Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya ji sauki kuma sai ayi shagalin biki, sai dare tukunna Safwan ya farfado kuma Alhamdulillah ya gane kowa, nan suka shiga hamdala su na godewa Ubangiji, da dare da suka koma gida bayan Ubaidullah ya yi wanka ya kwanta ya tuno dasu memories da lapton din da yasa aka kawosa gida dasu, kamar an zaburesa haka ya mike ya fito, yana fitowa itama tana fitowa,karo suka yi zata fadi ya riƙeta gami da jefo mata tambaya.
"Ina zakije?"
"Kitchen"
"Me za ki yi?'' haɗe rai tayi dan bata ga dalilin tambayar da yake mata ba, ganin ta hau turo masa baki ta ƙi basa amsa ya sa shi matseta ta yi yar kara tana harararsa.
"Au zasu tashi ne?"
Ya tambayeta yana kafeta da ido"
"Su wa?"
"Ƴan rashin kunyan mana, yanzu nayi maganinki" kwace jikinta ta yi tana cewa.
"Ai ban ga amfanin tambayarka bane" ta fada ta wuce kitchen, murmushi ya yi, ya fuskaci Abi'atu akwaita da gautsi, zama ya yi ya dauki lapton din ya bude ya hau bincike a ciki, fitowa ta yi daga kitchen din ganin system din a hannunsa yasata zuwa wajansa da sauri ta zauna, sai kuma ta fashe da kuka, da sauri ya kalleta ya ce.
"Lafiya?" cikin kuka ta ce.
"Na'ilah"
"Na'ilah,a ina?" bata tsaya basa amsa ba illa system din ta karba ta shiga in da ta ga samarin nan sun shiga, nan videos suka watso, zaro ido Ubaidullah ya yi, yana kallon tashin hankali, bincikawa Abi'atu ta ci gaba da yi har aka zo kan na margayiya, da sauri Ubaidullah ya karba yana gani, wasu zafafan hawaye ne suka wanke masa fuska ganin yadda ƙanwarsa ke neman taimako har wa innan azzaluman suka farmata, cikin gaggawa Ubaidullah ya dannawa Zaidu kira sannan ya ce ya duba email dinsa ya turo masa da sakonni, ko da Zaidu ya duba sai da ya yi danasanin meyasa ma ya kalla, kuka sosai Zaidu ke yi tamkar ba soja ba, Ubaidullah ya sake kiransa akan cewa, ina an kawo masu laifin barracks, Zaidu ya amsa da cewa ba a kawosu 9ja barracks ba, abacha barracks aka kai su, sai gobe za a shigo dasu 9ja barracks, Ubaidullah ya ce gobe idan jikin Safwan da sauki sosai zai bi jirgin yamma ya dawo abuja, da haka suka yi sallama da Zaidu, su na kiyasta kalar azaban da zasu gana musu kafin su kashesu, videos din ya turawa Zeey sannan ya kirata ya mata bayanin abun da zata yi, nan ta amsa masa cike da girmamawa, a ranar Ubaidullah bai rintsa ba, ko da washe gari da safe misalin karfe shaɗaya da rabi aka daura aure, kuma jikin Safwan din da sauki sosai, nan Ubaidullah ya musu sallama a asibitin gami da cewa zai wuce, Allah ya kiyaye hanya su Abba da Ummi da Safwan din da sauran wa inda suke wajan suka masa tare da fatan Allah ya ba shi sa'a, gida ya dawo dasu Mama, Hafiza da kuma matarsa Abi'atu, bayan ya gama shirinsa cikin kakinsa wa inda a ko da yaushe suke masa kyau, fitowa ya yi, a parlour ya sameta tana tsaye, cikin sanyin jiki ya zo gabanta ya kama hannunta ya ce.
"Zan wuce, kafin na tafi sai na tabbatar hukunci ta hau kan wa inda suka yi sanadiyyar ƙanwata da yaran jama'a, zamu tafi india kuma aiki ne mai hatsarin gaske, ban sani ba ko zan dawo ko bazan dawo ba, idan na mutu ki yafe m....." sauri toshe masa baki ta yi ta fashe da kuka ta rungumesa, dan murmushi ya yi, ya ce.
"My Abi'ah, ki jirani! Ki jira dawowata, zan ba ki mamaki" yana gama faɗi ya bata light kiss a gaba daya fuskarta, sannan yasa kai ya fice, ita kuma ta zube a wajan tana kuka dan ba zata iya jurar ganin tafiyarsa ba, dan ko ba komai fadan da sukeyi ba karamin sabo bane ya shiga tsakaninsu, kuma ko ba komai zaman da suka yi ta fara son mijinta, itama kuma ta ga alamun hakan a wajansa, addua ta hau masa tana durƙushe a wajan, ko da ya fito sallama ya yi da Mama da Hafiza, sannan ya ce, bai yarda su dinga fita ba, zai aiko musu sojoji mutum uku masu kula dasu, addua Mama ta yi masa da fatan alkhairi gami da ƙarfafa masa guiwa, ya yi murmushi ya amsa da ameen gami da yi mata godiya, da haka aka bude masa mota ya shige, basu tsaya ko ina ba sai airport, ko da suka isa mintinsa shabiyar jirginsu ya daga izuwa birnin tarayya, karfe huɗu dai-dai a barracks ta yi masa, ya yinda dubbannin sojoji aka zo tarban Ubaidullah abun har mamaki ya ba shi, da masu sara masa da masu miƙa masa hannu,shima ƙamewa ya yi yana sarawa manyansa, kafin daga bisani suka rungumi juna da aminansa, Zeey ce ta taho da murnarta tana sanye da kaki a jikinta murmushi ta yi masa sannan ta sara masa gami da cewa.
"Wlcm back Sir, Captain Ubaidullah Abdullahi" karo na farko da Zeey ta fara ganin dariyan Ubaidullah,dan kuwa dariya ya mata gami da cewa.
"Tnk u Zeey, a gaskiya ke din ta dabance,kuma kin zama ta musamman a wajana" itama dariyar ta yi ta ce.
"Kamar yadda kai ma kake na musamman awajan kowa ko? ya Madam? Fatan ka barota lafiya,dasu Mama da Ƙanwarmu Hafiza?"
"Duk su na lafiya Alhamdulillah"
"Ya mai jikin fatan yana samun lafiya?"
"Eh jikinsa da sauki sosai, dan yau ma aka daura aurensa, sabida dole akwai abun da zai bukata wanda dole sai muharramarsa ce zata iya yi masa hakan" jinjina kai suka yi, sannan Zeey ta kuma cewa.
"Ba a kawo masu laifin wannan barracks din ba fa, har yanzu su na Abacha Barracks, amma ka je ka huta, tun da ka iso, idan ka gama dasu, Rumaisa da mahaifinta da Ema duk su na kulle" girgiza kai Ubaidullah ya yi ya ce.
"No Zeey ban ga ta hutu ba, in dai wa innan azzuluman su na numfashi a doron duniya, bari naje na gana da General Of The Army, sannan na zo na wuce Abacha Barracks din" KB ya ce.
"Gaskiya kam, dan tun jiya nake cikin zaƙuwa a kawosu, jiya fa Zaidu kwana ya yi yana kuka, dama baka turo masa ba wallahi" Zeey ta girgiza kai cike da tausayawa ta ce.
"Ka je ku gama da General din, Captain, nima na gama aikin da ka sakani jiya" murmushi ya yi ya ce.
"Ina alfahari dake Zeey, just keep it up" itama murmushin ta yi sannan ta wuce.



Duk in da Ubaidullah ya ratsa sai an kallesa, masu sara masa su na sara masa, har ya isa office din General ba tare da bata lokaci ba, General Of The Army ya bawa Ubaidullah Umarnin shigowa, bayan Ubaidullah ya shigo ya sara masa suka gaisa, General ya sake ba shi hakuri, Ubaidullah ya nuna masa komai ya wuce sannan ya yi gyaran murya ya fara magana.
"Sir, akan yaran da aka kamasu da laifin aikata fyaɗe, gasu videos din b'arnan da suke aikatawa, daga cikin yaran da suka yiwa fyaɗe har da kanwata wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta har lahira, Sir! A ko da yaushe sai munji cases din fyaɗe sama da dari a garurruwa daban daban, Sir! Abun da yake daure min kai a matsayinmu na jami'an tsaro ban taba jin wanda aka kai shi kotu aka yanke masa hukunci, ko naji an hukunta masu aikata hakan ba, wanda zai zama izna ga masu aikatawa ko masu burin aikatawa dasu tsarota su hankaltu,dan masu iya magana su na cewa ana tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro, Sir! Ina neman alfarma, a barni na hukuntasu da hannuna ba tare da an kaisu kotu ba, dan naga alama akwai yaran masu kudi a cikinsu wanda suke da daurin gindin manyan ƴan ƙasa, hakika idan za a dinga zalunta bayin Allah marasa karfi sannan a danne musu hakkinsu, hakika duniya ba zata taba zama lafiya ba, dan yanzu an mai da ran muninai ba a bakin komai ba, taya ma duniya za a zauna lafiya bayan jinin bayin Allah da ake wanke kasa dasu sir? Lokaci ya yi da ya kamata ace an samu wani ci gaba a ƙasarmu ta nigeria, Sir! Dama nake so ka bani a karin farko, kafin muje yaƙin karbo yan matan ƙasata wanda aka yi garkuwa dasu" sosai General Of The Army yake kallon Ubaidullah, dan kuwa ba karamin burgesa Ubaidullah ya yi ba, a take ya ce.
"Captain Ubaidullah na baka go ahead, wish u oll the best" murmushi Ubaidullah ya yi, ya sarawa General Of The Army gami da cewa.
"Tnk u sir, Allah ya ɗaga ƙasata nigeria" sannan ya juya ya fice, yana fitowa suka hadu da Hanan, wani dadi ne ya ziyarci zuciyarta, da sauri tazo tana yi masa wlcm back, Ubaidullah ya amsa ba yabo ba fallasa, nan suka dan gaisa sama-sama, sannan suka yi sallama, wajan su Zaidu ya wuce nan suka shiga mota har da Zeey, Abacha Barracks suka wuce, sai da ya je suka gaisa da Major Usman, rungume Ubaidullah Major Usman ya yi, dan yana son Ubaidullah sosai, sannan Ubaidullah ya ce sun zo tafiya da masu laifi ne, nan Major Usman ya bada Umarni akawo su, su tafi dasu, hakan kuwa aka yi, tun akan hanya suke cin duka wajan Zaidu, har suka iso 9ja barracks, direct suka wuce guardroom dasu, inda suka rufesu da duka, tun su na ihu har suka kasa ihu, sai da suka musu lilis, kafin da kyar KB ya janye Ubaidullah da Zaidu, suka koma gefe suka zauna, Ubaidullah ne ya jawo kujera ya matso su sosai, sannan yasa aka kawo masa ruwa, nan KB ya sheƙa musu ruwan, wayar wuta Ubaidullah ya jawo, wanda daga gani kasan shocking zai jona musu ko ba a fada maka ba, a matukar galabaice wani ya ce.
"Yallabai! Dan Allah kayi mana rai, ka yafe mana, ba zamu sake ba, bamu san cewa kai din soja bane, da mun san cewa kai soja ne da bamu fara ɗau....." saukar naushi ne ya hanasa karasa maganar da yake yi, wanda Zaidu ne ya kai wannan naushin, a matukar tunzure zuciyarsa na ƙuna ya ce.
"Shut'up!!! Mutanen banza!! Allah yana arawa mugayen mutane irinku lokaci dan su aikata barna son ransu, kafin Allah ya dakatar daku a madakata, shin kusan wacece *NA'ILAH!!!!?* ita din Ƴa ce, ga tsohon *SOJA* wanda ya riƙe muƙamin Major kafin Allah ya ɗauki ransa a bakin aikinsa, sannan Ɗansa yake riƙe da mukamin Captain, *NA'ILAH! ƳA CE GA SOJA! ƘANWAR SOJA, MATAR SOJA!* amma ku ka yi sanadiyyar mutuwarta, tun da gaku yan iska ko!!! Shi ne ku ka kyetara ta gonawa kooo!!" ya faɗa gami da sa kafarsa mai dauke da boot army shoe ya take gaban ɗayansu ya saki ihun azaba, Ubaidullah ya jona musu shocking.





✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



*_SAKON BAN HAKURI GA MASOYANA 😪😪 A TAYANI DA ADDUA BUK YAZO GANGARA AMMA GAMAWA YA ZAMA AIKI, BUK DIN NAN ZAI KAMMALU NE A CIKIN SATIN NAN DA YARDAN ALLAH, AMMA DA TAIMAKONKU MASOYANA, TA HANYAR ZUBA MIN SHARHI WANDA ZAI SAKANI POSTING SAU UKU A RANA 😜🤪, INA KARA BAKU HAKURI, BARKANMU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEEN_* 👏🏻👏🏻👏🏻




MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*~UBAIDULLAHI~*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0
~~•~~•~~•~~•~~•
*Special gift to my 5 ☆stars★*
_Samira bint Abdallah_💋
_Fatima bintu Sagir_💋
_Farhat Mrs M'J_💋
_Princess (Nafeesat)_💋
_احلام فاطمة_💋

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*


🤔🤔🤔
*_OH ALLAH NA NI ZAHRA UWAR AHLAN, TUN BAN DAUKI MAGANAR DA WANI MAHIMMANCI BA DA ZANYI MAGANA AKAI, AMMA SAKON DA NA ISKE A PC DA KUMA KIRAN WAYA YA SA ZANYI MAGANA, AKAN PAGE DIN DA YA GABATA KAFIN WANNAN, WAI KAR NA KASHE UBAIDULLAH IDAN YA MUTU LABARI YA B'ACI, TO INA DA YAR TMBYA, "SHIN YA SUNAN BUK DIN NAN NE KAM? INA CE SUNAN SHI COLONEL UBAIDULLAH NE? KUMA HAR YANZU UBAIDULLAH YANA CAPTAIN NE BAI JE COLONEL BA, TO IDAN YA MUTU MA NI ZA A NAƊAWA COLONEL DIN? 🤔 ) DUK MA BA WANNAN BA, A RAYUWA BA KOMAI KAKESO YAKE ZUWA MAKA YADDA KAKESO BA, INA SO KU FAHIMCI HAKAN PLS, KAR MU DIN GA RAYUWA AKAN SON ABUN DA MUKE SO DAN ZA TA IYA KASANCEWA BA ALKHAIRI BANE, DA YAWA WASU BA WAI SU NA KARANTA NOVEL DAN SAKON DA YAKE CIKI BANE, WASU SU NA KARANTAWA NE DAN NISHADI KAWAI, PLS AND PLS, KAR MU DIN GA TAFIYA A NISHADI, A TAFIYA ANA SO A DIN GA WAIWAIYE( HAUSA CE) FATAN KUN FAHIMCENI, AHA MASOYANA MUJE DAI A CI GABA DA KAFTAWA_* 🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️



*page°°°°°101&105*




"Ubaidullahhhhhh!!!?" Zaidu ya furta da karfi ya dagosa yana jijjigasa cikin tashin hankali, da sauri shi ma KB yazo suka rungumi Ubaidullah su na ambatar sunansa cike da tashin hankali, cikin gaggawa sojojin india suka yo kan Ubaidullah, nan suka taimaka aka saka shi a mota sai asibiti ma fi kusa da Kashmeer, nan aka wuce emergency da Ubaidullah, faɗin halin da su Zaidu suke ciki abun baya misaltuwa, ko da suka sanar da barrack dinsu an harbi Ubaidullah nan barrack ta rikice, kafin kace me labari ya karaɗe barrack akan sojojin 9ja barrack sunyi nasara amma an harbi jarumi Ubaidullah.



Likitoci su na ta faman kokarinsu wajan ganin sun cuto rayuwar Ubaidullah in da babu bata lokaci suka shiga yi masa aiki dan cire masa bullet din da yake jikinsa, kasancewar kasashen waje sun fi kasarmu bada attention akan marasa lafiya, kusan kwana suka yi su na aiki akan Ubaidullah dan harbin da aka masa wajan gefen ƙirjinsa kiris ya rage bai wuce ya huɗa masa zuciyarsa ba Allah ya taimaka, amma da ace Zaffar ya sake harbinsa wajan saitin wajan ba ma kawa da ya mutu, bayan sun gama yi masa aiki ne suka saka shi a cormer dan kuwa yana cikin mawuyacin hali.



Satin Ubaidullah ɗaya a comer har yanzu bai san inda yake ba, dan ba fiddo shi aka yi ba, harta su Zaidu sai dai su hangosa ta glass, sosai yake samun kulawa wajan jami'ai da kuma hukumar sojojin india da na ƙasarsa nigeria, su ma su Zaidu sosai suke bawa Ubaidullah kulawa dan burinsu bai wuce su ga Ubaidullah ya samu lafiya ba.


@@@@



Da yawa mutanen nigeria sunji labarin cewa jaruman sojojin sun kwato yan matan da akayi garkuwa dasu, kuma da ake zantawa dasu sun fadi wanda ya fiddosu amma abun daurewar kai din shine ina *CAPTAIN UBAIDULLAH* din yake ? Dan kuwa ance kar a faɗi abun da ya same shi ya zama sirri har sai ya ji sauki tukunna.


A gida kuwa ganin labarai ya karaɗe yan mata sun dawo kasarsu da yawan sojojin ma sun dawo, daga ciki har da commender'n yaƙin amma babu Ubaidullah ba Zaidu ba KB, nan fa hankalinsu Mama ya tashi fiye da misali, nan suka din ga azalzalan yan barracks din su Ubaidullah inda a karshe Major Usman ya ce kawai a fadawa duniya gaskiya tun da Allah yasa Ubaidullah din bai mutu ba, nan kuwa aka yi kiran manema labarai inda Major Usman ya wakilci 9ja barracks da Abacha barracks ya yi jawabin akan mashahurin sojan nan wanda yake sadaukar da rayuwarsa wa kasarsa inda Major Usman yake cewa masoyan Ubaidullah su taya shi da Addua dan lokacin da ya kubutar da yan matan kwantenan karshe aka harbesa yanzu haka yana asibitin kasar india yana samun kulawa, a yankin kashmeer wajan kusa da inda suka yi yaƙin, kuma a halin yanzu yana cikin comer dan Allah masoya a taya shi da addua Allah ya tashi kafadunsa, domin ace an rasa mutane kamar su Ubaidullah ba karamin babbar asara aka yi ba, da haka jama'a suka gamsu yayinda kuma suke yiwa Ubaidullah fatan samun lafiya.



@@@@




Ko da Abi'atu ta ji labarin an harbi mijinta yana cikin comer a take ta zube kasa sumammiya, ruwa-ruwa aka yi da ita asibiti, ko da ta farka kuka ta din ga yi tana kiran sunan mijinta, kwananta uku aka sallamota, nan suka koma gida amma hankalinsu ba a kwance yake ba.


@@@@



Satin Ubaidullah biyu aka fito dashi daga comer inda ya farfado jikinsa da sauki amma da alama yasha wahala ya ji jiki, kwanarsa uku da fitowa ya fara shirin komawa kasarsa, kafin ya farka manyan sojojin nigeria duk sun zo duba shi, a daren ranar da zasu koma nigeria nan shugaban sojojin india yazo ya samu Ubaidullah da wani zancan, kallon marar hankali Ubaidullah ya masa kafin yayi wani murmushi mai wuyar fassara,ba wani abu bane illa su na so su siye Ubaidullah ya dawo kasarsu da zama ya shige cikin rundunarsu, dan sun yaba da jarumtarsa, ba yaudara ba boye-boye Ubaidullah ya ce.
"A yawan kasashe na duniya, dukkan dan ƙasa yana kaunar ƙasarsa,amma babu wanda suke nuna fiffiko akan kasarsu sama daku, kun mai da kasarku uwa kamar yadda kuke furtawa, babu abun da ba zaku iya yi ba akan kasarku sabida kishinta da kukeyi, nima hakan take a wajena, ina aikine wa ƙasata ba dan albashin da nake dauka ba, illa alƙawari da rantsuwan da nayi na kare ƙasata da dukkun baiwar da Allah ya bani, dabadin gumi na halak da nake ci ba, da sai na bar karban albashi, sabida son ƙasata da nake yi nima, *ALLAH YA ƊAGA NIGERIA!!*" Ubaidullah ya fada yana sarawa shugaban sojojin india, ba karamin sanyi jikinsa ya yi ba, haka ya tashi ya fita yabar Ubaidullah, ko dasu Zaidu suka tambayesa wani magana ne sukavyi da shugaban sojojin india dariya kawai Ubaidullah yabyi kafin ya basu labari, zare ido KB ya yi jin makuɗan kudin da zasu biya Ubaidullah, Zaidu ya ce.
"Su fa naga alama sun raine mutane wallahi" Ubaidullah ya ce.
"Manta dasu kawai" nan suka ci gaba da shirinsu, ko da washe gari da zasu baro india a motar asibiti aka kai Ubaidullah airport, su Zaidu ne suka taimaka masa lokacin da zasu shiga jirgi, an saka masa bandage a wuyarsa wanda aka rataye masa hannunsa, bayan sun zauna Ubaidullah ya lumshe ido yau yana cikin farin ciki marar misaltuwa zai je ya ga iyalansa wata kusan biyar kenan rabon shi dasu, su Zaidu ma haka murna suke yi.


@@@@



Sai dare su Ubaidullah suka sauka a airport din abuja, sojoji ne birjik aka zo tarbansu, da ɗima-ɗima motocin barrack, nan jama'a ake ta sarawa Ubaidullah masu mika masa hannu su na mika masu, Major Usman yana zuwa ya rungumesa Ubaidullah ya danyi kara kadan wanda Major Usman ne kawai ya ji, duk sun bi sun rame tamƙar basu ba tsantsar wahala da tashin hankali, nan aka shiga mota sai barrack, direct aka wuce da Ubaidullah part dinsa dan ya huta tun da baya da lafiya, bayan su Zaidu sun taimaka masa ya yi wanka ya fito yana dingisawa dan harta kafarsa na hagu a kumbure yake dan wajan faɗa akwai wanda ya buga masa ƙotan bindiga, zama ya yi a gefen gado ji yake kamar ya rufe ido ya gan shi a gida amma ba hali, muryan Zaidu ya ji yana tsokanarsa da cewa.
"Alhamdulilah mun tsallake teku da baya, dan mu kam ba zamu ce rijiya ba, wannan yaƙi da tashin hankali, wlh ban sa ran zan dawo a raye ba, gaskiya Malam ka dawo da matarka ta karasa jinyarka dan Madam ce kawai zata iya yi maka wasu abubuwan, amma mu kam ba zamu iya ba" harara Ubaidullah ya gallawa Zaidu duk da na wasa ne dan rabon da Zaidu ya masa irin wannan wasa tun Na'ilah na raye, ga shi baya jin dadi balle ya biye masa su dan capta, dan haka maganinsa yasha ya kwanta.



@@@@


Da washe gari bayan kananun sojojin sun zo sun yiwa Ubaidullah ya jiki, da misalin karfe biyu Major Usman ya zo shi ma, da sauri su Zaidu da KB suka miƙe su na sara masa, murmushi Major Usman ya yi ya kalli Ubaidullah, shi ma sara masa ya yi da gefen hannu da kyar ma yake iya motsa hannayen nasa, takardu Major Usman ya mika musu dukkansu, suka karba suka buɗe KB ne ya fara ihu da ya karanta, ya miƙe tsaye yana tsalle kamar karamin yaro, Zaidu ma haka murna ne ya cika shi, ticket Major Usman ya sake miƙa musu, nan Zaidu ya bude ya ga jirgin yamma na yau, bai san lokacin da ya kama kafar Major yana godiya ba, kallon Ubaidullah Zaidu ya yi ya ce.
"My Man gida zamu tafi yau an bamu hutun wata daya da iyalanmu, muje su ganmu" murmushi ne ya bayyana a fuskar Ubaidullah ya kalli Major Usman ya ce.
"Sir, nasan wannan dukka kokarinka ne,mun gode sosai"
"Haba dai, ku daina godiya,ni ina amfani da abun da ya kamata ne, shiyasa kuna dawowa jiya na samu General Of The Army muka tattauna da shi, kuma kai Ubaidullah kana bukatar kulawa, kunyi matukar kokari, dan haka ku koma gida ku huta, Ubaidullah zaka fi samun kulawa, In sha Allah a wata daya jikinka yayi kyau, sai ku dawo da iyalanku dan kuzo ayi liyafan karramaku" sosai suka din ga zuba masa godiya ba shiri suka mike suka hau tattara kaya, Zaid ne ya taimaka ya hadawa Ubaidullah na shi nan suka yi sallama da barracks aka wuce dasu airport, mintinsu talatin jirginsu ya daga izuwa bauchi, shi kuwa KB dan Kaduna ne dan haka suka yiwa KB sallama su suka wuce abun su.


Basu sauka da wuri ba sai wajan bakwai, tun kafin jirginsu ya sauka sojoji suka zo daukarsu, dan haka su na sauka sojoji suka sara musu sannan Zaidu ya ce zai raka Ubaidullah gida, amma sam Ubaidullah ya ƙi yace kawai ya wuce gida shi ma ya tabbata su Umma sunyi kewarsa su na son ganinsa, kawai su tafi idan yaso ya zo gobe, da haka suka yi sallama aka bude musu mota suka shiga Zaidu ya dagawa Ubaidullah hannu, shi kuma ya ɗaga masa kai, nan driver yaja su sai gida.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Kwance take a parlour akan 2sitter duk ta rame ta yi duhu itama, idonta a lumshe kamar mai jin bacci ta rufu da hijabinta, kamshin turaren da take kwana dashi ta tashi dashi, shine ya mata sallama wanda ya yi sanadiyyar zaburanta ta mike zaune, nan ta gansa tsaye a bakin kofar parlour wanda shi ma wa ita ya zubawa ido yana kallonta, murje idanunta ta yi ta rufe ta bude still dai ta ga ba gizo bane a hankali ta miƙe jiri na dibarta ga kyarman da jikinta ya ɗau lokaci guda, hannunsa daya Ubaidullah ya miƙa mata alamun tazo, a hankali take taku yayinda idanunta hawaye yake ambaliya har tazo gabansa tasa hannu ta shafi gefen fuskarsa, nan ta tabbatar da eh lallai shi ne, ihu ta saka tana kiran sunan Mama da Hafiza, dan dama a parlourn Maman take kwance, bata san lokacin da ta rungumesa da gefen da baya da rauni ba tana kuka mai tsuma zuciya, shi ma Ubaidullah din hawaye ne suka hau wanke masa fuska, Hafiza wacce take wanka ta ji Abi'atu na kwala kira haka bata gama wankan ba ta fito ta daura zani, ta saka hijabi, parlour ta fito ta tsaya turus ganin Yayanta, shima kallonta ya yi ya mika mata hannu da gudu tazo ta rungumesa gefe daya tana kuka itama, ɗaga kai Ubaidullah ya yi ya ga Mama tsaye kofar dakinta tana ta faman kuka, sake su Hafiza da Abi'atu Ubaidullah ya yi yaje gaban Mama yana kallonta yana murmushi tare da hawaye, bakin Mama na b'ari cikin raunin murya ta ce.
"Yaya Babba?" da sauri Ubaidullah ya rungumi mahaifiyarsa yana hawaye.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


A lallaba bani da chaji 😢




UMMU AHLAN TAKU CE👍🏻
[8/19, 10:59 AM] Zarahh:

1 Comments On COLONEL UBAIDULLAH
avatar
zainab-hassan

11 months ago

Reply

????

Please Login or Register in order to submit comment