Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a tare.

Zaidu ya ce.
"Wai meya faru ne kam?"

Mama ta ce.
"kai dai bari kawai Zaidu kanwarka bata jin magana, idan munje gida sai ta fada maka da bakinta"

Zaidu yayi murmushi ba tare da yayi magana ba
Suka zauna jiran Ubaidullah yau ne gobe ne shuru.

Mama ta ce.

"Zaidu kawai kayi abun da ya kamata mu tafi gida wannan
Abokin naka sai kai ."


Zaidu yana dariya yaje sa hannu aka basu sallama sai gida .




~~~~~~~~~



COMMENTS
&
SHARE


BY MOMYN AHLAN✍🏻👮🏻‍♀
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~~•~~
TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°15&16*



Basu zarce ko ina ba sai gidan Anty Ummu, sallama suka yi, Anty Ummu ta fito da sauri daga kitchen sakamakon jin murya ɗan uwa gudan jiki.

Tana ganinsa kuwa annurin fuskarta ta ƙaru, shi ma Ubaidullah dariya yake yi wanda har ya bayyana hakwaransa.

Hannu Anty Ummu ta miƙa masa cike da murna, tana cewa.

"Ɗan uwa kai ne ko kuma dai idona ne yake min gizo?"

Cike da zolaya Zaidu ya ce.
"Anty Ummu abu daya zai sa ki tantance ko shi ne, ko ba shi ba ne, bari na miƙo miki wancan tabaryar, ki shemesa da ita daga nan za ki gane gaskiyar tambayarki."

Anty Ummu ta kwashe da dariya, ta ce.
"Daga haka ma na tabbatar ƙanne na ne a gabana ku shigo daga ciki."


Su na shiga Anty Ummu ta cike musu gabansu da kayan ciye-ciye da shaye-shaye,sai nan nan take yi dasu.

Sai da ta tabbatar basu buƙatar wani abu tukunna tazo ta zauna kusa da kaninta suka gaisheta ta amsa,su na hira su na dariya.

Anty Ummu ta ce.
"Amma dai ina fatan bana zaku kwana biyu kafin ku koma ko?"

Zaidu ya ce.
"Ina kuwa jimawa Anty babba, wallahi 5days General Of Army ya bamu dan kwanan nan zamu tafi bakin bordern nijar domin kamo wasu y'an ta'adda."


"Oh Allah ni Ummu kenan yanzu shikenan ku haka rayuwarku zata ƙara a fagen da ga?"

Sai yanzu Ubaidullah ya bude baki yayi magana.

"To big sister ya zamu yi ai ya zama dole tun da munyi alƙawari tare da rantsuwar gare kasarmu ta gado wato nigeria, gashi mune jami'ai wanda aka fi ji dasu bana gaya miki a waya an yi mana ƙarin girma ba, to ai yanzu kam bamu ga wani hutu ko zama waje daya ba, kawai ku dinga tayamu da addua."


Anty Ummu ta numfasa ta shaƙi iska, sai ga hawaye yana zuba daga idonta wanda yayi sanadiyyar hankalin Ubaidullah tashi nan ya shiga jero mata tambayoyi ba ƙaƙƙautawa.

Girgiza kai Anty Ummu tayi ta ce.
"Ba komai dan uwa ka kwantar da hankalinka,Allah ya taimake ku Allah yasa ku gama da duniya lafiya,Allah ya ƙare ku da ga sharrin masu sharri."

Sosai Anty Ummu take ta zuba musu adduoi su na amsawa da amin.


Daga baya kuma suka hau hiran yaushe gamo har yaran Anty Ummu su biyu suka dawo suka samu kawun su, suka hau murna su na cewa.
"Oyoyo kawu"

Ubaidullah ya na dariya sai kace ba shi bane mai cin magani a barracks, amma in dai a cikin familynsa ne yana dariya har haƙorinsa ya bayyana , sai dai idan y'an halin ne suka tashi,dan a kwaisa da miskilancin magana wasu lokutan, ga zafin rai, wa in da basu san shi ba kuma suke cewa yana da girman kai.


Kallon yaran Anty Ummu yayi yana dariya ,Haidar da Sakina, ya ce.

"Yarana ya kuke? fatan lafiya kalau kuke ko?"

Suka amsa da eh, nan ya dan taba wasa da yaran kafin Anty Ummu ta korasu gidan kakarsu ta wajen uba.

Bayan sun fita Anty Ummu ta ce.

"Wai ni yaushe ne kam za a kawo min surka? gaskiya ina so naga matan ƙannena."

Zaidu ya kwashe da dariya ya ce.
"To Ubaidullah gareka fa ,big Anty tana son ganin in'law "


Hararan wasa Anty Ummu ta yiwa Zaidu kafin ta ce.

"Ai ba da shi kadai nake yi ba har da kai, ko sai na ba da sadakar ku ne?"

Zaidu ya zare ido ya ce.
"Big Anty ai wallahi my man yafi karfin sadaka dan baki ga yanda ladies a barracks suke haukan sonsa bane abun har tsoro yake bani wallahi."

Anty Ummu tana dariya tana kallon ƙaninta lokaci guda ya haɗe rai da fuska sai ka ce ba shi bane mai dariya yanzu-yanzun nan.


Zaidu ya ce.
"Ka ga Malam Ubaidu duk wannan haɗe ran naka bai taso ba, kai soja ne nima kuma soja ne, kawai fina kayi da zafin rai miye to ma na hade rai din danna faɗawa Big Anty gaskiya?"


"Mtswwww Zaid ka fa kiyayeni, kasan fa halina, Allah na tuba in ban da tsautsayi mai zanyi da y'an matan barracks? duk babu wacce take gabana, kai ne dai kake sha'awar aure yanzu, amma ni Captain Ubaidullah ba yanzu ba, dan har kwanan gobe ban ga yarinyar da tamin ba wanda zan buɗe bakina na ce ina sonta ba"


Riƙe baki Anty Ummu tayi tana kallon ƙanin nata cike da mamaki da al'ajabi, shi fa haka yake, idan ya rikiɗe sai ka kasa gane kansa, dan wani lokacin ma yafi hawainiya.


"To yanzu kai Dan Uwa idan baka yi aure yanzu ba sai yaushe zaka yi? karka manta fa kai Jarumin Soja ne, kuma Sojoji sai da mata a kusa"cewar Anty Ummu.


Zaidu ya ce.
"Kyalesa kawai big Anty, shi ma fa yana so kawai basarwa yake yi yana nunawa kamar baya so, kuma wallahi ranar da muka je gidan General naga y'arsa tana satan kallonsa duk yanda aka yi itama ta ƙyasa ne" ya ƙarasa managar yana dariya.


Iyakar ƙuluwa Ubaidullah ya gama tunzura, sai huci yake fitarwa yana hararan Zaidu.

Dariya Zaidu ya kwashe da shi kafin ya ce.
"Ai dama nikam sai dai na ƙare a harara amma babu abin da za a min aha"


Anty Ummu abun dariya ya bata ta ce.
"To shikenan naji ƙanina baya son aure yanzu, amma kai Zaid naji ya ce kana so dan haka wacece surkar tawa, tun da yallabai ya ce ba yanzu ba ina jira faɗamin ita yanzu?"


Sun kuyar da kai ƙasa Zaidu yayi yana sosa ƙeya ba tare da yayi magana ba.


"To ban gane ba na tambayeka ka hau sun kuyar da kai me hakan ke nufi?" Anty Ummu ta tambayi Zaidu cike da rashin fahimta.

Ubaidullah ya ce.
"Amma dai ba shirmen da ka fada min dazu bane kake wannan gulman sun kuyar da kan wa big Anty ba?"


Kallonsu Anty Ummu tayi ta ce.
"Kai ban fahimta ba me kuke nufi,kun sakani a duhu fa wace magana ce?" ta juya ga Ubaidullah.

Ubaidullah ya ce.
"Nifa wallahi har na manta ashe shi bai manta ba, kinsan jiya da nazo na yiwa su Na'ila duka har sai da na kaisu hospital"


Cikin firgici Anty Ummu ta ce.
"Me kuma su Na'ila suka yi da ka dakesu ,kuma har da Hafiza, ita da bata da hayaniya?"


"A'a Big Anty ba fa Hafiza ba ce, Na'ila dai da kawayenta,wallahi Big Anty bansan me yake damun Na'ila da yawo ba wai jiya sun je walima tun rana amma yaran nan basu dawo ba sai 9 ni kuma raina ya b'aci nayi musu duka ita da kawayen nata sannan na kaisu asibiti"nan ya dinga bawa Anty Ummu labari.

Anty Ummu ta ce.
"Na'ila kam ai sai dai Addua Allah ya shirya mana ita, amma Na'ila kam bata ji, to miye kuma Zaidu yake sun kuyar da kai din?"


Ubaidullah ya ce .
"Wai cewa yayi yana son Na'ila zai jirata nan da shekara biyar ya aureta"

Anty Ummu ta hau dariya tana kallon Zaidu.

Ubaidullah ya kuma cewa.
"Ina ma laifi ya ce Hafiza ita ma din tayi masa yarinya yanda yake b'ab'atun auren nan kam"


Sosai Zaidu yaji haushi yana hararar amininsa ganin yana so yaja ra'ayin Anty Ummu ita ma ta mai da maganar wasa yasa Zaidu tasowa yazo kusa da Anty Ummu fuskarsa babu alamun wasa, ya ce.


"My Big Anty plss karki biyewa Ubaidu ba zai gane bane amma Antyna ki yarda dani wallahi da gaske nake ina son Na'ila, kuma ko yanzu aka bani ita zan riketa ba tare da nayi mata komai ba har ta kai shekara sha shidda, zan ci gaba da kula da ita na raineta,amma bazan so na rabasu da ƴar uwarta ba saboda akwai shaƙuwa mai karfi a tsakaninsu, Anty karku duba cewa Na'ila tayi ƙanƙanta nima ai yaro ne, a wani kauyen ma wallahi Antyna karki yi mamaki kiga yarinya sa'ar Na'ila tana da yaronta a hannu, pls Antyna ki shige mun gaba ki bani kwarin gwiwa, am serious wallahi" ya ƙarasa cike da fuskar tausayi.

Sosai Anty Ummu ta natsu tana sauraron maganar Zaidu kafin ta numfasa ta ce.

"Karka damu ƙanina in dai har da gasken gaske kake yi, ni kuma nayi maka Alƙawari Na'ila matar ka ce"


Zaro ido Ubaidullah yayi kafin ya kalli Anty Ummu ya ce.

" What! Big Anty matarsa fa kika ce? ina wallahi Na'ila ba zata iya da kai ba, ka nemi wata mata" ya faɗa cike da sigar jin baki.

Anty Ummu tana dariya ta tashi tana cewa.
"ku kam halinku sai ku ,ba a iya muku ,yanzu dai idan naje gida zan faɗawa Mama ɗanta yana son ƴarta"

Sake sosa kai Zaidu yayi ya ce.
"Pls Antyna ki bari sai mun koma tukunna"

Dariya Anty Ummu tayi ta ce.
"Naƙi na bari ai gwanda Mama ta sani tun yanzu, kai kuma Dan Uwa zan ga ranar da zaka zo kace min ga zab'inka ina nan ina jira."


Tabe baki Ubaidullah yayi ba tare da yayi magana ba, haka suka ci gaba da hira cike da nishaɗi, sai da akayi sallarh la'asar kafin suka yiwa Anty Ummu sallama suka nufi gidan su Zaidu.


~~~~~~~~


Da sallama suka shiga Inna ce kawai a tsakar gida tana ta faman sababi.

"Haba ace ayi yara basu jin magana kwata-kwata sai kace ƴaƴan jinnu to wallahi nikam ƙaniyarku zanci ƴan buhun uba, yara sai rainin tsiya wallahi mai sunan ifrituwa zaki dawo ki sameni ne ha."


Zaidu ya ce.
"Oh Allah matar wa ya tabamin ke ne kam haka kike ta faman mita?"

"Kai dai bari kawai soja mugun mutum ni da ƙannanka mana masu kai kamar giginya, ai yau babu abin da zai hanani ban b'allawa yarinyar nan kafa ba mai sunan jinnu ifrituwa"

Zaidu ya ce.
"Yanzu dan Allah Inna ba zaki dai na kiranta da sunan ifritu ba, ba fa haka sunanta yake ba, sunanta (Afnan) ne"


"Mtswww dalla tafi can ka bani waje yara gaku nan duk suna babu tsari ba kan gado balle kan kujera, yanzu miye wani suna wai afirina?"

Dafe kai Zaidu yayi sannan ya ce.
"Ni dai Inna baza ki saka min ciwon kai ba, my man muje ciki"

"Au ka ce min tare kuke kai da aminin naka mai fuska kullum babu rahma,wallahi na tabbata idan na rantse bazan kaffara ba, wannan a alluran da ake yi muku shi nashi na musamman ne,dan ana yi masa ƙari da na rashin dariya, haba mutum kullum sai kace ana masa bishara da mutuwa?"


Girgiza kai Ubaidullah yayi sannan ya gaisheta ya wuce yayi gaba Zaidu ya bisa a baya nan Inna ta sake tasa wata sabuwar mita tare da zage-zage.


"Zaku ji dashi wato ina magana shine ku ka yi gaba, ku ka barni ina magana ni ka daina wato na ɗaɗe ban yi ba ko, da abokin kan nan da idonsa ƙifi-ƙifi kamar ta soyu gyada."


Su dai basu kulata ba parlour suka wuce suka gaida Umma ta amsa tana cewa.

"Me yasa kuke son tab'o Inna ne kam? Kuma nasan kai ne Zaid,dan baka jin dadi in dai baka tsokani Inna ba, to wallahi ku kiyayeni yanzu suka gama dasu afnan kafin su fita"


Zaidu ya ce.
"Wallahi Umma nikam ban tsokaneta ba ai kinsan halin Inna"


Umma ta ce.
"To naji bar maganar haka kafin tazo ta sake fata-fata damu baki ɗaya"


Tashi suka yi, Umma ta ce.
"Ku huta kafin na gama abinci,"

Suka ce a'a sunci abinci a wajan Mama da kuma gidan Anty Ummu.

Umma ta ce .
"To yayi kyau ai haka ake so sun taimaka muku gauraye"

Su na dariya suka wuce gaba.


Sai yamma lilis gafen magriba kafin suka fita yawon zaga gari, basu koma gida ba sai bayan sallarh isha'i wajan tara zuwa goma, kowa gidan su ya wuce.


~~~~~~~~~


Da washe gari ma haka suka dinga zagaye gari, Ubaidullah har gidan dangin Baba yaje ya musu alƙairi wanda ya saka su jin kunya suka dinga kame-kame, amma yayi kamar bai san suna yiba.


Yau kwanarsu hudu sun fara shirin komawa Abuja bakin aikinsu, kafin nan kuma, Anty Ummu ta fadawa Mama yadda suka yi da Zaidu dariya Mama tayi ta ce, Allah ya zab'a abin da yafi alƙairi aka bar maganar a haka.


A kwanaki hudun da Ubaidullah yayi sam baya shga hidiman ƙannansa , wanda hakan ya saka su damuwa, Hafiza ce ta kawo shawara su masa girki da kansu sannan suje su basa hakuri karya tafi yana fushi dasu, hakan kuwa aka yi.


Suka shiga kitchen, Mama take tambayarsu, me zasu yi, suka ce zasu yiwa Yayan su girki ne, Mama ta ce. " to Allah ya taimaka ta fita ta barsu"


Da misalin goma na safe, Ubaidullah yana tsaya a dress mirror yana shiryawa, waya ne a kunnensa, su na waya da K,B.


Sallama suka yi a hankali, jikinsu na kyarma saboda tsoro.

Amsa sallamar tasu yayi kafin ya ci gaba da wayarsa da K,B yana tabbatar masa akan cewa zasu dawo gobe, kafin suka yi sallama ya a jiye wayar ba tare da ya kallesu ba.

Na'ila ce tayi karfin halin cewa.
"Yaya mun shirya maka breakfast"

"Get out!! ya faɗa a tsawance, ba ƙaramin tsorata suka yi ba, a madadin su fitan kamar yanda ya bukata sai kawai suka ruga da gudu suka rungumesa sannan suka saki kuka a tare.


Nan take jikin Ubaidullah yayi sanyi dan yana da raunin zuciya wajan tausayi, ɗaure zuciyarsa yayi,daƙile ya kuma cewa.
"Ku sake ni!"

Amma sun ki sai kukan su dake ƙaruwa cikin ,Kuka Na'ila ta hau magana.

"Pls 4give me Yaya I promise u bazan sake ba, pls Yaya karka tafi kana fushi dani bazan sake ba na tuba pls Yaya trust me Yaya" ta ci gaba da kuka.

Ita ma Hafiza hakurin ta hau basa cikin sanyin muryarta.

"Yaya kayi hakuri mun san kana yine saboda son da kake mana but pls Yaya ka daina fushi damu"

Na'ila ta kuma cewa.
"Yaya idan ma duka ne na yarda ka sake min in dai zaka huce ka daina fushi, kwata-kwata wannan zuwan kan Yaya baka kulamu ba, Yaya nasan nice na jawo saboda bana jin magana, Yaya ka dakeni ka huce amma ka daina fushi kayi hakuri" ta faɗa ta hau wanke fuskarta da mari.

Da sauri Ubaidullah ya rike hannunta,sannan ya rungumesu idonsa har sun kaɗa sunyi ja.

A hankali ya ce.
"Is ok, but karki sake, muje na ga abincin da my flowers sister's dina suka min" ya fada yana smiling.

Sosai suka ji dadi.

Har parlour suka jera yana riƙe da hannun su, Mama tana ganinsu ta girgiza kai ba tare da ta kulasu ba.

Nan ya zauna ya fara ci su na hira kamar ba shi ba,yana santin abinci ya ce.

"Yanzu ku, ku ka girki wannan abinci mai dadi haka?"

Su na dariya cike da jin dadi suka amsa da eh, dan ba karamin dadi suka ji ba ganin Yayansu ya hakura.


Ko da ya gama cin abinci ya kwashesu suka yiwa Mama magana sun fita Mama ta ce, a dawo lafiya.

Gidan Anty Ummu yaje ya dauki Haidar da Sakina, sannan yaje gidan su Zaidu ya dauki Afnan da Manal da Nawaz (ƙannen Zaidu) yawo suka fita ya musu siyayya sannan suka koma gidan Anty Ummu, sai dare suka koma gida.


Da daddare suka gama shirin su dan gobe da safe zasu koma Abuja dan har General Of The Army yayi kira a waya.


~~~~~~~



Ina mai baku hakuri, kuma ku kara hakuri na rashin samun posting akan tym

Zazzabi ne ta sakoni gaba wallahi



COMMENTS
&
SHARE


BY MRS IS OK MOMYN AHLAN✍🏻
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~~•~~
TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘

____________


Kawata @⁨Nana Aisha⁩
Tawan @⁨Maman Twins⁩
My luv @⁨Khadija Jounalist⁩
Inayinku over Allah yabar ƙauna.

Dole na fara sa koku masoyan asali,

Doter @⁨Surayyah Dan Ango⁩
Antyn Ahlan @⁨6 Naphersarh⁩
Habibty @⁨احلم فطمة⁩
@⁨Samira Bint Abdallah🌹🌺⁩
@⁨Maryam Mrs M Lawal⁩
Doter @⁨Doter Fareesat⁩
Dear @⁨Fatima Bintu Sagir⁩
@⁨👩‍⚕Dr,Herpsert👩‍⚕⁩
@⁨Mrs M,j (Fans)⁩
@⁨Mrs Faruq💃⁩
@⁨MAMAN ZAHRA⁩
@⁨Mummy jidda⁩
@⁨Maman Basma⁩
@⁨Aisha Ibrahim Ummi😊⁩
@⁨Firdausi Hussain Namad💝🔐⁩


_~IYAKAR WA INDA NA GANI KENAN~_

*WANNAN PAGE DIN TAKU CE MY PPLS*❣


*_~KO BA WUYA ANA TSABTAR TARE~_*💔
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°17&18*



Washe gari da safe suka shirya tsaf cikin kakin su na sojoji, sosai suka yi ɗamara, yayinda kakin ya karb'esu, barin ma Ubaidullah yayi masa kyau sai kace a jikinsa aka halicci kakin.


Fitowa suka yi a tare da Mama, da Anty Ummu, Hafiza,Na'ila.

Ubaidullah yana tsakiyar su, Mama da Anty Ummu su na ta kwararo masa addua, sai amsawa yake yi da amin, yana so ya mai dasu barracks amma Mama ba zata yarda ta koma Abuja ba, duk ma ba wannan ba,da kunya ya ɗauki Mama ya kaita barracks saboda kajinan da suke bibiyar rayuwarsa ,ko wacce take kawo masa hari.


Su na isowa bakin mota Zaidu ya fito ya duƙa ya gaishe da Mama ta amsa, sannan ya gaishe da Anty Ummu ta amsa tana dariya, su Hafiza da Na'ila suka gaishesa ya amsa, Anty Ummu ta ce.

"To surkina dan Allah a kula sosai, Allah ya kaiku lafiya Allah yabaku sa'a a tafiyar da zaku yi, Allah ya ɗaura ku akan maƙiya tare da mahassada"


"Amin ya Rabbi Allah, Big Anty mun gode da wannan adduar taki Allah ya saka da Alkairi"

Anty Ummu tayi murmushi ta ce. "Ba komai ƙannena a kula dai da kyau dan Allah"

Zaidu ya ce.
"In sha Allah Big Anty zamu kula"



Kallon su Mama tayi a lokacin da suka iso gaban mota ta ce.

"Duk abun da ya kamata ace Uwa tana gayawa ɗanta a lokacin da zai fita neman halak dinsa Ubaidullahi ban rage ko guda daga ciki ba, na faɗa maka yanzu ma kuma zan ƙara nanata maka wasu daga cikin kalaman masu hatsirin gaske, Ubaidullah Zaidullah?" Mama ta kira sunan su a tare, suka amsa kansu duƙe su na kallon ƙasa.


"Zan ƙara yi muku tuni akan cewa ku gujewa haram, karku yi tunani da cewa ai kadan ce sam Allah ba ruwansa da wannan ,kuna samun rufin asirinku dai-dai gwargwado, na tabbata da ace baku riƙe gaskiya ba, da ba zaku taka matsayin da kuke dashi a yanzu ba, dan haka ku guji abun haram karku fito a cikin hadisin Manzon Allah sallallahu alayhi wa'sallam da yake cewa ( لايدخل اجانةجسدغذي بااحارام)
Wato dukkan gangar jikin da aka ginasa da haramun bazai shiga Aljanna ba, amma abun da zai baku mamaki a wannan zamanin da muke ciki bamu dauki haram a bakin komai ba,mun maida haram abincin mu, ruwan shan mu, gadon baccin mu, wajan zaman mu,komai namu, gabaki daya shagalar tai mana yawa, mun bar koyarwar Allah da Manzon S,A,W, mun bar hadisai mun bi ruɗin duniya da son zuciya da kyale-kyalen banza, wanda zata kai mu ga halaka, jin dadi duniya ƙadan ne wato (ADDUNYA MATA'UN ƘALILAN) dan haka Ubaidullah Zaidullah kuji tsoron Allah a duk in da ku ka kasance, karku biyewa neman mata kamar yadda aka yiwa sojoji ittifaƙin neman matan banza, ku ɗauke idanun ku ,ku yiwa idonku hijabi wajan kallon haram, abin da nake nufi shine abun da bai zama halaliyarku ba, idan kuma aure ne ga mata a gari da yaran yan uwa da abokan arziƙi, sai ku duba a ciki mu sha biki, maganganun basu kare ba, amma karna saka ku makara kuje Allah ya kaiku lafiya Allah yaba da sa'a Allah ya ƙare ku, gabanku da bayanku dama da hagunku, Allah yasa kuje aikin da aka tura ku lafiya ku dawo lafiya tare da manyan nasarori, Allah ya muku Albarka gaba'ɗayan ku"


Sosai jikinsu ya sake yin sanyi duk da sun saba da nasihan iyayen nasu, amsawa su Ubaidullah suka yi da amin, sannan suka ƙara da cewa.
"In sha Allah zamu kiyaye Mama, mun gade Allah ya ƙara girma da nisan kwana"

Mama ta amsa da amin tana murmushin karfin hali dan hawaye ne ya cika tam a idonta, juyawa tayi zata koma cikin gida, ta ji muryan Ubaidullah, "MAMA"
ya kira sunanta, tsak Mama ta tsaye amma bata juyo ba.

Takowa Ubaidullah yayi yazo gabanta sannan ya rungumeta idonsa yayi ja sosai,baya so ya kashe mata jiki gashi dama tana fama da hawan jini so yake ya ce mata, ta yafesa idan har yayi mata wani laifi amma yaga alamunta ma hawaye take son yi dan haka ya canza akalar maganar ta hanyar cewa.

"I gonna miss Mama"



Nan ma murmushi tayi ta shafo fuskarsa, "miss u more son Allah ya maka albarka kuje yanzu kam, karku makara uhum?"

Ɗaga kai Ubaidullah yayi, sannan ya saki Mama ya juya ya koma wajan su Anty Ummu da suke tsaye, Anty Ummu tana yiwa Zaidu tsiya , sai dariya yake yi yana sun kuyar da kai ƙasa yana satar kallon Na'ila, wacce suka takure waja daya ita da yar uwarta wanda da kaga alamun su kasan ƙiris suke jira su saka kuka, dama sun saba duk zuwan Yayan nasu idan zai koma sai sun masa kuka tun da yana shafe watanni kafin yazo idan kuma yazo baya wani jimawa zai koma ,idan har ya jima shine yayi 1week ya koma.


Kallon su Ubaidullah yayi sannan ya bude bakinsa ya hankalin ya kira sunan su. "My flowers" sannan ya bude musu hannayensa da gudu suka rungumesa suka sa kuka, ita ma Anty Ummu bata san lokacin da hawaye ya wanke mata fuska ba, hawaye ta hau yi, Ubaidullah ya sake su Hafiza ya juya yana kallon Anty Ummu girgiza mata kai yayi alamun tayi shuru, sannan yasa hannu ya goge mata hawayen,da sauri ya shige mota Zaidu ma ya shiga yaja su Anty Ummu dasu Hafiza su na ɗaga musu hannu , mai gadi ya bude musu gate suka bar gidan suka ɗauki hanyar birnin tarayya Abuja.



~~~~~~~~~



Sallah ce kaɗai ya tsaida su Ubaidullah a hanya.


Sai karfe 4:30pm su Ubaidullah motar su tayi parking a *9JA BARRACKS ABUJA*.

da K,B suka fara haduwa nan Zaidu ya fito da sauri suka rungumi juna,amma kafin Ubaidullah ya fito sai da ya gama shan kamshinsa tukunna har K,B yana cewa. "wai ina guy din nan yake ne,ko bai dawo bane shi?"

Murmushi Zaidu yayi sannan ya ce.
"Amma dai inaji K,B ka manta da waye Ubaidullah ko? shiyasa bai fito a mota ba kake tambaya idan bai shaƙi kamshi ba kafin ya fito taya za a gane cewa Captain Ubaidullah Abdullahi ya dawo?"

Suka sa dariya su na tafawa, dai dai nan Ubaidullah ya zuro kafafunsa ƙasa ,fuskar nan tamau ba annuri, K,B yazo suka rungumi juna Ubaidullah yayi wani miskilin murmushi sannan suka jera har part dinsu.


Bathroom Ubaidullah ya wuce direct domin yayi fresh up bcox a gajiye yake, ya kwashi kusan 30mnts kafin

1 Comments On COLONEL UBAIDULLAH
avatar
zainab-hassan

11 months ago

Reply

????

Please Login or Register in order to submit comment