Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙarfi aikam ya sunkuya ƙasa da sauri dafe da wurin yana sakin ihu mara sauti.

"Ragon maza kawai kana ambatar Brother Sardauna da rago a she kaima layin kake."

"Sadauki tafi kawai nafasa jin amsar."

Yana ambatar haka ya nufi Part dinsa da sauri har da haɗawa da gudu, dariya mara sauti Sadauki ya raka bayarsa da shi yana mai furta "Bana tsafi aminina amma ina iya yin wasu ababe tamkar mai sihiri duk a sanadin zamowana Gombon 'yan biyu kamar yarda ka ambata sannan tare da taimakon Aljanar can mara mutunci."

Yana ambatar haka ya tsare giran sama da ƙasa ya doshi part d'insa rai b'ace tamkar bashi ne ke nishad'i yanzu ba.

***
"Neerah idan muka tafi gidan Dadah kafin mu dawo dare yayi kinga Mami b'ata son tukin dare ga su yaya balle garemu mata, haka Abba zai hukuntamu domin kinfi kowa sanin dokarsa a kan 'yan matan Masarauta."

"Kaini gate din gidan ki juyo kawai Sister."

"Kina son janyowa kanki magana ko Doctor?"

"Gidan Dadah zan kwana ba wani wurin da banba Malama."

"Umurnin Abba ne dole kowa ya kwana gida in har ba gari mutum ya bari ba ko aiki irin naki ya riƙe mutum."

"Idan an tambayeki kice ina asibiti ina da tiyatan dare."

"Ba zanyi ƙarya ba."

"Shi kenan bani motar ki tari napep ki koma."

"Wannan isar ne kuma bakiyi ba sai dai ke ki hau Napep ɗin."

"Lailah ke ɗin ciwon kai ce wallahi, dan Allah ki barni na huta badan na isa ba."

"Bakiga hutu ba tunda kika bari ƙaunar abinda zai iya tarwatsa rayuwarki yayi miki kamun kazar muku."

"Kina cikin yan adawa kenan."

"No, but ina takaicin lamarin."

"Why?"

Sai da ta fesar da iskan bakinta sannan ta amsa "Yaya Sadauki nawa ne zanfi kowa murna da aurenku amma ɓacin ran da zai biyo baya shi ne bana son ji da ganinsa dan haka ki hak'ura da yaya ki kama na gaske mai yi miki ƙauna mara algus."

Lafewa Neerah tayi a seat tamkar mai barci, batare da Lailah ta kula da hakan ba ta cigaba da cewa "Mami zata shiga damuwa sannan Abba zaiyi fushi da yaya in har ya aureki ya saki kamar yarda yayiwa su Mubina kuma mu...

"Ina sonshi a hakan, in yaso ranar da aka daura mana aure ya sakeni, ni kuma zan nuna masa zama da shi yanzu na soma aurenmu mutu ka raba takalmin kaza."

Ta katse Lailah cikin ɓacin rai.

"Neerah ki dawo hankalinki kada so ya rufe miki ido ki kasa gano aibun lamarin, wallahi nafi ki son aurenku amma su...

"Da kata da motar Malama!"

Gefen hanya Lailah ta gangara ta tsaya, Neerah ta nemi ficewa ta yi saurin kulle motar baki ɗaya.

"Buɗe ni ko ranki yafi nawa ɓaci."

"Ina dakon duka tunda daga faɗar gaskiya sai ya zamo aibu."

"Lailah rayuwarki ko nawa?"

"Yours."

"To ki zuba ido zaifi miki."

"Ank'i zuba idon wallahi ko kina so ki ba kya so sai na sanar da ke illar zawarci dan haka bazaki auri yaya Sadauki ba ga yaya Najib nan ya mutu a da ƙaunarki dan haka shi ne zaɓinmu domin munga abinda zai iya ba dan mutuwa tayi masa yankan ƙauna ba da yanzu suna da albarkan aure."

"To Ammi sai ki ɗaukeni ki kaini dakinsa da wannan zantukan banzan kuma ki fita harkata tun raina bai ɓaci ba."

"Macizai ne turosu muga wanda zai afka ɓacin rai ni da ke domin kinfi kowa sani a fannin tankasar muke."

Shiru Neerah tayi tana sauke murmushin yak'e.

'Kai wallahi Lailah fitina ce bata tsoron a mutu.'

"Yes bana tsoron a mutu domin mai tsoron a mutu shege ne."

Idanu waje Neerah ke kallonta jin ta bata amsar zancen da tayi a zuci.

Harara ta zabga mata tare da tada motar da juya zuwa Masarauta, Neerah na kallonta bata tanka mata ba saboda duk tarin rigimanta Lailah ta damata ta shanye. Suna isowa bakin gate Sadauki na fitowa zuwa masjid, tsayawa Lailah tayi tana hararan Neerah dake doka murmushi.

"Daga ina Sisters?"

Ya ambata idanunsa na kan Neerah ba yabo ba fallasa.

"Hanyar gidan Dadah wannan yar rainin hankalin ta juyo bisa dalili mara tushe."

Neerah ta amsa a shagwabe.

Hancinta ya ja cikin sake d'aure fuska, ta saki ƙara ya janye hannunsa yana zabgawa Lailah harara ganin ta yi kamar bata a motar.

"Sorry Yaya bana jin daɗi ne."

Ta ambata da sauri.

"Saboda kina cikin 'yan adawa ba, kin san Allah kada inji kada in gani idan kuma kince wasa ni da ke ne mara kishin d'an uwanta kawai."

Idanu waje suke kallonshi ya ja siririn tsaki ya wuce da kallo suka raka shi har ya haye stairs na masallacin. A tare suka sauke ajiyar zuciya gami da tsirawa juna ido.

"Doctor ke ce kika bashi labari ko?"

"Tunda gani aljana ba."

"Be serious dear Neerah me yasa zakiyimin haka?"

Tsaki ta ja tare da bude kofar ta fice da sauri Lailah ta kunna motar ta zo ta wuceta zuwa ma'adanar motoci ta ajiye ta fito ta cimma Neerah dake daf da shiga falon Momy, hannunta ta fizgo suka kafe juna da ido.

"Sakeni to Uwata."

"Neerah me yasa kika bashi labari?"

"Kin san wallahi zan shuka miki rashin mutunci in kika ƙara zargina da gulma alhalin tare muke ko kira ban amsa ba balle tura sako."

"To ya akayi ya gane ina adawa da ƙaunarku?"

"Ki tambaye shi zaifi da wannan ihu cikin dokar dajin da ba bil'adam balle dabbobi, sannan bai san ina sonshi ba."

"Haka ne kuma fa amma anya yaya baida aljannu?"

"Layinku ɗaya tunda kema kina jiyo zancen zucci."

Hannunta ta matse ta ko kwalla ƙara bashiri ta saketa tana dariya tare da cewa "Ke dallah d'azun zancen zuccinki ne ya fito fili batare da kin sani ba."

"Kanki akeji dai, ni kinga tafiyata inyi dinner da Momy ."

"Uhm da kuma kishiyarki ba, 'yan wahala kawai."

A fusace Neerah tayo kanta ta kwasa da gudu zuwa Part din Ammi tana kyal-kyala dariya. Fasa shiga part din Momy ta yi sai ta sami kanta da nufar Part din Imam kirjinta na harbawa da sauri da sauri. Da Imam taci karo ya fito a gaggauce zai tafi masallaci, koda ta gaisheshi a hanzarce ya amsa ya wuce bayansa tabi da kallo tana son aminta da karatun da ruhinta ke biya mata na fallasa sirrin ruhinta gareshi ko tasamu ya yi mata jagora wurin mallakan Sadauki cikin sauk'i.

'Ki kame kanki Muneerah, namiji baida tabbas.'

"No, daina sanarmin da wannan zancen domin Yaya Yarima mai tabbaci ne."

Ta bawa zuciyarta amsa tare da turo k'ofar falon, Hafsat ta samu na shirya Mimi ganinta yasa ta tsaya tsak ta zuba mata ido cike da mamakin ganinta a sashinta domin shigowar Neerah na biyu kenan tun aurensu, na farko barkan Mimi tazo sai kuwa yau.

"Aunty Hafsat ya da kallo kamar na sanja miki?"

"Borin kunya ko Dr. Neerah?"

"No Aunty nidai bana son kallo ne sai duk naji na muzanta."

"Uhm to sannu da zuwa mai zumuntar ganin dama domin ba zance ni kaɗai kike yiwa haka ba dan har da su Aunty Hassana saboda nasha jin korafinsu akan rashin zumuncinki."

"Ayimin affuwa daga yau zan gyara shi yasa na soma da ke wacce ke kusa da Masarauta."

"To Allah ya nufa hakan."

"Amin."

Ta ɗauki Mimi da ke ta mik'o hannu saboda bata da k'yuya. Cillata sama tayi tako kyal-kyale da dariya sai lamarin ya taimaka wurin sanya Neerah nishad'i ta biye mata sukayi ta wasa, sosai ta yabawa Hafsat wurin tsafta ganin yarda gidanta ke ta k'amshin tare adana komi a muhallin da ya dace ga diyarta mai kyau cikin kamhi mai daɗin shak'a.

"Kawota kije ki ci abinci gashi can na shirya miki."

"Sallah zanyi Aunty."

"Ok shiga bedroom kiyo alwallah, ga k'ibla can."

Motsa kai tayi tana mai bin inda ta nuna mata da kallo. Bayan ta idar da sallah saita dawo cikin falon ta zauna saman Cushing ta lafe tare da lumshe idanu tamkar mai barci.

"Kina tare da damuwa ko Doctor?"

Zubawa Hafsat manyan idanunta tayi fuska kwab'e, mai nuni da k'iris take jira ta fashe da kuka.

"Don't cry Sister, oya sanar dani damuwarki, it may be I have the solution."

"Aunty laifi ne idan ruhi ya samu abincinsa a lokacin da ya ke cike da yunwa?"

"Ba laifi ba ne Doctor domin samun cikar buri kenan."

"To me ya kamata a faɗa masa lokacin da yake burin cika tumbinsa da wannan abincin?"

"Abu biyu a lokaci ɗaya su ne Ci a hankali domin kada ayi karo da tsakuwa wanda zai saka abincin ya fita a ruhin ko kafin a Ci ɗin a tabbatar da an duba babu wannan tsakuwa da zai iya kawo cikas yayin kaishi ma'adanarsa."

"Karin bayani Aunty domin na kasa gano inda kika dosa."

"Manufata shi ne idan ruhi ya samu abincinsa to kada ya sake ya bawa abincin damar shiga ma'adanarsa har sai ya tantance, wata kila zai iya illata shi dan haka ya san me ye nagartan abincin tare da manufar cinsa gami da amfanin da zai samu idan ya ci domin gamsuwar ruhin shi ne dace da abinci mai kyau da ɗanɗano da zai taimaka wurin tafiyar da lafiyar ruhin tare da gangar jiki harma jama'a suyi alfahari da samuwarshi gareka ta hanyar yiwa ruhin fatan dauwama tare da wannan abincin na har abada."

Shiru Neerah tayi tana nazarin zantukan kafin ta dawo tunanin ta tsinkayi muryan Hafsat na ambatar "Allah yasa k'anwata ba soyayya ta faɗa a makance ba?"

Maimakon amsawa sai ta mike tana gyara zaman hijab d'inta tare da jan hancin Mimi wacce ke lumshe ido tana son yin barci ta furta "Good night takwarar Mamina."

"Me kenan?"

"Zan wuce ai nayi miki hira insha Allah zan riƙa shigowa ko da a ƙarshen sati ne ina wasa da diyata mai kama da Yaya Imam sak dan tafiki kyau da iya ado."

Yar dariya Hafsat tayi kana ta ja hannun Neerah zuwa dining tana cewa "Sai kinci abinci zaki tafi."

Kan dole ta zuba ferfesun kayan ciki ɗan dai-dai ta soma ci a hankali nata nazarin zantukan Hafsa mai cike da fikrah.

'Lallai yaya Imam yayi dace da mata mai hangen nesa.'

"Hey Dr. Maida hankali ki daina karatun wasikar jaki wanda ba mai ganin ya rubutun ya ke sai ruhi kaɗai."

Murmusawa tayi tana mai sosa tsinin hancinta tare da gyaɗa kai. Taji daɗin ferfesun duk da baya cikin abinci ta, ta kora da Apple juice zamowarta mara son drinks masu gas, sannan tayi mata sallama ta rakota har bakin fita Part ɗinta tana ta son jin gwaninta amma fir Neerah tak'i bata haske sai zillewa zancen takeyi.

"Ai zanga Lailah ko Maryam nasan su zasu sanar da ni komi idan ke kin k'i buɗemin nayi fatan khairan tunda kun sami yancin zaban abokanan rayuwarku da kanku ba irinmu ba da ko ka zaba b'atawa kai lokaci kayi."

"Uhm nikam Aunty ban tashi yin aure ba yanzu dan haka bana da gwani."

"Samun wuri wato kunga an barku kun balaga kun balallage shi ne har da samun bakin salo? Mu yaushe muka samu gatan nan, lallai Masarauta ta sami canji."

"Kai Aunty kuma fa saida kuka gama jami'a sanan kukayi aure dama dai su Aunty Hassana kika ce su da secondary ma d'akinsu suka kammala."

"Eh da wannan kam amma dai kun fi...

"Good night Aunty yar jarida."

Ta katse Hafsat domin samun damar kufcewa zantukanta da ta lura basa da ranar k'arewa, dukan wasa ta sauke mata a baya ta saki ƙara cike da shagwaba'a zata sake kai mata duka tayi saurin ficewa da dan gudu tanajiyo dariyarta itama dariyar takeyi saboda ta sami nishad'i shigarta sashin. Tafiya ta cigaba dayi a hankali tana kallon taurari da suka k'awata sararin samaniya lamarin da yasa bata ganin abinda ke gabanta domin kanta a amsa take tafiyar hasken taurarin na sake haska ruhinta tana hasko kanta tare da Sadauki suna nishad'i cike da tarin ƙauna. Karo da juna sukayi wanda sam bai lura da ita ba yayin da itama bata san da zuwarshi ba. A tare suka sunkuya ita cike da tsoro shi kuma tunaninsa yaji mata raunine domin kafadarsa ne ya doki kirjinta, gano bataji ciwo ba yasa ya tsare gira yana kallon cikin idonta ya furta "Sannu amm me yasa bakya lura da abinda ke gabanki?"

"Haka ake bada hak'uri tare da tuhuma?"

Itama ta furta fuska a haɗe.

Kunninta ya ja ta saki ƙara ya saketa da sauri tare da mik'ewa ya nufi hanyar Part din Mami Fulani yana cewa "Kingama rainani amma da Ammi zan haɗaki kuma kika turomin macizai Allah sai na tsoma kanki cikin k'oramar Mungaye Garding kifin nan ya tsole idanun rashin kunya."

Lumshe idanu tayi cike da jin madarar ƙaunarsa na kuma cika ruhinta, bata furta masa kalma ba har ya b'acewa ganinta shima ya cika da mamaki jin bata tankashi ba alhalin yasan bata barin ta kwana komin k'araminsa sai ta maida martani musanman idan akansa ne domin ya gano tana d'agawa kowa ƙafa ban da shi marainin wayonta.

Zubkud'a shoulder yayi dai-dai sadda ya sanya kai a falon yana cewa "Nayi sake ta san gadon barcinsa amma zan gyara kurena dana bud'e mata sirrina da ko Imam bai sani ba."

"Waye ita Babana? Kuma meye damuwarka da ka kasa sanar da Amininka amma ka sanar da mace?"

"Mamina Funanin mai mar...

"Amsa naka Babana, wai me yasa ka mai dani kamar Hajiya Dadah ce?"

"Allah sarki grandma na kwana biyu ban lek'ata ba amma in sha Allah gobe zan d'auki mara kunyar can tayimin jagora dan ban iyawa da sababin Hajiya Dadah, Neerah ce dai-dai da ita."

"Allah Babana zan saɓa maka idan baka kiyayarmin tsohuwa ba."

"Kaina bisa wuya Mamina."

"Amsamin tambayana, wacce ita?."

"Mami yawan bincike fa baida kyau, dan Allah ki bari dan ba hurimin kiji sa ba ne."

Idanu ta tsira masa cike da zargi ganin haka ya kariso ya russuna ya gaisar da ita bata amsa ba sai binsa da ido takeyi ya ba'ata rai tare da nufar kujera ya zauna ya tallabe kumatunsa.

"Babana kada ka sake mace ta zamo abokiyar sirrinka idan har ba matar aurenka ba ce."

"To Mami."

"Ina saurarenka ka ce zamuyi magana akan Companies."

Gyara zama yayi cike da natsuwa ya soma koro mata bayanen cigaban da Companies d'in suke kan samu sai motsa kai takeyi cike da alfahari da ɗan nata, a ƙarshe ta sanya albarka tare da bashi shawarwari da zasu sake bunk'asa kasuwancin nasu zamowarta wacce ta sami ilimi akan kasuwanci.

Gyaran murya Mami tayi ya kalleta da sauri ta jinjina masa kai tare da soma magana "Babana kai ne tamkar Uba ga k'annenka a d'akin nan to ina baka shawara da ka guje aikin da mutuncinka zai zube kar wata rana su k'i yi maka biyayya, kaga yanzu Junaid da Jabir sun taso har sun kai minzalin aure domin a wannan lokacin Mai Martaba ya ce zasu fitar da mata, nan da lokaci kaɗan Allah zai basu rabo ya zamo 'ya'yansu ne manya a maimakon naka, dan Allah ba dan ni ba ka fitar da matan aure kayi tare da zama da su bisa igiyoyin shi tun ƙasa bai rufe idanuna ba, kaji Babana domin aure shi ne matakin cikar kalama."

Ta kai ƙarshen maganar idanunta na cikowa da ruwa.

"Zanyi aure Ammi dan Allah kada kiyimin kuka, wallahi zanyi a cikin tsakanin nan, ni dai fatana ki duba lamarin kada ki juyamin baya kinji Ammina."

"Ka sanja magana Babana domin ba zan amince da wannan maganar ba."

"Ammina na tuba, wallahi ba zan baki kunya ba."

Banza tayi da shi ya cigaba da yi mata magiya tamkar zaiyi kuka.

***
Neerah kam ta sami lokaci mai tsawo duk'e a inda Sadauki ya barta sai doka murmushi takeyi tare da bitan karatun ruhinta tana ƙara dilmiya cikin kogin ƙaunarsa.

"Hey Sis Neerah dama ina nemanki ido rufe."

Kallonta ta sauke kan Zuhrah wacce taci uban kwalliya tamkar zata party. Numfashi ta sauke tare da kauda kai gefe tana jin haushin ganinta saboda tunowa da tayi itama na son abinda take so.

"Please Sister zaki iya taimakona?"

"Me ke damunki?"

Ta ambata tare da mik'ewa tsaye fuska a haɗe.

"Makahon so."

"Me kike nufi?"

"Ciwon so ya kamani kuma ke ce hanyar samun maganinsa."

"Like how?"

"Ki taimakeni badan na isa ba sai dan shaƙuwar da ke tsakaninku da wanda kaf yaran Masarauta ba wanda ke sakewa da shi sai ke kaɗai shi ne nake neman tallafinki da ki sanar da shi sak'on karatun ruhina wato Yaya Sadauki cewa shi ne zaɓin ruhin Zuhrah mai cike da burin mallakanshi ita kaɗai dan har na sanar da Mamma shi ne zaɓina dan haka idan ya sami labarin ya amince na zamo abokiyar rayuwarshi ko da bai shirya sake yin aure yanzu ba nayi masa alk'awarin zama da shi har ƙarshen rayuwata domin da sonshi na rayu, zamowarshi auri saki bai dameni ba dan shi ɗin nake muradin ganin na amsa sunar mijin Zuhrah."

Da taimakon a'uziyya da Neerah ta riƙa ja tun soma maganar Zuhrah a cikin ranta yasa shedanin dake buga gangar kishin hauka a zukatan mata yasa bai rabeta ba, badan haka ba tabbaas da ba abinda zai hana bata kwashe Zuhrah da maruka marasa irga ba.

Momyn Haske ne.🥰

*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabiban Tsibiri
By Mrsjmoon.

Adabi Writer's Association.

14.

"Dan Allah Dr. Neerah ki taimakeni na sami amincewar yaya Sadauki domin shi ne muradina mahad'an ruhina a bisa igiyar aure."

Sabbin zantukan Zuhrah suka dawo da Neerah hayyacinta, sai da ta saita kanta kafin ta soma magana cike da kamewa "Kiyi hak'uri, Muneerah bata cikin sokayen matan da so ke kaisu aikin zubar da k'ima dan haka kai tsaye bazan iya taimakonki ba, hausawa suka ce iya ruwa fidda kai, tunda kin iya kamuwa da ƙaunarsa ai banjin tunk'ararsa domin fayyace masa karatun ruhinki zai zamowa abin wahalarwa ba da har sai kin kama ƙafa da ni saboda tsaban kin rainamin hankali, foolish girl, mitcheww!."

Ta kai ƙarshen maganar ranta a mugun b'ace tana maijin tamkar zuciyarta zata faso k'irjinta saboda zugi da takeyi maka.

"Hey Malama me ye na b'ata rai har da zagin cin mutunci daga neman alfarma."

"Kanki a jeji sokuwa kawai kuma wallahi kada ki sake tarana da wannan maganar banzan idan kuma kina son ranki ya ɓaci ne to ki sake jaraba tarana da maganar."

Daga haka tayi gaba, duk da Part dinsu taso tafiya amma sai ta nufi Part din Mami Fulani tama haɗa hanya domin bata ganin gabanta sosai. Ita kanta mamakin zafin da ta ɗauka akan maganar Zuhrah takeyi, anan ta sake gasgata ƙaunar da takeyiwa Sadauki. Tana shiga suka d'ago suka zuba mata ido da sauri ta sauke kai ƙasa ta iso gaban Mami ta zauna gefen ƙafanta ta riƙo hannunta tana sauke numfashi da sauri da sauri.

"Lafiya kike kuwa Muneerah?"

"Mami ina s...

Sai kuma ta fashe da kuka ta mik'e da sauri ta nufi d'akin Lailah, ta faɗa saman gado tana cigaba da rera kuka tamkar wacce akayiwa dukan tsiya domin tanajin idan batayi kukan ba jininta zai iya hawa.

"Babana jimin wani shiri-rita dai."

Shafo sajensa yayi cikin jin rashin daɗin ganinta a damuwa, ganin Mami na dakon cewarsa sai ya saita kanshi ya tab'e baki ya ce "Ita ta sani ai, tunda ita ba yarinya ba ce sannan tafi kowa sanin illar jefa kai a damuwa dan haka ki barta har sai ta sakko da kanta tanemi kiji damuwarta amma dan Allah kada ki saka kanki a sokancinta hawan jininki ya motsa."

" A she baka da imani Babana?"

Da sauri ya kalleta ta zabga masa harara zaiyi magana ta d'aga masa hannu "Gara da hakan ya faru na gane waye kai, daga yau Jabir ko Junaid zan soma kira baya goya marayu, Ubannin k'annensu ba kai ba."

"Mami wai me na...

"Sai da safe Babana zan tafi jin damuwar d'iyata yanzu bazan fahimci tatsuniyar nan naka ba."

"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, wai me nayi da zafi ne haka Mami?"

Tashi ta yi ta barshi da baki buɗe. Sosa goshinsa yayi cike da mamakin zafin da Mami ta ɗauka akan abinda bai kai ya kawo ba. Maimakon ya tashi sai ya gyara zama ya jingina da Cushing d'in da ta tashi sautin kukan Neerah nayi masa amsa amsa kuwa a cikin kunni hakan ya ƙara dagula masa lissafi inda ya tashi da sauri ya nufi wurin da zuciyarsa keyi masa jagora, tura k'ofar yayi a hankali idanunsu ya sarke da juna wacce take lafe a kafad'ar Mami na taping bayarta da ido yake tambayarka me ke damunta tura baki tayi tare da lumshe ido, k'ofar ya ɗan buga saboda ya lura Mami b'ata san da shigowarshi ba dan ta bama k'ofar baya.

"Babana ko maciji ka zama ka shigo a silale kana tunanin ba zan san da isowarka wuri ba ne?"

"Mami affuwan na janye kalamaina."

"Ya wuce Babana amma ga kanwarka nan ka tabbatar da ta sanar da kai abinda ya sakata kuka."

Daga haka ta fice, da ido suka raka bayanta sannan suka kalli juna na seconds, Sadauki ne ya d'age mata hira cikin tambayar kurame na meye damuwarta. Harara ta cilla mashi tare da hayewa saman gado ta rufe jikinta da bargo har saman kanta.

"Kin hutar da ni yanzu zan tafi in sanar da Mami kishin wanda baisan kina dakon son shi ba kikeyi."

Ai kafin ya rufe baki ta diro daga gadon ta cukumeshi ta baya tare da fashewa da sabon kuka mai sauti wanda ya janyo hankali Mami ta shigo a hanzarce ganinsu haka sai ta nuna Sadauki da yatsa cikin gargad'i batare da ta furta kalma ba. Murmusawa yayi ya janyo Neerah ta dawo gabanshi ya kalli Mami dake cillo masa harara ya kauda kai tare da cewa "Kiji tsoron Allah Doctor N ki sanarmin da gaskiyan damuwarki in har ba akan kishi ba ne"

Duka ta soma kai masa a k'irji ya kalli Mami ta watso masa dak'uwa tare da barin wurin ganin Neerah bata lura da wucewar Mami ba sai ya saki Murmushi mai sauti tare da janyota ya jefa cikin k'irjinsa ya matse da ƙarfi dan ji yake tamkar ya tsaga k'irjinsa ya tura ta cikin zuciyarsa.

"Wash! my boobs."

Ta ambata tana mai son kubcewa.

Sassauta riƙon yayi mata ta zame ƙasa ya bita suka zauna saman rug, ta tura kanta tsakanin cinyoyinta sai lamarin ya bashi dariya, ya kai bakinsa daf da kunninta ya hura mata iska ta zabura ta mike tsaye ya nunata da yatsa nayin dariya mara sauti mai bayyana cikar kamalarshi a fili.

"Yaya Yarima me ye haka? Allah bana so."

"I love you so much Dr. N, do you love me?"

Idanu waje take kallonsa ya tsare gira tamkar bai taɓa dariya ba ya sake maimaita tambayeshi cikin dakon jin amsarta, tayi tsit kanta sunkuye tana miƙa godiya ga Allah na jin furucin bakinsa.

"Baki so na saboda na zamo mai sauri saki ko?"

Da sauri ta d'ago ta zuba masa idanunta har lokacin ta kasa furta kalma, girgiza kai yayi cike da damuwa kana ya mik'e da sauri ya fice tare da bugo k'ofar da ƙarfi.

"Your are stupid Neerah."

Ta ambatawa kanta hakan tare marin fuskanta cike da takaicin barin damar da ta samu ya kufce mata.

"Amma ai kunyarshi naji."

"Kunyar Babana ko saurayin da kike kishi?"

A firgice ta kalli Mami ta gyaɗa mata kai cikin rashin walwala tare da shigowa d'akin ta kamo hannunta suka fito ta nufi ɗaya daga cikin d'akunar barcinta.

"Shiga kiyi wanka ki fito mu kawo ƙarshen maganar munafuncin nan taku."

"Kaina ciwo Mami kuma barci nake ji kuma walalhi bamuyi munafuncin komi ba ki yarda dani Mamina."

"To kwanta zuwa gobe mayi maganar kuma ki tabbatar da gaskiyan ruhinki zaki sanarmin domin ta nan ne zan gane abinda ya kamata inyi akai duk da ba'a son raina lamarin ya zo a haka ba."

Kai ta motsa tana kulle ido sanyin ac na son saukar mata da zazzaɓi sannan ruhinta cike yake da

Please Login or Register in order to submit comment