Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba"

Dafe ƙirji Abiatu tayi tace muje mu faɗawa Mama asan abunyi.


Ko da suka faɗawa Mama cewa tayi.
"Naila ce fa ko kin manta halinta ne Hafiza"

Cikin kuka Hafiza ta hau girgiza kai.
"Aa Mama wallahi Naila ta canza,Duk gidansu kawayenta naje amma bata nan wasu ma kam wai sun kai sati basu ganta ba, Mama Naila ba zataje wani waje ba, bayan tasan yau Yaya zai dawo" shuru Mama tayi tana nazarin maganar Hafiza kafin taji ƙirjinta ya bada dam!dam!dam!.

Ai nan Mama ta dauki hijab suka fita neman Naila har kasuwa amma basu ganta ba, har akayi sallar la'asar amma ba Naila, nan su Afnan dasu Umma da Inna suka zo domin su ji ko Naila ta dawo amma bata dawo ba,kafin wannan lokacin Mama ta fara fita hayyacinta, ta kira Ummu ta ce tazo yanzu, nan aka sake bazama neman Naila amma shuru har da yan gidan su Abi'atu.


Ubaidullah bai shigo bauchi ba, sai karfe shidda saura,a lokacin su na tsaye jingum-jingum Ummi mahaifiyar Abi'atu tana tambayarsa shin yaga lokacin da Naila ta fita, mai gami ya ce shi bai gani ba, zata sake yi masa tambaya sukaji ihun Safwan a wajen gate, da gudu suka fito har su na tutture juna, me zasu gani.?


Wata motace baƙaƙirim ta juya da mugun gudu tabar layin motar tana shan kwana ta Ubaidullah ta yanko kwana.

A kasa kuwa Naila ce kwance jikinta ya baci da jini ko motsi batayi wani razanarniyar ƙara Hafiza ta sake, yayinda Mama tayi baya-baya tangal-tangal zata fadi ko ka ba aduba ba Naila kam fyaɗe aka yi mata, da sauri itama Anty Ummu ta saki Ihu nan unguwa ta rikice, Su Umma(mahaifiyar Zaidu) da Inna sukayi kan Naila wacce take yashe akasa wanwar.

Hannunta Inna ta kama ta ɗaga ta saki hannun ya koma nan take Inna ta fashe da kuka tana cewa.
"INNALILLAHI WAINNA ILAYHIRRAJIUN! ai babu ita ta rasu"

Jin haka ya sanya Hafiza ihun da sai da Ubaidullah yaji, shi da bai kai ga ƙarasowa gate din ba,dan shi hankalinsa yana can akan abun da ya barota a barrack ashe zaizo ya ci karo da wanda ya fita ɗimauta, da sauri ya ɗago kai yana kallo jama'a akan layin nasu, bai karaso ba ya samu gefe yayi parking, dan babu inda zai wuce da mota saboda mutane, kuma ko ba a fada masa ba ihun kanwarsa yaji Hafiza.


Cikin hanzari da tashin hankali ya parka motar ya fito.

Hafiza kuwa ihun da ta sake ta zube kasa sumammiya, Mama zubewa ƙasa tayi sharab dan ji take komai na jikinta ya daina aiki.

Abi'atu itama kan gawar Naila tayi tana ihu tana kuka yayinda Anty Ummu ta rumgume Naila gam a kirjinta tana cewa ki tashi kanwata.


Faduwan gaban Ubaidullah ne ya tsananta jin muryoyin yan uwansa gashi kuma jama'ar da suke tsaye a kofar gidan su ne, haka ya dinga kotsa kai har ya samu ya shige, turus ya tsaya yana kallon Mama tana zaune sharab jingine da gate ga Hafiza sume a ƙasa ga Naila rungume a hannun Anty Ummu da wata yarinyar da bai san taba (ABI'ATU) su na Kuka.


ji yake kafarsa da gangar jikinsa su na neman gaza ɗaukarsa, murje idonsa yayi ya bude sannan ya wanka wa kansa mari har sau uku amma har yanzu abu ɗaya yake gani a gabansa, durƙusawa yayi, da rarrafe yazo gaban Ummu yasa Hannu yana so ya karbi Naila.


Sai a lokacin Anty Ummu ta ɗago jajayen idanunta ta kallesa ta kuma fashewa da kuka, a hankali Ubaidullah ya jawo Naila jikinsa yana girgiza ta yaga dilim, ya sa hannu ya bude idonsa ya ga duk sun kafe, dubansa ya kai kasar farin siket din less din dake jikin, wanda yasha yaga ta gefe da gefe ga jini kamar an yanka zakara,wani razanarniya kara Ubaidullahi ya saki tare da furta.

"INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN!!!!!! Noooooo! Innalillahi wainna Ilayhirrajiun!!! Ya Allah karka ɗoramin abun da bazan iya ɗauka ba" ya fashe da kukan rashin hankalin da ba asa masa rana.

"Su wayeeeeeeee!!!!! Su wayeeee!!!! Suka aikata min wannan. Ɗanyen aiki?"

Ya sake ɗago Naila yana jijjigata.
"Kanwata! Kanwata !kanwata! Ki..kki..ki tashi kinji gani nazo!.. Tashi ki faɗamin su waye suka aikata maki hakan kinji Nailata ki tashi..!"

Anty Ummu ta rungumesa tana kuka, jama'a da yawa a wajan kuka suke yi, da rarrafe Ubaidullah ya rarrafa da Naila a ƙirjinsa yaje gaban Mama wanda ke zaune kamar babu Ita.

"Mama dan Allah ki ce ta tashi Mama wai me ke faruwa ne!? Su waye suka aikata?" MAMA kallon Naila tayi babu abun da ya faɗo mata rai sai dazu da zata fita, ta juya ta fashe da dariya ta ce.
"Mama ina sonki ki yafe min" sai kuma lokacin da take mata fada ta ke cewa.
"In sha Allahu ni zan rigaki Mutuwa Mama"

Kuka bai ban tausayi da tsuma zuciya gami da tashar da hankali Mama ta sa ta rungume gawar Naila.





➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰



💲To🅿️

*STOP*


_A YAU NA DAKATAR DA RUBUTA LITTAFIN COLONEL UBAIDULLAH SABODA WASU DALILAI NA MASU KARFI._

NA FARKO.

_KAFIN NA FARA RUBUTA BUK DIN NAN SAI DA NA FUSKANCI KALU BALE MAI TARIN YAWA, WANDA NAYI HAKURI NA SHANYE NA CI GABA DA RUBUTAWA, A INA RUBUTUN MA ZUCIYATA BA ADAINA BATA MIN ITA BA_


_BAN CIKA SON INA BABATU AKAN MAGANA DAYA BA , GASKIA DAN NIMA INA DA ABUNYI_


NA BIYU.

_YANDA NASHA KALUBALE WAJAN RUBUTA LITTAFIN NAN KAMATA YAYI ACE KU FANS DINA KU KARAMIN KARFIN GUIWA HAR MUJE KARSHR KAMAR YANDA KUKA FARA A FARKO AMMA SAI KUKA SA JIKINA YAYI SANYI, A HAKAN BAWAI NA GAMA DA KALUBALEN DANA FUSKANTA BANE_


_KARFIN GUIWAR KUWA TA HANYAR YIMIN DOGON SHARHI NE A LITTAFIN, SANNAN KU DINGA TATTAUNA ABUN DA KUKA FAHIMTA A LITTAFIN DA ABUNDA KUKA KARO DA WANDA YA BAKU HAUSHI DA WANDA YA BAKU DARIYA, DOMIN NA GANE SAKON DA NAKE SON ISARWA YANA ISA YADDA YA KAMATA, AMMA BUN TAKAICI WAI NA TURO LITTAFI WASU MA KAM SAI DAI SU KARANTA SUYI SHURU ABUN HAUSHI KUMA BANYI TYPING BA A ISHENI DA WAI CI GABA, TO YAYA ZAN CI GABA KUWA? BAYAN BAKU BANI GOYON BAYA 100%BA, ZAN ZAUNA NA KASHE AIKIN GIDANA DA KULA DA YARANA, NA ZAUNA NA ZUBA MUKU TYPING KUSAN 4TO5 READMORE AMMA KU 1READMORE JUST FOR DOGON SHARHIN DA ZAI FARANTA MIN YA GAGAREKU._


_KWANAKI DA NAYI MAGANA, WATA MARAR KUNYA TA BINI PC TANA GAYA MIN CANZAN BANZA, NAN MA KYALETA KAWAI NAYI WLH DAN BANA SON DOGON TURANCI_


*_DAN HAKA BAZAN CI GABA DA RUBUTA LITTAFIN NAN BA KO DA KUWA, ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH NE_*



_INA GODIYA GA DUK MASOYANA WA INDA NA SANI DA WAINDA BAN SANI BA,INA MIKO MUKU GAISUWA TARE DA FATAN ALKAIRI_

ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MUKU A DUK INDA KUKE A DUK GARIN DA KUKE INA ALFAHARI DAKU.


SANNAN INA NEMAN AFUWAR WA INDA NA BATA MUSU TARE DA NEMAN GAFARA KU YAFEMIN NIMA NA YAFEWA KOWA,ALLAH KUMA YA YAFE MANA GABAKI ƊAYAN MU.

DAGA KARSHE INA ROKON MANA GAFARAR UBANGIJI,ALLAH YA YAFE MANA ZUNUBANMU YA GAFARTA MANA, YA YAYE MANA WANNAN ANNO BA TA CUTAR CORONAVIRUS(COVID19)ALLAH YASA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA AMEEN.



SADUWAR ALƘAIRI DAGA.


ZAHRA ABDUL MOMYN AHLAN.


BISSALAM.
[8/19, 10:57 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*



*page°°°°°37&40*



Ta rungume gawar Na'ila a jikinta, tama kasa magana banda kukan da take yi tana girgiza kai tare da jijjiga Na'ila, da kyar Mama ta iya fizgar magana a bakinta muryarta harta canza kala tsananin tashin hankali.

"Ƴata! Yarinyata Na'ila! Dan Allah ki tashi!"

Cike da ɗimauta Mama take magana, Ubaidullah ji yake duniyar tayi masa zafi har wani duhu-duhu yake gani, ga kansa dake juya masa, komai ya cakuɗe masa, yanzu sam yaji baya gane komai.


Jama'ar dake tsaye a wajan banda kukan tausayi babu abinda sukeyi dan tausayi iya tausayi sunji ma wa innan familyn yarinya da aka zo har kofar gate din gidan su, aka cilla gawarta.


Ana nan a tsaye cirko-cirko kowa ya rasa abun yi, an rasa mai lallashin wa innan bayin Allah, har kuma yanzu Hafiza bata farka daga sumar da tayi ba, itama tana nan a kwance a kasa.


Mahaifin su Abi'atu ne ya dawo yaga mutane rututu akan layin nasu, gabansa ne ya fadi ya ce.
"To meke faruwa ne haka a arean tamu ko dai mutuwa akayi ne?" yana tambayar kansa yayinda ya samu waje yayi parking din motarsa ya fito.


Cikin ikon Allah kuwa ya hango babban ɗansa Safwan a cikin mutanen yana tsaye a gefe yana share hawaye.


Karasowa Baban su Safwan yayi ya dafa kafaɗar dan nasa yake tambayarsa kan meya faru, nan Safwan ya kwashe komai ya fadawa Mahaifin nasu.

Baban su Safwan shine wanda yaje ya dafa Ubaidullah wanda da kayi masa kallo ɗaya zaka gane babu hankalin da natsuwa a tare dashi duk ya fice daga hayyacinsa.


Kallonsa da kyau Baban su Safwan yayi kafin yayi karfin hali irin nasu na manya ya ce.

"Haba ɗana kana namiji da kai, kuma daga ganinka kai din jarumin maza ne taya zaka saka mata a gaba kana kuka? Bai dace da kai ba plss, kayi hakuri, ku tashi mu kai yarinyar Asibiti a dubata, a tabbatar da abun da ya sameta watakila ma ba mutuwa tayi ba"

Ya juya ya ce.
"Am Safwan ɗauko mota, ku kuma dan Allah ku ɗan matsa a wuce"



Kamar mahaukaci haka Ubaidullah ya suri Na'ila, yayinda Safwan ya juya da gudu domin yaja mota, jama'ar dake wajan suka matsa.

Safwan yana kawo mota Ubaidullah ya shige gidan baya rungume da Na'ila a ƙirjinsa, Inna ta cire mayafinta ta miƙawa Ubaidullah ta ce ya rufewa Na'ilan jiki dashi.


Karba kawai yayi ba tare da yayi magana ba, Umma (mahaifiyar su Zaidu) da Inna da Mama su ne suka ɗauki Hafiza wacce tayi shame-shame a kasa tamƙar itama babu rai a tattare da ita, suka sakata a motar.


Baban su Safwan ya shige gidan gaba, Ubaidullah a baya shi da Na'ila ga Hafiza a gefensa itama.

Ta window Baban Safwan ya leƙo ya kira Ummin su Abi'atun akan ta shigo gidan baya su zauna tare da Ubaidullah da Na'ilan idan yaso saita rungume Hafiza, tun da Abi'atu ta iya mota sai su taho dasu Mama da Umma da Inna, da kuma Anty Ummu.

Hakan kuwa akayi Ubaidullah ya juya ya kalli Abi'atu dake tsaye wacce itama kallo ɗaya zaka mata ka gane bata cikin hayyacinta, ya ce.
"Idan har zaki iya driving motata tana can gefe akwai key a jiki, ki tuƙa kuzo dashi" ba ta iya ta amsa masa ba illa gyaɗa masa kai da tayi alamun to, sannan Safwan ya figi motar da karfin tsiya suka dauki hanyar Specialist hospital.



Da kyar itama Abi'atu taje suka shiga taja motar Ubaidullah suka mara musu baya, amma me kafin su bisu sun bace musu Abi'atu ta ce.
"Ban san fa wani asibiti suka nufa ba gashi sun bace mana"

Inna ta ce.
"To banda abunki ƴarnan ba bature ya kawo mana sauki ba, ina salularki, maza ki kira Umminki ki tambayeta kiji, haka kuwa akayi, ta kira Mamanta ta faɗa mata asibitin da suka nufa.


Cikin gaggawa aka fara karban Na'ila, kafin akazo itama aka karbi Hafiza duk akayi emergency dasu.

Ban da zirya babu abun da Ubaidullah yake yi, Adduarsa ɗaya Allah yasa kanwarsa tana raye bata mutu ba, sannan ta faɗa masa suwaye suka aikata wannan ɗanyen aiki.


Baban su Safwan ne ya dafa Ubaidullah dan a lokacin har kusan karfe takwass da wani abu ya ce.
"Ɗana ba muyi Sallar magriba bafa ga kuma Isha'i, Safwan kuzo muje muyi Sallah" ya juya ga su Umma Ummi(mahaifiyar su Abi'atu) da Inna da Mama ya ce.
"Ku ma ku tashi ku kai farali sannan muyi wa yaran nan addua tun da har yanzu likitoci basu fito ba, balle mu san halin da yaran suke ciki" da to suka amsa sannan suka fita dan yin sallah mazan kuma sukayi masallacin dake cikin hospital din.


Bayan sun idar da Sallah Ubaidullah ya jima yana kwararo addua inda a karshe ya sake fashewa da kuka dan ya kasa control din zuciyarsa.

Har ila yau dai Baban su Safwan ne ya ci gaba da lallashinsa, ɗago kai Ubaidullah yayi ya kallesa ya ce.
"Alhaji ban sanka ba amma naji dadin kulawarka a garemu Allah ya saka da alkhairi"

Ɗan Murmushi yayi ya ce.
"Ba komai ɗana amma karka sake kirana da Alhaji ka kirani da Abba dan haka yarana suke kirana, kuma ina ganinka naji ka shiga raina, ba lokacin da zaka san ko ni waye bane, bari komai ya dawo dai-dai, but still ya kamata ka sani, ni maƙocine gare ku, ban jima da dawowa unguwar ba" jinjina kai kawai Ubaidullah yayi, dan ko ba komai da yayi sallah yayi addua sai yaji sauki a ransa.


Da haka suka tashi suka koma cikin asibitin har yanzu su Mama su na zaune jingum-jingum, Mama Allah ne kaɗai yasan halin da take ciki gashi itama ba lafiyar gareta sosai ba, tunda hawan jini gareta.


Sai wajan karfe goma kafin wani likita ya fito ya cire marks din face dinsa yana sharbe gumi ya ce.
"Alhamdulillah mun samu damar ceto rayuwar dayan yarinyar kuma munyi mata allura, za a fito da ita nan da wani ƙanƙanin lokaci zata farka In sha Allah, amma ɗayar gaski......" sai yayi shuru bai karasa maganarsa ba yayinda Mama ta rintse idanunta gam zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.

Abba( mahaifin su Safwan) ya ce.
"Likita ka faɗamin halin da ƴata take ciki dan Allah?" Ubaidullah tamƙar shuka haka ya tsaya ya kasa katabus, Anty Ummu kuwa ta fashe da kuka tana cewa.
"Dan Allah likita karka ce min kanwata rasuwa tayi na roƙe ka!" cike da tashin hankali ta karasa maganar Umma itama hawaye take yi tana lallashin Anty Ummu yayinda Inna take dannar Mama, Abi'atu kuwa can gefe ta rakub'e tana kuka mai cin zuciya.


Likita yayi gyaran murya cike da tausayin ganin halin da suke ciki ya ce.
"Kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, bata mutu ba, tana raye adduar ku take bukata pls ba kuka ba, amm Alhaji ina son ganinka a office dina kai da wannan" ya nuna Ubaidullah da Safwan tun da yaga sune maza.



Da sauri kuwa suka bi likita office dinsa, cikin harzari Ubaidullah ya ce.
" na roƙeka doctor ka fadamin gaskia a wani halin kanwata take ciki karka boye min?" yana magana hawaye na ambaliya a fuskarsa dan bai san adadin kaunar da yake yiwa yan uwansa ba.


Cike da damuwa likita ya fara koro jawabi.
"A gaskiya sai dai kuyi hakuri, dan yarinyar nan fyaɗe aka yi mata, dan gaskiya idan zata rayu to sai dai wani ikon Allah ,dan gabaki ɗayan gabanta yayi damager, and a iyakar binciken mu ba Namiji ɗaya bane ya danneta mazan da suka hau kanta zasu kai biyar and she's to young ace maza biyar sun danneta a lokaci ɗaya gata virgin ce, babbar mace ko a first nyt tana shan wahala tun da ranar da aka fara buɗata kenan, namiji ɗaya, to balle ita wannan yarinya ce karama, kuma da karfi suka shigeta, duk sun dagargaza mat....." maganar da Ubaidullah bai jira likita ya karasa ba ya saki ihu ya kwanta kasa yana birgima.

Da sauri Abba da Safwan suka yo kansa, kuka yake yana toshe kunnuwansa dan ji yake sun gaza daukar jawabin likita.

Da kyar Abba da Safwan da likita suka ɗago Ubaidullah wanda duk ilahirin jikinsa rawa take ga jijiyoyin jikinsa da suka miƙe a tsaye kiƙam kana ganin su zara-zara, Abba ya share hawaye ya ce.

"Doctor yanzu miye abun yi"

Girgiza kai yayi ya ce.
"Gaskiya bazan boye muku ba, mu munyi iya yinmu sai kuma ta Allah" doctor yana gama fadi ya fice.


Haka suka tashi Abba yana riƙe da Ubaidullah, room din suka shiga tana kwance an rufeta da farin yadin asibiti fuskarta ce kawai a buɗe, wajan kasanta kuma an saka mata wani abu an rufe wajan dashi, kasa jurewa Mama tayi ta juya ta fice tana kuka.


Ubaidullah ne ya karasa jikin gadon ya kamo hannunta ya fara magana da muryarsa da bata fita.

"Na roƙe ki kanwata ki tashi ki faɗamin suwaye suka miki! " wata norse ce ta shigo ta ce musu.
"Pls ban da hayaniya dan anyi mata alluran hutu" tana gama faɗi ta fice abunta.

Umma da Inna da Ummi suka fice, suka yi dakin da aka kwantar da Hafiza, itama an ɗaura mata ruwa, anan suka zauna aka bar Ubaidullah da Abi'atu Anty Ummu da Abba da Safwan, Abba ya ce.
"Ɗana ku zo muje gida idan yaso mu kawo abun bukata" girgiza kai Yayi alamun A'a baza shi ba, babu yanda Abba bai yiba amma Ubaidullah ya ƙi sam, Abi'atu ma tazo suje ita ma tace sam ba zata je ba, haka Abba da Safwan suka baro asibitin da sunan zasu dawo da asuba.


Haka suka zauna cirko-cirko abinci kuwa babu wanda yayi tunaninta ko ya bi ta kanta.


Da asuba da kyar Ubaidullah ya tashi ya tafi masallaci, itama Abi'atu da Anty Ummu suka nufi dakin da aka kwantar da Hafiza nan sukayi Sallar asuba aka ɗan gaggaisa sama-sama.


Ubaidullah ya dawo kenan daga masallaci zai shiga ya duba Hafiza sai yaji yo ihun Na'ila da karfi take furta kalmar.

"Innalillahi wainna ilayhirrajiun!innalillahi wainna ilayhirrajun! Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Yayana!! Mamana!! Hafizata!! Anty Ummuna!! zasu kashe! zan mutu! Wayyoo Anty Abi'atu! Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!""

Da mugun gudu Ubaidullah yayi dakin da Na'ila ke zunduma ihu ,
Duk da ihun muryarta a dashe yake, ga wani baƙin azaban da take ji yana tashi a kasanta tamƙar ana hura mata wutar dalma.

A ɗari da saba'in Ubaidullah ya shigo ɗakin ya ɗagota cikin ɗimauta ya hau mata magana.

"Kan..kanwata! Gani gani! Gani a kusa dake" Mama da Anty Ummu matsowa sukayi suka kama hannunta gam.

Sai juyin azaba take a jikin Yayanta, tambayarta ya kuma akan cewa su waye suka aikata mata haka, amma azaban da take ji ya hanata magana.

Cikin dauriya da fizgar magana ta fara magana.
"Mam..Mamana..ina Hafizata?" kasa bata amsa akayi ta ci gaba da magana, tana fizge-fizgen azaba.

"Mama dan Allah ki yafe min duk abun da na miki Anty Ummu kema ki yafe min, Yayana kaima ka yafe min, Yaya su bakwai ne suka kamani suk....."maganar da Na'ila bata karasa ba kenan ta koma fizgan kalman shahada a bakinta.

Gabaki ɗayan su sun ruɗe da gudu Anty Ummu da Abi'atu suka fita neman likita, zuwa wani lokaci kuma tayi ɗiff ta daina murkususu da fizge-fizgen kamar cutar ya lafa mata.

A kiɗime likita dasu Anty Ummu suka shigo, nan doctor ya hau dubata ya gama tattabata sannan ya jawo farin yadin ya rufe mata fuska ya ce.
"Sai dai fa kuyi hakuri amma yanzu kam ta cika, ta amsa kiran mahaliccinta"

Mama ta kalli hannunta wanda suke sarƙame dana Na'ila ta riƙe gam, doctor yasa hannu ya raba hannun Mama da na Na'ila, tangal-tangal Mama tayi baya ta zube sharab a kasa Umma tayi kanta da sauri, yayinda Abi'atu ta kwalla karan da yayi dai-dai da isowarsu Abba da Safwan.

Ubaidullah tamkar almara yake ganin Abun,ihu ya saka gami da cewa.

"Haba Na'ila!! Haba Na'ila! Ya zaki min haka? Baki fa fadamin suwaye ba? Dan Allah ki tashi Kanwata!?Kanwata!?Kanwata!? Ki tashi kince su bakwai ne suwaye bakwai din!?" Da karfi yake magana yana jijjigata, su Abba da Safwan da kyar suka b'anb'are Ubaidullah daga jikin gawar Na'ila nan ya hau buge-buge, wannan shi ake kira tashin hankali wanda ba a sa masa rana, mutuwa kuwa bata sallama da lokaci yayi sai tafiya.



💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

ALHAMDULILLAH AM BACK MY FANS PLS KARKU BANI KUNYA, YADDA KUKAYI ALKAWARI TO KARKU KARYATA.


LATE COMER INA TAYAMU MURNAR ZAGAYOWAR SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEEN AMMA BA IRINTA 2020 BA.


ALLAH KUMA YASA IDAN KUKA KARANTA KUNA MIN SHARING DINSA.

ALLAH YABAR SO DA KAUNA MY PPLS

ZAHRA ABDUL
MOMYN AHLAN

TAKU CE😁
[8/19, 10:57 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*



*page°°°°°41&45*


Da kyar Abba ya jawo Ubaidullah suka fita haraban wajen asibitin, Abba ya ɗaga waya ya kira Malam Liman, na unguwar tasu yake sanar dashi akan cewa yarinyar ta cika,Allah ya mata rasuwa, Abba yana gama faɗawa Malam Liman ya kira wasu Aminansa ya ce dan Allah su zo da mota babbar asibitin Specialist za a dauki gawa ne.


Ubaidullah na tsaye lokaci guda ya nemi hawayen dake zuba a idonsa ya rasa, idonsa ya ƙafe babu ruwan hawaye, ajiyar zuciya ya koma saukewa ba ƙaƙƙautawa.


A can ciki kuwa Inna da Ummi sune suka kamo Mama sukayi waje da ita, yayinda Umma ta kama Anty Ummu da Abi'atu tayi waje dasu su ma.



Abokan Abba sun zo su uku da manyan motaci guda Uku da mutane biyar, nan aka tsaya maganar sa hannu a bada gawar Na'ila dan aje gida a mata sutura a kaita gidanta na gaskiya.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Da misalin karfe bakwai da rabi na safe.

Tsaye suke sanye da kakin sojoji a jikin su, Zaidu sai jeka ka dawo yake yi ya kasa zama sai trying din numbern Ubaidullah yake amma yanzu kwata-kwata wayar bata shiga switch up ake ce masa, cike da damuwa gami da faduwar gaba ya ɗago suka hada ido da KB ya ce.

"KB har yanzu fa Ubaidullah shuru anya lafiya kuwa? Gaskiya ni jikina baya bani lafiya, rabon da muyi magana dashi tun da ya ce min ya kusan shiga bauchi I told he will call me so that ya sanar dani cewa ya isa lafiya, but shuru fa" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka, KB ya ce.


"Gaskiya nima jikina yana bani ba lafiya ba, jiya na dauka gajiyar hanya ce ta sashi mantawa damu shiyasa bai kira mu ba, amma kuma Ubaidullah baya makara wajan sallarh asuba,kuma baya rabuwa da wayarsa a kusa dashi, kuma da asuba din nida kai duk mun kirasa bai ɗaga ba, gaskiya ya kamata ka kira Umma ka tambayeta tunda itama Mama ka kira bata ɗaga ba, gaskiya bana tunanin akwai lafiya"

Zaidu ya ce.
"To taya Umma zata sani? Ko da yake bari na kiranta idan yaso saita aiki Afnan da Manal su je su gani ko lafiya" Zaidu ya hau dealing din Numbern Mamansa, cikin sa'a kuwa a lokacin ita wayar yana hannnunta su na tsaye a waja ana jira Doctor yazo yasa hannu a bada gawar Na'ila, ta ji wayarta na neman agaji, tana dubawa ta ga Zaidu ne ke kiranta, ita tama manta da kiransa shakaf ta fada masa abun da ke faruwa, inama aka ga natsuwar kiraye-kirayen.

A lokacin Anty Ummu tana rungume a jikin Umma ita da Abi'atu su na Kuka mai ban tausayi, Umma ta dan ɗaga kansu ta tashi ta koma gefe tana sharbe hawaye da hijabinta kafin tayi karfin halin ɗaga wayar Zaidu.



Sallama ya mata ta amsa, a yanda yaji muryarta nan take ƙirjinsa ya bada dam!dam!dam, cikin damuwa ya ce.

"Umma lafiya kuwa? Ya naji muryarki kamar kina kuka meya faru? Dan Allah Umma ki fada min meke faruwa,haka kawai naji jikina yana bani gida ba lafiya ba, jiya Ubaidullah ya taho bauchi inata kiran wayarsa bai ɗaga ba yanzu kuma bata shiga, harta Mama na kirata bata ɗaga ba, yanzu kuma na kira ki naji muryarki kamar kina kuka dan Allah Umma meke faruwa?" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka.

Duk yadda Umma taso ta daure karta yi abun da zaisa Zaidu ya gane amma ta kasa, bata san lokacin da wani sabon kuka ya b'arke mata ba, cikin kuka ta ce.

"Zaidu, duk abun da kakeyi ka ajiyeta ka taho bauchi yau din nan kuma a yanzu, Zaidu babu lafiya,Zaidu ba kalau ba, Zaidu Mama ba zata iya daga waya ba, na tabbata bata san ma inda wayar take ba, Zaidu Abokinka yana cikin babbar damuwa da tashin hankali,Zaidu *NA'ILA TA RASU!! NA'ILA TA RASU!!* Zaidu" Umma ta sake fashewa da kuka.


Zaidu bai san lokacin da wayar dake

1 Comments On COLONEL UBAIDULLAH
avatar
zainab-hassan

11 months ago

Reply

????

Please Login or Register in order to submit comment