Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Haske ce 🥰

*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon.

AWA.

Page 9.

Bata amsa ba ta cire wayar a kunninta ta mik'e da kyar tana rangaji cike da izzar mulki gami da tarin damuwa.

Falo na musanman da suka saba sirri Umma tayiwa Mama Kilishi jagora suka zauna a saman manyan kujerun alfarma da suka k'awata matdakaicin falon, bayan sun kulle k'ofa, Mama Kilishi ta dubi Umma cikin son jin k'arin bayani domin ta zak'u taji abinda ke faruwa.

***
Sadauki

Motsawa ya keyi a saman lilon a hankali idanunsa lumshe, hannayensa zube saman goshinsa, sanye yake cikin kayan motsa jiki sky-blue sun manne da farar fatar shi, iskan da ke busowa daga bishiyon lambun ya taimaka wurin ƙara nutsawarshi cikin zurfin tunani, inda ya ke hango kyaky-kyawar fuskanta da surarta tana jifarshi da shu'umin murmushin da ta saba amfani da shi wurin birkita masa lissafi yaji kamar zai haukace a cikin buk'atuwa.

Daga nesa take hangoshi ta dauki mintoci biyar bata dauke idanunta akanshi ba zuwa can ta ja siririn tsaki tare da watsa masa mugun harara wanda baisan tanayi ba, har ta zauna a inda ta saba zama domin yin nazarin akan abinda ya shafi aikinta na kiyon lafiya sai kuma ta mik'e ta nufo inda ya ke nan ma ta dauki mintoci uku tana kallonsa batare da ya sani ba, nazartowa da tayi ya yi zurfi cikin tunani wanda tabbas zai iya zamowa barazana ga lafiyar yasa ta matsa gabansa ta motsa yatsunta biyu suka bada sauti mai ƙara ya motsa cikin kamewa duk da ya tsorata da jin sautin amma jarumta irin nasa ya hana tsoron baiyana a fuskanshi.

Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai tare da jan ƙaramin tsaki yana maijin tamkar ya rufeta da duka saboda katse masa yanayin da ke ciki na shagaltuwa da kallon Aljana domin bad'ini da zahiri sunar dake ambata mata kenan Aljana dan ta can-canci sunar dubi da yarda shi kaɗai ke iya ganinta.

Nuna halin ko ina kula da yayi mata ya tunzura Dr. Muneera inda ta yi nufin barin wurin cikin zafin nama ya fizgota ta dawo gabanshi tamkar zata faÉ—a jikinsa ta yi nufin ja baya cikin ambaton a'uziyya ya sake janyota gabansa yana auna mata harara.

Murmusawa ta yi domin ta gano abinda ya keson ji daga bakinta wato ban hak'uri dan zuwarta wurin har ya zamo abin laifi.

"I'm sorry Yaya YS (Yarima Sadauki)."

Sakinta ya yi ya koma yarda ya ke ya cigaba da motsa lilon. Kasa tafiya Dr Neera tayi ta gyara tsayuwa ta kafeshi da manyan idunta na gado domin zuri'ar Masarautan k'alilan ne basa da manya idanu masu burgewa.

"Kina son ranki ya b'aci ko Doctor N?"

"No."

"To b'ace a wurin nan."

"Saboda me?"

BuÉ—e idanu yayi ta rausayar da kai ya tsare gira tare da cewa "Ina buk'atar kaÉ—aici, zaki iya tafiya domin ban nemeki ba, shin ko nazo ganin likita ne?"

Bata amsa ba illa takowa da tayi ta zauna gefensa ta rike ƙarfen lilon da kyau saboda zamowarka mai tsoron hawa Lilo tun tana ƙarama. Ta soma motsa lilon a hankali kamar yarda ya keyi, sake lumshe ido Sadauki ya yi yana jin wani yanayi na ziyartanshi zamowar kusancin da sukayi da juna dan jikinta na gogan dantsen hannunsa da ya ke abude ga kuma k'amshin turarenta mai tada hankali da ya fahimci ya kame jikinta.

"Yaya YS ka natsu ka san cewa rayuwarka ba kai kaɗai take amfanarwa ba har da dubban jama'a daga cikin Masarauta zuwa wajenta dan haka ka kori damuwa ka maye gurbinta da nishad'i sannan ka k'ok'arta wurin cikawa su Mai martaba burinsu na zama da mata bisa igiyar aure mai tsauri kada ka sake aikata laifin da ka aikata a baya domin hakan zai taimaka ka samawa su Mamie sanyin idaniyarsu kafin ƙasa ya rufe idanuwarsu wato abin cikin kwai."

Shiru ta yi tana murmushi cike da tsokana, ganin baida niyyar magana saita sauka akan lilon ta yi dan taku biyu zuwa uku sannan ta juya ta fuskanceshi duk da tana da tabbacin ba kallonta ya keyi ba ta ce "Karfin sha'awarka na son kaiwa matakin da zaka kasa mallakan kanka har sai ka fitar da shi wanda bana fatar ka haik'ewa kuyangi ko k'adangarun bariki ka goga mana bak'in fenti, laifin da bamusan yarda aka aikatashi ba ya bibiyemu mu shiga uku."

Tar ya buÉ—e idanunsa amma sai ya ci karo da bayanta domin tana gama ambata ta juya ta nufi wurin zamanta da sar-sarfa. Bai daina kallon bayanta ba har saida yaga ta zauna tana shirin d'agowa sai ya maida idanunsa lumshe amma yana hangota dishi-dishi.

"Miskili kafi mahaukaci ban haushi, ai na gamu da wahala kam."

Ta ambata a saman lips dinta.

"Amma me ye damuwarshi? Yana da lafiya irin haka ya ke sakin matarshi sannan duk ba wacce ya aikata sunna da ita, kai anya ba Aljana ta aureshi ba? A'a Wanda Aljana ta aura baya jin feeling kamar yarda yaya YS ke ji, wallahi da lauje cikin nad'i a game da rayuwarsa, shin ta ina zan san bakin zaren?

Murmusawa ta yi tare da murza goshinta ta furta wata kalma a can k'asan mak'oshinta wanda ita kaÉ—ai taji kayanta.

***
"Ina jin damuwa da lamura ki Dr. Muneera tun kuwa baki san kanki ba."

Sadauki ya furta a hankali yana mai jin yanayin da ke ciki na ƙara tsananta gare shi. Sauka ya yi ya nufi k'oramar da ke ƙarshen lambun ya shiga ya nutse cikin ruwan tsawon mintoci biyar sannan ya taso yana girgiza sumarsa ruwa na tartsi,ya sake komawa ƙasan ruwan wannan karan ya shafi mintoci ashirin sannan ya d'ago rik'e da kan narkeken kifi yana zile-zillen son kufcewa. Bakin k'oramar ya fito ya zauna saman kujerar roba ya tsirawa cikin ruwan ido abin mamaki ita ce take nink'aya cikin sutura masu bayyana halittanta fili, ware idanu yayi tare da sakin kifin ya koma cikin ruwa aikam ta cafeshi ta cillo masa ya fad'o jikinsa lamarin da ya shi sakin siririn ƙara cikin fitar sauti saboda ya dukar masa cinya da ya yi, aikam ƙaran sai a kunnin Neera ta nufo hanyar da zai sadata da wurin a guje, jin takunta yasa Sadauki komawa ruwan tare da kifin domin baya son ta ganshi a yanayin bayyanar halittunsa fili dan shiga ruwar da yayi ya sanya kayan sun mamme a jikinsa surarsa ya fito fili.

Zama tayi ta kafe ruwan da ido tana mamakin yarda ke iya jimawa a ƙasan ruwa kuma yafito lafiyalau. Takalmansa ta dauka tana juyawa dan ta soma gajiya da zaman jiran fitowar na shi. Ruwan ya motsa da ƙarfi, ta kalli cikin k'oramar gami da ware ido saboda hango k'atuwar Kada na shawagi alhalin ta san babu ko kadangare a cikin tsafta-tacciyar k'oramar, murmushi ta yi tare da jifarta da takalmin hannunta aikam take ta ɓace.

Tafi ta yi tana furta "Haba yaya YS ba twins yayan gambo zaka gwadawa Ofi ba balle ka bani tsoro, wallah sai dai ni na baka tsoro da macizai."

Tana rufe baki babban kifin nan ta fado kusa da ƙafarta ta daka tsalle tare da kwalla ihu, kafin kobo ta bar wurin a guje domin Allah ya jarabceta da tsoron manyan kifaye shiya ko su Lailah na kallon chennel ɗinsu bata zama a wurin.

Fitowa ya yi yana murmushi ya zauna saman dutsen gefen k'oramar na sharce ruwan gashin kansa.

"Doctor Muneerat manya aida kin tsaya kin nunamin ke 'yan biyu ce da ni kuwa na gwada miki Gambo sha gaban 'yan biyu ne a Ofi."

Ya jima zaune a bakin k'oramar yana wasa da kifin inda ke kiranshi sai ya taho a juye idan zai kashi sai ya zille ya daka tsalle ya koma ruwa inda zai watso a fuskanshi, da ya gaji ya dawo saman kujera ya zauna ya daga kai sama yana kallon tsuntsaye da ke ta shawagi a saman bishiyar mango zuwa lokacin har kayan jikinsa sun bushe sakamakon iskan da ke kad'awa, yana ta mamakin yarda akayi Aljanan ke son yi masa wasa da hankali. Kiran sallar a Zuhur yasa ya mik'e ya nufi filin motsa jiki ya ɗauki jallabiyasa ya saka ya fito cikin takun k'asaida wanda ke ƙara fito da kwarjininsa a fili. Bayan an fito sallah suka hadu da Imam suka nufi cikin Masarauta gidan su Imam suka nufa suna shiga Neera na fitowa da gudu Maryam biye da ita, tsak suka tsaya kafin Neera ta yi magana Sadauki ya tareta cikin cewa "Kun girma ba kusan kun girma ba to aure za'ayi muku ku tafi can suyi ta haukan da mazajenku."

"Aikam da ka kyauta mana dan naga kamar an manta da mu ne gashi mun balaga da jimawa."

Kallon Neera ya yi idanu waje yana lek'en bayanta sai yaga bakowa a wurin sai shi da ita dan Imam wucewa ya yi ciki.

"Kin rainani ko?"

"A'a kawai banji daÉ—in kalman haukan da ka kiramu da shi bane kuma ina son magana da kai."

"Banda lokaci."

"Zakayi ne idan ciwonka ya sha k'arfinka."

"Neerah!"

Ya ambata da sauti.

"Yaya YS me nayi kuma?"

Ta furta a shagwab'e.

Sauke numfashi ya yi ganin Momy ta fito ya russuna ya gaisheta tare da juyawa ya fice.

"Muneera me yasa kika raina Sadauki ne?"

"Momy wallahi ban rainashi ba."

"Shi ne zai ambaci sunarki cikin fushi."

Sosa tsinin hancinta ta yi ta furta "Mahaukaciya ya cemin na ce masa aljanin ruwa domin wallahi d'azun a Garding ya dauki kusan awa É—aya a cikin ruwa bai fito ba kuma har da bani tsoro ya yi."

Girgiza kai Momy ta yi tana murmushi, bayanta Neera tabi tana cewa "Hajiya Momy bani sakwarar in kaiwa Ammina."

"Ita dama zan haÉ—a miki da kaina dan nasan Hajiya Safiyya tunda ta ce inyi mata kowa ya saka hannu zata iya ganewa na k'i ci."

"Ai Momy lamarin Ammie mamaki ke bani ita ba twins ba amma tafi twins tsirfa da gano abin da aka b'oye mata."

"K'ila ke da Sadauki kuka sammata Ofi."

"Nikam Momy ban da komi sai dai ko shi."

"Baki da shi kike hukunta duk wanda ya dukeki da macizai sadda kuke yara?"

"To ai Momy lokacin muna yara ne yanzu kuwa girma ya zo dole na watsar da shiriritan nan."

"Uhm Allah yasa haka ne kuma ki rage biyewa Sadauki dan tsaf Hajiya Safiyya zata hukunta ki inta gano kin raina mata shalele."

"Uhm nikam Momy ban raina shi ba kawai ina son ganin yana magana ne kamar kowa sam ban son ganinsa cikin shiru domin yin maganar zai taimaka wurin rage masa damuwa."

"Shi ya sanar miki yana cikin damuwa?"

"A'a Momy amma a kallo É—aya zakayima yaya YS ka gano na tare da damuwa duk da b'oyewar da ya keyi."

"Oh ni Hauwa kulu ina ganin wani salo a wurin Likita alhalin ita ba karatun sanin halayyan d'an Adam ta yi ba."

"Kai Momy, kawai damuwana da lamuransa ne yasa nake saurin ganowa in har yana cikin yanayi mara daÉ—i."

Dariyar da Momy ta sanya ne yasa Neera sunkuyar da kai ƙasa, sai kuma ta juya ta fice da sauri.

"Ja'ira bisa alamu iska na wahalar da mai kayan kara."

Momy ta furta tana jinjina kai fuskanta É—auke da murmushi.

Suna hira da Maryam Momy ta fito da kwando da sauri Neerah ta mik'e ta amsa tana mai furta "Allah ya rubu ce Momy."

"Amin Doctor."

Har Neera ta kai bakin k'ofar falo ta tsinkayi magana Momy inda take kiranta tazo suyi lunch.

"Momy zan shiga Asibiti nan da awa É—aya amma a haÉ—a dinner da ni dan anan zan kwana saboda haka Maryam ki dafamin abinda na fi so dafatan kin gane."

" 'Yar rainin hankali sai dai ki kwana da yunwa domin jirgi É—aya ya kwasomu kinfi kowa sani ba son shiga kitcken nakeyi ba"

"Kinji Momyna ki dafamin abu mai daÉ—i kuma Allah ba wanda zaici."

"Ko yaya Saudauki ne?"

Maryam ta ambata tana kallon idanun Neerah.

Ficewa falon ta yi da sauri Maryam ta kwashe da dariya, Momy ta yi mata dak'uwa ta gintse dariyar.

"Aikam gara da kika ambata mata haka yaya Maryam domin daga ke sai shi Yaya Neera ke sakemawa in ancire mahaifanmu nasha jin ana gulmanta domin har 'yar k'waya naji ana ambata mata."

"Ke Baby Nanah ban son k'arya."

"Allah kuwa yaya Maryam, naji yaya Sardauna na faÉ—awa abokinsa wai k'waya yaya Neerah take sha shi yasa bata ganin kowa da gashi dan kawai ta dawo a gajiya ta wucesu yana yi mata magana bata kulashi ba sai hannu ta d'aga mashi."

"Autana taho muci abinci kuma ban son na sake jin kin bada wannan labarin gudun haÉ—a fitina."

"To Momy amma dai zan sanar da yaya Neera saboda ta dauki mataki kada jama'a su soma yi mata wak'ar 'yar maye."

"Autana kada ki sanar da ita sannan 'yar k'waya da Sardauna ya ambatawa Muneera ba nufinsa tana shaye-shaye ba, nufinsa tafiye rashin son magana da kuma takawa ko waye burki in ya tab'ota."

"Oh Momy na gane yanzu amma ba kowa ne zai fahimci haka ba."

"Haka ne kam Autana mai kaifin basira."

Murmushi Nana ta yi cike da jin daÉ—in yabon da a kayi mata alhalin kashe bakin bada labarin Momy tayi zamowarta mai gudun fitina.

Bayan sun gana cin abinci Momy ta kira Maryam suka shiga bedroom d'inta ta dubeta ta ce "Me ke tsakanin Muneera d Sadauki?"

"Wallahi ban sani ba."

"Ban son wasa Maryam sanar da ni abinda na ke zargi."

"Momy a gaskiya Neera na son yaya Sadauki tun kafin ya soma auri saki karatun da takeyi yasa bata nuna masa alamu ba har zuwa yanzu tana son shi duk da hatsarin da ke cikin aurensa baisa ta sadduda ba sai dai in banda ni ba wanda ya sani hatta kuwa Lailah da Zuhrah ba wanda ya gano k'aunarta gareshi jama'a na ɗauka ƙarfin zumuntar da ke tsakanin su ne ya janyo suke shiri da juna dan kema sheda ce kaf 'yan matan Masarauta ba wanda yaya Sadauki ke sakewa fuska har ta gaya masa maganar da taga dama sai Neerah."

Numfashi Momy ta ja tare da cewa "Zanso Sadauki ya furta yana sonta."

"Saboda ne Momy?"

"Saboda duk wanda ya aura ya saki haɗa su akayi wata k'ila nuna ra'ayinsa akan auren wacce ya ke so zai kawo ƙarshen auri sakin."

"Momy yaya Sadauki na da matsala a fara neman masa magani kafin a sake yi mashi aure."

"Kema kinyi magana anan domin muna tattauna maganar neman masa magani da Mamie Fulani "

"Yawwa hakan dai yafi."

Sai abu na gaba shi ne maganar fitar da miji, shin wa kika tsayar cikin namemanki?."

"Miji fa Momy?"

"Eh Dadynku ya umurceni da in tambayeki saboda ya daina yarda da auren had'i sannan Mai martaba ya soke auren had'i amma in kun haÉ—a kanku ba ruwansu zasu sanya albarka."

"Momy wani abu na faruwa ne wanda bamu sani ba har akan ya faru?"

"Ko É—aya kawai Mai martaba ne da kansa kwanaki ya tarasu ya sanar da su soke auren had'i amma ina jin bai rasa nasaba da abin kunyar da Sadauki keyi na sakin matar da ake bashi."

"Momy bana da gwani saboda ina tsoron abin da ya sami yaya Khadijah ya sameni domin har yau tana begen Mahmud bayarda zatayi ne dole ta karb'i yaya Sardauna duk kuwa da yana kan cutar da ita."

"Ban tambayeki wannan labarin ba sannan tunda baki da gwani sai Dadynku ya zab'a miki ko cikin dogarai ne."

"Momy dogarai kuma?"

"Eh tunda na zama abokiyar wasanki ba."

"Sorry Mum zamuyi shawara da su Neera."

"Ke dai kika sani kuma ina baki shawara da kiyi nazari banda biyewa shawarar zuciya wanda ke haifar da dana sani."

Ganin ta faÉ—a tunani Momy ta fice daga d'akin cikin yi mata addu'ar samun k'warin zuciya akan duk abinda ta sanya a gaba.

Maryam ta kwanta a saman gado, matsanancin damuwa kwance a fuskanta.

"Yaya Sadauki."

Ta furta a saman lips d'inta tana mai lumshe ido tare da nazarin kalaman Momy na ƙarshe. Zuwa can ta zabura tamkar wacce a sokawa Allura ta fito, ganin ba kowa a falon sai ta dauki hijabin sallah ta fice da sauri, Hadiman da ke kai kawo a tsakanin sassan Masarautar suka soma jero mata gaisuwa amma ba wanda ta sami zarafin amsawa.

Momyn Haske ce 🥰

*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon

Adabi Writer's Association (AWA)

https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks 🖕

*Ayimin Affuwa kwana biyu ina cikin hidima ce shi yasa ku ka jini shiru.*

Page 10.

Part d'in Mamie Fulani ta nufa ta shiga k'aton falon da sallama, Lailah ce ta amsa cikin dishewar murya wacce ke zaune gaban Sadauki bisa alamu laifi tayi masa. Da sauri Maryam tayi nufin juyawa ya daka mata tsawa.

"Ke!"

Tsak ta tsaya batare da ta juyo ba.

"Zo nan dama ina shirin kiranki."

'Nashiga uku Allah yasa dai ba masifa Lailah ta janyomin ba.'

Ta ambata a ranta ya yin da a fili ta juyo jikinta na rawa tare da furta "Ni?"

Shiru shi ne amsar da ta samu sai tasami kanta da ƙare masa kallo sanye yake cikin kayan sarauta wanda yafi ta'amali da su domin kafin ka gansa da ƙananan kaya aiki ne sai ko suit wanda da an gansa cikin shigar ke nuni da zaiyi tafiya ne sai kuma a filin motsa jiki inda ke shigar sport wear.

"Please Maryam ki zo kiyi masa bayani wallahi ba ruwana da Muhib, shi ne ke takurani ke biyoni gida."

"Keep quiet!"

Ya ambata a fusace.

"Sorry Yaya, dan Allah ka taimakeni ka saurari bayanin bakin Maryam domin ita, Neera, da Zuhra ne shaiduna akan bayanin da nake yi maka, wallahi Allah ba ruwana da Muhib."

Kallo kin rainani ya auna mata sai ta fashe da kuka ta kama k'afarshi janye ƙafar ya yi tare da mik'ewa ya nufo k'ofar fita saboda kukanta ya karya masa zuciya kuma a take ya yarda da gaskiya take sanar da shi.
Maryam na ganin tasowarshi ta runtuma da gudu tamkar zata kifa sai lamarin ya bashi dariya ya murmusa tare da juyowa ya ce da Lailah "Ki fita sabgar mara natsuwar yaron nan idan kuma kina son mu sa k'afar wondo ɗaya da ke ne to in sake ganin ƙafarsa a cikin Masarautar nan sannan in har kin san kin kamu da son shi to kiyi gaggawan cireshi a ruhinki domin kinfi ƙarfinsa ta ko wani fuskan kuma ke mai tsarki ce dan haka ba zan bari ki auri mai cike da dattin najasa ba, a bisa umurnina ki koreshi koro na har abada."

Ya kai ƙarshen maganar na runtse ido domin yanajin tamkar bayyiwa masoyan adalci ba.

Gyada kai ta yi tana share hawayen da ke zubo mata, ganin na kallonta sai ta motsa baki a hankali ta ce "Nayi maka alk'awarin dakatar da shi daga zuwa Masarauta tare da nesantarshi na har abada duk da dama shi ke haukansa ni bai isheni kallo ba."

"Da kyau."

Murmushi tayi ya maida mata da martani ya juya, har ya fice ya dawo ya ce "Saura ki haÉ—a baki da wancan mara kunyar ku turomin macizai saman gadona kamar yarda kuka saba aikatawa idan anyi maku faÉ—a."

"Allah yaya ba ruwana Neerah ce da aikin kasan bana yin Ofi sai da babban dalili."

"Nadai sanar dake kada inga maciji a muhallina."

Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi domin tsayawa zancen nan na nufin ya huce kenan.

"Humm zan gyara maku zama ne musanman ita da ta rainani."

Ya ambata yana barin wurin.

"Ka soma gyara kanka Babana domin kai da su duk kanwar ja ce wani fanninma kafisu tsorata mutane da Macizai wai lamarin har kan Mai Martaba dan ya sanar da kai gaskiya."

Da sauri ya dawo falon ya rik'o hannun Mamie yana k'ifta mata ido, alamun tayi shiru.

"Yes, ka soma gyarawa kanka zama kafin ta zo kan wasu wanda basuyi kwatan-kwacin laifin da kake kan aikatawa ba."

"Wayyo Mamiena me na yi kuma?"

"Babban zunubi na auri saki da kuma tsoratar da Musulmi ta hanyar fito da macizai su razanasu akan laifin da baikai ya kawo ba, kwanaki Mai Martaba har kusan fad'uwa ƙasa ya yi dan tsoro, tabbaas da ba dan ina kusa ba da anji mugun labari sakamakon macizai da suka cika turakanshi marasa kyan gani sannan tamkar almara suka b'ace, ganin anyi binkice ba agano komi ba sai na tabbatar kaine ta turosu, anya Babana hakan ya kamace kuwa?"

"Mamie ya wuce fa."

Ya furta cikin tsare gira ganin Lailah na k'unshe dariya.

"Bai wuce ba, mai jin magana kawai kada a fad'i É—ayan."

"Please Mamie ki manta da lamarin, ai natuba da jimawa."

"Anya Babana kai kaÉ—ai ne kuwa?"

"Me nayi kuma Mamiena?"

"Watsi da cikar kamala wato aure sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

"Ayya Mamie ki bar maganar auri sakin nan domin yana daga cikin zanen ƙaddarar shi wanda bawa bai isa kufce masa ba saboda rubutacce ne daga Allah."

Duk kallon bakin falon sukayi a tare, Dr. Muneerah ce tsaye idanu jajur bisa alamu kuka tayi.

"A'a Likita bokon turai, lamarin Babana ko da ƙaddara to son zuciya ya soma yi masa jagora domin ba sau ɗaya ko biyu ya aikata laifin ba har fa sau hu...

"Mamiena ya tuba ai ba zai sake komawa ga zunubin ba ko yaya Yarima?"

Kafeta da idanu ya yi batare da ya amsa ba.

"Yes Neerah yaya ya yi tuba na gaskiya da yardan Allah ba zai sake komawa ga wannan laifin ba, zaiyi aure ya zauna lafiya da iyalinsa wannan a rubuce yake."

Lailah ta amshe da sauri tana kallon idanun Sadauki.

"Au, in na fahimta kuna bayan iya shegen da yarik'a aikatawa kenan?"

"A'a fa Mamie amma dai tunda ya wuce to abar d'aga zancen gudun É“acin rai kinsan abu kaÉ—an ke sanyashi cikin tunani ya soma wasan b'uya da kowa kuma hakan kan jefashi cikin kaÉ—aici sannan hakan bai kamata ba yana Sarkin Gobe na fuskantan matsin rayuwa."

"Muneera wai nawa Babana ya biyaki ne?"

"Na me fa Mamie?"

"Na campaign mana."

Ware ido ta yi Sadauki ya murmusa tare da russunawa gaban Mamie ya yi mata rad'a wanda ita kaÉ—ai tajiyo abinda ya ambata aikam ta sauke masa dundu tana furta "Allah ya tsare, ya kare, can ga su gada wai Zomo yaji kid'an farauta, wallahi a kul É—in ka da wannan lamarin kadaiji na sanar maka in ba so kake mu koma gidan jiya ba."

"Allah Mamie na zama kurna akan lamarin sam banji me kike cewa ba."

"Amsa naka Sadauki, Allah kada naji ko na gani kuma nan da sati biyu ka kawo mana matar aure ko ranka yafi dare duhu da fatan katuna maganar Mai Martaba."

"Mamiena dan Allah ki ami...

"Nagama magana Babana sannan kada na sake ganin ka tasa k'anninka a gaba da zancen baka son suna zance tunda ba jik'asu zamuyi mu sha ba."

"Mamie da dare zan dawo muyi maganar a gaban Abba domin a wannan gab'an banjin zan ja da baya ba."

"Na zama abokiyar wasarka ko Baba Ali?"

"Tuba na ke Fulanin Mai mar...

"Gidanku na ce Sadauki."

Girgiza kai yayi tare da sumbatar hannunta

Please Login or Register in order to submit comment