Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gane haka ba, ba zata iya hango tsananin son da muke mata ba, Mama har nawa Na'ila take duka-duka shekarunta goma fa Mama, amma take neman fin karfin mu?"


Mama ta share hawaye ta ce.
"Haka ne yanzu su na ina"


Na kai su asibiti"

Mama ta dafe ƙirgi ta ce.
"Ubaidu asibiti dai, asibiti fa kace? har da ƴaƴan mutane ka daka fa? shi ne duk ka kai su asibiti?"


"To Mama ai hakan shi ne daidai, baki ga ba saboda rashin kula irin na iyayensu akwai wanda ya zo nemansu ne? ba su zo ba ,ni a tunani na hakkin iyaye ne idan ba su ga y'ay'an su ba ko min dare ya kamata su je nemansu, amma ba su zo ba."

Shuru Mama tayi kafin ta ce.
"Ni fa wallahi bana son tashin hankali da ka bar yara sun tafi gidan iyayensu, bana son abun magana da ƙanwarka kaɗai ka hukunta."

Wani murmushi ya saki kafin ya miƙe ganin har karfe hudu ta gauta ,ya ce.
"Mama ba ki jin dadi ,ba ishashshiyar lafiya gare ki ba, yanzu ki kwanta ki huta gobe sai mu koma asibitin mu dubo su"

Mama ta ce.
"Yaran mutane kuma fa?"

Ya ce.
"Mama sai magana kike yi a kan yaran mutane , na ga fa harda Na'ila"

Girgiza kai tayi ta ce.
"Je ka huta, yau ka zo amma ko hutawa baka yi ba, Allah dai ya sa ka ci abincin ma"

Dan sosa ƙeya yayi.
"Wallahi Mama banci ba, zan ci idan Allah ya kai mu anjima", yana fadi ya sa kai ya fice a dakin,Mama ta bi bayansa da kallo kana ta ce.

"Allah ya daɗa shirya min ku"

~~~~~~~

ta ban garen Hafiza ma ba ta yi bacci ba, tana jin yadda y'ar uwarta ta dinga ihu tana kuka, ita ma haka ta dinga kukan a daki, ko da taji shuru tsoron fitowa take yi karya haɗa da ita.



~~~~~~~~~


Da washe gari.

Da safe misali karfe tara.

Ubaidullah ya dan koma bacci bayan yayi sallar asuba kafin zuwa sha biyu su je asibiti" ana tunanin kenan.

Cikin bacci yake jin kamar hayaniya na tashi, amma sai ya danganta hakan da mafarki, jin abun bana ƙarewa ba ne ya saka shi tashi ya dauki jallabiyyarsa ya saka ya fito, can wajan gate ya hango Mama da Hafiza tsaye gefe daya mai gadi da wasu samari su uku da yan mata biyu.

Cike da takun isa da izzan jarumtaka na ƙarfeffen soja ya ƙaraso mai gadi na ganinsa ya sara masa ya koma gefe.

Hafiza tana ganin Yayan nasu tayi saurin matsawa gefen Mama.

Cike da ɗaure fuska ya ce. "lafiya kuwa meke faruwa?"

Daya daga cikin samarin ne ya nuna Ubaidullah da yatsa yana cewa.

"Kai dalla malam, ma su waye zaka fito kana ciccin magani, idan kana gadara kai namiji ne ai muma ba ka ganmu da jan baki ko dan'kwali ba, ina ƙannan mu?su muka zo nema, kuma ance sun zo nan tare da ƙanwarka, yanzu kuma mun zo muna jin wata zance da bamu ganeta ba."


Ran Ubaidullah ya baci sosai ya tsaya yana masa wani kallon raini,

Kafin ya kalli Hafiza ya ce.
"Wuce ki shiga ciki"

Da gudu ta juya tayi abin da ya umarceta kafin ya kamo kafadar Mama ya juya da niyyar ya shige da ita ciki ita ma, sai ya ji daya daga cikin samarin yana cewa.

"Kaiiiiiii! ina ga baka san su waye ake kira da yan'bakaro ba, babu unguwar da ta kai mu sara suka a cikin garin Bauchi, idan baka fito mana da ƙannan mu ba, to wallahi sai mun yi gunduwa-gunduwa da kai."

Cak Ubaidullah ya ja ya tsaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur jikinsa ya ɗauki b'ari.



==============

MANAGER PLS


COMMENTS
&
SHARE

BY MOMYN AHLAN✍🏻👮🏻‍♀
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~~•~~
*MARUBUCIYAR*

*HALITTA DAGA ALLAH NE*
*GUDU A JEJI*
*SHUHADA*
*NIDA ƘANNAN MIJINA*
TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°13&14*



A hanya su na tafiya Mama sai mita take a ina Ubaidullah ya tsaya.

Zaidu ya ce.
"Mama maybe akwai abun da ya tsai dashi ne shiyasa a yiwa abokina uzuri"

Mama ta girgiza kai kawai, ta ce.
"Mu fara biyawa mu a jiye ƴaƴan mutane kafin mu wuce gida"

"To Mama" abun da Zaidu ya furta kenan.


Sai da suka a jiye yaran mutane a gidan iyayensu, Mama da kanta ta shiga tayi musu jawabi, wanda zasu fahimta sun fahimta, masu toshewar kwakwalwa kuma sun kasa fahimta, suka rufe Mama da ruwan bala'i, ganin yanda jikinsa ƴaƴansu ya kumbura da shatin belt, bisa alamu duka ba bana wasa ya musu ba.


Mama har sai da ta ji dadi da Ubaidullah bai zo ba,dan tasan wani abun kam sai dai a kunna ƙaramin yaƙi.

Zaidu ya ce.
"Mama wai mai ya faru ne kam haka na kasa fahimtar komai fa?"

Mama ta ce.
"Ai gata nan a gabanka sai tsilli-tsilli take yiwa mutane da ido, na rashin gaskiya, ai tukunna ma sai mun koma gida ki sake haduwa dashi"


Na'ila tayi rau-rau da ido alamun zata yi kuka.

Zaidu ya ce.
"No no my lovely kar kiyi kuka kinji ai gani nan ina nan bazan bari ya sake dukan ki ba."

Da haka har suka koma gida.

Mama tana tambayar mai gadi akan cewa "Ubaidullah bai dawo gida ba?"

Ya ce.
"Eh Mama ai tun da ku ka fita shi ma yaja mota wanda ya sakani tsinkewar zuciya ya fice bai dawo ba."

Girgiza kai Mama tayi sannan ta ce. "Allah ya kyauta"
Suka shige cikin gida, Zaidu ya ce.

"Mama ni zan koma part dinsa na zauna kafin ya dawo"

"To Zaidu ka huta kafin ya zo ma na gama muku girki, tun da yanzu kam sai dai abincin rana."


~~~~~~~~~~



Ta bangaren Ubaidullah ko da ya je hospital din aka tabbatar masa da an sallamesu, sun tafi tun dazu.

Wayarsa ya dauka ya bugawa Zaidu, a lokacin Zaidu na zaune a 2sitter yana latsa systerm dinsa.

Daukar wayar yayi yasa kunne.

Ubaidullah ya ce.
"ya ne, kun koma gida ne"


"Ah no Captain Ubaidullah muna hospital muna jiranka."


"Mtswwwww, Zaidu bana son raini fa"

Wani dariya Zaidu ya kwashe dashi wanda yasa Ubaidullah rumtse ido, kuma da gangan Zaidu yayi dan kawai ya sake ƙular dashi.

"Oh Allah, Yayana Ubaidu baka son raini, ni kuma kasan ai ina son raini, ka ga idan zaka dawo gida ka dawo, dan mu kam har mun manta da wai munje hospital yaran jama'a kuma mun kai su gida."

Ubaidu bai sake magana ba illa tsakin da ya ja, ya katse wayar.

Zaidu ma dariya yake yi, ya a jiye wayarsa a gefensa ya ci gaba da aikin da yake yi a systerm dinsa.


Sallaman samarin yayi gami da cewa su tafi gida, ƙannan su an kai su gida,kafin shi ma ya shiga motarsa ya dauki hanyar gida.


~~~~~~~~~


Wajan Mama ya fara wuce wa,tana ganinsa ta hau mita.

"Tun dazu muka fita tare da kai Ubaidu,amma kai sai yanzu ake ganinka, ina ka tsaya ko kuma nace ina ka wuce?"


Dan sosa gefen wuyarsa yayi dan shi bai cika son yiwa Mama karya ba amma yanzu ya zama dole ya suturta maganarsa.

ya kafin ya ce.
"Am so sorry my Momma, ina fita wani kiran ya taso min shiyasa dole na je nayi wancan aiki tun da nasan kun fita da Zaidu zai yi abun da ya kamata."


"Oh Allah to da Zaidun bai zo ba kuma fa?"

"Kiyi hakuri Mama tun da ya zo ai shikenan, yanzu ina Zaidun ya ke?"


Mama ta juya ta shiga kitchen tana ba sa amsa tana kiran sunan Hafiza.


Fita yayi ya je ya samu Zaidu zaune a kujera ya duƙufa akan systerm, sallama Ubaidullah yayi, Zaidu ya ɗago ya kallesa ya amsa, ganin sai wani cin magani yake yi yasa Zaidu ɗauke kansa shi ma ya ci gaba da abun da yake yi.


Can zuwa anjima Hafiza ta shigo da sallama, suka amsa kafin ta ce.

"Mama ce ta aiko ni na zo na tambaye ku, a kawo muku abincin nan ne ko zaku zo ku ci?"

Zaidu ya kashe systerm din dake cinyarsa ya tashi yana cewa.

"No my sister nikam a wajan Mama zanje na ci amma bansan wannan Yayan naku dan zafin kan ba"

Tsaki Ubaidullah yayi shi ma ya tashi suka fito a tare, har izuwa parlour, Mama ta shinfiɗa musu babbar lade na cin abinci, suka zazzauna.

Hafiza ta zauna can nesa dasu tana jiran fitowar Na'ila amma shuru ba Na'ila, ita kuma Hafiza ba zata iya cin abincin ba matukar y'ar uwarta ba ta fito ba.

Zaidu ya kula da haka ya juya yana kallon Mama ya ce.

"Mama meya faru ne kam, me aka yiwa my lovely aka faffasa mata jiki gashi yanzu taƙi fitowa ta ci abinci?"


"Zaidu wannan lovelyn dinka bata jin magana kwata-kwata jiya wai sun tafi walima yaran nan tun rana amma sai karfe tara na dare suka dawo, sai ka ce basu da mafaɗi, shiyasa Yayansu ya jibgesu har da kawayen nata ai kaga gobe ba zata sake zuwa ba, na rasa dalilin da yasa Na'ila bata jin magana tun dana iyanzunta take son tuburewa ai gwanda ya mai dota saiti."


Zaidu ya ce.
"Haba Mama yanzu a gabanki ya musu wannan dukar sai kace ya kama b'arawo a guardroom? abokina nan fa ba barracks ba ne, gida ne bai ka mata ka dakesu da belt din sojoji ba ,gaskiya ban ji dadin haka ba, yes punishment din da ka musu shi ne dai-dai kuma naji dadi da ka haɗa har da friends din gobe ba zasu ƙara zuwa su ja ta ba, amma dukan yayi worst gaskiya ka dinga sassautawa."


Mama dai bata sake cewa komai ba illa ma tashi da tayi ta shiga daki tabarsu a wajan.

Ubaidullah ma ko uhum bai cewa aminin nasa ba.

Zaidu ya kalli Hafiza wacce ta raƙube a gefe ya ce.
"My sister oya tashi ki je ki kira min my lovely"

Hafiza ta amsa da to , ta tashi tayi hanyar dakinsu.

Da sallama ta shiga ta samu Na'ila zaune ta zuba tagumi har yanzu fuskarta a kumbure yake, wani tausayin yar uwarta ne ya kamata, tazo ta zauna kusa da ita ta ce.

"Sister ki taso ki zo muje muci abinci mana?"

Girgiza kai Na'ila tayi ta ce.
"Na ƙoshi bana jin yunwa jikina ne yake min ciwo"


"To ki sha paracetamol sai ki zo muje Yaya Zaidu ya ce na zo na kira ki ,kuma na tabbatar mun zo tare ki taso muje kinji siaterna"


"Yaya yana parlourn?"

Ta tambayi Hafiza.

Hafiza ta ce.
"Eh mana yana parlor ina so idan mun je ki basa hakuri kinga Yaya yana sonmu amma ke baki jin magana ,Na'ila ba kyau Mama ta ce kibar abu amma ki ƙi ji Yaya ya hanaki yawo Anty Ummu ma ta hanaki amma duk baki ji, ki ga fa idan har Anty Ummu ta saka Yaya abu yana yi fa, to ke meyasa idan ya sakaki ba zaki ji ba ko kinga ni haka nake yi ne iyee?"

Girgiza kai Na'ila tayi alamun a'a.

Kafin Hafiza ta ce.
"To ki natsu kin ga dai yanzu Yaya, ya zama mugu amma bana mugunta ba dan haka mu bisa a hankali mu dinga jin magana, gashi karba ki sha muje"


Karban maganin Na'ila tayi tasha da kyar, kafin suka fito sai rakub'e-rakub'e suke yi dukkansu.

Su na fitowa Ubaidullah ya musu kallo daya yaga yanda jikinsu ke rawa alamun tsoronsa suke ji ,shi kuma ba haka bane burinsa ace ya zama dodo a wajan ƙannansa.

Dan haka su na fitowa ya tashi ya fice yayi hanyar part dinsa.

Zaidu ma fada yayiwa Na'ila sannan ya bi bayan amininsa.


Kwance ya samesa a 3sitter ya lumshe ido.

Zaidu yayi murmushi ya ce.
"Na ga kalar soyayyar yan uwa, amma shine duk da haka ka shirgiɗa musu na jaki?"



"Mtsww Zaidu ba zaka gane bane izuwa yanzu yaci ace ka gama karantar halina"


"Eh na fahimce ka my man addua zamu dinga musu, ni fa kasan wani abu kuwa?"

Ubaidullah ya girgiza kai yana kallonsa.

Zaidu ya ce.
"Ni wallahi da zaka ban Na'ila ita nake so wallahi zan jirata nan da shekaru biyar na aureta dan ina sonta."


"Hahahah Zaidu kenan ko dai ka fara shaye-shaye ne? Na'ila fa ka ce ina zaka kai wannan gagaran,dama Hafiza ka ce yauwa amma Na'ila sai a hankali" ya karasa maganar yana dariya sai ka ce ba shi ba.


Abun da Zaidu ya fahimta shine Ubaidullah ya dauki maganarsa a matsayin wasa shi kuma da gaske yake yi ,amma ba komai zai basa mamaki.

Zaidu zai sake yin magana ,Ubaidullah ya ce.
"Ka ga tashi muje na gano y'ar uwata Yayata Anty Ummu naje naga lafiyarta daga nan naje na gaishe da Umma, mu zagaye gari tun da 5days kawai zamu yi."

Zaidu ya ce.
"Ok mu je"

Fitowa suka yi a tare sai da suka yiwa Mama magana kafin suka shiga mota suka bar gidan.




~~~~~~~~



COMMENTS
&
SHARE

BY MOMYN AHLAN MRS IS OK✍🏻👮🏻‍♀
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~~•~~
*MARUBUCIYAR*

*HALITTA DAGA ALLAH NE*
*GUDU A JEJI*
*SHUHADA*
*NIDA ƘANNAN MIJINA*
TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°11&12*



Ganin haka yasa Mama hankalinta tashi, dan tasan ba ƙaramin aikinsa ba ne yan zun nan ya musu lahani.

Ubaidullah dake riƙe da kafaɗun Mama jin abun da dayan saurayin nan ke fadi ya saka shi sakin Mama ya juya a fusace cike da zafin nama, cikin hanzari Mama ta riƙosa gam kafin ta ce.

"Kul Ubaidullah ban yarda ba ban amince ba karka taba daya daga cikinsu ka kyalesu muje, mu shirya, mu wuce asibiti a duba yaran sannan a basu ƙannan su, dan ni gaskiya banji dadin haɗawa da yaran mutane da kayi ba, danni ban son damuwa da hayaniya ko tashin hankali basu da dadi."

Mama ,tana ta mita riƙe da hannun Ubaidullah wanda gabakid'aya jijiyoyin jikinsa sun fito raɗa-raɗa, tsantsan bacin rai, domin maganar saurayin yayi mugun bata mishi rai har gadara yake yi cewa shi dan sara suka ne kuma har yake fada masa ko dan bai san shi waye ba ne"? ya tambayi kansa.


Da kyar Mama ta janye Ubaidullah ,suka shige cikin gida.

Mama ta zaunar dashi ganin yanda jijiyoyin jikinsa ya fito ya bayyana, idanunsa suka sake ƙanƙancewa ,suka yi jajur dasu.


Mama ta buɗe baki ta kwalawa Hafiza kira.

Da sauri Hafiza ta fito ta ce. "Mama gani"

"Je ki kawo min ruwa mai sanyi"

Hafiza ta amsa da "to" sannan ta juya da sauri,ta dawo dauke da ruwa a glass cup ta miƙawa Mama.

Karba Mama tayi sai da ta gurb'a tukunna ta miƙawa Captain Ubaidullah, amma sam ya ƙi karba balle yasha, dan har izuwa yanzu jikinsa kyarma yake yi burinsa bai wuce ya ladabtar da y'an iskan samarin bakaro ba, masu ikirarin su yan sara suka ne.


Mama ganin fa tabbas Ubaidunta ransa ya baci ne ,ta sake kurban ruwan a bakinta, tukunna ta kamo kansa ta danna cup din ruwan bakinsa, da kyar ya iya karfin hali buɗe bakinsa, ya kurbi ruwan sannan ya sauke a jiyar zuciya mai karfin gaske, bakinsa yana fitar da tururi tare da hayaki.

Mamaki ne ya kama Mama sosai a zuciyarta ta ce.
"Tabdijam ni Salamatu gani ga ɗa, saboda bacin rai bakinsa harda hayaki? lallai kam da ake cewa soja marmari daga nesa."


Da kyar Ubaidullah ya dawo hayyacinsa,ya ɗan sassaita natsuwarsa, ya miƙe tsaye ya ce.
"Mama ki shirya mu tafi hospital din"

Mama ta ce.
"Dama wani hospital ka kai su?"

"Rimi hospital, naga yafi kusa that's why"

Mama ta ce.
"Ok to, ka shirya kayi sauri kaji?"

Ɗaga kai yayi, ya fice.

Mama ta bi bayansa da kallo, a fili ta ce. "Ubaidu Allah ya kawo zuciyarka sassauci dama tun da ya kake balle yanzu da ake ɗirka maka alluran sojoji ai sai ta Allah.

Mama ta ce.
"Hafiza ki shirya yanzu kafin ya gama, nima kaya kawai zan canza dan nayi wanka tun dazu,dan hankalina yana kan yaran mutane wallahi"

Hafiza ta ce.
"Mama nima fa nayi wanka tun tuni"

"To ki saka hijab dinki dan nasan ba jimawa zanyi ba zai fito" Mama ta fada tana shigewa dakinta.

Hafiza ma ɗaki ta shiga ta saka hijab dinta, ta dawo parlour ta zauna, bata jima da zama sosai ba, Mama ita ma ta fito.

Bayan zaman Mama kamar da minti biyar haka, sai ga Ubaidullah ya shigo parlour'n bakinsa dauke da sallama.

Amsawa Mama da Hafiza suka yi.

Mama ta ɗago ido tana kallon ɗan nata, sanye yake da wandon jeans and brown t-shart, mai ratsin tambarin sojoji a jiki, yayi matuƙar kyau amma fuskar nan jiya iyau.


A hankali ya buɗe bakinsa, cikin sanyin murya kamar ba shi ba ya ce. "Mama muje"

Tashi Mama tayi sai da ya ga tayi gaba tukunna ya bita a baya kafin Hafiza ita ma ta dauki basket din abinci ta bi bayansa ita ma.


Har yanzu samarin su na tsaye a gate, Ubaidullah yana musu kallo daya,ya saki dariyar mugunta wanda shi ka ɗai ya barwa kansa sanin manufar dariyarsa.

Ya buɗe mota zai shiga kenan sai ga Zaidu, wani farinciki ya sake mamaye Ubaidullah wanda shi kadai yasan hakan.

Mama tana ganin Zaidu ta faɗaɗa murmushin fuskarta, da sauri Zaidu ya ƙaraso ya duƙa a gaban Mama yana kwasar gaisuwa, cike da fara'a da sakin fuska tare da kulawa Mama ta amsa, gami da cewa.

"yasu Umma dasu Inna fatan kowa lafiya ko?"


Zaidu ya sosa ƙeya yana russuna kai ƙasa dan shi kunyar Mama yake ji.

"Kowa lafiya kalau yake,Umma ma ta ce na gaisheki sosai"

"Ayya Allah sarki ina amsawa"

Zaidu ya miƙe yana kallon abokin nasa, sannan ya juya yana kallon samarin da suke tsaye cike da neman tada zaune tsaye.

Zaidu ya buɗe baki zai yi magana Hafiza ta gaishesa ya amsa yana cewa.

"Lafiya kalau my dear sister Hafiza, where is my lovely sister Na'ila?.

kafin Hafiza ta basa amsa ya juya ga Ubaidullah ya miƙa masa hannu suka gaisa ya ce.
"My man wasu guys ne wa innan haka a bakin gate kuma ina zaku je?" ya tambaya yana kallon Mama da Ubaidullah tare da wa'innan samarin da yan matan.

Mama ta ce.
"Humm yanzu dai ba lokaci Zaidu muje asibiti."

Zaidu ya waro ido waje ya riƙe baki yana cewa. "asibiti dai waye ba lafiya?"

Mama tace .
"Ƙanwarka Na'ila"

Zaidu, zai kuma yin wata maganar Ubaidullah ya buga tsaki gami da cewa.

"Oh my god dalla! malam ka wuce mu tafi kai ba ɗan jarida ba, but sai shegen uban questions din tsiya, idan muka je ai zaka ga abun da ya faru da idanunka.

Mama ta riƙe baki tana kallon Ubaidu.

Zaidu ya sa dariya ya ce.
"Wallahi Ubaidu zaka ji dashi"

Zaidu ya juya Ubaidu ya ce.
"Zaidu pls dauki Mama da Hafiza da wa'incan ladies din, ni kuma zan ɗauki guys din nan ne."

Zaidu ya ce.
"Okay Mama and my sister let's go."

Har zasu shiga mota Ubaidullah ya kira Hafiza tadawo jikinta na b'ari dan wani bala'in tsoron Yayan nasu take yi yanzu, dan gabaki'ɗaya ya sake burkice musu.

Hannunta ya kamo ya mata raɗa a kunne, ɗaga kai kawai tayi sannan ta juya da gudu tayi cikin gida.

Duk akan idon Mama, tana so ta fahimci wani abu amma ta kasa, dan haka ta saka zuciyarta salama, ta danganta hakan da yayi mantuwa ne, ya aiketa.

Hafiza ko cikakkiyar minti biyu bata yi ba, ta fito ta miƙa masa abu ya karba ya shige mota, sai da Zaidu ya tada motar suka fita sannan Ubaidullah ya juyo da motarsa yana kallon gefe, ba tare da yayi magana ba.


Daya daga cikin samarin yayi tsaki sannan ya shige gaban mota, sauran biyun kuma suka shiga bayan mota.

Tun daga gate Captain Ubaidullah da yawani fizgi motar sai ka rantse da Allah duniyar taurari zasu.

Wanda hakan yayi sanadiyyar faɗuwar gaban wa'innan samari, Ubaidullah da gayya yayi hakan ,dan sai ya ci ubansu hankalinsa zai kwanta, dan bai dauki raini a barracks ba ma, balle kuma ba a barracks ba.


Cikin kaɗuwa na gaban ya kamo sitbelt zai ɗaura, saboda wani uban gudun da Ubaidullah yake sharan titi dashi yana tada ƙura.

Har ya sa hannu zai jone Ubaidullah ya janyo yar ƙaramar wuƙa a gefen takalminsa wanda ake musu ikirari da boost ya datse sitbelt din.

Sannan yayi wata smiling na gefen baki wanda zaka iya yi masa inkiya da mugutar soja.

A madadin Ubaidullah yayi Rimi Hospital, amma sai ya juya kan mota ya ɗauki hanyar filin unguwar rafin zurfi.

Da ɗan nisa a tsakani ,amma kasancewar gudun da yake bana wasa bane kamar giftawar ido da bismillah, sai gasu a filin rafin zurfi.

Sosai Ubaidullah ke juya mota, yana shatale'tale, dasu.

Ba ƙaramin jijjiga suka yi ba.

Kafin Ubaidu ya tsaida motar ya fito yana huci.

A hasale ya ce.
"Duk ku fito."

A galabaisa suka fito su na sauke wahalalliyar numfashi tare da ajiyar zuciya da kyar.

Ruwa Ubaidu ya ɗauko ya basu, da sauri suka karba, ko wannen su sai da yasha 2bottle.

Sannan Ubaidullah ya ɗane bayan motarsa ya zauna yana kaɗa kafarsa ɗaya.

Murya a sheƙe ya ce.
"Ku maimaita abun da ku ka ce dazu, ina so na tabbatar da cewa eh tabbas maza ne a gaba na idan kuma ba haka ba to ina muku albishir da cewa dole ku shafawa bakin ku wannan lipstick din, wasa za a buga tsakanin haziƙi gawurtaccen soja, da haziƙan tantiran y'an sara suka."

Ya fada yana jujjuyawa jan bakin da ya aike Hafiza ta ɗauko masa, a hannunsa ya wulla sama sannan ya cafke.

Tsoro ne ya gama mamaye zukatan maza uku, su har ga Allah basu yi tunanin soja ba ne.

Gashi yanzu sun taro wa kansu jafa'i.

Kallon-kallo suka hau yiwa juna options daya ne garesu shine su basa hakuri.

Ai kuwa nan suka shiga koro ruwan hakuri.

Ubaidullah ya ce.
"Haba maza ya ku ka yi saurin yin sanyi haka tun ba a kafta wasan ba?"

"Dan Allah yallabai kayi hakuri wallahi bamu san kai soja ba ne."


Ubaidu ya numfasa kafin ya fara magana
"Haƙiƙa na ɗaki ƙannan ku wanda a halin yanzu su na gadon asibiti tare da ƙanwata wanda ina mutuwar sonsu da kaunarsu, amma ni bana sake da ƙanne na saboda sha'anin rayuwa, ace yara ko shekara sha biyar basu kai ba amma wai sun tafi walima tun rana har karfe taran dare!" ya fada a tsawance zuciyarsa na sake yi masa zafi.

"To ni bana daukar nonsense any moment and bana careless akan watsewar tarbiyyan ƙanne na, ba ma iyakar su ka ɗai ba ,dukkan mace, yarinya, babba , budurwa, ni haka tsarina yake ni Ubaidullah!"

Ya karasa maganar cike da izza da jin ƙai.

Sai da ya shiga mota sannan ya ce.
"Sa'arku daya tak baku gwadamin iskancin samarin bakaro ba, dan wallahi da kun min taurin kai kun kawo min raini da ko wani ƙaramin dan iska ya kwashi kashinsa a tafin hannunsa, idan ku na da ra'ayi ku shiga mota mu tafi ko wallahi nayi tafiyata."

Ai tun bai karasa ba suka miƙe har su na rige-rige, da sun ga alama idan har zasu yi faɗa da Ubaidullah babu abin da zasu ɗauka a jikinsa.


~~~~~~~~~



Ta bangaren su Zaidu kuwa sun isa asibiti sun samu jikinsu Na'ila da sauki, har ma likita yana maganar sallamarsu.

Zaidu ya ce.
"Bari Ubaidullah ya zo"

Hafiza da gudu ta rungumi yar uwarta, suka saka kuka

1 Comments On COLONEL UBAIDULLAH
avatar
zainab-hassan

11 months ago

Reply

????

Please Login or Register in order to submit comment