Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tambayoyin inda zantukan Mamu Fulani suka dosa na abinda take ambata da ba a son ranta zai faru ba.

Ac Mami ta kashe tare da rage mata hasken wutan dakin ta fice, ajiyar zuciya ta sauke natsuwar ruhi na rab'arta saboda yarda kalaman ina sonki sosai Dr N, shin kina so na? Ke amsa kuwwan a cikin kunnuwarta, juyi tayi tare da furta "I love you too Yaya Yarima."

Tana rufe baki taji motsin tafiyar wani abu a jikinta daidai saitin zuciyarta ta lalibo da sauri sai ga ƙatuwar kunama jajur da ita, ta tsira mata ido sai kai da kawo takeyi tsakanin tafin hannunta zuwa tsin-tsiyar hannunta ba tare da tayi mata illar komi ba, murmushi ta yi tare da matseta da ƙarfi tana jin yarda bugun zuciyarta ya k'aru, ta lumshe ido tana mai furta "Where are you Yaya Yarima? Dan nasan kana kusa da ni tunda ga kayanka a hannuna."

"Yes I'm here my Doctor."

Da sauri ta kalli bakin k'ofan cikin hasken da bai wadaci d'akin ba, shi ne tsaye yana kallonta fuskansa ba d'igon annuri, murza idanu tayi dan tabbatarwa sai taga wayam ba kowa komawa kwance ta yi ta tsirawa kunaman nan ido da ta koma jikin bango tana ta shawagi sai sanja color takeyi from black to red, yellow, blue, brown and so on dan wani color d'in bata taɓa ganinsa ba tsawon rayuwarta. Murmushi kawai take binta da shi, har bata san sadda barci ya ɗauketa ba ta kife ruf da ciki barcin da su Mami ke yak'in ta daina yi saboda rashin alfanunsa ga Bil'adam.

***
'Na yarda da zancen Bokanki Mamma hak'ik'a ya sanar da ke gaskiya cewa ina da kishiya a kusa da ni, in ko haka ne wallahi sai dai kowa ya rasa Yaya Sadauki domin bazanyi kishi da ke Neerah ba kamar yarda nasan kema bazakiyi da ni ba saboda girman zumuntarmu ya wuce wasa, kai bama zai yiwu hakan ya kasance ba, tabbaas kai nawa ne Yarima Aliyu, ruwa da iska banga mai yimin shamaki da aurenka ba, Neerah wahalar banza kikeyi, ke da Yaya Sadauki sai zumunci na yan uwantaka da Allah ya haɗamu.'

Duk cikin zucci Zuhrah keyin zantukan idanunta na kan sashin Mami Fulani tana auna masa mugun kallo tamkar shi ne Dr. Neerah. Cin tayar mota da akayi yasa ta kalli wurin a hanzarce hango Ƴaƴanta Hud cikin maye yasa ta buɗe robar ruwar hannunta wanda ke da sanyi ta nufeshi a fusace ta watsa masa ya saki a jiyar zuciya yana kallonta idanu jajur sake juye masa ragowar ruwan tayi a fuska aikam ya rarumota ta kwasa da gudu ya rufa mata baya yana huci.

"Mamma kizo danki mara amfani zai illata miki ni."

Abinda take ambata kenan tana
maimaitawa sadda tayi nasarar shiga falonsu, Mamma ta fito zani na kufcewa dan tunda tajiyo kalaman Zuhrah ta san ita da Hud ne wanda tayi imani ya koma ruwane na shigowa Masarauta cikin maye lamarin da Zuhrah ke adawa shi kuma hakanne yasa tayi mugun rainashi duk da ba ita ce sak'onshi ba domin a kwai mutum biyu tsakaninsu kafin ita.

"Me yasa ne Hud? kamanta tijarar Abbanku Chiroma ko? Shin kana ganin wannan gaulancin zai kaika zuwa ga hawa karagar Sarautar Birnin Mungaye?"

Da sauri Zuhrah ta anshe da "Ina kuwa domin wallahi ko ni sai na yi sanadin rashin hawarsa domin mu ba 'yan maye ba ne balle ya hau ya maida giya ruwan fanfommu duk mu lalace, kanmu ya kwance kamar yarda nasa yake a kwance."

Tama rufe baki ta k'wallah ihu domin a fusace ya jefota da zobbesa mai kama da k'ashi, ya ko sameta a goshi a take jini ya wanke mata fuska, Mamma ta yi kanta tana rafka salati fadi take "Hud kiramin Dr Neerah ta bata taimakon gaggawa domin ban son Masarauta susan wannan abin kunyar da ka aikata."

"Sai dai ta mutu wallahi Mamma indai sai na kira an bata taimako ne."

Ya ambata cikin rabewar murya irin na 'yan maye.

Wani a shar Mamma ta mulmulo ta antaya masa ko ajikinsa sai ma ya kwashe da dariya ya tura kai d'akin Zuhrah ya faɗa saman Cushing yana sunbatun sai ya illata rayuwar Zuhrah tunda ta rainashi, daga haka barci yayi gaba da shi.

"Mamma jijiyar idanu zasu tsinke kiyi wani abu kada na rasa idanun gani, wayyo! Na shiga uku na lalace, walalhi ba zan yafewa ɗanki mara amfanin can ba."

A gigice Mamma ta kamota tare da tara d'ankwalinta a goshin tana zabga salati gami da toshe mata baki dan ta daina aibata ɗan uwanta tare da gudun kada wani ya jiyo.

"Mamma kaini Mungaye Clinic kada in rasa idanu cikar ado da k'walliyar duk kan mutane musanman mata."

Bata da zaɓi zai fito da ita zuwa Clinic duk da bata so hakan ba saboda bata son labari ya fito cewa Hud ne ya jima shalelenta ciwo domin a bayyane nakasu ne gareshi akan burinta na ganin ya haye karagar mulkin Mungaye.

***
Tsibiri.

Iskan bai tsaya a ɗauke masu gani ba har da halaka jama'a, a cikin abinda bai wuce mintoci biyar ba ya halaka mutane masu yawa. Tsibiri ya hautsine da iface-iface na neman dauki, cikin fushi Sarkin yaƙi wato mahaifin Buda ya aika sak'o cikin aikin alk'aliman sihiri zuwa ga Abun akan su dawo Tsibiri zai kama da wuta sannan ya soma ƙoƙarin tsaida guguwan cikin kwarewar tsafi sai dai lamarin ya sha ƙarfinsa, suka taru suka haɗa ƙarfi kamar yarda sukayima na farko nanma bata sanja zani ba sai kawai suka soma neman matseta tare da bawa jama'a taimakon wurin b'uya.

Rugugi ne ya doso Tsibirin abinda ya sanya iskan nan lafawa, tamkar k'iftawar ido iskan ta ɓace, zuwa can Lina ta bayyana fuska a daure, kafin su ankara ta soma huro sanyi wanda ke fitowa daga bakinta na shiga jikkunar Jama'a inda ke warkar masu da raunin da suka ji tare da tashin wanda suka jikkata, ta ɗauki tsawon mintoci goma tana huro iskan kafin ta dakata tana kallon al'umman da duk suka samu natsuwa suka sakata a tsakiya suna yi mata kirari da Gimbiyarsu mai tausayi.

"Kuyi hak'uri da matsalar da 'yar uwana ta janyo muku, yanzu ku tafi ku kauda wanda suka mutu tare da cigaba da harkokinku zanyi bakin iyawata wurin kare lafiyarku domin wannan shi ne burina kuyi rayuwar 'yanci wata rana."

"Mungode shugaban gobe, Sarautar Tsibiri naki ne Gimbiya Lina."

Suka ambata a tare cikin daga murya.

Jinjina kai tayi ciki da alfahari da su. Suna watsewa Abun ya bayya tare da Buda, Lina na jin alamun takunsu ta ɓace ta bayyana cikin Bukkan Kaka Gunu inda ta sami Lima sunkuye kan Mah tana aikin ceto ranta.

"Sakacinki ya janyo Mah zata mutu, wannan bak'ar ranar nake jiye mana har na umurceki da ki kula da ita amma saboda son zuciya irin naki kin kasa zama da ita kin taho neman cikar burinki, to ki zauna a nan tare da ita domin fitowarki kiran ajalinki ne domin Jama'an Tsibiri sun fusata da kashe masu dangi da kikayi sanadi sannan Abun yana farautanki kamar yarda yake faraunata da Mah."

"Me kike nufi da Abun na farautanmu? Alhalin mu ne kaɗai sanyin idanunsa."

"Lima yanzu Abun ya sanja dan shi ne ke wasa da rayuwar Mah domin ya samu hankalina ya dawo kanta inda zai hilace ni ya mallaki Zoben da ke hannuna wand zai bashi damar samun ƙarfin tsafin da ya zarce na kowa dake zamanin nan haka ya fiki burin son mallakan Ruwan Albarkan Kaka Gunu domin shima na ɗauke da sirrika masu girma akan tsafi da cikar mulki, ki sani a yanzu mu ne damuwarshi akan haka ya kudiri halakamu baki ɗaya indai zamu kawo masa tangarda a samun tsawon rayuwa akan mulki."

"Ta ya zan yarda da gaskiya kike sanarmin ba yaudarar da kika saba yimin ba ne? "

"Ifritu Mutuwa zai gasgatani."

"Tabbas zantukan yar uwanki Lina ba ƙarya duk da itama tana son shan ruwan albarkan domin ta sake finki komi dan hawa karagar mulki, ko ba haka ne manufarki ba ya ke Gimbiya Lina?"

"Tabbaas haka ne kuma har a yanzu ina cikin muradin rigaki mallakan ruwan albarkan sai dai ba yanzu shi ne a gabana ba domin haka kaima Mutuwa dole ka dakata da taimakonta na mallakan Ruwan har sai na kammala da abinda ke gaba in yaso sai kayi mana k'uri'a duk wanda ya ci shine mai mallakin gadon Kaka Gunu."

"Baki isa ba Lina, ni ce ke da gadon Ruwan Albarkan Kaka Gunu dan haka ki fitar da ranki akansa."

Murmusawa Lina ta yi batare da ta furta kalma ba ta isa gaban Mah da ke shimfida tamkar gawa ta sunkuya ta shafi fuskanta wani haske ya sauka a fuskan zuwa ilahirin jikinta aikam sai ta soma tari tana kiran sunar Abun da ya zo ya taimaketa.

"Mah kina tare da 'yan biyunki kuma bisa kulawarsu kika tsira daga baƙin iskan da Lima ta yi jagoran shigowarsa cikin al'umma, yanzu zan barki a wannan Bukar ta Kaka Gunu Lima zata kula da ke zuwa sadda zan dawo na maidaki inda duk ƙarfin tsafin matsafi yayi kaɗan ya iya zuwa wurin."

"Ki dawo lafiya Ruhin Sarki Goma ya baki kariya."

Motsa kai tayi tare da mik'e ta kalli Lima da ta tsare giran sama da ƙasa ta hurama fuskanta iska kan dole ta murmusa saboda tunowa da lokacin baya da take azabtar da Lina da iskan bakinta.

"Yawwa kin tuna muguntarki na baya ko? To ki natsu kiji me zan sanar da ke, ki zauna a nan kamar yarda na sanar da ke a farko, ki kulamin da Mah, Ifritu Mutuwa zai kula da ku sannan zan batar da Bukkan Kaka Gunu a idanun Abun wanda ke nufin isowa bada jimawa ba."

Lima zatayi magana Lina ta daga mata hannu tare da cewa "Kada kiyi yunkurin barin Bukkan nan dan zuwa watsewarki domin yin hakan wasa da rayuwarki ne domin kina fita zaki tsinci kanki a akurkin sihiri ko na Abun ko na Ifritu Baushe kuma ki sani bana da lokacin taimakonki saboda lamarin Mah d'ita ya fiyemin komi, in kinji gargad'i ruwanki, ni zan wuce ba zan jima ba zan dawo dan bana son na wuce kwanaki biyu rak ban kammala abinda naje yi ba."

Kafin Lima ta furta kalma Lina ta zama farin hayaki ta b'ace kallonta ta sauke kan Ifritu Mutuwa sai ya jijjiga kai tare da bude tafin hannunsa saiga wurin ya sanja, ya dawo dauke da kilisai masu laushi da makeken gadon alfarma, jinjina tayi masa ya gyaɗa kai tare da b'acewa, ta doshi gadon ta hau ta kwanta ba jimawa barci ya dauketa cike da burin sai ta fita wurin nan taga abinda zai faru. Mah itama gadon ta hau cike da tarin damuwa.

Lina na fitowa ta jiyo takun Dokin Buda sai ta zama balbela ta haye saman bishiya suna wucewa ta sakko ta watsa haske a baki ɗaya Bukkan ta lula sararin samaniya.

***
Abun tsaye a turakansa yana kai da kawo cikin tarin damuwa zuwa can ya ja iska ya fesar tare da zama akan k'ok'on kan Giwa ya na cije lebe, ya sharce Gumin da ya feso masa a goshi tare da mikewa a fusace ya kaiwa bango duka cikin ambatar "Ƙarya ne, saina Mallaki Zoben hannunki Lina sannan yar uwanki zata kasheki a gaban mahaifiyarki, a yanzu bana da abokiyar gaba sama da ke, zan nuna miki ta yaro kyau take amma bata k'arko, ki sani ba zan barki ki Mulke ni ba alhali ina rayuwa, tabbaas a yau na musanta kalman cewa bazanyi fito na fito da ke ba haka na gasgata kalamin Kaka Gunu da ya ce samuwarki cikinmu masifa ce domin zaki karya k'adarinmu ki sanja tarihinmu ki watsa mana Martaban Tsibiri hak'ik'a dana sani na bashi dama a can baya ya sanya kinbi rariya ya zamo Lima kawai zata zo duniyarmu."

Momyn Haske ne 🥰

*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabibin Tsibiri
By Mrsjmoon

Adabi Writer's Association.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕

15

Ya kai ƙarshen zance cikin ɓacin rai, yana jin tamkar ya dawo da baya ya goge samuwar Lina a cikin zuri'arshi.

"Da girman mulkinka ya mai Tsibiri, ya kamata ka fito dan jajantawa Jama'a masifar da ta afku wanda Gimbiya Lima ta janyo faruwarshi."

Sarkin yaƙi ya ambata daga bakin kofa kansa sunkuye.

Cikin ɓacin rai ya nuna Sarkin yaƙi bakinsa na fitar da tiririn masifa ya ce "Yau she mulkin Tsibiri ya kai ga lalacewar da Sarki mai ikon juya kowa da ke Tsibirin nan zai fito bawa Talakawa hak'uri abisa afkuwan lamarin da ya zamo cigaban Mulkinsa ne, to ka tuna idan ka manta ne Tsibirin nan bai ginu bisa Tausayi ba haka ba zai taɓa haɗa hanya da shi ba, ka ƙara sani, nai alfahari da afkuwan masifar nan domin samun cikar burina na mallakan ababen da ke hannun 'ya'yana sai da zubda jini k irin wannan, lallai aikikinki na kyau Gimbiya Lima, a kullum ina alfahari da zamowarki gudan Jinina tabbaas ke ce magajiyar Tsibiri na sake gas-gata kalaman Kaka Gunu na cewa nasaranmu naga hawa karagar mulkinki ne duk da ina da wani buri akanki amma ba zan k'i yaba miki."

"Ya shugabana ka natsu mu fuskancin masifar da wannan zubda jinin zai haifar domin Dodo yayi fushi ya bar Tsibirin domin Guguwan ta rainata masa mata yanzu haka ya killace kansa a Kogo yana shirin yak'ar Lima shin idan baka fito ka jajantawa Jama'a ba me kake tunanin yi wanda zai sakko da Dodo akan dokin nakin na ya hau?"

"Sarkin yaƙi ka rufemin baki tun fushina bai sauka kanka ba sannan Dodo zai dawo bakin aikinsa kuma fushin-shi na rashin samun damar san Jinin jama'ar da baiyi ba ne, ba wai na nak'asar matarsa ba, shin ko ka manta bata da lafiya a cikin ko wani lokaci zata iya samun rauni, tunda ta saci jiki taje ta sha Jinin wani dan Fulani shi kuma ya soma bin hakkin jinin Ɗansa lamarin da yaso shafar ƙarfin ikon Tsibiri, shin ko mutuwa tayi ai bamu da asara."

"Haka ne ya mai Tsibiri, tabbas na tuna da wannan masifar da muka kasa samun maganinsa sai da k'yar."

"To Dodo fushin karya ya keyi sai dai bazank'i ta bakinka ba zamu ɗauki matakin kare kai kada ya kawo mana matsala saboda ya soma nuna rashin amana wanda hakan zai haifar masa da rasa rayuwarshi ba damuwata ba ne."

"Me zamuyi masa?"

"Cin amanar tun kafin ya samu nasarar cin tamu, wato samo hanyar halakasu cikin dibara."

"Ya mai Tsibiri Dodo ya wuce da saninmu domin ya rayu tun farkon Sarkin da ya raya wannan Tsibirin, yana da nindarai kala kala sama da dubbunnai dan haka shawara mafi samun mafita shi ne anjima da dare zanzo mu tafi wurinsa mu rarrasheshi ya dawo mu cigaba da zaman amana amma ka janye batun halakashi saboda gudun matsala."

Jim Abun yayi daga bisani ya gyada kai alamun aminta da zancen, Sarkin yaƙi za ku saka magana Abun ya d'aga mashi hannu tare da nuna kofar fita, ya ko juya da hanzari ya fice yana mai cike da farin cikin hayewa matakin farko daga cikar burinsa.

Abun d'akin bincikensa ya shige yana mai jin rashin yarda da zantukan Sarkin yaƙi na zuwa muhallin Dodo sai dai burin son nemo hanyar da zai ladaftar da Lina har ya mallaki Zoben hannunta ya shafe binciko abinda Sarkin yaƙin ke shiryawa, sai ma watsar da lamarin da yayi saboda zuciyarsa na bashi tabbacin aminci dake tsakaninsu da juna.

A gafen Sarki yaƙi kuwa gidansa ya nufa inda ya sami ɗansa Jarumi Buda zaine na dakon isowarshi. Yana isa ya rungume Buda yana kyal-kyalan dariya sai da yayi mai isarshi sannan ya tsagaita ya doki kafadan ɗan nasa yana mai koro masa yarda sukayi da Abun, yana dasa aya Buda ya amshe da cewa" Ya Baba ina guje mana afkawa tarkon Lina dan zuwa yanzu na soma tsorata da lamarinta kada garin halaka mahaifinta mu ɗin mu halaka a banza saboda bata bari kayi nasarar halaka mahaifinta ba, ni dai da zakaji shawarata da mun hak'ura da son mulkin nan mu kare namu da muke da shi na Sarkin mayak'a."

Yana rufe baki wani taurari suka gifta a maganansa sakamakon marin da Sarkin yaƙi ya zabga mashi. A gigice ya durk'ushe gami da kwalla ihu wanda yayi amsa kuwwa a Tsibirin lamarin da ya sake gigita Al'umma suka soma fadawa mahallinsu suna kare kai ta hanyar tsaface kansu da 'ya'yansu domin tunaninsu wata masifar ce ta dawo. Ihun Buda ya sauka a kunnin Abun dake tsaka da bincike, tsak ya tsaya yana nazarin abinda ke shirin faruwa sai dai jin takun isowar Lina Tsibirin yasa shi barin komi ya soma shirin tunkararta tun kafin ta hayo, burinsa ya halakata kowa ya huta da ganinta.

Sarki yaƙi yaji rashin jin daɗin abinda ya aikatawa ɗan nasa sai yayi ƙasa da murya yana mai cewa "Kayi hak'uri ya kai ɗana amma ka sani burin mahaifina kenan mu gaji mulkin Tsibiri hakan bai samu ba saboda Kaka Gunu ya katange hanyar shi yasa na rayuwa da burin kawo karshen mai Tsibiri ko da hakan na nufin rasa raina zanyi dan haka kada ka sake ambatamin na ja da baya tunda kai baka son hawa mulki to ni zan hau duk da na soma tsufa."

"Zan hau Babana domin nima ina da burin mulkan jama'armu."

"Da kyau ɗana, ina alfahari da kai."

Kauda kai Buda ya yi yana mai buɗe k'ofofin hancinsa sai kuma ya mik'e a hanyarca, Sarkin yaƙi ya rik'oshi cikin alamun tambayar inda zaije.

"Babana Gimbiya Lina na daf da shigowa Tsibiri kuma ina jiyo alamun zata gamu da matsala dan haka zan kai mata ɗauki."

"Ta mutu mana ina ruwanmu."

"Ina sonta Babana, ka amincemin na kai mata ɗauki saboda sai da ƙarfinta zan samu damar hawa karagar mulkin Tsibiri."

"Kana hauka ne Buda? Lina tafi kowa son mulkan Tsibiri dan haka zan amince maka kaje gareta bisa aniyar kasheta ka riga mai Tsibiri mallakan Zoben da naji yana magana akai wanda ke hannunta."

"In haka ne Baba kaga kenan taimakonta zansoma akan duk abinda ta sanya gaba idan ta aminta da ni cewa masoyinta na gaskiya ne sai na yaudareta na amshe Zoben daga nan sai mu fito mata da manufarmu na yak'arta mu kaudata cikin sauk'i."

"Da kyau fasihin ɗana Buda, tafi gareta da albarka Takobin yaƙina, kai ne ke da nasara kan Gimbiya Lina."

"Godiya nake Babana."

Daga haka Buda ya fice ya doshi inda yake jiyo K'amshin Lina wanda ya kaishi ga fita yankin Tsibirin baki ɗaya. Shima Abun ya nausa wajen Tsibirin inda ke jiyo takon Lina har lokacin kuma ya kasa cimma ta sai ya ƙara k'aimi domin riskanta akan lokaci.

Sai dai abinda ba su sani ba shi ne duk kansu bayan Lima suka biyo wacce ta fice ta bar Mah na barci, lokacin da zata fita Ifritu Mutuwa ya so hanata amma tuno zaman cika umurninta yakeyi sai ya kyaleta ta fice cike da muradin son ganin abinda zai faru akan fitar nata, mutuwa ce ko rayuwa, nasara ce ko rashin nasara, ita dai burinta yin ido biyu da kalaman Lina domin ji take idan bata fito wajen Tsibiri ba to Lina ta gama samun nasara akanta na zamowa shugabanta tunda gashi nan ta bata umurni kuma ta bi.

Abun, Buda tare da Lima sunata yin nisa da Tsibiri a bisa hanya ɗaya batare da sun gano hakan ba domin Ifritu Baushe ne ya shiryo musu sihirin ficewa daga Tsibirin ta hanyar kusanto masu da takun Lima gami da k'amshinta da ya sauya da irin na Lina sak, saboda Hadimi Tsidau ya sanar masa indai suna cikin Tsibirin to ba zaiyi nasarar shigowa ya ɗauke Mah ba wacce ke son yin garkuwa da ita domin Lina tazo yankinsa da kanta inda zai mallaketa tare da Zoben sihirin hannunta daga bisa ya sadaukarwa da Dodonsa jinin Mah a gaban idanunta, kana yayi mata ciki ta haifa masa d'iyar da zai sha jininta duk akan idonta ya tabbatar da ganan labarinta ya zo ƙarshe dan ko bai halakata da hannunsa ba ya san bak'in ciki zaisa ta had'iye ranta.

Tunda Tsidau ya farka da barcin da ya kwashe shi sai ifrutu Baushe ya adana shi yana gana masa azaba kala daban daban domin ya fahimci makirci ke son shirya masa ya gudu dan ba zai taɓa kawo mashi Lina Fadar sa ba, yanzu haka yana can kurkukun tsafinsa da ke k'ark'ashin ƙasa cikin tsaron wasu bak'ak'en rindunar Aljannu suna aikin azabtar da shi, wuya yasa shi sanar da Baushe hanyar da zaibi domin samun nasarar shiga cikin Tsibirin har ya samu cikar burinaa wato sai ya kora su Abun sunyi nesa da Tsibiri domin yawan yin nisansu da Tsibiri shi kuma yawan kusanci ga nasararshi na shiga cikin Tsibiri. Yanzu haka Ifritun Baushe ya sami kusanci da Hatsabibin Tsiri saura samun nasarar shiga cikinsa tunda ga su Lima can na cigaba da lulawa cikin duniya ba tare da sun gano sihiri ke d'awainiya da su ba.

***
Masarautar Mungaye.

Cikin ikon Allah su Zuhrah har suka isa Clinic ba wanda ya gansu sai hadimai dake ta mik'o masu gaisuwa. An wanke mata ciwon inda anan aka gano ƙarami ne tsabar rakine ke damunta ta cika masu kunnuwa da ihu, a hanyarsu na dawo ne suka haɗu da Jabir inda ya gaisar da Mamma cikin girmamawa ta amsa tare da yin gaba ta barshi da Zuhrah, shi kuwa ya tsareta da tambayoyi akan sanadin raunin fuskanta batare da jin ko ɗarba ta koro masa bayanin abinda ya faru sai dai ganin ɓacin ran da ya nuna har saida tayi da ta sanin faɗan domin yarda ya rufeta da masifa sai da tayi zaton dukanta zaiyi, ta ja da baya ya fizgo hannunta suka isa sashin Mamma ya turata tare da rufa mata baya. Mamma dake zaune riƙe da robar ruwa tana sha ta mik'e a firgice tana tambayar abinda ke faruwa.

"Mamma ki gyarawa Zuhrah tarbiyya saboda yaya Hud ba sa'arta ba ne, shin taya za'a ce kina kallo ta gama rainashi? A gaskiya da sake, in sha Allah gobe zan sanar da Mai Martaba domin a dauki mataki dan ko me yakeyi ya fi gaban raini a wurin k'aninsa sannan rayuwar dake ciki ƙaddara ce wata rana zai zamo labari dan haka dole Zuhrah ta girmama shi a matsayinsa na babban yaya a d'akinsu."

Ya sauke dubansa kan Zuhrah dake risgan kukan baƙin cikin anayi mata faɗa alhalin ita aka zalunta. Ya nunata da yatsa cikin kaushin murya wanda ya koma irin na Sadauki sak ya ce "Wannan shi ne rana ta ƙarshe da zan ji kin sake aibata yayanki mai ɗauke da matakin uba, idan kuma kince wasa nakeyi to ga fili nan ga mai doki, kin sanni dai sarai magajin Abba Chiroma ne, so be carefull kuma ki hanzarta bashi hak'uri, zan tambayeshi idan naji saɓanin haka na lahira sai ya fiki jin daɗi."

Sai ya russuna gaban Mamma yayi mata sai da safe ta amsa jiki a mace, saida ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya tana ƙara tsirawa hanyar da ya bi da idanu saboda zantukansa sun nusar da ita wani kuskure da take aikatawa na sangarta Zuhrah ya zamo kaf yayunta bata ganin girmansu saɓanin sauran yaran dake kan girmama yayunsu, ta dubi Zuhrah kafin ta furta kalma ta buga ƙafa tare da fashewa kuka mai sauti, Mamma ta nufota ta zille ta fice da gudu tana gunjin kuka, komawa Mamma tayi

Please Login or Register in order to submit comment