Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗa min su waye mutum bakwai din ba, amma abu ɗaya na sani shine zan bazama neman mutum bakwai din nan na kashesu da hannuna duk da yanzu ni ba jami'i bane"

KB ya ce.
"Innalillahi wa inna ilayhirrajiun! Hakika wa inda suka aikata abun nan basu san su wa suka tab'o ba, basu san sun taba yar gidan soja kanwar soja wanda yake sa ran auranta soja ba, amma komai muyi hakuri mu kuma dage da addua Allah ba azzalumin bawansa bane sai dai bawa ya zalunci kansa amma zasu gane basu da wayo, ni dai abu ɗaya na sani shine duk rintsin rayuwa duk tsanani duk wuya muna tare da kai Ubaidullah"

Kuka suka saka a tare gami da rungumar Juna.

Sallama aka yi, wanda ya saka su sakin junansu suna share hawaye, Abba ya girgiza kai ya ce.
"Haba Ubaidullah, zaman gaisuwar kanwarka fa akeyi amma ka dawo ciki kana kuka kayi hakuri dan Allah mu dauki kaddara kowa lokaci yake jira Allah yasa Na'ila ta huta"
Suka amsa da ameen, kafin Abba ya saka su a gaba suka koma kofar gida ana karban gaisuwa amma kallo ɗaya zaka yiwa Ubaidullah shi da Zaidu ka fahimci kalar tsananin tashin hankali da damuwar da suke ciki.

Sai bayan sun fita ne KB ke sanar da Ubaidullah ai da Zeey suka taho nan KB ya basu labarin yanda sukayi da General Of The Army, girgiza kai Ubaidullah yayi gami da cewa.
"Dan Adam kenan, ba komai rayuwa ce, ta ishe kowa ishara, Hanan kuma Allah ya saka mata da alkhairi.

Tun da suka dawo daga maƙabarta basu koma cikin gidan ba,dan haka Ubaidullah bai san halin da Mama take ciki ba, sai da aka yi sallar la'asar tukunna suka shiga cikin gidan dan su gaisa da Zeey, nan Ubaidullah ya ga Mama tamƙar ba ita ba harta canza kamanni, nan hankalinsa ya sake tashi fiye da na da.

Hafiza ma haka ta koma bata um bata um um sai illa rungume pic dinsu da tayi a ƙirjinta duk wanda ya ganta sai ya zubar da hawayen tausayinta, harta Anty Ummu ta koma tausayin Hafiza.



Da dare kuwa ta shiga Kitchen dan ta dauko ruwa ma wata mata nan ta ci karo da tashin hankali.

ba komai bane illa girkin da suka fara shiryawa Yayansu babu wanda ya taba abinci yadda suka ajiye haka yake, da gudu da kuka ta fice tayi hanyar part dinsa.

Suna zaune jingum-jingum shi dasu Zaidu, sai ga Hafiza da Kuka kamar an wullota, tana zuwa ta faɗa jikinsa, ta ƙanƙame shi tana kuka mai mutukar tashin hankali.

Ɗauriya iya ɗauriya Ubaidullah ya ɗaure kafin ya ɗaga Hafiza daga jikinsa yana share mata hawaye yana girgiza mata kai alamun tayi shuru, tama kasa magana illa hannu da take masa nuni dashi akan zo, tashi kuwa yayi ta kamo hannunsa suka fice, sukayi cikin gida har izuwa kitchen, suna shiga suka samu Abi'atu a kitchen din tana kuka.


Nan Hafiza ta hau nunnunawa Yayansu abun da suka harhaɗa masa, dan kamar kurma haka Hafiza ta koma, Abi'atu ce tayi karfin halin fara magana.

"Haƙika da nasan alaƙata da kanwarka ba zata jima ba dana roƙi Allah bai haɗani da su ba, kwana ɗaya ne kawai yasa muka yi sabon da ko shekara biyu albarka, bansan me Ubangiji ya tanadar ba na haduwar mu dasu,amma ka gani duk wannan girkin sun shirya shi ne domin kai, ashe abincin da ba za aci ba kenan"


"Ƙannanka su na sonka tamƙar yadda kake son su, mun sha hira dasu shekaran jiya, jiya su na haɗa maka abinci har nazo na tayasu ashe duk aikin ban kwana muke yi da Na'ilah " ta karasa maganar da sabon kuka.

Duk da Ubaidullah baya jin dadi amma haka ya zauna ya dauki abincin da suka dafa masa ya hau ci yana kuka, nan itama Abi'atu da Hafiza suka hau tayasa ci su na kuka har suka ci wanda zasu iya ci, kafin Ubaidullah ya koma part dinsa.


Wannan family yadda suka ga rana haka suka ga dare, babu wanda ya rintsa Ubaidullah da Zaidu kwana sukayi su na sallah, Ubaidullah ma fita ya dinga roƙon Allah a cikin lamarinsa.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

A daddafe har aka samu akayi sadakar ukun Na'ila.

Babu laifi jikin Mama da sauki amma har yau bata magana, amma idan aka zo mata gaisuwa tana amsawa da kai.


Bayan jama'a an watse saura yan uwa na jiki wanda su na nan sai anyi adduar bakwai kafin su tafi su ma.


Bayan mutane an ragu Ubaidullah Zaidu KB Zeey nan suka shiga bincike da iyakacin basirar da Allah ya basu akan gano wa inda suka yiwa Na'ila fyaɗe, barin ma Zeey da take jami'ar bincike (CBI)




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


_DAN ALLAH MY PPL'S SU KARA HAKURI WLH INA BUSY NE SHIYASA BAKU SAMUN POSTING AKAN LOKACI NGD DA KULAWARKU A GARENI._



_GA MASU KORAFI AKAN MUTUWAR NA'ILAH KUYI HAKURI HAKA LABARIN YAZO KU DAINA GANIN LAIFINA FATAN ZAKU FAHIMCENI KU FAHIMCI INDA LABARIN YA DOSA NGD._

Nasan za a samu kuskure ayi hkr banyi editing ba.

COMMENTS


AND

SHARE


MOMYN AHLAN TA KU CE👍🏻
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*WALLAHI NA CI WUYA SAU BIYU INA TYPING YANA GOGEWA* 😰🥵



*page°°°°°51&55*


Babu kalar binciken dasu Ubaidullah ba su yi ba dan ganin sun gano wa inda suka aikata wannan danyen aikin,amma babu wani information da suka samu.


Da haka har aka yi sadakan bakwai din Na'ila sauran jama'a aka watse, amma babu wani hasken da suka samu, sosai Ubaidullah da Zaidu suka shiga damuwa akan hakan.


Zeey bincikenta ne ya kasu kashi biyu, ga wanda ta ke yi a barracks ta barosa ga kuma wannan, ita ma ta shiga damuwa, babban burinta ta taimaki Ubaidullah ya koma bakin aikinsa idan yaso bayan ya koma sai su dage da neman wa inda suka yi raped din kanwarsa ya hukuntasu da kakinsa.


Kwanar su Zaidu goma cif a bauchi su na gudanar da bincike kullum basu zama a gida, tun safe zasu fice ba zasu dawo ba sai dare, har wani rama Ubaidullah da Zaidu suka yi, saboda tsananin damuwa da tashin hankali.


A kwana goman nan kuwa da dare General Of The Army ya kirawo su Zaidu akan su dawo gobe idan kuma basu dawo ba, to a bakin aikin su.

Nan take Zaidu ya ce ba zai koma ba yabar aikin, sai da Ubaidullah ya yi da gaske kafin Zaidu ya amince zai koma a goben, a daren ranar ba su yi wani bacci ba.


Da washe gari Ubaidullah ya nemo driver ya ba shi mota ya mai dasu Zaidu Abuja, idan ya so sai ya dawo masa da motarsa.


Sosai Ubaidullah ya din ga yiwa Zeey godiya yana mata fatan alkhairi, murmushi kawai tayi ta ce.
"See u soon"

Da rashin fahimta ya kalleta, ta sake murmushi ta ce.
"A barracks nake nufi"

Girgiza kai kawai Ubaidulllah yayi sannan ya kalli Zaidu wanda ke tsaye har yanzu babu walwala a tattare dashi, kafaɗarsa Ubaidullah ya nausa cikin wasa, sai ga hawaye a idon Zaidu, da sauri Ubaidullah ya rungumesa shima ya fara hawaye, cikin dauriya Ubaidullah ya ce.

"Sai Hakuri sirkina, Allah ya kara mana hakuri, Na'ila ba zata dawo ba ,da ace zata dawo tun kafin mu kaita maƙabarta ta tashi ko dan saboda kukan da muka din ga mata , ta ri ga da ta tafi ta barmu da kewa, kana gani dai har yanzu Hafiza bata dawo dai-dai ba tun da har gobe bata magana, Mama ita ma gata-gata nan ne, yanzu idan ka bar aikinka abun zai yiwa iyayenmu yawa, ni na ajiye kai ma ka ajiye me aka yi kenan? Kayi hakuri duk inda ka ke na tabbata kai din masoyin kanwata ne na hakika, abu daya na sani shine bazan taba barin wannan abun ya tafi a banza ba, wa inda suka aikata min wannan abun ba su san waye ake kira da Ubaidullahi bane, amma zasu sani ranar da suka shiga hannuna."


"Za su yi nadama marar amfani a rayuwar su, dan duk randa nayi tozali dasu sunan su *GAWAWWAKI*."

Yana gama fadi ya saki Zaidu sannan suka rungumi juna da KB, Sosai Ubaidullah yake zuba musu godiya tare da adduar Allah ya barsu tare har abada.

Har cikin dakin Mama su Zaidu suka shiga mata Sallama.

Mama kasa hada ido tayi da Zaidu ,dan gani take kamar zata ga Na'ila a gefensa shima Zaidun hawayena tab a cikin idonsa, cikin rawar murya ya ce.

"Mama zamu koma bakin aiki, ki sa mana Albarka" duk dauriyar Mama sai da tayi hawaye ta ce.
"Allah ya muku albarka Zaidu Allah ya kai ku lafiya, Allah ya kara mana hakuri ka ji?" Zaidu ya jinjina kai, KB da Zeey ma Sallama suka mata, Mama ta musu godiya tana sa musu albarka, dan ba laifi yanzu Mama ta dan sake tana magana, duk kuma saboda Hafiza ne, duk ta zama wata iri da ita, wani lokacin ma idan tayi abu kamar mai matsalar kwakwalwa.


Ko da su Zeey suke yiwa Hafiza sallama da ido kawai take bin su dashi, kamar bata taba ganin su ba.


Har waje Ubaidullah ya rako su, a tare su ukun suka rungume juna cike da kewa da bakin ciki, suka shiga mota Ubaidullah yana ɗaga musu hannu har suka fita gate din gidan.


Su na fita ya koma part dinsa ya kwanta a parlour kan doguwar kujera yana tunanin da ya zame masa jiki kullum.


Mama kullum cikin addua take Allah ya sassauta mata, dan wani lokacin idan tana tunanin Na'ilah ganin abun take tamƙar ta saka film ne ya kare.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Ba su suka isa Abuja ba sai gefen magriba su na isowa Hanan ce farkon wacce ta fara taro su, tana tambayar su lafiyar Ubaidullah da kuma karin hakuri.


KB da Zeey ne kadai suka iya tsayawa bata amsa amma har yanzu Zaidu baya cikin hayyacinsa dan ji yake yanzu son Na'ilah yake sake shiga zuciyarsa, babu yadda ya iya dole ya yi hakuri ya roƙi Allah ya masa sassauci.



Sun yi waya da Ubaidullah sun isa lafiya, Allah huta gajiya Ubaidullah ya musu.


Zeey kuwa wa inda ta saka su din ga bibiyar Rumaisa da wani shiga da ficenta, direct ta wuce take tambayar su yayinda suke bata jawabi dalla-dalla.


Murmushin Nasara Zeey tayi ta ce.
"Rumaisa kin kusan ki shigo hannuna, dadin abun ma shi ciki ba a karyarsa idan tana nan dole ta bayyana idan kuma babu duk zamu gani, Captain ka kusan dawowa soon In sha Allahu" ta fada tana murmushi dan idan Zeey ta saka abu a gabanta sai ta ga karshensa.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Zaune suke su biyu a parlour sun yi jigum babu mai yiwa dan uwansa Magana, Ubaidullah ne ya yi sallama ya shigo amma Abi'atu ce kawai ta amsa, sab'anin Hafiza da ta bisa da ido.


Zama ya zo ya yi kusa da ita ya ce.
"Kanwata tashi mu fita muje mu ga gari ko? Kema ki zo muje" ya fada yana dan kallon gefen da Abi'atu take zaune.


Tashi tayi ba tare da tayi magana ba, ta shiga ɗaki domin ta ɗauko musu hijab din su, shi kuma Ubaidullah dakin Mama ya wuce ya same ta zaune a bakin gado, ga carbi a hannunta tana lazimi tana kallon kasan dakin.

A hankali Ubaidullah yayi sallama yazo ya duƙa a gaban mahaifiyarsa ya kamo hannunta ya ce.
"My Momma ki zo mu fita."

"Mu fita kuma? Muje ina.?"


"Momma mu dan fita shan iska ne kawai."

Murmushin yaƙe Mama tayi wanda yafi Kuka ciwo, ta lura Ubaidullah yana so ne ya kwantar musu da hankali ko da kuwa shi zai kasance cikin tashin hankali, ko ba komai Ubaidullah ɗana wanda kowace uwa zata yi fatan samunsa a matsayin ɗanta domin ya zama garkuwa ga familynsa.


" a'a Yaya Babba idan kuna so ku fita ne kawai kuje abun ku "

Shagwabe fuska Ubaidullah ya yi sai kace karamin yaro duk saboda Mama ta saki jiki ta zo su fita.

"Ni dai ni dai Mommana ki zo mu tafi kawai Hafiza da wannan yarinyar miye ma sunanta? Su na parlour har sun shirya dan Allah Momma karki ce a'a kizo mu fita yau kawai plssss!"

Riƙe baki Mama tayi ta dan dungure keyarsa ta ce.
"Kai Ubaidullah mai hali dai baya fasa halinsa wallahi, yanzu ƴar tawa ce baka ma san sunanta ba? Ai da a gabanta ka faɗa da naji kunya, to sunanta *ABI'ATU* saura kuma ka ce ka manta, duk irin kokarin da take yi a gidan nan kace baka san sunanta ba, kullum fa anan gidan take wuni tare da Hafiza."


Dan tabe baki Ubaidullah ya yi, ya mike tsaye ya ce.
"To Mama bazan manta ba ki fito muje" yana gama fadi ya fice daga dakin ya koma parlour ya same su duk sun saka hijab su na zaman jiransa.


Fitowarsa da mintu biyu Mama ta fito itama nan suka yi waje, Ubaidullah ya kira mai gadi ya shaida masa zasu fita.

Abi'atu ta bude bayan mota zata shiga Mama ta dakatar da ita da cewa.
"A'a ƴata ki shiga gaba da Yayan ku ni da Hafiza zamu zauna a baya" ba dan Abi'atu ta so ba tayi abun da Mama ta ce dan ta lura Ubaidullah din nan dan rainin wayo ne.

Shi ma Ubaidullah din wani kallo ya aika mata da gefen ido ta tabe baki.


Mama kuwa burin da yake ranta shi ne Ubaidullah ya auri Abi'atu dan duk wanda ya samu Abi'atu a matsayin sirka yayi sa'a.

Ita kuma Abi'atu a rayuwarta ta tsani mutum mai fadin rai da daure fuska sai kace wanda ake masa wahayi da mutuwa kullum, duk da yanzu mutuwar aka yi musu, amma tun can da daga ganinsa haka yake.

Shi kuma Ubaidullah a nasa ban garen, ya tsani yarinya karama da iyayin tsiya dan a ɗan zaman da suka yi ya fahimci kamar tana da iyayi, dan shi kallon yar shekara sha uku yake mata, Abi'atu kuwa shakararta 19 ne ,kawai karamin jiki gareta sosai.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


👯🏻‍♀️👯🏻‍♀️👯🏻‍♀️
_KUNAAAA INAAAA NEEEE 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ MASOYANA NA HAKIKA WANDA SUKE SONA DA ZUCIYARSU BA DA BAKIN SU BA 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ MAZA-MAZA KU HANZARTO KU GARZAYO KU NUNA MIN KAUNA, A WANNAN KARON ZAN TANTANCE MASU SONA DA GASKIYA DA KUMA SON LITATTAFAINA, GA WATA SABUWA MAI TAKEN *ITA CE ZUCIYATA* DAN ALLAH KARKU BANI KUNYA KU NUNA MIN KAUNA TA HANYAR SIYAN WANNAN BUK DIN NAWA KU MIN KARA, AKAN FARASHI MAI SAUKI #200 HAKIKA WANNAN KARON ZAN FAHIMCI MASU SO NA DA GASKIYA 👯🏻‍♀️👯🏻‍♀️ KARKU MANCE NICE DAI TAKU UWAR AHLAN DA NA KAWO MUKU FITATTUN BUKS DINA KAMAR *GUDU A JEJI* DA KUMA *SHUHADA* GA KUMA WANDA KUKE KAUNA INA KAN TYPA MUKU SHI *COLONEL UBAIDULLAH* MASOYANA KARKU BANI KUNYA 🗣️🗣️🗣️ GA MAI BUKATA SAI YA TUNTUBENI TA NUMB WAYATA KAMAR HAKA 08165550116 MOMYN AHLAN KIRA KO WHATSAPP, SAI NA JIKI MASOYA NA HAKIKA👯🏻‍♀️



Comments

&


Share



MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*


*KYAUTAR PAGE GAREKU, MY DOTER MA'EESHART AND MMN SON FADEELARH, WITH ANTYN AHLAN BLOODY SISMIETA INA YINKU SIS'S*💗

INSHA ALLAH MY COLONEL UBAIDULLAH FANS ZAKU JI SUNAN KU A PAGE NA GAMA IDAN NA SAMU NATSUWA KOMAI YA DAIDAITA MIN,
KYAUTA CE GARE KU MASOYANA INAYINKU DAMA SAURAN WASU GRPS DIN.😘

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*page°°°°°56&60*


Buɗe gaban motar tayi ta shiga ta dauke kanta ta juya masa ƙeya tana kallon window mota.

Ubaidullah ji ya yi kamar ya dungure ƙeyar tata amma sai ya fuske ya ja motar suka bar gidan.


Wajan shakawata ya kai su yana riƙe da hannun Hafiza yana nunnuna mata abubuwa, wani lokaci kuma ya tambayeta kina son wannan, amma sai dai kawai ta kallesa, dan fitar da suka yin ma sake tuna mata da yar uwarta ya yi, tun da yawancin fita irin haka tare suke yi.



Yawo sosai Ubaidullah yake yi da Mama da Hafiza Abi'atu, sai wajan karfe uku ya wuce dasu gidan Anty Ummu.


Sosai Anty Ummu taji dadin ganin su sai murna take yi, Mama da Anty Ummu sun sha hira sosai yayinda Mama take faɗawa Ummu ƙudirinta na son haɗa Ubaidullah da Abi'atu aure, nan take Anty Ummu ta bada goyon bayanta ɗari bisa ɗari dan kuwa itama ta yaba da hankalin Abi'atu.


Sai bayan la'asar suka baro gidan Anty Ummu daga nan suka wuce gidan su Umma( gidan su Zaidu) sosai Umma taji dadin ganin su Mama, nan aka gaisa aka sake yiwa juna ta'aziyya.

Abi'atu Hafiza Afnan Manal suka koma gefe su na dan taba hira wanda hiran Afnan da Manal sai Abi'atu dake jefa baki sama-sama amma ban da Hafiza.

Inna ta ce.
"Yauwa yarinyar nan, shekaran jiya dana kunna radio naji labarin mutuwar Na'ila a DUNIYAR MAMAKI RADIO, kuma naji muryar mai gabatarwar kamar ke?" Inna ta faɗa tana kallon Abi'atu.

Abi'atu ta buɗe baki zata yi magana bata kai ga yi ba, kamar daga sama taji muryan Ubaidullah yana faɗin.

"What! Labarin mutuwar kanwata a duniyar mamaki radio? Taya hakan zata kasance tun da ni dai ban yi hira da yan gidan radio ba?"


Abi'atu ta ce.
"Ni ce na kai kuma nayi magana akai, sannan nayi dogon rubutu akan fyaɗe, wanda ranar alhamis jaridar zata fito idan Allah ya kaimu, yan jarida zasu zo domin su tattauna da Mama da kuma kai, sannan...." maganar da Abi'atu bata karasa ba kenan Ubaidullah ya katseta da kakkausar murya.

Ya kalli Mama ya ce.
"Mama tashi mu tafi gida, Umma Inna sai an jiman ku, Hafiza ta so mu tafi" ya fada yana kama hannun Hafiza, itama Abi'atu tashi tayi jikinta duk ba kwari.

Su na fita Inna tayi tsaki gami da cewa.
"Iskancin banza kawai, ba ga irinta ba halin nasu, wai soja, soja ko mala'ikun duniya, dan Allah ki gani fa yarinya tana jawabi cike da natsuwa da ladabi amma ya katseta da kakkausar murya, ya figi hannun Hafizatu kamar wanda yake shirin zuwa sama jannati wai su tafi, yaro kullum fuska sai kace hadiri haba" nan Inna ta dasa mita tana yi tana karawa, ita dai Umma bata ce komai ba.



@@@@@@


Ubaidullah bai tsaya a ko ina ba sai a gate din gidan'su ,su na isowa ana kiran sallar magriba, dan haka ya yi masallaci su kuma suka shiga gida.


Mama tana dakinta Abi'atu da Hafiza su na zaune a daki sai ga Ubaidullah ya shigo ransa a b'ace ya damƙi hannun Abi'atu yayi hanyar fita da ita.

Tana so tayi magana amma bata so Mama taji kuma ta fito ta ga Ubaidullah ya riƙo hannunta, dan haka tayi shuru sai da suka fito daga parlour ta fara magana.


"Malam! Lafiya kuwa? Ina zaka kaini? Me nayi maka zaka min irin wannan rikon? Karka karyani mana ka sake min hannu" ko sauraronta bai yi ba ya yi hanyar part dinsa da ita.

Bai tsaya ba sai da suka shiga parlourn'sa ya cillata kan kujera yana kallonta yana huci.

"Akan me zaki kai labarin mutuwar kanwata gidan radio?" a masifance yake maganar.

Miƙewa tsaye Abi'atu tayi ta ce.
"To miye aibu? Dan na kai labarin mutuwar Na'ila radion mamaki? Naga kai soja ne, a sojan ma Captain na tabbata ba zaka taba barin wa inda suka kashe Na'ila ba, ni na kai labarin ne saboda idan ka kama su kayi musu hukunci ya zama izna ga yan baya masu sha'awar aikata hakan da su hankaltu, dan hausawa sun ce ana tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro, to miye laifina dan na kai labarin gidan radio? Eh tabbas nayi dogon rubutu akai wanda ranar alhamis zai fito kuma ma ai..."

"Pls malama! Ya isheki haka! Ni na faɗa miki cewa ni soja ne yanzu? Duk ba bukatar kiyi haka sai ki nemi izinina, wai shin ma miye sunanki wacece ke?"

Ran Abi'atu ba karamin sosuwa yayi ba da maganganun Ubaidullah.


"Sunana Abi'atu Abdul'Maleek shehu journalist, ni yar jarida ce kuma ni writer ce a gidan radio ina rubuta abubuwan da suka shafi mata."

Da mamaki Ubaidullah ke binta da ido, a ransa yake cewa.
"Wannan yarinyar ce yar jarida kuma har da rubuta abun da ya shafi mata wannan yar abun?" yake tambayar kansa amma a fili ya ce.

"Duk wannan ba damuwata bane, kuma karki kuskura wasu su zo mana gida da sunan wai yan jarida sun zo yi mana tambayoyi bamu da bukatar haka" nan ya gaggaya mata maganganu.

Kwalla ne ya cika a idonta ta kallesa bakinta na bari ta ce.
"Nakan yi shige-shige dan ganin na binciko wasu abubuwa dan na yi rubutu akai a samu mafita, bansan cewa nayi shishshigi bane, kayi hakuri idan ka sake ganina a gidan ku na yarda kayi min duk abun da ka gadama" tana gama fadi ta fice da gudu.


Duk wannan draman da suke yi Hafiza tana tsaye a bakin kofa tana jin su, har san da Abi'atu ta fice da kuka.

Rimtse ido Ubaidullah yayi wani bangare na zuciyarsa bai ji dadin kuma yanda ya mata ba.


Yana tsaye hannunsa ɗaya a kugunsa daya kuma a fuskarsa ya ji sautin muryan da yau kusan kwana nawa bai jita ba, a hankali ta furta.

"Yayana"

Da sauri Ubaidullah ya juyo yana kallonta da sauri yazo ya rungumeta yana hawaye ya dago fuskarta ya ce.

"Kanwata ke ce? Ke ce kikayi magana? Faɗa min?"

Jinjina kai Hafiza tayi ta ce.
"Yaya baka kyauta ba abun da kayiwa Anty Abi'atu, shin kasan kalar kokarin da take yi kuwa, wajan taya ka gano wa inda suka kashe min sismieta? Ita da Yaya Safwan kullum su na fadi tashi ,su na iyakar kokarin'su, Yaya, Anty Abi'atu tana da matukar kirki fiye da tunaninka bata da matsala ko kadan, ya kamata ka bata hakuri akan abun da ka mata."


Ubaidullah ya ce.
"Kina so na bata hakuri?" Hafiza ta gyaɗa kai alamun eh, ya ce.
"To shikenan idan tazo gobe zan bata hakuri kin ji?" Hafiza ta sake gyaɗa masa kai sannan suka fito a tare suka shiga dakin Mama.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Da sallama ta shiga parlourn gidan su Abba da Ummi su na zaune duk da fuskarta babu walwala amma sai da ta danyi fara'a tazo kusa da Ummi ta zauna, kafin ta gaishe da iyayenta, suka amsa Abba ya kara da cewa.


"Ah ai na dauka zamu bi ki da kayanki ne ai yau kusan kwana uku ina tambaya kina ina wai kina gidan'su Mama" dan murmushi tayi ta ce.

"Haba dai Abbana gani na dawo ai" Ummi ta ce.
"Ya jikin Mama da Hafizan?"

"Alhamdulillah Mama da sauki, itama Hafizan Alhamdulillah amma har yanzu bata magana"

"Allah sarki! Zata ware a hankali Allah ya basu lafiya" cewar Ummi suka amsa da ameen, Yaya Safwan ya yi sallama ya shigo ya ce.
"Ah journalist yau an dawo kenan" hararan wasa ta masa sannan ta miƙe ta shige ɗakinta bata kula Yayan nata ba, kwanciya tayi tana tunanin maganganun Ubaidullah, sake rimtse ido tayi ,ta dauko wayarta ta shiga wajan video nan ta ci karo da videon Na'ila, kukanta tasha kafin ta tashi tayi sallar isha'i ta kwanta.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Da washe gari Ubaidullah ya yi shirin faɗawa mahaifiyarsa cewa yabar aiki.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



*DA BABU GWARA BA DADI, KU LALLABA DA WANNAN KARKU ZAUNA SHURU PLS WLH YANZU BANI DA LOKACIN TYPING BUK BIYU, BAZAN IYA CE MUKU GA LOKACIN DA ZAKU DINGA SAMUN UPDATE BA, SABODA SABON BUK DIN DA NAKE TYPING, FATAN ZAKU FAHIMCENI, NGD*



GA MASU BUKATAR SABON NOVEL DINA NA KUDI MAI TAKEN SUNA *_ITA CE ZUCIYATA_* SAI KU NEME NI TA NUMB TA KAMAR HAKA, 08165550116 KIRA KO WHATSAPP NGD.



COMMENTS AN SHARE.


MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻,
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we

1 Comments On COLONEL UBAIDULLAH
avatar
zainab-hassan

11 months ago

Reply

????

Please Login or Register in order to submit comment