Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zauna ta dafe kanta cikin sake tsunduma nazarin kalaman Jabir inda take hango cikakken gazawarta wurin tarbiyyan yaranta.

"Ƴaƴan Fulani dai masu hangen nesa ne, komin hassadan mutum ya zauna da su sai sun shiga ranshi tare da ƙaruwa da su, Jabir nagode da tunatarwa amma duk da haka bashi ne zaisa na janye ga son Hud ya zama Sarkin birnin Mungaye ba, ina nan akan bakana sai na salwartan da Sadauki daga wannan nahiyar."

Tana ambatar haka ta mik'e da sauri ta shirya ta fice zuwa sashin Umma domin kamma aikin da suka soma na birne layun da Mai Martaba zai ambaci sunar Hud a matsayin magajinsa domin Mamma mutum biyu take aikin a kansu wato Sadauki da Sardauna, ta kora Sadauki ya b'ace a duniya shi kuma Sardauna ya nak'asa yarda mulki zaifi ƙarfin shi,a wannan gaɓar mai martaba zai ayyana Hud, duk ta manta idan ba Sadauki da Sardauna a kwai wasu zaratan samarin Junaid da Jabir.

***
Washe gari.

Neerah ce zaune gaban Mami Fulani, tambayar duniya tayi mata akan sanin gaskiyan ra'ayinta akan Sadauki sannan ta umurceta da kada ta b'oye mata komi dake ranta, amma taki yin motsin kirki sai shafar yatsun ƙafarta takeyi. Murmushi Mami tayi tare da umurtanta da ta tashi taje ta karya tunda tak'i yin magana.

"Ina Azumi."

Ta ambata a hankali kuma cike da shagwaba'a.

"Masha Allah, ai namanta yau Alhamis, to Allah ya karb'a ya bada lada."

"Amin."

Shiru ya sake ratsa wurin zuwa can Mami ta kalleta a natse ta gano da maganar da take son furtawa, kiran sunarta tayi "Muneerah."

"Na'am Mamina."

"Sanarmin da zancen dake ruhinki kada kiji komi, nayi miki alkawari kome ye shi ina tare da ke sannan ki haɗa da bani amsar tambayar da nayi miki, shin kina son Babana ko takuraki yayi?"

Tafi mintoci biyar bata ce komi ba har sai da Mami ta dafa kanta cikin cewa "Sarauta gadonsa kikayi ba haye ba d'iyata, idan baki zamo mai nazari kafin bada amsa ba tabbas baki cika d'iya ga Sarki Abdul Hakim ba."

Dagowa tayi tana murje ido cikin turo baki ta ce "Mami kiran sunar Abbanmu tsirara fa kikayi."

"To Abban su Doctor Neerah, shi kenan na lullub'e?"

Dariya ne ya kufce mata domin bata taɓa jin Mami ta kirata da sunar irin haka ba.

"Tubarkallah, masha Allah, Allah Alhamdulillah da ya azurtani da d'iya mai kyau koda kuwa kuka takeyi."

Kafad'ar Mami ta kife fuskanta tana cigaba da dariyan mara sauti.

"Tashi mugama magana domin yau yau ake da zama na musamman akan zaɓinku daga nan sai a tsaida lokacin biki."

"Mami nifa ba zan ƙaryata yaya Yarima ba kawai duk abinda ya sanar da ke hakan ne, dama shi ne abinda zan faɗa miki tun d'azun nake jin nauyi."

Tana gama ambata ta mik'e da sauri ta fice domin gujewa tambayoyin Mami wanda amsasu zasu bata kunya matuk'a. Bayanta Mami tabi da kallo baki buɗe sai kuma ta tsare gira tamkar an aiko mata da sakon mutuwa.

"Da sake bazan yarda da wannan gangancin ba na aurawa Babana jinin k'anwata ya ƙarasa kunyatani cikin dangi."

"Mamina kada kiyimin haka, tunda dai kinji gaskiya to ki kai maganar ga Abba tare da sanya mana albarka."

Tsirawa k'ofar shigowa falon tayi ido ba kiftawa har Sadauki ya iso gabanta ya zauna tare da riƙe ƙafarta muryansa cike da rauni ya ce "Natuba Mamina, bazan sake aikata zunubin da ya gabata ba, zan zauna da Muneerah har ƙarshen rayuwata domin ita ce sirrina, tasan waye Aliyu sama da ku mahaifana sannan bazan taɓa baki kunya ba nayi miki wannan alkawarin, dan Allah ki yarda da Babanki Mamina."

"Babana wannan daɗin bakin naka bai karɓu ba dan haka tashi ka bani wuri domin bazan taɓa amincewa da wannan auren ba dan kafi kowa sanin wacece Nana Safiyya gareni, ni ce na saki Nono ta kama to ba zan amince da wannan lamarin ba."

"Please Mamina am begin you, kada ki rabani da Muneerah domin ita ce zaɓin ruhina."

"Babana idan ka sake ambatar kalma ɗaya tak a wurin nan sai ranka yafi dare duhu, oya! Maza ka b'ace min da gani "

Maimakon ya tashi sai kawai ya kife fuskanshi a ƙafarta, tana jiyo saukan d'umin ruwa wanda hakan ya tabbatar mata da kuka ya keyi amma hakan baisa ta janye daga dokin nak'in data hau ba saima janye ƙafarta da tayi ta mik'e ta shige bedroom d'inta ta kulle k'ofa. Dafe goshinsa yayi cikin jin kansa na sarawa yanayin da baya so na son kawo mashi ziyara, a hankali ya mik'e ya shige dakin Lailah inda ya sami Neerah daren jiya, ya zauna a saman Cushing tare da d'an zamewa ya kwnta ya d'aga kansa sama ya tsirawa ceilling ido, abin mamaki sai ya ji barci na ziyartansa amma idonsa yaƙi kullewa. Fitinannen k'amshinta ya jiyo yasa ya sake ware idonu na kallon fuskanta da ya bayyana a saman fankan da ke juyawa, hannu ya daga ya nunata cikin cewa "Har a sashin mahaifiyata sai kinzo kin tozartani?"

D'age masa gira tayi cikin jifarsa da shu'umin murmushi sai kuma ta bayyana zaune gefenshi, ƙafa yasa ya hankad'ata sakamakon tuno makarkin da yayi jiya tamkar a irin haka abin ya soma kafin ta rikid'e masa zuwa sifar Neerah, ya haik'e mata ba d'igon imani.

K'irjinsa ne ya harba tuno baya, a mugun fusace ya mik'e ya nunata da yatsa cikin amo mai amsa kuwa ya ce "Kina taɓani na rantse sai na kasheki!"

"Ka taɓa ganin inda Aljani ya mutu?"

"Za a fara akanki, azzaliman banza kawai,mara addini!!."

Ya kai ƙarshen maganar cikin buɗe murya bai ko tunanin Mami zata iya jiyo shi.

"Kai ka koyamin zalincin ya kai Yarima Aliyu Sadauki takwarar mafarin Mungaye Malam Aliyu Malle kuma takwarar Baffan mahaifiyar shi Fulanin Sarki Abdul Hakim."

"Ya isheni haka nan ya ke banziya!."

"To nayi shiru amma in kamanta zauna in tuna maka zalincin da ka aikata wanda ya janyoni bibiyan farin cikinka."

Kafin yayi yunkurin magana ta turashi zaune ta hanyar hura masa iskan bakinta ya lumshe ido ya bude cikin jin mutuwar jiki, ta nuna bango da yatsa sai ga gidansa na dajin Tekun Kabobo ya bayyana, ya ware idonu ta gyaɗa masa kai cikin cewa "Ka tuna zalincin da kayi a wannan gidan?"

Bai amsaba illa kallon gidan dakeyi cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa.

"Nayi alkawarin sai ka ambatawa Masarauta aika-aikan da kayi da bakinka a gaban dubban Jama'a kuma a yau ɗin nan saboda aikina na daf da zuwa ƙarshe."

Lumshe ido yayi yarda lamarin ya kasance ya soma dawo masa a idanu tiryan-tiryan, kafin kwabo yaji tamkar gashi a bakin Tekun Kabobo da mafarin lamarin ya soma, wani iziyar ruwa ya zashi zuwa cikin Tekun duk yarda ya so kufcewa halaka ya kasa sai ya hango Neerah a tsakiyar Tekun na d'ago masa hannu ya zabura da ƙarfi, Mami ta zabga salati sai ya kalleta a razane, idanunsa sun sanja kala zuwa jajur, cigaba da karanto addu'a tayi tana tofa mashi ya ritse ido na jiyo amsa kuwwan ihunta, da hanzari ya toshe kunnuwanshi, Mami ta sake zabga salati, muryanta na rawa take cewa "Kada kayimin haka Babana indai akan aurenku da Muneerah ce kake son haukacewa walalhi na amince, Allah ya tsare afkuwan abinda nake tsoro, ya baku zaman lafiya da zuri'a masu albarka."

Komawa kwance yayi najiyo dariyarta a daf da kunninsa kana daga bisani tace "Na tayaka yaƙin samun cikar burinka na auren masoyiyarka saura samuwar nawa wanda ya ke nak'asu ne ga ci gabanka domin Birnin Mungaye baza su amshi azzalimi matsayin jagoransu ba, na tafi kada mamanka ta ƙarasa konani da gatan addinku wanda kake da sani akansa amma na haka su amfane ka."

Yanajin iskan tafiyarta ya juyo ya tsirawa Mami ido sai a lokacin yaga a she harda Abba, da Neerah a d'akin, bai lura ba sai yanzu. Runtse ido yayi tare da tura hannayensa a cikin sumarshi. Jan hannun Mami mai martaba yayi suka fice batare da Sadauki ya sani ba saboda ya amincewa kansa Sadauki na tare da shafan Junnu.

"Yaya Yarima."

Kollonta yayi ta sakar masa murmushi tare da matsowar ta zauna a hannun kujeran da ya ke kwance ta soma bashi labarin abinda ya faru cikin natsuwa.

"Ina fitowa daga falon Mami na hango zaka shigo sai na b'oye sai da ka shige sai na samu kaina da biyo bayanka, na jiyo duk yarda kukayi da Mami shi ne na biyo bayanka domin sake samun tabbacin kalaminka na cewa ni ɗin sirrinka ce sai na samu kana ta magana kai kaɗai, sam na kasa fahimtar abinda kake faɗa ga daishi da yaren da nasani kake maganar amma harshenta yana sark'ewa ta yarda maganar bai fitan da za'a fahimta, ganin kamar baka hayyacinka shi ne na kira Mami, tana zuwa ta soma tofa maka addu'a ganin abin na son fin ƙarfinta sai ta kira Abba inda yana shigowa ka dawo hayyacinka lamarin kamar shafan Aljannu."

'Innalillahi wa inna ilaihin raji'un.'

Ya ambata cikin rashi yana maijin harbawan halittarshi da ƙarfi wanda ya haddasa masa zabura tare da kai hannu gabanshi cikin dibara gudun kada Neerah ta gani saidai ita sam bata lura da sanjinsa ba, saima tambaya da ta jefo masa.

"Yaya Yarima wasu kalan mafarkai kakeyi? In da hali ka sanar da ni irin wanda kayi jiya tunda na zama sirrinka kuma zan cigaba da kasancewa sirrinka na har abada."

Kallonta yakeyi cikin jin wani kalan sha'awa na taso masa na daban da yarda ya saba shiga, sam bai fahimtar zantukan da takeyi.

Jin bai amsa ba sai ta kalleshi, mik'ewa tsaye tayi jikinta na rawa dan a take ta tuno mafarkinta na jiya mai wuyar sha'ani, ware idanu tayi a kansa tare da tsirawa inda hannayensa suke ido, ya cire hannun cikin dibara, suka tsirawa juna ido ba k'iftatawa, a take Neerah ta gano halin da yake ciki wanda a irinsa ta ganshi a barcinta na daren jiya, sai dai tuno abinda ya faru tsakaninsu yasa ta nemi barin wurin saidai ta makaro dan a zafafe ya damki dantsen hannunta ya jefata a k'irjinsa ya matse, yana sauke numfashi da sauri da sauri tare da jin harbawan halittarshi cikin salon da bai taɓa samun kansa ciki ba, sai ya sami kansa da ware ƙafa ya matse guk'unta gam.

"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, na mutu Mamina, dan Allah Yaya Yarima karufamin Asiri."

Abinda Neerah ta iya furtawa kenan cikin ƙaramar murya saboda tana gudan kada tayi ihu su Abba su dawo su gansu a haka Sadauki ya kunyata lamarin da zai iya kawo nak'asu ga samun damar mallakan junarsu a matsayin ma'aurata tare da hawa karagar mulkin Birnin Mungaye.

Jikinta ne ya soma rawa cikin jin shiga matakin da bata san ta inda ya afku ba wato feeling da take cikawa su Lailah bakin bata cikin mata masu motsawar sha'awa, duk in suka nutsa cikin hiransu na 'yamma, inda zasuyi ta tsokanar da cewa bata cika mace ba ne shi yasa.

Juyatan da Sadauki yayi zuwa ƙasan shi cikin fita hayyaci yasa ta dawo ɗan tunanin da ta afka, sai dai ta makaro wurin kwatar kanta domin ya saka mata ƙarfi yana kaimata summba a zafafe a duk inda bakinsa ya sauka.

*Alhamdulillah.*

This is the end of free pages.🤩

Affuwan idan na b'atawa masu jiran shi a kyauta, hakan ya faru ne saboda wahalar da rubutu ke da shi gami da kashe lokacin ayyuka.

Pay 300 only to 0468069082, Haruna Safiyya GTbank. Send the evidence via 08132166848.

*Yanzu labari ya soma.*

*Ga dai Sadauki da Dr. Neerah, shin ko ya zasu ƙare? Wani Zalinci Sadauki ya aikata da ya zamo kalubale a rayuwarshi? Wacce Aljana ce wannan? Shin burinta na wulakanta Sadauki a cikin fadar birnin Mungaye na samuwa kuwa? Waye Sarkin Mungaye cikin Sadauki, Hud, Sardauna da ɗan dogarai Salis? Burin Mamma da Umma na samuwa kuwa? Sannan ga Tsibiri can na shirin kamawa da wuta. Wa zai kawo masu ɗauki? Shin ta ina Gimbiya Lina zata soma? Burinta na hayewa karagar mulkin Hatsabibin Tsibiri tare da kawo canjin mulkin Aldalci na cika kuwa? Shin itama Lima na samun damar mulkan Tsibirin? Me ye sirrin da Lina take b'oyewa? Shin ta yaya Hadimi Tsidau ke kub'uta? Waye Sadauki Gauɗu da dalilin mallakawa Gimbiya Lina sirrukanshi na tsafi? Shin Ifritu Baushe na yin nasarar ɗauke Mah tare da mallakan Gimbiya Lina kuwa? Buda na samun cikar burinsa na auran Lina da hawa kan mulkin? Ya Abun zai ƙare? Shin na mallakan tulun ruwan albarka da Zoben sihiri kuwa?*

Waɗannan dama wasu bayanen duk suna tafe cikin cigaban labarin HATSABIBIN TSIBIBI( labari mai ɗauke da sashi biyu) A cikin farashi mai sauk'i #300 kacal. A turo ta asusun banki kamar haka 0468069082 Haruna Safiyya GTbank, sai a turo shaidan biya ta wannan layin wayar: 08132166848.

Thank you so much my fans. I said kada ku bani kunya dai.😊

Momyn Haske ne🥰

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment