Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*~UBAIDULLAHI~*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0
~~•~~•~~•~~•~~•
*Special gift to my 5 ☆stars★*
_Samira bint Abdallah_💋
_Fatima bintu Sagir_💋
_Farhat Mrs M'J_💋
_Princess (Nafeesat)_💋
_احلام فاطمة_💋

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*




*page°°°°°106&110*




Sun jima haka kafin daga bisani Mama ta dago tana shafa fuskar Ɗan nata, tana jin farin cikin sake ganinsa, Hafiza ce ta kira Anty Ummu ta sanar mata akan cewa Yaya Ubaidullah ya dawo, Anty Ummu ba shiri ta zari hijabi takalmi ma daban-daban ta saka ta fice, Hafiza ma ficewa tayi da gudu ta je ta kirawo su Ummi ta ce Yayanta ya dawo, kafin ka ce me maƙota an cika parlourn Mama ana yiwa Ubaidullah jaje da ya jiki tare da yi masa fatan alkhairi akan nasarar da suka samu, har Anty Ummu ta iso tana zuwa ita ma da kuka ta tari ƙanin nata, idan ka kalli fuskokinsu a yau kasan su na cikin farin ciki matuƙa, har wajan karfe goma gidan Mama ana hayaniya, har da yan mata, musamman suke zuwa ganin jarumi Ubaidullah ya yinda da yawa su na fatan su shiga zuciyarsa su samu matsuguni a gidansa, Ubaidullah gajiya ya yi da hayaniyar, nan ya miƙe yana musu sallama ya ce zaije ya yi sallah yasha magani ya kwanta, Mama ta ce.
"Abi'atu tashi ki taimaka masa, idan kuma ba za ki iya ba ki fada min" a kunyace Abi'atu ta miƙe ta kama Ubaidullah suka fice, itama Anty Ummu sallama ta yiwa su Mama akan cewa zata zo gobe da safe daga nan aka fara watsewa, har gidan ta yi tsit,
Ubaidullah kuwa su na shiga part dinsu bedroom dinsa kai tsaye suka wuce, bedroom din a gyare tsaf dashi, zaunar da shi tayi a bakin gado kanta a sunkuye dan haka kawai ta ji wani masifaffar kunyarsa take ji, a hankali ta yi magana ta ce.
"Ka fara watsa ruwa kafin kayi sallahn" ta juya zata shiga toilet ya riƙo ta da hannunsa mai lafiya din ya ce.
"Ina da magana" sake yin ƙasa da kanta ta yi.
"Hummm, to wannan dukar da kan da kike yi na miye ne?" shuru ta yi bata ba shi amsa ba illa wasa da yar yatsar hannunta da take yi, da ya ga bata da niyyar magana ne ya saketa, yana saketa ta shige toilet da sauri har tana tuntube, tana shiga ta lumshe idanunta tana murmushi, daga Allah sai ita tasan irin kalar murnan da take ciki wanda baki ba wai iya furtawa ba, ruwan ta haɗa masa ta fito ta zo gabansa tana kallonsa ta ji gabanta na faduwa, dan da alama jikinsa bai yi ƙwari ba danyen ciwo ne, yanzu ya zata yi, ko ta je ta kira Mama ne? Take tambayar zuciyarta, bata gama tunaninta ba ta ji yana cewa.
"Kin gama haɗa ruwan ne?" ta gya ɗa masa kai alaman eh, ya ce.
"To zo ki cire min kaya ki min wanka" zaro idanu waje ta yi tana kallonsa ta ce.
"Iyeeeee!?" ya ce.
"Eh! Nace ki zo ki ciremin kaya ki min wanka" turo baki ta yi tana dan kunkuni ya ce.
"Magana kike yi?"
"Eh magana nake yi, taya zan maka wanka?, kafin kazo wa ke maka wanka? ni gaskiya sai dai naje na kira Mama ta maka wanka, amma ni kam ba zan iya maka wanka ba, babba da kai"
"To ai ba hakkin Mama bane jinyata ko kula dani ba, hakkin ki ne, a matsayinki ta Matata" da sauri ta kallesa ya kashe mata ido daya tare da mika hannunsa ta cire masa riga.
"Ni fa da gaske nake yi bazan iya maka wanka ba"
"Ohh!! Abi'ah na fa faɗa maki banyi sallah ba gashi yanzu har sha ɗaya saura ki hanzarta" juyawa ta yi zata fice ta ji yana ce mata.
"Au dan bani da lafiya shine za ki gujeni ba za ki iya kula dani ba ko? Ashe duk kukan da kike min na dawo kinyi kewata ashe duk yaudara ce? Wai ni an turoni gida matata ta yi jinyata ta kula dani ashe ma ba zata iya min komai ba,da na sani ma da ban dawo ba, da na zauna a barrack masu so na su kula dani su yi jinyata har na warke" jiki a sanyaye ta juyo ta kallesa ta ga ya haɗe rai yana faman kokarin cire riga amma ya kasa sabida dayan hannunsa dake sagale a wuyarsa gabaki daya baya iya amfani da bangaren hannun, tausayinsa ne ya kamata ta dawo jiki a sanyaye ta sa hannu zata cire masa rigar ya tureta gami da cewa.
"I don't needed just leave me alone, ki tafi abunki" sake kai hannu ta yi zata kama shi ya daga mata tsawa wanda ya yi sanadiyyar fashewa da kukan da ta yi ta kama kunnenta ta durƙusa a gabansa ta ce.
"I'm sorry, bazan sake ba, sorry plssss" still bai kalleta ba, ya ci gaba da kokarin cire rigarsa, ya daga hannun kenan yana so ya cire dayan hannunsa ya bugi ƙirjinsa da ɗan karfi ya furta "wasssshhhhhh Allah" da sauri ta tazo ta kama hannun nasa a wannan karon bai tureta ba, kuma bai mata magana ba, cikin dauriya ta cire masa rigan ya rage vest a jikinsa, jikinta na kyarma ta cire masa vest din, a hankalin ya miƙe tsaye ya dan dafa bango, kallon kafarsa ta yi taga kafar a kumbure ta dago ta kallesa taga har yanzu fuskar nan tasa tamau take Ubaidullah ko hawainiya ba zata gwada masa canza kala ba, ta faɗa a zuciyarta sannan ta shiga cikin waswasin cire masa wando, da kyar ta yi jahadi ta cire masa belt ta zare kafin ta hau balle masa aninin wando gabanta na dukan tara tara, haka ta gama ta ja masa wandon kasa, sannan ya ɗaga kafarsa, ya rage da ga shi sai boxers, kama shi ta yi suka yi hanyar toilet bayan sun shiga ta ja ta tsaya ki ƙam tamƙar gunki dan bata san me zata yi masa ba kuma, a dan fusace ya ce "ba ki san yadda ake yiwa mutane wanka bane? Idan ba ki sani ba pls fita min anan ki ban waje malama" kin fita ta yi illa ƙura masa ido da tayi tana kallon fuskarsa dan ta kasa kallon gangar jikinsa, hawaye ne ke zuba a idonta, tsaki Ubaidullah yaja da dan karfi kafin ya juya baya yasa hannunsa daya zai zare boxers dinsa, da sauri ta riko hannunsa ta ce "dan Allah karka cire zan maka wankan amma karka cire, ance haramun ne kallon tsiraici pls" a mugun mamakince Ubaidullah yake kallonta amma tama raina masa wayau, wallahi badadin baya da lafiya ba da taji maza yau din nan ba sai gobe ba, amma haka ya kyaleta, nan ta hau murza masa soso da sabulu tana wankesa cikin daraba, sun bata lokaci dan sai sha biyu suka fito daga wanka, zama ya yi kan stool dinsa ta goge mi shi jiki ta shafa masa mai,ta saka mi shi jallabiya sannan ya tada sallah, ganin yadda yake sallah duk sai tausayinsa ya kara kamata, bayan ya idar ne ta tambaye shi ko yana bukatar wani abu zata tafi, cikin daga murya ya ce.
"Ki tashi ki tafi mana, na hanaki ne ko na riƙeki ne?" jiki a sabule ta miƙe ta fita, Ubaidullah ya rintse ido gabansa na faduwa aransa ya ce.
"Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!! Ba dai Abi'atu bata sona bane? Da na shiga uku ji Ubaidu, da ace tana so na ba zata min wannan tarban ba, wata biyar fa bamu tare na dawo kuma da ciwo amma ba zata nuna min kulawa ba?" ya sake rintse ido "dole ne na fahimci kina so na ko baki so na" wayarsa ya jawo ya duba yaga su miss calls har da na Zaidu da KB dasu yan barracks, Mama ya kira yana tunanin ma ko sunyi bacci, ringing biyu Mama ta daga ta ce.
"Yaya Babba, ya dai kana bukatar wani abu ne?"
"A'a My Momma, bana bukatar komai, amma dan Allah turo min Hafiza" Mama ta amsa da to, ta kira Hafiza tace mata Yayanta na kiranta, ita kuma Abi'atu tana fita dakinta taje ta watsa ruwa tana tunanin rashin kyautawar da bata yi ba, dan haka bayan ta fito wanka ta shirya ta fita kitchen tana haɗa masa simple food bai dan ruwa ruwa wanda zai ji dadin ci, wanda ba zai damesa ba, tana girkin ne taci alwashin zata kula da shi zata cire kunya tayi jinyarsa tunda mijinta ne, jikinta ne ya yi sanyi tuno ce mata da ya yi, ta tashi ki tafi ai bai hanata ko ya riƙeta ba, a ranta ta ce "laifina ne, zan ba shi hakuri" baya ta gama ne ta haɗa masa coffee mai kauri da madara tasa a karamin trey ta yi hanyar dakinsa da sallama ta turo kofar ta ga Hafiza na ba shi magani, nan jikinta ya sake sanyi ta ajiye tray din hannunta akan karamin center table din dake dakin tana cewa.
"Hafiza ba kiyi bacci ba?"
"Eh wallahi Anty da har zan kwanta Mama tace Yaya na nemana" jinjina kai tayi ba tare da ta sake magana ba, Hafiza tana gama ba shi maganin tayi musu sai da safe ta fice abunta, ko kallonta bai yi ba ya fara shirin gyara kwanciyarsa ta ce.
"Ga shi fa nayi maka girki ne shap-shap" ya ce.
"Am ok, bana jin cin abinci" shuru ta yi kafin ta miƙe a hankali ta dauki tray din ta fice ta koma kitchen ta dau supboil ta zuba masa kadan sauran kuma ta juye a rabo ta sa a freezer dakin ta dawo ta haura gadon nasa ta kwanta, Ubaidullah da ya rufe ido kamar mai bacci ya ji shigowarta bai gama mamakin me ya dawo da ita ma ya ji ta hayo gado ta rungumesa cikin sanyin murya ta hau basa hakuri tare da alkawarin ba zata sake ba, da kyar ta shawo kansa ya kalleta ta dinga rokonsa ya ci abinci, kafin ya tashi yaci ta taimaka masa ya yi brush suka kwanta.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




Da washe gari sun makara sallah dan bacci ya musu dadi, rabon da su yi bacci kamar haka sun manta, sai karfe goma suka yi sallahn asuba, bayan sun idar suka sake komawa bacci basu da farkawa ba sai karfe biyu, nan ma sai da Anty Ummu ta aiko Hafiza ta duba ko su na lafiya, tukunna suka tashi, ta taimaka masa ya yi wanka ta shirya shi, itama ta yi ta shirya sannan ta kama shi suka yi part din Mama, tun daga kofar parlour hayaniya ke tashi, su na shiga kuwa suka iske mutane, su Ummi ne dasu Umma, Inna, Zaidu, Anty Ummu, Yaya Safwan da Matarsa Shafa'atu, da sauran maƙotan arziƙi, su na shiga aka hau gaishe-gaishe, Inna ganin Ubaidullah ta ce.
"Ohh Allah Ubaidu? Sannu ansha fama,an wuce da kyar ko? Yanzu sabida rashin imani haka suka yi maka? Dan ma kana da taurin rai inaji da yanzu zaman makoki muke yi, ina dalili da wannan aikin soja, kun bar mu cikin firgici da tashin hankali, gaskiya ni kam abun ya isheni" ta karasa maganar tana haɗe rai, Ubaidullah suka yi dariya shi da Zaidu, ba tare da sun bawa Inna amsa ba, aka ci gaba da hira su na bada labarin tashin hankalin da suke gani kafin Zaidu ya fara bada labarin yan ta'addan da aka kashe da sojojinsu da aka kashe duk da sunji a labarai amma ance waka a bakin me shi yafi dadi, yawancin mutanen da suke wajan fatan Alkhairi suka din ga yiwa sojojin nigeria, tare da adduar Allah ya daga nigeria, su Safwan ne suka miƙe su na yiwa jama'ar dake wajan sallama dan Shafa'atu bata jin dadi tana faman da laulayin karamin ciki, tun da Ubaidullah ya fahimci Shafa'atu na da ciki ya ji shi ma fa a duniya yana son ya ga Jininsa kwanan nan, inda ya kudirta a ransa kafin ya koma barracks sai ya mai da Abi'atunsa cikakkiyar mace, hira aka sha da Ubaidullah kamar ba shi ba, duk da azaban ciwon da yake ji a jikinsa, sai dare kafin jama'a aka watse.



Haka aka din ga yi har na tsawon sati daya ana cika a gidan Mama tamkar wanda ake shagalin biki, jikin Ubaidullah Ma sha Allah yana samun sauki kasancewar Hajiya Abi'atu an zage dantse wajan kula da miji, abun da yasa ta kara mai da hankali sabida yan matan da ta ga su na shigowa masu baki kamar na jab'a wai su na zuwa gaishe da mijinta ko wacce da kalar fari da idon da take masa, shi yasa ta sake ƙaimi wajan ba shi kulawa, da haka har ya yi sati biyu, kuma yanzu alhamdulillah yana iya daga dayar hannun nasa, wajan ciwon ya fara kamewa, yau ma kamar kullum ta fito daga kitchen shi kuma yana zaune kasar carpet, zama ta yi kusa da shi hannunta dauke da cup, fara ba shi kunun ta yi a baki yana sha, ya dan ja kumatunta, ya ce.
"Abi'ah?" kallonsa ta yi ba tare da ta amsa ba, ya kuma cewa.
"Abi'ah, *KINA SO NA?*" gabanta ne ya faɗi, tabbas tana son shi mana, amma sai ta tsinci kanta da kasa ba shi amsa, shi ma ganin ta yi shuru bai sake ce mata komai ba, illa zullumin da zuciyarsa ta shiga, tashi ta yi sabida ya gama shan kunun, tana tashi ya bita da wani kallo wanda ya haifar masa da kasala da jan ido, hakika Abi'atu tana da sirhitaccen kyau, jinginuwa ya yi da kujera ya lumshe ido yana taro yadda take tafiya halittar jikinta yana motsawa, har ta dawo ta zauna kusa da shi bai sani ba, sai da ta da fa shi ta ce.
"Lafiya kuwa?" bude ido ya yi, ta ga yadda idonsa ya rine, ta zaro ido ta sake jefo masa tambaya.
"Ya salam! Me ya same ka ne? Ko wani waje na maka ciwo ne?" bai bata amsa ba ya sake lumshe idonsa, kamar da, 5mins haka ya ce.
" *ABI'ATU*, nayi miki tambaya amma ba ki bani amsa ba, ko me yasa?" sake yin kasa ta yi da kanta tana wasa da fingers dinta, ji ta yi ta furta masa tana son shi ya mata tsauri a baki, fizgota Ubaidullah ya yi ta zube a kirjinsa wanda sai da ta bugi ciwonsa da sauri ta ce.
"Ciwon ka fa?" zata sa hannu da hannunsa marar lafiyar ya ture hannunta kamar zai yi kuka ya ce.
"Ban damu da wannan ba kawai ni ki bani amsata, do u luv me?" Shuru ta yi tana dan wani nazari kafin ta gya ɗa masa kai alaman eh, sake matseta ya yi a jikinsa dan farin ciki,duk da dai ya so ta furta ne a baki ba wai da kai ba, amma ya san ta da kafiyar tsiya kuma sai ta furta da kanta, magana ya fara mata ya ce.
"Yauwa, ni dama magana nake so muyi dake ko nace ina so ne muyi yar wata shawara,kinsan matarka itace abokiyar shawararka hakane?"
"Eh, haka ne, ina jin ka to"
"Yauwa, ina so ne Zaidu ya yi aure kafin mu koma bakin aiki, dan kin ga ance za a karrama mu ne, zan so ace yana da mata shi ma, dan haka ina so ayi aurensa da Hafiza kafin mu koma, amma ke ya kika gani?" gyara zama ta yi ta riƙe hab'a ta ce.
"Maganarka abun dubawa ne, amma kai kana ganin auren nan zai yu kafin ku koma? Yanzu fa saura sati biyu ne kawai, har za ayi shiri kafin ku koma?" murmushi ya yi, ya ce.
"Me zai hana, sati biyu ai da lokaci, da kudinmu fa a hannu, kuma kin ga auren gida ne ba na waje ba, daga yau zamu fara shiri in dai kin bada shawarar ayi, to ki koma gefe kiyi kallo" dariya ta sa ta ce.
"Na bada goyon baya dari bisa dari, na bada shawarar ayi, amma mijina bai ji sauki ba fa?"
"Wa ya gaya miki Mijinki bai ji sauki ba?"
"Au yanzu kai a ganinka ka ji sauki?"
"Ke ba ki yarda da naji sauki ba?"
"Taya zan yarda?" tashi ya yi ya kamo hannunta ya ce.
"Zo muje bedroom dina na gwada miki naji sauki, za ki sha mamakina yau" ba tare da ta fahimci abun da yake nufi ba ta hau binsa, har sunje bakin kofa zasu shiga ta gane me yake nufi da sauri ta fizge hannunta tana dariya ta sa gudu tayi hanyar bedroom dinta har tana riƙe kirji, shi ma dariya ya yi ya ce.
"Ai da kin tsaya na nuna miki yar nema kawai" kaya ya shiga ya canza ya fito ya kwankwasa mata kofa "matsoraciya, fito muje wajan Mama" da sanɗa ta fito su na haɗa ido suka saki murmushi a tare, kafin suka jera izuwa part din Mama, a dakinta suka sameta, nan Ubaidullah ya mata bayanin shawarar da suka yanke, Mama ta yi na'am da hakan, sannan ta ce ya nemi Zaid din su yi magana, yanzu ita ma zata nemi su Umma su yi magana sai asan abun yi, amma yana ganin jikinsa ya warke ne da zai bullo da maganar biki, ya amsata da shi baya jin komai ciwon ne kawai da basu gama hadewa ba, Hafiza dake tsaye kofar Mama ta ji shigowarsu Yayanta tazo ta gaishesu taji su na maganar da ya daga mata hankali, da gudu ta koma dakinta ta sawa kofar key ta dauki pic dinsu ta kifa a kirjinta ta hau rare kuka.
"Anya zan iya kuwa? Zan iya auren wanda ya so auren yar uwata? Kuma har kwanan gobe yake sonta? Anya nayiwa kaina adalci nayiwa yar uwata adalci? Anya idan na yarda na aure sa banci amanar yar uwata ba? Kai inaaa!!! Gaskiya bazan iya auren Yaya Zaidu ba, zanje na sanarwa su Mama ba zan auresa ba" duk maganar zuci take yi tana kuka, har wani ciwon kai ya sauka mata nan bacci mai nauyi ya yi gaba da ita, tare da mafarkin Na'ilah tana ce mata.
"Sismieta!! Yaya Zaidu yana da kirki karki kuskura kice ba za ki auresa ba, idan kika yi haka na yarda baki sona, ki auresa za ki ji dadi zakiyi farin ciki, idan ba ki auresa ba kinci amanata, kuma bamu ni babu ke dan haka kin ga tafiyata!!!" a bacci Hafiza ke mikawa Na'ilah hannu tana "sismieta ki tadawo na amince zan auresa dan Allah karki tafi ki barni" Na'ilah tana b'acewa Hafiza ta farka gami da kwala wa Na'ilah kira da karfi wanda Mama da tazo wucewa zata shiga kitchen ta ji, da sauri ta zo ta hau bugawa Hafiza kofa dan ta tura ta jita a garƙame, da kyar Hafiza ta rarrafa tazo ta budewa Mama kofa, jikinta sai kyarma yake yi gashi duk ta jiƙe da zufa, kuka Hafiza ta saka ta kwanta a jikin Mama tana yi, rarrashinta Mama take yi ba tare da tayi magana ba, dan ta sani har abada Na'ilah ba zata taba fice musu arai ba, Mama ta ce.
"Dama kina daki kina bacci har magriba? Ba dole ki din ga mafarkai ba, idan kinyi mafarkin yar uwarki ki daina mata ihu ki din ga mata addua, yanzu ki tashi ki watsa ruwa kiyi sallar magriba kafin a kira isha'i, anya ma kinyi azahar da la'asar?" ta girgiza alamun aa, "to ki tashi ki yi yanzu ko?" ta amsa da "to" Mama ta fice jikinta a sanyaye dan har an gama maganar bikin Hafiza da Zaid, inda za ayisa nan da kwana goma, ko da Hafiza ta watsa ruwa a daddafe ta yi sallah sabida mugun zazzabin da ya sauko mata, tana kife a wajan akayi isha'i, tana yi ta kwanta ta shige bargo, wajan takwas da rabi ta ji an banko mata kofa ana dariya, ji tayi har da guɗa, cikin zazzabi ta daga ta bude idonta ta kalli su Afnan da Manal da Afrah da Iman, kawayen su Afnan din ne, Afnan ce ta zauna a bakin gadon ta yaye bargon ta ji jikin Hafiza da zafi radauu ta ce.
"Subhanallahi!! Ba ki da lafiya ne? Manal je ki kirawo Mama" da sauri Manal ta fita, Afrah ta ce.
"Tooo daga saka aurenki shine har kin kwanta ciwo?" cikin zafin ciwo da tsananin mamaki Hafiza ta dago tana kallon Afrah ta ce.
"Aure kuma Afrah? Auren wa?"
"Keee! Kina nufin kice bakin an tsaida ranar aurenki yau ba? Nan da kwana goma? Yoo mu fa abun da ya kawo mu kenan mu fara shirye shiryen abun da zamu yi, dan aradun Allah zamu cashe, babu mai faɗa mana muji sai manya" suka sa dariya su na tafawa, yayinda Hafiza ta ji zazzabinta ya ƙaru, da haka Mama ta shigo ta dubata ta ce ko a kaita asibiti ne,amma firrr Hafiza ta ƙi, dan haka aka bata magani, su Afnan suka mata sallama da cewa zasu dawo gobe Allah ya kara sauki, suka fice abun su, su na fita Hafiza ta koma cikin bargo ta ci gaba da rera kukanta, abu goma da ashirin ne suka haɗe mata waje daya.





@@@@





Da washe gari ma haka ta wuni a daki ko parlour ta kasa fitowa ta bangare uku kuwa shirin biki aka fara ba kama kafar yaro, Ubaidullah ya kira KB ya sanar da shi auren Zaidu dan haka ya yi kokari ya ga ya halacci auren, KB ya fadawa Ubaidullah ai idan bai zo auren Zaidu ba, bai cika amini ba, Abba shine ya zama wa su Ubaidullah Uba a komai, ana biki saura kwana biyar KB ya sauka a bauchin yakubu, tun ranar da aka sa bikin Hafiza bata sake ganin Zaidu ba, bata yarda sun hadu ba, shi ma bai nemeta ba, dan ba a natsuwar shi yake ba, bayan KB ya iso nan ya saka Mama dasu Umma a gaba shi ma wallahi ayi masa mata a bauchi, yanzu fa shi kadai ne kawai baya da mata, wallahi zasu saka shi a gaba ne, Inna ta ce.
"Zo nan dan Albarka" dan kuwa jinin KB ya zo daya da Inna, kasancewar KB akwai barkwanci "ina dai mata kake so ko?" KB ya ce.
"Eh Innata, gaskiya nima mata nake so"
"Ma sha Allahu! Nayi maka mata, amma sai kayi hakuri da ita, dan ba jin magana take yi ba" dariya KB ya yi ya ce.
"To Inna wacece?" sai da Inna ta murguda baki ta ce.
"Na baka Ifritu" Zaidu dake zaune kamar ba ya wajan ya ce.
"Inna ki daina batawa ƙanwata suna"
"Yoo to ni ina ruwana da iskancin banza da wofi, jama'a ba zaku dinga saka sunan mutane ba sai na aljanu,kai kam ma naga take takenka, tun da aka saka lokacin aurenka naga kana min wani jiji da kai, ita dai Hafizatun bata fini a komai ba, kuma duk arziki duk tsiya nicevta farko ehe" yawancin yan uwa da ake zaune a wajan dariya ake yi, Zaid ya mike a hankali yabar wajan Inna ta ce "Kabeeru, ina dai ka karbi zabina ko?"
"Ahh sosai ma Inna na karba hannun bibbiyu" da haka shi ma ya tashi.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Yau ta kama alhamis gobe ne kuma za a daura aure, yau ana ta shirin zuwa Family and friends, Amarya Hafiza tasha kyau dan kuwa Ummi ce ta dauko mai gyaran jiki ta gyarata a kwana goman nan, yau ma kuma Ummin ce ta dauko mai makeup ta fentawa Hafiza fuska tasa kayanta golden color, kawayenta su Afnan kuma sun saka maroon, sunyi kyau sosai su ma, Tun da aka fara hidimar bikin Hafiza Ubaidullah da Abi'atu basu samu zama ba, basu nan basu can, har aka gama shiryawa aka tafi, ana ta neman su Ubaidullah da Abi'atu ba a gansu ba, sai bayan da duk jama'a ana can wajan taro, har an dibi awa daya tukunna ka ji wani kiɗa na musamman na tashi, yayinda maroƙi ke wasa Ubaidullah da Abi'atu, jama'a an zuba ido ana jira aga wasu taurari ne haka ake koɗasu, kamar daga sama sai gasu sun shigo su na dauke ido cikin shiga ta alfarma, farar shadda ce

1 Comments On COLONEL UBAIDULLAH
avatar
zainab-hassan

11 months ago

Reply

????

Please Login or Register in order to submit comment