ita kuwa ta falla da gudu.

To sai ga shi yau Inna ta fadi wani abu kwatankwacin na Nabilah. Ta yi ajiyar zuciya, ta ce a ranta "Shin ko dai Nabila da Inna gaskiya suka fada ne? I fall in lobe with Uncle Junaidu? Neman tabbacin hakan abu ne mai matukar wahala a kwawalwarta".
Ta mike ta fito ganin shiru-shiru Inna ba ta dawo ba daga fita alwala har gari ya waye, gabanta ya soma bugawa da sauri da sauri, cikin matsananciyar faduwar gaba. Ta duba gabas da yamma, kudu da arewa, babu Inna babu alamarta.
Ta matsa kofar bayin ta kasa kunne babu motsin Inna. Cikin karfin hali da matsanancin firgici ta ce, "Inna kina ciki ne?"
Shiru babu amsa, ta ce "Inna ki yi min gyaran murya idan ba za ki magana ba".
Nan ma shiru, sai amsa kuwwar raunanniyar muryarta da ginin kasa ya dauka, ya dawo mata da abinta cikin kunnuwanta. A lokacin ne ta ankara da zanin da ke daure a jikin Inna wanda karfen guga ya makale ya yage. Ba ta son gasgata abin da kwakwalwarta ke son ankarar da ita. Ta matsa ga rijiyar ta leka jikinta babu inda ba ya kyarma. Kafafuwan Inna ta gani a sama, maganar motsi kuwa babu shi a tare da su.
Sai ta yiwo waje da gudu tana ihu tana kururuwa a kawo mata agaji, kanta ko kallabi babu, kafarta babu takalmi, hawaye shabe-shabe a idanunta. Abinki da jama'ar kauye, ma'abota hadin kai da taimakon junansu, nan da nan gidan ya cika makil da dan Adam, makotansu da abokan arziki kowa yana ta Allahu Akbar! Hure Allah Sarki!!
Nan da nan wasu samari majiya karfi suka hada doguwar igiya suka cilla, biyu suka kama hancin suka rike, daya ya bi ya dauko Hure suka fiddo su.
Mairo ta daga ido ta ga wai yau Innarta ce wannan babu numfashi, ta tafi har abada ta barta. Innan da ta rage mata a duk fadin duniya, ita ma ta tafi. Sai ta fadi, wuni guda cur ba tasan inda kanta yake ba.
***














F
arkawa ta yi ta samu kanta a gidan makociyarsu Karime. A lokacin har an yi wa Innar sallah, an kai ta makwancinta. Mairo ta ja jiki ta takure wuri guda sai a lokacin kuka ya zo mata. Ta yi ta kuka kamar ranta zai fita. Karime na ba ta baki tana rarrashinta. Ta ce, "Wannan ba shi ne karshen rayuwarki ba Mairo. 'Ya'ya nawa ne iyayensu suka mutu tun a wurin haihuwarsu, kuma sun rayu? Ki godewa Allah da Ya nufe ki da tashi tare da su, kika san dadinsu. Ni kin ganni nan ban taba sanin uwata da ubana ba, cikina da wata biyar Babana ya rasu, lokacin haihuwata uwata ta rasu, amma gani nan da nawa 'ya'yan goma sha uku. Ina yi miki ta'aziyya Allah Ya jikan Hure, mutumiyar kirki, mai alheri".

Mairo ba ta fasa kukanta ba, addu'a ta ke Allah Ya dauki ranta ita ma ta huta, maraici na uwa da uba ba karamin abu ba ne. Tunaninta shi ne, ina zata kuma samun mai kaunarta a duniya kamar iyayenta? Ina zata je? Da wa zata zauna? Mene ne amfanin sauran rayuwarta? Ba ta da kowa ba ta da komi sai Allah, domin ta fidda lissafin Habibu a zuciyarta. Ta samu kanta cikin kullatar Yaya Habibu, kullata mai tsanani. Ba ta ga ranar da haihuwarsa tai wa iyayensu ba.
Karime ta shigo da dambun masara a kwano da ruwa a kofi, ta sa ta gaba lallai sai ta ci. Ta dauki loma ta kai bakinta tamkar mai taunar madaci, haka ta ke taunar abincin. Ta tsame hannunta tana sharce wasu dunkulallun hawaye da suka zubo mata. A lokacin ta tuna babban kuskurenta a rayuwa, ba ta yi wa Inna addu'a ba.
Ta mike ta je ta dauro alwala ta zo waje mai tsabta a dakin Karime ta shimfida sallaya, ta suturce jikinta ta tayar da sallah. Tana sallah hawayenta ba su bar ambaliya ba. Da ta idar ta bude Alkur'ani mai Tsarki ta shiga karantawa Inna suratul Yasin da suratul Rahman ta rufe da (du'a'ul mutawaffa) tana addu'ar Ubangiji Ya yi mata masauki da aljannah.
Ranar kwana uku da rasuwar Inna Hure ta tattaro duk ajiyarta kudin mota kawai ta barwa kanta, ta ba wa Karime aka yiwa Inna sadakar gumba, waina da kosai. Mijin Karime da Dagacin Gurin-Gawa suka zo suka same ta har dakin Karime suka fara da yi mata ta'aziyyah, sanan Dagaci ya ce sun zo ne su kai ta gidan kanin mahaifinta su damkata a hannunsa, wannan ita ce amanar da za su sauke.
Hankalin Mairo ya tashi, zancen Inna ya dawo mata sabo tar! A kwanyarta, "Wata kila abin da nake gudu ne dole sai ya faru... Zaman Mairo da iyalan Abbas".
Ta sunkuyar da kai tana kuka, ta ki ba su amsa, Malam Tanimu ya ce "Hakuri za ki yi Mairo, mutuwa riga ce akan kowa, tafiyarki birni ya zama dole, domin ba ki da wanda ya fi shi. Sannan Abbas mutum ne mai ZUMUNCI ki dubi yadda ya rayu yana kyautatawa mahaifinki. Ina da yakinin zai rike ki da amana tamkar mahaifinki, har zuwa sanda zai miki aure".
Sai ta mike cikin karfin zuciya, ta yafa mayafinta ta sa takalminta. Karime ta rakata gidansu tana hada kayanta tana kuka.
Ta tattara zannuwan Inna da kayayyakinta ta sa a wata tsohuwar akwatun karfe ta rufe, ta tura karkashin gadon bononta. Ta tattara 'yan kudaden Innar irin wanda Junaidu ke ba ta ne a duk zuwan da ya yi, da kudin motar da ta warewa kanta duka ta zuba cikin jakarta ta makaranta. Suka fito Karime ta datse dakin da kwado, tana tafe tana waiwayen dakunansu da madafinsu da ta ke jin tana yi masu kallon karshe ne, wasu hawayen suka zubo.
Tana bayan motar Dagaci wata (mitsubishi) mai hayaniyar tsiya, in banda karar injina da salansa ba abin da kake ji, shi da Malam Tanimu suna gaba. Ta kama jikinta tsan-tsan sabida gwaruwar da kanta ke yi da jikin motar sabida rashin kyawun birjin Gurin Gawa. Shi da Malam Tanimu suna ta hirarsu ba abin da ya dame su, ita kuwa sake-saken da ta ke yi cikin ranta na abin da zata je ta tarar a gidan Baffanta da 'ya'yansa marasa adadi da rashin tarbiyya ta ke yi.
Sai da suka hau titin gidan zoo sosai sannan motar ta daidaita, tafi-tafi har suka iso gidan Sarki suka billa Yakasai ta nan.
Kugin karshe da kwarababbiyar motar ta yi a kofar gidan Alhaji Abbas Maigoro ne. Gida ne ginin siminti mai dakali hagu da dama da manyan zaure irin ginin masu kudin da. Yara kanana da samari suna ta shige da ficen su. Gabanta ne ya soma dukan uku-uku sabida haka ta yi hamzarin jan Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un har ta samu bugun zuciyarta ya yi dai-dai.
Suka ce ta shiga cikin gidan ta turo musu Alhajin suka fito kan dakalin gidan suka zauna. Cikin sanyin jiki Mairo ta fito tana tafe tamkar macijiya sulu-sulu abin tausayi. Ta yi sallama a tsakar gidan, Uwargidan Hajiya Habiba ta amsa, wadda ke tukin tuwon dare a bakin murhu.
Ta karasa inda ta ke ta tsugunna tana gaishe ta cikin nutsuwa. Ta amsa da alama ba ta gane ta ba, ta ce "Yammata daga ina? Ban gane fuskar ba".
Ta dukar da kai ta ce, "Gurin-Gawa".
Habiba ta kalle ta sosai na 'yan dakikai, nan da nan fara'ar da ke fuskarta ta bace. Ta juya ta ci gaba da tukin tuwonta. Cikin halin ko'in'kula ta ce
"Auyo! Ce min zaki yi MAIRON HURE shalelen HURE, sai yau tasan mu mutane ne da ta turo ki ki gaishe mu? Ce nake har jinya kuka yi anan ta tsayin watanni ba ku san hanyar gidanmu ba, sai dai kullum mu tuka mu ba ku? Ince ko yanzun ma ba tasan kin zo ba kada mu moran mata ke?"
Mairo ta share hawayen idanunta, ta ce "Tare muke da baki suna zaure, sun ce suna son ganin Alhajin ne".
Sai da ta mula ta ce "Ba ya nan, yana kasuwa, amma yana gab da dawowa".
Ta taso sumui-sumui ta fito dakalin gidan ta fadawa su Malam Tanimu sakon Hajiyar.
Ta ci gaba da tsayuwa a zauren ba ta koma cikin gidan ba. Malam Tanimu ya ce "Bude motar ki kwaso kayanki mana ki shiga da su?"
Jikinta ya yi sanyi lakwas ko numfashi da kyar ta ke shaka, ta ce "A'a, mu dai jira Baffan".
Dagaci ya yi nazarinta yana taunar goronsa, ya ce "Mairo ki saki jikinki, nan fa gidanku ne, gidan ubanki ne".
A ranta ta ce "Kayya Uba guda daya ne, na tabbata na rasa nawa".
Suna nan zaune ita kuma tana tsaye daga cikin zauren kusan rabin awa, Ladidi diyar Alhaji Abbas wadda ta ke kusan tsararta ta dawo daga unguwa rike da hannun kanwarta Rahma ta ci kwalliya kamar me? Tana yafe da wani dan gyale mai kama da abin tatar koko, ta daga ido tana kallon Mairo kana ta kyabe baki ta ce "Ah! Yau wace rana?"
Ta yi murmushi, ta ce "Ladidi ke nan, kuna lafiya?"
Ta sake kyabe bakin (ga alama al'adarta ne yin hakan a duk sanda zata yi magana), wanda kwata-kwata ba ya mata kyau, don ko daya ba ta da kyawun fuska. Ta ce "Gidan namu ne bai ishe ki shiga ba da zaki tsaya a zaure, ko kuwa wani sabon salon gulmar ne Hure ta koya miki, ta ce idan kin zo ki yi mana, don Baba ya ce mun wulakanta ki?"
Ta bude baki tana kallonta kawai cikin mamaki, ba ta ce komai ba, ta yi ciki sai ta danne zuciyarta ta bi ta a baya.
Suna shiga Habiba ta ce "Ai na dauka tafiya ta yi babu sallama, saboda uban nata ba ya nan".
Ta sake kyabe baki, ta ce "Can soro na ganta a tsaye, salon ta ja mana magana wajen Baba".
Amarya Aunty Hajara ta yane labulenta jin cece kucensu, ta ce "Wa nake gani kamar 'yar gidan Hure?"
Habiba ta ce "Ke ma dai kya fada, ai ni na dauka batan kai ta yo".
Hajara ta saki labulenta tana cewa, "Allah Sarki! Alhajin yana kan hanya don nasan dai ba wajenmu kika zo ba".
Mairo dai na tsaye tamkar mutum-mutumi. Tana mamakin rashin mutumci irin na matan Alhaji Abbas. Babban mamakinta daga Habiba har Hajara babu wadda ta ce ta shigo daki.
Haka Ladidi ta shige dakinsu na 'yammata ba ta kara bi ta kan Mairo ba. Ta ci gaba da tsayuwa sororo! Wannan yaro ya shiga, wannan ya fita duk ba su santa ba. Wannan ita ce rayuwar da Innarta ta ke guje mata ke nan ta matan birni marasa karah da rayuwar kowa yai ta kansa, ko kuwa abin nan da Bahaushe ke cewa, kowa tasa ta fishshe shi.
Sai ta jiyo muryar Alhajin yana gaisawa da su Dagaci, ta yi ajiyar zuciya. Sun dade suna magana tana jiyo tashin sautin Alhaji Abbas yana ta kiran Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ita ma sai hawayen ya zubo mata. Can anjima ya shigo dauke da jakar kayanta da kansa, nan ya ganta tsaye a tsakar gida tana share hawaye.
Ya ce "Sannu kinji Mairo, sannu Allah Ya jikan Bedi da Hure, Allah Ya ba mu dangana mu kuma Ya kyautata namu karshen. Ya ya zaki tsaya a tsakar gida kamar ba gidanku ba? Shige mu je wajen Habiba".
Ta bi shi a baya. Ya shiga dakin yana cewa, "Habiba 'yarki ta zo kin barta a tsakar gida, ko ba ki ganeta ba ne?"
Daga can kuryar daki ta amsa "A'ah 'yar Hure dai, don sanda na ce da uwarta ta ba ni na hada da nawa na rike cewa ta yi ba ita ba mu. Sai yanzu da ta zama budurwa gab gidan miji zata zo min? Wato na tattara jeren dakina na yi mata kayan aure?"
Ya yi murmushi, ya ce "Ina abin ya ke? Wannan jeren naki ko dari biyu bazan iya sayenshi ba, sai ka ce yau kika fara aurar da 'ya'ya? Cewa nake ‘ya’yan yayyaenki duk kekika aurar dasu batareda kin taba kayan jeren naki ba?"
Ta fito tana daura kallabinta, ta ce "Can dai, akai gaba. Da din ma da na ce a bani rashin godiyar Allah ne, yanzu kuwa ni ma sun yi min yawa, neman kai nake da su".
Ya nunawa Mairo kujera ya ce ta zauna, amma ita sai ta zame ta zauna akan leda tana gayar da Baban. Ya kwalawa Hajara kira ta shigo tana tambayar "Lafiya? Bashi na ci ban biya ba ne?"
Ya ce "Duk ku zauna". Sannan ya maida walwalar da ke fuskarsa ya ce "Hajara, Habiba, kowacce ta amsa da "Na'am".
Ya nuna Mairo wadda kanta ke sunkuye, ya ce "Wannan wace ce?"
Suka ce "Mairo".
Ya ce "To madallah, tunda kun santa, wane ne ubanta?"
Suka ce "Bedi".
Ya ce "Bedi wane ne a gare ni?"
Suka ce "Yayanka ne".
Ya ce "A yau babu Bedi, wadda kuke gaba da ita itama babu ita a duniyar, wato Hure. Sabida haka duk duniyar nan Mairo ba ta da inda zata je sai gidana, tunda ba aure aka yi mata ba, saboda haka ga amana nan a hannunku, ku rike ta yadda za ku rike 'ya'yanku har zuwa sanda Allah Zai kawo mata mijin aure.
Wannan yarinya marainiya ce, don haka wadda duk ta zalunce ta cikinku Allah ba zai barta ba. Idan ta yi ba dai-dai ba ku kwaba mata, ku sa ido akan tarbiyyarta kamar yadda zaku yi wa 'ya'yan cikinku. Ke kuma Mairo wadannan iyayenki ne, ba ki da wanda ya fi su, don haka ki yi musu biyayyar da zaki yi wa iyayenki. Ki kai kayanki dakin Ladidi ku zauna tare, Allah Ya jikan Bedi da Hure".
Cikin zuciyarta ta ce "Ameen". Hawaye suka kawo mata zarya.
Habiba ta ce "Dakata Alhaji, amanar maraya ka ce ka bani ko? Idan na ci Allah Ya ci tawa, to ban karba ba, balle ace na ci amana. Sai dai zama na kinzo-na-zo kowa zaman kansa yake. Ita zaman uba ni zaman miji".
Hajara ma ta ce "Ato! Gaskiyarki Yaya, ni ma abin da zan ce kenan sabida rikon maraya wuya gare shi. Da idan ba wanda ka haifa ba ko goyonsa zaka rika yi kullum ba zaka fita ba. Dubi Mairo gansamemiyar budurwa ce da tasan abin da ta ke yi. Don haka ta yi wa kanta fada, kada inyi ace don ba 'yata ba ce".
Suka karkade zannuwansu suka yi daka. Daga Mairo har Baffanta kowanne gwiwa a salube, ya dade kai a duke, haka ita ma. Daga bisani ya ce,
"Ki yi hakuri Mairo, na rasa me ke tsakanin Hure da su Habiba, ki rabu da su ki yi rayuwarki cikin walwala, duk wata matsalarki ki yi kokarin sanar da ni. Ya ya batun makaranta kuma?"
Ta ce "Nan da kwana uku nake son komawa idan na natsa".
Ya ce "To gaya min abubuwan da kike da bukata gobe sai na sayo miki".
Ta gaya mishi yana rubutawa, ya sanya takardar cikin aljihun gaban rigarshi ya mike ya ce, "Zo dauko kayan na nuna miki dakin Ladidin". Ta sungumi jaka ta bi shi ya nuna mata dakin ya fita.
***



MAIRO A GIDAN BAFFANTA
M
airo ta yi zugum ta zubawa jakar kayanta ido cike da tunanin yadda za ta yi rayuwa a wannan gida. A karshe ta tattara komi ta mikawa Allah. Ta ji tausayin Baffanta Alh. Abbas da bai yi dacen matan aure ba. Da ganin shi ba shi da katabus a gidan.
Ba ta gama tunaninta ba Ladidi ta yane labulen dakin ta shigo fuskar nan a turbune, kamar wadda aka yi wa shegen duka. Wannan fushi ba na komai ba ne, sai don hadata da Mairo daki daya da Baban ya yi, ba ta kuma da yadda zata yi.
Mairo ba ta kulata ba, ta maida kai ga littafin da ke hannunta tana karantawa.
Allah-Allah ta ke litinin ta zo ta koma makaranta, wannan ne kadai ta ke ji zai sanyaya mata zuciya. Washegari tun bayan da ta yi sallar asuba ba ta koma barci ba, ci gaba ta yi da lazimi har gari ya soma haske. Ta mike ta ninke sallayar ta fito tsakar gida ta tarar da tulin wanke-wanke a gindin famfo, ta nade zaninta ta ja kujera ta zauna ta soma wanke kwanukan, duk gidan ba wanda ya fito, ta gama ta share tsakar gidan tas! Dai-dai lokacin Habiba ta fito zata yi alwala ta ganta tana sharar ga kwanukan ta wanke mata, ranta ya yi dadi, ta dan saki fuska, ta ce "Ah'ah Mairo daga zuwanki? Ai aikin gidan nan ya fi karfinki, kada ki dorawa kanki abinda ba zaki iya ba".
Ta yi murmushi, ta ce "Ai babu komai Mama, abin da jibi zan koma makaranta har ina aikin ya ke?"
Ta wuce bayan gida ranta ya yi dan sanyi da Mairo, tunda da alamun za a yi zaman lafiya da ita, tunda ba ta da kiwa.
Da ta gama ta yi wanka, ta shafa mai ta sanya atamfa nichem wad, ta ci gaba da karance-karancenta. Ladidi ta shigo musu da kwanon koko da kosai, ta debi nata ta turawa Mairo ragowar ba ta ce ko uffan ba.
Mairo ta rasa wace irin yarinya ce Ladidi kamar ita ba jininta ba ce. Ta ga ba ta da alamun yi mata magana kamar ba daki daya suka kwana ba. Wannan sam ba ya daga cikin tsarin musulunci, don haka ita ta sauke kai ta ce "Mun kwana lafiya Ladidi?"
A lalace ta ce "Lafiya lau".
Da haka Mairo ta ja bakinta ta yi shiru, ita kuma Ladidi ta yi wanka ta fice daga gidan.
Da yamma Baba ya dawo, har dakin ya bi ta, ya same ta da ledoji niki-niki ya yo mata sayayyar komawa makaranta. Ta yi hamzarin mikewa ta karbe shi, ya ce "Duba ki gani, idan da abin da babu ki gaya min na koma na karo".
Tana bude kayan tana dubawa ta ce, "A'ah komai ya yi Baffa, madalla na gode, Allah Ya kara budi".
Ya fita yana cewa "Ki dai saki jikinki a gidanku, don Allah Mairo".
Tana kokarin hada kayan don ta maida su cikin ledarsu. Tsulum! Aunty Hajara ta bankado labulen dakin ta shigo. Idanunta akan kayan ta kama haba ta ce "Iye! Gata maganinka Allah! Mu yaushe aka taba saya mana kayan masarufi haka a gidan nan? To wallahi ba zata sabu ba, biyu zan raba su na dauki rabi".
Ta soma kasa kayan bayan ta zazzage su daga ledojinsu. Ta kwashe rabi ta zuba a leda guda ta yi waje da su, ko kunya babu.
Mairo na zaune tana kallon ikon Allah, ashe ba ta gama mamaki ba, don Habiba ganin Hajara ta fito da kaya fal leda ita ma ta zabura ta yi dakin, ta ce "Mairo miko kayan nan a cire na Ladidi".
Ba musu Mairo ta mika mata buhun baccon, ta kwashe na arzikin su kayan shayi da sabulai, ta tura mata sauran da ko sati ba zasu yi mata ba. Ita ma ta fice tana fadin "Gara mu ci arzikin albarkacinki, don idan namu 'ya'yan ne ai ba za a siya musu haka ba, ita ma Ladidi ta sha shayi ta ji ya dandanonsa ya ke".
Da ta ga idan ta biyewa wadannan mutanen za su sanyata kuka, sabida rashin imaninsu, sai ta dauko littafin addu'o'i na Hisnul Muslim ta soma karantawa idanuwanta cike taf da kwallah. Wadannan su ne 'MATAN BIRNI' ke nan.
Wato duk matan birni ba su da kirki, daga na masu kudinsu har talakawansu. Al'ummar kauye ba haka suke ba, mutane ne masu kara da karimci. Matan birni dansu shi ne nasu, dan wani kuma ko oho! Ta yarfe hawayen idanunta.
Wajejen karfe sha biyu na rana, Hajara ta kwaso jibgin wankin yaranta ta jibge a gindin famfo, ta kwalawa Mairo kira wadda wani matsiyacin barci ya soma fizga kadan-kadan. Nan da nan ta gyagije ta amsa, ta fito "Ga kayan kannenki nan ki taimaka ki wanke musu kan la'asar, saura ki zauna kailula har uban naki ya dawo ya ce don me na saki aiki".
Ba musu Mairo ta amsa da "Zan yi sauri Aunty Hajara".
Ta soma dirzar dukunkunannun kayan wanda kamin ta wanke wando daya ya fita, sai an yi minti ashirin sabida tsabar daudar da suka yi. Don haka wankin ya kai ta har karfe hudu. A lokacin an gama abincin rana, kowa ya ci nasa amma banda ita, sai da ta gama gaba daya, bayanta ya amsa, kugunta ya rike, 'yan yatsunta suka shiga zafi da radadi sabida ba ta taba yin wanki irin wannan ba.
Ta dawo daki ta kwanta, Habiba ta aiko dan autanta Hadi da filet din dafadukar shinkafa wadda duk ta bushe babu kuma alamun zata toshe mata dunkulalliyar yunwar da ke cinta.
Ta gabatar da sallar azhar da la'asar a tare, sannan ta zauna tana cin shinkafar. Dai-dai lokacin Baba ya yi sallama ya shigo rike da kwanon samira, ya ce "Amshi nan Mairo ki kara, idan kuma kin koshi ki ajiye zuwa anjima kafin a gama na dare idan kinji yunwa sai ki ci".
Cike da tausayin Baffanta mai son faranta mata, Mairo ta karbi kwanon samirar, hakan ya yi dai-dai da bayyanar Habiba a dakin tana huci kamar macijiya, ta ce
"Wannan salon da zaka fito da shi bazan yi na'am da shi ba. Yazan bai wa yarinya abinci kamar yadda na baiwa kowa a gidan nan amma ka dauko naka ka kawo mata, cewa ta yi ba ta koshi ba, ko kuwa wani sabon kinibibin ne don a zage ni?"
Ya ce "Idan ma kinibibin ne, ni ne mai kinibibin ba ita ba, tunda dai ni na dauko na kawo mata har inda ta ke, ba zuwa ta yi wajena ta roka ba".
Ta sa hannu ta dauke na filet din, ta ce "Wallahi ba zata ci rabon mutum biyu ba, kai dai da ka zabi ka zauna da yunwar kai ta zama, amma na dauke wannan".
Ko kulata bai yi ba, ya sa kai ya fice daga dakin, ta wani fannin kuma kunyar Mairon ya ji.
Mairo ba ta saba ganin irin wannan rayuwar ta matan birni ba. Wadanda suka dauki miji, ba a bakin komai ba.
A matsayinta na marubuciya 'articles' a take ta ji tana son yin rubutu akan mata irin Habiba da Hajara. Wannan ne ya tuna mata da mutum ma fi muhimmanci a gare ta a yanzu (Uncle Junaidu). Ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, a take ta dauko full-scap da biro ta soma rubutun da tasan Uncle zai yaba da shi.
A tsayin kwanaki ukun da ta yi gidan Baffanta, ta ga rashin mutumci da rashin darajja miji kala-kala wajen matan Baffanta. Sannan ta ga rashin tarbiyya da rashin mafadi wurin ‘ya’yan su, hart a soma yiwa kanta fatan kada Allah Ya sa ta yi aure a birni. Gara ta koma can Gurin-Gawa ta yi aurenta kada ita ma ta zamo daya daga cikin matan birni, wadanda ba su dauki mijinsu da 'yan uwansa a bakin komai ba.
Wannan tunanin da ta yi, yasa ta yi murmushi. To idan ma auren zata yi wa zata aura? Babu wanda ya taba cewa yana sonta. Babu wanda ta taba gani ta ji tana so a duniya, ba ya ga iyayenta da Yaya Habibu. Wata irin faduwar gaba ta same ta, tare da jin wani dal-dal-dal a cikin kirjinta, gami da tashin da tsigar jikinta ta yi, duk a lokaci daya. A lokacin da zuciyarta ta ambato mata UNCLE JUNAIDU. Wani irin matsayi ne da shi mai GIRMA a zuciyarta, wanda a duk lokacin da tunninsa ya fado mata, ta ke tsintar kanta a cikin wannan yanayin.
Mu biyo Mairo da Junaidunta a littafin na biyu, wanda tare suke da dan uwansa.,

Maman SAFAH da MARWAH ce…….!







Ku nemi littafin

4 Comments On A BARI YA HUCE
avatar
fatimah-1

12 months ago

Reply

Pls book 2

avatar
shuraih99

12 months ago

Reply

Replying to fatimah-1

Tuntubi nambar nan 07030137870

avatar
hajara-muhammad

12 months ago

Reply

An interesting Novel

avatar
hajara-muhammad

12 months ago

Reply

An interesting Novel

Please Login or Register in order to submit comment