Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko aljana? Me yasa na aikata mata haka? Shin har sai yaushe zan fita daga wannan rayuwar na fitinuwa da son kasancewa mace amma ko ta zo gareni sai naji banda mak'iya irinta?"

Kwalla ne ya taru a kwarmin idanunsa ya kai hannu ya goge tare da tsirawa ruwan hawayen ido da ya shafo.

"Narantse duk ranar da na sake ganinta sai na wulak'antata fiye da yarda take kan wulak'antani yarda zatayi jinya tare da shiga damuwa sama da wanda ta jefani ciki."

"Wacece ita Aliyu?"

Kallon Imam ya yi wanda bisa alamu ya jima tsaye bai sani ba.

Ganin da Imam ya yi ba zai sami amsar tambaya ba sai ya tako ya zauna gefenshi ya kamo hannunsa cikin sanyin murya ya soma magana "Please Sarkin gobe ka daure kayimin bayani yarda zan fahimta wanda zai fitar da su Mamie Fulani daga zargin sihiri akayi maka wanda ba dare ba rana suke mik'a kukansu ga mai warware k'ulli batare da gajiyawa ba akan abinda ke jikinta ya fita ka yi aure ko saga jininka kafin su koma ga mahalicci su."

Shiru bai tanka ba saima kwanciya da ya yi yana jin mararsa na kartawa tamkar yarda ya saba ji duk in ya shiga tunanin sanin wacce ke alak'anta silar rashin zamanshi da matarsa na aure.

"Yar gidan waye? Me ta ke tak'ama da shi? Shin zan iya samun wadannan tambayoyin daga bakin Aliyu Abdul Hakam?"

"No."

"Why?"

"Imam ban santa ba haka ban san me zance maka akanta ba."

"Ikon Allah, wato ta tabbata Aljana dai kenan?"

"Ina tunanin hakan."

"To aina ka gamu da ita?"

"A Barci."

Ya samu kanshi da ambatar hakan alhalin ya san ba hakan ba ne.

Shiru Imam ya yi na kallonshi ya yin da shi kuma ya kauda kai gefe,murmushi ce ta kufcewa Imam har da zarcewa da guntun dariya lamarin da ya fusata Sadauki ya mik'e ya nuna masa kofar fita sai kawai ya kulle bakinsa da tafin hannunshi ya cigaba da dariya har da fitar kwalla.

"Na haukace ko Imam?"

"No Brother kawai dariya k'aryar da ka yanko ne ya bani domin k'arara ka tona kanka ba gaskiya ka ambatamin ba."

"Me kake nufi da kalamanka?"

"Nothing, but sit and tell me the truth, dan wallahi ba zanyi kaffara ba, ba gaskiyan kenan ba."

"Nagode da maidani mak'aryaci da kayi kuma ka fice alamarina, bana son sake ganinka kusa da ni, yes na amince na rayu cikin kaɗaici kamar yarda Mamie ta furtamin, Abba ya bawa sokon danshi mulkin Mungaye, Umma ta cigaba da kirana mara amfani."

"Innalillahi! Sadauki yaushe Umma ta ambata maka wannan mugun kalman?"

"I said get out! Malam."

Ya ambata tare da jan hannun Imam ya mik'ar ya soma ja har zuwa bakin falonshi sannan ya sakeshi ya koma saman Cushing ya zauna ya rik'e kanshi gam wanda ke jin tamkar zai fice daga muhallinsu.

"Affuwan A...

Hannun da ya daga masa yasa Imam gintse ban hak'urin da ke nufin bashi.

Tsawon mintoci uku ba wanda ya yi magana sannan Sadauki ya mik'e ya doshi hanyar bedroom saida ya tura kofar sannan ya yi magana cike da izza ya ce "Ka shirya idan anyi sallah zaka rakani sake bawa su Abba hak'uri a turakarshi dan yau Mamie ke da girki kamar yarda Lailah ta sanarmin."

"Ok Allah ya kaimu."

"Amin."

Ya amsa can ƙasar mak'oshi wanda ko Imam bai jiyoshi ba.

***
Durk'ushe suke gaban Mai Martaba Abdul Hakam da Mamie Fulani. Imam ne ke ta ban hak'uri ya yin da Sadauki yake ciccira hawaye nayi masa zarya na bak'in cikin jin kalaman da Mamie Fulani ta ambata sadda ta ganshi gabanta.

'Ban son sake ganin fuskanka Babana domin k'unci nake shiga a duk sadda ka ziyarceni dan haka kada ka sake zuwa inda nake na rok'eka.'

Toshe kunnuwansa ya yi tuno kalaman, ya d'ago kanshi hawaye wani na bin wani duk da zamowarshi mara saurin kuka amma kalaman Mami ya sakashi kasa jurewa. Ya sarrafa cikin sarsarfa ya isa bagan Mamie Fulani ya sauke kanshi a saman k'afafunta yana furta "Ki yafemin Mamiena wallahi ina cikin iftila'in rayuwa ne domin fushinki guba ne gareni dan ba zan tab'a sake yin tasiri ba har abada."

Sai ya fashe da kuka mai sauti wanda rabon da ya yi irinsa ba zai tuna ba. Ganin haka sai Imam ya tashi ya fice da sauri yana goge hawayen tausayin Amininsa.

Momyn Haske ce🥰
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabibin Tsiri
By Mrsjmoon.

ADABI WRITER'S ASSOCIATION (AWA)
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕

Page 5.

Kuka Tsidau ya fashe da shi abin da ya sanya Lina dakatawa daga rikiɗan da ta so yi zuwa tsun-tsuwa domin komawa inda ta fito, ta zuba masa idanu shi kuma bai saurara da kukan ba lamarin da ya karya mata zuciya taji kwalla ma ciko mata ido sai ta lumshe idanu gami da ware hannayenta zuwa can ta nuna Tsidau haske ya sauka saman kansa tamkar walkiya sai gasu a wani fada mai cike da shimbud'u na alfarma ta dubi Tsidau da ya ɗauke kukan ta ce "Samo mana abinci mai rai da lafiya kana na saurari matsalarka da ya sanyaka kuka daga jin ka kusa samun 'yanci zuwa ga iyalenka."

Motsa kai yayi ta murmusa cike da Izza tana mai fesar da iska daga bakinta, kafin kiftawar ido Tsidau ya bacewa ganinta, gyara zama ta yi a saman kilisan ta ɗauki kwalban turare ta ɓalle murfunsa ta kafa a bakinta, tas ta shanye tamkar ta sami ruwan roba, ta cillar da kwalban tare da tsirawa gefen hagunta ido zuwa can ta mik'e da sauri ta kaiwa iska cafka saiga wata budurwa riƙe ba hannunta, suka zubawa juna ido kafin Lina ta furta kalma budurwan ta zama ƙatuwar Kura ta ja baya tana sakin haniniya, ita kam ko motsi ba tayi ba illa zubawa Kuran ido da tayi tana mai nazarin abinda take nema a gareta da take bibiyan duk takun sawayenta tsawon lokaci. Tsidau ne ya bayya dauke da abinci mai rai da lafiya kafin kwabo Kuran ta ɓace.

'A sannu zan gano abinda kike nema a gareni.'

Ta ambata cikin ranta tana mai wadata fuskanta da murmushi.

***
Abun da Lima.

Sunyi tafiya mai tsayi sannan Abun ya kalleta yaga hankalinta baya kanshi sai ya daga dafadarta ta saki ajiyar zuciya gami da kafeshi da ido.

"Ya ke 'yata mafi soyuwar gareni, hak'ik'a ina sonki so matsananci shi yasa na ke son taimakonki domin kina fita na shiga taskan bincikena aikam na ci karo da isowar yar uwanki Lina tare da binciko manufar zuwar Tsidau shi ne na taho a hanzarce na tasheki domin inda ban iso ba a haka zaki wanzu cikin barci tsawon lokaci ko sadda zaki farka Lina ta gama mallake gadonki domin a yanzu shi ne babban burinta."

"Abun zan kashe Lina!."

Ta mabata bakinta na fesar da hayak'i saboda ɓacin rai.

"Kul! Na sake jin wannan kalami mai cike da abin kunya na fita a bakinki."

"To ka dakatar da ita daga shigamin gona."

"Zanyi wannan domin idan mukayi sake ta mallaki Tulun ruwan albarkan to ba ke ba har ni zan fuskanci matsala ta hanyar mallake min Tsibiri duk da ina hango wani babban kalubale da zata fuskanta bayan ta samu cikan burinta lamarin da nake jin ban son ya afku gareta."

"Me ye shi Abun?"

"Binciken da zan shiga kenan na tsawon kwanaki uku dan haka ina baki umurni da kada ki sake komawa Bukkan Kaka Gunu har sai na fito."

"To Abun amma ina son ka bani dama na tafi Tekun Kabobo na dakaceta zuwa sadda zaka fito."

"Na yarje miki wannan ya ke yata mafi soyuwa gareni."

"Godiya nake Abun."

"Kafin ki tafi ki shiga wurin Mah domin tana bukatar sanyaki a ido."

"To."

Ta amsa da sauri. Kanta ya shafa tare da shigewa turakanshi tana ganin shigewarshi ta rikida zuwa bak'ar tsun-tsuwa ta tashi sama da gudu ta nufi inda Abun ya ce kada ta koma sai ya fito daga bincikesa.

Lima na isa bakin Bukkan Kaka Gunu ta samu yana ta cike hanyar shiga ta ja da baya cike da fushi ta watso wuta sai dai yana sauka ruwa ya taho da mugun gudu ya kasheshi, iska mai ƙarfi ta turo daga bakinta shima yana isa guguwa ya maida iskan baya ya tafi da ita gefe ta zube ƙasa, numfashi ta sauke da karfi ta mike ta tunkari bukkan da dukkan ƙarfin sihirinta sai dai bisa mamakinta sai ta ga Lina Zauna a saman kujera bata sama bata ƙasa ta kare hanyar shiga Bukkan, kallon kallo suka yiwa juna na sokonni sannan Lina ta sakar mata murmushi tare da mik'a hannu container ya bayyana cike da farfesun kayan ciki sai fitar da turiri keyi, ta kalli Lima cikin izza tare da sake sauke mata murmushi tamkar zata furta kalma sai kuma ta gintse ta maida hankali wurin cin farfesun hankali kwance.

Iya fusata Lima ta yi sai kawai ta ja baya ta dunk'ule ta zama k'aton dutse mai fitar da hayaki ta nufo Lina gadan gadan saidai kafin ta isa Jarumi Buda ya bayya cikin gaggawa ya ture dutsen tare da kai masa naushi a take Lima dawo sufarta ta tashi tsaye tana murmula goshinta da ya kumbura sakamakon naushin da ta sha, kalonsa ta yi cikin mugun fushi kafin ta furta kalla ya iso gabanta shima a fusace ya kwasheta da mari yana mai cewa "Me yasa baki san ciwon kanki ba ne? Shin idan kika shiga Bukkan a wannan yanayin kin san kalan barnan da zakiyi? Ko ance miki fadar kaka Gunu wurin wargi ne? To maza ki bar wurin nan har sai Abun ya fito daga bincikensa kamar yarda ya bani umurnin zuwa dakatar da ke daga aikata barna wanda zai iya zanyowa Tsibiri nak'asu."

"Ka bani hanya Buda na illata Lina domin gata nan tanayimin dariya dan ita nake son kaudawa a doron ƙasa dan ta gane bakin rijiya ba wurin wasan yaro ba ne haka faɗa da Giwa bana 'yan kuikuyo ba ne, burina ta gane ni babban goro ne mai taɓani ya kwana lafiya sai wanda ke neman turb'aya ta kulle maganenshi na har abada."

"Karya kike Lina bata zo nan ba sai dai in gizo idanunki keyi miki dan haka ki ɓacemin da gani tun ban aikata miki mugun aiki ba."

"Buda na rantse da kabarin Kaka Gunu Lina na tare da mu dan haka ka kaucemin a gaba ko in sauke fushin a kanka wanda ya wuce naka fushin da kake karad'in cika baki a kai."

"To nunamin ita domin na hukuntata akan wani rainin hankali da ta yimin wanda ya janyomin rasa sihirtaccen Dokina Mardu."

Da hanzari ta tureshi daga bakin Bukkan sai dai abin mamaki ta nemi Lina ƙasa ko sama ta rasa alhalin ko sadda take maganar ta ganta zaune bayan Buda.

"Tabbas Lina ta koma Aljana."

Ta ambata da fushi hucin hayaki na fita daga bakinta saboda tsabar masifa.

"Tare kuka zama ai."

"Buda!."

Ta kira sunarshi da ƙaraji.

"Lima!."

Shima ya maida mata martani.

Sunkuyar da kai ta yi tana hasko wani lamari da ke yi mata wasi-wasi akan sabon halayyar Buda wanda sam a da bai daga mata murya hasalima miskili ne mai takama da Izza a kan Lina kawai ke zamowa soko saboda kaunar da keyi mata.

"Maza wuce muje ki huta, tunaninta da kikeyi ne ya ke son maida ki sokuwa har ta soma yi miki gizo."

"Kaine Babban soko amma bani Gimbiya Lima ba."

'Lallab'ata ta wuce tun kafin ta hargo jirgin.'

Murmushi ya sakar mata jiyo abinda Lina ta ambata masa a kunni. Ya gyara tsayuwa cikin tsare gira ya ce "Biyoni kawai ta salama Basarakiyar gobe."

Bata musaba ta rufa masa baya cike da sake nazartan halayyar da ya aro da rana tsaka sannan a gefe kuma ta ci alwashin hukunta shi haka komin rintsi da sa idonshi kafin mahaifinta ya fito daga dakin bincike sai ta mallaki Tulun gadonta domin batajin zata raba gadon da kowa hatta kuwa da shi Abun.

***
Suna barin wurin Lina ta bayyana gaban Bukkan ita da Hadimi Tsidau inda keyi mata fifita da fatar kunnin Giwa fuskansu dauke da murmushi.

"Uwargijiyata kina da kaifin basira duba yarda na koma Jarimi Buda na tasa miki keyarta cikin lumana sai dai marin da naushin danayi mata zai bar baya da k'ura domin ta rikeshi hanyar fansa akan Jarumi Buda kuma kinsan shi ɗin ba kyalle ba ne barinma da yanzu ke cike da haushin ajalin dokinsa da kikayi sanadi."

"Bar soko ai da gangar nayiwa dokin illa saboda na gano shi ke hasko masa lamuran dana boye."

Shugabana kina ƙara kutsa kanki cikin ayyuka masu hatsari domin kin haɗa Lima faɗa da Buda lamarin da zai iya haifar da ɗa mara ido a Tsibiri bayan burinki zaman lafiya ya wataci yankin naku."

"Bana dana sanin komi akan hakan dan kome zatayi matsalarta ce haka zalika Buda ya wuce da saninta hasalima baida lokacinta na tabbata kome zatayi mashi ba zai daga kai ya kalleta ba ko ni da nayi masa babban laifi ba zai kulani ba dan na tabbata ita ba za tayi masa mai munin wanda na aikata mashi ba."

"Haka ne Shugabana, kin gini hango gaskiya."

"Mu bar zancen haka Tsidau, yanzu zan tafi domin dauko Zobe na."

"Uwar gijiyata mu bar yankin nan na baki shawara mai b'ullewa domin na jiyo kamshin tahowar dan leken ashirin tsibirin na tinkaro inda muke cikin alk'aluman sihiri bisa umurnin Lima domin ta gano makircinmu."

Yana rufe baki suka b'ace b'at inda suka sauka a saman Dutsen dake tsakiyar Tekun Kabobo suka shige wani rami inda cikinsa ruwa ne ke kwaranya fari k'al, duwatsune masu suffar kujeru sun zagaye ruwan akan ɗaya daga cikinsu Tsidau ya zauna ita kuwa Lina kujerarta ya bayyana na zauna cikin mulki ta kalli Tsidau ya sunkuyar da kai tare da soma magana "Shugabata bana son ki d'auko ajalinki da hannunki domin ina jiyo amon sautin fitar ruhinki daga muhallisa shi ne d'azun ya sakani zub da jirwaye(hawaye), wannan hatsarin ya sanya Shugaba Gauɗu ya birne shi a ƙasan Teku dan haka kema ki barshi a inda yake inma da hali ki fita sabgarshi har abada dan bala'in da ke cikinsa yafi nasarar da kike hange."

Shiru ya ratsa wurin na tsawon mintoci goma sannan Lina ta sauko saman dutsen kujerar da take zaune ya b'ace ta tsomo kafafunta cikin ruwar dake da mugun sanyi ta lumshe ido kana ta bud'esu tar akan Tsidau da ya sake sunkuyar da kai ƙasa cike da ladabi.

"Ya Amintaccen Hadimina na fahimceka amma in kaga ban sanya Zoben nan ba to numfashina na ne ya bar jikina sannan kada kayi kuskuren boyemin ganinsa domin na gano kana shirin aikata hakan sannan ka sani son mulki a jinana yake dan ko da zan hau karaga da dak'ik'a ɗaya ne numfashina ya bar jikina sai na hau a sanya lissafin sunana cikin Sarakunan da suka mulka Hatsabibin Tsibiri."

"Allah huci zuciyar Shugabata, nasara naki ce nabarki lafiya zan tafi hutu amma ki sani ban shirya komawa ga Iyalaina ba."

"Sauka lafiya hadimin gaskiya, ka huta sosai bana tare da matsala."

Motsa kai yayi tare da komawa jemake ya fice daga kogon dutsen a guje.

Tsirawa hanyar da ya fice ido tayi zuwa can sai ta murmusa tare da cewa "Hadimi Tsidau mai amana ne, kada ka yarda wani ya yi nasarar rabaka da halin kirkin nan."

Ta jima zaune tana hasko abinda ke taɓa mata zuciya wanda batajin zai bar ruhinta ya huta domin a duk sadda ta kaɗai ce lamarin ne k yae mamaye zuciyarta. Numfashi ta ja idanunta ya kad'a ya koma jajur da sauri ta sunkuya ta tura hannu a cikin ruwan dake gangara, aikam take duwatsun wurin suka b'ace sai wata kofa babba ta bude ruwa na tartsi daga cikinsa, ta fadawa cikin ruwan kofar ta kulle duwatsun da suka b'ace suka dawo muhallinsu.

***
"Affuwan Shugabata ba zan taɓa tafiya na barci cikin tarin hatsari ba ina tare da ke bakin rai bakin fama indai Zobe ne a jalinki ba zan taɓa bari ki sanyashi a yatsarki ba ko da kin d'aukoshi."

Tsidau ya ambata bayan ya sauka a wani Tsibiri domin ganawan sirri da wani gawurtaccen Ifiritun Bil'adam, shi ɗin masanin warwaran lamura ne shi yasa ya taho gareshi duk da yasan rashin imaninsa amma haka ya yi kasadan zuwa saboda bawa Lina kariya.

***
Lima na tura ɗan sak'o dan ya nad'o mata abinda su Lina ke tattaunawa sai ta zarce gidan shak'atawar jama'ar Tsibiri inda suke cin karensu ba babbaka tunda suna gudanar da lamarin bisa son zuciyoyinsu ne shi yasa doka bata hawa kan Mazajen dake tayasu watsewar.

Tana shigowa hargowa da kid'an da ke tashi ya ɗauke, hatta da wanda suka killace kansu suna aikata shed'anci sai da suka yatsa cak, haka maja'ar wurin suka riƙa mik'o gaisuwa bata kula kowa ba ta sami wuri na musamman ta zauna wanda tana shigowa aka tanadar mata, saida ta ɗauki tsawon mintoci goma da zama sannan ta bada umurnin a cigaba da abinda a keyi wato kid'a da rawa tare da fasik'ancin da suke aikatawa a gaban kowa batare da alkunya ba domin wurin daki ɗaya ne a gefe wanda shima Lima ce ta bada umurnin gina mata tun sadda ta soma kawo ziyara wurin dan more k'uruciyarta.

Wasu samari ne kyawawa guda biyu ba kaya jikinsu sai gajerun wando suka taho gabanta suka zube, ta fesar da iska cikin Izza sannan ta yi masu nuni da kafad'arta suka tashi da hanzari suka soma matsa mata zuwa hantsen hannayenta, sai miƙa take saki cikin 'lumshe idanu cike da jaraba bajimawa wasu 'yan mata suma kyawawa suka zauna gabanta ta ɗora kafafunta a saman cinyoyinsu suka soma matsawa suna ja mata yatsu ta tana lumshe ido cike da jin daɗin yanayin abinda ya gusar mata da kaso mai yawa na damuwar da ta iso wurin da shi. Sun sami kusan awa ɗaya suna aikin yi mata tausa sannan ta dakatar da su ta mike zuwa dakin da yake tilo a wurin samarin suka rufa mata baya suna masu zame gajerun wandunarsu tun kafin su shiga d'akin yayin da 'yan matan kowa ta kama gabanta, sautin kid'a da ihun banza ya sake hautsina wurin ganin Lima ta basu wuri su baje hajarsu son rai saboda duk wanda ke wurin a buge ya ke domin antanadi giya na musamman domin nishad'i a wurin kowa zuwa yake ya sha yarda ya so ba mai yi masa iyaka, sai hauka sukeyi suna shiga jikin juna tamkar dabbobi.

***
Abun kuwa duk abin da ya faru yana kallo a madubin tsafinsa illa shigar su Lina cikin kogon dutsen ne lamarin ya b'oye masa sai halin da Lima ke ciki a wurin shak'atawa ya baiyana a madubin, cikin fushi ya mike tsaye sannan akaran farko kunyar abin kunyar da Saurauniyar Gobe keyi a gaban jama'ar da zata mulka ya k'ona masa rai, ya ja tsaki yafi sau shurin masak'i a ƙarshe ya koma zaune ya tsirawa allon tsafinsa cike da burin son gano abinda Lina ke b'oye masa musamman bayani akan Zoben sihiri. Hankalinsa ya kasu biyu ya rasa da wanne zai soma.

"Hak'ik'a yanzu nafi ku son dauwama a karagar mulki Tsibiri, zan jajirce dan ganin nayi tsawon rayuwa fiye da na Kaka Gunu yarda zanga mutuwarku batare da kunga nawa ba."

Ya furta cikin kaiwa wata batta duka a take ta fashe wani bakin ruwa ya malale ƙasa ya kai hannu ya kwalfe ya shanye sai ga kamanninsa ya sauya sai ya bushe da dariya na kaiwa k'irjinsa duka cike da gadara.

***
BIRNIN MUNGAYE.

Masarauta ce da ta kafu shekaru aru-aru wacce ta fara daga daji zuwa yanzu da take a matsayin babbar birni mai yalwan al'umman Barebari, Fulani da Buzaye, su ne manyan yarukan da suka kafa Masarautar domin Aliyu Malle da ya zamo tushen kafuwar Birnin babarbare ne, shi ne ya soma yada zango a dajin saka makon matsin 'yan uba da suke son ganin bayanshi sai ya baro garinsu ya dawo cikin dajin , ya cigaba da rayuwar kadaici, abokanansa su ne namun daji inda ke farauto na halal ya samu abinci. Yana a wannan rayuwa ce wata raba ya haɗu da 'yar Fulani da ta yi makuwa ya fitar da ita hanya daga nan fa ya sami wurin zuwa hira rigarsu har ya zama tamkar d'an gida, suka shaƙu da Fulanin matuƙa inda in ya kwana biyu bai zo ba zasu biyo sahun shi zuwa dajin Mungaye wanda a da yake gagaran su shiga kiwo saboda miyagun namun dajin dake halakasu.

A hankali Fulanin suka soma yo hijira suna dawowa sansanin Aliyu Malle inda suka nadashi Limaminsu domin shi ne silar musuluntarsu dan ya samesu kara zube ne basu san abin bautawa da gaskiya ba. Zamowarshi mai tarin ilimin addini sai ya riƙa fad'akar da su a ilmance har mafi akasarinsu suka amshi gaskiya, suka gane Allah subhanahu wata'ala ɗaya ne tilo baida abokin tarayya.

Momyn Haske ce🥰
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon

AWA.

Page 07

"Is ok my son, stop crying, mun huce Allah ya tsare gaba."

Mai martaba ya ambata cikin taping bayarshi ammsa sai ya girgiza kai ya sake dank'e k'afar Mamie Fulani yana sake fitar da sautin kukanshi tamkar ƙaramin yaro.

"My Fulani say something please, bana son jin sautin kukan nan."

Mai Martaba ya sake ambata cikin sigan rarrashi.

Itama girgiza kai tayi cikin b'oye fuskanta a lafayar da yazame daga kafadarta sakamakon jijjiga k'afarta da Sadauki keyi wacce itama kukan takeyi cikin b'oye fitar saurinsa hakan yasa ta kasa furta kalma.

A fusace mai martaba ya janyo Sadauki ya jefashi cikin k'irjinsa ya matse ya soma magana a kausashe.
"Me ye haka Aliyu? Shin a haka kake son zama sarkin Mungaye? To maza ka dawo natsuwarka bisa wannan sokanci dan baka gajeshi ga kowa ba, kai jarumi ne, Sadaukin babban Masarauta irin Mungaye domin tun kana yaro ka ci sunar Sadaukantaka dan haka ganinka cikin wannan raunin sunar zai iya b'atan dabo daga kanka zuwa wurin autar my Fulani Mu'allim."

Ya ƙarasa maganar cikin raha irin ta uba mai son farin cikin 'ya'yansa.

D'ago kanshi ya yi mai martaba ya jinjina masa kai sai ya maida yana mai goga tsinin hancinsa a k'irjin mahaifin nasa cike da jin natsuwar ruhi domin alamun hucewa ne hakan da ya yi masa.

"Abba fushinku ne ke son mai dani ragon maza, dan Allah a gafarceni na tuba ba zan sake maimaita kuren ba."

"Tuni ya wuce a gareni Aliyu domin ko wani bawa da kalan zanen ƙaddarar shi, to kai naka a auri saki ya fad'o."

"Godiya na ke Abbana."

Ya ambata cikin sake kafewa a k'irjin Mai martaba."

"Sake ni kada ka kadawa My Fulani miji."

Da sauri Sadauki ya janye jikinsa yana murmushi cike da farin cikin sakewar da Mai Martaba ya yi masa, ya dawo gaban Mamie ya langabe kai, tsare gira ta yi ya kalli mai Martaba cikin alamun ya sa baki sai ya zunkud'a kafada tare da kauda kai gefe sai ya tura baki tare da maido hankalinsa kan Mamie ya kamo hannunta ta janye cikin cewa "Kalli idon mai kuka kamar na ɗan yaye."

Murshi ya saki tare da saukewa bayan hannunta sumba ya furta "Nagode sosai Mamiena."

Shafo kansa tayi cike da kulawa, sai yaji malolon da ya tsaya masa a kak'oshi da faɗa ciki a fili ya furta "Ya Rabbi Alhamdulillah."

Ya mik'e dan nufin ficewa Mamie tayi masa nuni da ya koma ya zauna, lankwashe ƙafafu ya yi gami da tsira mata ido cikin neman sassauci, hancinsa ta ja ya saki numfashi tare da sake narkewa zuwa kalan tausayi.

"Yallab'ai a kira mai rukiyya ayima yaronka domin lamarinsa yayi kama da mai shafan shed'anun junnu."

"Aikam hakan za'ayi My Fulani domin nima mafarkaina na haskomin yana da Junnu."

"Wallahi bana da komi, ku yarda ina cikin azal ɗin ƙaddara ce."

Ya ambata cikin hanzari yana sake kama hannun Mamie Fulani.

"Babana ta ya zamu gamsu da hakan? Alhali ka bijirewa raya sunnar Manzon rahma, bayan kaima ta nan ka zo duniya."

"Zanyi aure Mamie, wallahi zanyi, kudai cigaba da yimin addu'ar had'uwa da zab'in ruhina."

Had'a idanu Fulani da Mai martaba sukayi suka jingina kai domin hasashensu ya tabbata kenan Sadauki bai son auren had'i kamar yarda suka ruk'a yi masa.

"Har zuwa yaushe zamu ga zab'in naka Babana?"

Shiru ya yi tsawon lokaci baida niyyar amsawa.

"Ok tashi ka tafi gobe da safe ka zo ina son ganinka nasan zuwa lokacin ka samo amsar tambayar Fulani dan nima ina dakon jin lokacin bayyanar zab'in ruhin naka Aliyu."

Godiya ya yi masu tare da mikewa natse ya fice sai dai kallo ɗaya zakayi masa ka hango jikinsa a sanyaye ya ke. Karo sukayi da juna kowa ya dafe goshi inda suka bugu, suka zubawa juna

Please Login or Register in order to submit comment