Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk inda taga dama a kuma sadda ta so dan har ta kan kwana a can amma bata wuce kwana ɗaya zuwa biyu duk tanayin tafiyar ne bisa amincewar Abun tare da neman albarkan Mah.

Lima hankalinta ya tashi sadda ta fahimci yawon da Lina ke fita wani sabon ilimi take samowa wanda nan gaba zai iya zama bara zama a gareta, sai itama ta soma yin nisan zango saidai ita ilimin zalunci take sake koyowa inda zata dawo tayi ta azabtar da bayi tare da jama'ar gari hakan kuwa na faranta ran Kaka Gunu domin alamomin gadar karagar mulki na ta ƙara bayyana a gareta, sai ya ƙara mara mata baya tana cigaba da zalintar wanda basu ji ba basu gani ba, har saida Abun ya tsawatar mata tare da nunawa Kaka Gunu illar hakan ya ce a bari ta hau mulkin zaifi wannan kalamin nasa ya fusata Kaka Gunu har ya ce ba wanda ta gaji ruwan tulun albarkansa sai Lima sai Abun ya rokeshi da ya b'oye zancen zai cika masa wannan wasiccin.

A cikin wannan tsakani Kaka Gunu ya mutu, Abun ya tafi dan mallakan Ruwan Tulun da sauran sirrikan tsafi amma ifritan da ke gadin Bukkan suka hana shi da ya matsa sai suka nemi halakashi kan dole ya hak'ura amma yana cike da burin mallakan wannan ruwa na albarka.

Bayan wasu shekaru burrin Lina ya cika domin ta samo ilimin da take burin mallaka wato tsafin da ya doke na Lima wanda yanzu take shirya fito na fito da wanda ya nemi kawo mata cikas a cikin manufarta na zamowa magajiyar karagar kujerar HATSABIBIN TSIBIBI domin shimfid'a mulkin adalci gami da samar masu da abin bauta su daina zama kara zube, su sami ilmomi mabambanta haka tana burin ganin wayewar su ya zarta na biranen da take shiga tana ganin cigaba da suke tare da shi mai burgewa haka babban burinta shi ne su sakko daga kan Tsibirin (Tsauni) su gyara dajin ya zamo birni mai zaman kan shi tare da kayan more rayuwa in yaso saman tsibirin ayi masa gyara ya zamo wurin shakatawa na musamman da jama'a daga birane daban-daban zasu riƙa zuwa yawon buɗe ido kuɗin shiga na halal na samuwa ga Tsibirin daga nan ƙarshen zalincinsu ya zo su kowa rayuwar 'yanci mai cike da farin ciki tare da zumuncin ga kowa, baƙi su zamo abar karramawa a tsibirin. Tarihin Hatsabiban Tsibiri da Sarki Goma ya gina ya zamo ya tarwatse sai wanda ta ingana da kanta, sunarta ya zagaye Duniya da tambarin Adalci. Saidai a gefen Lima duk kishiyar burin Lina shi ne nata wanda a kullum da shi take kwana da tashi.

*Wannan shi ne asalin labarin Tsibirin da rayuwar jama'ar cikinsa gami da burikan tagwayen Gimbiyoyin.*

Cigaban labari.

***
Lima a Bukkan Kaka Gunu.

Ta tura kai cikin Bukkan bayan ta yi amfani da alkaliman sihiri k'ofar bukkan ya buɗe, cikinsa katon wuri ne da ya cika da k'okunar kan namun daji kala daban-daban a can daga nesa wani kilisa ne mai daukan ido samansa da kujerar na alfarma ce, wurin Lima ta nufa ta hau saman kujeran ta zauna tana fesar da iska cikin nuna izzar jinin sarauta.

"Barka da isowa uwar gijiyata, me ke tafe da ke?"

Kallon tsamurmurin tsohon ta yi cike da mamakin bayyanarshi ba neman iso daga gareta.

"Affuwan uwar gijiyata na kasance zaune a wannan bigire shekaru masu yawa domin tun sarki na biyu nake a matsayin hadimisa sannan nine sirrin dukkanin sarakunan da suka shude dan haka kema nine idonki akan komi umurninki kawai nake jira yanzu kiga aiki da cikawa."

"Me ye sunarka?"

"Tsidau uban yan binciken wannan fada."

"Madallah, yanzu na zo ne domin sanin abin da 'yar uwata Lina ke boyemin game da tafiyarta da duk abin da ya faru gareta tun kafin tafiyar har zuwa yanzu."

"Kwanta ki huta uwar gijiyata kina tashi na yi alkawarin bayyana miki duk abin da ya shige miki duhu akan Gimbiya Lina."

"Tsidau bana jin barci domin bashi na zo yi ba."

"Dole kiyi shi uwar gijiyana."

"Kada ka kawomin wargi na hukunta ka y kai Tsohon wofi."

"Tuba nake Sarauniyar Gobe, fushinki kukan yaro."

Tana shirin sake magana ya hura mata iskan bakinsa a take ta zame daga kujerar kanta langabe alamun barci ya ɗauke ta, da yatsarshi ya nunata sai gata kwance saman kilisar ta yi matashin kai da wani filo mai zanen fatar jakin daji.

"Shin ta ina zan soma boye miki sirrin abin da kika zo bincike?"

"Bar wurin don ka gama aikinka kafin ta farka na nade sirrin da aka barmata gado."

Muryan Lina ya ratso.

"Na barki lafiya Gimbiya mai jiran gado."

"Ko da yake kafin nan zauna da ita ya kai amintaccen hadimin Sadauki Gauɗu bari in koma na sallami wancan lalataccen kada maikon kogin da ya yi jagorar samar da shi ya halaka shi."

"A dawo lafiya ya ke adalar Sarauniyar Duniya."

Murmushi ta yi tare da b'acewa shi kuma ya gyara zama gaban Lima ya tsirawa hawa da saukan numfashita ido tamkar mai irgawa. Rugigi ya ji a bayanshi kafin ya tantance dalilin afkuwan lamarin Bukkan ya ɗauki rawa wani gaton dutse ya d'ago daga ƙasa inda ke zaune ya nufo inda ya ke yana fesar da koren wuta, tamkar walkiya Tsidau ya b'ace a daidai lokacin Lima ta farka a firgice sai dutsen ya koma mazauninshi tamkar bashi ba. Abun ne ya shigo a rikice ta tashi da hanzari ta isa gabanshi ya rik'o hannayenta ya soma magana.

"Ya ke farin cikina wannan binciken yafi karfinki dan haka ki lamuncemin amsar gadonki domin na samu damar taimakonki."

"Abun zan iya, kabarni da kayana."

"Bazaki iya ba tunda ga shinan an sakaki barci bisa hila wanda saninki da ilimin tsafi bai amfana miki komi ba a wannan gab'an."

"Abun waye Tsidau?"

"Hadimin ne ga 'yar uwanki Lina."

Ware ido ta yi cikin cewa "Lallai Lina ta shiryawa taran aradu."

"Biyoni kawai domin sanin ta inda zaki bullowa lamarin."

Biyo bayanshi ta yi cike da zantukan zuccin wanda ta sanyawa ranta sai ta nemo sanadin afkuwansu dan hatta Abun ta soma wasi-wasin a kansa.

***
Lina ce tsaye a saman ruwan Tekun Kabobo fuska a haɗe ta watsa wani haske da ya fito daga babban yatsar hannunta na dama,a take maikon da ya b'ata ruwan ya soma tafiya har ya b'ace amma launinsa na yellow bai sanja ba. Ta sake tsuke fuska tana fitar da huci zuwa can ta yi gunji ta soma tafiya a saman ruwan a hanzarce har ta isa tsakiyarshi kujerarta ga gold ya baiyana a saman dutsen da ke tsakiyar Tekun inda wasu halittun ruwan sukayi dandazo domin gudun hijira daga halaka, ta zauna tare da tsirawa ruwan Tekun ido da ya ke sake komawa yallow mai duhu, zuwa can dokin Buda ya taso sama ruwa ya yi tartsi tare da fitar haniniyarshi mai firgitarwa inda halittu suka sake rudewa da neman mafaka sai kuma ya koma ciki tsundum! Tamkar an janyoshi, kimanin mintoci biya ya sake tasowa sama wannan karan Buda na kwance saman bayarshi tamkar Gawa, tafiya yasomayi a saman ruwan cikin jan ƙafa saidai kafin ya kai bakin gab'a wani igiya daga kasan ruwan ya fito kamar walk'iya ya maidashi ciki sai ruwan ya sake rukid'ewa zuwa bak'in-k'irin tare fitar k'ugi tamkar rugugin hadarin damina.

Lina da ke kallon komi ta mik'e tsaye da sauri tare da kulle ido ta nuna ruwan a ta ke dokin da Buda suka taso sama ta tura hannunta gaba suka tafi a guje tamkar tsintsaye suka zube a saman yashi da ke gefen Tekun. Ta sauke numfashi ta re bud'e hannayenta ta nuna ruwan ya dawo launin shi fari k'al yana murdewa yarda ya keyi a tun farko, ai kafin kwabo Halittun nan sun soma rige-rigen komawa muhallinsu, ido ta zuba musu tana sakin murmushi ta sunkuya tamkar zata fad'a cikin ruwan sai kuma ta tashi tsaye tana mai shafan gefen fuskanta cikin cewa "Na sami cikar burina na taimakon dabbobin ruwa tare da sokon can Buda, mulkin Adalci ya soma sauka daga hannuna, godiya gareka Sadauki Gaud'u da kayimin komi na ganin na mallaki ilimin tsafin da ya zarce na ko wani matsafi dake nahiyar nan harma da waje ta, hak'ik'a zanyi aiki da Adalci tamkar yarda hakan shi ne cikar burinsa, ganinan tafe zuwa mik'o gaisuwa ga ruhinka abar girmamawata, tabbas idan na zama Sarauniyar Tsibiri kogon da kabarinka ya ke nan ne wurin bautarmu."

Tana kulle baki ta rikid'a zuwa k'aramar tsuntsuwa mai shegen gudu ta lula sararin samaniya ta ɓace tamkar kibiya sai dai tana sauka a cikin kogon dutsen da kabarin Sadauki Gauɗu yake idonta ya sauka kan Hadimi Tsidau kansa sunkuye cikin tsantsar ladabi ya soma magana.

"Uwar gijiyana ayimin gafara lamarin ne ya sha gabana domin na kusa halaka kuma a faruwa hakan na gano ma'adanar tulun sirrin da kike burin mallaka sai dai zamowa mallakinki da kamar wuya saboda manyan iffiritai ne ke gadinsa kuma mahaifinku shima na burin mallakan tulun ya tura 'yar uwanki ne domin ta binciko Tulun sai ya tabbatar ta nemo sai ya taho ya amshe cikin hikima saboda ya san iffiritan da ke gadin Tulun ruwan albarkan baza su yi mata komi ba sabanin da in shi ne zai iya rasa ranshi dan ya taɓa jaraba mallakansa ya sha da k'yar."

Numfashi Lina ta sauke tare da buɗe idanunta da suke kulle tun soma maganar Hadimi Tsidau ta kalleshi na sakonni ta jinjina kai batare da ta furta kalmar ba ta matsa gaban Kabarin Sadauki Gauɗu ta russuna gabansa ta miƙa hannunnta na dama ta ɗora saman Kabarin kanta sunkuye, ganin haka sai shima Hadimi Tsidau ya taho da sarsarfa ya russuna a bayan Lina tare da sauke kansa ƙasa, ta sami mintoci goma sha biyar a haka sannan ta mike tsaye shi kuma Hadimi Tsidau na nan sunkuye cikin girmamawa. Murmushi ta yi kana ta soma magana cikin tsantsar isa da mulki inda kallaman ke fita ɗaya bayan ɗaya.

"Tsidau zanyi aikin da kaina domin ina tare da Zobben sihiri na Sadauki Gauɗu duk da saka Zoben tamkar na yafa mayafin mutuwana ce ga rayuwata amma akan cikan burina zanyi wannan kasadan saboda da in mutu a hannun Lima gara na ƙare rayuwa a matsayin baiwa a masarautar Sarki Gamji ko ba komi shi ɗin mahaifi ne ga shugabana Sadauki Gaud'u."

"A'a Uwar gajiyana banayi miki fatar shiga hannun azzalimin Sarkin nan wanda har 'ƴa'ƴan cikinsa bai bari ba saidai kafin ina baki labarin hatsarinsa zanso sanin sirrin da Zoben ke tare da shi da na kasa ganowa tun sadda mai gidana Gaud'u ke sanye da shi."

"Tsidau bana buƙatar jin komi daga masarautar Sarki Gamji domin Sadauki ya sanarmin da komai sannan Zoben da zan fito da shi yana ƙasan Tekun Kabobo sirrinshi mai faɗi ne domin duk wanda ke tare da shi a cikin yatsarshi yafi ƙarfin duk wani matsafi haka duk abin da ya tunk'ara sai ya samu nasara komin wuyar lamarin, in barka haka."

"Tafdijan amma Shugabana yana da wannan Zoben ya yi sake mugun nufin mahaifinsa ya yi nasara akanshi?"

"Ya sanarmin ya wuce shekaru bakwai da cire ainihin Zoben a yatsarshi jabun ke sanye da shi tare da boyewa mahara Zoben gano jabun ne ke yatsarsni cikinsu har da mahaifinsa domin burinsa ya mallakamin."

"Shugaba ya sanki da jimawa kenan?"

Jim ta yi domin bata son ambatar ƙaddarar da ya taɓa afka mata wanda ya kasa b'acewa a ranta haka ta kasa maida hankali akan gano dalilin faruwar lamarin kamar yarda tak'i amincewa ruhinta a hukunta mai laifin duk da tarin damar da take da shi na aikata masa komeye da ta so amma ganin Tsidau na dakon amsarta sai ta amsa a takaictda " Eh."

"Affuwan Uwar gijiyana, ban gamsu da amsar nan ba a matsayinsa na sirrintaccen Hadiminki bai kamata ki riƙa bani bayani a dunkele ba dukda ina aljani zan iya gano kome kika boye saidai alkawari nayiwa Shugabana cewa bazan taɓa binciko sirrinki ba kamar yarda ban taɓa gigin binciko nashi ba bisa alkawarin da na daukan masa wanda wannan lamarin yasa aka kawo masa hari batare da na nasan meke faruwa ba dan haka a yau ina neman alfarman ki amince alkawarin da na ɗaukawa Shugabana ya zamo tarihi inda zan riƙa sanin abin da zai sameki na kangin rayuwa kafin ya iso na tareshi na maidawa wanda yayo aiken."

"Godiya nake ya kai Tsidau amma ban amince ka zamo cikin marasa cika alkawari ba, ina son ka yarda komi nawa kada ka binciko sai wanda na baka dama, ka dauwamma a aikinka na ɗan aike tare da rakiya zuwa inda nake da muradin tafiya da kai."

"Angama ya ke Uwar gijiyana, Gimbiyan gobe bisa amincin mahaliccin tsuntsaye da tsirrai."

"Tsidau ina yawan jin kalaman nan a bakin Sadauki Gauɗu sannan duk in ya furta na kanji kaina ya yi girma basirana ya toshe inda nake hango kaina cikin wani duhu tare da haske daga nesa can, shin me hakan ke nufi?

"Uwar gijiyata rayuwar Shugaba na tarin ababen al'ajabi domin duk nacina akan ya bayyamin sirrin da ke cikin kalaman nan ya k'i dan haka ban san komi akai ba domin harshesa nake kwaikwayo har na ambata miki hakan sai dai ina ta tabbacin wani abin bautane mai girma da ƙarfin mulkin da ya doke wanda su Sarki Gamji ke bautamawa."

"Zanzo sanin shi ko da kuwa hakan zai iya zamowa ajalina ne."

"Uwar Gijiyata kidaina ambatar mutuwa baki zamo Shugaban Tsibiri ba wacce adalcinta zai kewaye Duniya."

Murmushi ya kubce mata sannan ta fuskanci Tsidau tana mai cewa "Ya kai amintaccen Hadimina hakika mun kusa rabuwa domin da zarar na sanya Zoben, zan bacewa ganinka na har abada kai kuma zaka tsinci kanka cikin jinsinka cike da yanci daga nan kazamo yantacce daga bawa ni kuma zan mallaki Tulun ruwan albarka saidai ba zan jima ba akan karagar mulki Tsibiri Sarki Gamji sai aikomin da sako walau irin wanda ya aikowa Sadauki Gauɗu ya halaka ko ya ɗaukeni daga yankin zuwa kurkukunsa na karkashun ƙasa na tabbata a can har zuwa sadda mutuwa zai riskeni dan haka yanzu zan koma Tekun Kabobo in d'auko Zoben, ina godiya da taimakon da ka riƙa bani na duk abin da nake son ci da sha tare da sutura, gaisuwata mai yawa zuwa ga iyalenka, sai wata rana."

Momyn Haske ce 🥰
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabiban Tsibiri
By mrsjmoon

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.

https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks.🖕

06

Tafiya na ƙara nisa inda zuwa lokacin Aliyu Malle ya tara iyali mai yawa dan ya auri bafullatanan da ta yi makuwa mai suna Mero haka ya nemi aure a wurin wani Buzu shima da ya fito ci rani yaga dajin Mungaye ya zama maraya sai ya zauna da iyalinsa, sannan ya koma Asalinsa ya auro 'yar uwarshi Kanuri inda ya auro har guda biyu, a lokacin danginsa suka soma nuna masa ƙauna tunda suka gansa cikin rufin asiri musamman sarautan da yake da shi yanzu na matsayin Sarkin Birnin Mungaye. A wannan komawa danginsa da yayi wasu daga ciki suka biyoshi tare da iyalansu sai Masarautan Mungaye ya sake cika da al'umma. Daga nan auratayya ya cigaba da kulluwa tatsakanin kabilun uku wato Barebari, Fulani da Buzaye.

Wannan auratayya da ya kullu tsakaninsu sai ya tsakud'a ya fitar da wata kalan al'umma masu kyawun sifa gami da kyawun launin fata, fuska dana sura. Kowa ka gani a cikin birnin Mungaye mai kyawu ne musanman 'ya'yan gidan sarauta domin Sarki da matarsa masu tsan-tsar kyau ne, wasu masu hasken, wasu mai sirki da ja da kuma masu haɗi da duhu kaɗan amma duk wanda ka kalla mai kyau ne a Masarautan dan har akanyi masu kirari da Birnin Mungaye mai kyawawan Mata.

Birnin ta sami wayewa bisa ziyartan turawa inda suka gina makarantun Boko tare da kawo malamai suka riƙa koyar da su ilimin zamani duk dama can akwai masu Ilimin daidai misali musanman Sarki Aliyu Malle tare da danginsa, sai dai hak'ar Turawa bai cimma ruwa ba na samun nasarar rabasu da addinin da suka samesu akai wato Musulunci wanda burin sanja masu tunani ne su koma bin addininsu ya sanya suka shigo birnin sai suka samu Sarki Aliyu Mallae ya yi namijin kokari akan al'umman shi na ganin sun ginu akan turban gaskiya na kaɗaita Allah Subbahanatu Wa Ta'alah gami da riƙo ga sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, shi yasa har izuwa yanzu Birnin Mungaye cike ya ke da musulmai, malamai gami da tsirarun mabiya addinin Yahudu da Nasara wanda suke zaman lafiya da juna domin tun tarihin kafuwar Birnin babu abin tashin hankali da ya taɓa kawo matshi ziyara ko riciki a bisa bambancin Addini ko wani tarzoma na daban sai dai su jiyoshi a makwaftansu saboda sunyi imani da Allah ɗaya ne kuma suna masu jajircewa wurin zaman addu'o'in samun kariya ga Birnin tare da zaman lafiya tsakaninsu suma sauran k'abilun nayin irin tasu addu'ar awurin bautarsu. Wannan tsarin ginin tubalin zaman lafiyar duk ya samune bisa jajircewar mai Mungaye wato Malami, Sarki kuma Limamin Birnin Aliyu Malle wanda ya rasu shekaru masu yawa sai tsa-tsonshi sukayi ta gadan Sarautar har zuwa kan sarki na yanzu Sarki Abdul Hakam. A dalin jagora tamkar 'yan uwanshi da suka gabata sai dai shi ne Sarki mafi wayewa domin dan Boko ne na gaske wanda ya taka har zuwa matakin Professor, shi yasa hawa karagar mulkinsa ya zo da sauyi wurin shigo da abubuwan Zamani fiye da sarakunar da suka gabace shi.

Abin burgewa ga wannan ƙasaitacciyar masarauta shi ne riƙon Addininsu domin har zuwa yanzu sarakunarsu sune Limamai kuma masu gabatar da tafsirai a lokacin Azumin Ramadan dan haka babban masallacin Juma'a na garin a kofar Fada take kamar yarda mafi yawan masarauta aka sani da gina Masallatai da ake sallar Juma'a a Fadar su, saidai wannan a cikinta ake sallar Idi dan takasance mai girma tamkar wata Masarautan kaso sake ginawa haka a gefen Masallacin wani daji ne da aka killace shi aka cika shi da shuke-shuken kayan marmari wanda ina mutum ya shiga zai dauka a wani yanki na daban ya ke saboda yalwar bishiyoyi tare nisan tafiya kafin a isa k'arshenta, aka ba wurin suna da Mungaye Garden.

Wannan ak'idar da Masarautar ta ginu da shi na son Musulunci da Musulmi shi yasa jama'anta suka kasance masu karamci ga bak'i masu zuwa fatauci da zama na mundun rai. Dan ƙasar Mungaye Allah ya hore mata kyawun fitar tsirrai (Amfanin gona) shi yasa Manoma suka cika garin ta ko wani sassa da ke makwaftaka da ita, lamarin da ya kara daga darajar Birnin ta zamo abar yabo ta ko ina haka duk inda ɗan Masarautar ya shiga yana da alfarma.

Mai martaba Abdul Hakam na da Matan Aure biyu. Uwar gida Hajiya Hafsatu (Umma Babba) da Amarya Hajiya Murjanatu (Mami Fulani) da yara maza da mata sai dai 'ya'ya matan ne manya domin wasu sunyi aure tare da albarka zuri'a. A yanzu Mai martaba girma ya soma kamashi, babban burinshi ya yi murabus ya dank'a mulkin hannun ɗaya daga cikin zaratan matasan 'ya'yanshi wato Ahmad (Sardauna) da Aliyu (Saudauki) Sai dai ƙurar da ke hangowa ya sa ya tsuke bakinsa akan ayyana wanda zai zamo magajinsa cikinsu, ya zuba masu ido yana sake lak'antar halayyan kowa tare da wanda Jama'a sukafi nuna k'aunarsu da ya zamo jagoransu makar yarda mahaifinsa ya yi sadda aka bashi mulkin duk da baida ra'ayi amma jama'ar gari suka nuna shi ne zaɓinsu kuma ba jayayya 'yan uwansa sukayi masa mubaya'a sai dai a wannan lokacin baijin shi zai sami sauk'in dank'a mulki da ɗaya daga cikin 'ya'yan nasa ba saboda kowa yana nuna mulkin ya ke so bakin rai bakin fama.

A fannin Yarimomin Mungaye kuwa duk sun can-canci hawa karagar mulkin sai dai jama'ar gari sunfi nuna ra'ayinsu akan Sadauki sama da Sardauna duk kuwa da matsalar da ke ga Sadaukin na auri saki domin a shekaran da ya gabata sukayi auren fari amma zuwa yanzu ya mata huɗu ya aura ya saki batare da sanin laifin da suke aikata masa ba domin ya k'i yin bayanin da yasa ke aikata sakin haka suma matayen idan an tambayesu amsar ɗaya ce suke bayarwa ita ce basuyi masa laifin komi ba ya sallamesu ba tare da ya haɗa shimfida da su ba.

Cikin matar na ya saka akwai ta farko 'yar kanwar Sarki mai suna Mubina wacce aka aura masa tana da k'arancin shekaru domin kammala secondary dinta kenan a ka yi mata aure cikin rashin son ranta inda shi kuma Sardauna aka aura masa 'yar Waziri wanda shima ya ke kani ga sarki kuma har wayau k'anwa ce ga aminin Sadauki wato Abubakar ana yi masa alkunya da Imam, wacce ta kasance babba mai yalwar komi na cikar halittar mace sama da Mubina, wannan bambancin da ke tsakanin matan nasu yasa sadda Sadauki ya saki Mubina a washegarin kaita gidanshi yasa hankali bai wani tashi ba musamman da ita Mubinar ta yi ta murna har aka ɗora laifin akanta ganin yarda ta yi ta boren bata son auren sai ake zargin ita ce ta nemi sakin da kanta.

Matarsa ta biyu 'yar Aminin Sarki ne wacce ta zamo mai wayewa domin ita tana da degree har biyu amma kwanarta uku a gidanshi ya saketa hankali ya tashi a wannan karon amma Sadauki ya nuna ko a jikinsa, akan haka Mai Martaba ya ce ya gama samo masa matar aure. Bayan watanni Mamie Fulani ta matsa sai ya amince da auren 'yar aminiyarta inda ya amince bisa takurashi da tayi saidai shima auren kwanarshi daya ya bata sallama inda kafin ta isa cikin Masarautar da labarin ya tsere gidanshi da ya gina a b'oye da ke dajin Tekun Kabobo wurin da ba wanda ya sani sai amininsa Imam da turawan da sukayi aikin. Bayan wasu watanni ya dawo ya sha faɗa tamkar Sarki zai dukeshi ya yi ta basu hak'uri, anan suka rutsashi sai ya sanar masu da matsalarshi Amma yak'i magana akan dole suka rabu da shi, daga nan bai sake aure ba sai wata ɗaya da ya wuce inda Na'ibin Sarki ya bashi sadakar d'iyarshi mai wadataccen ilimin addini sai dai yana jin labarin ya hankalinsa ya tashi inda Mami Fulani ta rufe shi da faɗa tare da gargadi akan kada ta sami labarin ya saki yarinyar inko ya kuskura ya aikata mai rabata da shi sai Allah wannan kalma ya hura wutar jin rabuwa da Sakina wacce a ranar da aka kawo mashi ita ya bata saki wanda faruwar haka ya saka Masarauta shirya taron zama na musamman akanshi a karan farko tun soma wasa da auren da keyi gami da son zubar da Martaban Masarautar su domin lamarin na taɓa ran manyan masarautar musanman Baba Chiroma da yafi kowa zafi haka ansha mamaki da har zuwa lokacin bai nemi ganawa da Sadauki ba shi yasa yanajin sakon kiran da yafito daga bakin sa sai ya gudu mab'oyarshi tare da gargadin Imam akan kada ya sake ya tona inda ya ke. Sai da ya sami wata ɗaya da kwana biyar wato sati biyar kenan sannan ya dawo inda ya ke kan fuskantar fushi daga mahaifanshi ya yin da dan uwanshi Sardauna ke yi masa shagub'e na kiranshi da kalman mai auri saki mara godiyar Allah, duk da kalaman nayi masa ciwo amma ko kallo bai isheshi ba balle ya tsaya bashi amsa wanda ke kallo a matsayin bata lokaci sannan duk da hakan kauanrshi ga Jama'ar gari bai rage komi ba wannan lamari ya rage masa damuwar da ke ciki na fushi da mahaifanka keyi da shi. Duk da b'oye halin da ke ciki da ya keyi amma kallo ɗaya zakayi masa ka gano yana cikin matsanancin damuwa wanda Amininsa Imam ke aikin bashi baki.

***
Aliyu Sadauki.

Tsaye ya ke a bakin window dake bedroom dinsa inda ke kallon kai da kawon hadimai bisa alamu manyan baƙi ne zasu halarci Masarautan. Bushe-bushen da aka soma ne ya sashi barin wurin ya koma saman sofa ya kwanta idanunsa na kallon sama zuwa can ya tashi zaune ya furzar da iska mai huci tare da kaiwa k'irjinsa duka ya rintse ido da hanzari jin yarda zafi ya ziyarci wurin da ya duka. Ya juya kai cikin furta "Why ta zamemin masifa a rayuwa? Shin aina zan sake ganta? Shin ita din mutum ce

Please Login or Register in order to submit comment