Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ina magana kana kallon k'ofa tamkar warkewar makanta."

"Abba anyi lafiya?"

Ya sami kansa da furtawa.

"Alhamdulillah Imam."

Ya amsa tare da mik'ewa ya nufi d'akin barcinsa ganin su Imam nata mazurai ya ce idan sun shirya magana da shi su sameshi a ciki dan bai shirya kallon shirmensu na fama ba.

"Kai Sadauki ban son iskanci wato Ofin naka har kanka amininka zai sauka?"

Imam ya ambata cikin fushi.

"Tashi muje ko ranka ya b'aci."

"Ban zuwa sai na bada labarinka da Aljannu."

"Zakuwa ka zama bebe nan bada jimawa ba, tunda baka ji magana."

"Aliyu me kake aikatawa a b'oye? tsafi ko me?"

"Amsa wannan mara jin magana kawai."

Aikam kafin ya ankara wani dum ya shiga kanshi ya tafi luw zai fad'i Sadauki ya tare shi zuwa jikinsa tamkar walk'iya suka suka b'ace daga falon. Tun Mai Martaba na dakon shigowarsu har ya gaji ya tashi ya shiga toilet ya d'auro alwalla ya zauna gabatar da azkar d'in marece cikin rashin damuwa da lamuran shiri-ritansu domin sunar da ya bawa lamarin kenan.

***
TSIBIRI.

Tsidau ya sauka a wani tsauni mai yalwan bishiyoyi wanda suka taimaka wurin ƙara duhun da tsauni ke da shi, amfani ya yi da haskensu na junnu ya cike tsaunin da haske sannan ya samu hango Tsibirin da ke nema wato fadar Ifritu Baushe wanda ya zamo Bil'adam amma yafi Aljani shed'anci ta ko wani fuska shi yasa ake yi masa lak'abi da sunan mugayen Aljannu wato Ifritu.

Tsibirin sai fitar da bak'in hayak'i keyi hakan ya ƙara munana dutsen da ya zamo fadar Baushe, ƙasan dutsen kuwa wuta ne ke ci cikin fitar koren harshe, da ganin wurin zuwarsa sai an shirya baga Bil'adam ko Ajani ba.

"Lallai ka ci sunarka Baushe domin ko a itatuwan daji, itacen Baushe ba mai saukin k'onawa ba ne kamar yarda na ke hango shiga fadarka ba mai sauk'i ba ne."

Tsidau ya ambata yana nazarto yarda zai shiga fadar domin ganawan sirri da Ifritu Baushe akan uwar gijiyarshi Lina.

Bai samo mafita ba ya jiyo ruguji a bayanshi bai waiwayo ba ya buɗe zafin hannunshi domin sanin me ke faruwa, wani dutse ne ke fitar da wuta ya nufoshi irin dai wanda ya so halakashi a fadar Kaka Gunu kwanakin baya. A gigice ya juyo tare da neman hanyan tsira sai dai ya makaro domin dutsen ya cimmasa ya bangajeshi a take ya cillashi ƙasan tsaunin inda ke kai inda farin hayak'i ke fitowa mai kama da tafiyar giragizai a sararin samaniya. Kafin ya sauka ƙasa yaji anyo sama da shi wani iska mai ƙarfi ya nashe idanunsa. Bayan wuce mintinan da basu wuce biyu zuwa uku ba ya ji an saukeshi ya zabura sai ya yi ido biyu da Ifritu Baushe, ya bushe da dariya mai fitar amo tamkar cidan hadari ya jima yanayi kafin ya dakata ya soma yiwa kan sa kirata...

"Sai ni Baushe mugun itace, Baushe mai hayak'in masifu, Baushe bai san na gida ba tunda ya zamo ajalin ubanshi mahaifi, Baushe k'i sabo dan ko hadimansa bai d'awa ƙafa ba, ko ank'i ko amso sai nayi mulkin sarkin sakakunar Aljanu da Mutane."

Ya dakata yana kallo Tsidau da ya koma tamkar d'an tsako a gaban giwa.

Momyn Haske ce 🥰

Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon.

Adabi Writer's Association.

12.

" Ya kai Tsidau amintaccen bawan Sadauki Gauɗu da Gimbiya Lina ni Baushe k'i sabo na san buk'atarka sai dai ka makaro domin nima hanyar nake nema tsawon shekaru tun kafin a haifi Uban mahaifin Gauɗu domin Zoben na Kakan Uba na ne aminci yasa ya sadaukarwa Kakan Sadauki Gauɗu na huɗu, Ubana, ya yi bakin iyawarshi yaga ya mallako Zoben ya dawo a halinmu saboda shi ne yafi k'ulafucin mallakan Zoben tun sadda ya sami labari a wurin aminin mahaifinsa amma ya kasa hasalima ya kasa tun k'arar inda Zoben yake ajiye, da wannan baƙin cikin ya rayuwa to bayan na girma na fahimci burin Ubana sai dai bincikena ya tabbatarmin sai na kashe shi na sha jininsa sannan zan soma taka k'amshin mallakan sihirtaccen Zoben sai na aikata hakan a wani dare da muka fita na koyar da ni sanin alk'alaman tsafi sai nayi amfani da dmar na halakashi na shanye jininsa tare da nad'e duk alk'aliman tsafinsa. Dama ni kad'ai na rayuwa cikin 'ya'yansa, Uwata ta mutu bisa cin amanarta da yayi inda ya sadaukar da ita duk bisa neman hanyar Mallakan Zoben.

Daga nan ban koma gida ba na nausa cikin daji na yi ta neman ilmomin sihiri kuma duk wanda na k'aru da shi to nine a jalinsa a haka na haɗu da gawurtaccen matsafi wanda ya haskamin amfanin da Zoben sihirin zaiyimin kana ya riƙe ni tsawon shekaru har zuwa sadda aka haifi uban Sadauki Gauɗu daga nan ya mallakin duk kan tsafinsa tare da hadimansa dangin hatsabiban aljannu da mutane wanda suka maidani Ifritu na zamo k'wan jimina gagara ɗaukan Shaho, na gagari har da su kansu hatsabiban shed'anun alhjannu da mutane na zamo tamkar ba zan mutu ba domin bana jin zan bar Duniya sai an hura k'aho tamkar yarda aka halicci aljanu haka nake jin kaina domin naga zamanai na matsafa daban-daban, ni kuma an kasa ganin nawa "

Ya bushe da dariya wacce bishiyoyi suka soma rangaji suna busar da iska mai ƙarfi.

'Hak'ik'a Baushe yafi ƙarfin hilata dole na samo mafita domin tsira da rayuwata kada na ƙare a yi masa bauta.'

"Tabbas Tsidau daga yau kazama hadimina, dole kayimin bauta tamkar yarda wanda suka fika komi suke k'asan ikona in kuma ba haka ba dole ka amince da sharad'ina akan shugabanka Gimbiya Lina."

"Sanarmin inji me ye sharad'in? Dan ba a yoni domin bautawa azzalimi irinka ba."

Wani dariya ya sake bushewa da shi domin abu mafi yi masa daɗi shi ne a ambata masa kalman zalinci.

'Duk da nayi biyayya ga zantukanki Gimbiya da ban kasance a wannan wuri mai cike da hatsari ba.'

"Ka natsu Tsidau domin zantukan zuccinka ba zai amfaneka da komi ba."

"Ina sauraren sharad'in naka."

"Idan na ambata dole sai ka amince da shi, kai ko ban ambata ba amincewarka wajibi ne."

"Ina sauraronka ya Sarkin Sarakunar Aljannu da Matsafa."

Ya ambata cikin ladabi.

"Hilarka ba zaiyi tasiri a wannan Fadar ba ya kai Tsidau garama ka ajiye kalaman yaudararka wata k'ila gaba za suyima amfani."

"Sanar dani buk'atarka ya Ifritu Baushe."

Wannan karan cikin rashin tsoro ya ambata.

"Da kyau Sadauki Tsidau, to maza buɗe masu jinka ka saurari bayanina wato kawomin Lina fadana tare da Zoben sihirin dake tare da ita, a daidai lokacin da ta sanya ya zamo nine mutum na farko da zanyi ido biyu da ita bayan kai."

"Ko zan san dalilinka na neman hakan?"

"Cikar ikona ba zai samu ba sai Gimbiya Lina ta zamo ɗaya daga cikin Matana ta haifamin yarinya mai kama da ita na sha jininsa to daga ranar burina zai zamo tabbatacce ita kuma zan kasheta da hannuna bayan na sha jinin 'yarta a gaban idonta."

"Ba zan yarda a kashemin uwar d'aki a irin wannan kisan wukak'ancin ba domin nayiwa Jarumi Gauɗu alk'awarin kula da ita har ƙarshen rayuwata, dalilin da yasa kenan na zo Fadarka samun wani ilimi da zai bani damar hanata saka Zoben sihiri saboda sakashi mutuwarta ne ya kusanto."

"Tabbas ni ne ajalinta kuma wannan bayanin shi ne ya buɗe maka kake hango mutuwarta sannan tunda ka saurari manufata cikamin aiki dole ne ko in ɗauko iyalanta na halakasu a gaban idonka, in na ce iyalanka ina nufi kaf zuri'arka zan tiso k'yeyarsu."

'Tirk'ashi na kawo kaina gidan jafa'i da masifa."

"Ko baka kawo kanka ba za'a kawomin kai domin na soma gadinka tun sadda Sadauki Gauɗu suka soma faɗa da Ubanshi akan Zoben."

"Ko zan san abinda yasa tun a lokacin baka nemo Gimbiya Lina ba?"

"Bata da abin so ne sai sadda Sadauki Gauɗu ya sadaukar mata da tsafinsa to a lokacin ta shigo cikin k'omata dama ina jiran zuwar ranar domin tun kafin a haifeta nake da tabbacin a hannunta zan sami cikar burinsa."

"Shugabata ba zata zo fadarka ba domin nasha jin tana ambatar tsanar azzalimi, tana adawa da mulki irin naka hatta kuwa da irin mulkin Babanta, tabbaas tana da burin kawo ƙarshen irinku a doron ƙasa dan haka ban san ta yarda zan faɗa mata ta zo gareka ba."

"Dole ka zamo maci amana idan zaka yimin aiki dan bana harka da masu gaskiya gami da tausayi ko Lina domin zan amfana da ita ne amma da yaƙi ne zai rabani da ita duk da ina hango wani al'amari na tun ƙarota wanda ya b'oyu gareni dan haka zan barka ka huta ga abin more rayuwa nan sai wanda kaga damar amfani da shi zan dawo gareka bayan kwanaki biyu sannan a lokacin zaka tafi kazomin da Gimbiya Lina ko ta wani hali sai ka wanzu cikin nemo mafita ina sake sanar da kai cin amana shi ne matakin tsirarka daga hannuna."

Daga haka ya b'ace Tsidau ya fad'a kogin tunani daga haka wani barci ya sureshi wanda rabonsa da yin barci har ya manta domin baya cikin jinsin aljannu masu barci.

***
Lima ta fito daga gidan shak'atawa bayan ta halaka samarin da suka d'ebe mata kewa ta kuma b'atar da su tare mantar da jama'ar mashaya lamarin wanda ta saba aikata hakan duk wanda ya kusanceta to bai kai labari sannan ba wanda zai sake neman d'ansa wannan sa'ar ta sameshi ne daga Kaka Gunu domin duk wanda ta b'atar yana zamowa arzikin Masarautar ne inda kuɗi zai ƙara taruwa a baitul mali sannan mafi ƙarancin mutanen da ta ke halakawa a duk sadda ta ziyarci mashaya to mutum biyu zuwa uku ne saboda zamowarta mai ƙarfi sha'awa, wannan hali nata na ciwa Gaimbiya Lina tuwo a k'warya har da shi ya zabura da ita ta fita nemo ilimin tsafi domin kawo ƙarshen k'adarin 'yar uwan nata.

Cikin Izza Lima ta cigaba da tafiya tana fatahi da duk wanda taci karo da shi a hanya, kafin ta isa gida ta raunata jama'a masu yawa ciki harda tsoffi, shi yasa ba wanda ke son yin karo da ita, ƙaunarsu naga Gimbiya Lina. Muhallin Mahaifiyarsu ta nufa tana ƙara haɗe rai. Ta sami Mah zaune gaban bangon ɗakin tana hira da Gimbiya Lina wacce ke kwance saman ruwan Tekun Kabobo, jikinta babu kayan kirki, fatarta sai ɗaukan ido keyi mai nuni da hutu ya gama ratsata. Mah na ganin Lima ta shigo ta kirawota da hannu ta iso gabanta tana gabgowa Lina harara yayin da ita ke murmushi cike da nishad'i.

"Lina ga Lima ku sasanta bana son rabuwar kanku kunji 'yan biyuna, farin cikina?"

"Ni kam Mah ina sonta ita ce bata sona."

Lina ta ambata a hankali.

"Eh bazan taɓa sonki ba, munafuka kawai, mai fuska biyu."

"Kin jita ko Mah?"

"Kiyi hak'uri Lina, 'yar uwanki mai zafi ce komi zai wuce zanyi magana da ita domin yaɗuwar kanku nake buƙata sama da komi yanzu."

"To Mah ni na wuce zan tafi ceton rai a wani kogi, ga jirjin ruwa can na shirin faɗi da mutane ciki."

"Nasara na tare da ke ya ke 'yata."

"Godiya nake Uwa abin farin 'ya'yanta.

Daga haka ta b'ace daga jikin bangon Mah ta fuskanci Lima cikin tsuke fusaka ta ce "Daga yau ban son nasake jin kin ambaci tsana ga 'yar uwanki idan kuma kika sake zan nunamiki wacece ni sannan bana son zuwa mashaya da kikeyi shi ke janyo miki tsana ga Jama'ar Tsibiri domin hatta da mahaifinku baya son abinda kike aikatawa, kiyo koyi da 'yar uwanki zaifi miki khairan ko kya samu damar hawa karagar mulkin Tsibiri wanda ya ke babban burinki."

Sai a nan ta saki rai jin ta ambaci hawa mulkin Tsibiri ta dawo gaban Mah ta zauna tana wani langab'ewa kana ta ce "In har kina sona da mulkin Tsibiri to kije d'akin Abun ki tsareshi kada ya biyoni domin mallakan gadona na wurin Kaka Gunu."

"Kunfi kusa Lima ki rok'eshi ya bar maki kayanki."

"Ba zai bari ba Mah domin shima na burin mallakan Ruwan Albarkan."

"To ki gyara mu'amalanki da Lina na san zata taimakeki ki mallaka."

"Idan itama burinta na ta mallaki Ruwan ne fa?"

"Zata bar miki domin adala ce kinfi kowa sanin hakan."

"To zan nemeta mu sasanta."

"Haka na ke son ji 'yata."

Juya kai gefe Lima ta yi tana haskowa ruhinta wani mugun nufi akan Lina sai ta saki murmushi tare da hayewa gadon Mah ta kulle ido ganin haka yasa Mah ta fice zuwa turakar mijinta wannan damar Lima ta samu ta mik'e ta shafi bangon da Mah ke hira da Lina sai kuwa ga Lina ta bayyana saman dutsen kogin Babobo iska na kad'a gashinta na rufe mata fuska tana yayewa.

"Ya akayi Lima? Na san zaki nemeni shi yasa na tura Tsidau ya taimaki mutanen girjin na dakata jiranki, ina saurarenki."

"Ki zo ki taimakeni na ɗauko gadona a Bukkan Kaka Gunu."

"Zan zo amma ba yanzu ba sai Abun ya taho nemana dan haka ki nuna mashi kin hak'ura da gadon hakan zai bashi damar barin Tsibiri a sirrance domin yanzu yafi buƙatar mallakan Zoben dake gareni akan ruwan albarkan."

"To sai kinzo ina da abinyi."

Murmushi Lina ta yi tare da mik'ewa ta kalli Lima ta ce "Zan zo mu kwana tare yau sannan zan baki labarin da kike nema na cikin jikina da wanda yayimin."

Cike da zumud'i Lima ta buɗe baki zatayi magana Lina ta d'aga mata hannu tare da b'acewa a take bangon ya dawo yarda ya ke. Dafe kanta ta yi cike da takaicin b'acewar Lina. Ta fito zuwa d'akinsu dake saman wani dutse daga gefen turakar Mahaifinsu.

***
Mah na shiga turkan mijinta ta fahimci yana d'akin sirri sai ta sami wuri ta zauna ta tsirawa wani taswira ido wanda sai a yau ta ganshi a turakan sai ta shiga mamakin lamarin abinda ya ɗauki hankalinta har ta shagala da kallonsa sai ta soma ganin tamkar ta koma wani wurin ba turakan take ciki ba, mik'ewa tayi dan isa gaban Taswiran sai taga haske na fitowa daga cikinsa da ta matsa sosai sai taga hanyace ta buɗe daga cikin Taswiran sai taja da baya cike da tsoro amma sai taji ana janyota sai ta soma tattaro tsafintata dan amfani da shi sai dai ya kasa tsiri wurin bata kariya, ihu ta soma dan neman taimako amma sai muryanta ya daina fita illa ita ɗaya takejin fitar kayanta, tsawon lokaci ana son jefata cikin Taswira ita kuma tak'i shiga duk da tsafinta ya k'i aiki sai dai tun can ita ɗin mai ƙarfi dantsen ne.

Mah ta jigata iya jigata har ta sare, ƙafarta na hagu ya soma shiga hanyar inda takejin hucin zafin wuta na dokar ƙafar. Sauka wani abu taji dif!! Kafin ta tantance meye iskan guguwa ya nad'eta ya jangota. A take Taswiran ya nad'e kansa ya b'ace b'at, bangon ya koma tamkar wani abu bai taɓa zama ba.

" 'Yata Lina."

"Na'am Mah, kwanta ki huta nadawo Tsibiri bazan sake barinki ba ko da hakan na nufin ajalina ne."

"Me ke faruwa Lina?"

"Mah cin amana yayi yawa, zalunci ya kewaye duniya ya zamo har da na jikinka za'a cuceka."

"Waye ya so aikatamin mugun abun nan?"

"Mah saninsa tarin damuwa ce gareki amma da sannu zaki san ko waye ke farautan rayuwarki domin ya sami cikan burinsa na samun Duniya."

"Lina taho na runguneki."

Ba musu ta iso gaban mahaifiyar nata suka rungume juna, hawaye na zubowa daga ida uwarsu na sauka a gadon bayan junarsu.

"Zan sanja miki wurin zama mai cike da tsaro Mah."

"A'a Lina ki barni a nan mahaifinku garkuwa ne gareni."

"Idan shi ne ke son halakaki fa?"

"Ba zai taɓa faruwa ba Lina, duk tarin zalunci mahaifinku ba zai taɓa sadaukar da abinda yafi so sama da komi ba dan haka ki barni tare da shi tunda kin dawo ba abinda zai sameni."

Janye jikinsa Lina ta yi batare da ta sake furta kalma ba, ta soma zagaye d'akin zuwa can ta tsaya ta dubi Mah ta ce "Ina da aiyuka a gabana wanda ban san adadinsu ba kuma ban san mai taimakamin ba haka ban san ranar kammalasu ba."

"Ki sassautama kanki lamaura ya ke 'yata kada na rasaki."

"Mah banzo duniya dan samun hutu ba, ina cikin matsala tunda nace zan saka Zoben can mai makon naga lamura nayimin sauk'i sai sake rikicewa sukeyi shi yasa nake neman amincewarki da ki yarda na nesantaki da Tsibiri na wani lokaci in komi ya daidaita sai na dawo da ke saboda zamanki anan barazana ne a gareni domin za'a taɓamin ke dan a sami galaba a kaina, Mah ki amince na maidake saman Tekun Kabobo na killaceki ko kogon da gangan jikin Sadauki Gauɗu ke ciki nayi miki alk'awarin zuwa ganinki kullum dan ɗebe miki kewa haka komi kike so na dangin abinci da bin sha zaki samesu."

"Lina kincemin fa kin dawo Tsibiri to me yasa zaki ɗaukeni a cikinsa ke ki zauna."

"Na sanar miki da hakan ne dan hankalinki ya kwanta amma ban dawo ba."

"Lina ba inda zanje."

Tamkar zata fashe da kuka take duban Mah sai kuma ta zabura ta nufi k'ofar fita tana cewa "Mah zan dawo anjima kada ki sanar da kowa zantukanmu ko da kuwa Abun ne ko Lima."

Kafin Mah ta yi magana ta fice a gaggauce, hawaye ne suka zubowa Mah na tausayin rayuwar da 'yarta ke ciki domin tana burin rayuwa da 'yarta a kusa da ita tamkar yarda takeyi da Lima.

"Lina dole ki janye son hawa karagar mulkin nan ko na samu kusanci da ke kamar can baya."

Mah ta ambata cike da tarin damuwa.

"Mah."

Da sauri ta waigo Lima ce tsaye.

"Kin haɗu da 'yar uwanki Lima?"

"A'a, shin ta zo ne?"

"Eh."

"Me ta sanar da ke?"

Batare da tuno gargadin Lina ba ta sanar da Lima duk abinda ya faru tundaga zuwarta turakan Abun har tafiyar Lina.

"Ina zuwa."

Itama ta fice da sauri tana fita ta yi girgiza sai ga Abun ya bayyana fuska a murtuke.

"Hak'ik'a Lina kina da wayau dole na san waye Sadauki Gauɗu kafin na mallaki Zoben sirihin hannunki ta wannan hanyar na basaja tabbas yanzu zanyi fito na fito da ke duk da ba hakan raina ya so ba."

Ya ambata cike da ɓacin rai.

Ba jimawa Buda ya isa saman ingarman dokinsa Abun ya hau ya zabura cikin takon dake motsa ƙasa zuwa can ya d'aga sama tamkar tsuntsu ya b'ace cikin gajimare.

Lima da duk abinda da ya afku akan idonta ta shiga mamakin lamarin sai kuma ta saki murmushi tare da shigewa d'akin Mah ta isa gaban bangon da Mah ke hira da Lina ta shafa take kuwa Lina ta bayyana cikin shigar yak'i fuskanta babu d'igon annuri lamarin da ya razana Lima domin bata taɓa ganinta cikin ɓacin rai irin wannan ba tun tasowarsu.

"Me ke faruwa 'yar uwa?"

Lima ta jefo mata tambayar a rikice.

"Ya wuce ɗaukan tunaninki Lima, ni dai ina son ki kulamin da Mah, kada sakacinki na yawon zuwa mashaya ya janyo na rasa Mah, domin in hakan ya faru na rantse da ruhin Sadauki Gauɗu sai na illata rayuwarki ki zamo baki da mamora balle ki sami damar zuwa timb'ele a mashaya."

"Kada kiyimin barazanar da har abada nafi ƙarfin sa kawai ki sanar dani abinda ke faruwa ko ina da halin taimakawa akai."

"Ki kula da Mah shi ne kaɗai taimakon da zaki iyayi."

"Kin san shirin Abun kenan?"

"Eh wanda hakan na nuni da rayuwarsa na daf da zuwa ƙarshe."

"Me kike nufi?"

"Zan tafi idan na dawo zan sanar da ke komi batare da kin tambayeni ba."

Sai kin dawo amma ki sani ba zan zauna gadin Mah ba tunda ba dan shi na zo duniya ba."

"Shi kenan na barki lafiya amma ki kwana da sanin rasa Mah tamkar nak'asarki ce, wata ƙila makanta, kurumta ko gurgwanta sai kiyi nazarin abinda zai fish-sheki domin tabbas sakacinki yasa na rasa farin cikina wallahi kema kinyi ban kwana da naki farin cikin. Ki kula da Mah shi ne ƙarshen umurnina gareki Lima."

Kafin Lima ta yi magana bangon ya dawo yarda yake tamkar komi bai wanzu ba a mugun fusace ta fice batare da ta kula kiran da Mah ke yi mata na kula da ita ba dan ta shiga rud'anin kalaman Lina har tayi da ta sanin k'in binta da tayi.

Bukkan Kaka Gunu Lima ta nufa ta shige batare da samun tangarda ba.

"Zannuna miki ni ce shugabanki Lina kuma magajiyar karagar Tsibiri, a yanzu banjin ko Abun zaifini ƙarfin iko balle ke 'yar tsako abar tausayi."

Ta na rufe baki dutsen dake Bukkan ya dare biyu wata gawurtacce mikiya ta bayya ta iso gabanta ta zube tare da rikida zuwa mutum maiji da Sadaukantaka ya russuna cikin cewa "Barka da zuwa magajiyar Tsibiri shalelen mai gida Gunu, raina fansa ne gareki ya ke uwar gijiyata."

"Waye kai?"

Ta ambata cike da izza duk da tana kokwanto ko Tsidau ne ya sanja salon yaudara.

"Ki kwnatar da hankalinki ba mayaudari Tsidau ba ne a gabanki wannan amintaccen Hadimi ne sunana Mutuwa babban hadimin Kaka Gu...

Ai kafin ya k'arasa zancensa Lima ta fice Bukkan a guje lamarin da ya janyo Mutuwa ya bushe da dariya a take Bukkan ya soma motsi tuno illar da dariyarsa zai iya haifarwa ga Tsibirin sai yayi gaggawan tsuke bakinsa amma duk da haka saida wata dunk'ulalliyar Guguwa ta fice ta rufawa Lima baya ya so bin guguwan ya dawo da ita amma ya kasa saboda aikinsa iyaka kula da cikin Bukkan ne da kuma tulun ruwan albarka.

*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.*

Momyn Haske ne 🥰
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon

Adabi Writer's Association.

13

Guguwar ta wuce Lima ta nausa cikin Tsibirin inda ta soma b'arna domin duk wanda taci karo da shi nad'eshi takeyi ta yi yaga-yaga da namansa ta watsar. Kafin 'yan mintoci tayi mugun b'arna musanman ga tsoffi da ƙarfinsu ya ƙare. Kuru-ruwan da ke tashi ya cika ko ina a Tsibirin yasa Mah fitowa domin ganin abinda ke faruwa saidai bisa tsau-tsayi Guguwan ta yi karo da ita wacce ta juyo domin komawa inda ta fito bisa arangamar da tayi da matsafan Tsibiri suka haɗu suka dakushe tasirinta shi ne ta juyo a fusace sai Mah ta faɗa komarta. Cikin kiftawar ido tayi awon gaba da Mah, ganin haka ya sanya Lima kwalla ƙara da ya haddasa zubowar ganyan-yaki daga jikin bishiyoyi, a take suma suka rikid'e zuwa guguwa mai karfi wanda ya doke wacce tayi barna, suka watsu cikin al'umma suka soma illata ganinsu.

***
MUNGAYE.

"Sadauki banda Ofi da ka gada zamowarka Gambon 'yan biyu har da tsafi kake haɗawa?"

"Imam tafi wurin iyalinka am not in good mood gobe zamuyi magana."

"Kasan Allah ban wucewa sai ka amsamin tambayata."

"Nacinka yayi yawa Imam."

"Naji kome zaka kirani, ina dai jiran amsarka."

Tsaki Sadauki ya ja tare da dukan goshin Imam da

Please Login or Register in order to submit comment