Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mahaifiyarku na yi miki kashedi kina watsi da kamarin saidai a yau na hango alamun ta samo sanin alk'aluman tsafi fiye da wanda kike tare da shi dan na kalli artabunku na d'azun duk da ta yi dubarar b'oyewa cikin iskan guguwa dan ta san zan gani sai amma ta makaro dan komi ya bayyana gareni tamkar kuna gabana."

"Abun dama ba mafarki na yi na had'u da Lina ba har muka goge raini?"

"Eh ba mafarki ba ne, tabbaas kin had'u da Lina wanda hakan ya bawa Buda damar gano inda ta ke ta bayan b'atan dabon da ta yi na tsawon shekara d'aya da watanni ta hanyar jiyo k'amshinta wanda ta nan mafi akasarin jama'ar Tsibiri ke ganeku.."

"Abun me kake son sanar dani akan 'yar uwata Lina?"

"Babu komi 'yata illa hatsarin da Lina zata zame mana musanman ke domin zuciyarta ya ginu da tausayi ne ya yin da na ki ya ginu da tsabar mugunta, Kaka Gunu ya sanarmin d'abi'unki na kamanni da kakan-kakanninmu wanda shi ne silar samuwar Tsibirin nan wato Sarki Goma na farko."

"Abun rabani da wannan zantukar gaibun na Kaka Gunu yanzu babban damuwata shi ne sanin gaskiyan abin da Lina ke b'oyewa."

"Nafiki son gano lamarin da ta birne wanda bokayenmu suka kasa gano shi hatta kuwa da ni sarkinsu kuma jagorar wannan tsibiri."

"Abun, shin yanzu Lina tafika k'arfin tsafi kenan?"

"Bata isa ba Lima."

"To meye yasa ka kasa gyara Mata zama?"

"Har abada bazan tab'a fito na fito da ita ba saboda ina son 'yata haka itama bazata tab'a yin gaba da gaba da ni ba domin girman da ta ke ganina da shi ya wuce tunaninki tana kawai nuna miki tafi damuwa da mahaifiyarku ce kamar yarda kika fi nuna damuwa da ni sannan zan baki aiki wanda na san akanshi kike wato na son gano lamarin Lima baki dayanshi na tsawon tafiyar da ta yi."

"Ina saurarenka Abun."

" 'Yata Lima a yanzu nake son ki shiga bukkan Kaka Gunu kiyi wannan binciken."

"Abun yau da kanka ka amince in shiga taskan sirrin Kaka Gunu wanda ya ke kulle tun bayan mutuwarshi?"

"Eh na baki damar shiga ya ke 'yata, dama can gadonki ne dan ya tabbatar min ke kad'ai ya mincewa shiga bukkar amma bisa babban bincike shi yasa na baki umurnin shiga dan gano mana abin da Lina ta b'oye da kuma wanda ya koyar da ita dabarun ilimin sihirin da ya ke son doke wanda muka gada Kaka da kakanni."

"To Abun kasan da wannan wasiccin ka barni ina ta wahala tsawon shekara d'aya da rabi akan wancan sokuwar yarinyar?."

"Akul Lima! 'yar uwarki ce bana son wannan tsanar da kike nuna mata wanda na yi imani shi ne silar b'oye miki sirrikanta ga shinan zai wahalar da ke a banza."

"Abun bana sonta tunda Mah ta nuna da ita take yi ba ni ba."

"Lima kin sanfa an raba ne ke ce nawa ita kuma na Mah ɗin ku."

"Na barka lafiya Abun gobe da safe zan taho maka da bayanai wanda na amince tono sirrin Lina ce kaf d'inshi."

Ta ambata tare da mik'ewa bayan ta subbaci bayan hannunshi.

"Baburdo ya taimakeki 'yata."

"A'a Abun ruhin Kaka Gunu ya bani sa'a zakace domin Baburdo Dodon gadin Tsibiri ne bai isa bani taimakon komi ba saima ni ce keyi masa alfarma na shaƙar ni'imar Tsibirin."

"Haka ne Lima to ki fito lafiya cikin kiyayewar Ruhin Kaka Gunu."

"Amin."

Ta fice cikin sauri tana yarfe hannaye cikin salon mugunta inda yarfin ke fitar da iska na watsar da mutanen da duk ta ci karo da su a kan hanya wasu tsoffi ne da yara k'anana ya yin da masu ƙarfin tsafin ke kare kansu tun kafin ya iso inda suke, ganin jama'a na neman wurin buya saboda giftowarta sai tayi amfani da wuta da kunna a tsakiyar Tsibirin a take mutane suka soma kulle gidajensu masu sana'a suka tsere wutar ta soma bin kayansu tana lashewa, sai hakan ya wadata k'irjinta da nishad'i tayi ta zabga murmushi, batare da ta kula da illar da wutar takeyiwa jama'ar ba tayi gaba abinta tana dariya.

Ruwan ƙanƙara ne ya sauko a cikin minti ɗaya ya kashe wutar tare da ɗaukewa batare da sanin Lima ba hakan ya afku, jama'a suka dawo bakin kayansu suna tsinewa Lima a cikin zukatansu.

Tafiya mai tsayi Lima ta yi kafin ta isa bakin bukkan da ke cikin kogon wani dutse duk a saman Tsibirin.

WAIWAYE A DON TAFIYA.

*Asalin Tsibirin da mutanen da ke rayuwa a cikinsa.*

Hatsabibin Tsibiri, Tsibiri ne mai dogon tarihi domin sarakuna masu dama ne suka shud'e a cikinsa kuma dukkannunsu abisa turba d'aya suka ginu wato tsafi da kafurci domin basa da abin bauta balle wurin bauta, gasu nan dai kara zube domin ko Dodo Burda da ke TSIBIRIN basa bauta masa dan a mai gadi suka ajiyeshi ta hanyar yin bishara idan bak'o ya shigo ko samun wanda ya karya doka na yiwa mata fyad'e dan duk da wannan duhun da suke ciki suna kyamatar ketawa mata haddi.

Mafarin TSIBIRIN ya samu ne bisa jagorancin sarkin farko mai suna GOMA wanda aka ci shi da ya k'i inda ke mulkin al'uma masu yawa, sakamakon rashin nasarar da ya yi ne ya yi hijira da iyalansa ya yada zango a Tsibirin lokacin wurin sansanin miyagun namun daji ne da suka kashe dajin mafarauta da makiyaya suke tsoron haurowa samansa,.

Saukan sarki Goma ya sa suka koma gefen TSIBIRIN suka kewayeshi cikin yi masa mubaya'a domin k'arfin tsafinsa kad'ai ya isa zamowa bara zana ga rayukansu.

Sarki GOMA ya yi nasarasar k'awata TSIBIRIN cikin alk'aluman sihiri yarda kowa ya keto cikinta sai ya burgeshi kuma ya zamo ganimansa in ya so ya maidashi bawa in kuma ya so ya kasheshi musanman idan ya bincika yaga mai addini ne. A haka ya cigaba da shimfid'a mulkinsa tamkar yarda ya keyi a birninsa da yayo hijira sai dai ya k'ir-k'iro wasu ababe ya sanya su doka mai zaman kansa wanda d'aya da ga ciki shi ne sanadin yo hijiransa wato dokar ita ce ta hana mazaje haik'ewa Mataye wato yi musu fyad'e amma bai hana zinace-zinace ba abisa ra'ayin juna amma ayiwa mace da k'arfi wannan babban laifi ne domin duk wanda ya aikata hakan kafin macen ta kawo k'ararsa fadar Sarki Dodon Burda zai yi kuwwa mai razanarwa kuma a take kowa zai halarta gaban faɗar Sarki inda wanda ya aikata laifin zai fito da kansa tsirara mahunta lamarin su sanya takofi mai kaifi su datse masa al'aura tare da d'aukansa zuwa wata muguwar k'orama da Sarki GOMA ya k'irk'ireta na musaman domin hukunta masu laifi mai suna k'oranar sihiri, su jefashi ciki, wacce ba komi cikinta sai ruwa mai rai da lafiya tare da manyan Kadoji wanda abincinsu ya zamo manyan namun daji da mutane masu laifin aikata fyad'e da masu hayowa tsibirin dan ganin k'wam. Haka duk sarkin da ya hau sai ya k'ara inganta wurin da salon muguntarshi na daban inda kudin shigarshi zai sake ninka na sarkin da ya gabata.

Wannan doka na hana fyad'e Sarki Goma ya aiwatar da ita ce saboda 'yarsa d'aya tilo wacce ya ke tsananin so da k'auna Gimbiya Aya da wani cikin jama'arsa ya yi.mata fyad'e lokacin da tafita shak'atawa bayan gari a sanadin ta rasa ranta sai gawarta aka kawo masa cikin jini babu kyan gani hankalinsa ya tashi ya bazama duban wanda ya aikata laifin sai ya baiyana d'an sarkin yak'insa ne ya aikata a ta ke ya sanya aka kamosa ya datse masa kai da hannunsa a bainar jam'a lamarin da ya haifar da k'azamin fad'a tsakaninsa da rundunar Sarkin yak'i inda Sarakunan da suke yammaci da na kudanci suka taho suka marawa Sarkin yak'in baya suka rufuma rundunar Sarki GOMA inda suka sami nasara akansa tunda ya fahimci kutunguilar da suka shirya na su sami nasara akansa su maidashi bawa sai ya silale da kafatanin ilalansa wanda suka had'a shi da matansa biyu da 'yayansa biyar dukansu maza dama Aya ce d'iya mace tilo cikinsu. 'Yayan ba wanda ya yi aure sai mutum d'aya wanda matarsa ke goyon jariran 'yan biyu suma maza.

Cikin mabiyansa an sami wasu sun rufa masa baya sai ya sami nasarar tafiya da jama'a masu d'an yawa.

Dukkan kulawan Sarki Goma akan 'yan biyun nan ne har suka samu isowa HATSABIBIN TSIBIRIN da yaga dacewar ya zamo fadarsa amma akan hanya ya yo fashin zuk'a-zuk'an 'yan mata guda biyar wanda suma sukayo gudun hijira bisa jagorancin wani Sadaukin mayak'i inda ya amince zai tserar da su amma bisa sharad'in zasu zama matarsa a take kuwa suka amince shi ne ya biyo hanya da su bisa gudunmowar alk'aluman tsafi sai kuma ya yi rashin sa'a ya gamu da tawagar Sarkin GOMA ya ritsashi ya kasheshi ya kwashe 'yan matan inda ya mallakawa 'yayansa suka angwance a lokaci d'aya bayan kammaluwar gyaran Tsibirin wanda ya bashi suna da HATSABIBIN TSIBIBI domin bak'o bai tab'a shigowa TSIBIRIN ya fita ba fa ce wannan Dodon ya kamoshi ya bawa wad'an nan Kadoji sunyi watanda da Naman shi ko a maidashi bawa daga bisani ya zamo dan Tsibirin na har abada ya manta da Asalinsa balle burin komawa garesu. Wannan zalincin yasa mafarauta da sauran ma'abota shiga daji basa bin ko gefen TSIBIRIN duk kuwa sonsu da yankin saboda ababen tsoratarwa dake kewaye da Tsibirin yafi ƙarfin ji da ganinsu har gara kafin bayyanar Sarki Goma sukanyi shiri na musanman su hau, yanzu kam ba wanda ya san yarda TSIBIRIN ya koma balle ya bada labari dan duk wanda zai bada labarin an halakashi ko ya zama ganimar Tsibiri.

Mrsjmoon ce🥰

Ku daure ku buɗe Arewabooks👇

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕

*Shafin na Mum twins ce Kawalliyata Billy Galadanchi, Allah ya bar kaunar ta har abada mara algus, Amin ya rabbi.*

Page 03

Wad'annan manya dokoki sunyi matuƙar tasiri wurin d'aukaka darajar TSIBIRIN ta inda mutanen cikinta ke alfahari da kansu domin sukan sakko yin farauta inda suke razana makiyaya su d'auka wasu halittu ne na daban ko aljannu ne suka bayya garesu inda zasu gudu subar dukiyarsu sai su kame shanye tarw da tarkacensu ciki har da yaransu maza da mata wanda basa iya gudu ceton rai, su dawo kan TSIBIRIN su sadaukarwa Sarki shi kuma ya d'iba ya bar musu sauran su raba tsakaninsu domin lokacin basu da yawa sosai kome suka samo na wadatarsu. Yara da suke rabosu da iyayensu kuwa suna zuwa Sarki ke tsaface zukatansu su manta da danginsu su saje da jama'ar Tsibirin in suna da addini su koma marasa shi.

Shi yasa babban yare a Tsibirin Fulatanci ne sai yarensu na gado wato Dusanci sai ko tsillin yaren Hausa domin cikin mafarautan da tsau-tsayi ya kan ritsa da su zuwa farauta yankin an taɓa kamo Bahaushe inda ya zauna a fadar Sarkin zamanin tare da miƙami mai girma wanda yanzu a cikin tsatsonsa ne Sarkin yaƙi ya fito wato mahaifin Jarumi Buda.

Jama'ar Tsibiri mafi aka sarinsu suna da hasken fata mai daukan ido musanamam matansu shi yasa suke da kyau na ban mamaki ko da kuwa baƙin fata garesu to zaka gansu masu cika idanun mai kallonsu ne dan haka maza da matansu masu d'aukan hankali ne ainun sakamakon gauraya da jinin Fulanin usul da sukayi.

Suna da zumunci na ban mamaki tare da rufawa juna asiri, jimlatan sun kasance masu amfana da kayan juna ne sam basu san k'eta da mugunta ga junarsu ba shi yasa suke zaune tamkar Uwa ɗaya Uba ɗaya.

Tafiya ya yi nisa inda TSIBIRIN ya cika da 'ya'ya da jikoki inda duk a tsarin da Sarki GOMA ya ginasu suke wato tsafi da kwace wanda tuni ya mutu shekaru masu yawa da ya shudewa, sai babban d'ansa ya gajesa bayan ya rasu shima d'ansa ya gajeshi, haka dai suka cigaba da rayuwa bisa gadon-gado tare da cigaba da gina mulkin zaluncin na fashi da makami gami da sace 'yan matan Fulani su zamo uwayen ƴaƴansu sai dai ba wacce ake haikewa sai tare da son ranta domin a zamanin wani sarki mai suna Numan babban bafadensa ya taɓa haikewa ɗaya daga cikin wanda sukayo fashin dan nuna isarshi a fadar tunaninsa ya wuce ayi masa hukunci, aikam yana gamawa Dodo ya kwalla ihu kafin ace kwabo jama'a sun taru gaban fadar Sarki, ana haka cikin dakon jawabin da za a yi masu saiga Bafaden nan ya bayyana tsirara, batare da duba girmansa gami da mikaminsa ba aka datseshi tare da jefashi a kogin sihiri tun daga ranar jama'ar suka sake shiga taitayinsu suke gujewa aikata wannan zunubi.

A wannan karnin Sarki Barde ke mulkin TSIBIRIN wanda ya kasance jika ga sarki Gunu wanda ya sauka mulki batare da ya mutu ba dalilin mutuwar magajinsa wato mahaifin Barde dan haka ya nad'a jikinshi Barde dan shima ya kasance yana da halin zalinci amma yana kawo tsari mai b'ullewa ga masarautar tamkar yarda Sarki na farko ya ke yi dan ba'a tab'a sarki mai kawo mafita ga Tsibirin ba irin Sarki Goma sai kuwa yanzu da sarki Barde ke kamantawa amma duk da haka suna da bambanci mai tazara domin shi Sarki Barde wani lokacin yana kamanta adalci sab'anin Sarki Goma da zaluncin kawai ya sanyawa gaba tare da wad'anda suka biyo bayanshi ciki har Kaka Gunu.

A kawo sauyi ga Jama'ar Tsibiri Sarki Barde ya sanya mutanensa sun soma Noma da kiwo a gefen Tsibirin inda duk wani makiyaya da suka jiyo k'amshinsa zasu bi bayansa su yake shi su mamaye dajin baki ɗaya. Da yaga sun tara abin duniya sai ya hanasu fashi da makami sai bisa lalura ta rashin abinci sannan ya nad'a mutum uku da zasu rik'a kaikawo a tsakanin jam'ar TSIBIRIN.

Sai ya killace TSIBIRIN ta inda ba mai iya fita gefenta da zarrar sun cire amfanin gona face mutum uku sun amince masa, kome mutum ya keso a nan TSIBIRIN zai samesa domin ya bud'e musu kasuwa na cinikayyan kayan abinci da sutura dan yanzu suna saka kaya sab'anin a baya da suke saka ganye da fatu. Na mijin da ke da aure zai saka dogon wanda da rigar 'yar shara mara aure kuwa gajeren wando zai saka da rigar sak'i na Fulani, mata kuwa da mai aure da mara aure zani da riga na sak'i suke sakawa su nad'e kansu da bak'in sak'i sai dai 'yan matan sunfi saka godayen riguna na farin yadin karen miski da ratsin ja.

Su wad'annan mutum ukun da Sarki Barde (Mai Tsibiri) ya wakilta sun had'a da Sarkin Noma wanda alhakin kula da kayan amfanin gona ke hannunshi shi ne ke fitarwa da Sarki kasonshi kafin mamoni ya soma amfana da kwayar hatsin da ya noma haka shi ke hada-hadar sai da musu da kayan ya kawo musu kudinsu ba cuta ba cutarwa. Sai na biyu shi ne mai dawa wato sarkin mafarauta wanda shi ne ke kula da abu-buwan da ke faruwa a dajin da kewayen Tsibirin gudun samun tangarda mahara su kawo samame duk da Tsibirin na kewaye da alk'aluman tsafi. Sai mutum na ƙarshe shi ne Sarkin yak'i wanda shi ke sanya ido a kai da kawon kowa dake cikin Tsibirin da shirin ko ta kwana idan mai dawa ya yi nisan zango zuwa farauta.

Musanman Sarki Barde yasa aka farauto driver da motarsa, ya sami wata biyar yana ko yawa mutane uku nan mota bayan sun kware ya korashi daji inda Namun daji sukayi watanden namansa bayan ya turawa 'yan matan Tsibirin sun gama zuk'e masa ruwan jiki da jarabarsu daga nan labarinsa ya zamo tarihi. Sarkin ya sama musu motoci uku lafiyayyu inda suka soma shiga cikin gari suna mu'amala da su ta hanyar fitar da amfanin gonansu su siyar su siyo wanda basa shukawa tare da sutura irin tasu sai dai duk in zasu shiga gari sukanyi shiga irin na makiyayan usul wani zubin kuma suyi irin na kabilun da suke hurd'a da su shi yasa abokan huld'an kasuwancin nasu basu gano daga inda suke fitowa ba balle su zama abin tsoro.

Duk wannan lamari da ake ciki Tsibirin baida magaji domin matar Sarki Barde bata taɓa yin bari ba, ganin haka sai ya dukufa yin tsafi akan ya samu haihuwa inda kakanshi Gunu ke tausarshi da cewa zai haihu da zarar lokaci ya yi. Kwatsam bayan shudewar wasu shekaru matar sarki ta sami rabo inda ta haifi 'yan biyu dukansu mata masu kama d'aya tamkar an tsaga kara, ranar suna anyi bidiri na gaban kwatance daga bisani aka sanya musu suna Lina da Lima inda suka ci gaba da girma bisa kulawan mahaifansu da kakan mahaifinsu wato tsoho kaka Gunu.

Sai dai tun suna tsumman goyon suka taso da bambancin ra'ayi inda Lina mai tausayi ce Lima kuma muguwa, hakan yasa basa ga maciji da juna.

Lima ta soma cutar da 'yar uwanta Lina tun kafin su san kansu sai Mahaifiyarsu wanda suke kira da Mah ta maida kulawarta ga Lina shi kuma Abun ya maida nasa kulawan kan Lima inda Tsoho Guna ya mara mashi baya. Sadda suka soma tasawa sai Kaka Gunu ya killace Lima ya soma koya mata dabarun tsafi da yak'i ya yin da itama Lina ke amsar horon wurin d'an sarkin yak'i Buda a b'oye batare da sanin kowa ba wanda ya kamu da sonta batare da ta san yanayi ba, dalilin da ya k'udiri aniyar horar da ita kenan domin yana sane da wariyar da Kaka Gunu ke nunawa tsakaninta da yar uwanta sai dai abinda bai sani ba horarwan baiyiwa Lina amfanin komi saboda kafin ta dawo gida Kaka Gunu zai lalatashi idan ta dawo nanma mahaifiyarta kan cigaba da koya mata tsafi domin tasan ilimin sosai wanda shi ne ke amfanarta domin Kaka Gunu bai lalatashi bisa wani dalili nashi na daban.

Ganin sun soma taka makakin girma sai burin Sarki Barde ya koma kan tagwayen 'ya'yan dan yana aiyana wata rana d'aya daga cikinsu zata jagoranci jama'an Tsibirin domin su kad'ai ya mallaka saidai burinshi yafi karkata akan Lima saboda muguntarta da k'arfinta tamkar babban sadaukiya sabanin Lina da ke da sanyi tare da gudun zalinci dan lokacin suka shiga shekaru goma sha ɗaya a duniya amma a haka Lima ke iya dambe da manyan sadaukai kuma ta samu nasara akansu. Tunanin mai Tsibiri daya dana Kaka Gunu duk da a tarihin Tsibirin mace bata taɓa jagorantar su ba.

Lokacin da suka taka matakin cikakkun 'yan mata sai rashin jituwar su ya k'ara tsanani sakamakon ganowa da Lima ta yi Sadauki Buda na son Lina wanda ta ke ganin bata isa kaiwa matsayin ba alhalin gata wacce ta tara abin so fiye da ita kamar k'arfi da tarin ilimin tsafi, wannan dalili ya tunzurata ta ƙara k'aimi wurin murguna mata ya zamo bata jin dadin zaman Tsibirin kwata-kwata, sai ta soma keb'e kanta tana rayuwa ita d'aya inda Lima zata binciko wurin taje ta mallake a cewar ita ce ke da ikon mallakan wurin hutawa sama da Lina.

Tsananin Lima ya soma kai Lina bango gashi bata son suna fada da juna, sai kawai ta koma duk in ta fita rangadi sai ta ajiye kuyanginta a bayan gari ta zama tsun-tsuwa mafi gudu cikin tsin-tsaye ta nufi biranen da ke da nisa da su inda zatayi ta ganin ababen al'ajabi musanman bauta da taga jama'a na yi a killatattun d'akuna masu kyau abin da yafi bata mamaki shi ne ganin yarda suke gudu idan ana magana a abin fitar sauti (Kiran sallah kenan) sai ta lalace wurin kallonsu gami da sauraren muryan da ke fitowa (Karatun Qur'ani kenan) ta kan b'ata lokacin tana saurare tare da son shiga wurin amma sai ta riƙa jin hucin zafi na dawo da ita baya inda zatabar wurin a d'imauce amma idan ta nemi shiga dayan ginin da ake kida da rawa gami da wak'a sam bata jin hucin zafi sai tafi maida hankali a wurin inda zatayi ta binsu suna tikan rawa batare da ta bayyana masu fili ba balle su koreta har ta soma ƙaunar yaren da suke magana da shi ta soma fahimta kaɗan-kaɗan. Wani zubin kuma in ta shigo birnin sai ta tare a makarantun boko inda wannan ya bata damar jin yaren turanci managarci har take fahimtar abinda ake koyarwa a d'akin da ake yin rawa da wak'a.

Sosai ta sami ilimin boko batare da sanin kowa ba sai mahaifiyarta wacce bata boye mata duk abin da ta aikata, sannan tana halarta Masarautu kala-kala tana naɗo salon mulkinsu domin wata rana ta shimfida a Tsibirin su da take da burin mulkansa ko da hakan zaizamo ajalinta ne.

A kwana a tashi Lina na nad'o labarai na samun 'yanci sai watsam ta soma aiwatar da manufarta cikin dibara inda ta kawo sauyi a tafiyar mulkin Tsibiri inda ta soke tsarin hana jama'ar Tsibirin fita lamarin gabansu sai da izini wanda ba dan mahaifin nata ya so ba ya amince rok'onta sai dan manufar da ta gina maganar akai mai amfani ne na abar kowa na fita shan iska duk inda suka so da harkan cinikaiya da kansu saboda ta nan zasu kara wayewa na daga abin da basu sani ba sannan tanan za su iya ƙarowa Tsibirin sanin da bata da shi ta fannoni da dama. Ganin ta samu nasara a nan bayan wani lokaci ta sake wargaza wani tsarin inda nanma ta sauya musu shigar sutura ta kawo tsarin 'yan gidan sarauta dole su bambanta da jama'ar da basu da sarauta inda ta ce suna da damar saka suturun da suka so a duk sadda suka ga dama kuma mai tsada da burgewa irin wanda yayi daidai da ra'ayinsu musanman ga 'ya'ya mata ababen ado da kwalliya su kuma jama'ar gari ta ce suna da damar saka sutura masu rufe jiki duk kalan da suka so amma banda irin na gidan Sarauta. A nan gefen ne tasha wuyar janyo hankalinsa har ya amince da tsarin inda Lima ta yi ta fushi wai Lina na son juya kan mahaifinsu son da keyi mata ya dawo kanta sai da kyar ya iya shawo kanta ta janye ik'irarin sai ta yi yaƙi da Lina.

Jama'ar Tsibiri kam sun ji dad'in wannan sauyi dan a take suka soma bata girma sama da wanda suke bawa Lima dan killace su a wuri ɗaya yayi mugun takurasu basa da bakin magana ne kawai ya sa dole sukayi biyayya ga abin da iyaye da kakanninsu suka wanzu a cikin shi.

Mrsjmoon ce🥰

Ku daure ku buɗe Arewabooks👇

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon.

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕

Page 04.

Sai dai abin da basu sani ba Lina ta yi yaƙin k'wato masu 'yanci ne domin kanta saboda gudun kada mahaifinsu ya gano tanayin nisan zango zuwa wani yanki batare da saninsa ba haka tana da burin shiga ta alfarma kamar yarda take ganin a masarautun da take zagayawa da ke birane daban daban sannan tana da burin samo ilimin tsafin da zai bata kariya daga zalinci Lima tare da samun damar shiga fadar da jama'a ke turu-ruwan shiga musaman ranar juma'a suma taga wani kalan bauta sukeyi tare da iya yarensu mai ratsa zuciya. (Masallacin Juma'a da karatun Alqur'ani Lina take magana)

Burinta ya cika inda ta cigaba da fita yawo

Please Login or Register in order to submit comment