Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya suka amsa da cewar sun amince da wannan shawara. Ba tare da ɓata wani lokaci ba aljani Durfus ya suri tsafaffen keji sannan ya buɗe fukafukansa ya yi sama. Cikin daƙiƙu kaɗan ya ƙule a cikin sararin samaniya.
Aljani Durfus bai iso fadar tsafinsa ba sai bayan yayi tafiyar sa'a bakwai sannan ya sauko ƙasa ya dira a wani baƙin daji mai dogayen tsaunuka da
dogayen bishiyoyi. A gaban wata mitsitsiyar bishiya ya dira, a jikinta akwai wani mitsitsin rami wanda saboda ƙanƙantarsa ko allura aka zura a ciki ba za ta shige ba. Nan take Boka Durfus ya shafi tsafaffen keji, da shi da kejin da mutanen dake cikin kejin duk suka zama siriririn farin hayaƙi. Hayaƙin ya dinga shiga cikin wannan mitsitsin rami na bishiyar har ya ƙule gaba đaya. Ba zato ba tsammani sai su Samaratu suka tsinci kansu a cikin wata tangamemiyar fada wadda aka ginata da zunzurutun đanyen gwal. Ko ina ka duba abubuwan al'ajabi ne iri-iri birjik ba
adadi. Boka Sulbaini ya ƙarewa fadar kallo tsaf ya tuna tasa fadarsa wacce ya ke taƙama da ya ga cewa wannan fadar ta ninka tasa sau arba'in a komai don haka sai ya sallamawa Durfus. Cikin alamun karayar zuciya ya dubi Durfus yace "Ya kai Durfus haƙiƙa yanzu na tabbatar da cewa ka taka babban matsayi a harkar tsafi. Ko da yake ban yi mamaki ba domin ai dama almajiri na iya fin malaminsa wata rana."
Yayin da ya ji wannan batu na tsohon
maigidansa sai ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Ya shugabana ai kun yi sake đan zaki ya girma. Koda yake dole ne na girmamaka a matsayinka na ubangidana na da shi ya sa ma na yi kiranka shugabana domin sai ɗan halak ke tuna alheri. Haƙiƙa na ƙaru
sosai da kai to amma fa abin da na sani a hallarar tsafi ba ka san kaso ɗaya daga goman sa ba."
Ba tare da ƙara cewa komai ba sai ya ɗebo waɗansu garin hoda kala uku ja, fari da shuɗi ya zuba su a cikin wani kasko sannan ya ɗebo wani tafasasshen ruwa ya zuba a ciki. Nan take wannan gari kala uku ya cakuɗa kansa ya rikiɗe ya zama tiriri. Shi kuwa tiririn sai ya lulluɓe wannan tsafaffen keji wanda su Markahul Sabus ke ciki. Kawai sai kejin ya narke ya zagwanye ya ɓace ɓat.
Tiririn ya sake lulluɓe jikin su Markahul Sabus waɗanda sun kasance yan ƙanana mini-mini. Kawai sai kowannensu ya dawo izuwa ainihin siffarsa,cikin tsananin farin ciki suka gurfanar da kansu gaban Alhaji Durfus kuma cikin haɗin baki suka ce "Mun sallamaka maka ya shugabanmu. Bamu da abin yi face bin umarninka, yanzu menene abin yi?"
Aljani Durfus ya ƙyalƙyale da dariyar mugunta sannan ya haɗe fuska yace, "Kamar yadda na faɗa muku a baya dole ne mu haɗa kanmu idan muna son mu sami nasara akan Shamharu. Abu na farko dole ne mu dawo kan batun mallakar littafin KUNDIN TSATSUBA na biyu wanda ke tare da Rafkanagu. Kun sani cewa ba zamu mallakeshi ba har sai mun mallaki abubuwan nan uku wato Tsumin Dodo Kirayanu, aljani Rafkanagu da kuma makamin farko wanda aka ƙera a duniya wato tsafaffiyar adda ce dake ajiye a fadar boka SHAMHARU wacce ke can tsibirin Bahar Zus. Amfanin aljani Rafkanagu a wajenmu shine mu tsafeshi ya je da kansa ya sato mana wannan adda to amma fa bincikena ya nuna min ccwa yanzu ba zamu iya mallakar aljani Rafkanagu ba, domin shirinsa ya fi namu. Aljani ɗaya ne rak a duniyar nan wanda zai iya zuwa fadar SHAMHARU ya sato mana wannan adda. Ba wani bane face aljani Balbus Sarkin ɓarayin aljanu. Shi kuwa Balbus yana zaune a can wani jeji da ake kira Zarwal a ƙarshen birnin Hindu. Tabbas zai iya zuwa tsibirin Bahar Zus a cikin kwana arba'in kuma zai iya shiga tsibirin Bahar Zus a cikin kwana arba'in kuma zai iya shiga cikin fadar SHAMHARU ya sato wannan adda. To amma fa ku sani ƙarfi ko tsafinmu ba zai iya tilasta Balbus ba akan ya yi mana wannan aiki face mun yi masa alƙawarin wani abu guda đaya wanda ya gagareshi mallaka shekara shekaru. Wannan abu ba komai ba ne face wani kambu dake jikin hannun Sarki Lu'umanu na birnin Teheren. Balbus ya san cewa idan ya mallaki wannan kambu zai iya sace gaba dayan dukiyar sarakunan duniyar nan ya ɓoyeta a wajensa ya zamana babu wani attajiri kamar sa. Yayin da Durfus ya zo nan a zancensa sai Markahul Sabus ya
daka masa harara yace, "amma ka ɓata rawarka da tsalle. Haƙiƙa baka san waye sarki Lu'umanu ba, shi yasa kake zaton zaka iya mallakar kambun."
Durfus ya ce dakata ai nasan ba zan iya mallakar kambun tsafinsa ba, amma kuma ai zan iya yaudarar Balbus ya gamsu cewa zan iya ɗin, indai buƙatar mu ta biya ai shike nan tunda munfi ƙarfin kowa a sannan babu yadda Balbus ɗin zai yi da mu yi shirin kwana biyu sannan mu tafi jejin zarwal domin ganawa da aljani Balbus, kar ku sami damuwar komai, ni ina tabbatar da cewa zamu samu nasara akan sa." Wannan shine abin da faru tsakanin aljani Durfus da su aljani Markahul Sabus bayan ya kuɓutar da su daga cikin tsafaffen kejin aljani Rafkanagu.
(Matsalar page,yazo a blank amma dai zan iya summarizing nasa).

*****************************************

A can fadar sarki Dujalu kuwa,bayan kuyanga ta kawo shayi an zubawa kowa ya sha,sai Ruziyal da boka Hajarul makurus suka yi gyatsa tamkar waɗanda suka ci nama suka ƙoshi.
Boka Hajarul makurus ya dubi sarki Dujalu yace,
"Ya kai wannan sarki mai tarin hikima,kayi sani cewa haƙiƙa yanzu ma mun sake jijjige gajiyar da take jikinmu,kuma babu yunwa ko ƙishirwa a tare da mu ko kaɗan.
Don haka sai ka fara bamu labarin/hikaya ta uku mu ji abin al'ajabin dake cikin ta."
Sarki Dujalu yayi murmushi sannan ya dubi tsoho Rafkangu,shima tsoho Rafkangu sai ya girgiza kai alamun ya gamsu da shayin da ya sha yace,
"Tabbas nima na ji abinda sauran 'yan uwana suka ji a jikin su."
Sarki Dujalu yayi gyaran murya sannan yace,
"To sai ku kimtsa, kai mai rubutu ka aza alƙalamin ka akan takarda domin wannan hikayar da zan baku na ɗauke da matukar abubuwan jarumta,tausayi da kuma ban al-ajabi.
Ni kai na ko tunowa nayi da labarin sai
nayi kuka.
Hikaya ce ta wani kyakykyawan saurayi kuma jarumi wanda ake kira NAZMIR bin HALUFA da gimbiya LUZAIYA 'yar sarki FAHALUL BAHAFUS.

Anan zamu dakata, sai wani karon idan Allah ya kaimu.
Fatan alheri.Matsatsubi 1
Typing:-Ahmad Munir Muhammad
Posting:-Ahmad Munir Muhammad
Part I

A baya mun tsaya inda:-
Hikaya ce ta wani kyakykyawan saurayi kuma jarumi wanda ake kira NAZMIR bin HALUFA da gimbiya LUZAIYA 'yar sarki FAHALUL BAHAFUS.

*****************
A wani zamani can mai tsawo da ya
shuɗe anyi wata babbar ƙasa wadda
ake kira DUHAMUL.
Wannan ƙasa ta bunƙasa a girma,arziƙi da kuma ƙarfin mayaƙa.
A bisa wannan dalili ne ƙasar DUHAMUL ta shahara kuma ta zama
Gagarabadau a cikin dukkanin ƙasashen kewayenta.
Ya zamana ana matuƙar tsoranta.
Sarkin da ke mulkin a wannan ƙasa ta
Duhamul wani azzalumin sarki ne ana
kiransa Bashakur.
Sarki bashakur ba tsoho bane kuma
ba yaro bane domin shekarunsa ba zasu gaza arba'in da huɗu ba zuwa
da biyar.
Saboda zalunci irin na bashakur ko a cikin garin nasa indai mutum bai shafi jinin sarauta ba ko kuma bai zamo ɗaya daga cikin attajirai ba to yana cikin tashin hankali,domin ba ka da 'yancin kan ka.
Dukiyarka da matanka zasu iya zama na sarki a koda yaushe.
Haka kuma ana ɗorawa talakawa haraji mai yawa ta yadda ko kaɗan basa morar arziƙin su baya ga wannan idan sarki bashakur ya bushi iska sai ya tura mayaƙa izuwa wata ƙasar ya basu izinin murƙushe ƙasar a kamo masa bayi kuma a ɗebo dukiya mai yawa.
Bisa wannan halayya ne ya tara dukiya
mai tsananin yawa wacce shi kansa bai san abin da zai yi da ita ba.
A wannan zamanin na sarki Bashakur tsafi bai shahara ba a cikin al'umma. Babu abinda ke tasiri face ƙarfin damtse da ƙarfin yaƙi.
Sarkin yaƙin wannan birnin na Duhamul wani tsoho ne ɗan kimanin shekara saba'in da shida wanda yayi suna a duniya saboda tsagwaran jarumtarsa da kuma iya yaƙinsa. A tarihin rayuwarsa bai taɓa jagorantar yaƙi an rasa nasara ba.
Ana kiran sa da suna HALUFA.
Da yake Allah ya kan yi mutane iri-iri kowa da hali dabam. Halufa ya kasance mutum mai tausayi da taimakon talakawa. Duk irin zaluncin da sarki Bashakur ke yi ba'a son ransa ba ne. Duk da kasancewar Halufa sadauki, kuma babban mayaƙi bai son ya ga ana cin zali, sau tari idan ya je yaƙi gari sai ya nemi sulhu da sarkin garin akan ya miƙa wuya ta lallami don bai son zubar da jini face bisa dole. Wannan halaiya ta Halufa na matuƙar baƙanta ran sarki Bashakur domin akwai wani lokaci kamar shekaru ashirin baya, wata ƙasa mai nisa bisa izinin ya yanko kan sarkin da na duk 'yan majalisarsa sai ya ƙi zartar da hakan. Kawai sai ya kamo su ya zo da su a ɗaure kuma ya kai su kurkuku a cikin dare.
Yayin da sarki Bashakur ya sami wannan labari sai ransa ya ɓaci, ya harzuƙa ainun. A daren ya tura aka kirawo Halufa ya rufe shi da faɗa,sannan ya ce da shi lallai ya je ya fito da wannan sarki da jama'arsa ya sare musu kawuna kuma ya kawo masa kawunan yanzu. Cikin matuƙar damuwa yabi umarni ya tafi izuwa wannan kurkukun. Halufa ya tafi yana mai saƙe-saƙen zuci har ya sami dabara.
Kafin ya ƙarasa kurkukun sai ya sauya kamanni yayi wata irin shiga ta baƙaƙen kaya ya naɗe fuskarsa
da rawani in banda ƙwayar idanunsa ba'a ganin komai ba. Kawai sai ya zare takobi da isarsa kurkukun ya hau masu gadi da sara. Duk da cewar yawan masu gadin ya haura dubu sai da ya tarwatsa su da ƙarfin tsiya ya ɓalle ƙofar ɗakin da aka sanya wannan sarki da jama'arsa ya fito da su sannan ya nuna musu wata ɓarauniyar hanya ya ce su gudu.
Sarkin da jama'arsa suka waigo suka dube shi cikin tsananin mamaki sai shi sarkin yace, "kai kuwa wane ne kai? Mene ne dalilin da yasa ka kuɓutar da mu?"
Halufa ya cire rawanin fuskarsa suka yi arba dashi sai mamaki ya daɗa turnuƙe su. Ai kaine wanda ka je har cikin ƙasarmu ka cimu da yaƙi,kuma ka kamo mu da ƙarfin tsiya, to ya kuma yanzu ka kuɓutar da mu?"
Halufa ya yi murmushi ga wannan sarki yace, ''Abin da ya sa na kuɓutar da ku shi ne bana son zaluncin da sarkina ke aiwatarwa. Ku yi sani cewa sarkina ya umarce nine da in je ƙasarku na murƙushe mulkinku kuma na yanko kawunan ku ba dan komai ba sai don bakwa yin biyayya ga umarninsa na haraji mai yawa duk shekara. Ni kuma da naje gareku sai na ƙi kashe ku na kamo ku nazo da ku aka kai ku kurkuku.
Koda labari ya riski sarkina sai ya tura aka kirani ya rufe ni da faɗa kuma ya ce lallai yanzu a daren nan na zo na yanke kawunanku na kai masa.
Maimakon na yi hakan ne na yanke hukuncin kuɓutar da ku. Yakai wannan sarki ka yi sani cewa ban kuɓutar da kai don komai ba sai don naga kana da wata 'ya ƙarama kyakykyawar gaske wadda kake matuƙar so itama kuma na fuskanci ta shaƙu da kai don haka ba zan so na zama sanadin raba wannan
soyayya ba ta ɗa da mahaifi domin nima ina da ɗa wanda nake matuƙar
so fiye da komai a rayuwata.
Ba zan so a ce ya zama maraya tun
yana ƙarami ba."
koda Halufa yazo nan a zancensa sai
ƙaunarsa ta mamaye zuciyar wannan
sarki da jama'arsa.
Dukkaninsu basu san sa'adda idanunsu ya ciko da ƙwallah ba.
Nan take suka yiwa halufa godiya sannan suka yi bankwana dashi.
Halufa ya kamo musu dawakai suka
haye suka kama gabansu.
Tafiyarsu keda wuya yayi sauri ya
sauya kayan jknsa sannan yayi wa
kansa raunuka a jiki ya koma gidan
sarki.
Koda sarki bashakur yaga jini na zuba
a jikin Halufa sai ya miƙe zumbur ya
tareshi cikin firgici yana mai cewa, "ya
kai sarkin jarumai me ya faru gare ka?"
Halufa yace, "ya shugabana ai lokacin
da na isa kurkukun sai na iske mayaƙa dubu biyu sun afkawa masu gadi har sun buɗe ɗakin da aka kulle fursunoninka sun fito dasu.
Koda nayi ƙoƙarina akan na hana su
tafiya da fursunoninka amma sai abu ya gagara don kasan sarkin yawa yafi
sarkin ƙarfi.
Da ƙyar ma na kuɓutar da kaina.
Kafin na dawo cikin gari na nemi mataimaka tuni sunyi mana nisa."
Koda jin wannan mummunan labari sai
zuciyar sarki bashkur tayi baƙiƙƙirin ya
cika da baƙin ciki kawai sai ta sallami
Halufa ya shiga tunani mai zurfi.
Daga can sai ya miƙe ya yi hawa ya
tafi can kurkukun da kansa.
Da zuwa ya iske masu gadin a kwankwance cikin jini magashiyan.
Da ƙyar ya samu mutum ɗaya wanda
bai raunata ba sosai.
Sarki ya durƙusa gabansa ya cakumi
wuyan rigarsa cikin tsawa yace, "wane ne ya zo yayi muku wannan ɗanyen aiki?"
Mai gadin ya bude baki da kyar da ƙyar yace "ai wani mutm ne shi kaɗai cikin shigar baƙaƙen kaya ya zo ya tarwatsamu ya fito da fursunoninka ya kuɓutar dasu."
Koda jin haka sai sarki bashkur yayi
jifa da mai gadin yace, "wannan zancen
banza ne duk faɗin ƙasar mahazus
babu wani sadauki mai irin wannan
jarumtarkar. Lallai ka tabbata maƙaryaci."
Kawai sai sarki bashkur ya zare takobi
ya fille kan wannan mai gadin. Nan take ya sake hawa dokinsa ya sukwane shi cikin fushi ya koma cikin gari.
Da zuwa bai zame ko'ina ba sai gidajen
manya mayankan garin yana tambayar su ko jarumi Halufa yazo neman taimakon su a cikin wannan daren bisa farmakin sumame da aka kaiwa kurkukunsa?
Kowa sai yace shi ba a neme shiba hasalima yanzu yake jin labarin abinda
ya faru.
Yayin sarki bashkur ya gaji da yawan
tambaya sai ya koma gd ya kwanta cikin tsananin baƙin ciki kashe gari da safe sarki bashkur ya tara dukkan 'yan
majalisar sa ya sanar dasu duk abinda
ya faru jiya da daddare kuma ya tabbatar musu da cewa shi kam yayi tunani kuma yayi bincike ya gano cewa ba kowanne ya aikata wannan mummunan aiki ba face jarumi Halufa.
Nan take ya kawo hujjojinsa guda biyu hujja ta farko itace babu wani sadauki a gaba ɗaya wannan nahiya wanda zai iya tarwatsa barade dubu face jarumi Halufa.
Hujja ta biyu itace halufa yayi masa
ƙaryar cewa ya dawo cikin gari ya nemi
taimakon wasu mayaƙan amma da aka tambaye su sai suka ce ba wanda ya
nemi taimakonsu.
Duk wannan bayani da sarki Bashakur
yake Halufa na zaune gefe guda yana
saurara kawai sai yayi shiru bai ce komai ba yana muzurai kawai.
Sarki bashkur ya dubi fadawansa yace to kunji laifin da Halufa ya aikata don haka sai ku yanke masa hukunci da kan ku.
Gaba ɗaya 'yan majalisar suka yi tsit
aka rasa wanda zai ce wani abu. Daga
can sai waziri yace, "ya sarkin sarakuna
ai ni a ganina wannan hukuncin ba zai yanku ba yanzu muna buƙatar muyi
zama na musamman."
Koda jin haka sai sarki yace, "Ƙwarai kuwa nima na amince da wannan shawara." Suma sauran 'yan majalisar suka amince akan hakan. Daga nan fada ta watse kowa ya kama gabansa. Sai da aka shafe kwana arba'in ana mahawara a majalisa akan irin hukuncin da za'a yankewa halufa.
A ƙarshe dai aka yanke masa hukunci
cewa an dakatar dashi daga kan matsayin sa na sarkin yaƙi har tsawon
shekara ashirin masu zuwa nan gaba.
Kuma dukiyarsa aka raba ta kaso biyu
aka ɗauki kaso guda aka raba wa masu gadin gidan kurkukun aka bar masa guda.
Daga wannan rana Halufa ya cire hankalinsa daga harkokin fada gaba
ɗaya ya maida nutsuwarsa akan ɗansa guda daya wanda suka haifa tare da matarsa Zuwaisa.
Wannan ɗa an rada masa suna NAZMIR.
Nazmir ya taso yaro mai kwarjini ƙwazo da basira ya zamana mahaifinsa na koyar dashi kyawawan ɗabi'u kuma yana koya masa juriya,jarumta da dabarun yaƙi.
Nazmir ya shaƙu sosai da iyayensa domin dare da rana yana tare dasu kuma ko kaɗan baya son abinda zai ɓata musu, domin ya kasance mai tsantsar biyayya a gare su. Yayin da Nazmir ya cika shekara sha huɗu sai ya zamo jarumin gaske kuma farin jininsa ya yawaita tsakanin al'umar garin, saboda irin kyawawan halayensa na tausayi da jin ƙai da kuma biyayya ga
na gaba dashi.
A ɓangaren jarumta kuwa sai da yabar
abin tarihi a kasar Duhamul domin shi
kaɗai yake shiga daji ya yi farautar manyan dabbobin dawa masu haɗari.
Sai dai aga yazo da gawarsu.
Tun yana jarraba jarumtarsa a tsakanin sa'anninsa har ta kai cewa yana tunkarar manyan baraden ƙasar ɗaya bayan ɗaya.
Duk wanda suka gwada yar ƙashi ko
tsagwaron yaƙi sai ya sami galaba akan sa.
Cikin ƙanƙanin lokaci labarin jarumi Nazmir ya yadu ko'ina a fadin ƙasar ya
zamana ana zuwa ganinsa daga gari-gari.
Shi kuwa Halufa da matarsa Zuwaisa suka kasance cikin tsananin farin ciki bisa wannan da Allah ya baiwa ɗan su.
Lokacin da nazmir ya cika shekara ashirin a duniya sai kyawunsa ya ƙara
bayyana a fili ƙarara.
Jarumtakarsa ta ninka ta da ya zamana bashi da abokai sai 'ya'yan sarautar ƙasar amma da yake shi mutum ne na mutane mai sauƙin kai bai yar da wasu abokansa ba su shida waɗanda suka taso tun yarinta.
Wandannan abokai gaba ɗaya 'ya'yan
talakawa ne.
Kuma dare da rana suna tare da Nazmir duk da cewa mahaifinsa yafi iyayensu arziki da ɗaukaka.
Daga cikinsu akwai Sharhil, Bagwan,
Hasuf, Iklam, Bardil da kuma Huzaik.
A cikin su gaba ɗaya babu wanda yafi shaƙuwa da Nazmir sama da Huzaik domin maƙotan juna suke,gidan su Huzaik yana kallon gidan su Nazmir. Babu abinda ke raba su face kwanciyar
baccí kai wani lokacin ma har musayar kwana suke,wato yau idan Nazmir ya kwana a gidan su Huzaik,kashe gari kuma sai Huzailk ya kwana a gidan su Nazmir. Dama mahaifin Huzaik yana zumunci sosai da Halufa. Sai dai tsoho ne tukuf don a ƙallah ya baiwa Halufa tazarar shekara goma sha đaya.
Mahaifiyar Huzaik ta rasu tun yana jariri, a halin yanzu Huzaik ba shi da kowa a duniya face wannan mahaifi na sa wanda ake kira Marnush, kuma ko ƙuda bai son ya taɓa lafiyar Marmush ɗin.
Huzaik yaro ne mai juriya da bajinta, amma ko kaɗan bai kama ƙafar jarumi Nazmir ba. Da yake an ce zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai. Shaƙuwar Nazmir da Huzaik ta sa shi ma Huzaik ɗin ya zama cikakken jarumi, kuma mara tsoro, domin duk sa'adda da Nazmir zai fita farauta jeji tare za su fita.
Yayin da Halufa ya fuskanci amincin da ke tsananin Namzir da abokansa guda shida ya kai ainun sai ya rinƙa koya musu yaƙi tare ko yaushe.
Haƙiƙa kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa,Nazmir ya ƙware wajen iya sarrafa takobi matuƙa gaya, kuma duk ya fisu jarumta da juriya shi kuma Huzaik ya ƙware ne akan iya harbin kibiya, sannan ya kasance magujin gaske. Komai gudun dabba yana iya ƙure mata gudu ya harbota. Idan kuwa ka kabi bayansa da gudu to in dai ya baka rata har abada ba za ka kamo shi ba.
Haka kuma yana da juriyar gudun don yana iya shafe sa'a goma yana gudu a cikin jeji ba tare da ya tsaya ya huta ba. Shi matsalarsa guda ɗaya ce indai babu ruwa a tare da shi ƙishirwa na galaɓaitar dashi nan da nan. Don haka wani lokacin ma yana cikin gudu yana shan ruwa abinsa.
Shi kuwa Sharhil ya ƙware ne a fagen iya faɗa da mashi. Shi kaɗai yana iya shiga tsakiyar mutum đari ya tarwatsa su da mashi guda, ko da kuwa za su rufar masa da sara da harbi don yana da zafin naman iya kaɗe harbin kibiya kuma ya kare saran, idan kuwa ya taɓe ya harba mashinsa in dai ya caki bishiya komai kaurinta sai ya nutse a cikinta.
Sharhil na iya cake mutumin da ke nesa da shi tsawon kamu ɗari uku daga inda yake tsaye.
Husuf, Iklam, Bagwan da Bardil kuwa
cikakkun mahaya doki ne,in dai suna kan doki komai yawan taron abokan gaba za su iya ratsawa ta cikinsu su yi ta sara da suka ba tare da an samu galaba a akan su ba. Haƙiƙa sun ƙware ainun akan yaƙin kan doki.
A ranar da Nazmir ya cika shekaru ashirin cif a duniya, sai Halufa ya shirya masa walima,a wannan rana Zuwaisa ta sha ɗawainiyar girke-girke.

Anan zamu dakata, sai wani karon idan Allah ya kaimu.
Fatan alheri

Matsatsubi 1
Typing:-Ahmad Munir Muhammad
Posting:-Ahmad Munir Muhammad
Part D

A baya mun tsaya inda;
"Gulzum ya ciza leɓensa cikin tsananin baƙin ciki yayi takaicin ƙarewar kibiyar akan nau'urar,domin inda akwai sauran kibiya da guda ɗayar ma ba ta tsira ba. Dama kibiyoyin guda biyar ne kacal kuma an yi amfani da guda ɗaya sa'adda aka yi gwaji akan ƙatuwar bishiyar nan ta kuka.

Koda aka ga babu sauran mutanen Galbasa sai mutane suka dawo cikin hayyacinsu. Nan da nan sarki Azbir ya sa aka tattare gawarwakin mutanen da aka shanye jininsu aka bunka musu wuta. A lokacin ne su Jafar suka farfaɗo daga doguwan suman da suka yi, suka ga sarki Azbir da jama'arsa sun taru a waje guda sunyi zugum-zugum suna kallom mutanen Galbasa guda huɗu waɗanda ke kwance kibiya ta tsire su har yanzu ba su daina kururuwa ba,kuma ba su fasa ƙoƙarin cire kibiyoyin ba, amma sun kasa.
Koda Jafar ya ga ana ƙona gawarwaki sai ya ruga gaban sarki Azbir yace, "Yakai wannan sarki ina dalilin ƙona waɗannan gawarwakin?"
Sarki Azbir yace, "Ashe ka manta da
bayanin da na yi muku tun a farko. Ai idan ba mu ƙone su ba,suma zasu zama irin mutanen Galbasa ne su zoƙe mana jini."
Azbir ya dubi Mashrila ya ce, "Yanzu ya zamu yi da waɗannan mutanen Galbasan waɗanda ba su mutu ba, kuma ba su kasance rayayyu ba, tun da ba za su iya tsinana komai ba?"
Mashrila ta yi ɗan jim, ta ce, "Babu abinda zamu iyayi akan su face sa ido domin zamu iya aikata kuskuren da zai janyo su tashi."
Azbir ya yi ajiyar zuciya, sannan ya sake duban Mashrila yana mai murmushi, yace, "Godiya gareki ya ma'abociyar hikima, haƙiƙa kin cece mu daga shairrin mutanen Galbasa. Yanzu zan bayar da umarni a shirya ƙasaitacciyar walimar girmamawa a gare ki,saboda wannan gagarumar nasara da kika kawo mana, kuma a wajen walimar ne zamu gabatar da babbar kyauta a gare ki da kuma ta Aljani Gulzum bisa ƙoƙarin da ya yi na harbo waɗannan mutanen Galbasa guda huɗu."
Koda jin haka sai mutane suka ɓarke da shewa. Cikin hanzari Jafar ya kama mumbarin ya hau can sama, sannan ya ɗaga hannu sama. Take wurin ya yi tsit.
"Ku yi sani cewa da ku da mu baƙin ku muna cikin mugun haɗari. Ku tuna cewa ɗaya daga cikin mutanen Galbasa ta tsere,kuma tabbas zata je ta sanar da Galbasa abinda ya faru ga 'yan uwanta.
Shin bakwa tsammanin cewa Galbasa zai yi gagarumin shiri ya taho da kansa ya zo ya ƙarar da mu gaba ɗaya,tun da ya san cewa in ya ƙyale nan gaba ma za'a iya yiwa jama'arsa ɓarna?"
Sa'adda Jafar ya zo nan a zancesa, sai hankalin kowa ya tashi aka fara kace-nace. Koda ganin haka sai sarki Azbir ya miƙe ya ce, "Yaku jama'ata haƙiƙa batun wannan yaro gaskiya ne,amma ina son kowa ya kwantar da hankalinsa domin kafin labari ya riski Galbasa sai nan da kwana bakwai. Kun ga ashe muna da isasshen lokaci na tunanin abin yi."
"A'a ranka ya daɗe bamu da wani lokaci lallai tun daga yanzu ya kamata mu fara shirye-shiryen tunkarar gagarumin yaƙin da ke gabanmu."
Koda jin haka sai sarki Azbir ya yi
murmushi ya dafa kafadar Jafar, ya ce,
"Yaro kar ka damu babu abin da zai faru."
Nan take aka fara kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, masu shirya walima kuwa suka tafi suka fara aiwatar da aikinsu. Jafar, Yelisa,Mashrila da Gulzum kowa suka yi zugum cikin tsananin damuwa. Ita kanta Mashrila da Gulzum kuwa waɗanda ya kamata su fara farin cikin walimar da aka shirya musu sai suka kasance masu taya su Jafar jimami.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar yayin da suka faɗa cikin wani gari shafi na goma sha biyu na KUNDIN TSATSUBA.
Al'amarin macen nan guda ɗaya wadda ta tsira daga harin kibiyar nan wadda Mashrila tasa aka ƙera, wato ɗaya daga cikin cikon mütum biyar na Galbasa, wacce ake kira Darzil sai ta ƙara ƙaimi,taci gaba da tafiya a sararin samaniya, har tsawon kwanaki bakwai sannan ta iso fadar Galbasa.
Sarki Galbasa na zaune bisa karagarsa ta mulki, fadawa sun kewayeshi, sai ga-Darzil ta faɗo gabansa tana haki da numfashi. Cikin fushi da zafin nama Galbasa ya cakumo gashin kanta ya kara

2 Comments On MATSATSUBI Book 1
avatar
armiyau

11 months ago

Reply

For fun

avatar
muhammad-musa-2

10 months ago

Reply

Akwai matstsubi

Please Login or Register in order to submit comment