Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji Addahna? Ba zan kai ki inda za ki cutu ba, ba zan bari a bata miki rai da gangan ba sai in ba na raye. Ki yi hakuri ki yi min biyayya yadda shi ma da ya fi ki shekaru ya yi mini. Na yi miki alkawarin insha Allahu dukkanku ba za ku yi da na sani ba, sai kun yi alfahari da wannan aure naku, sai kun gode min watarana”.
Baba Azumi daga falo tana shara ta ke jin tashin muryar Mammah da alamun kukan ‘yar gidanta. Ta ajiye tsintsiyar ta taho. A bakin kofa ta tsaya tana kallon ikon Allah.
“Kukan me ta ke yi? Ke fa abin kuka ba ya miki wuya, don Mamarki na shagwaba ki?”
Murmushi Hajiya Maryam ta yi, “Wannan kukan mai dalili ne. Yau Mommah ta yi laifi dole ta ke lallashi, kukan aure ne na rabuwa da Mammah da Baba Azumi, ko Suhaana?”
Ta daga kai ta ce, “Eh”.
Duk sai ta ba su dariya.
Mammah ta share mata hawaye, Azumi ta ce “To ai mijin na gida ne, ba za ki yi nisa da mu ba. Ni na taba ganin auren gata ma irin naki Hansai? Babban Yaya gabadaya fa, uban gida magajin gida, lauya na al’ummah na Hansatu bada kanka a sare, Yayan Isma’ila, Yayan Usmanu, Da daya tamkar da goma Mammah ta zabo miki duk cikinsu. Daina kuka kin ji? Yi farin ciki ki gode wa Mamarki, ita mai sonki ce”.
Nan fa Hafsat ta hau zazzare ido tsakanin Mammah da Baba Azumi tana so su yi mata karin bayani, wane Babban Yayan Baba Azumi ke nufi?
Sai dai ba ta samu komai daga karin bayanin da ta ke son jin ba don Mammah ficewa ta yi kawai tana murmushin wannan kirari da Azumi ta yiwa Abdul’azeez.Da yake tayi maganar da ita tun jiya. Inda ta bada goyon bayanta dari bisa dari da kyakkyawar addu’a. Baba Azumi kuma ta wuce ta ci gaba da shararta suka barta cikin ci-da-zuci, sakar zucci da tunanin zuci mai nauyi. Ba dai wannan ‘baren’ (total stranger) na cikin ‘ya’yan gidan nan ba? Ba dai wannan wanda ya fi kowa odd hali cikin gidansu ne ake nufin zai zama mijin nata ba????
*****

“Kina ina Mu’azatu?”
“Har yanzu ina Apo, sai gobe zan bar abuja, mene ne? You sound worried?”
“A ina zan same ki? Magana ce mai muhimmanci da ba ta bukatar distraction, gidan Anty kuma ba ya rabo da jama’a”.
“To ko in zo office dinka yanzu? Sai direba ya kawo ni, ina ganin za mu iya tattauna kowacce irin magana a can”. Ta fada cikin faduwar gaba, jin muryar Abdul’azeez na rawa, abin da ba ta taba ji daga gare shi ba. “Alright” Kawai ya ce ya kashe wayarsa.
Mota kirar matrix ta sauke Mu’azatu Rufa’i a Federal High Court da ke kan titin (OAU Quaters, Kashim Ibrahim Way Maitama, Abuja), cikin tafiyarta mai kama da tana taku a kan kwai ta karasa zuwa ofishoshinsu. Daya bayan daya ta ke wucewa tana duba sunayen da ke rubuce jikin wani dan karfe a saman kowacce kofa har ta zo inda ta ke nema.
‘Barr. Abdul’azeez H. Dakata’. Shi ke rubuce a saman ofishi mai lamba (24). Ta kwankwasa daga ciki ya amsa, ta murda ta shiga.
A kan doguwar kujerar leather ruwan kasa yake zaune cikin daya daga kujerun tattaunawa da baki da ke ofishin. Sanyin air-condition ya ratsa ta kamar yadda ya mamaye ofishin da kamshin turaren mamallakinsa.
Mu’azatu na mamakin son sanyi irin na Abdul’azeez a gida ne, a mota ne, a ofis ko yaushe za ka same shi ya kure A.C shi ba wanda ya yi rayuwa a kasar sanyi ba.
“Koma ki yi sallama malama, sannan ki shigo”. Ya fada cikin sanyin murya.
“Ai na yi knocking ka ce in shigo”.
“To ni bana son knocking saboda ni ba arne ba ne, sau nawa zan gaya miki?”
Ta zumbura baki, ta koma ta yi sallamar ya amsa. A ranta tana fadin “yana cikin damuwar ma ba ya fasa ba da order, order dai! Da kyar nan gaba in bai zama Alkali ba”.
Kusa da shi ta zauna suka zuba ma juna ido, idanunsa sun kada sun yi jajir. Ba ta taba ganinsa cikin rashin nutsuwa irin na yau ba. Duk ya birkice kamar ba shi ba (smart-guy) mai tafiya da imaninta, yau har wani cukurkudewa gashin kansa ya yi ga wani gashin fuska ya karu na babu gaira babu dalili.
“Wai me ke faruwa ne Abdul’azeez? You look worried. You sound worried, ni ma ka dugunzumar min da hankali, da ina da hawan jini na tabbata da yanzu kafin na iso ofishinnan ya hau”. Ta fada a jere ko numfashi ba ta tsaya ta shaka ba.
Tana rufe baki ya ba ta amsa.
“Duk a dalilinki ne Mu’azatu”.
“A dalilina? To me ya faru?”
“Kin yarda ina sonki Mu’azatu?”
“Na yarda, amma me ya kawo wannan tambayar?” Ta fada da hanzari.
“Na tambaye ki ne saboda ki yarda da ni, ki yarda da abin da zan gaya miki babu karya ko yaudara. Ba ni da nufin su gare ki shi ya sa na yanke shawarar gaya miki gaskiyar halin da nake ciki da iyayena a yanzu, kada ki ji a wani wuri daban ki yi wa zancen fassara a baibai ko ki yi tunanin na yaudare ki, amma in muka hada kai muka amince da juna za mu shawo kan mastalar, mu samu cikar burinmu a lokacin da ya dace da burin iyayenki. Kin yarda da ni Mu’azatu?”
Jikinta a sanyaye ta ce, “I trust you ka sani, ko mene ne ka gaya mini zan fahimta. Amma don Allah kada ka ce Mu’azatu ba zan aure ki ba...!!!” Sai hawaye.
Karo na farko da ya yi kuskuren kai hannu ya rungumo Mu’azatu a jikinsa. Nasa idanun na fidda kwalla. How he wish Mammah za ta fahimci karfin wannan soyayyar? Ba zai iya barin Mu’azatu saboda wata mace ‘yar uwarta ba, wadda ya tabbata ba ta da abin da ya fi na Mu’azatun, ba ta fita da komai ba. Sai ma dai ace bata kaita ba.
Ko ma ta fitan shi son da yake wa Mu’azatu (has no reason), wato babu dalili. Abin da ya sani kawai yana sonta, ita ma tana sonshi, ba don uwa-uwa ba ce sai ya ce wannan abun da da ta yi masa zalunci ne. Ba ruwanta da feeling dinsa, ita dai kawai a biya mata tata bukatar. Kwalla mai zafi ta gangaro masa, ya yi saurin dauke ta kafin Mu’azatu ta gani. A lokaci guda kuma ya sake ta ya janyo ta suka kalli juna.
“Ba zan taba cewa ba zan aure ki ba, it’s a promise. Zan aure ki komi runtsi, yanzu dai ki ba ni hadin kai ki ji damuwar tawa, kina kara min damuwa da fitar hawayenki Mu’azatu, bayan na kira ki ne don mu fahimci ta yadda za mu billowa matsalar, ba fa wata gagaruma ba ce (we can overcome it)”.
Mu’azatu ta share hawayenta, ta ba shi hankalinta.
“Mu’azatu, kin san girman iyaye, kin san karfin ikonsu a kanmu, kin san tsattsauran umarnin Ubangiji a kanmu na mu yi musu biyayya, Ya ce (Ubangiji)‘Wa qada rabbuka alla ta’abudu illa iyyahu Wa bil walidayni ihsaana’, Ya kara da cewa, ‘Wala taqul-lahuma uffin walaa tanhar humaa wa qul-lahumaa qaulan-kareema’(Isra’i). A wata ayar ya kara cewa, ‘Daga bautarsa sai kyautayi ga iyaye.......’
Allah (SWA) ya kara cewa ma mu dinga nema musu gafara ko suna raye, kamar yadda suka ji kanmu muna kanana.
‘Wakhfidh lahuma janahazzilli minar rahmati Wa qul rabbir-hamhumaa kama rabba yaani saghira... (Isra’i).
Mu’azatu duka wannan kadan ne daga ayoyin Ubangiji da suka yi umarnin mu zamo masu kyautayi da biyayya a gare su, wallahi Mu’azatu duk da wannan sanin sai da na sa kafa na take, na yi PROTEST (tawaye). Na yi jayayya da su a kanki, na shiga na fita ta wasu hanyoyin duk don in kaucewa umarninsu in tsira da ke.......”
Mu’azatu ta shiga girgiza masa kai alamar, “A’ah”.
Ya ce, “Yes, ban yi nasara ba ai, don haka na amsa wa bukatarsu. AURE za su yi min Mu’azatu da wata macen ba ke ba.....!!!”.
Girgiza kai kawai Mu’azatu ke yi, numfashi na neman dauke mata, tana neman shidewa. Tallafo ta ya yi ya rungume suna amfani da nasa numfashin. Kawai sai ga kira a wayarsa da ke gefe, juyawa yayi a hankali yana kallon sunan da ke yawo a fuskar wayar ‘Precious Mammah’. Da sauri ya saki Mu’azatudon gani ya yi kamar itace tsaye a kansa ta kama shi rike da macen da ba tashi ba, rike da macen da ba su halatta mashi ba. Bayan ture Mu’azatu da ya yi daga jikinsa har dada ja baya ya yi ya sanya rata sosai a tsakaninsu. Hannunsa na kyarma ya amsa wayar Mammah.
“Kana ina?”
Ta tambaya cikin muryarta mai sanyi. Kunuwanta na zuko mata kukan Mu’azatu.
“Ina... ina... office Mam....mah...”
“Idan ka gama da ita, to ka zo ka gana da ita wannan ita ma. I think is high time ku fara fahimtar juna lokaci yana kurewa”. Ta kashe wayarta tare da sakin tsaki, “Me ake da matan bariki? Bin namiji har ofis don rashin mafadi?” Ta fadi cikin bacin rai da tafasar zuciya.
Anya wannan yarinyar ba za ta zame wa Hafsat barazana ba in an yi auren nan? Anya da gaske Abdul’azeez yake zai iya rabuwa da ita? Tunanin da ya cunkushe zuciyar Hajiya Maryam kenan.
Shi kuwa Abdul’azeez a sanyaye ya ajiye wayar, kalaman Mammah tas! A kunnen Mu’azatu, kamar da gayya ma Maman nashi ta fada don ta ji, kamar ta bugo da gayya ne don sanin cewa suna tare a lokacin, ta tabbatar mata da abin da ya gaya mata. Kafin ya ankara sai ganin Mu’azatu ya yi ta kai bakin kofa ta kama ‘handle’ za ta murda. Yunkurawa daya ya yi, Mu’azatu ta ganshi gabanta ya kare kofar, ya sha gabanta. Kokari yake su hada idanu, amma ta ki. Kuka kawai ta ke yi. Ta gama gane irin auren da ake son yi masa, irin na yarinya (sweet 16) din nan da (Proffessional) wanda ya gama mallakar hankalin kansa, to ita zai rainawa hankali? Kamar shi za a yi wa auren dole idan ba yana so ba? Ko macen da ta yi karatu irin nasa ana yi wa auren dole balle shi namiji? Shi ne ya zauna yana tsarata yana jawo mata ayoyi shi ga Ustazu? Da wata makirar Mammansa mai muryar karuwai.
Cikin tsananin fusata ta dube shi, “Ka ba ni hanya in wuce Malam, lest you regret knowing me (don kada ka yi nadamar sanina”.
“Minti goma za ki kara min kacal, zan ba ki hanyar...”
Cikin gunjin kuka ta ce, “Bana son kara jin kowacce kalma daga gare ka, Allah ya hada kowa da rabonsa.....”
Ya runtse ido. Ji ya yi saukar kalaman tamkar digar dalma a zuciyarsa.
“Duk kokarin da na yi da wanda nake yi da wanda zan yi DOMINKI abin da za ki ce min kenan Mu’azatu? A halaka fa zan saka kaina don in tsira da ke Mu’azatu...”
Ta zame kasa, kan gwiwoyinta ta kifa kai tana kuka. Shi ma ya bi ta ya durkushe.
“Wallahi zan aure ki Mu’azatu komai rintsi. Ki barni in yi auren don in zauna lafiya da iyayena. Na yi miki alkawarin na SHEKARA DAYA ne da wasu watanni, lokacin kin kammala BL dinki”.
Ta dago rinannun idanunta jike da hawaye, ta dube shi. Bai iya karya don ya burge ba! Wannan halinsa ne da ta dade da sani. Ba ya yi maka karya don ya faranta maka, kai shi kwata-kwata a halayyarsa babu karya, yana fadin abin da ke zuciyarsa ne kawai ba tare da tunanin zai yi maka dadi ko akasinsa ba. Tana son Abdul’azeez, tana son komai nasa, in ta ce za ta iya barinsa ga wata mace ‘yar uwarta, mai halitta irin tata data tabbata da cewa ba ta fita da komai ba ta fadi ba nauyi. Abin da ba za ta iya ba shi ne, tarayya da wata a son nasa, ko mallakarshi tare da wata.
Sai ta yi shiru da kukan tana goge hawaye, tana hadiyar zuciya.
“Kin amince da abin da na fada Mu’azatu? Zan yi auren, zan rabu da ita a lokacin da iyayenki suka shirya aura min ke, zan aure ki”.
Kallonsa ta yi cikin ido, tana kara jin wutar sonsa na fizgarta, losing him easily is not easy (rasa shi cikin sauki ba abu ne mai sauki ba). Ta samu muryarta na fita cikin tangardar harshe,
“Amma... amma..... ka san ba zan iya hada ka da wata ba ko? Ba zan iya zama da kishiya ba...!”
Girgiza kai ya yi, “Ni ma ba zan iya zama da mata biyu ba. I know... na ce miki rabuwa da ita zan yi in lokaci ya yi, ki yarda da ni, ki amince da kalamaina. Bana magana don in bata lokacin ki da nawa. Ungo hannuna mu kulla alkawari...”. Ya mika mata karamin yatsansa, yana kallon cikin idanunta da yanayin da ta ke masifar so.
Wani tattausan murmushi ya subuce mata. Ta mika nata karamin yatsan, suka sarke su suna jifan juna da wani mayataccen murmushin SO. Sun amince an halicce su ne domin junansu. Don su zama abokan rayuwar juna, babu wata SUHAANAH da ta isa ta shiga tsakanin wannan soyayyar.

*****











To mai karatu, kai ka yarda da hakan? Anya kaddarorin rayuwa suna tafiya yadda muka tsara su ne? Anya Abdul’azeez bai yi kuskure ba? Abin da yake shirin yi me sunansa? Bravity ga Mu’azatu? Dishonestness ga Mammah? Unfairness ga Suhaanah? Ko ko me yake nufi???
****

Mu karasa a littafi na 2, kada ku damu, tare suke. Taku har abada
Sumayyah Abdulkadir
20th May, 2019



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On AUREN KWANGILA
avatar
saratu-7-7

11 months ago

Reply

Auren kwangila complete pls

Please Login or Register in order to submit comment