Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ke riƙe da shi tun dazun kana ya saki ya iso daf da Neerah ya rage murya ya ce "Iyayi kawai to ban gode ba."

"Gobe ma rana ce da Muneerah kake zancen ɗan Samari."

"Mamie 'yarki ta rainani fa."

Ya ambata cikin kawo mata duka ta gofce.

Banza Mamie ta yi masa sai ya fice yana cije lips gami da nuno Neerah da yatsa cikin salon wasa ya yin da ita kuma keyi masa gwalo. Murmusawa Mamie Fulani tayi domin abinda ke saurin sakata farin ciki shi ne ganin walwala a fuskan Sadauki Aliyu.

"Ke kuma taho naji damuwarki da kika tahomin da idanu kamar jan nama."

"Ciwo sukemin Mamiena."

"Kika sake ambatarmin k'aryan nan sai na saɓa miki."

"Affuwan Mamie kaina ke ciwo kuma kin san ban da juriyan ciwo ko kaɗan, shi ne nayi kuka Ammi ta koroni wai na dameta da jan hanci kada in saka masu mura ita da yaranta."

"Ayya sannu, kyale Nana ai ciwo na kan kowa, taho kisha magani domin na san halinki na gaba da magani wai kina Likita amma kina gudun magani, Allah ya kyauta kam."

Cikin murmushi ta iso ta zauna gefen Mamie tare da manno jikinta da ƙafarta, sai ta dafa kanta cike da kulawa take yi mata sannu kana daga bisani ta bawa Lailah umurnin ɗauko mata maganin ciwon kai a d'akin barcinta, cikin dibara Neerah ta gudu kafin Lailah ta dawo ta nunawa Mami a biyota da shi dakin Lailah saboda abinda Neerah ta tsani shansa shi ne magani.

***
Hajiya Umma ta ya kika yi wannan waftar na fed'ewa Sardauna biri har wutsiya shin kin manta waye shi akan gaba da bin bokaye? To wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki ki sanja dabara domin ina da tabbacin bazamu taɓa samun haɗin kansa ba tunda kinayi waftar sanar da shi gaskiyan lamarin da muke kai."

"Ki bari kawai Hajiya Kilishi wai a zatona in yaji Aljana na tare da Sadauki zaifi yin farin ciki tare da bamu haɗin kai har mu kai ga nasara."

"Kin manta har kwanar gobe suna fita rangadi tare domin ginuwar ƙaunarsu kuma ƙaunar da mai Martaba ya dasa a zukatansu bai taɓa gogewa sai dai zan sanar da ke hanyar gaskiya domin kawo nak'asu a ƙaunarsu shi ne sai mun tashi tsaye mun sa an raunatashi yarda zasu zamo basa ga maciji ko kaɗan shi ne zamuyi nasarar ɗora shi akan turban da muke so haka game da son kud'insa sai anyi mana aiki ta yarda kome kika nema ya baki batare da kai ruwa rana ba tunda yana da dukiya kuma ba mai amfana da shi sai makirar matarshi da uwarta ke kuwa sai hange daga nesa to sam hakan ba mai yiwuwa ba ne, yarda kika sha wahalar haihuwar sa gami da rainon sa dole ya zamo ke ce ta farko da zaki mori dukiyarsa tare da sanin duk kan bayanen ƙaddarorinsa."

"Tabbas kinyi gaskiya Hajiya Kilishi, zantukanki masu amincewa ne gareni, yanzu zan baki wuk'a da nama ki zamo idanuna na kai da kawo tsakanin lamarin saboda yawan fitana a b'oye nada hatsari dan idan Mai Martaba ya sani kashina ya bushe wata k'ilama aurena ya sami tangarda tunda angama da shi bai kallona da daraja sai muguwar Fulanin can wacce ba zata gama lafiya ba."

"Kibari kawai, gata bata jin Asiri."

"Kin manta waye Uwarta kenan? Ai Hajiya Dada cikakkiyar matsafiya ce domin maganar Malam Sale kenan duk in ya buga ƙasa Uwarta na tsaye kanta shi yasa sai yarda tayi da Mai Martaba."

"Aikam na yarda Hajiya Dada na tsafi domin dubi zafin Chiroma amma a gaban Nana Safiyya sai ya koma fulawa saboda laushi."

"Uhm ai ƙarshen su ba zaiyi kyau ba in sha Allah."

Allah ya amsa."

"Amin Aminiyata."

Murmushi Hajiya Kilishi tayi sannan ta maida hiran kan abinda suka zauna a kai, inda cike da kisisina take cewa "Dama ina shirin yi miki wannan maganar fitar da kanki sai nayi nazarin a wakilta Hud yana amsowa tare da sanya Sardauna amfani shi wanda ba sai ya zo hannunki ba kinsan Hud da iya kalaman makirci na tabbata cikin sauk'i zai sakashi yin amfani da maganin hankali kwance, kinga ko wanda zaici a abinci ne duk Hud zai bashi saboda in muna son ya sami farin jinin jama'a sama da wanda Sadauki ke da shi dole sai mun hada na ci a abinci da sha da wanka har da hayak'i."

"To ba matsala hakan za'a yi, zan turo maki sak'o anjima amma kada a amso na hayak'in nan saboda zai harbo jirjinmu."

"To madallah, bari in koma kada mai gidan ya neme ni."

"Yau ke ce da turakar kenan."

"Eh fa."

"Ok tafi nima ina da baƙi anjima kaɗan."

"To na wuce, Allah bamu yinin lafiya."

Motsa kai Ummu tayi cikin lumshe ido dan kanta taji na ciwo, harara Hajiya Kilishi ta zabga mata ta gefen ido tana zund'enta a fakaice sannan ta buɗe k'ofar ta fice cike sak'e-sak'en yarda tsarinta zai tafi batare da samun tangarda ba na ganin d'anta Hud ya haye karagar mulkin Mungaye tunda shima Babansa ɗan Sarki ne yana da sarautar da zai iya Mulki ba sai lallai 'ya'yan Sarkin dake kan karagar mulki ba

"Wallahi bana son Sadauki domin tuni na kamla rabashi da Masarautar baki ɗaya lokaci nake dakon ya yi a nemeshi a rasa daga ganan Hud ya zamo Sarki mai iko domin bazan bari Sardauna ya zame masa matsala ba a tafiyar ba."

"A'a Mamma ina mutuwar son Yaya Sadauki kuma shi nake burin gabatarwa Abba a matsayin zab'ina kamar yarda kuke dakon jin gwanina sannan ina tare da ke kan zamowar yaya Hud Sarki saboda lokaci ya yi da za a kawo sauyi ba lallai sai 'ya'yan Sarkin dake mulki ne zasuyi ta gadon sarautan ba, duk da a gefe ɗaya ina jin kamar ba zai iya ba dan ban taɓa jin mashayi ya hau karagar mulkin Mungaye ba."

A razane Hajiya kilishi ta dubi inda mafi soyuwar 'yar nata ɗaya tilo mace cikin 'ya'yanta maza huɗu. Gyara tsayuwa ta yi tare da jinjinawa mahaifiyar nata kai alamun bata tabbacin furucinta tare da cigaba da cewa "Yes Mamma ina yin Yaya Sadauki kuma shi ne mijina da yardan Allah dan na k'udiri aniyar d'aura d'amarar jure zama da shi a duk yarda ya ke, ni ce zan kawo ƙarshen auri sakinsa insha Allah"

'Wata sabuwa inji 'yan ca-ca, hak'ik'a aiki ya sameni ni jikan Magaji.'

"Momma muje nasan baki rasa shawarar da zaki bani akan auren sannan kada ki kushemin zab'i a kan abinda ya ke zanen ƙaddararshi ne wato auri saki."

Dafe kai Hajiya Kilishi ta yi tana jin wani mak'ak'in d'aci na sauka saman harshenta.

'Tirk'a haka zakiyimin Zuhra? To wallahi ko zaki mutu ne ba ki isa hanani kora Sadauki duniyar da bazai kuma waiwayen Masarauta ba.'

Ta sake ambata cikin ranta tana dallawa bayan Zuhra harara wacce take shirin shiga d'akin barcinta.

***
"Hey Doctor Neerah, me ke faru ne har ya sakaki kuka?"

Motsa yatsunta Neerah ta yi tamkar zata furta kalma sai kuma ta tsuke bakinta tare da hayewa saman gado ta juyawa Lailah baya.

"Dan Allah Muneera sanar dani damuwarki ko in had'a ki da Mamie nasan ita zaki sanar da ita."

"A'a Lailah kada kiyimin haka, yanzu taso muje ki rakani gidan Hajiya Dada."

"Asibitin da kikace zaki shiga fa?"

"Na fasa."

"No ki muje na rakaki domin ba kyau saɓa alƙawari."

"Na tura masu Dr. Hassana harma ta isa kinga sak'on da ta turomin yanzu."

"Ok amma gaskiya kada ki sake irin haka tunda kin san ke suka fi buƙata."

"In sha Allah."

Suka fito bayan Neerah ta gyara fuskanta ya yi kyau suka sami Mamie zaune hadimai kewaye da ita suna yi mata hira cike da sakewa zamowarta mara girman kai irin na mafi akasarin matar sarakuna. Bayan sun amsa gaisuwar hadimai sai suka sanar da ita inda suka nufa ta tsare gira kafin tayi maga Neera ta rigata da cewa "Please Mamina gidanmu na biyu zan kai ziyara fa Allah daga nan ba inda zamu wuce kinsan halinmu.."

"Muneera bana son yawo ne alhalin kuna 'yan manyan gida musanman yanzu da ake maganar aurenmu"

"Mamie dubo fa sanyin idaniyarki zamuyi ba yawo ba sannan baza mu wuce awa biyu ba zamu dawo in sha Allah."

"Ok to shiga kitchen ki wuce mata sak'onta dama Junaid yanzu zai kai mata kun hutash-sheshi kam."

"A'a Mamie suyi tafiyarsu inyi tawa da Maryam dama na ce ta shirya zamuje gidan tsohuwar Mamie ziyara.

"Mun huta kam."

Lailah ta ambata cikin murgud'awa Junaid baki, ya kawo mata duka ta koma bayan Mamie tana dariya.

"Affuwa dai Yarima Junaid."

Kuyangi suka ambata cikin girmamawa kansu sunkuye.

Hannu Mamie ta d'awa su Neerah suka fice sunayi mata godiya yayin da Junaid ya dubi wata kunyanga ya bata umurnin da ta d'auko masa sak'on a kitchen, ta wuce da sauri tamkar zata kifa.

"Bi a hankali Dudu."

Mamie Fulani ta furta cikin kulawa saboda yarda ta ke daraja d'an Adam, ko zaman kuyangi a sashinta na dole ne dan zamowarta matar sarki amma tafi son ta kasance daga ita sai 'ya'yan dana al'umma sosai take tausayawa bayi shi yasa wad'anda ke sashinta suke jin daɗi fiye da wanda ke sashin Umma da sauran matan masarautar kuma hakan ya ƙara mata k'ima a idanunsu da zuri'arta dama duk wanda ya ziyarci sashin to zaka samu kuyangin na karrama duk bukatun sa.

Momyn Haske ce 🥰

*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI.
By Mrsjmoon.

Adabi Writer's Association (AWA)

https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks 🖕

Page 11.

Su Lailah na fita wajen Masarauta Neerah ta doshin Mungaye Garding maimakon gidan Dada da ta ce zasu.

"Dr. Ya dai?"

"Nafasa zuwa can muje Lambu saman Lilo."

"Lilo kuma? Yau ke ce ki ke ambatar hawa Lilo?"

"Eh Ina son tuno da wani yanayi ne da ya wuce."

"Ikon Allah, anya ba soyayya kika faɗa a gofce ba Sister?"

Bata amsa ba ta tura hancin motar cikin garding dogarawa masu gadin gate ɗin suka soma mik'o gaisuwa hannu suka d'aga masu kawai suka wuce. Can kusa da filin motsa jiki ta yi parking suka fito zuwa wurin Lilo sula hau suna motsawa a hankali. Neerah ta yi lum idanu lumshe fuskanta cike da murmushi, ita dai Lailah da kallo take binta cike da mamakin sauyin yanayinta daga mara walwala zuwa mai walwala daga hawa saman Lilo.

"Uhm in tayi wari maji."

"Me ne?"

"Komi da kike b'oyemin."

Wani murmushin ta sake cika fuskanta da shi, Lailah ta kaiwa cinyarta duka ta buɗe ido da sauri tana shafa wurin batare da tayi yink'urin ramawa ba, cike da mamakin hakan Lailah ta kamo hannunta tana cewa "Me ke faruwa Neerah da za a yi miki abu ki hak'ura batare da kin rama fiye da yarda akayi miki ba?"

Bata kula ta ba illa ta sake lumshe ido tana motsa Lilon da ɗan sauri

***
"Imam ina cikin damuwa domin a yau ina jin k'aunar d'iya mace sama da komi sai dai k'alubalen da na ke hangowa na son dakushemin k'warin guiwar da nake da shi na tunk'arar yarinyar."

"Buɗe min lamarin bana son wannan kwane-kwanen Malam."

Rintse ido Sadauki ya yi tamkar ba zaiyi magana ba zuwa can ya buɗe ido yana fuskantar Imam cikin serious tare da yin ƙasa da voice kana ya ce "Ita ce nake hangowa zata iya hak'uri da lalurata, ita ce zata b'oyemin sirri, ita ce jinin jikina gaba da baya dan haka ina jin k'aunarta domin zamowarta mai bani kariya tun sadda na fuskanci ina da lalurar haka ita ce ta fi kowa fahimtar lamuran da na aikata ƙaddarata ce ba son zuciyata ba, shin me wannan karamcin gareni da me ta dace a wurina?"

Shiru Imam ya yi domin bai ɗauka jiran amsarshi Sadauki ke yi ba.

Duka Sadauki ya sauke mashi a arm ya kalle shi da sauri yana shafa wurin.

"Uhm answer please."

"Au wai tambayata kakeyi daman? Ai nazaci duk cikin tsarin salon labarin ne."

"Wato ka maidani mai zancen kihayoyi ko? Thank you."

Yana ambatar haka ya mik'e ya shige bedroom ya bar Imam da baki buɗe.

"Anya Sadauki baida shafan aljannu kuwa?"

Imam ya furta cikin tsirawa k'ofar d'akin da Sadauki ya shiga ido. Ba jimawa ya fito cikin sport ware ya d'ora alkyebba saman su ya wuce ta gaban Imam cikin takun k'asaita.

"Uhm sarauta ba k'arya ba magajin Gobe."

Jiyowa ya yi cikin tsare gida ya motsa lips a hankali ya ce "Mu haɗu a filin motsa jiki inkaga dama."

"In kuma ban gani ba fa?"

Cije lips Sadauki ya yi kamar zaiyi magana sai kuma ya fice da sauri.

"Aliyu rigima, ai sai ka sanar da ni abin da ke damunka tunda A har zuwa Z, ina sane nake nuna ban gane yarenka ba, fatana Maryam ce kakeyiwa wannan k'aunar tabbas dana tayata murnan na dakon k'aunarka da tayi tsawon lokaci."

Mik'ewa yayi zuwa dakin barcin Sadauki ya sanja kaya zuwa na motsa jiki kalan da Sadauki ya saka wato white da rashin red, ya sako jallabiya mai hula akai ya fito sai ya sami Sadauki tsaye a bakin k'ofa yana jiranshi dukan wasa ya sauke masa a kafad'a ya dalla masa harara aikam ya kawo hannu kamar zai tsole idon ya yi saurin kauda kai.

"Au ashe Sadaukantakar na bogi ne tunda har d'iya mace ta iya raunata hamshak'in basarake kamar Aliyu Baban Mamie Fulani shalelen Mai Martaba Professor Ab...

"Malam ya isheka wannan shiriritan in zaka zo muje, kaji damuwata kazo in kuma neman magana zaka tsaya sai ka sami wurin zama ga guzirin paper can a saman bola ka d'auka kayi ta rubutu."

"Wato na zama mahaukaci kenan?"

"Kusan haka."

"Ni dalla muje kada Matana ta nemeni."

Wani mugun kallo Saduaki ya wurga masa ya ko kwashe da dariya domin ya rama mai dashi mara aikinyi da ya yi cikin sauk'i.

"Inaga zanyi hijira daga Masarauta domin samo mafita da kaina batare da masu mata sun tsomamin baki ba."

"Sorry Aliyu muje naji damuwarka da fatan ina da mafita."

"Malam na fasa sanar da kai zan nemi mafita da akai ko wurin Muneerah."

"Haba Yallab'ai yaushe kafara shawara da k'annenka kuma mata?"

"Tun sadda ka zama mai iyali."

"Oh ya rabbi affuwan Sadauki kafahimceni ba da wata manufa na ambata maka hakan ba sai dan in rama abin...

"Is ok nasani wasace, oya wuce muje Aminin sirri tun yarinta."

"Nagode Sarkin Gobe."

"Allah ya amince hakan ɗan uwa."

"Amin."

"Mubi ta baya bana son bi ta babban gate su dameni da kirari."

"Ok amma ka sani matsayinka ne ya kai."

Bai kula ba uka jera Imam natayi masa magana cikin rad'a shi kuma na gyad'a kai tare da murmusawa, zuwa can Sadauki ya kawo masa naushi ya yi saurin tarewa, jinjina Sadauki ya yi masa cikin sake faɗad'a murmushinsa.

"Yes jiya ba yau ba boss, ko ka manta mun halarci makarantar koyon dambe a b'oye da muke Japan?."

"Imam ina jin wata rata sai kayi sub'ul da baka ka tona mana asiri a Fada, mu shiga uku da masifar Abba Chiroma."

"Kai Allah ya tsare wannan rana na shigarmu karejin haƙoran Abba Chiroma."

"To Amin dai."

Suka murmusa tare da shigewa garding, batare da b'ata lokaci ba suka yi shirin soma buga wasan basketball.

"Za'a ga wanda yafi zira k'wallaye araga, idan har ka wuce ni ko da tazarar ɗaya ce to ka can-canci sauraren damuwata inko na wuceka da good 5 goal to Muneerah ce zataji damuwata, do you agree?"

"Yes."

"Ok let start."

Ya cillawa Imam ball ɗin, ya ko cafe suka soma wasan cike da k'warewa. A cikin mintoci k'alilan Sadauki ya yiwa Imam 5 one. Cikim dariya ya dakata yana cewa "Ina baka tazarar biyar ka tashi daga aminin sirrina Dr Neerah zata maye gurbinka, right?."

"No Aliyu mu bar wasan da ba zai fish-shemu ba, taho muje bakin k'orama ka sanar dani damuwarka kuma na yi alk'awarin fitar da kai hanya mai b'ullewa tamkar dai yarda na saba."

"A'a taho mu cigaba da wasa ina jin nishad'in buga kwallon."

"To ni na gaji sai kayi kai kad'ai ko ka kira Doctor Neerah sabuwar Aminiyarka."

"Eh gani a kusa ai zan tayashi tafi kayi hutawarka Yaya Imam."

Neerah ta ambata tana mai buge ball d'in a hannun Sadauki ta rungume.

Idanu suka zuba mata ta rausayar da kai tare da zare ƙaramin hijab ta cillawa Lailah sannan ta b'alle abayarta, ta bayyana cikin best iyaka cibiya da gajeren wando da ya matseta wanda ya tsaya iya guiwarta, ta ajiye ball ɗin ta tubke gashinta sai reto yakeyi saboda tsayinsa sai ta fito tamkar yar wasan na zahiri.

"Oya taho mu soma na baka tazara fiye da wanda ka bawa Yaya Imam."

Ta ambata cikin ja da baya ta soma buga ball d'in cike da k'warewa.

Kallon Imam ya yi yaga ya tsira mata ido, wani harbawa k'irjinsa ya yi ya zabura yayo kanta a fusace, aikam sai ta zille da ball ɗin kafin ya kamota ta daka tsalle ta cilla sama ya zabura ya buge balla din tare da hannayenta tayi baya zata fad'i ya tarota ya jefa a cikin k'irjinsa ya matseta da k'arfi, ihunta ya fito tare da nashi inda shi ya furta "Bani rigarta Lailah!"

Kafin Lailah ta d'auko Imam ya miƙa masa ya fizga tare da rufa mata sannan ya sake ta ya juya baya ya kare ta yana mai bata umurnin ta suturce jikinta. Jikinta a sake ta sanya sannan ta iso gefensa ta tsaya ya kalleta idanu jajur lumshe nata ta yi sannan ta juya ta soma tafiya ya riko hannuta ya matse ta kallo ƙara ya kalleta cikin kaushin murya ya ce "Wannan shi ne karo na farko da zan sake ganin kina bayyana tsiraicinki tunda baki da tunani sokuwa kawai."

Ya cillar da hannun ya nufi inda alkyabbarsa ya ke ya saka ya nufi bakin k'orama ya faɗa ciki tunjim!!.

Duk suka zabura saboda sautin ya razanasu.

"Nima abinda zan sanar da ke kenan dan Allah kada ki sake aikata hakan Neera, ko ba komi ki tuna matsayinki na 'yar Masarauta kuma mai tarin sani ga addini."

"Baza ta sake ba Yaya Imam."

Lailah ta ambata a hankali. Motsa kai ya yi ya nufi bakin k'oraman cike da tarin tambayoyi game da abinda Sadauki yayi wanda bai taɓa aikata kwatan-kwacinsa ga d'iya mace ba wato rungumarta cikin nuna tsan-tsan kishi.

***
"Muje ko?"

Girgiza kai ta yi.

"To me zaki tsaya yi tunda giyan k'aunar ya kaiki aikata abinda baki taɓa yi ba."

"Me na yi Lailah"

Neerah ta furta cikin rawar murya mai nuni da tana daf da fashewa da kuka.

"Ni taho muje kada ki sake bada kanki har ki shafamin."

"Ya gane ina son shi wai?"

Tafi Laila ta sanya gami da fashewa da dariya lamarin da ya dawo da Neerah hayyacinta ta dafe goshinta cike da takaicin fallasar karatun ruhinta.

"Nagano karatun ruhinki Sister sai dai abun da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa haka fagen da 'yan hamayya sai kin nemi makaman ya k'i domin Zuhra da Maryam na cikin filin dagan."

"Maryam? Wacce Maryam?"

"Maryam tamu k'anwar yaya Imam d'iyar Momy da Abba Sarkin Fada."

Wani dum taji, jiri ya ziyarceta tayi baya zata fad'i, daidai Hud ya iso wurin sai ya tareta da sauri yana ambatar sunan Allah, lumshe ido tayi tana nanata sunar Maryam aminiyarta itama na son Sadauki domin sam jin Zuhrah na ciki bai d'aga mata hankali ba.

Ruwar da taji an fesa mata a fuskan yasa ta buɗe ido tana sakin ajiyar zuciya, tundaga saman sumar kansa ta soma kallonsa har ta dire a fuskanshi wanda ke d'igan ruwa.

"Yaya Yarima."

Ta furta a saman lips d'inta tana sake lumshe idanu.

Harara ya zabga mata tare da fizganta daga hannun Hud ya nuna mata hanyar waje "Maza ku b'ace min dagani tun ban karya ku ba kuma daga yau na haramta muku sake shigowa lambun nan sai da izinina, idan kuma kun isa in sake ganin sillayen ƙafafunku cikinsa."

Da sauri Lailah ta ja hannun Neerah suka fice, wacce jikinta yayi mugun sanyi.

"Malam ba da haka ake nuna k'auna ba ka natsu mu buga game d'in duk da ba ni kad'ai ke cikin 'yan wasan ba, Ni, kai, Sardauna wata k'ila har da d'an korenka Imam na ciki ko da yake na san kai baza ka haye ba saboda warin kashin kajin dake manne da kai na auri sa...

"Ya isheka Hud bama son rashin tunani, dan haka ka kiyaye kalaman da zai sake fitowa a harshenka."

"In ank'i fa?"

Kafin Imam ya bashi amsa Sadauki ya janyo hannunsa na girgiza masa kai alamun kada ya sake magana, tsaki ja tare da nuna Hud da yatsa alamun gargad'i sannan ya biyo Sadauki na bambamin faɗar bai son hanashi gogewa masu kawo masa raini hadda da keyi.

***
"Aikin banza da wofi wallahi sai na zama sarkin Mungaye ko da hakan zai zamo fansa ne ga ruhina."

"A she muna da yawa masu fansar da ruhunan namu akan hawa karagar mulkin Masarauta Mungaye."

A razane Hud ya kalli inda maganar ya fito ya yi raba da Salis d'an Babban Dogari kuma d'a ga Jakadiyan sirri.

"Ai wai cin dank'o har da su Kaza?"

"Eh sai dai na wuce Kaza sai Jimina."

"To mu zuba shege ka fasa."

"Tam zaka sha mamaki kuwa."

Saboda takaici Hud bai sake magana ba ya bar wurin, Salis ya rakashi da harara daga bisani ya ɗauki Basketball d'in ya soka bugawa shi kaɗai cike da nishad'i.

***
Nagaji Imam! Nagaji na ce! Wallahi zanyi hijira, zan tafi inda ba wanda zai sake jifana da kalman auri saki sannan auren ma na fasa yinsa, ka zamo shidata insha Allah ni da aure har aba...

"Kul! Baban Mamie, kada ka sake ka shiga hurimin Ubangiji, auri saki na cikin zanen ƙaddarar ka dan haka kada ka yanke k'auna daga samun rahamar Ubangiji, ka sama ranka zakayi aure kuma zaka rayu da matarka batare da saki ya shiga cakaninku ba."

"Banjin hakan zai tabbata gareni ba Imam."

"Na ce ka saka a ranka zakayi aure ka yi rayuwa tamkar yarda kowa keyi."

"Ta yaya hakan zai faru, alhalin wancan shed'aniyar na bibiyan bad'ini da zahiri na, shi yasa zan koma inda babu mutane na k'arasa rayuwata hankali kwance."

"Aliyu ka dawo hankalinka, wai me ke damunka ne?"

"Damuwa mai tsanani."

"Nasar da ni Please."

"Not now Imam domin baka da abin magancemin shi."

Yana ambata ya mik'e ya shige dakin barcinsa ya murza key.

Cike da tarin damuwa Imam ya fice domin tunda yaga Saudauki ya kulle kansa ya tabbatar ba zai taɓa saurarensa yanzu ba dan haka cikin Masarauta ya nufa, direct turakar Mai Martaba ya nufa yana addu'ar samun nasara a k'udirinsa wanda ke hasko samun yayewar damuwa ne ga
Amininsa.

'Tuni na jima da sanin kana tare da aljannu, In banda aljana ta aureka taya zaka riƙa zancen ganinta a zahiri d bad'ini, kai wallahi da sake ba wanda ya isa taɓamin amini ya kwana lafiya ko da kuwa Aljan ne.'

Shigowar sak'o a wayarshi yasa ya katse masa zantukan zuccin da keyi ganin daga Sadauki ne sai ya waigo ya kalli volcany ya hangoshi tsaye hannaye rungume a k'irji sai ya maida kallonsa ga sak'on.

"Ban amince ka sanar da Abba komi ba domin baza su fahimta ba, ka tafi wurin iyalinka zaifi maka."

Kallon inda Sadauki ya ke ya sakeyi har lokacin na nan tsaye sai ya girgiza masa kai tare hawa barandar sashin Mai Martaba, wayarshi ya soma ringing sai ya maidata silent ganin Sadauki ne ke kiranshi, yana zama gaban Mai Martaba ko gaisar da shi baiyi ba sallamam Sadauki ya doki kunninsa waigowa ya yi a razane domin bai isa ya iso da hanzari haka ba duk kuwa saurinsa.

'Anya aljannu ba su maidamin da Amini jinsin su ba?'

"Imamundeen ya dai kake kallon k'ofa?"

Murza idanunsa ya yi babu Sadauki tamkar yarda ya gansa cikin 'yan sakonni da suka wuce.

"Uhm kana lafiya kuwa?"

Ya katse masa tunani.

Maido kallonsa kan Mai Martaba ya yi kafin ya furta kalma ya jiyo Muryan Sadauki na gaisar da Mai Martaba.

"Au ka ce tare kuke shi

Please Login or Register in order to submit comment