Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manyan idanunsu da suka gada wurin Mai martaba Sarki Abdul Hakam.

"Kai makahon inane da kake tafiya baka kallon gaba ka?"

Sardauna ya ambata cikin kaushin murya domin jin labarin zuwar Sadauki turakar mai martaba ya daga hankalinsa dan burinsa su cigaba da fushi da shi abinda zai bashi damar hawa karagar mulkin Mungaye hankali kwance domin ya gama cika sharudd'an zama Sarki tunda nada aure da albarka auren wato haihuwa, yayin da Sadauki yake fanko a wannan fannin.

Rab'e shi Sadauki ya yi ya wuce batare da ya tanka masa ba domin tankawarshi naushi ne lamarin da ke gujemawa faruwarsa dan in har ya sakawa Sardauna hannu sai ya suma wannan lamarin ya samo asali ne tun suna yara duk in faɗa ya haɗasu to Sadauki sai ya sumar da Sardauna da zarar ya kai mashi duka.

"Mara amfani mai auri saki kawai, mijin Aljana!."

Kalaman sun k'ona ran Sadauki amma duk da hakan bai sa ya waiwayo ba.

"Kai! ne mara amfani, wawa mai fuska biyu kawai."

"Kai! Imam ka taka a sannu ko in antayo k'anwarka gida a satin nan na angwance da mata huɗu a lokaci ɗaya."

"Wanda ya fasa antayota ya raina kanshi da mai dattin d'ankwalinsa."

"Umman kake zagi saboda baka da hankali?"

"Gaka nan babban mara hankali, gab'on banza mara amfani."

Sardauna ya nufo Imam a fusace shi kam ya gyara tsayuwa na jiran ya shigo shi ganin haka sai Sardauna ya ja baya ya juya ya nufi sashin Umma na aiki bambamin faɗa. Dariya Imam ya kwashe da shi ya furta "Matsoraci kawai kuma ka sani lusari irinka ba zai tab'a zama jagorar babban Masarauta irin ta Mungaye ba."

Jiyowa ya yi cike da baƙin ciki aikam Imam ya yi masa gwalo sai ya watso masa dak'uwa, Imam ya zabura kamar zai biyoshi, Sardauna ya kwasa da gudu ya b'ace. Dariya Imam ya sake kwashe da shi har da tafawa, Sadauki dake hangen abin da ya faru shima murmushi ya yi yana Allah wadai da sokancin d'an uwanshi Sardauna.

"Ga daishi a fuska da cikar zati kamar jarumi amma saidai ko wata macen tafishi k'wanjin iya kare kai."

"Ka bari kawai Sarkin gobe, shi yasa na ke bak'in cikin bashi auren Khadija da akayi domin tafishi komi na jarumta, ni dai Allah yasa kada yaransu suyi gadon mugun abu na zamowa sokaye a cikin tsararrakinsu kamar yarda ubansu ya kasance."

Duka Sadauki ya kawo ma Imam cikin cewa "Baka da dama fa Brother."

"Uhm ba za ka gane haushin da nake ji ba ne na wannan had'in auren da akayi da sokon can."

"Kaganka da neman magana, nikam taho muje nayowa su Mamie siyayya."

"Da kyau mutumina bisa alamu an karb'i tubanka."

Murmushi kawai Sadauki ya yi mai nuni da bashi tabbacin hasashen shi, aikam cikin jin daɗi Imam ya rungumeshi daga bisani ya sake shi suka jera zuwa inda ake ajiye motoci cikin nishad'i.

Sai da suka hau kan titi sannan Sadauki ya kalli Imam cikin rashin wasa ya ce "Ya kamata zuwa yanzu kai da Sardauna ku dawo natsuwarku kudaina abu kamar yara dan kun zama iyaye ko ba ma haka ba sirukan juna kuke tunda kamar yarda ke auren k'anwarka haka kaima kake auren k'anwarshi to Please Aminina kadaina biye masa kuna raba hali ka zamo tamkar ni yarda sam baya gabana kome zaiyimin ban tankashi dan bai kai matsayin na tsaya b'ata lokaci da shi ba, haka ka rik'a duba girman dangartakanku da juna na zamowa daga tsa-tso ɗaya."

"Ok in sha Allah zan jaraba d'auke kai amma fa Aliyu ka sani yayanka baida tunani dazunfa cemin yayi wai zai antayo Khadija gida ya angonce da mata huɗu rana ɗaya."

Karya ya keyi domin na sami labarin ko Khadija hak'uri takeyi da ragwantarshi kawai ya ambata ne dan ya b'ata maka rai kuma yayi nasarar hakan tunda gashi nan ka biye masa kunyi shiririta."

"Kai Yarima yaushe ka sami labarin Sardauna rago ne a turaka?"

"Kai dai zauna nan ana batun arziki kana can kana shiririta."

"Ban son rainin hankali fa Sadauki, shin kai da ba mata ba gareka ba ta ina aka zauna tattauna lamarin masu iyali da kai?"

"Zancen kake so na bar maka to."

"Allah baka isa ba sai ka fitar da ni duhu nan."

"To tafi ka tambayi Mamie gaskiyan zancen domin a bakinta naji in shima musamin zakayi to bissimillah."

Idanu waye Imam ke kallon Sadauki yayin da shi kam ya tsare gira ya cigaba da tuk'insa hankali kwance.

"Shin kana nufin ita Khadijan ta iya zuwa gaban Mamie da zancen bata gamsuwa da mijinta?"

"Kai kada fa ka dameni da zancen banza tam na kwanciya tam."

"Ai wallahi baka isa ba tunda ka takalo zance baka isa ka waskewa ba sai ka fed'emin biri har wutsiya."

"Ai zaka iya shak'eni in na jiyo k'amshin barzahu na ambata maka gulman da kake son ji."

"Kaga malam dawo hankalinka ina saurarenka."

"Kaga Imam zan ci maka mutunci, sannan in kaima ragon ne ai sai ka sanarmin mu tafi neman magani kafin matarka ta raina ka."

"Allah ya tsareni mugunji da gani."

"Ina tayaka murna da ka tsalle sharrin basir."

"Sadauki da magana a bakinka Please tell me."

Banza Sadauki ya yi masa har suka isa babban mall din dake dauke da tambarin Fulani store wanda wurin ya zamo mallakin Mamie Fulani. Duk nacin Imam akan sanin gaskiyan labarin Sadauki ya yi kunnen shegu da shi.

Suna shiga ya juyo ya aunama Imam mugun kallo a take ya tsuke bakinsa domin jinin sarautan ya motsa kan dole ya yi mubaya'a duk da shima ba baya bane wurin nuna mulkin sai dai Toron Giwa ya take na Rak'umi.

Turaruka masu tsada ya daukan musu kowa set huɗu sannan ya zarce wurin lafaya ya zab'ama Mamie Fulani masu kyau kana ya dawo wurin takalma ya daukanma Mai martaba kalan na sarakuna itama Fulani ya siya mata daga nan ya soma zab'ama k'anninsa duk abinda kowa ya fi so suka fito tare da barin kayan a kai mashi gida. Yawo Sadauki yasomayi da su a birnin baiko duba dare sakamakon birnin ya cika da hasken Soler ta ko ina, sannan duk inda suka ratsa sai masoya sunyi masa kirarin da Sarkin Gobe mai Mungaye da yardan Allah, inda Imam zai fito ya yi masu yayyafin kuɗi sannan su wuce, a k'arshe suka dawo Masarauta da misalin k'arfe ɗaya da rabi na dare, har bakin gidan Imam ya kaishi yaga shigarshi ciki sannan ya nufo sashinsa cike da jin barci, a gajiye ya faɗa saman kushin yana maida numfashi zuwa can ya kai hannu saman maranshi idanunsa lumshe yana yamutsa fuska dan hakan ya gujemawa shi yasa ya yi ta gara-ranba da su har dare ya tsala a she a banza ya yi fitinar na nan mak'ale da shi, tsaki ya ja yana mai tausayin kansa.

Tamkar ko yaushe ta bayyana cikin shigar daukan hankali ta zauna gabanshi tana jifarshi da shu'umin murmushi. Motsawa ya yi ya tashi zaune da kyau ya tsira mata ido cike da buk'atuwar ka sancewa da ita duk da a ƙasan ranshi baya maraba da lamarin amma gangar jikinsa ya kasa bashi haɗin kai.

"Who are you?"

Ya furta cikin shak'ewar murya gami da matse cinyoyinta.

"Your wife."

Ware idanu ya yi ta kyalkyale da dariya gami da huro masa iskan bakinta wanda ke dauke da wani k'anshi na musanman, shi ne ke kuma haukatashi matuk'a. A gigice ya nufeta hankalinsa a tashe cikin son kasancewa da ita ko ta halin k'ak'a. Ta shi ta yi ta soma ja da baya ya kai mata cafkota ta zama haske ta b'ace tana cigaba da yi masa dariya wanda ke sake hautsina masa lissafi, toshe kunnuwansa ya yi amma sai yaji dariya makar sake ƙaruwa ya keyi sai ya cire hannun cikin furzar da iska mai huci ya ce "Na rantse idan kika sake shigowa hannuna a karo na biyu sai na illata miki rayuwa ba aljana kike ba ko ifritiya ce ke sai na gana miki a zaba mai rad'ad'i fiye da wanda kike kan ganamin."

Ya k'are furucin cikin kaiwa iska naushi, ta saka ihu cike da tantiranci, ya ja tsaki mai ƙarfi ya nufi bathroom tamkar zaki ya sakarwa kansa ruwan sanyi, ya ɗauki mintoci ashirin tsaye ruwan da dukanshi sannan ya fito jikinsa na digan ruwa dan ko kayan jikinsa bai cire ba ya nufi firij ya zuba ruwa a cup ya ciko k'aramin spoon da gishiri ya juya a ruwan ya matse lemon tsami a kai ya daga ya shanye domin ko yasha tablet ya kan jima kafin ya dawo dai-dai amma wannan had'in take yanke ke samun natsuwa, yana jin kak'oshinsa tamkar zai tsage amma haka nan ya jure.

'Wata rana zaka sami matsala game da lafiyarka Aliyu.'

Jinjina kai yayi alamun ya sanda da hakan ta hanyar bawa zuciyarsa amsa.

***
Sardauna da Sadauki tagwayen ne ga mai martaba Professor Abdul Hakam duk kuwa da ba d'umin ciki ɗaya suka sha ba dan an haifi Sardauna da hantsi da marece kuma aka haifi Sadauki wanda faruwar haka ya so tada k'ura inda Umma ta ce Sadauki shegene girkinta Mamie Fulani ta ci dan haka bashi da gadon sarauta domin a wanna lokacin Mai martaba ya soma samun haihuwar 'ya'ya maza. Hajiya mai babban zaure ce ta tsawatar wato mahaifiyar mai martaba sannan ta kafa dokar duk ranar da Umma ta sake ambatar wannan kalman a k'arshen zamanta a matsayin matar d'anta, aikam ta shiga hankalinta inda ta kame bakinta har zuwa yau bata sake furta kalmar ba amma ta raini zuciyar Sardauna akan son mulki bakin rai bakin fama dan ta kance da shi ko zai hau karagar mulkin da second ne ya koma ga Allah sai ya hau kujerar sarautan Mungaye.

Umma irin matar nan ne masu fuska biyu inda cikin dubara take cutar da duk wanda ta tsanani ganin warwalanshi batare da makusantarshi sun gano ba.

Momyn Haske ce 🥰
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon.

AWA.

Page 8

Umma ta wargaza zaman lafiya tsakaninta da Mamie Fulani cikin salonta mai wuyar ganewa, duk da ita Fulanin bata kulata tana bata girmanta amma hakan baisa ta kame kanta ba wurin maida k'aramin abu zuwa babba a tsakaninsu ta hanyar makirci kala-kala wanda kafin mai martaba ya farga Mamie Fulani ta k'unsa bak'in ciki har ya kaita ga kamuwa da hawan jini sai dai bisa amincin Allah Mai martaba ya gano tungun Umma batare da ita Umman ta san hakan ba wanda shima mahaifiyarsa ce Hajiya babban ta haska mashi fitila a take kuwa ya warke makanta da ke ciki ya yiwa lamarin tubkan hanci ta siyaya ba tare da nuna fifikon da zai janyo tashin hankali ba inda maimakon Umma ta gyara sai ta sake k'aimi cikin fito da sabon salo.

Hassada gami da kishin Umma ga Mamie Fulani ya samo asali ne akan tazararsu da juna tun daga kan Ilimin addini dana boko zuwa dukiya wanda idan bata zarta mai martaba ba to zasu iya zuwa kunnen doki dan mahaifinta mai tarin arziki ne wanda kowa ya shaida a cikin birnin Mungaye da wajenta, ya rasu ya bar musu gado wanda ita da yayanta na miji ɗaya da k'anwarka suka gada sannan tun kafin ta auri mai martaba tana kasuwanci wanda ke kawo mata kuɗi domin tun kafin ta shiga Jami'a ta mallaki restaurant na kanta wanda a yanzu shi ne wurin cin abinci mafi girma da k'ayatuwa a cikin birnin Mungaye. Wannan ya tsole idon Ummu duk kuwa da tana amfana da shi ita da 'ya'yanta dan Mamie Fulani mai kyauta ce bata taɓa nuna bambanci tsakanin 'ya'yan Umma da nata, ko me suke so ta kanyi musu domin kusan ita ta raini Sardauna da Sadauki tare da Imam shi yasa duk fitsarar Sardauna baiyi mata sai dai ya k'are a kan Sadauki marainin wayonshi wanda ke d'aga masa ƙafa ba dan tsoro ba sai dan koyi da halin fiyayyen halitta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam inda ya ce da mu zamo masu yawan hak'uri.

Har izuwa yanzu Umma tana kan sanya rashin jituwa tsakanin 'ya'yanta dana Mamie sai dai ba dukansu ne suke bayanta ba, tafi samun kan Sardauna sama da kowa, shi yasa take ji da shi tamkar kwai duk da shima Sardaunan a cikin Masarauta ne ke nuna mugun halin da tsanarshi ga Sadauki amma da zarar sun fita wajenta tamkar babu komi tsakaninsu ke nunawa wannan halin ya aroshi ne dole ya yafa saboda gargadin mai martaba dan ya tabbatar masa duk ranar da labari ya zo masa ya wulak'an 'yan uwarshi a bainar jama'a to ya tabbatar da ya bar masa Masarauta bari na har abada, ba Sardauna ba hatta da Umma gargad'in ya ratsa kwa-kwalwanta sai ta d'orashi a tsarin fitowa a mai fuska biyu irin yarda take yin takonka shi ne dalilin da Imam kan ambata masa kalman a wasu lokuta in har ya taɓa Sadauki sai ya zamo Imam ne abokin karawarshi amai makon Sadauki.

Kaunanr Sadauki da Imam ya samo asali ne tun yarinta inda aka kawoma Mamaie Fulani yayen Imam ta haɗashi da su Sardauna ta raina har zuwa sadda sukayi hankali kowa ya koma gaban mahaifiyarshi sai dai har kwanan gobe Imam yana yiwa Mamie Fulani daukan uwa tamkar wacce ta tsuguna ta haifeshi shi yasa ba'a yi masa shamaki da shiga shashin mai martaba a duk sadda ya nemi hakan.

A b'angaren 'ya'yan Mamie Fulani kuwa ba ruwansu da rashin d'a'a ga Umma domin Mami Fulani ta horesu da kada su sake su shiga faɗar da babu ruwansu ciki. Sai dai duk wannan zaman lafiyar da Mamaie Fulani keyi ga kowa a masarautar hakan bai hanata gamuwa da mak'iya ba wand'anda suke takewa Umma baya irin matar Sarkin Fada dama wasu kamar dai yarda mafi akasarin gidan Sarauta aka sanshi bai rasa 'yan bani na iya, ma hassada da 'yan birne-birne asirai duk dan ganin bayan wanda ya fi su samun Ni'imomin rayuwa har da wurin Mahalicci domin duk wanda yafika tawakkali na yarda da ƙaddara khairan ko kishiyarta to ya fika samun duk kan Ni'imomi wurin Ubangiji Allah Subhanahu wata'ala.

(Allah ka ƙara cire mana tsa-tsa a zukata domin alfarman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Amin).

***
Washe gari a makare Sadauki ya tashi dan ko masjid bai sami zuwa ba lamarin da ya bak'anta masa rai ya k'arajin tsanar budurwan Aljanar domin ita ce silar makarar shi dan bai samu barci ba sai wuraren ƙarfe uku na dare wanda ya yisa cike da mafarkan daji mai duhu yanata neman hanyar fita ya rasa a ƙarshe ita ce ta bayyana cikin guguwa ta d'aukeshi sukayi sama. Lamarin da ya kasa b'acewa a kwakwalwar shi ganin taimakon da ta yi masa alhalin ita d'in azzaluma ce.

"Mitcheww! Hak'ik'a ina cikin damuwa matsananci, shin aina zan sake gamuwa da ita?"

'Aliyu ko dai fansa take ɗauka?'

"No! Banyi mata komi ba sai bisa tsautsayi wanda ita ta janyo afkuwanshi."

Ya ambata cikin bawa zuciyarshi tabbacin shi mara laifin ne duk da wani shashi na zuciyarsa na ƙaryata hakan amma kaso mafi rinjaye bashi gaskiya keyi. Wanka ga gabatar sannan ya yi sallah ya koma saman gado ya kwanta dafe da k'irjinsa ya fad'a kogin karatun wasik'ar jaki wanda bai amfanarsa da komi sai sake shiga damuwa. Babban damuwarsa yarda yake kasa neman tsari da yarinyar haka yanzu bai iya tashi raya dare da nafil-fili kamar yarda ya horu da yin hakan a baya, jin bak'on lamarin na son sake ziyartanshi sai ya soma hailalah zuwa can ya tashi ya shirya cikin shigar sarauta har da yin rawani wanda ya k'ayata fuskanshi ya fito a Mai Martaba sak.

Siyayyar da yiyowa su mai martaba ya ɗauka ya bar na k'anninsa. Yana fitowa da Saudauna ya haɗa idanu yana zaune a daf da shiga babban falon sashin Mai martaba, cikin nuna kulawa ya karasa gabanshi ya miƙa mashi hannu tare da ambatar sallama, k'eme-me Sardauna ya k'i amasawa balle bashi hannun dan musabaha, shanye ɓacin ransa Sadauki ya yi ya doshi shiga falon Sardauna ya kara masa ƙafa ya daka tsalle gefe k'iris ya rage bai faɗi ba, kallonsa ya yi tamkar zaiyi magana sai kuma ya gintse ya shige falon cikin sar-sarfa.

"Sarauta dai sai gani ga masu gani"

Sadauki na jiyo kalamamshi wanda ya soki zuciyarshi domin yana son Sarauta tamkar rai da ajali, a hasashenma ya fi Sardauna kaunar zamowa magajin mahaifinsu.

Mai martaba ya samu yana ƙaryawa ya tako a sannu ya russuna ya kwashi gaisuwa sannnan ya zauna sosai cike da ladabi kansa ƙasa yana wasa da yatsun hannunsa.

"Aliyu Saudauki Baban My Fulani, ina godiya."

Mai martaba ya furta yana janyo jakan da Sadauki ya ajiye a gefenshi.

Motsa kai Sadauki ya yi yana murmushi domin lamarin mahaifin nasu game da ambatawa Mahaifiyarsu kalma mai nuni da tsan-tsar kaunarsa gareta ya daina bawa kowa na gidan kunya domin a gaban kowa ambatarta ya ke da My Fulani ko my Queen.

Gyaran murya Mai martaba ya yi yasa Sadauki maida hankalinsa kanshi tare da gyara zama ya tsira masa ido.

"Aliyu ina da magana da kai mai mahummanci a game da abin kunyar da kake aikatawa wanda lamari ne da ya taɓa martaban Masarautarmu domin auri saki babban zunubi ne a tarihin kafuwar Masarautan Mungaye dama cikin addinin musulinci. Domin ba'a taɓa samun wanda ya taɓa sakin matarsa ba har sai mutuwa ce ta rabasu sai yanzu akanka dan haka ina mai sanar da kai hukuncina na ƙarshe akan lamarin shi ne duk ranar da ka sake sakin matarkata ta sunnah wallahi kaji na rantse bani ba ...

"Na tuba Abbana, ku yafemin dan girman Allah, na rok'eka kada ka furta kalman da zai iya zamemin matsala ko ya zamo ajalina."

Ya katse Mai martaba da sauri yana mai d'aga hannayensa sama alamun ban hak'uri.

Shiru Mai martaba ya yi yana kallonsa wanda har lokacin ke saman guiwoyinsa.

"Zauna da kyau ga kayan karin kumallo nan kayi."

"Na k'oshi Abba."

"Na soma wasa da kai ne?"

Girgiza kai ya yi tare da ɗaukan kofi ya zuba kunun alkama ya soma kurb'a a hankali yana jin gard'in Nono tare da madara da aka wadata kunun da shi na ratsa harshensa sai ya lumshe ido zamowarshi masoyin duk abinda ke da alak'a da Nonon shanu.

Bayan ya kammala hira mai cike da fahimta suka b'alle da Mai martaba wanda a cikin dibara ke tunasar da Sadauki mahimmancin aure ga baligi musamman wanda ke burin zama jagorar al'umma. Sadauki na amsar nasihohin cike da alfahari da samuwar mahaifinasu a matsayin uba mai tarin nagarta. Suna tsaka da hirar Sardauna ya nemi izinin shigowa Mai Martaba ya dama ya shigo cikin ladabi ya zauna tare da mik'o gaisuwa ga Mai martaba da Sadauki suka amsa daga nan aka ɗora hirar da shi har zuwa lokacin fita fadar Mai martaba ya yi ya sallamesu Mamie Fulani ta shigo ta taimaka masa ya shirya ya fice ta rakoshi har daf da k'ofar shiga fada da ke k'ofar sirri wanda Sarki ne kaɗai ke shiga ta nan duk ranakun girkin Mamie Fulani domin tana yi mara rakiya yayin da Umma ba ruwanta da bashi wannan kulawar dan tana kiranshi da munafunci ne k'anin karuwanci.

Hak'ik'a a wurin kula da Mai martaba tundaga kula da cikinsa zuwa walwalanshi ya fi samunsa a wurin Mamie Fulani dan ko ba ranar girkinta ba ne ya kan sanya ta yi masa girki tun Umma na masifa har ta gaji ta bari domin mai martaba Abdul Hakam tsayayye ne akan iyalinsa yarda ya ke shugaban al'umma haka ya ke shugaba a wurin iyalinsa sam bai ɗaukan rainin hankali akan abin da yake ikonsa. Shi yasa yake girmama duk abin da Mamie Fulani tazo masa da shi ko da kuwa bai cikin tsarinsa zai amsa da hannu biyu ballema bata fiye zuwa masa da abin da bai zamowa dai-dai da ra'ayinsa ba.

Soyayyarsa gareta ya samo asaline na kaunar da sukeyiwa juna tun kafin a aura mashi Umma wacce ta zamo k'anwa gareshi domin da maifinsa da na Umma ubansu ɗaya, ya ci burin soma aure Mamaie Fulani a farko amma mahaifinsa ya ce a'a ga zaɓinsa da yake mai biyayya ne ya amsa baki alaikum, shi yasa ko haihuwar fari Umma batayi ba ya auro Mamie Fulani sai dai bata sami haihuwa ba har saida Umma ta haihu uku duka mata sannan Allah ya bata kyautar 'yan biyu suma duk Mata, a haihuwar Umma na biyar ne Mamie Fulani ta yiwa 'yan biyunta gambo inda ta sami Aliyu, bayan shi ta sake haihuwar 'yan biyu maza Junaid da Jabir. Yanzu haka Mamie Fulani na da set din 'yan biyu uku, mata uku maza uku saboda a set na uku mace da namiji tayo, Saifullah da Lailah sai ta yi auta takwarar mai martaba suna kiranshi Mu'allim. 'Ya'yanta bakwai kenan, mata uku maza huɗu yayin da Umma ke da goma, mata takwas maza biyu. A nanma Umma na cike da hassadar Mamie Fulani akan finta da 'ya'ya maza da ta yi, sam ba ta gode Allah ba da ya albarkaceta itama da samun 'ya'ya mata jigon ginuwar al'umma.

***
Sardauna

"Umma dan Allah ki bar batun nan ban son jinsa, matata ta isheni rayuwa, ni bana cikin maza masu ra'ayin tara mata duk da ina son mulki amma banjin zan iya ajiye mace sama da ɗaya ba."

"Saboda kana ragon maza ba."

"Umma kema kin bi hanyar kirana da sunar da na tsana ko?"

"Eh nabi d'in kuma ba k'arya akayi ba, rago ne kai ta ko wani fuska, izzar mulkin kawai ka ajiye gami da bak'ar zuciya amma a nuna k'wanji ko sakaryan mace ta fika katab'us."

"Umma wallahi zan bar miki falonki tunda hakan kike so."

"Gaskiya ne baka son a fad'a kuma sai na faɗa, sai dai kafi ruwa gudu. Wallahi ina kam takaicin zamowarka mai tarin rauni a cikin 'ya'ya mafi soyuwa gareni, in dama a ce ana canji da bilahil azim dana canjaka da autana Sayyid ya dawo kai ka koma shi ko burina ya cika na zamowa uwa ga Sarkin Mungaye."

A fusace ya juya zai fice ta daka masa tsawa ya dawo ya zauna jikinsa na rawa saboda ɓacin rai.

"Aifa kam a fushi nan kafi auki kamar wani jarumi."

"Umma Please stop saying such kind of things dan wallahi suna k'omanin rai, ina jin tamkar zuciyata zatayi bindiga tayo waje ta tarwatse."

"Natsu! Sardauna, ka samu bani hankalinka nan."

Ta ambata cikin daka masa tsawa cike da takaici.

Idanu ya tsirawa Umma fuska a haɗe, murmusawa ta yi tare da cewa "Kaga Sarkin birnin Mungaye ba, ta kawarka lafiya dan Sarki jikan sarki magajin Mai Martaba Abdul Hakam Hashim Malle."

Murmushi ya yi tare kare fuskanshi da tafin hannunsa na dama cike da jin daɗin kirarin da ta yi masa kuma a take fushin da ya ke ciki ya sauka.

"Ko kai fa Yarima, yanzu buɗe kunnuwanka ka saurari labarin fitar da na yi daren jiya cikin b'adda kama."

"Duk kan natsuwata na tare da ke ya ke Ummata."

Muskutawa ta yi daga kishingid'en da ta ke ta soma magana cike da walwala bisa alamu bayanin na faranta mata rai sai dai ga Sardauna abin bai yi masa daɗi ba domin sai tab'e baki ya keyi tare da girgiza kai tana dasa aya kuwa ya mik'e tsaye rai a b'ace ya soma magana.

"No Umma bana son jin irin wannan shirmen na bokaye, shin in banda ya rainawa mutane hankali ta ya zaici miliyan biyu da rabi ya tsaya yiwa Aljanu karyan wai suna bibiyan Sadauki dan daukan fansa, k'ila Ubanshi ya turosu daukan fansa! To wallahi tun wuri ya dawo hayyacinsa dan baici bulus ba dole sai yayo kashin kud'ad'en nan tunda ba da Kakan Uban Ubanshi muka nemosu ba."

"Sardauna koma ka zauna ko ranka yafi nawa ɓaci kuma kada na sake jin ka zagi Malam Sile dan ba sa'arka ba ne sannan duk wanda ya ce zai taimakeka ai fi gaban wulak'antawa."

"Nifa Ummu bai taimakeni ba ya dai taimaki kansa dan haka sai ya biyani dukiyana."

"Na ce ka zauna muyi maganar."

"Affuwan Ummu sai anjima zan dawo jin tatsuniyar rainin hankalin da sile ya yi miki domin na gama kiransa da Malam daga yau."

Baki buɗe Ummu ta raka bayansa da kallo har ya fice falon, tashi zaune ta yi daga kishingid'en ta dauko wayarta ta latsa kira ana dauka ta ce "Hajiya Kilishi maza ki zo in ban takuraki ba."

"Lafiya kuwa Hajiya Umma?"

"Ba lafiya Hajiya Kilishi."

"Innalillahi! To gani nan zuwa ta k'ofar baya ki fito ki buɗe min a sirrance kinsan munafukai sun soma saka mana ido."

Momyn

Please Login or Register in order to submit comment